Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake fidda sauti mai dadi tace.
"Ur highly welcome drinker guy."
Ta fada tare da saka duka hannayenta biyu tana tallabe da flower ta mika masa,tana sake nitsar da idonta cikin nashi.don yana isowa ya jare glass din.
Wani dakikin murmushi ya sakar mata,yana tsareta da kyawawan idanunsa ya juya gefensa yayiwa yaronsa guda nuni da flower hannunta yace atakaice"take this john."
Zuwa yayi zai ansa ta janye daga garesa tana dan matsawa daga garesa cikin kallon banza tace"ai bashi na kawo ma wa ba,bacin haka taya zan rike abu arene ya rik'e it's not possible."
A bun mamaki da al,ajabi dariya suka gayi yana isa wajen john yana dafa kafadarsa cikin nishadi yace"kina kyamarsa ne?"
Juyar da kai tayi gefe tace"fadi bacin baki."
Jinjina kai yayi yana ciro hankcif daga aljihunsa ya nade hannun sannan ya isa gareta kamar zai koma cikin cikinta yana kallon cikin idonta yace"tunda kin matsa saina ansa ba laifi,asar yayi yana gogata ga fuskarta,muryarsa kamar yana rad'a yaci gaba da magana still yana gogamata flower ga fuskar,hakan yasa mata tilas runtse idonta don karya tsole mata shi.
"toni nafi kowa kyamarki,dana ta6a abunda kika taba gara naci abinci da wancen da kike kyamar,kin ga kau su basa tsarki amman na gwammace hakan.saboda kinfisu datti."
Wadannan kalaman na Abdoul sun rushe mata duk wani juriya da take ciki,sun narkar mata da zuciya ta yadda har takejin d'acin su akan halshenta,hawaye suka taro tab cikin kwarin idonta ta rasa yadda za tai ta mayar dasu.......saboda kalaman sa suyi nasarar jefa zuciyarta cikin kunci sai taji inama dukanta yayi basu ya gaya mata ba,ashe daman akwai kalaman da zakaji gara ayita dukan ka da agaya maka su..........murmushi ya saki ganin yayi nasarar cusa bakinciki cikin ranta,kila ta fita daga rayuwarsa yanzu ya samu weakness dinta,dungure mata kai yayi saboda yadda jikinta babu kwari saida tayi taga taga zata fadi,kafin taci nasarar tsayuwa daker........tunda suka iso wajenta malik yaja gefe wajen mota yana kallonsu,da farko yaga kamar za,a rabu lafiya har yana murna ........sai kuma yaga abun ya cakude.
Har Alfah yakai jikin mota anbude mashi zai shiga yaji takunta bayansa,tsaya wa yayi bai juyo ba cikin raunin murya wadda da kaji kasan kuka kiris yake daya subuce mata tace "Duk mutumin dake fifita kafiri akan musulmi yayi asara ba yar karama ba,kuma wannan mutumen ya cancanta duk wanda yake tare dashi ya nisancesa,sai akai sa,a bayan fifita kafirin mutun da kayi akan musulma. ka kasance wanda Annabi ya tsinewa ya la,ancesu don duk mashayin mutun wanda keshan abunda zai gusar masa da hankali Allah yana fushi dashi.kuma Annabinsa ya tsine masu,kaga kuwa wannan ba baurgewa bane asarace ta sameka kuma ina maka fatan Allah ya shiryeka.don Annabinmu yayi mana hani da la,antar la,ananne saboda zai sake lalacewa don haka ina sake maka addua Allah ya shiryeka,ya maidoka hanya madaidaiciya in kuma baka shiryuba Allah yayi mana tsari da kai da masu take maka baya."

Malik daskarewa yayi a inda yake tsaye,don ba ma Abdoul ba shi kanshi malik kalamanta sunyi bala,in daure masa kai ya kuma ji dadi data rama don aga yau zaisa cewa idan baki yasan me zai furta bisa me za,a maido masa ba.
Idanun Abdoul sunyi jajawur har fuskar sa saida tayi jaa saboda yadda ransa ya b'aci.......tabbas ya san kalamanta gaskiyane akan sa,amman ba wai ya furta mata haka bane don hkan yana nufin har cikin ransa ba,aa don ya kuntata mata zuciya yadda take masa,amman sauran kalamanta dasuke nuni da cewa giyar da yake sha sunyi mashi tsayuwar giginya cikin ransa.....inama zai iya gaya mata cewar rabonsa da giya tun anan kasar,inama zai iya shaida mata yabar shanta amman yadda yakejin zafin kansa bazai iya sanar da ita ba,hakan yana nufin kamar yana tsoronta kamar ya ji zafin zagin da take masa ne ya daina,bacin tsoron Allah ne yayi masa kwaranya lokaci guda.duk da hada gudun mawar kalamanta ayadda yakeji yanzu bazai iya ce mata komi ba kuma bazai iya kai hannunsa jikinta da sunan duka ba,ya ma rasa ta kamaimai abunyi don kuwa yadda mutane ke kallonsu idan yace yadauki action to sunan sa sake baci zai,kuma ba hakan yaso.
Lumshe idonsa yayi na seconds ya bude ya sake xuba mata su yayinda kwallarta ke mata zarya kan kuncinta........duk tsirarun mutane kallonsu ake sai yayi anfani da wannan damar ya isa gareta kamar zasu zama abu guda.
Sunkuyowa yayi sosai daidai fuskarta abun mamaki da al,jabi da kuma rud'ani jitai halshensa yanabin kuncinta har zuwa saman idonta,dayan gefen shima yayi masa haka........cikin rudani da tsoro ta ja baya afirgice yayinda mutanen suka fara bajewa,daman haka ya keso kurin sai juyawa yayi yabarta nan tsaye kamar gunki.......daman malik na ganin haka ya shige mota maimakon naga canjin yanayi da nuna haushi akan fuskar mali,sai naga murmushi mai kyau akan fuskarsa.ya shiga yazauna ya kwantar da sit din gaban ya silale ya kwantar da bayansa da kansa,idonsa rufe ruf.
Jin malik yatashi motar yasa shi magana batare daya iya bude idonsa ba .
"Kasan nan zaka barta meyasa kazo da ita?"
Daman haka yake jira ya bude motar yafota ya iso wajenta magana zai mata ta juya ta barsa wajen.
Gudu gudu sauri sauri haka take hadawa don isa inda zata samu abun hawa...........jitai kamar tana bisa iska zuwa sadda zata dawo cikin hayyacinta saidai tajita anyi jifa da ita cikin mota.........sannan suka tafi.
Wai ashe Alfah ne yabiyita yadaukota kamar yar tsana yasata motar,don yayi imanin kafin ma ta isa inda zata samu taxi sai kafarta ta kusan cirewa don ciwo........shiyasa kawai yaje yadaukota don idan suka tsaya janjani zata bata masu lokaci,shiyasa kawai yayi mata haka.
Kuka ta fashe dashi don tama rasa me zatayi tama hana zuciyarta yin wani tunani ta kuntace ta waje guda,babu mai magana amotar don su ukune yaran sa sun wuce company da kayan d suka duko.
Sutin kukan kurin kakeji mai cike da bakin ciki kafin ta gaza jure k'un cinta take cewa.
"Allah ya isana ban yafe ba mug.........kasa idasa mugun tayi tana shashshekar kuka Alfah dake gaba kwance idonsa lumshe jinta kurin yake murmushi yayi mai sauti har saida malik ya juyo yana kallonsa,
"Malam Kalli gaban ka karka zubar damu."
Dole malik ya kauda kai don shi yau Alfahn duk ya zamema sa kamar wani sabon mutun.
"Haka kawai ka samun wana kazamin bakin naka mai shan giya,gashinan ji nake kamar zanyi amai wlh kaida Allah ban yafe ba."
Sika sakejinta tana fadar haka.
Bai motsa ba yace"naga dai alamar giyar nan sonta kike kina sha,awar d'an d'anawa karki damu zan baki kisha."
Bata sake magana ba har suka isa gidan su Malik,don babu abunda taki jinin ji daga garesa irin yace zai bata giya,tasan kadan daga cikin aikinsa ne tsaf zai danneta ya dura mata ita.wai Allah da tashiga ukunta kau.
Fitowa tayi tana sharben majina ta wuce titi bata saurari kowa ba ta tari taxi ta wucw gida.........koda taje anty tace ta huta tayi masu girkin dare cewa tai bata da lfiya,dole sai Mai aikinsu ce tayi masu.

Mrs bbce
Mom muhseen
09034722970.
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ..........

Wannan dare safiyya bata iya runtsawa ba ta tayi kiskuren runtse idonta sata ganshi yana lashe mata kumatu,dandanan zata ji tsikar jikinta tatashi tayi zunbur ta tashi zaune ta rabka tagumi..........ga baccin yana cinta amman bata son ganinsa cikin baccita,meyasa ya tsaya man garai ni fiyah?meyasa wulakancin sa bai tsaya man sosai irin yadda salonsa ya tsaya mata ba.hatta kayan jikinta yau ta gagara musanya su saboda kamshinsa dake jikinsu,dandanan Allah yasa mata kaunar turaren.daga ta mirgina can saita mirgina can har dai mulmulowa tayi kasa bata ma san tayi ba saida tajita tim kasa.........dafe kai tayi tana mamakin kanta wai meke damuna ne yau,akan wancan dan rainin hamatar na ke duk wannan,aa ba zai yuwuba shidin banza da wofi wlh saina yi baccina yau insha Allah.
Koma wa tayi kan gadon tana sake wata adduar tana gama wa ta tofe ko ina ta shafe jikinta ta kwanta.
Duk yadda take dambe da zuciyarta abun yaci tura,amman haka ta daure ta runtse idonta gam da tsiya sai baccin ya dauketa.
Ganin babu sarki sai Allah yasa tatashi tayo Alwallah tazo ta fara sallah,saida tayi raka,a shidda sannan tadauko qur,anin ta tafara jero karatu cikin tsantsar tajwidi.........saida ta shafe akalla awa daya da rabi sanan ta ajiye ta koma ta kwanta.......dan danan baccin yazo ya sureta.

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Tunda suka shigo ya wuce ya watsa ruwa sanan yyi sallar magrub a cikin dakinsa yunwa yakeji da gajiya baison yin magana kwata kwata yanzu,soyake ya kwanta yana bukatar tunani.
Yasan malik inzai shigo zai taho masu da abinci tunda kukun nasu baya nan.
Kasa ya kwanta yana filo da hannayensa idonsa rufe kafafunsa ya dora su bisa wani dan table,yayi crossing dinsu yana girgiza guda.

_haka kawai kasa mun wannan qazamin bakin naka mai shan giya gashinan ji nake kamar zanyi amai wlh.kaida Allah ban yafe ba_

Murmushi ya subuce masa mai shegen kyau,har fararen hakoransa kyawawa suka bayyana.
Kafin Annurinsa ya fara b'acewa saboda kalamanta na farko.
_ur highly welcome drinker guy_

Runtse idonsa yayi yana jin zafin kalamin cikin ransa,tabbas yasan ankirasa da wadanda sukafi wadanna ada bama da ba har yau akwai masu yi mashi wannan kallo,amman zuwa sadda ya rikice ya daina jin zafi da dacin kalaman shine lokacin da ya kulla damarar shanta.daga lokacin baya jin haushi baya jin radadi don ance masa mashayi.........ammman yanzu da yaji din rad'in kansa ya barta bari na har abada,sai yaji kalaman basu dace dashi ba,Allah shike ganin zukatan bayin sa amman yasan badan wannan yarinyar yabar giya ba,saidai yasan cewa kalamanta suntaka rawar gani wajen taimaka barinsa da ita,don tunda yaje Australia daya shata ma sai yayi amai kuma sai yayi masassara,lokacin ya dan gana da asibiti don radin kansa wanda shi knsa yayi mamakin ganinsa gaban likita wai ya kawo kansa,bacin kullum hanyar da zata lahanta rayuwar yake nema.
Amman baisan meyasa yanzu yakejin yashirya yin rayuwa mai kyau koda shokadaine cikin duniya,yaji haushin kansa lokacin da dr yohana yake gaya masa cewar wine din takai limit din da bata kara iya daukar hunhunsa,saboda ta mashi rauni a wajen wanda muddin ya sake yasha ta ko yasha lemo mai gas yana iya rasa ransa,haka zalika ya hana shi shan abu mai zafi sosai da kuma mai sanyi sosai,don zasuyi mashi lahani........sannan abun daya sake bashi mamaki da haushin kansa wai arne da baisan kansa ba wanda bai yarda da Allah da manzon sa ba yake mashi nasihar zaman duniya,da kuma abunda zaiyyi maikyau da marar kyau.
Ranar yayi kukan da tunda yabar gidan iyayensa baiyyishi ba,yayi nadama da dana sani yafi akirga,saida ya kwana biyu baifita ma aikin daya kawoshi ba.
Mafarin ya fara ansar magani daga shi dr yohanan yace masa duk bayan wata uku yazo aduba shi don zai iya yuwiwa amai aiki,idan kuma yana warkewa to basai anyi aikin ba......duk sanda ya tuna wannan lamarin saiyaji kansa yana sarawa,hakika yayi sake yabari shaidan da sherin zuciya sunyi galaba akansa.meyasa abunda ake masa kallo dashi bayyi yunkurin kiyaye kanshi dashi ba,yanzu kenan da Allah bai sa ya bar sauran shaye shayen dayayi ba Allah kadai yasan abunda zai faru da rayuwarsa.da mezaice ma mahaliccinsa baida bakin da zai iya kare kansa.
Hawaye suka silalo mashi yaji wata kaunar malik ta cika mashi zuciya,tabbas malik abokine na musanman duk wanda yasamu aboki amini irinsa yadace yayi dacen da har tutiya ma inyayi babu laifi.
Don yasan irin wuyar dayasha kafin ya rabashi da sauran kayan mayen.sannan binciken dayasa akai mashi ya nuna mashi cewar shine ya kawo wannan yarinyar cikin rayuwarsa,don ta taimakeshi yadawo dashi daidai..........meyakai wannan arayuwa inda wanine fita sabgarsa zaiyi yaje koma me zayyi yayi aiba dan uwansa bane ko wami nashi.........wannan dalilin yasa yaji zuciyarsa tayi sanyi tayi cool dinda baisan rabonsa dajin haka ba,yaji natsuwarsa na dawowa yaji happenes dinsa cikin kaso dari kashi arba,in yana dawo wa jikinsa da ruhinsa.dalikin kenan yasa ya nuna masu canjin da suke ta fafatukar nema shida wannan yarinyar da baisan sunan taba har yau.
Kuma yyi kudurin basu goyon baya har sadda zai idasa dawowa normal,insha Allah bazai sake daga hannu da sunan duka gareta ba,don tana yin komene don yaji haushi yabar abunda yake,kuma sunyi nasara kuma suna kan yin nasara.
Amman alwashin sa guda daya dauka shine koda gaskiya ta bayyana tsakaninsa da iyauensa bazai sake komawa cikin zuriarsa ba,don kozai manta komi bazai iya manta wa da irin tozarcin da yafaru dashi ba shekara ta shidda kenan.
Sun bata mashi suna ga duk mutanen dake masankallon nagari kuma natsatstse,tome ma zaije yayi masu baida zuciya kenan.........."Abdoul!!!"
Muryar malik ce ta dawo dashi daga hayyacinsa,goge fuskarsa yayi dake ta hawaye,mamaki tsantsa ya kama malik tunda suka farazaman kansu cikin wannan gidan baitab'a ganin hawaye afuskar saba sai yau.kallonsa yake sosai yana idasa shigowa cikin dakin ya zauna yana ajiye takeaway din daya shigo dashi.
Alfah tashi yayi zaune yana tankwashe kafafunsa irin zaman nan nacin tuwo,bai kalli malik ba ledar yajawo yana budewa don yunwa yakeji sosai.
Bai kallesa ba yace"i need water pls."
Tashi yayi yaje yadauko mashi cikin firg dinsa dake cikin dakin.
"No pls bani marar sanyi in akwai."
Kallonsa kawai yake yace"Kaoda baka shan ruwa marar sanyi."
Hanunsa yasa yana shafa fuskarsa zuwa gashin sajensa konace kasumbarsa data kwanta tayi lub yace"yanzu kuma inso."
Komawa malik yayi yadau ko mashi ya dawo ya tusa si yana son tamayarsa kukansa amman yasa ba zaishi ba shi ansa ba.
Ruwa yasha kadan sanan yafara cin kazar dae ciki don bai iya cin shinkafar zata saka cikinsa nauyi,gashi yakwana wajen biyar bai motsa jikiba duk ba yajin dadin jikin.
Saida ya cinye kazar an tas ya idasa shanye ruwan yana adduar gama cin abinci kasa kasa.
*Alhamdulillahil lazi ad'a amana wasa qana waja alana muslimin.*
Duk yada yayita ciki ciki hakan bai hanaa malik yaji ba.
Shidai yau Alfah duk ya zamar mashi wani daban,Alfah da baison ma katusa shi gaba inzaici abinci,kuma bai magana ko kadan sannan bai tabajin koda wasa ya yi wata addua ba.
Ko salla ya gama zai tashine kurin inya gama tazbihi,baya rokon komi.
Amman yau shine da adduar gama cin abinci!lallai akwai wani abu,wannan aikin asu shida fiyah bai kai har hakaba,
Yana gama wa tashi yayi ya hau wani abun exercises yana yi,don abunda yaci ya narke yaje ya kwanta.
Gajiya yayi a kallon da alik yake mshi yace"man what's happen"
Ajiyar zuciya yasauke yana sake kallonsa yau Alfah ke tambayarsa meke damunsa gaskiya lamarin azimunne.
"Katai ka kwanta kagaji kila,ko kabar yi mun wannan kallon"
Cewar Alfah
Malik kamar jira yake yace"ba dole nake kallon ka ba."
Bai jiyoba yace"dana yi me kenan?"
"Uhmm kaima kasan abunda kakeyi wai shin wani abune yafaru can da bazaka iya gaya man ba saidai kazauna kayita rusa kuka"
Saukowa daga kan machine din gudun yayi yana kyalkyala dariya malik hangame baki yayi yana kallonsa cike da rudani,after six years saiyau Alfah yake dariya. dariyar ma irin wadda tun taletale yakeyi.
Saida ya gajiyace mashi"ni ake rusa kuka malik,na lura kafara koyon karya wajen wannan marar kunyar yarinyar,ols kace mata tadaina koya maka karya babu kyau."
Toilet yashige donyin bush yabar malik da saki baki galala.......(nikau ace maza dao sauro ya atayaciki🀣🀣)
gajiya yayi da zaman ya fita yabarsa shima ranar yajima bai bacci ba,yana mamakin lamarin Alfah kamar wani mai aljanu.

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Wayarta dake ta ring ta tasheta daga baccin bayan sallar asubah data koma.
Tana murtsike ido tatashi badan baccin ya isheta bata lalubo wauar bata ma tsaya kallon mai kiran ba ta dauka.
"Assalamu alaikum"
Cewar fiyah da muryarta cike da bacci.
"Wa alaikumussalam,sorry na tasheki daga bacci"
Ciro wayar fiyah tayi don ganinwsye sunan zakiyya data gani yasata idasa wartsakewa.
"Aa ba komi wlh ai gara ma dakika kira intashi haka nan ashe ma har shadaya tayi inanan ina bacci."
"Aikuwa dai tayi,dama.kira nai ince maki don Allah kozaki zo mu hadu tun jiya da muka rabu awaya kin barni cikin tunani wlh."
Mik'a fiyah tayi tana salati tace"zuwa karfe nawa kenan?."
Tace"arond 4:00"
"Okay ba damuwa kimun text din wajen da zan sameki saina zo karki damu ba wata matsala babba bace,inhar kin bani hadin kai yadda ya kamata"
"Kome kenan dai sister sai kinzo."
Ta kashe wayar saukowa tayi ta shige kewaye .
Wanka tayi tay brush ta dauro alwallah harta mance rabonta dayin walha.
Shirya wa tayi tana tunanin yau wayayi masu karin safe don ita bata masan yadda ta kaya ba bayan sallar asuba data dora masu ruwan wanka,tasan dai ta dawo daki kila daga nan bacci ya saceta b'arawon banza shida bai kunyar satar kowa.
Dariya tayima kanta ta shirya cikin doguwar riga mai kyau,dirarren jikinta ya bayyana yadda rigar take dashap sosai.
Turare tafesa dandanan kamshinsa ya fado mata arai da dramer su ta jiya kamar wata zararra ta kama dariya kafin tace"mugunbanza saina rama wlh"
Wayar ta ta saka caji tabarta tarufo kofar ta fito kasancewar jibi suna yasa gidan tun yanzu da yawaitar jama,a amman ba sosai ba.
Dakin maijogon ta nufa tun kan ma ta karsa take jiyo kukan princess dinta.
Da sallama ta shiga tana cewa.
"Mun shigesu princess wannan kuka haka kamar ana zarar ranki,Anty mekika ma haka da zafi nasan dai princess dina bata kukan banza."
Wata kanwar uncle dake gefe ita da wata mata inajin kawar Antn ce tace"aikuwa safiyyah wannan princess din taki bama kukan banza ba hardana wofi yi take,tunda ita bata son uwarta ta huta bata son goyo kuma bata son adauketa azauna kijimun wana mulkin mallakar."
Dariya fiyah tame tace"Uhm Anty falmata kenan don bakusan yadda Anty jamila ta ba wa mama walaba ba da ba zakice haka ba."
Harararta antyn tayi tana jijjiga babyn tana bata nono tace"aikau safiyya kin cuceni da kikai fatan ta biyoki,da yesmin ce nayi imanin har nagama goyonta bata mun wannan masifar,amman yarinya tun randa tazo duniya sai azabtardani take."
Duk dariya suka saka mata nan kuma suka shiga hirar kuruciyar juna suna raha saida fiyah taji cikinta naniyar kullewa tatashi taje tayi break.

DA yake babu aiki daya wa ta gama duk abunda zatayi har sanwar rana ta gama ta koma daki ta dauko handout dinta tafara karatu don tasan exams is around the corner.
Ta jima tana karatun kuma cikin yardar Alkah da kuma jajircewa da takeyi duk abunda take karatun yana zama,wani kuma dan dubawa zatai tariga ta rike bayanin sa tun cikin class.
Ana kiran la,asar ta ajiye tayi alwallah tayi sallar sanna tafoto ta tambayi antyn idan akwai abunda za,ai tace mata"babu komi gaskiya amman fa inason kidan hadama Muhseen don wani abu zuwa anjima zaizo ko bakuyi waya yace maki yazo ba."
Wani irin faduwar gaba taji ta sameta rasss ita yau ita tashiga ukunta ,wai wanna kaddarerren mutumin bazai shafa mata lafiya ba,wlh ita fa bata son sa.
Yak'e tayi tace" kai anty nafa sani Amman bai gaya mun time din da zai zoba gashi xanje yanzu makaramta xan anso hand out don exam tataho zuwa next week insha Allah."
"Yace sai dare inhar bazaki dade ba ai har kinje kidawo"
A haka suka rabu tafice don inba haka tayi mata ba balbalin masofarta ma sai ya hana fitar.

Mrs bbce.
Mom muhseen
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........25

Tana fitowa sukai cibis da yaya Jalal shida wani abokinsa sunxo ganin baby,wani duka kirjinta yayi don wlh yana iya hanata fitan ma gabaki daya.
Kallonta yake Sama da kasa cike tuhuma,ita Kau banda yak'e babu abunda take,ta gaida abokin nashi ya na tambayarta baby tana ansa mashi cikin kulawa.
"Yaya ashe zakazo nai zaton yar taka ma bazaka zo ganinta ba."
"Ina zaki haka da yamma?"
Bazata banbanta karyar da tayi ma Anty da wadda zatayi ma shi ba ana iya samun Matsala,."yaya na gaya ma Anty zanje makaranta kasan exams tataho shine Zan anso handout in fara karatu."
"Salan kikai dare,naga take takenki kafafunki sunfara sanin gari kin iya yawo."
"Bazan Kai dareba yaya Amman don Allah kakara man kudin taxi wlh basu isata wannan."
Kafinma yafiddo abokin yaciro Dari biyar yabata,godiya tayi mashi sosai sannan suka shige.
Wucewa tayi itama tana murmushi itadai ai hankalinta ya kwanta tunda tayi nasarar ficewa,text din data turo mata babujima ta shiga dubawa.
_ina nan magic land,inkinzo ki kirani saina zo na shigo dake._

Dandanan ta tari taxi ta gaya ma shi inda zai Kai ta,jingina tayi da kujerar da take tana tunanin hikimar daxatayi Mata anfani da ita wajen shawokanta harta gaya mata abunda take bukata,Amman muddin taji gaskiyace zatafada bawai karyaba dole zata kunna recording,don shine abumafi sauki damutun zaiji yayarda dakai,Yakuma yi amanna da cewar wancen bashida laifin komi sharrine na mahassada.
Duk da cewar abunda take shirin fadan tanajin faduwar gaba kuma tana tsoron faruwar wani abu,Amman dolene tayi hakan don shine hanya mafi sauki data dace tatunkari zakiyyar.

Amman harga Allah tana tsoron wani abu guda dayake mata yawo cikin kai,wata xuciyarce takegaya Mata "inaruwanki safiyyah,kedai ba burinki gaskiya tafito ba to inaruwanki da duk abunda zaifaru tsakaninsu."
Ajiyar xuciya tayi tana jin wani zuka cikin kirjinta,duk da haka dai batason hakan ta kasance.
Har bakin Kofar shiga wajen ya sauketa ta salameshi ta fito,
Kiranta tayi awaya saigata ta fito,wannan ne karon farko da tahadu da ita.....gabanta taji yafadi ganin zakiyyar kyakkyawar gaske duguwa Mai dirarren jiki,gaskiya dole Alfah take rikicewa akanta,aman tana tantamar idan gaskIya tafito tabbas wannan tsuhuwar soyayyar zata iya tashi.
Wani lugude taji kirjinta yayi Mata saitaji haka kurin tana tausayin kanta,murmushi shimfide akan fuskar zakiya Wanda ya sake bayyana ainahin ruwan kyanta,Amman kuma azahiri safiyya tacewa zakiyya kauban wuri Amman saboda wani abudake ranta yasa ta kasa tantance itada zakiyyar waye yafi wani.
"Assalamu alaikum."
Zakiya tafada tana mikawa fiyah hannu.
Cikin rashin kwarin jiki ta na mata yake ta mika mata nata hannun tace"Wa,alaiki salaam,zakiyya muazzam ko?"
Cikin Fara,a tace"haka yake sunan,muje ciki to nima har kinsanar dani naki."
Jerawa sukai suna tafiya hakanan zakiyya taji fiyah ta kwanta mata arai,Ku ma ta yardarma ranta bazata cucetaba.
"Ai tun ranar dana kiraki nafada maki sunana kindai manta ne"
Cewar fiyah dake kusada ita tana kallon wajen gwanin burgewa.
"Ohhh anyi haka,Amman wlh na manta kasancewar abubuwa sunmun yawa."
Fiyah tayi murmushi tace"haba aiba komi kasancewar ki amarya aianama amare uziri hidima ce tayi masu yawa."
Dandanan fuskar zakiyya ta canza,yanayinta ya canza sosai harta kasa cewa fiyah komi akai.
Tun anan fiyah taharbo jirgin,zarginta ya tabbata cewar zakiya bata son auren Alh kwangila,to meyasa zata auresa.?

Wajene ta tanadar masu Mai tsananin kyau da burgewa,kuma wajen is save zasuyi maganarsu cikin sirri babu Wanda zaijisu ko yasa musu ido.
Zama fiyah tayi tana ajiye jikkarta agefe,ta tsurama zakiyya ido tana kallo tana sake karantarta tsaf.
Zakiyya zaman tayi itama Amman gabaki daya fuskarta ta canza babu wannan walwalar da tazo da ita afarko.
Hannu tasa tana dafeda fuskarta natsayin wani lokaci kafin ta iya dagowa tana cewa cikin sanyin murya.
"Bari akawo maki a bun ta'bawa ko."
Cikin kulawa tace"Aa zakiyya,kibarshi har nakoma gida ban bukaci wani abunba,yanzu dai ga pos dinki duba kiga komi dakika San yana ciki yana nan yadda yake."
Murmushin karfin hali tayi tana cewa"bama sai na duba ba nayarda dake gani nafarko dake,nasan bazaki cuceni ba."
Murmushi fiyah tayi tace"karkiyi saurin yarda dani taya kikasan bazan cutar dake bah."
Ajiyar xuciya zakiyya taja tace"nasan ki ai,sunanki ne kurin ban rikeba Amman yadda nasan gidan dakika fito ya tabbatar mun bazaki cuceni ba,duk da ganin danayi maki baiwuce uku ba."
Cikin mamaki fiyah "inakika sanni."
Dariya tayi tace"nikinga banzanyi mamaki ba da kika sanni,dafarko nayi lokacin dakika kirani,Amman ganina dake yasa mamakin yafita,don unguwa daya ba wasa bace gidanku yana opposite danamu kohar yanzun kina mamaki."
Jinjina Kai tayi tace "nabar mamakin yanzu ai"
Shiru sukai fiyah tana jinjina halin kirki da rashin wulakanta mutane irin na zakiyya,Sam batayi Kama da yangidan masu kudin dasuke wulakanta Wanda sukasan kasansu Yakeba.
"Kince zamuyi magana dake,tundaga ranar hankalina baisake kwanciyaba har yanxu,sonake naji abunda kikeson muyi magana akai."
Sadda Kai fiyah tayi tace"inhar kinyi amanna dani cewar bazan cucekiba, zakiyya kiyimun alkawarin cewar duk abunda nake da bukata zaki fadamun gaskiya."
Kallonta take tana nazarinta kafin ta iyacewa"mezai hana,ai koda kingujeman gidanku bazai gujemun ba,balle nasan ba zaki yi abunda zasakani cikin damuwa bah."
"Karkiyi saurin cawa haka zakiyya,don kuwa abunda nazo dashi zaijefaki cikin damuwar da wata kila kinyi bikin binneta cikin ranki,abunda nazo dashi zaifama maki wani ciwo da kikatabaji cikin ranki,Amman Ina maitabbatar maki yadda na fama makishi haka insha Allah zanwarkar maki dashi ki bani yardarki

Please Login or Register in order to submit comment