Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda takeji yanzu dayake isarta da magana da ya kyaleta,amman bata son yaga tayi mashi wulakanci dole ta ke dannar xuciyarta take bashi ansa.
Uncle yace ma Antyn"meyasamu safiyya ne?"
Dariya Anty tayi har muhseen yana juyowa yace"kinga kina hana mu sakewa wallahi"
Harararsa tayi tace"nan gida nane kabari sai kayi naka idan naje saika mun iko kajiko"
Ta share sa tana bawa uncle ansa"waifa daga tayo na biyar isalamiyya shine take fushi,da kuka ma ta shigo gidan nan don ta sana yo na biyu ko na ukku anbata na biyar take ta fishu"
Murmushi yayi yajiya ga fiyar daketa cin magani yace"safiyya haka abun hake ba kullum kake nasara ba,dole daman wata ran kaga juyin mulki badan hakan nanufin kasawa ko rashin maida hankali ba,aa hakan na nufin rabon wanine ba naki ba kiyi hkr next exams saiki dage ki dawo da position dinki"
Murmushin dole tayi tace"nagode uncle insha Allah zan gyara"
Muhseen yace"kice dai yar gidana akwai kokari ban result din in gani tawan"
Batare dataji komi tace"yana gida na barsa wajen mama"
Duk yadda yaso hirar tayi tsayi abun ya gagara don taki bashi hadin kai,tashi tayi ta yi masu saida safe ta wuce dakinta.
Bata da natsuwar yin karatu amman ya ta iya dole zatayi saboda baifi saura kwana biyar sufara exams ba,haka ta runtse ido tanayi ba laifi kuma yana shiga don fiyah inhar tasa kanta abu ba kamar in kan karatu ne tofa ba dagaske yitake har saitaji ta gamsu da abunda ta karan ta.


💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Tunda ya kaita asibitin ya dawo resuption ya zauna ya dafe kanshi dake wata irin sarawa,wani irin juyawa kanshi hakeyi dashi zuciyarsa kaikomu kurin take,duk yabi ya gigice yarasa natsuwarsa.
Malik ne yakira sa ya kasa daukar wayar saida yayi mashi kira uku sannan ya iya dauka.
"Kana ina haka"
Atakaice yace dashi"tarauni specialist hospital"
Cikin tsoro malik yace"mekake yi awajen ne haka Alfah baka lafiya ne koko mekaje"
"Kazo kasaman wajen"
Yana gama fadar haka ya kashe wayar ya dafe kanshi dake cigaba da ciwo,baisan ma kalar tunanin dazai ba.
Yanan zaune ya iso Allah yasa baisha wuyar ganin sa ba.
"Lafiya Abdoul,bakada lafiya ne meke damunka."
Idonsa jawur yace"zakiyya na kawo"
Zaro idonsa malik yayi yana kallonsa cike da tsananin mamaki "zakiyya!!!,zakiyya fa kace kai ina ka gamu da zakiyyar kuma meyasameta"
Cikin wani irin yanayi yayi mashi bayanin abunda yafaru atakaice............likitan dake dubata ne ya karo wajen yace"Alhamdulillah ansamu nasarar samunta,kozamuje office ne nayi maku bayani"
Malik ake kallon sa yace "oky ba damuwa muje"
Kamar bazai tashi ba haka ya tashi suka wuce office din likitan,rubutu yayi kafin yace"Am tayi sa,a sosai don an shak'a mata koken,Allah ne yasa abun yazo da sauki,don haka zata jima bata tashi ba zata iya kai gobe ma har yamma,mun mata allurai mun saka mata drip,zakuje wajen biya kubiya ga bill din ku"
Ansa malik yayi yai mashi godiya suka fito.
"Suwaye zasu yi mata haka?metayi masu ne"
Abdoul ya daga kafada yace"karka tambayeni ban sani ba wata kila wannan yarinyar zata iya sani"
Kallonsa Malik yayi yace"yarinya kuma,wai baka san sunan ta bane Abdoul?"
Tsaki yaja yana zama saman wani benci malik ya isa wajen biyan kudin ya biya yadawo ya zauna kusa dashi yace"yanzu yazamuyi da ita"
Kauda kai yayi Allah kadai yasan yadda xuciyarsa take ciwo,ba kuma dan karamin ciwo ba da wuya idan ba sai yasha magani ba.
"Munyi mai wuyar don haka muwuce gida randa ta tashi saita kama gabanta ko"
Kallonsa yake cike da nazarinsa "ba zai yuwu mubarta ita daya ba Abdoul,don haka ina ga zanje in samu likitan ya tura nurse guda ta zauna da ita,kafin zuwa goben"
"Can matsalarka"
Inji Alfah.
Tashi Malik yayi ya nufi wajen likitan,yayi sa,a kuwa aka sanya nurse guda dazata kula da ita,sannan yadawo suka tafi.
Tafiyar so silent babu Mai magana kowa da abunda yake sakawa cikin ransa,kallon Alfah malik yayi yace"fiyah fa fushi yake dakai,don ayadda ka gaya mun tabbas ka bata mata rai,kuma kowaye dole zaiji haushi ka kirata ka bata hkr"
Jajayen idanunsa ya watsa ma malik yace cikin muryar sa da saika rantse dukan tsiya akai mashi"ta shekara dubu tanayi"
Jinjina kai malik yayi yana murmushi yasan cikin bacin rai yake,amman tabbas yasan wannan ban hkr sai Alfah yayi shi,don daga jiya zuwa yau ya fahimci wasu abubuwa tsakaninsu.
Koda sukaje gida shigewa yai yakulle kofarsa ya fada kan gado dafe da xuciyarsa,murgina kurin yake yana nishi shikadai yasan azabar dayakeji aciki,yau ciwonsa na shekara shidda ya dawo sabo,wani radadi yakeji cikin xuciyarsa.fadowa kasa yayi timm har malik dake falo saida yajiyo karar faduwarsa,gabansa ya fadi ya rugo ya banko kofar dayake ba sosai ya rufe ba saigata tabude..........asume ya yadda shi duk inda hankalin malik yake ya tashi ainun,ya rude sosai rabinda yaga Alfah cikin wannan halin bazai iya tuna wa ba..........yana kerma yana karkarwa ya dauko phone dinsa yashiga kiran dr Alfah din.
Bakinsa yana rawa yake gaya mashi halin da ake ciki,yace gashinan zuwa insha Allah.
Haka malik yaringa kwaraya ma Alfah ruwa Amman baifar fado ba saoda likitan yazo yashiga nemo numfashinsa yasha wuya ba karama ba, kafin Allah yasa numfashin dawowa,amman dole saidai karamin oxygen aka saka mashi yadda zai taimaka mashi wajen numfashin,dr yace"xuciyarsa ce ta halba dakarfi,wanda hakan yajawo sumar tashi da alama dai yana cikin damuwa da tsananin tashin hankali,meya faru ne?"
Dafe kai malik yayi yana sauke ajiyar xuciya yace"yaga abunda ya tuna mashi rayuwar sa ta baya,bacin ransa na shekaru da yawa shine yadawo mashi sabo,ya kasa control din kansa har hakan tafaru."
"Allah ya kyauta gaba,ka kula dashi gobe zan dawo na sake dubashi yanxu dai kabarshi yayita baccin har sanda zai tashi,na xuba allurai acikin ruwan drip din zaitaima ka mashi wajen samun arfin xuciyar"
Rakashi yayi yadawo ya tusa Alfah gaba yana kallo kamar yasamu tv ,tausayinsa ne ya kamashi sosai dole zai shiga wannan haki don kuwa kana ganin rayuwa.
Koma wa yayi daga can saman kujera ya kwanta yana kallonsa.
Ya jima yana cikin tunani da sakawa da kwancewa,kafin ya dauki wayarsa yashiga kiran fiyah.
Ta gama alwallar bacci kenan ta fito tajiyo rurin wayar,kallonta tayi taga sunan malik,da dai kamar ta share amman sai xuciyarta takasa yin hakan.
Ahankali ta dauki wayar tana sawa ga kunnenta.
"Qanwata ban sanki da haka ba,yaushe kika b'aci da fushi ban sani ba"
Turo baki tayi kamar yana gabanta ta haye kan gado tana jingina bayanta ga allon gadon cikin sassanyar murya tace"yaya haka ma zakace bacin,bacin abunda akaimun har zaka ce kar nayi fushi"
"Ni bance karkiyi fushi ba,amman saiki yi mashi uziri abunda ya sakashi yin hakan kinsani meyasa bazaki mashi uxiri ba,"
Sake sunburo bakin tayi kamar zata yi kuka tace"yaya malik Amman basai yazo ya ban hkr inshiga ba amman fa gabansa na tsayar da taxi natafi baiyyi yunkurin dakatar dani baya kyaleni natafi"
"Sorry qanwata zaibaki hkr Amman saiya samu sauki"
Gabanta yafadi rasss "yaya malik baya da lafiya ne"
Iska yafesar yana gyara kwanciyarsa yace"fadowa yayi daga kan gado ya suma xuciyarsa ce ta halba numfashinsa ya tsaya,amman ya samu sauki don gashi can likita ya saka mashi oxygen.xuwa safe zai farka cikin koshin lfiya insha Allah"
Kwalla suka zubo mata cikin kermar murya kiris yarage ta fashe da kuka tace"yaya malik ka tabbatar yana lafiya,ya samu sauki sosai yaya malik nice na bata mashi rai ko?wlh yaya malik ni banson hakan zai bata ransa ba kuma wlh ni kai nakoira bashi ba,amman sai kurin naganshi yazo.......kasa cigaba tayi da magana don kukanta ya kusa fitowa"
Jinjina kai yake yajiyo sautin kukanta tabbas safiyya ta kamu da abunda yake zargin cewar shima Abdoul din ya kamu,duba da yadda duk yabi ta rude ta tashi hankalinta.
"Kuka kike fiyah,miye na kukan to?bakison wani abu yasamai ne"
Shashshekarta ce ta fito fili takasa ansashi murmushi yayi yace"ki kwantar da hankalinki babu abun da zai sameshi,kiyi mashi Addua daya farka da safe zan kiraki sai kimasa ya jiki ko"
Shiru tayi tana jin kamar tayi tsuntsuwa tazo ta ganshi,amma bata son Yaya malik ya fahimci kotana jin wani new feelings akan Abokin nashi.
"Kinyi shiru qanwata"
"Saida safe yaya malik zan kwanta"
Murmushi yayi yanajin ina mace shine yayi dacen samun wannan tsadaddar yarinyar mai kunya da tarbiyya.
"Shikenan qanwata Mma i promise u immediately daya tashi zan kiraki kizo ki ganshi,sannan zakiyya na asibiti ta samu sauki itama da safe ko zuwa yamma zata iya farkawa ai zaki xo ganinta ko saimuyi magana daganan"
Daker ta iya ce mashi "oky,goodnight"
Ta sauke wayar tana silalewa saman gadon tana jawo filo tana kwakwumeshi ga kirjinta.

Plssss kuyi hkr gobe ba zaku samu posting ba saboda muna aikin suna sorry plsssss nasan ba zakuji dadi ba,amman inhar nasamu lokaci zanyi maku

Pls don't share it i beg
[9/17, 3:41 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*
FOR SALE 300 VIA KISIYA KISHA KARATUNKI CIKIN NATSUWA.
GA MAI BUKATA TA TUNTUBI WANNAN LAYIN 09034722979

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ALFAH FANS GROUP*

🅿️.........33

"Anty bazan iya zama har kigama wanka ba,kinga exams ke gareni ina bukatar inje na natsu gida nayi karatuna,kiyi hkr nidai kibarni natai tunda kinga wlh yya muhseen baxai barni nasake ba inhar yasan ina nan gidan gara dai na tai can gida."
"Shikenan,Bari na dauko maki naman ku kowa na mashi kullinsa don haka babu wata rigima,halinki nasani kan nama idan na sake na hadaki dana yesmin wlh kwararta xakiyi,har gara inkeda mamane wanan tana iya ma raba nata biyu takara maki ita ko baba,don naga dagaske kin anshe ma yesmin fadarta"
Dariya fiyah tayi tana yiwa little fiyah rawa tace"uhm shedar da zakiyi mun kenan Anty?kuma ai dama can fadata ce tana zuwa naga alamar da niyar juyin mulki tazo saina zage don kar na rasa matsayina,amman duk da haka Anty Ai yesmin tafini fada aji wajen mama,da dai babane wannan nasan bai bari abunda zai bata raina,don ta nama ma saiya hkr da nashi yabani incinye"
Tafada tana dariya antyn dake cikin daki tace"wlh karma kifara,kowa anbashi nashi kiji tsoron Allah kibarshi yaci,haba safiyya wlh nasan zaki aikata don Allah karkiyi haka"
Tana dariyar tace"to inbaki so inyi nawa yafi na kowa yawa aradu"
Fitowa tai da babar lea viva ta ajiye gabanta,ta fido wata bakar leda cike tab daker aka kulleta tace"wannan na kine kici kiyi kashi don ubanki,wanna kuma na mama gashinan nayi alama,wannan kuma na baba shima ga shedar shinan,inna balaraba tunjiya suka wuce da nasu banda su anan ciki,ga na yesmin ga na yaya jalal asaka mashi akitse tunda ya tafi randa ya dawo sai yaci"
"Kai Anty,saikace dole nidai gaskiya ki kyale yaya kiban shi in cinye in yadawo sai inbashi hkr"
"Uban hkr zaki bashi wallahi karnaji wannan labarin kinji dai na gaya maki,kodayake ma bari kigani."
Ya daukeshi daga cikin sauran tace"nizan ajiye mashi dakaina"
Suna cikin haka uncle ya shigo yace"safiyya badai tafya ba?"
"Wlh uncle tafiya zanyi,inje na natsu infara karatu lokaci yana kure mana"
"To gama bari nazo na saukeki,muhseen baya nan da nasaka ya kaiki."
Aranta tace"nagode Allah"

Sunyi sallama da Anty jamilar tana tayi mata godiya akan hidimar da tai mata,kamar zatai kwallah haka taji don dan zaman da sukai saitaji inama taita zama da qanwar tata,koba komi sunyi wasa da dariya kuma ta rage mata ayyuka,amman tasan baba bazai yarda ba kuma itama fiyar tafison kusada mama da baban.
Suna tafiya yana janta da hira tana biyesa,har yazo kan maganar abokinsa.
"Nikau safiyya ina kika san Alfah,ayadda na fahimta ranan ba bankeki yayi ba,karki boyemun inason in sanine saboda wani dalili"
Saitaji bazata iya boyewa uncle din nata ba ta sadda kai ta fara bashi labarin haduwarsu da kuma dalilin shigarta rayuwarsa,har kawo abunda ya tsayar da ita bata dawo gida da wuri ba,harda cigaban da ya samu tadalilinta.
Shiru yayi yana jinjina kai kafin yace"niyyarki mai kyauce safiyyah,amman kinsan hakan akwai hadari ga rayuwarki,wannan aikin namiji ne ya dace dashi ba ke mace ba,saboda yadda amana tayi karanci cikin rayuwar nan,kuma nima nasan da wannan labarin,shiyasa na tambayeki tabbas nima raina ba yadda Alfah zai aikata haka ba,duk da kowane lokaci mutun zai ita canza wa,amman da kamar wuya gaskiya.don haka ki kula ki kiyaye ya dace tun farko ki sanar da mama koyaya dai in wani abu yabiyo baya duk da ba fata ake ba,atleast tasan mekike ciki"
"Uncle wlh bazata barni na taimakesa ba saboda abunda ya faru tsakaninsu da mahaifinsa,gabace maitsawo tunma ba aifemu ba muduka,abun ya faru shiyasa duk unguwar babu mai kulamu bamu banda yan tsirarunsu,shiyasa na boye abun babu wanda yasani cikin gidan mu don kar ahanani kuma Alhamdulillah komi yana zuwa da sauki nanda dan lokaci komi ya kammala,nima inhuta in samu natsuwa."
Murmushi yayi baice komi ba don yayi imanin shigarta rsyuwar Alfah baya nufin ta fita,don ga dukan alamu ita dashi kowa yana jin wani abu game da dan uwansa,shiyasa bai bada karfi wajen ganin muhseen din sa ya sameta ba,yana da burin ta dawo da abokin nashi cikin hayyacinsa,kuma zaiso ace sunyi aure sauran halayyarsa ta idasa daidaita shi,shiyasa ma zaifara nema wa muhseen din Auren yesmin,don bazai so ace ya rasa daya daga cikinsu ba,don yarane da suka samu kyakkyawar tarbiya yadda ya kamata.
Sauketa yayi suka shiga ya gaida mama lokacin baba bai dawo gida ba,yaba fiya dubu goma ladar aikin data sha na zaman bakwai.taba kowa naman sa na ajiye nata gaba tanaci saida tayi rbin ledar sannan mama dataga bata da niyya saurara mashi ta anshe tana fada.
Wajen karfe sha daya na safe tana dakin mama yesmin taje islamiyya,maman kuma tana kitchen. Ta dora sanwar rana.
Karatu take sosai duk da xuciyarta bata gareta hankalinta ya kasu kashi daban badan,ga zakiyya tana son jin halin da take ga Abdoul tana son sanin koya tashi jikin yayi sauki bata sani ba,shikuma wanda xai kiratan ya gaya mata shiru bai kiraba...........tana cikin wanna halin wayarta tayi kara,saurin kallonta tayi yaga sunan sa tai saurin dauka tana kanga wa ga kunne.
"Yaya malik ina kwana"
"Lafiya lau qanwata ya kika tashi,fatan kinyi bacci daren jiya"
Juya ido tayi alamun me yake nufi da tayi bacci jiya lobatai ba,
"Na tashi lafiya yaya malik"
Kallon Alfah yayi dake kurban tea mai dan gumi don ya gasa cikinsa,kamar baisan da wadda yake waya ba.
"Kinjini shiru ban kira kiba,walh sai yanzun ya tashi babu jimawa inbashi ko"?
Tana son ansa kodan taji muryarsa,don harga Allah Abunda take son jikenan,amman idan tayi hakan wane irin kallo zai mata,kenan ma fushin nata baije ko ina ba,tunda daga jin baida lafiya duk na rikice.
"Kinyi shiru"
"Kyalesa yaya malik,kadai gaidashi da jiki Allah ya sawake"
"Aa karmuyi haka dake,sannu fa kurin zakiyi mashi"
Rutse idonta tayi tanajin kamar tace eh yabashi amman ajinta zai zube,
"Ka kyalesa yaya malik,aibadole saina yi magana dashiba daga nan ma idan na mashi Addua zatazo,rabu dashi yanzu ma karatu nake zan ajiye wayar,kila idan na samu time anjima da yamma infito inga jikkin zakiyyar"
"Shikenan,amman banji dadi ba da kikace kar abashi,kingashi nan fa har ya miko hannu sa...........karka mun sharri ta dauka dagaske kake ban son wanna game din"
Cewar Abdoul dake shan tea din sa.
Ras taji abunda yace wani abu ya tsaya mata ga makoshi,watau shi ko ajikinsa bai damu ba.kwalla taji sun silalo mata ta kasa gogewa muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka tace"yaya malik sai anjima,kayo mun text din asinitin da aka kaita da no din dakin"
Saiyaji ta bashi tausai,hands free ya saka wayar yadda Alfah zaiji muryarta wata kila shima yaji abunda tajin.
"Shikenan qanwata zan turo maki,amman kizo nan basai muwuce tare ba"
Kwamciya tayi ta dora kanta kan filon mama hakanan kuka yana son kubce mata tace"yaya malik aina ce maka bazan sake xuwa gidan nan ba,kayi hkr bazan iya zuwaba mu hadu dakai Asibitin akwai maganar da zamuyi"
"Shikenan saikinzo din"
Kashe wayar tayi tana kwantawa ta dunkule waje guda tana kuka kasa kasa,wanan abun ya cuceta wai meke faruwa da xuciyata ne haka,Allah kaga niyyata karka saman Abunda zai wahalar dani bacin taimakone nayi,.......ta jima tana kukanta kafin bacci ya sureta.

Tunda suka gama wayar ya silale inda yake ya kwanta,idonsa alumshe sautin muryata yake jin yana amsa kuwwa cikin kunnensa,tabbas kuka take wannane karon na biyu dake iya gane kukanta ta sautin muryarta,yana jin bai khauta ba abunda yayi matan shekaran jiyan,ya zaiyyi ba laifinsa bane zuciyarsa ce ta buga da ganin zakiyya,wadda tsawon shekara shidda ko mai kama da ita bai gani ba,haka xalika baya iya cewa ga lokaci guda daya zauna yayi tunaninta,saboda ya dora ma kanshi wata irin tsanarta da kinta gani yake tunaninta ma inyayi yacuci zuciyarsa,wani iri yakeji wanda bazai iya tantance meyakejin ba,amman shima da yana iyawa to tabbas kukan zaiyyi,don abun yafi karfi sa.
Inama Zai iya lallashinta yanzu inama zai iya ansar no dinta yayi kiranta,bazai iya ba mezai ce mata dawace kalmar zaifara.
Saiya tuna ranar da yake gidan yayarta fushin da yayi biyonsa da tai tana kwalla don ta bashi hkr,kenan ita bata camcanta dayayi mata hakan ba,dafe kansa yayi tare da saitin xuciyarsa don ciwo suke mashi.
Malik ne yafito yayi shirin zuwa company tunda yau shibazai iya fita ba,kallonsa yayi yaga yadda yake shafa kirjinsa da kanshi ya iso inda yake ya zauna yace"daka taimaka ma xuciyarka kabar tunanin tunda bata so,inkuma inbaka no dinta kakirata niba wahala bane wajena,inkai kana ganin hakan kamar da wuya,gata nan na saka maka ka kirata ko karka kirata ya rage naka.daka cire ma kanka wannan nauyin ka fuskanci reality da yafiye maka sauki Abdoul,amman nasan indan nafurta abun da yake damunka zaka karyani kuma zaka dauki zafi,don haka nidai karufa man asiri kacire damuwa,zanje company daga can zan biya store.likita zai dubaka anjima amman kafin nan zanje naga jikin zakiyya."
Uffan bai cemashi ba idonsa a kulle bai bude ba,har malik din yafita kallon wayarsa yayi yaga digit din numbers din daya kera mashi,daukar wayar yayi yana kallonsu na dan lokaci kafin yasa hannu ya goge su tas. Ya maida ya ajiye.

Kuyi hkr babu yawa wlh masassara nake. Daker idan zanyi sanyin idaniya plsss kumun uziri.

It's for sale if u need it meet me 09934722970
Don't share it plsss I beg
[9/17, 3:41 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

*ABDOUL-NASSER NA KUDINE,INKIKA KARANTA BAKI BIYA BA KEDA LILLAHI,GA MAI BUKATA ZAI IYA TUNTUBAR WANNAN NO DIN 09034722970.

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........34

Bata tashi daga baccin ba sai bayan azahar,tatashi tayi wanka ta dawo tayi sallar azahar tana bitar haddarta ta dade bata biya ba,yesmin ta shigo masu da abinci falon mama sun kallon wani film merlin,mama itama hada ita ake kallon.
Suna ci suna hira hankalinsu akan film din yayinda fiyah hankalinta nacan wajen tunanin karyar da zatayi ta fita anjima.
Mama tace"safiyya duk don na hanaki naman nan kike fushi"
Shagwabe fuska tayi "mama bafa haka bane,kawai dai tunanin exam nake wlh banyi wani karatun kirkiba,gashi ko time table bana da ita"
"Addana garin ya haka,to ya za,ai kisan lokacin da zaku fara,kinma tunamun jiya Anty rafeea tazo nemanki"
Mama tace"kitambayeta kila ita bazata rasa ba"
Murna ta kamata ganin ta samu hanyar da take so.
"Aa itama inajin ita tazo nema wajena,amman bari inkira Amatullah nasan ta siya."
Tana jawo wayarta kamr gaske.
Dandanan tayi wayar karya ta ajiye"mama tace ta siya zanje in ansa sainayi photocopy"
Mama tace"haka din za,ai maida hankali kigama kokinje kidawo kar babanku ya tadda bakinan"
Kamar zatai kuka tace"mama yanzun fa rana tayi kibari ayi sallar la,asar basai inje ba bafa nisa keda akwai ba unguwar tasu."
"Shikenan Allah ya kaimu anjiman bandai so kikai magaruba awaje shiyasa."
"Insha Allah mamana bazan Kai ba"
Haka suka cigaba da hirarsu suna kallansu har suka gama cin abincin.
Mama tana mitar baba baidawo gida yaci abinci ba,fiyah nadariya tace"Kai mama Kika Sani ko aiki ya mashi yawa yau."
Ana kiran sallar la,asar tatashi tayi salla tana gama wa tacanza kaya xuwa doguwar riga pink ta wani material da sukai ankodinsa su uku Anty da yesmin sai ita.
Yar karamar jikkarta tadauka ta saka wannan m.card din ciki,sannan ta fesa turare tafito tana cewa mama "mama zan tafi saina dawo"
"Baki tafiya da yesmin"
Bata fuska tai"Kai mama kamar dai wata wace zata bace"
"Aisaiki ta tafiyar tunda kinfison kiyi tafiya kedaya kamar mayya"
Ficewa tayi tana saurin nufar get din estate din.
Cikin Sa,a ta samu taxi bata tsaya ko inaba sai asibitin,ta biyashi ta fito tana kallon asibitin kamar wadda zataga zakiyya saman allon sunan asibitin.
Gefe guda taja tana fiddo wayarta don Kiran yaya malik ta sanar dashi ta iso..........motar data tsayace ta dakatar da ita daga kiran nashi,kallon motar take harta tsaya cikin parkin space din asibitin,kofar farko da aka bude ta driver malik ne cikin manyan kaya saidai banda hula,bayan wani lokaci kuma dayar kofar maizaman banza aka budeta,kafafunsa kurin yafara zirowa amman ta ganesa,bakuma donta taba tsaya wa kallon kafafun nashi ba,aa kawai tasan shikadaine wanda tasan cewa yana mu,amala da combus different colors inyau kaganshi da blue and white to gobe zaganshi da red and onother color din,da alama yana son sakasu.
Tsaye tayi bakin kofar shiga entrance din asibitin don tasan idan sunzo shiga zasu ganta,ba saita kira saba.
Dauke kanta tayi gefe don karma su hada ido dashi.
"Ah qanwata Ashe kinxo yanzu nakecewa bari na kiraki,karaso to saimu wuce cikin"
Jerewa sukai suna cigaba da tafiya yana mata magana.
"Yaya malik ina wuni"
Murmushi yayi yace"lafiya lau qanwata yasu little safiyyah"
"Wlh suna gidansu dazun da safe nabaro gidan,daga gidanmu ma nake"
Tunda takuya baya yake kallon bayanta,tayi halin ko inkula dashi har yanzun dai fushin take kenan,jinjinakai kurin yayi yana take masu baya.
Dakin da aka kwamtar da ita suka shiga,cikin ikon Allah da yardarsa tatashi nurse cema take bata tea abaki,kallonsu take daya bayan daya safiyya ta karasa kusada ita gefen gadon tana riko hannunta I donta yacika tab da kwallah.
Ogan kuwa yana jikin kofa ya harde kafafunsa,ya na tafaman danna waya alamun ko ajikinsa.
"Zakiyya ya jikin naki"
Kanta ta sadda kasa tana jin hawayenfa suna sauka saman hannunta.
Daker ta iya furta kalma guda biyu"dasauki,ya kikaje gida"
Ajiyar xuciya tasauke tana kallon yaya malik matsowa yayikusada su yace"zakiyya yajikin naki fatan kinsami sauki?"
Kwalla take fitarwa sosai muryarta tana rawa tace"nasami sauki yaya malik"
Shiru sukai banda shashshekar kukanta bakajin komi,likitane yashigo yana cewa"alhamdulilla harkun Kara so kenan gata nan tawartsake insha Allah,Amman zata ringa shan wadannan magungunan na kwana uku don mayen daya kamata ya idasa sakinta Allah yasawake Zan salameta yanzun,saiku tafi."
Yaya malik ne kurin ya iya bashi respond.
Ya anshi takardar magungunan yafita yatai pharmacy,za man kurame mukaita yi,shi wancen banda faman dane danne awaya babu abunda yake,zakiyya kuma kukanta take bilhakki da gaskiya.
Nai zuru Ina sakawa da kwancewa nikadai,har yaya malik yaje yadawo.
"Muwuce ko"malik yafada yana kallonsu itada fiyah,kallonsa fiyah tayi tace"ina zaku kaita yanzu,ince dai ba gidansu ba"
"Inbanda can Ina zamu kaita ne uwar tsarawa"
Cewar Abdoul cikin wata irin murya Mai amon mazan taka,wani kallon banza ta wurga Mai tace"to uban shishshigi kaji nakasa dakai?sai kabari nasanyo ka cikin maganata Sanan saika nuna halin naka."
Zaro idonsa yayi yana kallonta cike da bacin rai wanda yasan cewar ba itace takar xomon ba"karkisake kice zakimun rashin kunya,don Zan dagula ranki ne"
Tsaki taja tana sake maka mashi harara tanajin wani abu yana tokare mata wuya,kwallarta nason fitowa.
Kauda kai tayi tana ma malik magana"yaya malik,inaganin karka kaita gidansu,akwai matsala don Allah kakula da zakiyya ina neman Alfarmarka,domin tana bukatar taimakon wani,inda hali kar tasake fita ko ina"
Jinjina Kai yayi yace"shikenan safiyya duk vansan dalilinki na casa haka ba,amman insha Allah za,ai yadda kikace. Kamota muje mota"
Kamota fiya tayi suka nufi hanyar fita,dogon tsaki yaja yana wucewa yabarsu nan.
Fiyah tace"aikin banza ta tsukeka can Mai xuciyar karfe dabatasan tausayi ba"
Yana jinta baitsaya ba ya wuce motar dasukazo da ita,gaba ya bude yashiga,kamar zaifashe don haushi daidai da second guda ya bude idonsa yaga zakiyyar wata irin tsanarta yakeji,zaiga inda malik zaikaita don badai gidanshi ba,mezai zauna yayi gida daya da ita.
Bude masu bayan motar malik yayi fiyah tashigar da ita ta rufe.
Kallonta kurin yake ta glass banda yabonta babu abunda xuciyarsa keyi,amman bazaka taba ganin hakan akan fuskarsa ba,inbacin haushin dake kwance sama.
"Kika rufe ke bazaki shigaba"
Murmushi tayi tace"yaya malik aini nan gida Zan wuce,don bance xan dadeba gaskiya amman ina zaka kaita."
Shafa kansa yayi yace"banda wajen ajiye zakiyya daya wice gidanmu"
"Amman wancen zaibari kuwah"
Dariya yayi yace"rigima ce kurin zuyi dashi karshe baida yadda zaiyyi dani"
Numfashi ta sauke tace"shikenan,banda ishashshen lokaci yaya malik,zan wuce ga wannan m.card din ka ajiyesa wajenka ranar Monday muke fara exams,Zan samu time dazamuje ga daddy sai akunnashi ani meke ciki,nan da kwana biyu kenan,nasan xuwa lokacin zakiyya ta Samu sauki saitayi mana bayanin abunda yafaru da ita

Please Login or Register in order to submit comment