Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

awaya shima bata taba dauka ba.kuma baya fushi zai sake kira saidai yesmin din ta dauka matsayin fiyar suyi firar ta kashe,tunda ance baya kasar sai karshen shekara yake xuwa amman yanzu da an daura auren zatabi jirgi ta sameshi can.

Kwance take tana ta kallon no dinsa duk wasu moments dinsu dashi wanda tundaga kan haduwarsu ta farko da karshen haduwarsu saita fashe da kuka,kukan da tunda akafara hidimar bikin batai ba,don xuciyarta ta dunkule ta dake wanda takejin bata jin akwai abunda zai sake sata kuka ashe fadane kurin tai,haka taita kukan har yesmin ta shigo.
"Haba Addata kiyiwa girman Allah kiyi hkr baki isa ki canza kaddararki ba,abunda Allah ya hukunta dole zaki ansheshi hannu bibbiyu,tabbas akwai ciwo akwai tashin hankali amman bamusan dalikin dayasa haka ta faru ba,kidauka Allah sonki yake dahar ya maki musaya da wani kila shine mafi alkairinki........."rungumeta tai tana cewa"yesmin nasani nasan dahaka amman taya zan cire shi daga cikin raina,yesmin yya Abdoul yayi reshe acikin xuciyata har ya fitar da tsiro,duk iyakar kokarina abun ya faskareni,yazanyi haka zanje gidan wani ina fama da wani cikin raina,ina jintsoron Allah ya kamani da wannan laifin"
Kukan suke tare mama na baking kofa tanajinsu bata san sadda hawaye suka silalo mata ba,hakika Safiyya na cikin halin damuwa,kuma bata da yadda zatai da damuwar tata zata dai roka mata Allah yasa mata hkr da dangana.
Yesmin har anje anmata jerenta unguwarsu Anty jamila,fiyah kuma kudin kayan dakinta baba ya danka mata ga hannunta yace tunda baza,a iya daukar kaya har kasar waje ba yaga bari yabata kudin tayi sana,a idan har mijin yabari acan ma saita karasa karatunta.
Rungume baban tai tana kuka yana lallashinta tare daa mata albarka,nasiha yayi masu sosai don yasan ba lallai ya samu amar yi masu ba na da kwaa uku da yarage daurin aure.
Dole fihay ta saka danaa dataga dai dagaske auren nan yinsa za,ai taroki allah yasa hakan shine alkairinsu ita dashi,shima allah ya bashi lafiya yakuma samashi juriya da dangana.
Ta saduda kodan nasihar da baba yayi mata da kuma wacce yan hwanta suke mata,mama kam kullun ne saita bata baki tana bata labarin irin wadanda akaima aure irin nata da irin nasarar dasuka samu.

Baba da Abbin Abdoul sun sasanta don har gaisawa suke yake mashi allah yasa alkairi,ai baisan biki za,ai gidan ba tunda shima baya zaune nan dai har ybashi gudun mawa mai yawa gaske haka dady ma.

Tun dawowarsu Abbi yasa aka shiga hidimar gyaran gidanshi ba kama hannun yaro,don rana guda zai aurar da yara uku Amina da zuwairat da haulat.khadija yabarta said ni,ima ta samu miji sai ahadasu.
Komi da komi aka canza ma gidan idan ka shigo unguwar bazaka gane shine ba.
Sati biyu kacal aka dauka ana gyaran don komi yayi lafiya lau bazata yakeson yiwa su mami idan suka dawo duk da babu ranar dawowar bikin ma duk baifi saura wata guda ba.

*Rana bata karya aidai uwar diya taji kunya*

😭😭😭😭ina tay Abdoul kishi tsakani a Allah mom banji di ba.
πŸ˜‚πŸ˜‰
Muhadu next page da sorry typing error
[10/13, 5:31 PM] Mom Muhseen: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

πŸ…ΏοΈ...........61

Kasancewar masallacin juma,a aka daura ba kofar gida ba bakowane yasan an daura ba,saida aka fara shigowa abokan baba sunayi ma mama Allah yasa alkairi,saitaji kwalla ta cika idonta haka take daurewa tana ansawa,su yesmin suna gidan Anty jamila labarin ya samesu saitaji duk dokinta na kasancewa da muhseen yakau,kewar mamanta da Addarta yasakata ta rushe da kuka,ga kawayensu nan wasu na lallashi wasu na mata dariya.

Fiyah na fitowa daga wanka maiyi masu make up tazo ta fara gyareta tana mulketa da wasu arnayen turaruka da tunda akafara yimasu gyara dasu ake mulke masu jikinsu,shiyasa dasun gifta ka zakaji sun barka da tarin kamshin.komi suka rike saiya kamu da wannan kamshi,ana cikin kwallaiyar ne dayake tace kartayi mata heavy make up simple takeso,wata kawar yesmin ce ta shigo tace"Adda safiyyah ga yesmin can tana kuka dagajin an daura aure"
Wani irin duka taji ga kirjinta,har saida taji sautin cikin kunnuwanta dan danan jikinta yadauki rawa dakarkarwa daker tace mata"don Allah salaha kilallasheta kafin inxo idan akwai masuyi mata dariya sudaina hakan zai tun xurata"
Tace "to bari naje"
Tana fita tacigaba dajin wanan dukan a kirjinta,tsawon lokaci tana haka kafin wasu zafafan hawaye su sulalo mata,cigaba da xuba sukai babu kakkautawa mai kwalliyar ta dakata tana kallonta cikin murmushi.
"Kema kukan kike,to inkekinayi ya za,ai ita tadaina.kuyi hkr kowace mace da haka ta saba agidan mijinta,kuma kugodema Allah wasu nacan neman mazan dazasu auresu suke sun rasa,amman kuganku ku da kananun shekarunku kunyi aurenku kun huta,kuyi hkr daman dole wataran duk shakuwarku da yan gidanku dole zaka barsu,ni kinga burgeni kuke wlh shekarata goma da gama secondary har yau Allah bai ban mijin ba,ba kuma don banda masu sona ba aa lokacine Allah bai kawo ba."
Goge kwallarta fiyah tai tana shanken majina tayi murmushi na karfin hali tace"na gode Anty,insha Allah zandaina kuka itama zan lallasheta,kuma insha Allah zaki samu miji wanda baki taba tsammani ba"
Murmushi tai tana jin dadin Adduarta cigaba da kwalliyar sukai tana janta da fira,don ganin har lokacin tana cikin damuwa.
Bakomi take tunawa ba illa Abdoul,yanzu shekanan ta zama ta wani,duk wahalar dasuka sha akan juna daman bazasu rayu tare ba,wannan abunne idan ta tuna yake sata jin kirjinta yana zafi fiye dakima.
Haka aka gama ta tayata shiryawa cikin wasu dankareren less na cikin lefenta da aka kawo akwati shabiyu,harda gwal aciki da xinarai abunda yafi dakar ma masu kallon lefen hankali irin jewelrys din da aka saka tsalatsala da daukar ido,hakika anma fiyah lefe na nuna ma sa,a haka yesmin ma akwatunanta goma ras,masu shegen kyau.
Sunsha saka albarka wajen dangi da abokan arxiki,qawayen fiyah uku kacal ta gaya mawa daga feea sai yan class dinsu su biyu zuhra da ziyada.
Zanso kuga yadda fiyah ta dauki kyau,hotuna mai kwalliyar tayi mata da wayar fiyah tana janta wai ta nuna ma angonta idan ta isa kasar,don karfe takwas na dare jirginsu zai tashi.yan rakiyarta duk mutun ukune daga yakumbo hajara yayar baba sai inna balaraba da Anty jamila saifa hasana diyar inna balaraba.yesmin ana gama sallar la,asar za,a mikata.
Shiyasa tunda suka kulle kansu daki ita da fiyah basu bar juna ba,kuka kurin suke ita fiyah abun ya hade mata goma da ashrin,ga rashin masoyi ga rashi iyaye ga na yar uwarta rabin jikinta,tunda suka xo duniya basayin nisa da juna irin haka saigashi yau aure zai rabasu don dole.
Motace akazo da ita ta abokin yaya jalal zai dauki amaren akaisu gida aimasu fada za,akai yesmin nata gidan.
Ai jisukai kamar ance za,akaisu makabarta kuka kamar zasu mutu,Inna balaraba ce da Anty jamila suka jasu suka sasu motar sanan suka tai,gidan acike da mutane mama kokadan batai tunanin yan unguwar zasu shigo mata ba,bacin momin su feea.
Saigashi har mutanen da batai tunani ba sunxo kuma ta samu abun arxiki sosai,dakin baba aka ajesu fura mai kindurmo aka dama masu harda xuma akasaka,don cikinsu babu wace tasaka ko ruwa aciki ta tun safiyar yau.
Baban da kanshi ya tsaresu saida sukasha furar sosai,sanan shida baffa ubaidullah kanensa da yayansa baffa kalil suka sasu gaba da nasiha sosai,har jikinsu yayi sanyi suka daina kukan.
Sannan yan uwan mama ma suka zo suka dora nasu,yinayi bari nabari ta rabaki da kowa tsafta,biyayya,ladabi,girmamawa da girmama iyauensa yan uwansa da duk wanda ya kawo.sune ke saka kiga miji yana bin matarsa,yana mata duk abunda takeso shike sawa har ace masa mijintace,idan kin tsare wadannan kin zama sarauniya kuma gimbiya agidanki,babu boka babu malam zaki kame mijinki kihanashi kallon wasu sai ke,idan har kin dauki duk abunda ake gaya maku ina mai tabbatar maku zakusha mamaki."
Cewar goggo ladidi diyar wansu mama.
"Hakuri shine jigon zaman aure,kiji kikiji kigani kikigani,ki kawar da idonki akan komi kiringa wa mijinki uziri komi kike idan har yashigo gida ajiye ki kula dashi,wannan na daya daga cikin abunda yasa maza da dama basa son dawowa gidansu kan lokaci.inhar kikai hkr dashi ananma xakici riba ba yar karama ba,sannan ki rike mashi amana kirike sirrinki kedashi kunyi karatun addini kunsan hukuncin mai tona sirrin ta tsakaninta da mijinta,don haka kurike sirrinsa kowane irine,sannan ku kula da dukiyarsu kuzama masu taka tsantsan da duk abun daya mallaka,karki zama mai saka mashi ido kan lamarranshi."
Haka sukaita basu shawarwari da nasihu da kalamai kala kala da zasu natsu su zauna gidajensu.
Har abokan muhseen suka iso da motoci dan daukar amarya,mota ashirin ce cif kowa dakeson xuwa saida ya samu waje.
Harda fiya aka tafi raka yesmin kafin lokacin tashin nasu jirgin yayi.
Motarsu guda da yesmin suna makale da juna,sai inna balaraba jusa dasu sai Anty agaba,dayake uncle yahya ne kejan motar.
Gaskiya gidan yesmin yayi babu karya,don gudane na kere sa,a giane dan gaske wanda tawon rayuwarta bata taba kawo cewar zatai aure aciki ba,tana ganinsu unguwanni masu hali amman bata taba saka hakan aranta cewar wataran zata mallakeshi ba.
Kowa idan yashigo saiya yi magana ana ta saka mata albarka,da fatan dorewa acikinsa har iyakar rayuwarsu,bed room dinta uku amman guda biyu baba da mama sukai kokarin cika mata da kaya,sai falukanta biyu suma acike da kaya na zamani masu kyau.
Kawayenta harda hotuna daya daga cikin dakunan aka sauketa ita da Addarta,can suka shige kowa ya buga tagumin sabuwar rayuwar dasuka shigo,wanda tazo masu abazata don kokusa fiya bata kawo aurenta nan da shekara mai xuwa ba na balle wata uku.sunsha addua ga
Mutane kafin suka fara ragewa ahankali ahankali har ya rage daga su sai inna balaraba da hasana saint feea da ziyada sai Antyn.
Hira akeyi yadda abubuwan suka kasance inna na sake jawo hankulansu tana kwantar masu dashi,har yesmin ta dan fara dayayewa.
Amman fiyah sauraren bugun kirjinta kurin take,zata so tayi ido biyu da wannan mai karfin halin daya aureta,taya zata fara rayuwa da wani namiji bacin ba wanda taje tsara rayuwarta dashi bane........sai hawaye tayi kukanta mai isarta ta hkr.
Anayin magruba kawayen duk suka watse sai kawayen yesmin su biyu da zasu jirayi anguna kafin sutai,don baza,a kwana ba gaskiya.
Babane ya kira Anty yace tayi maza tazo ta hada kayan da za,a tafi dasu na safiyya suma su idasa hada nasu lokaci na tafiya.
On ready daman tun daren biki babban aminin angon yazo ya tai da lefenta da sauran tarkacenta,yanzu kurin kayan sawarta ne datayi amfani dasu za,a hado kamar zatai kuka tace"Anty dagaske dai barinku zan,barin garin nan zanyi nidai wlh bana so har cikin raina banso".
Tausayinta ya kamasu inna ta rungumota tace"kwantar da hankalinki diyata zaki samu rayuwa mai kyau,kuma zakiyi mamakin mijinki da ikon Allah,kicire damuwa karki tadama kanki ciwi kinga ba lafiya gareki isassaba"
Kai ta iya dagawa kurin tana kwanciya kan cinyar innar,Anty jamila ta shafa kanta ta fice don ganin anata kiran sallar magruba kamata yayi ace tanzu suna airport............

**************
******************

Fiyah da mama kamar bazasu bar juna ba saboda kuka da jin inama karsu rabu,shi kanshi baban karfin hali yake kurin shine ya janye mamar su yakumbo sukai ciki da ita,shikuma ya kama hannun fiyah ya sata cikin mota,shafa kanta cikin rauni yace"Allah yayi maki albarka safiyya,kamar yadda kikemun biyayya Allahu yabaku xuria mai irin halinki,Allah ya albarkaci zamanku ya baku zaman lafiya,idan naimaki abunda kikejin ban kyauta ba kiyafe mun kinji yar albarka........kuka ta fashe dashi tana riko rigarsa "baba wlh bakayimun komi ba,nice zance ka yafe mun zantai wata duniya inbarku badan raina yaso ba don Allah baba kakula da mama inasonku kuduka,ina alfahari daku zancigaba da yin biyayya gareku don kune jigon duk abunda nazama arayuwa........kuka yaci karfinta duk wanda yake wajen saida yayi hawaye dalha kanshi kukan yake,yaya jalal juyawa yayi yanajin wani iri cikin ransa,lallai wannan soyayya tasu ajinjina mata.
"Allah ya maki albarka uwata Allah ya saukeku lafiya kibi mijinki kicigaba da hkr kamar yadda kowa yasanki.........juyawa yayi yakoma don ga kwallarsa nan afili,kuka ta cigaba dayi tana jin inama bata girma ba har ta isa wani aure dazai rabata da iyayenta masu sonta da kaunarta.duk nacikin motar kukan suke amman na hawaye ita kadai akejin shashshekarta.
Karfe takwas daidai jirginsu ya tashi sai *Australia*

Gobe bazan typing ba gaskiya kila sai dare tunda har kukaja nai maku update biyu at d same time.
[10/15, 3:03 PM] Mom Muhseen: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

πŸ…ΏοΈ.............62

Kafin su isa jikin fiyah ya rikice da zazzabi,da ciwon kai sosai duk hankukansu ya tashi addua kurin suke su sauka lafiya,su duka babu wanda ta bata tunanin nan kusa zai hau jirgi saigashi silar safiyya sun hau lallai dole su shimata albarka,ajikin inna balaraba ta rungumeta tana shafa mata addua idan ta karanto mata,sune basu sauka ba sai wajen karfe shabiyun dare suka sauka,nan fa idanun su yahau kalle kalle,har saida Anty tayiwa hasana magana.
"Don Allah ki adana kauyancin ki har muje masauki,karkija ayita kalonmu"
Dariya sukai su duka fiyah bata san ma mesuke cewa ba,zafin zazzabinta ya saka duk bata ma gane komi.
Zaman jiran zuwa daukar su sukai awajen na minty biyar saiga mota har biyu tazo,aka kwashi kayansu aka loda ga but din motar sannan inna da fiyah suka shiga baya,sai abokin angon dake jan motar.
Ciki mutuntawa yake gaida inna yana masu sannu da xuwa,tace"mun sauka lafiya yaro amman kam amaryarku ba lfiya don tun ajirgi jikin ya rikice zazzabi sosai ne ajikinta."
"Subhanallahi aikuwa to bari mu wuce asibiti ku adubata ko magani sai surubuta mata."
"To hakan ma yayi"
Waya yayi wa driver daya dauko su anty jamila da hasana yace ya wuce dasu gidan zaikai amaryar asibiti.
Kamar cikin mfarki take jiyo muryar malik,amman saita dauka ko tsananin begen Abdoul ne yasa takejin haka,da kuma zafin ciwo da takeji ajikinta,bata dai dagoba tana kwance jikin inna.
Suna isa inna ta kamota suna binsa abaya,yaje yayi duk abunda xa,ai taga likita ya dubata sosai yace wannan saitasha drip akwai stress jikinta,da damuwa sune suka sakarmara fever and jininta ya dan hau kadan shima zadai muriketa nakega gaskiya."
Inji dr dame magana da turanci shikuma yake ma inna bayanin komi,hankalinta yadan tashi"yaro ya zaai kenan"
"Karki damu inna bari muyi magana dashi za,asamu maslaha"
Ya fice yabi bayan dr har xuwa offce dinsa.
Fiyah dake kwance anmara allura dazata rage mata zafin zazzabin,idonta arufe amman har yanzu ta gaza yarda da abunda xuciyarta take gaya mata,cewar malik ne to idan shine meya hadata da malik ahalin yanzu?bacin ba abokinsa ta aura ba.wata xuciyar ce tace mata to koshine mijin?
Xunbur tayi tatashi tana zare ido inna tayi saurin riketa.
"Safiyya kina lafiya kuwa menene kika zabura haka"
Idonta ta kwalla tana kermar baki tace"inna......wan....wannan dayake magan.....magana waye shi"
"Bangane waye shi ba,wani abunne yafaru ko kinsan sane"
"Inna waye nidai nake tambaya,?
Jin za,a shi go yasa tayi saurin komawa ta kwanta tana rufe idonta,karma taganshi taga dagaske din shine mijinta din yauni nabani Safiyya,kai gaskiya ba gaskiya bane bashine ba mai kama da murya shi ne.........."ya kukai dashi yaro"
Inji innar.
"Yace zai bada nurse muje da ita tayi mata komi,ta dan zauna da ita har xuwa safe aga yadda jikin yayi sai ta dawo,yanzu tafiya zamuyi gidan."
Fiyah nason bude idonta tanajin tsoron ganin abunda take sake tabbatarwa da xuciyarta.
Nurse din ce ta shigo ita ta kama fiya suka wuce mota yaja suka tafi gidan,inna sai kallon gari take tana jinjina kai ko amafarki bata taba tunanin haka ba.
Ai bata sake shiga wani mamakin ba saida taga gidan da motar su ke danna kai ciki,dogon tsaunine wanda saida ta daga kai tabisa da kallo har iyakar karsheshi........tana zare ido ita dai kome xa,ace wlh saita kalla aibata bata xuwa ba balle ace,haka inna tafito tabi bayansa nurse tana rungume da fiyah saboda bata da karfin jiki har lokacin idonta rufe inna sakin baki da hanci tai tana kallon inda zasu bi sushiga gidan,sai an danna wasu malatsai sanna ta bude babu abunda take sai jinjina kai kamar kadangaruwa.

Su anty jamila dasuka riga isowa har sun kammala mata mominta acikin bedrooms dinta sun sake kwata gidan banda kamshi bakajin komi saifa sanyin Ac dake ratsa kiji,har cikin daya daga cikin dakunanta aka kaita sai lokacin fiyah ta iya bude idonta tana karewa dakin kallo,ta ko ina ya gama hadewa komi White and pink color ne na dakin,gwanin ban sha,awa fessss dakin sai rabar saniyi da kamshi yake har saida ta rufa da duvet din da aka shimfida daga bakin bed din nata,hakika itama ta yi kyauyancin don gadon kanshi binsa da kallo take,tunda take ma ita bata tabaganinsa ba.
Dandanan nurse din tace asamo mata wani abu taci ta watsa ruwa sannan sai a saka drip din.
Cikin kankanen lokaci yaje ya siyo musu abinci isassashe wanda zai wadace su suduka,amman na amarya daban yake saida tayi wankan Anty ta zabo mata kaya marasa nauyi ta canza suka tusata gaba da lallashi taci abincin,saigashi tadanci dayawa don daman tunda aka fara hidimar bikin bata cin komi sai abu mai ruwa shiyasa duk ta rame,drip din aka samata sannan nurse din tace suje falo abarta tayi bacci.
Hasana akabari don ta dan jata da fira kafin baccin ya dauketa,don harda allurar bacci akai mata cikin ruwan drip din.

"Fiyah kin dace gida anan aduniya dai,sai fatan nacan dinma kidace kamar haka,wlh gidanki yayi bala,in haduwa gaskiya ki yadda maka manki kiyi rayuwarki mai kyau,bafa kece akafara yin irin wannan auren akanki ba.kuma naga ma mijin naki kamar nasanshi wlh amman na manta inda nasanshi,ki godewa Allah kiyi miji inhar wanda Anty ta nuna man ne.mun samesu anan harda yan gidansu kinga wai yadda suka tarbemu"

Idonta rufe tana sauraren maganganun hasana yayinda gabamta yake bugawa,tabbas ita kanta tasan gidan yakai makura wajen kyau,kuma yayi mata yaburgeta amman ita bata san awane matsayi take ba wai waye wanan da bai nuna mata kanshi ba.
"Naji ki kyaleni da maganar nan haka"
"Uhmm zan kyaleki idan kinyi bacci amman inhar idonki biyu wlh santin gidan nan zan kamayi maki,wlh ni banma taba ganin miji da matar dasuka dace irin ku ba uhmmm zanso ganin yaranku wlh"
Dammm taji gabanta ya fadi data san abunda xa ai har asamu yaran,tabdijam aikwai aiki gabanta wanan abunne zai yi mata tsananin wahala ta dauki budurcinta taba wani,wanda bata taba tunanin yin raywa irin wannan dashi ba,saitaji tausayin kanta dole fa wataran zaici karfinta kuma koba wannan,hakkinsa ne Allah zai kamata da lafin hakan inko har hakane dole ta xubar da duk makamanta ta rungumi kaddararta.
Haka hasana taita mata surutu har bacci ya dauketa hasanar ta fita tabarta.

Zuwa safe jiki yayi sauki sosai ta nemi ciwon ta rasa saidai abuna ba,a rasa ba na gajiya da rashin kwarin jiki,nurse din ta rubuta magani tace asiyo ta ringasha saida aka siyo sannan tatafi,sai lokacin Anty da inna suka jata dole saita kewaye gidan ta gani,daker ta iya binsu sako da lungu data gaji ta dawo falo ta zauna tana kalonsa,hakika komi sai sambarka yanzu damuwarta tafiyarsu anty gashi sunce gobe zasu juya,ai tunda sun kawota sunga waje Allah yasaka albarka,sai sundawo suna wannan kalmar ta sai sundawo suna ita tasata kuka har kanta yayi ciwo.
Dadaddare suna hira falon ga kallo sunayi wanan mai murya irinta malik yayi sallama ya shigo,bayansa wasune dauke da kwalaye da ledoji manya yaudai saitaga waye wannan mai muryar yaya malik........jiyowa tai ta sauke idonta akansa yana murmushi suna gaisawa dasu Anty............duk idanunta ta fiddo tana zuba mashi su cike da tsananin mamaki da alamomin tambaya,amman sai ya wayence yana gaidata.
"Amarya barka da dare ya bakunta".sarawa kanta yayi mehakan ke nufi miyanta ya kafe daker tayi gyaran murya tana yake tace"ina wuni"
Kin ansawa yayi yana dire kayan gabansu yana ware wasu yana bayani.
"Inna ga wadannan kayayyakin zaku tai dasu gobe duk nakune,inji angon yace kuyi hjr da safe zai zo kuyi sallama wadannan kuma amarya bari ashigar maku dasu store"
Ya fada yana duka wa yana daukar su ya nufi store din,da murmushi fuskarshi bin bayansa tai da kalo kamar wata sakara kafin ta sauke wata nannauyar ajiyar xuciya tana dafe goshinta,duk a rikice take wannan lamarin da daure kai yake.
Fitowa yayi yana cewa"zan wuce Anty saida safen zamuzo tare yayi maku sallama"
Godiya sukai sosai suna saka mashi albarka.
"Gaskiya mutanen nan suna da kyauta Allah dai ya zaunar daku lafiya safiyya kiyi hkr kinjiko,aure babu inda baya kai mutun kuma ki saki jiki da yan uwan mijinki suna sonki suna ji dake,shima kiyo kokari ku gyara tsakaninku Allah yabarku tare"
Inji inna hasana na mata gwalo da dariya.
Cikin muryar kuka tace"inna kinganta ko,dariya take mun tana mun gwalo"
Murmushi innar tai tana ma hasana fada tace"kema kwanan nan zamu tsayar da magana ai,nagaji da laben da jalal yake mana duk sadda yazo,ana fakewa da zumunci"
Duk mamaki da al,ajabi ya kama mu nida anty,itakuma tana rugawa daki tana cewa inna tayi shiru.
Anan innar kecewa ai sun kai shekara suna soyayya shirutai dai taga gudun ruwansu,ganin basu d niyyar baiyyana kansu yasa tace zata gaya ma su baba.
Abun ya mana dadi sosai har hakan yasa nasaki jiki dasu muka sha hirarmu ta bankwana,jinake inama zasu zauna dani amman nasan hakan ba mai yuwuwa bane.
Bamu kwanta ba sai karfe daya ranar banyi bacci ba tunanika suka cika xuciyata,ina cikin kokwanto komi ya cushe man.duk yadda naso baccin gagarata yayi nai salla raka,a biyu na roki ubangiji daya sakamun salama acikin xuciyata,ya sanyaya mun raina nayi zaman aurena kamar kowace mace,ya ban ikon yin biyayya wajen mijin da bansani ba yaba ikon danne duk wani miki na soyayyar danake ciki.
Rashin baccin yasaka na kamara sadda na tashi na nemi su inna ban gansu ba,duk inda zan ga daya naduba babu su dakin da suke kwana arufe falo na dawo na zube gefen kujera ina kuka,meyasa xasu tai bamuyi sallama ba meyasa haka kuka nake sosai da sosai.
Gashi ko karya wa ban ba kuma yunwar nakeji sosai,na kasa tashi naje dining naci abincin tunda gashi can ankawo.
Ina nan zaune naji anshigo mata ne biyu suka shigo turawa ne suduka,gaidata sukai suna cewa sune masu aikin gidan dayar zata iso.
Kallonsu tai cike da haushi tanuna masu hanyar cikin gidan,tana binsu da harara kamar sune sukai mata laifin.
Saida taji yunwa na niyar kassarata taje tahau cin abincin,tana hawaye gashi bata taho da waya ba mama ta barwa wayarta.
Haka ta wuni cikin kewa daga tai salla taci abinci saita kwanta,har gajiya tai da yin bacci ita bata saba zaman haka ba babu aikin fari balle na baki,ahaka dare ya cinmata duk atsorace take haka tayi wankan ta ta dawo falo tai sallar magriba,itama sallar badan alam dake bugawa ba duk time dinta bazata gane ba,don bataga agogoba,itafa atakure take bata saba da wadannan abubuwan ba tafisaba wa dana kasarta nigeria.
Tana gama salla mai aikinta linder ta iso cikin girmamawa tamika mata waya.
Ansa tayi tana binta da kallon tambaya,cikin harshen turanci tace mata"ogane yace abaki akwai sako aciki kiduba"
Harara ta maka mata amman ba gane metake nufi da hakan tai ba,ta juya ta koma bangarensu.
Duba wayar ta cigaba dayi tana shiga ko ina bata ga komi ba,tsaki taja ta ajiye tana rabka tagumi,bayan minty biyu taji sako yashigo har kerma hannunta yake ta dauka tana dubawa.

_"KIYI WANKA KISHIRYA IN THE THIRTY MINUTES AND WAITING FOR ME"_

kallon wayar take kamar zata cinyeta don haushi,au bazai iya kiranta ba saboda girman kai,shin wai taya ma zata iya zama da wannan bahagon mutumen.kodan yana ganin yana da kudi zaimun wulakanci shiyasa ya kawoni kasar da babu uwa babu uba babu dangin iya balle na baba,hawaye suka silalo mata tana sharewa itafa tasan sun kulla amana da kuka yanxu.daman gata sa arhar kuka,kallon jikinta tai taga bata jima da wanka ba,kawai dai kayan baccine jikinta.
Tatashi tanufi bedroom din cike a tsoro,bata saba zaman gidansu babu kowa ba balle wannan uban gida mai girma ga sako da lungu gani take kamar wani xaixo ta shaketa ya kasheta yajefar da gawarta..........wani marron less ne da zanen manyan flowers milk sai kyalkyali yake,baya da nauyi shiyasa ta daukoshi riga da siket ne siket din yayi bala,in fitar da shaf dinta don randa ta fara sasu ranar alhamis din auren mutane sai magana suke gaskiya amarya tasha kyau,masha Allah tubarkallah.karshe saboda haushi ciresu tai saboda bata son ma abunda zai sa ace tai kyau abikin da ba sonshi take ba.
Ajiyar xuciya tai bayan ta sak kayan,rigar irin mai budaddar kafadar nan ce akai mata,an kawata gabanta da wani style mai kyai.
Powder ta saka da marrom

Please Login or Register in order to submit comment