Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin nace
"Nidai inajin magana dan nakiraki na faɗa miki abbu yasiya min waya shine zakice min haka, ko Ummi na ban kira ba ina gama waya da Inna naga Number'n ki kusa da nata shinefa na kira".
Nakarasa cikin ɗan ɗaga murya da gatsali kamar dai yanda kullum idan muka haɗu sai munyi faɗa.

Tace "To an ji ƴar masu baki ko yaushe ne zaki nutsu? Allah yasa ma kina tare da wan da zai gyara miki maza Allah yasa kiyi masa halin ya nakaɗa miki duka".
Baki nakuma turowa nace
"Daga kiran ki sai ki kama yimin sururu toma bazan sake Kiran kiba".
nakatse kiran ina ci gaba da mitar.


Cikin tsananin zakuwa da begen Aunty Rafee'at na danna Number'n ta
bai daɗe yana ringing ba ta ɗaga
sinkayo muryarta nayi daga cikin wayar tana faɗin
"Ah ƴargidan Inna kice dai har wayar tashi hannunki".
Dariya nayi nace
"La Aunty Rafee'at dama kinsan nice?".
Aunty Rafee'at tayi murmushi mai sauti kana tace
"Nasani mana ai ɗazu Abbu yakirani da layin yace min nakine".
dariya nakuma yi dafaɗin
"Ai ɗan ɗazu kaɗan Abbu yakawomin wayar".
tace "Kinji daɗi kenan?" nace "Naji daɗi sosai Aunty Rafee'at".
tace "Ah to madalla lallai yaukam kice waya zatasha danne-danne".
dariya mukayi gaba ɗayanmu.
Cikin dariyar nace
"Aunty Rafee'at kince zakizo kuma bakizoba".
"Zanzo a cikin satin nan, ina fata dai duk abin da nace kirika yin nan kinayi".
ɗan shiru nayi tace
"Iye HAMDAH kinayi kuwa?".
nace "Eh". tace "An ya kuwa?". nace "Allah da gaske"
tace "To har da girkawa Ya SALEEM tea in da nace".
ɗan shiru na kuma yi sai kuma nace
"To zan yi idan yazo zan girka masa".
"Yauwa ko kefa ko bai zobama ki girka ki kai masa ɗakinsa kuma ɗan abin makulashe idan kika girka shima kiɗan rika kai masa ko bai cibama watarana zai ci".

Nace
"Kai Aunty Rafee'at Aunty Na'ima cefa ke yimasa girki"
Tace "Ina ruwan ki da Na'ima ai bata isa ta hanaki girka masa ba kafin ya santa ai ke yafara sani kin fita kusan ci da shi ke dai kiyi abin da nace miki".
To nace.

nan muka ɗan taɓa hira daga bisani mukayi sallama jin an tada salla a masallaci yasani mikewa nanufi bedroom.

Ina shiga na a je wayar saman mirror sannan na nashige bayi ruwa na kunna yafara sauka cikin bath kana nasoma tuɓe kayan jikina ina gamawa nashige cikin bath ɗin da sauri dan na zaku najini cikin wuwan wan da yacika cikin bath ɗin tam.
zama nayi cikin ruwan naɗan ƙwantar da bayana na ɗago kaina nayi pillow da bakin bath ɗin ruwan yakawo min har haɓana.

Lamo nayi a cikin ruwan inajin daɗin yan da ruwan yake ratsa ko ina na jikina wutsilwutsil haka narika yi kamar mai yin iyo cikin kogi, nakai minti 30 a cikin ruwan kana namike na ɗau soso da sabulu wanke jikina koda nagama wanke lungu da sako najikina ruwa na sakarwa kai na daga tsayen da nake ya wanke kunfar sabulun, kana nafito daga cikin ruwan bawai dan nagaji da ruwan ba sai dun ganin lokacin salla natafiya,
nazaro towel naɗaura a kirjina al'wala nayi kana nafita a cikin bayin.

Gaban wardrobe na isa na buɗe naciro zani na kunce towel ɗin naɗaura zanin sannan na mai da towel ɗin bayi nashanya na dawo ɗakin nazura hijabi na shin fiɗa sallaya na tada sallah.

Koda na idar nacire hijabin tare da naɗe sallayar na ajesu ma ajin su,
gaban mirror na isa nazauna,
mai na shafa naɗan murza pauda a fuskata tare da ɗan goga man baki kan lip ina kana namike naje naciro wata doguwar riga robal material mara nauyi nazura bayan nasaka pan da bra,
gaban mirror'n na dawo na feshe jikina da turare kana naɗau wayata wan da duk abin da nake ida nuna na kansa naje bakin gado nazauna naja pillow nakwan ta,
nan nafara latsa wayar.

Number'n Ya Masa'ud na laluɓo nakai wayar kunne na gyara ƙwanciya ta lokacin da naji layin tashiga,
har kiran ta katse ba'a ɗaga ba, kuma mai da kiran nayi harna cire rai da ɗaukar wayar nasa jin wannan kiran ma na kokarin katsewa.

Acan kasar India
Masa'ud ne zaune cikin ɗan ma dai-dai ciyar parlour'n wan da yake masau kinsa,
littattafai ne a gaban sa ya mai da hankalin sa kansu sai dubasu yake,daga can cikin bedroom yarika jiyo sautin ringing ɗin wayar sa,
ture littafan yy gefe yamike tsaye yanufi bedroom
yatako gaban bedside drowar in da wayoyin sa ke ɗaure a kai,
ɗau kar wayar yy tare da zama saman bedside ɗin yy saurin ɗaga kiran yaka wayar a kunne.
fuska ɗauke da murmushi yace
"Kaji manya ƴar gidan Inna".
Baki nawashe jin abin da yafaɗa cike da mamakin yan da akayi yagane nice na kirasa tun banyi magana ba.
nace
"La Ya Masa'ud kai ma kasan nice?".
ya ce "Eh ai Abbu faɗamin wannan layin nakine".

Baki nakuma washewa kana nace
"To ykk ya India da mutanen garin".
Dariya yaɗanyi mai sauti kana yace
"Suna lfy zance kina gai dasu".
Yafaɗa da yanayin zulaya
"To". nace cike da jin daɗi tare da cewa
"Ya Masa'ud har yanzu baka kusa da wowa ba?".
Yace
"Nakusa in Allah ya yarda".
Nace to kakawo min tsaraba".
"Bakida matsala jaka guda zan ciko miki na tsaraba amarya to ya Yayan namu yake?".
Baki natura nace
"Nidai kabar cemin a marya ba kai ne kaki da wowa ba ai da ma Inna tace da kai za'a mana aure gashi kaki zuwa ammana da Ya SALEEM".

Dariya yy kana yace
"to ai dani da Ya SALEEM ɗin duk ɗaya ne"

Da sauri nace
"A'a kam ai kai kana dariya shikuma bayayi kullum yayita ɗaure fuska kamar dodo nidai idan ka dawo zancewa Inna amana auren da kai kawai".

Kai ya jinjina tare da mikewa yazo bakin gado yazauna
yana mai cigaba da dariya haɗe da zallar shauki da jin-jina shiririta irin na HAMDAH kodaga maganar ta zaka gane ɗin bin yarin ta tattare da ita,
yace
"To ai mace bata auren maza biyu a lokaci guda kuma nan gaba zakiga yana miki dariyar, ina dai baya dukan ki?".

Kai na gyaɗa kamar ina gaban shi kana nace
"Eh ai Inna tace duk ran da yabigeni sai tasa Abbu yabigeshi shima".

Yace "to kin ga bazai ma faraba tun da yasan idan yabigeki shima dukan shi za'ayi".

Dariya nayi har da buga cinya sai kuma na rike haɓa naɗan waro ido ina ɗan girgiza kai nace
"Cab Kato dashi ai sai dai Abbu yaɗau katon bulala in ba haka ba bazai ji zafi ba ko Ya Masa'ud?".

Yace "ai dama babban bulala zai ɗauka yan da zaiji zafi sosai".

Kai na jinjina alamar gamsuwa
Hira sosai mukayi da Ya Masa'ud sai dariya muke dan shi Ya Masa'ud bashida ɗaurewa.
Nan yace min yana karatu ne idan yagama zai kirana mukayi sallama na sauke wayar.

Yau kowa sai da yasan an siyamin waya dan ina katse kiran Ya Masa'ud Ummi na kira muka gaisa har da Fauzan.
Sannan na kira Mamei ita ma muka gaisa nasa tabawa Nusaiba.
Abba ne kiran karshe daganan na aje wayar gefe na gyara ƙwanciya ba jimawa bacci ya ɗaukeni.

Ban far kaba sai wajen karfe 5 alawala nayi nazo nayi sallar la'asar koda na idar nafito parlour na nufi kitchen, abinci mai saukin dahuwa na girka taliya ce miyar jajjage
ina gamawa nazuba wan da zan iya ci cikin plt sannan nafito parlour, TV na kunna kana nazauna nan tsakiyar parlour'n Ina cikin cin a bincin a ka kira sallar magriba, bayan na gama naɗau plt ɗin na kai kitchen nawan keshi kana na Mai dashi mazau ninsa sannan nafita na koma ɗaki.
Wanka nashiga ban wani jima cikin bayin ba nafito dan ban tsaya wasan ruwa ba yanzu, wata riga da wandon bacci na ciro nasaka rigar takai min har guiwa wandon kuwa dogone har kasa, sai hula mai raga dana murza a kaina.

Kasan cewar nayi alawala sai na shinfiɗa sallaya nazura hijabi nagabatar da sallar magriba ban tashi kan sallayar ba har sai da nagabatar da sallar Isha.

A ɓangaren Ya SALEEM karfe 6 yadawo daga offece koda yashiga bedroom in sa rage kayan jikin sa yy yafaɗa bathroom wan ka saosai yy da ɗan ruwa mai zafi dan son cire gajiyar daya ƙwaso.
Na'ima ta turo kofar tashigo jin motsintsa a bayi sai tafi takoma ɗakin ta dan dama waya take da wata a miniyarta jin da wowarsa ne yasa akatse wayar nan suka ci gaba da wayar su.

Shiko SALEEM ko da yafito wata farar tattausar jallabi yazura yanufi masallaci da sauri jin an tada salla,
da misalin karfe 8 yashigo gidan ta kofar side in sa ta baya yashiga batare da yabi ta babban parlour ba, yana shiga ɗaki ida nunsa suka sauka kan laidar da Abbu yabasa ɗazu zuwan sa yace yabawa HAMDAH,
ɗan guntun tsaki yaje har ya juya zai haye gado sai kuma yakuma juyowa ya isa in da ya aje laidar yaɗauka tare da kuma jan wani tsakin yanufi kofa,
takofar da yashigo tanan yafita yanufi kofar side ɗin ta dake tanan parfajiyar gidan.

Yatura kofar yashiga asannu yatako cikin parlour'n babu kowa sai tv dake tafaman ai ki shi kaɗai,
ɗan tsurawa tv'n ido yayi ganin wani Amirican Film in da a ke haskowa.

Mikewa nayi zaune jin karar buɗe kofar da akayi a sannu nazuro kafafuna kasa namike tsaye natako bakin kofa buɗe kofar nayi a hankali naɗan leko kaina ganin shine a tsaye saina karasa buɗe kofar nafito na tsaya nan bakin kofar.
ɗan juyowa yy yakalleni sai kuma ya mai da idanunsa kan tv'n,
a hankali na juya zan koma ciki na najiyo muryarsa cikin faɗa
"Ok komawa zaki kibarni rike dashi sabo da ni ɗan ai kenki niko".
cak natsaya tare da juyowa na kalle shi sai kuma na kalli hannunsa jin ya ambaci rikewa
"To in banda abin shi taya zanyi nasan wani abune tafe dashi tun da ba faɗa yayiba ko Allan musuru gareni da zan sani".
Baki na turo "shidai kullum a masifa zai kare".
Nafaɗa can kasan makoshi ina takowa in da yake,hannu na mika na rike lai dar da nagani rike a hannunsa, wan da nafi tunani shi yake nufi nabarshi da shi rike, ina rike lai dar yasake da sauri na daɗa rikewa dan tun kan na ida rikewa yasake kaɗan yarage yasuɓuce kasa,najuya nanufi ɗaki.

Shiko gyara tsayuwar sa yy yayin da ida nunsa ke kan tv,sai kuma yaɗanyi baya kaɗan yazauna saman kujerar dake bayan sa sosai ya mai da hankalin sa kan suburbuɗar da a ke da bindiga a cikin TV'n.

Ina shiga na isa bakin gado nazauna nafara buɗe laidar wani ɗan ma dai-dai cin ƙyaƙƙyawar kwano ce mai murfin glass a ciki,
naciro shi daga jikin murfin ina iya hango abin da ke cikin ƙwanon,
da ɗan saurina nabuɗe marfin wani kamshine yabigi hancina na haɗiye miyau daya taru cikin bakina,
Lafiyayyiyar dambun namace wan da yaji kayan kamshi da ɗan-ɗano sai fidda wani kamshi na musamman yake,
ɗebuwa nayi nakai baki dan na gama zakuwa najishi cikin bakina a sannu nashiga tauna shi yayin da da ɗin ha ɗeɗɗiyar danbun naman ya gauraye cikin bakina,
Ko ba'a faɗa min ba nasan wannan haɗin na Mamei ce.
Aje ƙwanon nayi gefe na mike da sauri nafita dan naje kitchen na ɗauko plt.

Ina fita naɗanyi turus a bakin kofa hangoshi zaune kan kujera yaɗan ƙwanto da bayansa ya jingina da jikin kujerar hannayen sa kuma suna sakale a bayan keyarsa yayi pillow da su.
Mayar da dubana nayi kan TV'n daya kafe da ido sai ai kin harbe-harbe da naushe-naushe suke.
Asannu nanufi kitchen har na ɗau plt ɗin zan juya sai kuma na tsaya tare da ɗaura yatsata kan kumatu alaman nazari
"Yauwa tun da gashi yazo bari na girka masa shayin da Aunty Rafee'at tace".
gaɗa kai nayi alamar gamsuwa da zancen zucin da bake Nan take na ɗaura tukunya nazuba ruwa kofi ɗaya da ɗan kaɗan naɗibi ganyen na'ana'a nazuba sai ƙwayan citta guda biyu da ɗan kanumfari shima baisfi silli huɗu ba nawa ciki na kunna wuta.
Ina nan tsaye ruwan ya tafasa kasan cewar ruwan bashida wani yawa ɗan barinsa nayi yakara tafasa saboda kayakin da ke cikin sa suɗan nuna,
Zuwa can na kashe wutar nasauke na tacesa cikin cup ƙwalbar zuma na ɗauko na siyaya cikin cup ɗin kana nasa spoon na mosa, naɗau ƴar karamar tray na ɗaura cup haɗe da spoon akai kana naɗauka nanufi parlour'n.

In da na barshi a haka na taddashi a sannu natako in da yake naɗan sun kuya na aje tray'n saman table in dake gefe da kujerar da yake kai,naɗago da niyyar ce masa ga tea na kawo masa, sai kuma nayi shiru ido naɗan tsura masa ganin yan da yabaje kan kujerar ƙafarsa ɗaya yana kan kujerar yatan ƙwashe sa ɗayan kuma yana kasa har lokacin hannunsa nanan in da yy pillow da shi ta bayan keyar sa.

Sosai na zuba masa ido nan take zuciya ta tafara tunano min Film ɗin damuka kakalla ni da Rabi a wayan Ya Maheer wato yayan Rabi'n.
Ahan kali na lumshe ida nuna sai gashi kamar yanzu ne nake kallon, murmushi ne yasuɓuce min
"Ai sai na gwa da yan da ake soyayyar nan".
nafaɗa a hankali saman lip ɗina,
Ido na buɗe kansa sai kawai nafaɗa jikin sa nasau ke hannuna kan.........



*Sai kunyi hakuri nasan zakuga typing error ban sami damar editing ba*


*Page biyu na haɗa muku nayau da gobe🤗*



Mommyn Twins ce




*🌺HAMDAH🌺*

*NA*

*RASHEEDA S DIRECTOR*


_(Book one)_


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*


MARUBUCIYAR👇🏻
*BA ABIN DA BAN GANI BA*
*INA SANE DA HAKA*
*ALFARMA*
*BAZAWARA CE ITA*
AND NOW👇🏻
*HAMDAH*



*Free page*


My no 08034690723



🅿️9


Na sauke hannuna ɗaya kan faffaɗar kirjin sa ɗaya hannun kuma nacusa ta bayan sa sakanin kujera da bayansa, babu zato babu sammani yajini nafaɗo jikin sa, wani numfashi ya sauke wan da sai da nayi sautin sa.
niko daɗa cusa hannuna nayi sosai ta bayan sa na kanainaye shi
yayin da nadaɗa kife hannuna kan tanfatsetsen kirjin sa,
kasan cewar yana ɗan kishin giɗene hakan yabada dama wajen dai-dai tuwar
fuskar mu.

Cikin wani irin tarin mamaki yake kallon fuskata dake daf da nashi kallo ne mai cike da zallar mamaki da al'ajabi, kamar wan da a ka zabura yariko kafaɗata yacironi a jikin sa tare da hangizani nafaɗi kasa,
Dasauri namike tsaye ina wiki-wiki da ido dan naji zafin faɗuwar, a zafafe yamike tsaye cikin tsananin fushi da kunar zuciya yake bina da wani irin kallo mai ɗauke da masha huriyar zallar mamaki,
Niko ɗan tura baki nayi gaba,
cikin tsananin ɓacin ran da yake ciki yanuna ni da yatsa cikin murya mai nuna zallar fushi yace
"Ke meye hakan?baki da hankaline!".
Yafaɗa cikin tsawa da yasan yani zabura tare da ɗan ja baya,wata tsawar yakuma bugamin tun kan na dawo da nutsuwata gareni.

Baya nashiga ja ganin yana ɗan matsoni cikin zaro ido da tsoron ganin yanayin sa murya na rawa nashiga faɗin
"Ya SALEEM soyayya nefa".
cak yaja yatsaya tare da nanata kalmar da karfi yafurta
"Soyayya?!!!".
yafaɗa ida nunsa a kaina fuskarsa ɗauke da zallar mamaki.
kai nashiga gyaɗa wa cikin muryar tsoro ganin yan da yaketa matsoni nace
"Ai a wayan yayan Rabi muka kalli soyayyar kuma ai suma haka sukayi."

Ido yadaɗa tsuramin a hankali yake ɗan gyaɗa kansa a lamar zallar mamaki,
sosai yatsura min ido kamar mai son karan tar wani a bin
kallone mai cike da da mamaki da kunar rai wani tsawa mai firgitarwa ya dakamin cikin ɗaga murya yace.

"A wayan yayan Rabi kuka kalla!?".
Yayimin tanbayar cikin tsawa da karaji,
Kai na gyaɗa tsoro fal cikin raina da fuskata gaba ɗaya.
Yace "Iskanci! iskanci kike kalla a wayar nasa sexx yake baki kike kalla a waya!!".

Kai nashiga gargizawa ina cigaba da ja da baya ganin yana kuma matsoni cikin kuma ɗaga murya yace
"Idan ba iskanci ba ne uban me kuke kalla cikin wayar nasa!".
Cikin firgici da tsoron ganin yanayin sa yan da fuskarsa ke daɗa juyewa izuwa na bantsoro nace
"A'a wlh ba iskanci bane soyayya ne wlh soyayya nagani ba iskanci ba, na rantse Ya SALEEM ba iskanci nakalla b.."
Wani irin gi-gi tacciyan mari ya ɗauke Ni da shi da yahanani karasa fursa sauran kallamar b. dana furta, dafe fuskata nayi tare da kurma kara mai karfe kai nashiga juyawa wani irin duhu ne ya gilmamin, dumm haka kunnena ke bada sauti, ga wani irin a za bebben zafi da raɗaɗin da fuskata keyi tam kar ruwan zafi yawatsa min kan fuskar.

Hannu yamika yana kokarin rikoni yana ci gaba da faɗin
"Iskanci kika soma a she har a bun naki ya girma?!".
juya wa nayi da gudu nashige ɗaki na mai da kofar da karfi narufe.
yaɗaga kafa zai bita sai kuma yaja yatsaya ganin tana murza key,
tsayuwar sa yaɗan gyara tare da tsurawa kofar ido kana yarike kugunsa da hannu ɗaya ɗaya hannun nasa kuma yacusa cikin sumar kansa tare da shafa sumar kan nasa zuwa bayan keyarsa,
Iska mai zafi yafurzar da ga cikin bakin sa.

Dogon tsaki yaja kana cikin fusa tacciyar murya yace
"Ina ga irin ta,wancan fitinanniyar tsohuwar can ta matsa wai sai an bata waya to ina gashi tun kafin a bata wayar ma taje
tana kalle-kallen banza da na hofi bare kuma yanzu da
a ka batan,wai a hakan ne take cewa wai tayi mata tarbiyyan ina tarbiyyar anan".
tsaki yakuma ja
yajuya rai ɓace yabar parlour'n.

Nafi minti 20 ina kife da fuskata a jikin pillow tun bayan shigata ɗaki, kuka sosai nake har lokacin fuskata bata
dai na yin zugiba,
Haka nata kuka na daga bisani nayi shiru dan kai na sai
sauke ajiyan zuciya nake a haka har bacci yasami
nasarar ɗaukata.

Washegari da misalin karfe 9 na farka daga baccin dana koma bayan danayi sallar a suba, zamowa nayi bakin gado
A hankali na zuro kafafuna kasa hannu na ɗaga nashafi fuskata gefen da yamare ni jiya,
jin kamar shatin hannunsa jikin fuskar sai na mike tsaye nazo gaban
mirror, kallon fuskata nayi daga cikin mirror'n da har lokacin shatin hannunsa nanan ƙwance,
Baki na turo baga nasaka yatsata ina bin shatin yatsunsa uku da ke ƙwance gefen fuskata dasu basu ɓace ba har lokacin.

"Allah ya isa kuma Allah in yasake taɓani sai na faɗawa Inna tahaɗa shi da Abbu shima a masa dukan, ko imani bayi da shi mugu mai fuskar dodanni".
Nafaɗa tare da juyawa na nufi kofa parlour naje na share haɗe da gogewa duk da bawani datti yayi ba,
na komo bedroom ɗin shima nagyara kana nashiga
bayi
Natuɓe kayan jikina nacika bath da ruwa nashe ciki,
Sai da nayi wasa da ruwan ma ishi kafin nayi wankan nafito.


Nashirya cikin wata riga da sket na atamfa kayan yazauna ɗamas a jikina ɗan ƙwalin kayan na coke shi a kaina kana na ɗau wayata nanufi kitchen,
tea na haɗa na dawo parlour
Ina gama yin breakfast in na janyo wayata nasoma game.
Sallama akayi daga kofar babban parlour a ka turo kofar,
Amsa wa nayi tare da ɗago kaina dan ganin mai shigo war
Rufa'ila ce wacce take yiwa Aunty Na'ima wanke-wanke da shara takara so cikin parlour'n ta ɗan sun kuya gefe tace
"Barka da safiya".
"Yauwa" nace
Kai ta ɗan rusunar tare da cewa
"Wai kizo in ji Hajiya". Kallonta nayi da niyyar in tanbaye ta wace Hajiyar sai wayata tafara ringing sai nayi saurin juyawa naɗau wayar wacce na ajiye shi lokacin da tashigo,
itako Rufa'ila mikewa tayi takoma, kallon Number'n da ake kirana da shi nayi Number'n ne basuna ɗaukar kiran nayi nakara a kunne tare da yin sallama.
muryar goggo Hauwa nayi tana amsa sallamar cikin matukar murna nace
"La goggo Hauwa".
Sai kuma nasa dariya, itama dariyar tayi cikin muryar da riya tace
"HAMDAH manya ya kuke ya gidan".
Lfy lau nace,kana na ɗaura da faɗin
"Goggo Hauwa kina gidan Inna ne?". tace
"A'a jiya naje gidan shine ma na amshi Number'n ki a gunta". Kai na jinjina nace
"To ke yaushe zakizo Bauchi'n?".
tace
"Ina nan tafe insha Allah zamuzo da Inna". Nace "To Allah ya kaimu". nan mukayi sallama na aje wayar, juyowa nayi sai banga Rufu'ila ba, bin kofar babban parlour'n nayi da kallo to wace Hajiya ce ke kirana.kawar da kai na nayi kamar bazan tashiba sai kuma na mike nanufi kofar parlour'n.

Natura da sallama nashiga babu kowa
cikin parlour'n ɗan ware ida nuna nayi ina bin parlour'n da
kallo, can na hango Na'ima zaune saman kujera ta ɗaura kafa ɗaya kan
ɗaya sai wani kaɗa kafa take,
ɗan jim nayi tsaye ganin banga wani cikin parlour'n ba sai ita sai najuya ina kokarin komawa.

Tace "Ke bata ce miki ni nake kiran kiba ne kin ganni kuma shine zaki koma".
Baki na taɓe tare da
Juyowa nakalli in da take, daga in da nake tsayi nace
"Gani".
sauke kafarta data harɗe ɗaya kan ɗaya tayi kasa kana taɗau tsintsiya da ke a je a gefen ta tawurga min a dai-dai kusa da kafata. tace
"Ɗau tsintsiyar nan kishare min cikin parlour'n nan".
Ido na ɗan waro
"Shara".
na furta da muryar mamaki, tace
"Eh kishare ki goge yanzu nan".
Kallon tsintsiyar nayi sai kuma nakalli katon
parlour'n da take cewa na share shi
"Cab ni wlh bazan iyaba haka kawai ni ban ɓataba a ce in share
to ai ko Inna da take sani na yi shara ma cewa take mun ɓata tare,
idan ma bana gida natafi makaranta ma bata cewa nayi dan tasan ita ɗaya ta ɓata dan haka ni ɓan ɓataba bazan gyara ba".


Nafaɗa cikin muryar kunkuni najuya ina kokarin barin gurin.
Ina juyowa karaf muka haɗa ido ɗan tsunkuyar da kai na kasa nayi ganin yan da fuskar sa ke ɗaure tamau,
daɗa suke fuska yayi a sannu ya idda fita daga cikin corridor ɗin side ɗin sa, cikin shigar kananan kaya sai baza kamshe yake, gashin kan nan nasa yasha gyara sai sheki da ƙyalli yake,
"Zaki ɗauka ne ko yaya".
da sauri na ɗago jin a bin da yafa ɗa,
Wani mugun kallo ya watsamin ba shiri na sun kuya naɗau tsintsiyar ina kun-kuni kasa-kasa,
Shiko wuce wa yy yanufi kofar parlour da sauri tamike tabi bayan sa,
tana wani karairaya tana wani karkaɗa mazau nan ta
tace
"My SALEEM har kafito kenan da ma yanzu zanje natayaka shiri a she dai har ka gama."
tafaɗa dai-dai lokacin da ta isa in da yake tawani riko hannunsa tana manna jikin ta da nasa.
Komai bai ceba sai zame hannunsa da yayi yabuɗe murfin kofar yafita tabi bayan sa.

tsaki naja dan ba kar ya nacika har wuya ko hutawa ban yi da gyaran side ɗina ba awani kakabamin wani,
In badun yace nayiba ba a bin da zai sa nayi tun da ga mai ai kinta,
fara sharar nayi daga in da nake haka narika sharan fayau-fayau ko in ce zane dan dai bawani sharan kirki nayiba in share nan ne in sallake can, a haka nagama nayi wurgi da tsintsiyar.
najuya abina zan shige sai gata tashigo tace
"Ke dawo nan ai baki gama ba sau ra mopin".
Kallon kofa nayi da kyau kana najuyo gare ta dan ina da tabbacin yanzu kam yatafi nace
"Nifa nagaji ki kira mai ai kin ki tamiki mana".


Karaso wa take cikin parlour'n tana faɗin
"Lallai yarin yarnan kin cika fisararriya to na rantse sai kin yi, ai middin kina cikin gidan nan to yazama dole kiyimin ai ki
Nan gida nane sai abin da nace a yi za ayishi".

Haɓa narike da mamaki nace
"Oh a she Ya SALEEM ya tsai da miki gidan ne amma dai iya nanne ban da tacan ko?".
Nafaɗa ina nuna tagefen part in da nake.

Ido ta gwalalo cikin masifa da kumfar baki ta ce
"Kutumar uban can ni zaki faɗa wa haka
to bari kiji ba gidan nan kaɗai ba har shi SALEEM ɗin ma nawane,
yazama dole kiyimin biyayya dan ni ba sa'ar ki bace, idan kuma wasu ke
zugaki to ki dai na yau da rar kanki har a bada bazaki taɓa zama matar gidan
nan ba, na barki ne kizauna cikin gidan nan a matsayin kanwar mijina ba mata ba badun haka ba da najima da shafe babin ki,
Kinsan meyasa kike numfashi har yanzu a duniya? saboda SALEEM bai nuna wata kulawa irin na mata a kanki ba,
ke kanwar sa ce kisa hakan a ranki har gaba da abadan".

Baya narika yi dan gani nake kamar

3 Comments On HAMDAH
avatar
zarrah

1 year ago

Reply

Amazing story

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to zarrah

Thanks for your feedback

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Littafi

Please Login or Register in order to submit comment