Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gani da zata sadata falon gidan tabita wajen tana tura kofar mama na zaune yesmin na mata kitso.
Mama bata san sadda taji wata kara ba yesmin tatashi daga kanta tai wake kofa suna rungume junansu.
Suna karadin ganin juna mama sakin baki tai tana kallonsu cike da ji dadi sai dariya suke suna makale da juna,suka idasa shigowa ciki fiyah ta saki yesmin ta nufi mama da gudu cike da kwaba mamar tace"bargudun nan karki isomun nan kina gudu baki gudun kije kija wata matsalar."
Xubewatai jikin mamar harda kukanta "mama nai kewarki wlh ba saa haka ai kewarku a saida aganku idai gaskiya bazanbi yaya Abdoul ba inanan wajenku"
Ta fada tana kuka.
Dariya sukaata mamar tace"kinanan kina wannan kukan ko safiyya,bakisan kingirma ba "
Share kwallar take tana kallon gidan cike da jin dadi yadda aka gyara ma iyayenta gidan yayi kyau yazama kamar ba nasu ba nada.
"Ama waye yayi wannan aikin wlh gidan yayi kyau ya hafu kamar indawo inyita zama nidake"
Yesmin na dariya ita da mamar tace"lallai Adda kice kema irin nawa zakiyi wlh nima ranar danazo haka nace"
Mama tace kuda nan gidan kuwa insha Allah Ai saidai yini ya kawoku ko idan wata ta haihu cikinku tazo wanka gida."duk sai sukai shiru don kunyace ta rufesu baba ne ya shigo da sallama har fiya tatashi zata ruga sai kunya ta kamata ta koma ta zauna don jitake kamar ta fada jikinsa yadda tai kewarsa.
Murmushi yake har ya iso ya zauna shima kowa ya gaidashi dayi mashi sannu da zuwa.
Idona ya ciwo da kwalla na sauko kasa ina gaidashi sai kukaya kubcemun mama da yesmin na dariya baban kuma murmushi yake cike dajin dadin ganin uwar tashi cikin koshin lafiya dagani bata cikin wata damuwa.
Cikin kulawa yace"xo yaki uwata kukan namiye bacin kin samemu cikin koshin lafiya kuma kema muna fatan haka"
Matsawa tai kusa dashi tana ajiyar xuciya "baba nai kewarku a nidai kace mashi karya tai dani yabarni wajenku."
Murmushi yayi yace"inbanda abunki ga inda mijinki ke aiki meye anfanin zamanki nan kuma uwata?"
Cikin kuka tace "baba nidai bana sin nesa nan wlh ina kewarku koda yaushe"
Dariya duk sukai mata yace"kiyi hkr uwata aure babu inda baya kai mutun,don haka kiyiwa mijinki biyayya inhar yace zaitai dake kibishi bazaiji dadi kice bazaki koma ba knjiko keda ma zaki koma makaranta"
Cikeda mamaki da jin dafin maganar baban ta dago kanta "dagaske baba,yafada maka ne ni baimun maganar ba kuma tsoro nake nayi mashi yace bazan koma ba shiyasa"
Murmushi yayi mta ganin ta daina kukan tana dariya yace"insha Allah munyi maganar dashi tunma kafin kudawo kedai kicigaba da mashi biyayya kina hkr nasan ki gwanar hkr ce kikara kinjiko"
Ta sadda kai tana cewa cikin sanyin murya "insha Allah baba"
Have"mijinki yana da halin kirki kiyimashi addua koda yaushe kikuma yi mashi godiya don shine da wannan aikin na gidan nan,ya kuma samar ma yayanku aiki mai tsoka yanzu haka yana legos,nima kaina babanshi ya budemun wajen furnitures na xuba ma ,aikata sosai kuma alhadulillah muna samu fiye da tunani gaskiya,haka mijin yesmin duk watan duniya shine siyen kayan abincin mu uncle dinkuma wannan kunsani tun kuna gida albashi yake ban na musanman duk watan duniya,ban haifesu ba amman kasancewarku suna jin dadin zama daku yasa suke mana wannan hidimar,ina sake jawo hankalinku daku dage wajen biyayya da nuna kulawa kuna hkr duk mai hkr zaici ribar zaman duniya Allah yayi maku albarka."
Duk muka ansa da ameen.

Ranar ina gidan har bayan salar isha,i nabasu tsarabarsu masu uban yawa mama harda fada wai duk ina zasu da wadannanen kayan.
Na ware na anty jamila da takwarata don ita akwati nai mata na daban.
Wajen ten da rabi saiga yaya Abdoul din dasu zakiyya da malik sun shigo gaida su baban.
Aikuwa nan aka dasa wata sabuwar firar duk da kunyar baba da Mama da Abdoul keji.
Sai wajen shadaya baba yace mutai hakanan dare yayi na fashe da kuka nace nidai saina kwana amma ya rufe idinsa yace inbi mijina.
DA man yes min tun da aka gama salar isha,i yaya muhseen yazo har muka gaisa dashi yana jana wai na koma baturiya irin yan kasar Australia.
Haka ina kuka nabisu ina cewa kuma gobe saina dawo na kwana.
Dari ya suka ringa man zakiyya na cewa duk son jikin na habibi ashe za,a iya barinsa akwana wani waje."
Hararar zakiyyar yayi yace"ba wani nan ko love dina aidai don kar ace bakice zaki kwana a yasa kikai kuka ko."
Bata kulashi ba ta shige shashen mami tana turo baki.
Zakiyya da malik suka kama mashi dariya

Wahse gari taje gidan Anty jamila bata dawo ba Sai can dare sosai yaje ya daukota sunsha hirar yaushe gamo.
agidanta ma tasan tana da ciki don har PT strip ta bata tace wlh tayi awo tana mata kallon mai ciki,saigashi kau ya nuna kasa boye murnarta tayi har saida yagane ya isheta da tambaya ta gaya mashi aikuwa asibiti suka wuce aka aunata saiga cikin wata uku cif jikinta mamaki ya kamata tana tunano urin abubuwan data ringayi ashe duk alamunsa ne taga murna wajen Abdoul har goyata yayi ya kawota har cikin mota don murna.
Wanna cikin yazo mata da sauki don bata komi saidai kwakwar mijin ta datake duk dare bata yarda idan ba,ai ba.

taga kulawa wajen mami da mama kowa dake sonta yana son cikinta yaya jalal yazo sai lokacin suka shirya sosai yana kuma nuna mata jin dadin samun aikin sa,feea tazo har gidan mami inda suka sauka sunsha fira da ita take cewa har yau ba,a fiddo dady ba amman Abbi ya sauko yace zaitaimaka insha Allah zai fito lokacin bikinta ya taho baifi saura sati uku ba.
Shima yaya jalal ansaka ranarsa da hasana ta wajen inna balaraba anyi bikin feea da sati guda za,ai nashi.
Zakiyya ma cikinta yafito amman fiyah saita rigata haihuwashoyasa mami tace Abdoul nan zaibar fiyah harta haihu shikuma yace bazai koma ba har saita haihu sukoma tare.
Mami tace"kota haihun saita gama wanka inkana kama hanya katai katafi ajiko"
Badan ya so ba fiyah harda kuka ranar daxai tai dama malik shi yana nan abunsa,bayan tafiyarsa da sati uku akai bikin yaya jalal ya dawo ya hakarci taron daurin aure ya kuma ba ango kudi masu dama sosai.
Anan cikin estate din Abbi ya bashI gida akasa hasana aciki,lokacin cikina wata tara zakiyya kuma bakwai kuma kamar yadda Yaya Abdoul kefata twis ne mace da namiji kullum zullumin zuwan haihuwar nake karshe dai tazo da matsala dole akai cs akafiddosu yara masu ruwan kyau inji Anty da yesmin.
Yesmin din itama lokacin danata rabon wata shidda ,wadannan jarirai sunga gata baga ubansu ba baga kakarsu mace ba ba kakansu maza ba kowa dokinsu yake naga gata nikaina ,babansu kamar zai cinyemu nidasu haka muka dawo gida nai jinyar ciwona komi mami da ni,ima keyi mun mama da nata gujiri take aikowa ana kawomun ranar suna yara sukaci mamana da Abbin yaya Abdoul.
Munga hidima mai sunan hidima tunda babansu ya dawo yaki komawa har saida na gama wanka duk da na towel ne saida nacika arba,in cif

Nasha gyara mami gwanace sosai ganin ina samun kulawa daga mami yasa mama ta kwantar da hankalinta duk da banma haihu da kaina ba saida ta gyarani sosai yadda bazan cutu ba har kunyarta nakeji amman ita babu ruwanta.
Jaririyar ana ce mata afnan jaririn kuma Affan sun ganin kauna kowa sonsu yake yadda suke da shegen kyau kamar ba diyar africa ba.

Dazamu wuce kuka riris nake yi daker na baro gidan mama itama mamin kamar zan ballata haka aka rabamu jirginmu yatashi sai zakiyya ta haihu kozan zo ni.
Mami ta hadani da yar aikinta guda yar yarinya ce bata wuce shekara sha biyar ba uwarta ma tana tare da mami.
Nakoji dadinta don tana kulawa dasu Affan.
.
Yaya Abdoul kuwa kamar zai maidani cikinsa haka yake likemun gani nake ma yanzu yafi nanikemun akan sadda ina ina amarya nima kuma ina enjoying sosai don kamar wani sabon amarci mukeci don yayi hkr sosai rabonshi dani yafi wata hudu tun cikina yana wata takwas naji kuma ban son abun.
Har na haihu kuma nai wata wajen biyu sannan ai yayi kokari.
Muncigaba da rayuwarmu cikin kwanciyar hankali ina kulawa da twis sosai Abdoul yana sonmu yana mana komi zakiyya ta haihu ta samu namiji sunan baban yaya malik akasaka suna kiransa da walid.
Yesmin ma ta haihu itakuma mace ana ce mata salma haka rayuwar ta cigaba cike da jin dadi duk da baka rasa kalubale ba ni nawa yan matane suka addabi habibi kullum ina cikin kishi amman ganin shi bata su yake ba yasa na maida hankalina kan mijina ina kulawa dashi yadda ya kamata.

Dadyn feea ya fito bacin bakar wahakar ya caza kamanni ba ma lallai ka ganeshi ba.su mamman har yau suna magarkama babu ma ranar fiddosu.umma kau saidai mukaji labarin mutuwarta gawar kuma gudaje suka hau kai sunaci abundai babu kyaun gani bayan shekara biyar na sake haihuwar mace sunana aka samata saboda Abdoul yana masifar sona muna kiranta mimi daga nan ban sake haihuwa ba muka cigaba da tarbiyartar da yaranmu na gama karatuna amman bana aiki saboda Yaya Abdoul ya gama mani komi kasuwanci nake kasa ruka zan iya cewa komi sai hamdala zakiyya yaranta biyar cif yesmin kuma uku kamar ni Anty biyar itama hasanar yaya jalal daya.
Rayuwa tayi kyau komi Alhamdulillah munzama family na gaske nidasu Abdoul


*ALHAMDULILLHAI TAMMAT ANAN NAKAWO KARSHEN ABDOUL-NASSER DARASIN DAKE CIKI ALLAH YASA YAJE GA MASU KARATU NGD DA SOYAYYARKU ALLAH YASADAU DA ALKAIRI IDAN NAIMA WANI BADAIDAI BA YAYI HKR HAKA TSARIN RUBUTUN YAZO,SAI MUN HADU CIKIN ABU KHALIPHA INA ALFAHRI DAKU*

BISSALAM.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment