Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan ba harsai Dana Mata alkawarin zanyi duk abin da tasani hardama wad'anda takara d'auramin su akarshe, har bakin get narakasu dafari nace ni zanbisu Aunty Rafee'at tace nazauna ita zatazo gobe Ina tsaye harsai da naga sun shiga nape kafin najuya nakoma ciki, nasa kaina zan shiga parlour sai ganin Aunty Na'ima nayi tsaye cikin parlourn rikeda wuka a hannun ta tana ganina tayi kaina..............



HHHHHH🤔 uhum Bari nayi shiru nafece🏃🏻‍♀️




Mommyn Twins ce




*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*


*Free page*

My no 08034690723



🅿️6



Kara nakwalla ganin tayi kaina tana juya wukar,
kafin nayi yunkurin gudu harta isoni tashako kwalata tad'aga wukar takawoshi daf da fuskata,
tana cigaba da juyashi,
tsananin tsoro had'eda firgici su suka dirarmun kad'an yarage nasaki fisari a jikina, duk wani barazanar da Inna takeyimin nazata yankani Bata tab'a d'aukar wukan har takawoshi kusadani irin hakaba.

Wani gigitaccen Kara nasake Mai cike da tsananin tsoro nadaddage narike hannunta data da ta shako wuyata da shi, da ƙyar na iya sun kuyar da kaina na yanka mata cizo a hannun, da sauri tasaki wuyana najuya da mugun gudu nashige d'aki, namai da kofa narufe da karfe namurza key, najin ginu da jikin kofar tareda dafe kirjina da ke dukan uku-uku, sai sauke numfashi nake kamar wacce tayi tsere,
zamewa nayi kasa nazauna har lokacin hannuna nadafe a kirjina.
"Nashigesu yaushe Aunty Na'ima tahaukace?".
Nayiwa kaina tanbayar.
Jin tana dukan kofar yasani mikewa zunbur, sosai take dukan kofar tanafad'in
"Wlh da kin tsaya da sai dai yau uwarki tahaifi wata shegiya munafuka ai ni tun sanda nafara ganin ki nasan bakaramar hatsabibiya za'ayi anan ba, ina zama da mijina kk zab'a to kuwa kin zab'i tarwatsewar rayuwarki!".
Tajuya fuuu tafice.
lekawa nayi tajikin kofar na hangi bayanta tana ficewa daga parlourn, da sauri na Isa bakin gado nazauna Kuma dafe kirjina nayi
"dama ashe Aunty Na'ima tahaukace shine Inna tasa aka kawoni gidan Nan Allah bazan zauna ba ko sati d'ayan ma nafasayi".

Ta babban parlour Na'ima tabi tana shiga Ya SALEEM nafitowa da ga part insa, da sauri taja tatsaya tamai da hannunta dake rike da wukar tabaya,
A sannu yakaraso in da take yatsaya daf da ita, kirjin tane yafara dukan uku-uku tabbas idan yasan a bin da taso ai katawa yau kashin ta yabushe,
Dan tana da tabbacin yaga ta in da tafito, ji tayi zuciyarta tama bushe tashirya
d'aukar koma menene zama da kishiya Kam tad'au alkawari wa kanta sai dai a lahira idan a nayi.

Cikeda karfin hali da bushewar zuciya tad'ago kanta,
Ga mamakin ta
saitaga yatsareta da idanunsa wacce
suka kankace suka Kuma sauya kala,da wannan alamar kawai take iya fahimtar yanayin sa idan yana hannu,
"Jiya bakiga miscall
Ina bane".
Yy tanbayar yyn da ida nunsa yake kafe a kanta,
Numfashi tasauke a kasan zuciyar ta
Dan tafahim ci halin da yake ciki Kuma ta tabbata da
shi yakwana,
ta ce "nagani mana".
Ya ce "to meyasa Baki d'agaba Kuma Baki zoba".
Yy maganar fuskarsa a murtuke
tace "Nazo nayi maka meye bayan ka auro wacce zata maye
maka gurbina ai zuwana baya da
wani am fani
meyasa baka kirata
taje tabiya maka bukatar nakaba".
Tafaɗi maganar ne cikin karfin hali da tsoron a bin da zaije ya dawo dan kuwa karshe ita zai ɓare mata, dan dai tasan koshi waye duk da kasan cewarsa mabukaci yakan iya danne bukatar sa har idan ba ita ta neme shiba, in zasu shekara bazai taɓa neman taba, wani bin takanyi tunani da zargin taya yake iya jure bukatar nasa ko dai yanada mai biya masane a gefe tayi duk wani iya binciken ta daga karshe dai duk amma ɗaya ce babu.👌🏻 kariyarsa shine AZUMI. takan gane zallar bukatarsa ne ta ƙwayar idanunsa.
Had'e Rai Yakuma yi yajanyota jikinsa
yad'an ja da baya
yazauna saman kujera tare da zaunar da ita a gefen sa yakalleta
da kyau ya ce
"Kinsan me kk fad'a
kuwa? HAMDAH d'ince zan kira? Me kike nufi ma tukun?".
Kawar da kanta tayi gefe har lokacin hannunta dake rike da wukar namakale
a bayan ta dad'a mikashi tayi tabaya
sosai,
ta cusa wukar tasakankanin kujerar dasuke Kai ta ce "tun da har
kariga da ka a mince a ka kakaba maka ita to mekuma yarage,tun
da Wannan ya'iya kasan tuwa to meye
bazai iya faruwa ba".
Takarashe cikeda gatsali tayun kura
tana kokarin mikewa,
yaki Bata da ma tahanyar sauke hannun sa a
kafad'arta ya dad'a suke fuska tare da tsareta da ido Yana d'an kyakykyafta su.
kallonsa tayi idanunsa duk sun kankance murmushi tayi a cikin ranta, tace "Dama an faɗa min zaka kawo kanka da kanka".
Wannan ma wata kofa ce na mafita a gareta.
Kawar da kanta tayi tamike tsaye tanafad'in
"Kyaleni inada abin yi".
Mikewa yy tareda riko hannun ta yakuma d'aure fuska cikin nuna Isa
da bada umurni ya ce
"Kafin kiyi wani ai kin sai kinyi nawa tukun Dan haka muje".
D'an zabura tayi ta
ce "wa ni?ai Wannan Kuma babushi ai SALEEM tun da kaje ka auro
wata ka ajeta cikin gidan Nan to babu
Wannan maganar sakanina da kai sai
dai karika kunshe abinka kokuma kaje can kasaukeshi cikin mararta".

Kansa yashafa tareda furzar da iska daga bakinsa ransa ya b'aci datake Dan gantashi da kanwarsa, duk jarabarsa bazaije gun HAMDAH da bukatarsa ba to ta inama zai fara 'yarda a ka haifeta a gaban idon sa, yakuma rasa dalilin da yasa yakasa iya danne abinsa har kuma yake kokarin nuna mata halin da yake cikin. Dogon tsaki yaja tare da
Fizgo hannun ta yanufi cikin bedroom in sa, suna
shiga yasaki hannunta yanuna Mata gado yy Mata
alama da tahau.

Wani kuka tasake
Mai cikeda zunzurutun makirci da tsigar Jan hankali tazube bakin gadon har da
Jan sheshsheka cikin muryar kukan takefad'in
"SALEEM tun yanzu
harkafara nunamin cewa kakaro aure A she kaima kana daga cikin mazaje masu irin Wannan halin?,nasan Dan ka
kuntatamin kanunamin ni ba komai bace zaka kwanta Dani,wlh
SALEEM idan ka cutar Dani dan kana tunanin kana da wata Allah sai
yasakamin".
Wani kukan takuma sakewa Wanda duk
Wanda yaganta saiyaji tabashi tausayi.

Kallonta yatsaya yi
hanikam tadage take rusar kukan,
Tabbas yasan ko wata mace irin haka yakasan ce da ita bazato bb sammani a karo Mata abokiyar Zama dole tagirgiza, musamman Na'ima da yasan halinta da kafurin kishi wasu matan sukan iya b'oye kishinsu a wasu lokutan Na'ima kuwa batadaga cikin irin wad'annan matan.
Sai dai a yanzu yanayinta ya banbanta da na sauran lokutan yanayin ta nayanzun yabashi tausayi,
musamman dayaga kishin gauraye da rauni a tattare da ita.

Asannu yamaso in da take yazauna
kusa da ita Yana fuskan tarta ya ce
"Meyasa kk son tada hankalin Ki a kan Wannan?, HAMDAH fa kanwatace kisa a ranki HAMDAH an kawota gidannan ne
Dan ta tayaki wasu ai'kace-ai'kace nagida,
duk wasu a bin da
yakamata ita zata
Rika miki to meye
wani abun tada hankali".

"tabbas Wannan
damace".
tafad'a a kasan zuciyarta
Ganin yadage da lallamin ta gashi
Kuma a bukace yake sai tarika basarwa tana jam
Masa aji.

Rungumota yy yashiga kokarin samarwa kansa nutsuwa Nan ma
Bata bashi dama ba bukatar ta dai yacigaba da fad'ar
magana maraddad'i a kan HAMDAH a hakadai harya samu yabiya bukatarsa.
Bayan komai yalafa
tana kwance a gefen sa hannunta na d'auren saman kirji sa cikin salon yaudara da kirsa da kisisina tanarke
murya tasoma magana.

"My SALEEM ni a ganina ace yarin yarnan tazauna a gidan Nan kawai Dan d'an wani 'yan ayyukan da bazasu gagareniba kuma ga Rufa'ila ma tananan, inaga hakan zai iya zame Mata takura kawai a maidata gida in yaso tarika kawo Mana ziyara lokaci zuwa lokaci, Kar yazamo mun takura mata".


Janye hannunta yy daga kirjinsa yamike zaune ya ce
"hakan
bazai yuwuba bakuma zanso su Abbu su sami wanna
labarin ba, hakan bazai yuwuba tacigaba da zama a
hakan kawai".
D'an shuru tayi zuciyarta na kuna, "dama nasan za'ayi haka shegen wani son biyayya da wani nuna shi Mai iyaye sai yarika nuna shi yafikowa yiwa iyaye biyayya".
Tayi maganar a cikin zuciyarta.
Tabbas tasan abune
Mai wuya ya amince da Wannan kudurin natan Dan SALEEM mutun ne
Mai matukar Jin maganar iyayensa da yimusu biyayya ko da bayason a bu
har idan suka nuna Amin cewarsu a kan
a bun tofa shima ya Amin ta.
Tab'e Baki tayi a je a
haka wataran wanna biyayyar taka sai ta
durkushe.

Saukowa yy daga saman gadon yashige bathroom Dan sarkake jikin sa.


★★★★

Tun bayan fitar
Aunty Na'ima dana koma saman gado ban tashiba saima
kwanciyar da nayi tunani narikayi ta yadda zanyi nafita a
gidan batare da taganni ba, Dan ni banji kamar zan
cigaba da zama watarana ciwon haukanta Yakuma
tashi takasheni babu Wanda yasaniba, gara
kawai nakoma Dass gun Inna.
Mikewa nayi nazauna tare zuro
kafafuna kasa namike tsaye,
gaban wardrobe na Isa da zummar d'iban kayana natafi
Dass, daga in da nake tsaye ina iya hango tajikin window kasan
cewar glass in windown da labulen duk abud'e suke,
Mai da marfin wardrobe in da
nabud'e nayi narufe natako jikin windown, Ido naware hango Mai
baiwa fulawa ruwa yanata zagayi cikin fulawa nazuba musu ruwa,
Washe Baki nayi,
Nan take namance dawani batun tafiya,
Dasauri nabar jikin windown nanufi kofa nafita waje,
da sassarfa na Isa inda
Mai baiwa fulawa ruwa yake banyi wata-wataba na wafci tiyon hannunsa nad'agashi sama
Ina sallen murna, ruwan Yana dawowa jikina,
Na ce "la Salele
Ashe dama kazo garinnan kana irin ai kin da Baba na lambu yakeyine?, ai daga yau kullum
zan Rika tayaka Yasin."

Da sauri Salele yamika hannu Yana kokarin amsar tiyon, nasauke hannuna
nayi baya dashi
ya ce "ƴar gidan Inna bani nacigaba da ai kina tun oga
bai fito".
Ban saurareshiba saima watsawa furannin ruwa Dana
soma cikeda Jin dad'in ganin abin kaunata ruwa.

Salele d'an Dass ne
unguwarmu d'aya dashi, ta hannun Inna yabi harya Sami aiki agidan Ya
SALEEM.

Duk yanda yaso
nabashi tiyon fir naki na ce nidai yabari zan tayashi
ne,haka narika d'aga tiyon sama ruwan nasauka a kaina dakuma cikin fulawan tsalle narika yi cikeda Jin
dad'i, karshe dai hakura yy yatsaya Yana kallon ikon
Allah.


Ya SALEEM ne tafe Yana gyara d'aurin tsadadden agogon
dake d'aure a hannun sa, Ga dukkan alamu sauri
yake Dan yanayin tafiyar da yake yanuna hakan.
Da sauri wani dattijo dake share mota yy hanzarin bud'e Masa marfin motar tareda d'an risinawa tun kafin yakaraso in da motar take.

Da sauri Salele yamasa kusa da ni yamiko hannu Yana kokarin amsar tiyon tare da fad'in

"Yargi dan Inna bani Kinga Oga yafito".

Da sauri najuyo Jin ya am baci Oga, dai-dai lokacin Ya SALEEM yakarasa sauka daga saman step in sashin sa, da zai sadaka da farfajiyar gidan.

Idona nasauke kan fuskarsa bb ko alamar rahama a tattare dashi, mayar da dubana nayi jikina daga sama zuwa kasa gaba d'aya najike.

Rai b'ace Ya SALEEM yanufo in da nake Yana maganar zuci,
"Kaduba shashanci irin na yarin yarnan da wannan tsanyin tafito tana jika jikin ta yanzu idan mura yakama ta Ina ni za'abari da damuwar siyan magani tun da an kakabamin da muwa, yarin ya saikace wata mayya
wannan uban sanyi tafito tana zuba ruwan sanyi ajikin ta!".

A zafafe ya dunfaro in da nake.
b'ari jikina yasomayi Dan nasan yau Kam banida wani mafaka bamu tare da Inna bare tahanashi dukana.
Wayar dake rike a hannun sane yafara tashi da wani sassanyan sauti alamar shigowar Kira, batare da ya tsaida tafiyar da yakeba yad'ago wayar tareda kallon fuskar wayan,
Sunan Abbu ne yabayyana kan screen in wayar,
Cikin hanzari yaja yatsaya.

Ganin ya tsaya Da sauri na wurgar da tiyon najuya a guje nayi ciki.

Gyara tsayuwar sa yy da kyau ya Kara wayar a kunne tare da yin sallama ya ce "barka da warhaka
Abbu".
A b'angaren Abbu ya amsa Masa da "yauwa".
Sannan Abbu yad'aura da fad'in "yagidan da iyalin?".
Ya ce "alhmdllh".
"Masha Allah, idan kafita yau kaje kanimawa HAMDAH makaranta tacigaba, Bai kamata ace an dakatar Mata da karatunta ba, kayi Mata duk wani abinda yadace inyaso ko zuwa satin samane saita fara zuwa".
Shuru yy batareda yace komai ba, Abbu ya ce "hello SALEEM kanatare da ni?". Tafiya yasoma sannan ya ce "Eh". Atakai ce,
Abbu yaci gaba da fad'in "Sannan kazuba Mata duk wani abun bukata kamadaga kayan abinci da na Sha da sauran su, duk da nasa an Kai wasu jiya Amma yanada kyau ka Kara mata, kadaiji abinda nafad'a ko?".
"Eh". Yakuma fad'a tare da sauke wayar a kunnen sa Jin Abbu yakatse Kiran.
Dai-dai lokacin ya Isa jikin mota yashige ciki Yana am sa gaisuwar da Malam Sule Mai wankin mota keyimasa,
Salele yakaro jikin motar da sauri yarusuna yashiga gaida shi, Rai b'ace yadubi Salele batare da ya am sa gaisuwar da yake masaba ya ce
"Zaka iya tattarawa kakara gaba tunda ai kin ya isheka!". Kuma durkusawa yy kamar zai zuba goigowonsa kasa ya ce "wlh Oga nace tabari ita taki a gafar ceni".
tsaki yaja yafigi motarsa yy gaba.

Ina shiga d'aki bayi nashige dagudu narufe kofar, Jin karar tashin mota yasani d'ale saman toilet naleka ta window, ganin shine yafita sai naduro daga saman toilet ɗin, kayan jikina dasuka gama jikewa yatub'e nawurgasu cikin washing machine,
Najanyo towel dake sakale jikin karfe na silver dake gefen bayin Wanda yake mazaunin igiyar shanya,
Nad'aura,nafito nanufi jikin wardrobe Ina tura Baki had'eda kunkuni
"Shi wanna yafiye takuri baya tab'a barin mutun yasake, Kuma an jima komawa zanyi naje nacigaba".
gajeren tsaki naja naji haushin yadda yakatsemin wasana da yanzu inacan Ina kan zuba ruwa Mai dad'i a jikina.
Kaya nasaka nafito parlour.
Kitchen nanufa, Ina shiga nafara bud'e-bud'e ko zan Sami ragowar breakfast in da Aunty Rafee'at tagirka d'azu, Dan zuwa yanzu nafara Jin yunwa, bb ko alamar abinci agun Dan haka nashiga tunanin mezan girka Dan nasawa cikina.

Jinayi kamar ana buga kofa ido nawaro tareda kasa kunne da kyau,
Tabbas kuwa knocking ake, da karfi kirjina yabuga gaba ki d'aya nagama sinkewa dan nasan Ya SALEEM ne ko wancan mahau kaciyar matar tasa,
Jin an cigaba da knocking in, ahan Kali nafara taku na Isa jikin kofar kitchen, ahan Kali nabud'e kofar Saida naleko na tabbatar da babu kowa cikin parlour'n sannan nafito, Jin an daina buga kofar sai naja natsaya cikin parlour'n,
Nakai minti 5 a tsaye, sai Kuma aka cigaba da knocking in.
Zurunayi Ina kallon kofar a yanzu Kam nasan cewa ba Aunty Na'ima bace Dan ko d'azu da tashigo ai Bata tsaya bugun kofa ba Kai tsaye tashigo,
Saidai banada tabbacin cewa ba Ya SALEEM bane,
Wani numfashi nasauke.

Tabbas inko shine bashakka yau saiya b'allani cikin gidan Nan, Yakuma Hana a d'aurani haka zan cigaba da rayuwa a gurgunce.
Hawayene yasoma gangaromin batare da nasan da zuwan suba,

Ahan Kali nasoma tafiya na Isa jikin kofar, hannuna na rawa nad'aura saman handlle ɗin rumtse idanuna nayi naja numfashi da karfi sanda na murd'a handle in, nad'an Masa da baya naja kofar batareda nabud'e idanuna ba,
Baya nakuma yi lokacin Dana gama bud'e kofar nabud'e idanuna dasauri Jin yace b.........




Mommyn Twins ce





*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*


*Free page*


My no 08034690723



🅿️7



"Barka da warhaka Hajiya".
Nannauyan ajiyan zuciya nasauke a fili,ganin ba Ya SALEEM d'in da nake zato bane, Kai kawai na iya gyad'a Masa Dan har lokacin jikina Bai daina cirawaba,
Mutumin ya ce "Oga SALEEM ne ya yace nakawo wad'annan".
Yafad'a Yana nuna kayakin abinci daki jibge a gifen sa,bin kayan nayi da Ido, katon-katon in taliya da macaroni Indomie Couscous mangyad'a yello da manja shinkafar dafawa da farar shin kafa da semo buhu d'ai-d'ai, Arish Naman saniya Dana kaza wacce aka gyarata aka yayyanka kwai kiret-kiret sai busashen kifi da d'anye Maggi curry time dadai sauransu, kayan d'and'ano kala-kala.
Sai kayan tea suma komai akwai.

Muryarsa na sinkayo Yana fad'in "Hajiya Bari nashiga dasu ciki".
Kai nakuma gyad'a Masa namasa gefe nabashi hanya, buhun shinkafa yad'auka ya ce "Ina kitchen in yake".
Da hannu nanuna Masa kofar kitchen, asannu nakoma cikin parlour nazauna kan 1str,
Jidan kayakin yasoma Yana shiga dasu ciki tas yakwashe yashiga dasu sannan yakimsa komai in da yakamata kana yafito yymin sallama yafita.

Mikewa nayi nashiga Bedroom Jin sautin Kiran sallah dake tashi cikin masallacin kofar gidan,
Direct bathroom nashige nayi alawala nafito nagabatar da Sallah, Ina idarwa namike nanufi kitchen,
Tsayuwa nayi Ina karewa cikin kitchen ɗin kallo yakimsa komai yadda yakamata, a sannu na Isa jikin kofar store da ke Nan cikin kitchen ɗin.
Natura nashiga Shima yashirya komai yadda yakamata,

katon ɗin macaroni nabud'e naciro laida d'aya, nad'ibi albasa 'yan madai-daita guda uku nakomo kitchen,nad'au 'yar madai-dai ciyar roba namaso jikin Fridge Wanda suke jere subiyu babba da karami,
Nabud'e karamin, Jan namace da kayan ciki sai d'anyen kifi aciki, nad'ibi zallar hanta d'an dai-dai sannan narufe Nazo na aje, nad'au wuka na yayyankashi d'an madai-dai ta nawanke nazuba cikin tukunya, sannan nakunna Gas nad'aura tukunyar,
Nayanka albasa guda biyu cikin ukun dana d'ibo nazuba,na b'are Maggi da curry nad'ibi garin citta da kanumfari sai d'an gishiri d'an kad'an,
duk nahad'a nazuba sannan narufe tukunyar.

Babban Fridge ɗin nakuma bud'ewa gefe d'aya kayan ganyene irinsu karas kabeji green beans latas da dai sauransu su,
D'aya gefen Kuma drinks ne kala-kala nad'ibi karas da green beans, na yanka karas sirara sannan nawan kesu natsane guri guda,
Tattasai da taruhu na nikeshi d'an dadai, sannan
Nabud'e tukun Yar hantar tanuna, nasauke,
wata tukunyar nad'aura kan Gas nazuba ruwa cikin sa narufe, batareda b'ata lokaciba ruwan yatafasa kasan cewar ruwan bashida yawa,

Rabin laidar Macaroni nazuba cikin ruwan dake tafasan,
Dan nasan ko wuni zanyi bazan iya cinye laida guda ba,
Bayan 7min nasauke najuye cikin 'yar karamar kwando,nawanke tukunyar Dana tafasa macaroni'n nakuma maidashi kan Gas
nasulala mangyad'a d'an dai-dai yadda nake bukata na yanka albasa cikin sa yana soyuwa najuye kayan miyar Dana rigada na jajjaga minti 4 yy nazuba Masa ruwa d'an kad'an nazuba kayan d'and'ano sannan narufe,Saida yatafa sosai na tabbatar da maggi'n Dake ciki sun narke sannan nazuba tafashashiyar hantan namota nakuma maida marfin narufe,
Zuwa can nabud'e nazuba Macaroni nayuya sosai yadda zasu garwaya da juna,sanin Macaroni da hantan sun d'an nuna tun agun tafashe sai na zuba yankakken karas da girinbins iɗin narufe sanna narage wutan namasa gefe Ina sauke numfashi.

Lumshe idanuna nayi Jin daddad'an kamshin Dake fita daga cikin girkin,
Banyi mamakin yadda na'iya had'a girkin batare da yabani wuya wajan iya sarrafa shiba,sanin cewa hakan koyar wace ga Aunty Rafee'at Dan duk Randa taje Dass ita takemana girki harta koma, duk sanda take kitchen Ina tare da ita, hakan ne yasa nau ikan girki iri da kala suke zaune cikin kwakwalwata, duk kiwuyata banayiwa girki Dan Yana burgeni sosai akasin wanke-wanke da shara dasuke cimin tuwo a kwarya.

Numfashi nakuma sauke sanda nakalli inda nab'ata,Baki naturo gaba,tuno maganar da Aunty Rafee'at tayimin d'azu dazasu tafi har narakasu bakin get Bata fasa fad'amin ba,

ta ce
"Duk sanda kikayi ai ki kitabbata kin tsaftace inda Kika b'atan kada kibar jikin ki da datti kada kibar muhallin ki da datti kidage sosai wajen saftar jikin ki da muhallin ki,nasanki da kiwuya HAMDAH Dan Allah kirage".

Asannu namaso nafara
Tarkasa kwanunkan danayi amfani dasu nawanke namaida komai mazau ninsa,
Nashare cikin kitchen in har inda ban b'atan bama nakuma gogeshi tsaf,ni kaina gurin yabani sha'awa tabbas tsafta wata abace Mai girman gaske.

Tuni ruwan cikin macaroni'n yatsane nakashe gas in nasauke tukunyar,
Kula Mai d'an girma nad'auka nakwashe girkin a ciki sannan nazuba Wanda zanci a plate,
Parlour nadawo nazauna nasoma cin abin cin.

Ina gamaci namaida plate in kitchen, Nazo nakulle kofar dazai sadaka da babban parlour'n gidan, wan da tanan ne Aunty Na'ima tabi tashigo,kasan cewar akwai hanya nakowani part dake cikin gidan tacikin babban parlour'n,
Nakuma je namurza key na asalin kofar parlour'n,
Sannan nazo nakunnan TV nakwanta saman doguwar kujera, ba jimawa bacci yad'aukeni.

Ban farkaba sai wajen karfe 6, asannu natashi nashiga Bedroom naje nayi alawala Koda na idar da sallar, ina kan sallayar aka Kira Sallahr magriba namike nagabatar da shi.

Bayan na idar shiru nazauna Kan sallayar, ahan Kali naketa jin tsoron danaketa danneshi natasomin ganin guri yafara duhu,
Ban tashiba Saida nagabatar da Sallah'r Isha,
Tuni guri yagama duhu duk da kuwa hasken wutan lantarkin daya haska ko Ina nacikin gidan,Amma duk da hakan acikin d'ar-d'ar nake, gagurin yatsaya cak bakajin motsin kowa.

asannu namike na ninke sallayar na aje nazauna bakin gado gaba d'aya kewar Inna yacikani,
"Ko yatake?".
Nayi maganar afili, sai Kuma nakwab'e fuska "namasan ita batunani takeba tunda da gangan tasa aka kawoni gidan Nan, ai dafarko da Ya Masa'ud tace za'amana aure shine zatasa a canza da Ya SALEEM,
Kuma sati d'ayan zanyi bazan Kara ko kwana d'ayaba".
Nakareshe maganar tareda yin rau-rau da ido.

Najima sosai zaune agun daga bisani namike naje kitchen nazubo a binci, bedroom in nadawo Ina gama ci naje nawanko bakina, Nazo nahaye gado,
Ganin baccin bazuwa zaiyiba kasancewar ban Jima datashi daga baccin ba, sai nafito parlour nakunnan TV don yad'ebemin kewar Inna, sai wajen karfe 11 nakashe TV'n nashige bedroom lokacin Kam bacci ne Tam idona.

Washegari
Bayan nayi Sallah kwanciya nakumayi bani nafarkaba sai karfe 9,
Nasauko a gadon duk jikina a mace Dan baccin Bai isheniba, nadai tashine kawai saboda hud'ubar da Aunty Rafee'at tayimin na baccin safe,
Har nakai bakin kofar bathroom saikuma najuya na wuce cikin window nazuge labule,
"La harya fara". Nafad'a tareda sakin labulen najuya da sauri nanufi waje.

Da dariya d'auke a bakina nakaraso in'da Salele yake,
Yana ganina yy saurin gyara rikon tiyon hannusa,
Na ce "Salele barka da safiya". Namiko hannu Ina fad'in
"Kawo tiyon natayaka".
Cikin sauri ya ce "a'a 'yargidan Inna kirufamin asiri karkisa narasa ai kina, jiyan nanma bansaniba ko Oga yahakura ko Bai hakura ba, idan yanzu Yakuma fitowa yasameki shikenan nakad'e".

Baki natab'e najuya inafad'in "ohon ku Allah yasa akwai ruwa a bayi".

Ya ce "yauwa yimaza kije na bayin kiyi wasanki hankali kwance".

Nidai ban Kuma kulashiba nawuce a bina,
Ina shiga ciki direct bathroom nashige natub'e kayana nasun kuya zuba ruwa a jikina Saida nagaji Dan kaina kafin nayi wankan soso da sabulu nad'auro towel nafito.

Gaban dressing mirror nazauna,
Mai nashafa sannan nayi simple makeup, namike na isa gaban wardrobe naciro wata doguwar Riga robal material nasaka, sannan nasaka d'an kwalin a kaina batare da na d'aura ba nafito.

Kitchen nashiga na kunna gas nad'aura ruwan zafi, bud'e karamin Fridge nayi nad'au kifi guda d'aya wanda dakyar na'iya ciroshi saboda kankarar da yy duk sun manne da junan su, acikin roba nasaka nabud'e tukunyar Dana d'aura Kan Gas nasaka Kofi nad'ibi ruwan zafi nazuba Kan kifin,
Bayan 10 second duk kankarar jikin sa yazamo ruwa nasiyaye ruwan, sannan nayayyan Kashi gunduwa-gunduwa nakuma wankeshi tsaf nad'au wata tukunyar najuye ciki, d'aya gefen Gas in nakunnan nad'aura tukunyar kifin nazuba Masa ruwa d'an dai-dai.

Nazuba citta na yanka albasa nazuba kana nazuba kayan d'and'ano sannan narufe,
Ganin alamar ruwan zafinnan yafara tafasa ne,nad'auko flakes nazuba ruwan ciki tareda jefamasa Lipton Mai citta narufe flakes ɗin na'aje gefe.

Nad'ibi taruhu kwalli uku da albasa 'yar madai-dai ciya na jajjagesu,
Sannan nad'ibi kwai guda hud'u nakad'a na juye jajjagen taruhu da al'basan Nan cikin sa,kayan d'an-d'ano nazuba d'an dai-dai saboda kada yayi yawa, saboda idan yy Masa yawa nasan bazai yi dad'iba.

Bud'e tukunyar kifin nayi, saurin rage gas in nayi ganin yy yadda nakeso yanuna luguf ruwan ciki yakafe, juye kifin nayi cikin wani roba Mai d'an fad'i,
Saida nabarshi yad'an wuce yanda zan iya sa hannuna ciki,kasussuwan kifin nacire gabad'aya sannan najuye kifin cikin kwan Dana kad'a namosa,
Tukunyar tuya nad'aura nasulala Mai Saida yy zafi sannan had'in kwai da kifin Nan nazuba ciki,
Haka narika soyawa kamar waina.

Ina gamawa nakimsa gurin, sannan nakwashi breakfast Ina nakaisu parlour,
Ina Zama cikin parlourn naji ana buga kofar shiga Side in Dake ta babban parlour, Ido nawaro sai Kuma

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment