Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

giɗen da take
tadubeni ta ce
"Wai kije in ji Ya SALEEM".

Ido nawaro nace "Ni". nafada tare da nuna kai na, kai ta gyaɗa a lamar Eh
ji nayi gaban kirjina ya yanke murya na rawa dan na mugun tsorata da jin irin wannan kiran bazatan na ce
"To ni me namishi Allah babu a bin da namishi".
Nan da nan hawaye yataru a idona kiris yarage suzubo.
murmushi Aunty Rafee'at tayi kana tace
"To in ban da ke dan ya kira ki sai yazamo wani laifin kika ai kata, kidai tashi kije kada kuma garin tsoro ki ɗaura laifin wa kanki yanzu gara dai kiyi sauri".
tuni ɗan guntun hawayen yazubo jin kalmar ta na karshe da sauri na mike. dariya Aunty Rafee'at tasaka tariko hannuna ta ce
"Ke da alla share hawayen ba komai fa wakai cewa yayi kizo kuma cikin sanyin murya ma yayi maganar".
Kai na gyaɗa namike nanufi side ɗin sa.

Tun daga kofar parlour'n sa nafara sallama, na daɗe ina tsaye ina ta rafka uban sallama, dan ban mance dokokin da ya gin da yamin a gidan Inna a Dass ba,
Jin shirun yayi yawa yasani tura kofar naɗan leko kaina, babu kowa cikin parlour'n sai na tura kofar gaba ɗaya tare da kuma yin sallama cikin ɗaga sauti,
Namma shiru babu motsin kowa, a hankali na taka na isa bakin kofar bedroom ɗin sa.

Cikin ɗaga murya nashiga yin sallama tare da ɗan bubbuga kofar a hankali,
daga cikin ɗakin a kace shigo, ɗan jim nayi sai kuma na tura kofar ina kusa kai na cikin ɗakin sai..............





*HAMDAH SHALELE FANS GROUP*
👇🏻
*Duk naji kora fin ku kuma duk ina sane da komai kubiyoni a nex page zakuji am soshin ku in Sha Allah*🥰




Mommyn Twins ce




*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*


*Free page*


My no 08034690723




🅿️12





*KAMAR YAD DA NACE IN SHA ALLAH ZAN BAKU DUK KANIN AM SOSHIN KU ƳAN HAMDAH SHALELE FANS GROUP TO GA AMSAR KU A GURGUJE*
👇🏻
*tabbas nayi alkawarin cewa book ɗin HAMDAH kyautace tun daga farkon sa har karshen sa a baya tun lokacin da nafa posting ɗin sa tun a january. tabbas Ni nafaɗi hakan*
*Sannan kuma yan zu dana dawo naci gaba da typing nasa nace na mai dashi na kuɗi.*
*Eh tabbas na janye alkawarin da na ɗauka na cewa ƙyauta zanyi shi a bisa da lili mai karfi kamar ha.*
👇🏻
*bazan zauna na bata lokacina na kashe duk wasu sab gogina nayi typing a cemin Thanks ko kuma a turamin sticker kaɗai ba👌🏻*
*Na kuɗi kuwa dole sai kinsa nairan ki kafin kisameshi ko kiyi min sharye da comments ko karkiyi bai dameni ba na fanshe da nairan ki*
*Abu na karshe shine idan kuka gyara naci gaba da ganin ruwan in gantaccen comments da sharhi mai rasa zuciya ba ku kaɗai ba har da sauran group's ɗin da nake posting a ciki bawai nace ba ƙwayi bane amma dai kukara Ni kuma nayi muku alkawari har idan nacigaba da ganin sharhi na musamman narantse duk wan da na karɓi kuɗin sa zan mai da mishi naci gaba da posting ƙyauta.*🤗






Sai naja na tsaya da sauri nan bakin kofar, hango Aunty Na'ima da Ya SALEEM ƙwance a kan gado, Na'ima na gefen sa manne da shi daga ita sai wani ɗan yalolon gyale da tayi ɗaurin kirji da shi.
Yana ƙwance yabata baya fuskarsa na kallon garu, single da boxes ne kaɗai a jikin sa yana ƙwance rike da waya yana latsawa.


da sauri na janye idanuna a kansu
nayi baya da hannuna nariko handlle ina kokarin boɗe kofar najiyo muryar ta,
"HAMDAH".
takira sunana juyowa nayi naɗan kalli in da take batare da na am sa ba,wani irin mika mai haɗe da hamma tayi tasuke voice ɗin ta taɗan ɗago tadube Ni cikin muryar gajiya ta ce
"Jeki girka ruwan zafi a kitchen ki kawo".
Da sauri na waro idanuna a kanta jin a bin da tafaɗa,
fuska ta yamutsa tana faɗin ko baki ji bane?".
ƙwayar idanuna najuya kan Ya SALEEM da ke ƙwance kamar baya gun sai faman latsa wayarsa yake, sai na mai da dubana gare ta na kaɗa kai tare da murguɗa mata baki najuya nayi waje.

Kitchen ɗin babban parlour nashiga na kunna Gas kana na cika ruwa cikin tukunya mai ɗan girma na ɗaura kan gas ɗin,
naja kujera na zauna ina zaman jiran ruwan yayi zafi.

Ina nan zaune har ruwan yayi zafi naɗau boket da na ganshi a cikin kitchen ɗin na juye ruwan a ciki naɗau ka nanufi side ɗin shi,
Sallama nayi daga bakin kofar bedroom ko da a ka amsa ban shiga ba sai da naɗan tsaya kaɗan kafin daga bisani na tura kofar.

Wannan karon yana zaune a kan kujera, ita kuma tananan in da na barta ɗazu tayi shame-shame,
Kokarin dire boket ɗin nake nan tsakiyar ɗakin tayi saurin cewa
"Shiga dashi cikin bayi mana".
A sannu nanufi kofar bayin ina shiga ciki bra da pant ɗin ta nafara ka karo da su yashe a kasan bayin,kafa nasaka na turesu gefe na isa na a je boket ɗin najuya nafita.

Koda na koma part ɗina a ƙawance na iske Aunty Rafee'at tana ganina tayi murmushi tare da faɗin
"Um mata masu miji daga tafi amsa kira sai a mance da ni har na fara tunanin ko in tafi ne".

Murmushi nayi na ce
"Ai girka ruwan da nayi ne yasa na daɗe ayya Aunty Rafee'at da tafiya zakiyi?".
Nayi maganar a marairaice,
tace
"Ruwa kuma?".na ce
"Eh ai Aunty Na'ima ce tace na girka musu ruwan wanka da ita da Ya SALEEM shi yasa ma na daɗe".


Da sauri tamike zaune tare da waro ido tace
"Mene girka musu ruwan wanka da ita da Ya SALEEM??!"..
kai na gyaɗa,
daɗa waro idonanun ta tayi da ƙyau da ƙyau tace
"Ke baki da hankali ne nikam ke HAMDAH wace iri ce ke, ke babu zu ciya ne a jikin ki, HAMDAH yaushe zakiyi hankali ne kam wai har yanzu bakisan ciwon kankiba baƙyajin wani a bu a cikin zuciyar ki ke,
Ke bakida kishine a rayuwar ki, girka musu ruwan wanka??!
sugama a bin da zasu yi kece ƴar girka ruwan wanka dan tsabar rashin mutun ci da rainin wayo babu ruwan zafi ne a bayi da har sai kinje kin girka musu a kitchen kin kawo musu,
dayake kema sha-sha-sha ce mara zuciya shine zaki biye musu.
to wlh bari na faɗa miki daga yau sai yau nakarajin makamancin irin haka sai ranki ya ɓaci. da ma a she har yanzu tana kan saki ai kin kina yima ta??"....

Kai na girgiza na ce
"Allah bana yi".
Ta ce
"Bagashi yanzu tasaki kinyi ba".
"Aunty Rafee'at yanzufa yana nan Allah in banyi ba duka na zai yi".
tace
"Ya kashe ki ya kashe kima, dan rainin wayo sai kace ƴar ai ki a ka kawo masa gida wlh Allah bazai barshi ba".

Haka tarika masifa Ni dai shiru nayi nazuba mata ido,
ta mike taja maya finta taɗau jakar ta, tace har idan ban gyara ba babu ruwan ta da Ni kuma bazata sake zuwa gida naba, haka tatafi da ɓacin rai.

Ko da tafita a farfajiyar gidan suka haɗu da Ya SALEEM ko kallon in da yake batayi ba tafice daga gidan,
koda cewa Ya SALEEM ɗin wanta ne wan da suka fita ciki ɗaya, amma sam bata jin daɗin rashin daraja wa da nuna rashin kulawar da yake yi kan HAMDAH.....★


★★★

Yau tun kafin a tashimu a makaranta hadari ya haɗu baki kirin,kan kace me ruwa yafara sauka, koda a ka tashe mu haka ɗalibai suka zauna cikin aji wasu kuma motocin gidan su suka zo suka ɗauke su.
Muna zaune da wasu ƴan a jin mu hira a ke amma ni gaba ɗaya hankali na da ido na nawaje kan ruwan da ake shekawa, a hankali namike nadubi
Bilkisu wacce sit ɗinmu ɗaya da ita nace
"Bilkisu Ni zan tafi ga jakata ki tafi min dashi gidan ku gobe sai kizo min dashi?".
Ido tawaro tace
"Acikin ruwan nan kidubafa ruwan karuwa yake daɗa yi ki bari mana a ɗauke tukun".


Mika mata jakar nayi ina faɗin
"Gashi Ni dai natafi bana son ruwan yajikamin littattafai ne" .
tana amsa najuya da sauri nafita dan gaba ɗaya na masu najini cikin ruwan.
Haka nafita a cikin makarantar naɗau hanyar gida a kafa,
ahankali nake tafiya ruwan na sauka a kai na,
har na iso kofar gida zuwa lokacin kam ruwan yafara sauki natura karamar kofar get nashi.

Ina isowa dai-dai parking space kamar an ce na waigo kuwa ina juyawa muka haɗa ido da shi, yana tsaye cikin parking space ɗin da a lama dawowarsa kenan,
wiki-wiki nayi da ido sai kuma nashiga wasa da ƴan yatsuna.

"Ke zonan!". yafaɗa cikin kakkausar murya,ɗan zabura nayi a hankali na tako ɗan nesa da shi na tsaya,
gefe da gefen sa ya waiga da alama a wani a bun yake nema,ido na waro ganin ya sunkuya yana kokari ɗaukar wani bulala da ke gefen sa,
Yaɗa go ya cafko hijabi na,
yaɗaga bulaliyar zai zabgamin, kai nashiga girgizawa cikin muryar tsoro da sanyin da naji yana shigana murya na rawa.

nace
"Dan Allah Ya SALEEM kayi hakuri".
Nafaɗa ina ja da baya
gaba ki ɗaya jikina ya ɗauki ɓari,
Cikin muryar faɗa yashiga faɗin
"Me yadawo da ke a cikin ruwan nan, me yasa baki bari an ɗauke ruwan kafin ki dawo ba, shine zaki biyo cikin ruwan nan ki da wo!".
yafaɗa cikin tsawa,
"Dan Allah Ya SALEEM kayihakuri wlh ruwan ne yaki ɗauke wa".
Saukar bulalan naji a baya na, kara nasake tare da tuɓe hijabin naruga a guje nayi ciki na barsa nan rike da hijabin a hannu.

Direct bayi nashige nasoma tuɓe uniform ɗin jikina da sai ɗiga yake da ruwa zuwa lokacin sosai nakejin sanyin nan nashiga na a gaggauce nayi wanka nafito ina saka kaya nahaye gado dan masifar sanyin nakeji har ina karkarwa,
Blanket naja na dukunkune ciki ina cigaba da rawar sanyi.

Har yamma ina ƙwance zuwa lokacin jikina yahaɗa zafi rau, ga masifar ciwon kai, ga hancina da ya toshe da ƙyar nake iya jan numfashi,
da ƙyar na lallaɓa nata shi naje kitchen nahaɗa zallar tea nazo nasha, sai sannan nasamu nayi sallah.

Ranar haka na ƙwana da masifaffen ciwon kai da toshewar hanci,
Washe gari kam ban iya zuwa makaranta ba haka nayita ƙwanciya, a wunin ranar ma.

Haka nashare satin nan bana zuwa makaranta ko parlour bana iya zuwa, in kaga naje to kitchen nawuce shima ɗin nakan wuni ban lekaba da zarar na zuba tea cikin flaks to sai washe gari nakuma shiga,
babu wani abincin kirki da nake ci zallar tea ne kawai nake iya sha...

Yau Monday ana tashin ɗalibai Bilkisu tanufo gidan su HAMDAH rike da jakanta ƙwanƙwasa kofar get tayi mai gadi yataso yabuɗe tare da liko kansa yana tanbayar wanene,
dai-dai lokacin motar Ya SALEEM ke danna hon ɗin fita daga gidan,
mai gadin yayi saurin cewa tashigo tashigo tatsaya nan gefe da get ɗin,
Shiko yayi saurin buɗe get ɗin a sannu ya iso in da suke kamar zai wuce sai kuma yatsaya ganin tanayiwa mai gadin magana da a lama dai tambaya take.

Zuge glass ɗin motar yayi kasa kana ya kalleta yace
"Gurin wa kika zo?".
Da sauri Bilkisu tace
"Ina yini".
Kai kawai yagyaɗa batare da ya amsa ba,
tace "Nazo gun HAMDAH ce nakawo mata jakarta ne, tun wancan satin tabani na aje mata kuma naga tun lokacin bata kara zuwa makaranta ba shine na kawo mata".

Mamaki mai haɗe da takaici ne yacika shi, wato makarantar ma bata zuwa tana nan jakar makarantar yana wani gun,sai yanzu yatuna ma ranar da ta dawo daga makaranta a cikin ruwa babu jakan a tare da ita.
tsaki yaja kana yaja motar sa yafice batare da yakuma bi ta kan Bilkisu'n ba.
Mai gadi ne yace tashiga ciki tananan yanuna mata hanyar part ɗin.

Ina zaune bakin gado rike da cup ɗin tea na zuba masa ido shima yanzu sam bana iya shan sa dan ƙwata-ƙwata ma yunwar bana jin ta, sai na wuni banci komai ba dan banajin sha'awar komai.
najuyo sallama a parlour a je cup ɗin nayi namike nanufi parlour'n.

Bilkisu nagani tsaye murmushi namata takaraso in da nake tana faɗin
"HAMDAH lafiya dai ƙwana biyu baƙya zuwa makaranta?".
Cikin murya ta da mura yagama toshesa nace
"Bana da lafiya ne".
tace
"Ayya sannu, dama jakar kine nakawo miki". Na am sa ina faɗin "Nagode dan Allah kisanar a makaranta bana da lafiya ne yasa bana zuwa".
Tace to tayimin sallama tatafi,nakoma ɗaki naƙwan ta.
Daren yau kasa bacci nayi dan ciwon yafina kullum haka kawai hawaye ke tsiyaya a idona, ga idon yayi ja sai nauyi da zugi yake min, ciwon kan ma haka sai nakeji kamar kan zai fashe numfashi kuwa sai da baki nake yinsa,ga masifaffen san yin da nake ji har cikin kashina.
Kuka na saka ina kiran Inna da Ummi na, haka nata kuka sai wajen asuba kafin nasamu bacci yaɗau keni,
Na ɗan jima kuwa ina baccin sai wajen karfe 10 kafin na farka, sai dai har lokacin babu a bin da yaragu daga ciwon da nakeji.
na lallaɓa
Naje nayi wanka da ruwa mai zafi, nazura doguwar riga mara nauyi mai gajeren hannu na dawo kan gadon nakuma ƙwanciya na dukun kune cikin blanket, narufe ida nuna bawai kodun inajin bacci ba sai dun kai na da idona da nake ji kamar zasu cire.



"HAMDAH! HAMDAH!! HAMDAH!!!".
Muryar Ya SALEEM najiyo daga bakin kofa yana kiran sunana,rumtse idanunna nayi da karfi jin yan da yake ƙwaɗa min kiran cikin tsawa.
Yaturo kofar da karfi yashigo, kaina na da ɗa dannashi sosai jikin pillow jin yana daɗa saramin da karfi-karfi,a fusace yanufo bakin gadon yana faɗin
"Zaman me kike yi a gidan da sati guda bakije makaranta ba".
Kankame ida nuna na daɗa yi da karfe,
yakai hannu yafizgo blanket ɗin Dana dukun kune ciki, yafincuko ni na mike zaune yaɗaga hannu zai kai min bugu,na buɗe ida nuna a wahalce cikin disashshiyar muya ta da mura yagama toshewa,

Nace
"Wayyo Allah na wayyo kai na dan Allah Ya SALEEM kayi hakuri".
Nayi maganar a wahalce yayin da hawaye ke gangaro wa kan fuskata,
yanayin yadda yaji nayi maganar ne yasa shi sauke hannun sa da ya ɗago zai kai min bugu da shi,
Ido yaɗan tsuramin,
Nan take yafahim ci cewa murace tayimin mugun kamu.
Niko cikin muryar kuka da baya fita sosai ma naci gaba da faɗin
"Wayyo Inna Ummi na, kai na zai cire".

"Rufamin baki da wani ne kekai ki cikin ruwa?
ai bakiga komai ba in dai junan ki wasan ruwane".
Ni dai ida nuna na mai da na rufe dan banajin zan iya barin su a buɗe sabo da a zabar ciwon da nake ji, sai hawayen da yake cigaba da sauka a cikin idon.
haka yayi tayimin faɗa sai dai wannan karon muryar sa tayi kasa bakamar yan da yafara yimin farkon shigo warsa ɗakin ba.
Daga bisani yajuya yafita, nakoma na jingina da jikin gado.


Fitarsa da kamar minti 30 yadawo jin shigo warsa yasani buɗe idanuna, yatako in da nake lai dar da ke rike a hannunsa ya aje saman bedside,yaɗan sun kuyo yabuɗe laidar yafidda magungunan da suke ciki yaɓɓare, ya buɗe gorar ruwa wanda duk da shi yazo.
yaɗa go yamika min gorar ruwan na am sa kana yamiko min magani,
Ido na tsurawa maganin da ke hannun sa,nan take naji zuciya ta yafara tashi,
cikin rawar murya nace
"Nawarke ma ba sai nasha maganin ba".
Wani kallo yawatsa min cikin tamke fuska yace
"Zaki karɓa ne ko ya".


rau-rau da ido nayi sai ga hawaye sharr.
Bana son magani ko kaɗan ko ganin sa idan nayi sai naji zuciya na yatashi, idan bana da lafiya sai Inna tayi kamar tanayi kafin nasha magani, idan kuma Ya SALEEM ɗin yaje Dass dai-dai lokacin ina ciwon to shi take sashi yabani maganin, dan dai tasan in ni da ita ne kam komi masifarta bashi zaisa Ni nasha ba kona sha kuma sai nadawo dashi dan sai nayi a mansa. danni dana sha maganin na gwammaci nazauna haka har ciwon yagama gaukar sa nawarke.


Nabuɗe tafin hannuna yazuba min maganin ciki, narika juyasu cikin hannuna ina cigaba da masar ƙwalla,
Shiko fuska yadaɗa sukewa ya tsare ni da ido,
A hankali na ɗago hannuna mai rike da gogar ruwan na kai baki na kurɓi ruwan,narufe idanuna da karfi kana nawasa maganin a baki na haɗiye da ƙyar yawuce.

A kiɗi me nashiga yunkurin mikewa har sai da gorar ruwan da ke hannuna yafaɗi kasa, wani irin juyawa naji zuciyata keyi,
Nazuro kafafuna kasa kasan cewar yana tsaye a gaba nane hakan yasa na aje kafafuna daf da nashi.
Na mike tsaye cikin kiɗi ma narufe bakina da tafin hannuna, yayin da idanuna ke rufe gam, kafata ɗaya na yi gaba da shi don so nake natafi bayi nayi a man da naji ke kokarin fitowa, sai ji nayi nayi karo da shi,da sauri na ware ida nuna kan shinfi ɗaɗɗin kirjin sa da na buga goshina da shi,
Cikin tsananin tashin hankalin jin yan da aman keta kokarin tahowa nasaka tafin hannuna nashiga ture kirjinsa.

Ɗago hannunsa yayi yaɗaura kan hannuna dake kan kirjin sa yarike, sannan yarika tafiya da hannunsa a kan hannuna har zuwa kan kafaɗa ta sai ya ruko kafaɗata da ƙyau,
ɗaya hannunsa kuwa hannuna da na toshe bakina yazareshi kan bakina sai yarike gefen kafaɗata na wannan hannun sai ya mai da ni ya zaunar da ni bakin gadon.
kai narika juyawa inata yunkurin mikewar sai dai nakasa sabo da har lokacin yana rike da kafaɗata.


Yago hannu sa ɗaya yazura cikin aljuhun tattausar jallabiyar jikinsa, wani sweet yaciro namusamman yab'are yamika hannu zuwa bakina da sauri nabud'e bakin yacusamin shi cikin Baki, da sauri narufe bakin Jin mintin yashiga cikin bakina, wani irin daddaɗan kamshi da daɗi su suka ziyarci cikin bakina, lumshe idanuna nayi inajin yadda kamshin mintin da daɗin sa kedaɗa baibaye ne, daɗa manna harshena nayi sosai da sweet ɗin, nashiga tsotsar sa a hankali narikajin Aman na lafawa sai Kuma nashiga sauke numfashi ahankali-ahankali narikajin zuciyata na kwanciya,
Tsit nayi Ina cigaba da tsotsar mintin sai na daɗa lumshe idanuna sosai.

Ido yakurawa kyakkyawar fuskarta wan da ya kawato da man Yan idanuwa da bakin gashin gira Kamar an zana suna kwance lup dasu juya idanunsa yy zuwa Kan dogon hancin ta Wanda da yawan mutane sukan ce hancinsu iri d'aya ne haka hasken fatarsu,
Taɓe Baki yayi aransa yace "ni Banga wani kamaba wannan hancin ne irin nawa".
Kan lips in ta yakuma sauke idanunsa Ido yatsurawa Kan lips ɗin yanda take motsasu.


"Sakemin yatsa idan ba cinyeshi zakiyiba"

Da sauri nabud'e ida nuna nazubashi Kan fuskarsa, kwayar idanunsa yajuya yasaukeshi Kan lips Ina ɗan girgiza Kai yayi tare dayimin nuni da idanunsa kan lip ɗina Yana fad'in "sakemin".
Ido naware sosai cikeda mamakin ganin yatsarsa cikin bakina.

"Kenan da yatsar sa nahada da sweet in nayita tsosa?".
Nayi maganar a kasan zuciyata,
Wani kallo yayi min nakasan Ido a hankali najuya harshena naturo yatsar tasa waje nayi kasa da kaina tareda haɗiye miyau in da yataro a bakina, tsayuwarsa yagyara kana yajuya yasoma tafiya yana faɗin.
"Kici a binci yanzun nan".

Yana fita ƙwanci yata na gyara bajimawa ko bacci ya ɗauke Ni.

Na daɗe sosai ina bacci sakamakon maganin muran da nasha, koda na farka bakaɗan ba naji daɗin jikina har na iya cin Indomie dana girka.
Bayan sallar Isha Ina zaune yashigo da sallama na ɗago tare da amsa sallamar,
wayace kare a kunnen sa da a lama dai waya yake, yatako ya iso gaba na sai ya..........




*Kada ku mance sharhin ku shine sadakin book ɗin nan🤗*




Mommyn Twins ce




*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*


*Free page*


My no 08034690723




🅿️13







Sai ya sauke wayar ya ɗan dubeni kana ya ce
"Ina maganin?". yayi maganar a takai ce.
kallon saman bedside nayi nace
"Gashi can".
nafada muryata can ciki dan jin a bun da ya am bata,sayuwar sa ya gyara ganin hakan yasani mika hannu naɗau laidar maganin,nashiga buɗe laidar tuni ida nuna suka cika da ƙwalla,
ciro magungunan nayi a cikin laidar na siyaye ruwa a cikin cup, naɓare ƙwayoyin kamar yadda naga yayi ɗazu, narika juya su cikin hannuna,
ganin ya ɗago hannunsa yana duban a gogon da ke ɗaure a hannunsa,sai ji nayi hawayen da suka taru cikin idona sun fara siyaya sai nayi hanzarin kai maganin baki na nahaɗiye da ƙyar, baki yataɓe kana yamiko min sweet ɗin da ɗazu yabani na am sa da sauri najefa shi cikin bakina tare da lumshe idanuna nasoma tsotsar mintin.

Karar buɗe kofa da naji yasane buɗe ido bayan sa na hango yana fita daga ɗakin,
A sannu nakoma na ƙwanta da baya naci gaba da tsotsar mintin har sai da naji zuciya ta ta ƙwanta.

Yau kwana uku kullum sau uku yake zuwa a rana yasani na sha magani yana tsaye har sai nasha, ina haɗiyewa kuwa zai bani sweet ɗin nan, da zaran na sa shi cikin bakina sai naji a man ya koma......
Yanzu kam alhmdllh naji sauki sosoi sai dai ɗan abin da ba a rasaba,
Zuwa yanzu naci gaba da tafiya makaranta na.....★


Rayuwa kenan inji masu iya magana sukace rayuwa sirri. ƙwanta tashi a ran mai rai.
Haka naci gaba da gudanar da rayuwa ta cikin gidan, a haka lokaci yayita tafiya ƙwanaki sukayi taja,
Yau kimanin shekara ta ★3★ a cikin gidan.
Abubuwa da dama sun faru masu daɗi da a kasin hakan.

Yanzu ina a jin karshe a secondary. kamar yadda nakai wannan matakin haka sassan kijina,
Idan nakalli kai na har mamakin kaina da kaina nake,Ni kaina nasan nakara girma a cikin ɗan waɗan nan shekarun,duk wasu halitta najikina sun daɗa baiyana,Ni kaina nakanyi mamakin yan da albarkatun jikina suka daɗa bai yano da kansu a fili, sun ciko sun yi tup-tup da su.
Rayuwata nake gudanarwa Ni kaɗai ɗina a cikin sashin da yake mallakin zamata a cikin gidan, sai nafi wata 5 bansa masu gidan a idona ba.sai dai kayan a binci baya yanke wa duk karshen wata Ya SALEEM yanasa a kawo ko, ayita jibgesu cikin stor dan nidai wasu kayakin abincin ma ban san iyakan suba, dan banayin rabin amfani da kayakin za a jibgo wasu,in dai naga gun zai cike idan a ka kawo sai nasa a koma dasu.....★


Da sauri nafito rike da mayafi da jakata sauri nake naje gidan Aunty Jaleela takara haihuwa yau suna, nanufi waje a farfajiyar gidan na karasa saka mayafin sabo da sabar saurin da nake,
Ina fita na natari mai adai-dai zuwa gidan Aunty Jaleela dake ɗorawan dillalai,
Muna isa nabiya mai a dai-daita nawuce cikin gidan da sauri,tun daga get nake jiyo hayaniyan yan'uwa kara sauri na nayi nashiga cikin gidan,a parlour na tadda su Mamie da Aunty Hafsat matar Uncle Sadiq kanin Ummi da Umma Habiba ƴar autar su Ummi da sauran ƴan uwa da abokan arziki.

Da sauri nakaraso in da suke cike da murnar ganin su cikin muryar dariya nace
"Laa Aunty Hafsat Umma Habiba yaushe kuka zo?".
nafaɗa tare da zama hannun kujeran da suke kai,
murmushi Umma Habiba tayi kana tace
"Ɗiyata jiya mukazo inata tanbayar ki a kace bakizo ba kina gidan ki".
gefen da Mamie ke zaune nakallo nace
"Ina yini Mamie".
murmushi tayi tana faɗin "Lafiya Lau HAMDAH yagidan".
nace "Lafiya kalau".

murmushi mai sauti nayi jin Aunty Hafsat tana cewa "Kaga ƴargidan Inna girma yazo babu tsalle-tsalle".
dariya Umma Habiba da Mamie sukayi kana Umma Habiba tace
"Ai kam ɗiyata an girma yau she zaki zo mana Maiduguri".
nace
"Sai Alhj Dikko yamutu zanzo". dundu Umma Habiba tasake min a baya tana faɗin "Baza muga mutuwar shi yanzu ba dan wata naki".
mikewa nayi da gudu nayi cikin bedroom ɗin Aunty Jaleela ina dariya da faɗin "Akan wannan tsohon Umma zaki karya min baya dan muzama iri ɗaya da shi".

Acikin bedroom ɗin Aunty Rafee'at ce da Aunty Jaleela da kawayen su tam ciki, ina karaso wa ciki na saɓi jariri yar da

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment