Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bace yanzu".
"Ya SALEEM yaushe zaka dawo?".
ɗan shiru yayi kana a hankali ya furta
"Bana kasar kinaso na dawo ne?".
shiru nayi,kuma jefo min tanbayar yayi
"Kinaso na dawo?".
nan ma shirun na kuma ina wasa da ƴan yatsuna,
" *HAMDAHHH*"
yakira sunana cikin wani irin sauti mai rasa ƙwaƙwalwa da shiga jiki,wannan shine karo na farko da nataɓa ji Ya SALEEM yakira sunana haka kawai,
rausayar da kai nayi tare da kaɗa ƙwayar idona nace
"Na'am". numfashi ya furzar,a hankali na ciro wayar jin alamar ya katse kiran,bin wayar nayi da kallo tare da sauke numfashi....


na mike a hankali nashiga bayi,
da damuwa nashiga tuɓe kayan jikina dan son kimsa jikina karo na biyu a safiyar nan,ba shakka zuwa yanzu nafara tsorata da lamarin jinin nan,iya adadin kwanakin al'ada ta kwana huɗu ne a na biyar kuma zanyi sarki ban taɓa kai wa ko da kwana shida ba sai gashi wannan karo har kimanin sati biyu,
nafara damuwa ganin kwanaki suna ta ja jinin kuma bai tsaya ba.
wanka nakuma nafito na kimsa cikin riga da zani na atamfa,
ina gama shirin na mike dan yau ina son zuwa gida, na yafa gyale naɗau ƴar karamar side bag da waya ta nanufi waje na kulle kofar side ɗina gaba ɗaya kana nafita a gidan,na tare mai a dai-dai zuwa gidan mu...

Koda muka isa na sauka nabiya mai adaidai kuɗin sa na shiga cikin gidan direct part ɗin Ummi na nawuce,da sallama nashiga parlour'n cike da ɗokin ganin ta.
Aunty Jaleela Fauzan Nusaiba Fadil babban yaron Aunty Jaleela Ummi duk suna zaune cikin parlour'n kasan cewar yau Saturday.
da gudu Fauzan Nusaiba Fadil suka taso suka rungume ni suna ihun murna,
Nima rungume su nayi cike da son yaran kana na janyosu muka karasa cikin parlour'n,
Muka zube saman kujera kusa da Ummi,masawa gefe Ummi tayi tana faɗin
"Jimin sha-shan ci zasu karya min kafa". fuska ɗauke da dariya nadube ta ina faɗin
"Kai Ummi karya kafa kuma".
Aunty Jaleela dake baiwa Feedrah nono ta harareni tare da faɗin
"Ai HAMDAH hankalin ta ɗaya dasu babu girma sai na jiki".
baki na murguɗa mata naruko hannun Ummi nace
"To ina Ummi na ne".
tace "To sai ki karya ta ki huta".
ido na waro nace
"Cap bakin ki ya tsari kuntun a yaba".
Ummi kam ido taɗan tsuramin kamar mai son gano wani abu,
sake hannunta nayi na mike ina faɗin "Fauzan Nusaiba Fadil kuzo muje sashin Mamie".
naɗau Feedrah data saki nono tana ta juyo kai kamar mai jin abun da ake faɗa na saɓe ta a kafaɗa muka nufi kofa.
Aunty Jaleela tace
"Ai gara kuyi tacan daga zuwan ki kincike mana guri da surutu".
gyara rukon Feedrah nayi ina faɗin
"Ai zan dawo ma"....

A parlour muka iske Mamie zaune,ta ɗago da murmushi tana amsa sallamar mu,hannu ta miko tana faɗin
"Kawo min kishiyar nan nan na rankwashi kanta ɗazu sun shigo da ma ashe baccin gangan take".
dariya nayi ina zama gefen ta tare da gaishe ta,ta amsa fuska ɗauke da murmushi ta karɓi Feedrah tana faɗin
"Zo nan mai gajeren hanci".
"Kai Mamie mai dogon hanci dai, tazo nunawa Abbu kwalliyar tane".
Mamie tayi dariya tana faɗin
"To ai sai ta koma babu abun da zaiyi da kwalliyar tata".
Da gudu Nusaiba ta mike tanufi ɗakin ta tana faɗin
"Bari naje na ɗauko pawda a kara shafa mata".
nace
"Yauwa yi sauri".
har ta isa kofar ɗakin ta sai ta juya tanufi kofar bedroom ɗin Mamie tana faɗin
"Bari na ɗauko na Mamie a shafa mata".
dariya mukayi dukan mu ta shige ɗakin tafito ɗauke da pawda, karɓe pawdar Mamie tayi tana faɗin
"Ai ba kalar ta bane wannan"....
Mamie tarika zolayar Feedrah tana cilla ta sai dariya take ganin ana ta yi mata abun da take so wato rawa da cilla ta sama.
Muna zaune har aka kira sallar azahar,
Mamie tace Fauzan ya kama Fadil sutafi masallaci dake nan kofar gida,
ta mikawa Nusaiba Feedrah tace
"Rike ta ke HAMDAH kije kiyi sallah sai ki dawo ki riketa sai taje tayi itama".
tafaɗa tana mikewa,
mika hannu nayi na amshi yarinyar nace
"Je kiyi sallar".
nafaɗa ina duban Nusaiba,
dubana Mamie tayi tare da faɗin
"A'a je kifara yi ke sai kizo kici abin ci".
kasa nayi da kaina tare da ɗan murza yatsuna nace
"Ni nayi". ido Mamie ta ɗan tsuramin na lura tun shigo wata irin wannan kallon take ta bina da shi irin dai kallon da Ummi tayi min ɗazu, kai ta jinjina kana tace
"Ai ho to shikenan".
tafaɗa
ɗan jim tayi idanunta a kaina kana tace
"Amma dai baki da lafiya ko? naga kin ɗan zuba kaɗan".
Kai na girgiza alamar a'a
juyawa tayi bata kuma cewa komai ba tashige ɗaki tana faɗin
"Je ki zubo abinci a kitchen".
"To. nace,
A file na furta
"Ba dole na rame ba jinin jikina na ta kan tsiyaye wa, dan dai wannan jini bana al'ada bane".
numfashi na sauke ba shakka ni kaina inajin ƴar ramar da nayi har da haske ma kuwa sai dai nasan ba komai bane yasani yin rama da hasken face wannan jinin dake zuba babu ko kakkautawar,a ƴan kwanakin kuma zazzaɓin dare na yawan damuna sai dai duk na alakanta hakan da wannan zuban jininne.
yau ma nayi niyyar yin wanka naci gaba da ibada na dan dai nasan wannan jinin shine jinin ciwon da ake faɗan nan kuma nasan shi baya hana yin ibadar Allah...
Bayan naci abincin sashin Ummi muka koma muka yada zangon mu a can sai yamma barista Aliyu mijin Aunty Jaleela yaza ya ɗauke su.
tun a lokacin Ummi tace nima na shirya natafi nace mata ni kwana zanyi, faɗa takama yimin wai dan Ya SALEEM baya gari shiya nace zan kwana wata mace ne naga take yin haka kowa ma in mijinsa yayi tafiya zama yake a ɗakinsa batare da yaje ko ina ba.
ni dai ɗaki na shige naje na sarkake jikina nagabatar da sallar magriba da yanzu a ka kira......

Ina kwance a kan gadon Ummi kiran Ya SALEEM yashigo wayata,a hankali naɗaga kiran tare da yin sallama,shiru yayi bai amsa sallamar ba bai kuma yi magana ba har na fara tunanin ko kiran ya yanke ne, ina kokarin ciro wayar najiyo muryarsa
"Wa kika tanbaya kika fito *HAMDAHHH*".
shiru nayi ina daɗa gyara rukon wayar a kunnena,
a hankali yakuma furta
"Dare yayi yanzu kikwana amma gobe kikoma gida kada ki kuma fita sai da sanina in ba School zaki ba".
da sauri nace "To".
jin yace nakwana koma ya akayi yasan nazo oho....

Washegari da yamma yakirani yace nakoma gida sabo da gobe Monday a kwai School.
ganin bana da niyyar tafiya yasa Ummi korani dan a gaban ta mukayi wayan tasa direba ya mai doni gida....



★★★★
*After 2 week*
★★★★



Hakan yayi dai-dai da watan Ya SALEEM 1 kenan da tafiya,har kuma yau wannan jinin nanan nazuba min sai dai bakamar na sauran kwanakin da suka wuce ba, yanzu nakan wuni jinin bai zuba ba sai idan dare yayi sai ya dawo wani sa'in ma har na kwanta bacci bazan ganshi ba sai da asuba idan natashi yin Sallah sai naga ɗigonsa a pant ɗina,
zazzaɓin daren kuwa sai ma karuwan da yake daɗayi,yanzu ba dare kaɗai ba har da rana yana yimin,
Yau tun a makaranta nake jin wani mugun sanyi har jikina na rawa haka na dawo gida da zazzaɓi mai zafi a jikina,
da kyar na iya cire uniform nasa wani doguwar riga mara nauyi na haye gado,duk yanayin juyawar zafi irin na Bauchi da aka fara amma Ni ji nake kafar acikin fridge nake tsabar sanyi.

Wani irin sanyi nake jinsa har cikin soka da kashin jikina, har dare ina rufe ruf,
ina jin wayata nata ringing tun ɗazu amma bana jin zan iya tashi bare har na iya ɗau kar kiran,
dakyar na iya miko hannuna in da nafi tunanin wayar tana gun na laluɓo ta na ɗauka.
koda na ɗaga kiran ban iya kai wayar kunnena ba sai aje shi nayi daf da fuskata, can najiyo muryar sa yana faɗin
"Hello *HAMDAHHH*".
sai da ya nanata kalmar har sau uku.
idanuna na rumtse sai ga hawaye sharr cikin tsananin jin azabar ciwon da nake ciki murya na rawa nace
"Na..na.na'am".
sai kuma na fashe da kuka
da sauri yace
"Ke menene me ya faru??!".
kukan na cigaba da yi kuka irin na wan da yake cikin jin azabar ciwo,
cikin muryar damuwa sosai yaci gaba da faɗin
"Meyasa me ki menene??!".
yafaɗa cikin ɗan ɗaga sauti,
ida nuna na rumtse da karfi jin jiri na fizga ta
a wahalce nace
"Sanyi sanyi sanyi nakeji Ya SALEEM wayyo Allah na".
"Ya salam!".
yafurta cikin ɗaga sauti.
kife fuskata jikin pillow nayi na daɗa dukunkune jikina cikin blanket ina fidda numfashi'n wahala,ina jiyo muryarsa yana ta magana sai dai bana fahimtar me yake faɗa yanzu...
ranar haka nakwana cikin matsanancin zazzaɓi kamar zai buɗa min ƙwaƙwalwa,
washegari da misalin karfe 9 inanan kwance kamar jiya dan ko sallar asuba ban iya tashi nayi ba..
da karfe a ka turo kofar cikin zafin nama nake jin taku cikin ɗakin sai kuma wani sassanyan kamshin dake daɗa matsoni,
idanuna na rumtse a wahalce,cike da tsoron jin takun mutum cikin ɗakin kukan azaba haɗe da tsoro na sake, a bakin gadon a ka zauna sai naji ana Jan blanket ɗin da na tukuikuye ciki,
kuka nakuma sakewa duk da sautin muryata baya fita sosai nakuma kankame idanuna sosai.
da sauri a ka janye blanket ɗin sai saukar hannun mutum naji a kan kirjina zuwa gefen wuyana,
cikin sananin tashin hankali nashiga yunkurin mikewa duk da nasan abune mai wuya na iya mikewan.
"Subhanallah ya akayi haka zafin jikin yayi yawa!".
muryar sa ce ta doki kunnena da mamaki tsoro da wahalar da nake ciki nashiga buɗe idanuna na sauke idanuna akansa,
Kyakkyafta idon nayi dan son tan-tan ce shi ɗin ne koko gizo ne.

Shi ko cikin hanzari yashiga ɓalle boturan rigar sa yazame rigar a jikin sa tare da cire singlet ɗin ciki, da sauri yakai hannu yaɗa go ni gaba ɗaya daga kasa yariko doguwar rigar dake jikina yazare shi ta sama rigar ce kaɗai a jikina babu ko bra sai pant kawai, cikin hanzari ya haɗani da jikinsa ya rungume ni sosai ya cusani cikin jikinsa,
wani irin numfashi na sauke jin ɗumin jikin sa,sai na daɗa lafewa sosai cikin jikin nasa ina sauke numfashin wahala,
shi ko shafa kaina zuwa baya na yarika yi,
mun jima sosai a haka kana a hankali yaciro ni cikin jikin sa yakwantar da ni tare da jan blanket yarufe ni, da ɗan sauri yamike yashiga bayi zuwa can yafito ya ɗaukeni yanufi bathroom ɗin dani yadire Ni cikin bathtub da ya cika ruwa cikin sa a hankali na lumshe idanuna ina mai jin daɗin ruwan ɗumin da ya saka ni ciki,a hankali narika sauke numfashi akai-akai,zuwa can yaɗau sabulu yashiga wanke min jikina ko ta ina ya wankeni tsaf kana yanaɗoni cikin towel yafito dani,har lokacin idanuna a lumshe suke dan nagaza buɗe su jin wani irin jirin dake fizga ta.

A kan gado ya ajeni ya isa gaban wardrobe yaciro doguwar riga mara nauyi da pant yazo ya saka min, kana ya ɗau rigarsa daya tuɓe yasa ka.
yafita zuwa can yadawo ɗauke da cup ɗin tea Mai kauri ya ɗago ni ya tallafo ni jikin sa yakai cup ɗin bakina a hankali cikin muryar tausaya wa yace
"Buɗe baki kisha".
A hankali nabuɗe bakina yadaɗa manna min cup ɗin nakama shan tea ɗin a hankali kurɓa ɗaya zuwa huɗu nayi da sauri na kawar da kaina jin tea ɗin kamar baya wucewa a wuya yake tsayuwa yana shirin dawowa.
ganin yan da nake jujjuya kai yasashi a je cup ɗin da sauri
ya mike tsaya yaje ya ciro hijabi cikin wardrobe yazo yazura min,
kana yanaɗe hannun rigarsa yasun kuce ni yanufi kofa da ni,
a hankali na buɗe idanuna kan fuskarsa sai kuma na mai da da sauri na rufe saboda jiri,cikin disashshiyar muryar wahala nace
"Ya SALEEM Ina zamuje?".
"Asibiti zamu".
yafaɗa yana daɗa gyara rukon da yayi min.

"A'a Ya SALEEM kar muje zasu bani magani"
"A wannan yanayin da kike ciki me yafi dacewa da ke in ba maganin ba".
kaina na daɗa mai dashi kan kirjinsa ban kuma cewa komai ba dan maganar da nayi yanzun ma cikin karfin hali na yishi amma ni kaɗai nasan irin azabar ciwon da nakeji.
Yana isa gun mota yabuɗe gefen mai zaman banza yasakani ciki kana yagyara min zama yaɗan kwantar da sit ɗin ta yadda zanyi daɗin zama na kwantar da kaina jikin sit ɗin,ya mai da marfin yarufe kana da sauri yazaga gefen direver yashiga ya tada motar mai gadi yayi hanzarin buɗe get yasakai yafita.
yana tukin ne amma rabin hankalin sa nakai na dan duk bayan dakika sai yajuyo ya kalleni,
Hannunsa ɗaya yaɗa go yayin da ɗaya hannun sa ke kan sitiyarin motar,
a hankali yasauke hannun kan gefen fuskata yaɗan shafo shi,
cikin yanayin sa yamosa lips ɗin sa
"Idon ma ciwon yake ne uhum *HAMDAHHH*"
kai na ɗan girgiza a hankali nace
"Ina jin jiri ne in na buɗe sai na rika ganin guri yana juya min".
iska ya furzar daga cikin bakinsa tare da faɗin
"Kin bar ciwo yayi yawa a jikin ki meyasa baki faɗa min ba".
shiru nayi,kai na yaɗan janyo zuwa kafaɗar shi sai nazamo jikin sa nakwanta gefen jikinsa a haka muka isa asibitin.
ya gyara fakin a cikin gunrin da aka tana da domin adana motoci yafita yazaga gefen da nake yabuɗe,
a hankali na ɗan buɗe idanuna jin yana kokarin ɗaukata,a hankali nace "Kabari zan tafi da kaina".
nafaɗi hakan ne saboda ganin mutanen da suke cike a harabar asibitin,hannuna yariko yana faɗin
"Ok to sauko".
yafaɗa tare da taimaka min nazuro kafafuna kasa namike tsaye, gefe na ya dawo ya tallafo ni gefen jikin sa a sannu nashiga ɗaga kafa ta,wani irin jiri ne ya fizgeni sai wani duhu ya gilma min natafi luuu zan faɗi sai yayi saurin rukoni ya mai dani jikinsa,tundaga lokacin ban kuma sanin abun da ke faruwaba.....★



*After 10hr*

Sai a lokacin na farka daga doguwar sumar danayi,sai dai idanuna suna lumshe,muryoyin mutane da dama narikaji sama-sama,can nasinkayo muryar Abbu cikin damuwa yake faɗin
"Faruq har yanzu fa bata farfaɗo ba gaskiya a sake duba ta sosai ace mutum tun safe har dare yana kwance babu motsi tun ɗan motsin da tayi ɗazu da ake ta jan jinin ta bata kuma motsawa ba har yanzu sai uban ruwa da allurai da ake ta narka mata, in ma yaya ne muyi mai yiwuwa kawai yau ɗin nan mubar kasar nan da ita".
sautin murmushin Dr Faruq najiyo tare da faɗin
"Ai Abbu ta farfaɗo tun ɗazu abun da yasa bazaku gane farfaɗo war nataba a cikin bacci ne tafar kan, yanzu kam bacci take kuma wannan baccin da take shine nasarar da muke hangowa na samin lafiyar ta, in Sha Allah idan ta farka daga baccin da take zataji sauƙin jikin nata sosai".
Abbu yace
"To Allah yasa a dace". kaf gurin suka amsa da ameeeen.
hannuna da naji yayi min nauyi sosai nashiga kokarin ɗagoshi a hankali nashiga buɗe idanuna har na ware shi tarrr saman pop'n room ɗin,muryar Inna naji a kusa dani tana faɗin
"Idris Shu'aibu gashi tana motsi da hannunta sosai yanzu, la tama buɗe ido".
tafaɗa tana daɗa rike hannuna da nake ta kokarin ɗagashi, a hankali nashiga juya ƙwayar idanuna cikin ɗakin,inda tuni
Abbu Abba Ummi Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Dr Faruq barista Aliyu suka nufo gadon da nake kwance kowa bakin sa ɗauke da hamdala.
nan suka shiga jera min sannu ba adadi,Ni dai da ido nake bin su..


Baki Inna ta washe tana faɗin
"Ikon Allah sai kallo sannu kinji ƴarnan".
Dr Faruq yaɗan matso yana duba ruwan da ke ɗaure a hannuna hannun da Inna ke rike dashi ganin inata kokarin ɗago hannun,yace
"Inna saketa ruwan ma yakare bari nacire mata".
yana cirewa na ɗago hannun da kyar naɗan yarfe shi, dubana yayi yace
"Ya kike jin jikin dai ƴargida Inna? akwai jiri ko ciwon kai??".
kai nagirgiza
a hankali nace
"Banajin jirin yanzu kaine kawai yake min ciwo".
murmushi yayi dafaɗin
"Zai bari shima".
nan suka fita shida barrister Aliyu,
Mamie da tun ɗazu taketa sakin murmushi tace
"Kai ma dallah Alhamdulillah sannu kinji ɗiya ta".
kai na gyaɗa mata sai sannan naga ashe ba ita kaɗai ba fuskokin kowa ɗauke yake da yelwa tacciyar murmushi Ummi na kam ido ta zubamin tanata sakin murmushi,Abbu da Mamie wani tsagwaran farin ciki ne a kan fuskar su,Mamie nata ya gaza ɓoyuwa har sai da ta matso kusa dani sosai tariko hannun da naketa ɗan tanƙwashe yatsun hannu tariko shi tana faɗin
"Yaya dai HAMDAH hannun nayi miki ciwo ne?".
tafaɗa cikin bayyana murmushin ta a fili da nuna tsantsar kulawa,
kai na gyaɗa mata alamar Eh,
hannun ta ɗan rika matseshi a hankali tana yimin sannu.
Inna tace
"Yo ba dole hannu yayi tsami ba yasha ruwa da allurai".
kallo na na mai da kanta kana nace
"Yunwa nakeji". da sauri Aunty Rafee'at tajuya gefen ta inda basket ke ajiye cikin hanzari ta haɗo tea tazo in da nake,Mamie ta taimaka min namike zaune karɓar cup ɗin Mamie tayi tace Aunty Rafee'at ta taimaka min naje na wanko bakina tukun.
Aunty Rafee'at tariko hannuna nasauko a gadon a hankali muka nufi bayi,na wanko bakina muka fito,
a bakin gadon na zauna Mamie ta mika min tea ɗin da tariga da tafifitashi yahuce haɗe da yankan bread,tea ɗin kawai na amsa ban da bread Dan ni ban fiye shan tea da bread ba,nakuwa sha da ɗan yawa kana na mika mata cup ɗin,Inna ta samin pillow ta bayana najingi na dashi tace na huta da kwanciyar nan haka,
"Inna yaushe kika zo?".
nafaɗa ina duban ta ganin itama bakin ta yakasa rufuwa,
washe baki takuma tace
"Tun lokacin kina rai ahanu Allah yo ai ni tun da naji kina kwance a gadon asibiti a sume mayafi na kawai na ɗauka nahayo mota nayiyo nan".
Aunty Jaleel tace
"To da rantan a hannun wa yake".
"Tafi can da alla yarinya karama da babban ciwo koke da girman ki ma irin wannan ciwo yaka maki sai kin wujujjuge bare ita kankanuwa da ita".

A hankali a ka turo kofa a sannu na ɗago kaina kasan cewar ina fuskantar kofar ce,
yana rike da laida a hannunsa
gaba ki ɗaya jikin sa a sanyaye yake kallo ɗaya zaka yi masa ka gane hakan,
karaf ida nunmu ya haɗu da na juna,waro ido yayi a kaina da alama mamakin ganina azaune yake,
wani irin murmushi yasake yayin da yake bina da wani irin kallo mai cike da ɗinbin farin ciki,gaba ɗaya mutanen cikin ɗakin suka juyo jin an buɗe kofa ba a shigo ba,
ganin gaba ɗaya hankalin sa yayi nisa yasa Abbu yin gyaran murya,a kunyace yamai da kofar yarufe ya tako cikin ɗakin,a gefen gadon ya tsaya sai dai har lokacin fuskarsa da sihirtaccen murmushi,
Inna ta dubeshi tana faɗin
"Yauwa mai sunan Malam kasiyo maganin ko, ta ɗan taɓa shayi sai tasha yanzu maza bata yanzu tasha".
rau-rau nayi da ido jin abun da Inna ta faɗa na kalleshi idanuna taf da hawaye shima ni yake kallo,
murya na rawa nace
"Ya SALEEM zanyi amai".
ɗan jim yayi dan yasan tabbas nasha zanyi aman gashi babu ta yan da zaiyi ya dakatar da aman a wannan lokaci,
Inna kuwa daɗa duban sa tayi tace
"Yo bin nata zakayi bazaka bata ba jinya za'ayi shi bashan magani ne".
tuni hawaye yafara sauka a idona
Inna kuwa taci gaba da faɗin
"Maza bata tasha".
a hankali ya buɗe laidar yaciro magungunar yabuɗe ya mika min,Mamie ta mikamin gorar ruwa ina rike da maganin a hannuna hawaye naciga ba da zuba a idanuna Inna tace
"Iya shegen banza baza kayi mata tsawa tasha ba ka zuba mata ido ne".
idanunsa ya lumshe tare dakuma buɗe su lokaci guda,miko hannunsa yayi ya karɓi maganin da gorar ruwan yawasa maganin cikin laidar.
salati Inna tashiga yi da tafa hannu tana faɗin
"Kai mai sunan malam bin nata zakayi ina ɗazunnan take kwance kamar gawa shine yanzu taki shan magani kamara mata baya".
Abba yace
"SALEEM ya ka karɓi maganin kabata tasha mana".
bayan keyarsa yaɗan sosa kana yace
"Dr yace sai taci abinci kafin tasha kuma tea kawai akace tasha".
Ummi tace "To ai ga abinci nan sai a saka mata taci".
da sauri nace "Ni bazanci wannan ba".
Abbu yace "To shikenan Rafee'at da Jaleela kuje ku girko mata wani sai taci tasha maganin".
To suka amsa dashi.

Baki Inna tawashe kamar ba ita ke masifa yanzu ba ta dubeshi tare da faɗin
"Wai cikin wata nawane yace maka Mai sunan malam?".
kamar bazaiyi magana ba jin takuma maimaita tanbayar nata a hankali yamosa lips ɗin sa
"Wata ɗaya". yafaɗa a dakile akuma takai ce".............!★


*FREE PAGE YAKUSA KARE WA*😉
*A MATSO A CIGA DA BIYA WAƊAN DA BASU BIYA BA SUZO SU BIYA*





Mommyn twins ce




🌺 *HAMDAH*🌺



*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*



*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*




_Free page yakusa kare wa amaso acigaba da biya 👉🏻my no 08034690723_



🅿️28



Nan take wani farin ciki yakuma lulluɓe fuska da zuciyoyin kowa,Abbu yasake wani kayataccen murmushi irin nasu na manya,a ɓangaren Abba ma haka,Mamie Kam ma ba'a magana sai yi take kamar zata rungume ni,har sai da taɗaura hannunta a kaina tashafa,
Ummi kam na gefe itama da ka ganta kasan tana cikin mashahuriyar farin ciki sai dai ita nata tana haɗawa da kawaici, Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela sai washe baki suke musamman Aunty Rafee'at sai in munhaɗa ido da ita sai tayi min dariya.
cikin rashin fahimta nake bin su da ido,a raina nake faɗin
"To wacece mai cikin acikin Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela dasuke ta murna haka dajin watannin cikin?".
maganar Inna ce yadawo dani daga duniyar tunanin dana lula,
"Kai madallah Allah yaraba lafiya".
tafaɗa tana washe baki, ameen Aunty Jaleela da Aunty Rafee'at Mamie suka amsa dashi.
Ummi kam laɓɓanta ne suka motsa alamu ta amsa acikin zuciyar ta ne. nan Abba da Abbu suka fita suka nufi masallaci dake nan cikin asibitin jin ana kiran sallar Isha, zuciyoyi da fuskokin su ɗauke da farin ciki mara misaltuwa. Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela ma suka fita waje gun mazajen su
Inna kuwa duban ta takuma mai dawa ga Ya SALEEM sai kuma ta taɓe baki tace
"Yooo ina tanbayar ka sai wani amsa kake bani ciki-ciki wane mai ciwon hakori,iya shegen banza yanzu wani ɗan kaniyar ne yamata cikin, da bacewa kayi baka so ba ina har ɗaki kabini kanayi min taɓara saboda an aura maka ita, yanzu ina gashi ka saka mata ciwo yooo ciwo mana haka zatayi ta fama ta haifa maka iya shegen banza"...

Wani irin sinkewa gaban kirjina yayi cike da tsoro nawaro ido sai yanzu nagane cewa batun akai nane "Nice da ciki?!!!" nayi maganar acikin raina.
nan da nan hawaye yacika idona tuni suka fara tsiyayo wa cikin jin tsoron yan da naga Inna ta haɗe rai sai nashiga juya kai murya na rawa nashiga faɗin
"Wlh babu ruwana Inna wllh Ya SALEEM ne ai sai da nace masa kin hanani shine ya...."!
wani irin tsawa Ummi ta daka min bashiri nahaɗiye ragowar maganar tawa ɗaga inda take tsaye tadubeni tare da faɗin
"Rufawa mutane baki waya tanbaye ki🤦🏻‍♀️ sha-sha-sha kawai, kisake buɗe baki agun nazogun na faffasa miki baki".
ganin Ummi na maganar tana ɗan matsowa yasa Mamie dawowa tagabana ta tsaya tana faɗin
"A'a Ummi'n Fauzan barta taji da abun da take ji ina yanzu tasami kanta".
Ummi ko ƙwafa tayi takoma in da take tsaye tana ai kamin harara.
Ya SALEEM kansa ya sunkuyar kasa a sannu yazame jiki yafice a ɗakin.
Mamie ta dubeni da kyau cikin tausasa murya tace
"Tun daga parlour har cikin ɗakin ki sirrinki ne kada ki sake kokarin buɗe shi kinji?".
kai na gyaɗa tare da yin kasa da kai cikin jin kunya.
Inna kuwa cewa tayi
"Yooo ai tarbiyya ce kunga irin tarbiyyar mu ba irin nakuba wannan ƴar ma Nusaiba in zan koma da ita zan koma dan ni ban yarda da irin tarbiyyar ku na zamanin yanzun ɗin nan ba, yo mu zamanin mu har akai mace ɗaki batasan menene zaman auren ba miji shi zai nuna mata, amma azamanin yanzu tun ƴa bata tafasaba zata kone, babu abun da bata sani ba, yooo wata tsiyar ce ba gasunan muna gani ba wacce taji tarbiyya ayanzu itace take iya ɗan daurewa har takai budurci gidan auren ta ita ɗin ma addu'ar iyaye da jajircewar su ne, wasu kam a iska suke yada nasu dan basusan muhimmanci da darajar saba sai sun shiga gidan aure surika ciza yatsa, shikuma kamar madara yake da zarar yaɓare ba'a kwashe shi
abune mai daraja da kima agurin kowata ɗiya mace,
in kika tattala kanki

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment