Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akai mashi ba karamar d'imuwa zai shigaba.cikin tsananin tashin hankali Rafeea ke kuka tana dafe da fuskarta,cikin kaushin murya yace"daga yau zakiyi gigin zagin wani bama niba,don ubanki yar iska da iyayenta basu bata tarbiyya ba."
Ya fizge daga hannun dr da malik,yajuya tari taxi zai shiga yajiyota tana cewa"shege d'an iska,azzalumi ban yafeba wlh saina yi silar zuwanka gidan yari mugu........azafafe yadawo wajen malik na rik'eshi yana cewa"haba Alfah karka biyeta macece zaka iya rauna ta tafa,wani irin juyowa yayi yana kallon malik yace"nasan da cewar macence ai shiyasa zan koya mata hankali yadda zata ji tsoron tunkarar namiji ko bani ba,don ubanki ba gidan yari ba kisaka akaini lahira inkikai hakan zan dawwama ina saka maki albarka jakar banza,"
Kuka take tana cewa"wlh sai babana yayi sanadin ajalinka,inhar yasan kaine ka mareni zaka gane kurenka mugu........k'afa yasa zai halbeta yaji anrik'e k'afar caraf cikin mamakin wanda yarik'e kafar sa yake kallon wajen........ *fiyah* ce tayi han zarin rik'e kafar tana hawaye duk sun wanke mata fuska,wani irin wurgi tayi da k'afar tana share kwallarta ta mik'e daga durk'ushen da take gaban Rafeea,cikin d'aurewar fuska kamar ba fiyah ba,cikin masifa da y'ar muryar ta kamar ta yan yara tace,
"Kar ka sake gangancin dukanta,kai baka da imanine ehy,bakasan kima da darajar mace ba,ana gaya maka cewa macece karka biye mata kaji mata ciwo,shine kake son sake kaimata duka,to kasani wlh muddin mahaifinta yaji bakaiba kaf danginka sai akulle tsinann..........cikin fita hayyaci Alfah ya yunk'uro zai kwasa mata nata marin,tai saurin ja baya Malik da dr suka rik'eshi......cikin zafin xuciya yace"kubarni na lahanta yan isaka.....janshi sukai har cikin taxi d'in daya tsayar d'azun suka shigar dashi daker, sadda xai shiga saida ya juyo idonsa cikin na Fiyah ya nunata da yatsa,yana girgizashi alamun worning.
Harara tabanka mashi tana mashi alama da hannu wuce kaidai.
Dr yace wa malik"abokina kaban no dinka pls don koda kai baka nemo niba nizan zo har gida induba jikin nashi,don zamanshi babu kulawar likita hadarine ga rayuwarsa."
Babu damuwa ya ansa wayar yasa mai sannan yayi mashi asauka lfy.

Lallashin Rafeea take tana cewa"kiyi hkr muje gida kinga dare yayi nasan sai nasha fad'a wajen baba da mama,tashi kiyi hkr inkinje gida kisanar da Abbanku nasan dole zai daukar maki mataki,dole ne ma wannan."
Tashi tayi tana share kwallarta don har ga Allah mari ya shigeta ba kadanba.
Dr ne ya iso wajen yana cewa"kiyi hkr Rafee,atu karki sanar da Alhaji kiyafe mashi bai cikin hayyacinsa hakan tafaru."
Cikin masifa tace "shine zai juye haukanta sa akaina wlh saina fad'a ai gabanka yayi man wannan zalincin ko kuma baka dauki mataki ba",ta nufi motarta tana masifa.

Tafiya suke zuwa gida fiyah tace"kinsan dr ne Rafeea."
Tsaki taja tace"likitan kakane shike zuwa har gida yana dubata duk karshen wata."
Jinjina kai tayi tace"amman baza kiyi hkr ba Rafeea kiyafe mai tun da kinji cewar baya cikin hayyacinsa hakan tafaru,don inkin lura hannunsa jini yake fitarwa,kuma sai yanzu na ganeshi shine wanda d'azun na taso makaranta aka bankeshi kan titin central park,na yarda da dr da yace bai cikin hayyacinsa ki yafe mai."

Tsaki taja tana kara gudun motar don tuni angama sallar mangaruba,
"Ki kyaleni fiyah,wlh saiya gane cewa ya tab'o yar gidan Alh muazzam Canji."
Shiru fiyah tayi don daman tasan za,ai hakan Rafeea na da fada aji wajen mahaifinta,don kuwa ita dayace mace wajensa,jida ita yake sosai duk abunda takeso yi mata yake,kuma duk wanda ya tab'ata yashiga uku don bazai kyaleshi ba.
Saboda haka mahaifin fiyah baison alakarsu,don dai kurun mahaifiyarta macece mai tsananin kirki da mutunci,shiyasa yake d'an barinta tana shiga gidan kuma take hudda da Rafeea,badan ransa yasoba.don yadda duk estate din suka kafa mashi k'ahon zuk'a akan zamanshi cikinsu,shiyasa yake iyakar yinsa don ganin ya kiyaye abunda zai saka suci mashi mutunci.

Har suka isa gida fiyah bata sake cewa komi ba godiya tayi mata da kuma saida safe kowace ta shige gidansu.

"Assalamu alaikum...........ina kika tsaya sofiyya badai kijin maganata ko,bance inkinga wannan yarinyar zata shiriritar dakeba ki kamo hanya kidawo gida,banson wannan alakar taki da ita ko kad'an kinsani,amman ina hakuri ne saboda mutuncin uwarta,amman inbacin haka bazan bari kina shigewa wadannan mutanen a da basu san mutuncin mu ba."
Duk Malam kabir El-ladan ne yake wannan fadan watau mahaifi ga sofiyya.
Sadda kai tayi tana idasa shigowa cikin gidan,durk'usawa tayi gabanshi cikin ladabi da biyayya tace"baba kayi hkr wlh akullum ina kokarin kiyaye duk abunda kake gaya man,matsala aka samu shiyasa amman dawuri muka taho."
Ta zayyane mashi duk abunda yafaru tacigaba da cewa"wlh baba dagaske Rafeea take zata iya fa da ma Abban su kuma har prison yana iya kaishi."
Baban yace "Allah ya kyauta,ni shiyasa banson kina shiga motarta yanzu dada tsotsai wani abu yafaru fa,ki kiyaye ba koda yaushe zaki ringa shiga motar ta ba kinjiko mamana."
D'aga kai tayi tace"insha Allah baba zan kiyaye kayi hkr."
"Shikenan,nayi tashi kije kiyi sallah Allah yayi maki albarka."
Tashi tayi tana ansawa da Ameen maman tace intayi sallar tazo ga abincinta nan ta d'auka,shigewa tayi d'akinsu tana magana da yesmin dake ta faman gugar uniform.
"Yaushe kika dawo yesmin."
Tace"Adda nah nima ban jima ba uncle yahya ya ka woni bajima wa,anty tace gobe inkin taso kibiya tana da magana dake."
Kayan ta ke cirewa tare da cewa"uhm ni wlh Anty zata matsaman kan wani kanen mijinta,ki kyaleta kawai yesmin ni 6allemun wannan abar."
Tana juya mata baya ta 6alle mata bra d'inta.

*************

Tunda suka dawo gidan malik baiyyi gigin sake mashi magana ba,don yasan yanzu zai sake burkicewa babu mai taimakonsa kuma,don unguwarsu ba sosai mutane ke shiga sabgar da batasu ba.
Malik ya dawo daga masallaci sallar isha,i ya samai falo shima ya gama tashi sallar agida yana d'auke praymate d'in.
Girgiza kai yayi kawai don baisan yadda zai yasa Alfah cigaba da yin sallah cikin jam,i ba,ko masallacin bai zuwa duk sallar dazai tofa cikin daki zaiyyita.fuskarnan kamar kullum tur6une babu walwala babu rahma kanta.
Zama yayi yana kallonsa kafin yace mashi.
"Me zakaci abokina"
Kallon banza ya wurga mai kurun yana cigaba da opreting system d'insa,xuwa can ya ajiye ya tashi yaje gaban frig ya bude win d'insa ya dauko ya cire hancin,ya bulbula ga cup ya koma mazauninsa yana kurb'a yana aikinsa,....kallon bakin ciki da takaici kawai malik kemashi,don baima san yazaiyyi da Alfah ba,idan akwai abunda yatsana cikin halayyarsa sabbi to bai wuce wannan shan win d'in da yake ba.
Kasa hakuri yayi yace mashi"Wai Alfah mai yasa kakeson kashe kanka,meyasa kai rayuwa baka daukar komi da sauki,duk abunda Allah ya kaddara maka baka hkr karok'esa sassauci,ina anfanin wannan halayyar daka k'irk'iro ma kanka...........cikin masifa dazafin zuciya ya jefar da cup din glass din dake hannunsa ya fashe kasa,yana huci.
Yanuna malik da hannu yace"kafita harkata malik,kadaina takurani da kalamanka,komi nake komi zanyi is not ur business."
Hawaye suka cika idon malik yace"komi zakace kuma kome zakayi man Alfah wlh saina gaya maka gaskiya,koda kuwa kasheni zakai wlh saina fad'a,don kuwa ina kaunarka inason rayuwarka idan kai bakason ta,ka taimakeni ka kulaman da ita,idan narasaka Alfah yakake son inyi,banfa da kowa saikai.Allahne gatana kaine gatana.plsss karage shan win d'inan koda baka bari dukaba dr ya sanar dani yadda tayi maka illah."
Kwallarsa suka silalo kan fuskara yaciga ba da cewa"Allah yasan da abunda yafaru baka da laifi,amman ya6oye gaskiyarsa saboda yana son jarabtarka yaga iyakar imanin ka,duk wannan ba daidai bane,kuma kaima kasani kake take sanin.....cikin sanyin murya ya katse malik da cewa"enough!and i'm sorry to hut u."
Tashi yayi yashige bedroom d'insa da system d'in sa ga hannu.

Murmushi malik yayi yace "thank god,yaushe rabon da naji irin wannan sweet voice d'in naka Alfah,ina maka fatan Allah ya sanyaya zuciyarka ya kuma kawo mani matai makin da zamu taru mudawo dakai cikin rayuwa mai kyau.

*sorry jiya banyi update ba in busy ne kuyi hkr.*

Mrs bbce
Mom muhseen😘
[9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........4

Tun asuba da ta yi salla bata koma ba,kasancewar itakeyin duk ayyukan safe kafin tatafi makaranta,sharar tsakar gida ta farayi sannan ta gyara wajen dabbobi,ta samasu abinci da kajin suma.sannan ta wanke bayinsu ta fiddo wanke-wanke ta share kitchen din,sanwar kalaci ta dora sannan ta fara wanke-wanken,sai lokacin yesmin ta fito daga cikin d'aki tana hamma.
Kallonta tayi tana murmushi tace"kasa uwar bacci sai yanxu aka samu damar tashi,to azo ayimun d'auraya."
Dariya tayi tana kallon gidan tace"sannu Adda nah,kina kokari fah ni ban sanma baccin ya sace ni ba bayan sallar asuba."
Tana d'auraye plet cikin ruwa tace"hada gajiya ke damunki bakya samun hutu sosai,don ma kun samu interval aida abun ya maki yawa."
Zama tayi tana yi mata d'aurayar suna hira.

Tsakaninsu Babu nisa don ashekaru,duka shekara biyuce ta shiga tsakaninsu,suna matukar son junan su duk abunda ya samu guda kamar suduka yasama,mahaifiyarsu tayi tsaye wajen tarbiyyarsu,don suna girmama yayunsu jamila da jalal,watau babban wansu yana aiki ne a kaduna,bai cika zama ba wata secondary school yake koyarwa.
Malam kabir El-ladan shima malamin makaranta ne,amman ya jima dayin retire tun tuni yanzu yana zuwa wani karamin company na hada kujerun amare da gadaje,yana aiki wajen babu laifi yana d'an samun na rufin asirin sa,don kullum ake biyanshi.
Ita kuma maman su kiwo take na dabbobi da kaji,tana daukar d'aid'ai tana siyarwa idan bukatar hakan tatashi,kuma ta kafa shagon sayar da kayan masarufi ak'ofar gidan,babu laifi suna ciniki don duk unguwar babu shago sai nasu,don dole masu kudin unguwar suke siyayya wajen,don inkana son abu dole saika je bakin titi.,ganin wiyar fitar yasa suka hkr suna siye awajensu,don bayarda suka iya,don basu son duk abunda zai hadasu da wannan kaskantaccen talakan,cewarsu kenan.

Kafin mamansu ta fito har fiyah ta dama koko,ta dora juluf din taliyar hausa da zasu had'a da ita.......kafin karfe takwas har tagama komi tayi wanka ta shirya,sai albarka maman take saka masu baban daman tun shidda yake fita,sai goma yadawo ya karya sanan ya koma sai kuma dare don can yake cin narana.
Yesmin ta fiddo wankinsu nata dana Addar ta dana maman,tana yi don yau bazata ko ina ba kasancewar weac da suke amman sun samu hutun kwana biyu.
Fiyah ce ta fito sanye da doguwar rigar atamfa purple and pink sai lemon green,tayi masifar daukarta duk da babu kwalliya fuskar sosai,hakan bai hana tsananin kyanta bayyana ba,purple din hijab tasa iyakar guiwa mai hannu,sai jikarta itama purple din da takalmata,fiyah badai daukar wankaba ta iya had'a matching color,bata yarda tayi hadin gambiza,kuma antyn ta jamila ta koyar da ita salon daukar wanka.........ruwa tasha tana tambayar maman su karfe nawa tace mata ,
"Kina da sauran lokaci ki natsu kigama."
Tana goge takalminta tace"mama jiya ban samu morning lecture ba yadda ya kamata,yau bazan so haka ba."
Takalmin ta sa mamar tana mik'o mata dari biyar tace,
"Gashinan Dari uku yabaki naga bazata isheki ba yasa nace yesmin ta anso maki dari biyu wajen dalha kikara."
Rungume maman tayi tana murmushi"nagode mamana Allah ya barmana ke."
Ta sun baceta ta fice tana ma yesmin by by.
Sauri sauri haka ta fita cikin estate din zuwa bakin titi ta tari taxi.

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Tun safe malik ya fita zuwa company don yana aiki da company Alfah,mai suna *FATION&DESIGNER'S BANGLES COMPANY* nasa ne na kansa,suna siyarda sumfarin yan kunne yan hannu,sark'a da links na maza,agoguna new moden design ba karamin kudi suke samu ba,daga kasashe ake zuwa wajensu siyen d'ai d'ai ko sari,babu kasar da Alfah baya zuwa shida malik akan wannan kasuwancin,gefe guda kuma ga shopping mall d'insa duk malik ke kulawa dasu,bakamar yanzu da abubuwa suka rikice komi yake neman tsayawa ya lalace,dole malik ya tashi tsaye don ganin basuyi asara ba kuma basu rasa customers ba,dafarko cewa yayi yabar aikin bazai sake zuwa ba,saida malik yatusasa gaba yana kuka da ban baki sannan ya amunce yake yin aikin kan computer,duk abunda zaiyi acan office yana yinsa ga computer,saidai guiding din ma,akaitan da ya saka shakikansa dake cikin company suke mashi CID,kuma yana lura da komi ta computer shima,don kwanakin baya saida yakori wasu ma,aikata dasuka so sujawo masu matsala.
haka zalika malik tsaye yake akan dukiyar abokinsa safe rana dare ,kuma duk wata yana fidda albashin ma,aikatan su aba kowa hakkinsa.
don ma kayan yanzu sunyi ramai ramai,suna bukatar sabbin kaya amman yayi-yayi da Alfah su shirya sutai paris da sauran kasashen dasuke zuwa saro kaya masu inganci,yace bazaije ba inkuma ya matsa mashi wlh saida company zai ya kyautar kudin,mafarin ya kyakesa kenan.

Kwance yake wajen swimming yana shan iska,ga table dinsa nan kwalaben win d'insa wajen uku,ya shanye biyu saura guda itama ya sha rabi.
Ko ka dan giya bata bugar dashi,irin yadda take bugar da wasu sukoma kamar mahaukata,zaiji shi yana layi amman daya kwanta yayi bacci zai wartsake,amman idan akai kuskuren tunkarar sa cikin wannan condition din tofa akwai damuwa,don shikanshi baisan 6annar da zai aikata wa kowaye ba,hakan da malik ya lura yasa idan yana cikin mayensa baya kulasa.fita yake yabar mashi gidan har sai ya tabbatar ya lafah sai yadawo.

Malik ne ya iso wajen yana rik'e da computer akwai wasu bayanai da yake son nuna mashi,na email,don sakonnine na abokan kasuwancinsu suka turo suna bukatar zuwa cikin satinan idan ya anshi gaiyyatar, zasuyi wani ciniki idan yana da lokaci.
Idonsa arufe yake yad'ora d'aya kan d'aya,girgiza kai malik yayi zai juya don yasan bazai bashi hadin kai suyi magana ba inhar yanancikin wannan halin.

Jiyai yace mashi"kafasa abunda kazo yine"
Ajiyar zuciya yasauke yana dawowa ya zauna,laptop d'in ya tura mashi gabanshi yana cewa"bak'i garemu suna neman iznin zuwa don suna son siyen kaya,gashi kayan babu masu kyau sosai duk an zab'e shiyasa nace maka yadace kaban dama ni naje idan kai bazaka ba."

Tura mashi system din yayi yana cewa"katura masu acceptance latter,zuwa opper week sai suzo kafinan har kaje kadawo."
Dadi yaji koba komi yau ya sauraresa duk da yana cikin halin maye,mikewa yayi zaibar wajen wayarsa tayi kara,ya duba yaga ba suna dauka yayi yana sallama.
"Wa'alaiku mussalam,da malik nake magana."
Malik yace"yes i'm malik muazzam."
"OK Dr ne don Allah katuro mun address din inda zan sameka."
Kallon Alfah yayi daya kai cup din win dinsa bakinsa yana sha cikin kwanciyar hankali,amman fa kokadan hakan bai nuna kan fuskarsa ba,malik yace"ok dr bari na turo maka ina gida ban kaiga fita ba."
Text ya tura mai sunan unguwar da kuma stress dinsu da no. Gidan nasu.

Wucewa yayi cikin gidan don cigaba da aikinsa.

********
"Yallabai gashi yaturo,amman don Girman Allah yallabai karka saka adaure wannan bawan Allahn,wallahi nagaya maka baicikin natsuwarsa hakan tafaru,kuma naba Rafeea hkr cewar baiyyi don yana sane bah."
Cikin fushi Alhaji kwangila yace"karka raina man wayau Dr fahad,ya d'aga kantamemen hanunsa k'azamin hanunsa ya wanke y'ata da mari,sannan ya zageta har ya hada dani sannan kace inkyalesa wlh ko waye ubansa yau sai ya gane kurensa,saidai shi yaji tsoron sake aikata haka akan wata badai Rafeea ba."
Shiru Dr yayi yana daya sanin sanar dashi cewar yasan sa.
Waya Alhajin yake cikin fushi cewar"yanzu yanzu nakeson kuje ku kama shi,karku ragar mashi har sai nazo zan biya na dauko feea makaranta zamozo tare,ga address din gidan nan zan turo maka."
Kashe wayar yayi yana kallon dr daya sha jinin jikinsa"kodai dan gidankune sai haka dr jibeka yadda duk kawani lafke,garama katashi katai don wlh bazan ragar masa ba,da dai wani yata6o mani ba Yarlelena ba to da saina sassauta mashi,amman wlh bazan lamunci abunda zai ta6a man feea ba."
Ta shi Dr yayi yana jin babu dadi kuma yasan malik zaiga yayi anfani dashi don ya cutar da Alfah bacin ba haka yaso ba,abun yafi karfinsa Alhji kwangila baida tausayi ko alama.

Malik na cikin gida yaji an danna bell d'insu tashi yayi yasan ko za,a shekara dubu ana danna wa Alfah bazai tashi ba balle ya bude.
Ajiye aikin dayake yayi yasaka rigarsa akan singlet din dake jikin sa.
Wuce Alfah yayi yana exercise dinsa,awajen swimming d'in.
Bude k'ofar yayi yana cewa"Dr u Are welcome.......wad'an da yagani ne yasa gaban sa faduwa sosai,bankesa sukai suka shigo cikin gidan,biyosu yayi yana magana cikin tsananin rudewa"yallabai lafiya,ya zaku shigo mana gida kai tsaye,"
Wani daga cikinsu ya shak'osa yana tambayarsa ina guy din daya mari diyar Alhaji kwangila.
Duk abunda kefaruwa Alfah yana hange,ganin yada suka shak'e malik ne abun ya tunzurashi ya jefar da karfen dayake d'agawa ya doso wajen cikin wani irin fushi da zuciya.
Basu san da tahowar shiba kawai ya finciko dan sandan da yashake malik ya wurgar dashi gefe har yana fad'uwa kasa.
Malik ya sha gaban Alfah yana mazurai duk ya gigice don yasan tabbas aikosu akai su kama Alfah......."Aa Kadaina karka jawo mana wani tashin hankali",ogansu da sukazo tare yace"ku fiddo mana wanda ya mari y'ar Alhaji,kokuma mutai daku kuduka."
Cikin muryarsa dakakka yace"nine nan sai akai yaya."
Kallon mamaki suke mai ogan yace"u are under arrest."
KO akwalar rigarsa ya mik'a masu hannunsa suka sa mashi unka,malik duk ya gigice yace"wlh saidai mutai tare bazaku daukesa ba wlh. kunko san kowaye shi kushiga taitayinku kafin .........cikin tsawa yace mashi " *malik!!! Karka sake wata magana anan"*
Ya kalli ogan yace "muje."
Aguje malik ya fito ya bisu abaya taxi ya tara yarufa masu baya,sai station.

Fiyah da Rafeea school din su guda,amman kowa da couse dinsa sun fito hutun minty talatin Abbanta yakirata yace ta taho da qawarta da abun yafaru jiya zasuje police station.........jikin fiyah yayi wani irin bala,in sanyi tace"yanzu fisabilillah feea kin kyauta,saida kika sanar da Abbanku wlh baki kyauta ba to ni innaje mezance sokike nabada shedar dazata saka akullesa,nidai banji dadi bah wlh."
Rafeea itama duk taji jikinta yayi sanyi tace"wlh fiyah shine ya gane bani na sanar dashiba ,ganin shatin marin yayi ga kuncina yace inban fada mashi abunda yafaru ba saiya b'ata man rai,kuma koda nasar dashi cewa nai yabarshi na yafe mashi basai ya dauki mataki ba amman wlh su yah hashim suka tirashi cewar karma araga ma kowaye."
Jinjina kai fiyah tayi tace amman inkinje ai kina iya sake rokon sa asake shi kin yafe kilan ya hakura."
Tace"to zan jaraba muje yace yana bakin get yana jiranmu."

Mrs bb ce
Mom muhseen.
[9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.......5

Tunda take ba ta tab'a shiga mota irin tasu Abban feea ba motar kamar ba tafiya take ba ga wani irin sanyi mai dadin bala,i mai tsananin shiga jiki.
Kan kace me har sun isa station din mamaki ya cika fiyah idan da akan taxi ne sai sunyi tafiyar one hour basu je ba saboda dan banza nisan dake akwai.
Kamar karta fito taji amman dolenta ta fito dandanan kuma taji gabanta yayi wata irin fad'uwa,"nashiga ukuna fiyah, idan mama ko baba yaji labarin zuwa na police station ya zanyi wlh wannan karon baba dukana zai.saida Rafeea ta jawota sannan suka fara dosar cikin station din,gabanta yana faduwa dan danan tausayin wannan bawan Allah ya kamata,tana adduar Allah yasa Aban feea yayi hkr asakesa.

Malik suka fara cin karo dashi yabuga uban tagumi idonsa duk yayi ja saboda yasha kuka.
ba karamar kauna ce tsakaninsa da Alfah ba,duk abunda ya samu guda to dayan yana shiga tashin hankali,wanda zaka ce shine abun ya faru dashi,haka inhar na farin cikine tofa bazaka gane wanda abun yasama ba,ko yanzu babu irin roko da magiyar da bai masuba,akan su sakeshi zaibasu ko nawa sukeso.
Amman sai DPO din yace wanda yasasu aikin yafi karfin su anshi cin hanci da dai wanine bashiba,dasai su ansa su sakeshi."
Alfah dake kulle cikin cell yace"malik idan har kasake magana wlh kaji narantse zanyi abunda bakaso,donme zaka ringa masu kuka iyayenka ne su don ubura ubansu wlh karka sake kask'antar da kanka kana masu magiya,idan sunga dama su barni nan har mahdi ya bayyana."
Wannan maganar ta janyo tashin hankali,don kuwa ran DPO yakai mak'ura wajen b'aci yace sushiga su mashi dukan mutuwa.
Malik yace"yallabai,karka yi haka wlh zaiyyi b'anna fah karsu tab'ashi za,a samu matsala."
Amman bai sauraresa ba ya tura wasu constable guda biyu suyiwa Alfah mugun duka,yana jinsu baice komi ba ko motsawa baiyi ba zuciyarsa takai mak'ura rabon ma dayaji irin wannan temper d'in shikanshi bai saniba.............jiyai kurun an kai mashi duka ga baya da wata k'atuwar k'ota, cikin tsananin zuciya ya d'ago ya kalli wanda ya buge sa,ganin zai sake kawo mashi bugun.baisan ma sadda ya kai mashi duka ga fuska ba,dan danan hakorinsa guda yafita. dukanshi yake kamar Allah ya aikoshi saida yaga baya motsi sosai ya juya kan gudan wanda yafara jin fitsari don ganin irin dukan da akaiwa dan uwansa.ko kadan Alfahbai ragar masuba k'wanjinsa ya saki ya dunga naushinsu iyakar karfinsa.
banda kiran sir babu abunda suke,sun kasa kwatar kansu saida Alfah yayi masu dukan da suka kasa tashi,ya bud'e kofar ya watsosu waje.....daidai shigowar su Fiyah da feea da Abban su kallon su yake yana mamaki,baki bude yake kallonsu kafin yace"mezan gani haka meye haka"
Duk sunyi tsuru tsuru suna kallon kallo,koshi DPO din ya kasa cewa komi saida ya daka masu tsawa sannan yace"yallabai wlh wannan guy din dan dabane,zaginmu yayi nasa adakeshi shine yayi masu haka."
Kallon Alfah Alhaji kwangila yake cikin tsananin mamaki,takowa yake yazo har gabansa yana kallonsa ya dora hannunsa kan kafadar Alfah.
Cikin fusata Alfah ya ture hannun daga jikinsa yana ma Alhaji kwagila wani irin k'ask'antaccen kallo.ya jefar da hannun na Alhaji kwangila cikin wata irin murya yace masa tare da nuna sa da hannu
"Kar ka sake hannunka k'azami ya sake tab'ani."
Dariya Alhaji kwangila yayi yana kallon sa k'asa zuwa sama yace"ban yi mamaki ba,ai indai kaine zaka aikata abunda yafi haka,domin iyayenka ma basu iya dakai ba balle.........cikin wata irin anger yace"stop telling nonsense about my parent,if......"
Shima Alhajin cikin fushi yace"if me ehy,kai har mutunne,nace kai mutunne har da zaka daga kazamin hanunka ka mari y'ata,idan iyayenka da kayiwa sun kyaleka to kuwa banga ubanda ya isa ya hanani kulleka ba wlh,muddin ba hkr kabayar ba."
Feea dake bayansa idonta yaraina fata don ganin yadda fuskar Alfah tayi babu rahma ko kadan,kiris yake jira yajuye tirar dake cinsa.
"Abba kabari wlh nidai dayayi wa na yafe,na hakura kazo mutai."
Zare mata ido yayi yace wa DPO "ku kullesa har sai nina bada damar fiddoshi"aguje malik ya iso wajen yana tare Alfah agigice yace"baza su sake kullesan ba wlh,sannan kushiga taitayinku zaku yi dana sani akan hakan."
Alhaji kwangila shima cikin bala,i yace"ubansa kadai zaizo nan na hakura kuma bazai tab'a zuwaba domin kuwa wannan dan iskan yaron ya riga yafita daga cikin zuriar su,kunsan kuwa abunda yayi kunsan irin bala,in dayayi har iyayensa suka korai to bari kuji wannan dakuke gani,matar.............jikake tas tatas Alfah ne tsaye gaban Alhaji kwangila ya wankesa da kyawawan maruka har uku.
idonsa yayi wani irin fitinennen jaa,dai-dai sadda wani babban mutun yashigo station din wada tacika da mutane,cikin shakewar murya da ta dishe saboda tsananin bacin rai "wlh kasake furta magana marar dadi akaina saina kasheka,saina fiddo yan hanjinka don ubanka katon banza katon wofi,b'arawon gwamnati baka iya komi ba sai yad'a karya da sharri.........kai *Abdoul-nasser* kul akul nace in ka sake magana saina sasab'a maka awajen nan."
Wannan babban mutumen daya shigo yanzu yake fad'ar haka.
Ajiye hannunsa yayi da yake nunnuna Alhaji kwangila dashi kamar zai kaimashi naushi,huci yake fiddawa yanajin kamar yadunga dukan bango kozai huce haushinsa......yace"Daddykabarni na koya mai hankali,kabarni na keta mashi rashin mutunci.ni....ni..zai....wulak'anta.......sai wasu zafafan hawaye suka shiga zarya kan kuncinsa.
Malik kanshi hawayen yake na tausayin amininsa kuma dan uwansa.
Mutumen yace"nadai ce karka sake magana idan ba haka ba zaka ga b'acin raina.
tunda ya shigo duk aka k'ame ana sara mai,saboda shine comissioner of police. kallon su yake shima fuskarsa babu walwala ya kalli Alhaji kwangila yace" kagani ko,u see i tall u last time ka guji tun karar shi kar watarana ya baka kunya,Abdoul ba kunya ce ta isheshiba tun wancen karon balle yanzu da yasake firgicewa baijin kunyar yaga maka rigar mutunci,gashi kuma hakan akai bacin malik yaje ya kirani da banson iyakar abunda zai maka ba wlh awajen nan."
Zufa yake share wa yana jinjina kai duk ya gigice,feea na gefe na kuka ganin yadda aka wanke ubanta da mafi,wanda yafi nata. fiyah kuwa kamar kazar da aka tsamota daga cikin ruwan zafi,duk ta firgice.
Cikin taushin murya Alhaji kwangila yace ma

Please Login or Register in order to submit comment