Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shak'oni ya dunga jibga karshe ya kasheni abanza.don naga jiyake da karfi kamar doki."
Dariya fiyah tayi tace"ba take yake ba lokacin ai."
Feea tace"wlh kuma guy din ya gama had'uwa ban tab'a ganin ruwan kyau ga namijiba irin nashi Zan so in samu saurayi kamarsa."
Dariya fiyah tayi tana kallonta tace"kozaki shiga daga ciki naimaki hanya."
Zaro ido feea tayi tana rufe baki tace"rufaman asiri wlh ko k'ashina bazai bari ajikina ba,keee wannan guy d'in banga fitsararrar dazata tunkarai da maganar soba,aikoba so wannan ixxarsa ma da kwarjininsa sun sata rugawa,balle yadda naga yana da bakar zuciya."
Dariya kurin takeyiwa feea ganin duk ta rud'e lokaci guda alamun dai wannan Marin bata manta dashi ba.

Karfe d'aya da kwata tafito daga cikin makarantar,feea tace tazo suwuce tace ai bagida tayi ba,zata dawo karfe hud'u suna da test.
Bata sha wuyar samun abun hawa ba tawuce gidan Anti jamila,don yau idan bata jeba tashiga ukunta wajenta,takakkiya zatayo Mata har gida.
Babu laifi mijinta yana dashi,don babban gidane Mai plat biyu shiga tayi tana doka sallama,Mai aikinta ce take ta ansawa,shiga tayi cikin falon tana kallonsa an sake mashi kujeru da TV plasma,ansaka wata kantamemiya ga sabon canis kafet Mai shegen laushi,andai gyara falon kamar na sabuwar amarya,bama falonba ta lura gyaran duka gidanne.
Magana tajiyo cikin bedroom d'in kamar ita da wata ne, kasa kunne tayi tajiyo muryar wata tana cewa"wlh jamila maganin nan shayanzu magani yanzu,kinsan da kanwata tayi anfani dashi,saigata da kanta tana nemana ruwa ajallo,dakau kamar bazata siyaba,kinga wannan sunan sa rijiya tunjum,wlh shima badai aiki ba nake gaya maki makociyaya data siyai,can cikin dare naringa jiyo ihun maigidanta,washe gari saigata wai insiye matashi duk,Abban Ahmad bai tab'a Mata kuka ba insuna tare sai jiya,ai ban sayar da kayan banza kinsani.yo in gaya maki da mijin yayata dan rainin wayau ne,yaraina ta nake gaya maki,baya kusantarta saiya ga dama haka bai zaman gida,ke Abu yazo har yakai ga Saki jamila,dakerfa iyaye suka shiga lamarin,lokacin Ina Ibadan Dana dawo lokacin ta koma najefa na tsumata,nahad'ata yadda yakamata karshe saigashi duk inda zata shine kekaita yana rik'eda jikkarta."
Ajiyar xuciya ta sauke tace"lami ya isa haka,ki ajiyemun wannan da wad'annan,na wane kud'insu."
Tana washe baki tace"wlh don kece Zan maki sauki ki bada 10k ai babu cuta tsakaninmu."
Tace"toshike nan ki ajiyemun sy wajenki karki sugar wa da kowa,in na ta shi zan ansa."
Dahaka suka fito tana yimata sai anjima,ganin fiyah falon yasa ta rik'ebaki tace"shegiya kin zo shine baki sallama."
Matar ficewa tayi tabarsu fiyah tace"anti ya za,ai kiji bayan kunshige ciki sai ciniki kuke,wai anty da wannan uban cikin ma sai kinsha kayan Mata,baki bari ki haihu."

KUYI HKR WLH NAGAJI,MUHADU GOBE IDAN ALLAH YASA MUNKAI DA RAI DA LAFIYA.

MRS BB
MOM MUHSEEN.
[9/17, 3:35 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞
💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........9

"Don ubanki cewa nai zan sha."
Dariya fiyah tayi tana kunna kayan kallo tace"Allah yabaki hkr,naji ai sai bayani take kora maki kuma inba siye zakiyi ba mezai kawota."
Tsaki taja tana shigewa wata k'ofa tana cewa"to siyen zan don uban mutun ya hanani,ince kud'i nane bana wani ba."
Fiyah dai dariyar take don sun saba indai halin anty jamcy ne.
Fitowa tai da wata fation leda ga hannu ta zauna daker don cikinta yatsufa.
Tace Mata "inkina jin yunwa ga abinci can kan dining,akwai kunun aya a frig don naga kinaso nasa akai maki."
Cikin jin dadi tace"aikuwa wlh ngd Anty kinsan kuwa na kwana biyu ban sha ba,Allah yasa baiyyi k'ankara ba."
Ta fad'a tana isa wajen frig din ta dauko"aikuwa baiba nagode anty,Allah yaraba lfy."
Hararata tayi tana murmushi "baki cin abincin kenan"
Kunun ayar take sha tana lumshe ido tace"aa anty ban jima da cin julluf a cap ba,barni da wannan ma wlh ya isan.ina uncle yahya."
Gyara kishingidar ta tayi tace"bai kai ga dawowa ba,mezai maki."
Dariya tayi "aa nikuwa mezai mani anty,daga tambaya."
Tab'e baki tai tace"ga sak'onki inji muhsen,naso ku had'u kuyi bankwana da Allah kadai yasan arzikin da zaki samu."
Fara,ar dake kan fuskarta ta ragu sosai,cikin halin ko in kula tace"ni wlh da baki ansa ba,banson wannan bibiyar da yake mun ni nace bayanzu zan fara soyayya ba,balle akai ga maganar aure duk wannan hidimar bata da anfani ki ajiye mashi kayansa sadda ya dawo kibashi ni gaskiya bana so."
Wani kallo take mata cike da haushi,cikin fad'a tace"iyye,oh ke baki tashi soyayya ba balle ai maganar aure,kina nufin duk godolon da yake akanki baida wani anfani,yaro natsatstse kyakkyawa son kowa k'in wanda yarasa,kimaida hankali ki sakeshi ba fata nake maki ba daker zaki samu kamar sa."
Turo baki take tana k'unk'uni k'asa k'asa.
Dungure mata kai tayi tace"ubanme kike cewa halan ma zagina kike."
"Ni anty ba zaginki nake ba,wlh idan baba yasan ina kula wani fada xai man kuma yace aure zanyi in bar karatuna."
Harara take dalla mata "dallah can sokuwa ni ba saida nai aure na gama karatun ba,meyasa man kuma shikanshi baban idan yasan kin samu tsayayye ai murna zaiyyi,tunda baida wani buri daya wuce yaganki gidan miji."
Murmusa ido take tana y'an harare harare aranta tana cewa "wlh insha Allah kozan aure saina ga bayan matsalar *ABOUL-NASS*."
"Ubanme kike cewa kikiyayeni wlh,kibar ganina da wannan cikin ubanki zanci anshi nan kisata caji kafin sadda zaki tai,kuma inkinje gida kicewa mama da baba uncle dinku ya baki nasan bakinsu zai mutu."
Cikin rashin walwala ta ansa tana dubawa kwalin waya ne sabuwar Samsung galaxy s9 pink color dandanan kaunar wayar ya kamata,badan komi ba saidan suringa communicating da malik,murmushi tayi tace"ashe wayace anty,aikuwa ngd kice ina mashi godiya."n harare harare aranta tana cewa "wlh insha Allah kozan aure saina ga bayan matsalar *ABOUL-NASS*."
"Ubanme kike cewa kikiyayeni wlh,kibar ganina da wannan cikin ubanki zanci anshi nan kisata caji kafin sadda zaki tai,kuma inkinje gida kicewa mama da baba uncle dinku ya baki nasan bakinsu zai mutu."
Cikin rashin walwala ta ansa tana dubawa kwalin waya ne sabuwar Samsung galaxy s9 pink color dandanan kaunar wayar ya kamata,badan komi ba saidan suringa communicating da malik,murmushi tayi tace"ashe wayace anty,aikuwa ngd kice ina mashi godiya."
Kallon mamaki take mata da tuhuma.
"Ai nai zaton wani abunne na daban ba waya ba don yanzu nafi bukatar ta wlh."
Sake dungure mata kai tayi tace"banza kawai ki hanzarta kisa caji ga no dinsa nan ki kirasa don har sabon layi yasa maki da katin dubu da dari biyar,don Allah fiya kikirashi wlh muhseen yana masifar sonki,zanso ki samai kinga gani gaki kuma mahaifiyarsu batada wata matsala wlh lafoya lau zaku zauna kina ganin dai yadda nake zama dasu kamar zasu goyani."
Tabbas maganarta haka take iyayensu mutanen kirmine kuma yan gidansu basu wata matsala,muhseen da uncle yahya uwa daya uba daya suke,kuma suka dai ne maza sai kannensu mata su biyu,sun matukar son Anty jamila kamar yaua haka suka dauketa mamansu kau d'iya ta dauketa,sunada arx'iki sosai kuma baisa sun dauki kansu wata tsiya ba.
Kasai muhseen dinne ya cika yaga ko wata macen bata gwada mashi iyayi,kilan in iya saurarensa idan nagama da matsalar su ABDOUL-NAS.
murmushi tayi tana kallon Antyn tace"sorry anty zanty tunani akai don allah kiban lokaci,kuma zan kirashin idan naje gida yanxu test zan je nayi makaranta."
Cikin jin dadi antyn tace"kokefa sofyn mama,wlh muhsen baida matsala zakiji dadinsa."
Nata ce komi ba ta tashi ta sata cajin sannan suka cigaba da hirar su kamar komi bai faru ba.
Sai wajen karfe uku tatafi kasamcewar tayi waya da wata yar class dinsu cewar malamin bai zoba yace kowa yatai sai gobe da yamma.
Gida ta wuce tana murnan wayar,don asaukake basai tayi ta daukar ma mama waya ba.
KO da taje gida da wayar mama said mamaki take saida taji daga inda wayar take sannan hankalinta yakwanta,amman duk da hka tana tsoron abunda baban su zaice kan wayar.
Yes min kuwa kamar itace mai wayar sai jin dadi take,wayar tashiga dubawa kasancewar irin wadannan wayoyin tasan su tana anfani dasu wajen y'an class dinsu,yanzu kuwa ta huce wulakanci idan zatai browsing,basai taje tayi ta are are ba.
No din malik ta saka tayi save da sunan sa Abdul-malik.
Bayan dawowar baban su mama take sanar dashi wayar da mijin jamila ya ba fiyah,kiranta yayi tazo da wayar ahannu yace"sofiyya bazan hana ki rik'e waya ba,amman don Allah zan rokeki kirike mutuncinki,kar waya ta canza maki d'abi,u kar waya ta canza maki hali kar ta jaki ga abunda kika san zaki samu damuwa kisaka kanki."
Gabanta yafadi saitake ganin kamar Baban yasan manufarta,amman ai Allah bazai kamata da laifi ba tunda dai harga Allah taimako take niyyar yi tana son mai doshi cikin rayuwa irin wadda yayi duk da dai basanin abunda ya faru dashi tayi ba.
Cikin sanyin jiki tace"insha Allah baba zan kiyaue kasa mun Albarka to"
Murmishi yayi yace"sofiyna kenan to Allah yayi maki Albarka ya baku miji na gari."
Yesmin ta shagwabe fuska tayi tace"baba nifah to."
Dariya duk aka yi mata yace "kema Allah yayi maki Albarka ya baki miji nagari."
Tana jin dadi tace "ameen baba."
Bayan sun koma d'aki ta shiga kiran no d'in malik,lokacin ma yanata aiki don cikin satin yake saka ran zuwa switzerland saro kaya.
Alfah yana zaune kan kujera idonsa a lumshe ya shiga duniyar tunani,ahankali kuma zaka ga hawaye suna bin gefen idonsa,gorgiza kainkawai malik yake don baisannya zayyi da Alfah ba,yakasa daukar kaddara yakasa hkr da rayuwar ya ansheta ayanda tazo mashi.
Wayarsa yaji tayi kara ya dan kalla yaga babu suna kamar zai share saikua ya tsaya da aiki ayakin ya dauka,
tare da sallama.
Tana kwance lokacin ma harnyesmin tayi bacci don bata da wuyar bacci .
Itama cikin cool voice d'inta tayi mashi sallamar.
"Assalamu alaikum,ina wuni yah malik."
Jingina yayi daga jiin kuerar yaa maida hakalinsa kan wayar don yamaso saiwaye.
"Wa,alaiki salam wake magana pls."
"Sofiyya E-ladan."
Murmushi yayi yace"okyy fiyah ce,ykk yakika koma gida."
Idonsa nakan Alfah da har lokacin bai bude idonsa ba kuma ba bacci yake ba.
"Lafiya lau wlh yah malik ya na barka ya kuma rikitacce abokin ka."
Murmushinsa ya fidda mai sauti yace"bari nabaki shi sai ku gaisa."
Zaro ido tai kamar yana gabanta tace"rufan asiri ina zaman lfy wannan ai saika yah malik,wazai iya da wannan rikicin."
Dariyarsa ta fito har Alfah ya bude idonsa yana kallonsa "kin cika tsoro wlh,amman soon zaku saba yanzu ya zai muhad'u gobe around 4:00."
Ajiyar zuciya tayi tace "inada test lokacin yah malik amman mezai hana da safe zuwa yammar."
"OK hakan ma is ok 10:am yayi mki ko."
Murmushi tayi tace "yes yayi insha Allah amman ina zan sameka."
D'an shiru yayi yana kallon yadda alfah yake mashi kallon tuhuma yace"zan maki text da safen."
"OK yah malik sai da safe zan kwanta."
Sallama sukai ya ajiye wayar har lokacin idon Alfah na kanshi yasan soyake yayi mashi bayanin wacece amman miskilancinsa bazai barshi ya tamaya ba,shima kuma sai ybiye shin yayi shiru ya cigaa a aikinsa.
Zuwa can ya tashi cikin fushin sa na farillah yayi ball da table d'in dake gaban sa ya wuce bed room d'in sa.
Malik yace "Allah ya yaye maka ya kawo maka sauki cikin lamarinka."

DON ALLAH KUYI HKR HIDIMAR SUNA MUKA SHIGA SHIYASA BAKWAJINA KULUM,AMMAN DAMUN GAMA INSHA ALLAH ZAKUJINI KUYI MALEJI DA WANNAN.

MRS BB CE
MOM MUHSEEN.
[9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

*Wannan page d'in nakune masoyana,inhar kinsan ke masoyiyata ce mai nuna kauna gareni to nakine na sadaukar dashi gareku,saboda irin soyayyar da nake samu daga wajenku,Allah yabarmun ku ya kuma kara mana kaunar juna,kuma baby humaira tana gaida kowa da kowa da irin aduar da take samu daga gareku.*


🅿️.........10

Fiyah ta gama komi yau da safe kasancewar yau Wednesday baba baya fita da wuri sai takwas na safe koda ya fito yaganta har takwas bata yi shirin fita ba yace"sofiyya yau babu makarantar ne."
Tana sauke tukunyar danwaken da zasu ci da safen tace"baba ina kwana"
Ya ansa cikin kula tace"aa baba akwai amman sai ten saboda malamin bazai zo ba da zai ma na seven to nine thirty baida lafy"
Ta gilla mai karya nashi ta zubo mashi da kununsa na gyada data dama,yana kalacin suna hira har sadda mama ta fito daga d'akin sa ta gama gyara mai,itama ta zauna aka hau hirar tare yesmin ce cikin uniform na makaranta ta fito tana ma su saita dawo,naira dari yabata ta yi break sannan ya bata dari uku tayi abun hawa.
Godiya tayi sosai ta fita tana d'aga ma addarta hannu.
Shima tashi yayi bayan ya gama yaba fiyah kudin ta itama ya yimasu saiya dawo suka bishi da addua,mama tace"tunda bazaki makarantar ba ki tashi ki kwab'a alkubus yayanku yana tafe yace mun kiyi mashi."
Gabanta ya fad'i don sunyi da malik zasu had'u karfe goma,intace saitayi wani alkubus bata san ranar fita ba,cikin murna tace"mama dagaske yah zaizo aikuwa zanso in shirya mashi abinci wlh,amman karfe goma inada lecture wlh kuma kanta zai mana test gobe,bacin haka aida bama zan je ba."
Maman tace"to abunda zai ai kafin lokacin yayi tashi ki d'ebo fulawar ki kwab'a mun,saina idasa nima da fita zanyi inje gidan yaya balara ba,ingano hasana bata da lfy."
Tashi tayi ta je ta dauko kayan had'in tazo ta fara kwab'in tana cewa"meyasa meta mama"
Tace"kinsan tana da iska to daga makaranta aka maidota sun matsa mata wlh,basu bari ma tayi karatun karshe dai kilan day zata dawo."
Nan suka ci gaba da hirar suna jajanta abun,hasana diyar yayar mamace dake can wata unguwa bama nan cikin abujar suke sosai ba.
Karfe tara da rabi tayi wanka ta shiga shiryawa doguwsr riga tasa mai dan karen kyau,don Antynsu ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta tare masu sitira,duk da shima baban ba baya ba duk salla kala biyu yake masu,jamila ta kara masu kala gida da gyaluluwa da takalma,har mada kayan kwalliya da turaruka shikuwa jalal shike dauke duk rabin hidimar gidan,yana da kokari sosai don inzai zo daga kaduna d'unkuna yake zoma baban dasu da kuma takalmomi kayan abinci da dadai sauransu.
Tana cikin saka turare text d'insa ya shigo wayarta,saurin ajiye turaren tayi taduba.
_ina silver bird place guiding yanzu haka ina jiranki._

Shiru tayi tana tunanin yadda zatai ta isa wannan wajen,anya Malik yasan kuwa inda yake cewa ta samai,wannan wurin ai ba na irinta bane,kuma kudin taxi kansu sun isheta don dari bayar bata kaita ta maidota..........abayarta milk ta saka tana jimamin abun,wsta yar jakace mai kyau ta dauka ta fito mama na tsakar gida tana yankan alayyahu na taushen da za,ai tace"har kin fito."
Tace"mama don Allah in anshi dari uku wajen dalha,hand out zan siya na manta ban gaya ma baba ba."
Kalonta take kafin tace"shikenan kije ki ansa allah ya kiyaye kiyi addua idan zaki fita."
Sallama tayi mata ta fita ta anshi kud'in ta wuce.
Taxi ta tata bakin titi ta gaya mai inda zai kaita saoda sukai ciniki sannan suka tafi.
Sadda suka je get din arufe ta rasa yadda zatai don wajen yana da k'a idoji wayarta ta fiddo ta mashi text cewar ta iso yazo yayi mata iso.
Tana nan tsaye na wasu minty na sannan taji an bude wajen,malik ne yasha kananan kaya sunyi masifar ansar jikinsa,don shima malik badai kyau ba,murmushi yayi mata yayi mata nuni da cewar ta taho.
Itama ansar murmushin ta bashi ta isa inda yake suka jera har cikin palace din,waje ya had'u yahad'u iyakar had'uwa,fad'an yadda yake b'ata bakine don wajen sai wane da wane suke zuwa don wajene na shak'atawa ne.
Wajene na musamman ya sauketa rumface wayayya anjera kayan cinye cinye da lashe lashe.
Zama tayi shima ya zauna yana kawata fuskarsa da murmushin shima,lemu ya samata tare da tura mata plet d'in snacks gabanta.
"Bismillah tukunna,kafin infara zuba maki surutu in kwareki."
Dariya tayi tace"haba dai yah malik."
"Ehy mana,inason in sanar dake waye ABDOUL-NASSER ALFAH,don kisan ta ina zamu shawo kan abun."
Jinjina kai tayi ta d'an kurb'i lemun ta d'anci springros ta goge bakinta da tishu.
"Yah malik ina jinka,naci ai wlh bana jin yunwa nayo kalaci sosai."
Baice komi ba ya gyara zaman shi yafara magana kamar haka cikin sanyi da tausasa harshe.
"Abdoul Nasser muazzam kabir canji d'ane ga Alh muazzam canji shugaban y'an canjin Abuja gaba d'aya,yyi suna yayi fice a k'asa baki d'aya,domin bai anan kadai arxikin sa ya tsaya ba,ya rik'e minister a oxport sannan yana da kamfanin motoci M.K motors dake cikin garinnan,wande kika sani sannan yana kasuwancin shinkafa babu inda motocin sa basa zuwa,legos,ibadan,adamawa,maiduguri state daban daban.atakaice Alh muazzam mashahurin mai arzikine na bugawa ga jarida,babu inda sunansa baiyyi yawo ba sannan manyan yan siyasa Suna hudda dashi saboda jama,arsa mutunne shi da Allah bai hore mashi yawan kyauta ba,ba marowaci bane amman kafin ya bayar ana jimawa,baidamu da talaka ba hasalima baisonsu baison su rab'eshi ko kadan,inkinga wani na cin arxikinsa to kuwa abokinsa ne mai kudi irinsa,ko wanda bai kaisa ba.wannane babban kalubalensa.
Agefe guda Alh muazzam matansa biyu hajiya mariya itace uwar gida,Allah ya basu zuria itada Alh duk mata guda hud'u,akwai Amina da Haulat zuwairat sai khadija.sai agolarta data zo da ita gidan zakiyya duka yarinyar bata wuce shekara ashirin da daya ba ayanxu sa,ar ni'imah ce kanwar Alfah.
Amina da haulat yayyene ga Abdoul-naseer yayinda zuwairat da khadija suke k'anensa,hajiya Ushe itace mata tabiyu ga Alh muazzam kuma uwa ga Abdoul,Allah ya azurtata da samun d'a namiji daya tamkar da dubu ko ma ince miliyan,don shine d'a na farko wajenta dayar macece maisuna ni,imah don su biyu kadai Allah yaba mami.
Hakikanin gaskiya zaman lfy yayi karamci gidan Alh muazzam,domin hajiya mariya wadda ake kira da umma wstau uwar gidan tana bala,in jin zafin mami badan komi ba saidan ita kadai ce wadda ta haifa ma Abbi magaji,kuma magajin jarumi mai dakakkar zuciya,mai tsayuwa kan lamarin gidan baki daya,don komi dakika sani game da dukiyar Abbi Abdoul shine ja gaba wajen tafiyar da komi,har su matan nashi komi suke so to shi zasu tambaya,haka kannensa da suma yayyen nashi.
Wannan ne ya jawo matsanan ciyar tsana da kiyyyar su wajen umma da yaranta.
Bata kaunar Abdoul ko miskala zarratin,yayinda shikuwa kamar ya kwanta mata wajen biyayya,domin wannan umurnine daga mami ta bashi shida ni'imah,cewar kome umma zatayi masu karsu kuskura suyi mata koda kallon banza.
Bayan yaran yaran umma daga baya ta d'auko d'an kanwarta rik'o gidan mai suna Mamman.saika rantse anan aka haifeshi,Abbi bai ce don me ba don shi bai cika damuwa da irin wadannan abubuwan ba,sannan rigimar cikin gidanshi yasan da ita amman bai tab'a magana ba.
Shiyasa umma take tsula tsiyarta yadda takeso sannan abu na mai ciwo ga halayen Abbi shine duk abunda akazo akace mashi wane yayi,bazai tab'a bincike ba zai yarda kuma yayanke hukunci,ko waye kau amman banda Abdoul,don babu wanda yayiwa yar da irin wadda yayi wa Abdoul.umma tasha kai mashi karar Abdoul cewar yayi mata kaza yayi mata kaza amman kullum maganarsa guda itace "Naseer baxai yi abunda zai b'ata rai na ba mariya,kidai ji tsoron Allah."
Shiyasa ta dauki tsawon lokaci batayi nasara akan Alfah ba,don kuwa Abdoul ya zama tauraro mai haske xuciyar iyayensa,mutunne mai fara,a koda yaushe zakiga fuskarsa cikin walwala,ko b'ata mashi kayi zaiyyi murmushi kawai ya wuce bazai tab'a ce maka don me ba yanada jama,a sosai don yana hud'd'a da talakawa sosai,yana kuma sakarmasu aljihunsa ko fita sukai da Abbi marok'a suka rufesu tofa shizai ringa masu b'arin kudi.Alfah Allah yayi shi mai dogon hannu,jin dadinsa da Abbi keyi yasa ya gina mashi Wani kantamemen store dake cikin garinnan nasan zaki sanshi ALFAH STORE SHOPPING MALL ya cikashi da kaya ta ko ina kuma du abunda kikeso na b'angaren more rayuwa inkika shiga Alfah store kin samu.
Bacinan ya sakarmashi ragamar kamfanin MK motors duk wasu kudi dake shiga da fita to sai sun biyo ta wajen Alfah sannan suje ga Abbi.
Fiyah ta katseshi tace"waye daddy wanna da muka ganshi station."
Ajiyar zuciya yayi yace"Daddy babban aminin Abbi ne,kuma d'an uwansa guda tal dasuka fito ciki guda,shima yana cikin estate dinan cikin mai tama."
Shiru tayi ta sake cewa meyasa aka samai Alfah."
Murmushi yayi yace"wannan sunan daga mami yake,don tace tunda tataso wajen yayarta bayan rasuwar iyayensu take son yaron yayarta mai suna Alfah,sunyi soyayya kamar su cinye juna karshe uwar mijin yauar tata ta zab'a mashi mata.mafarin kenan mami data haifi Abdoul tace inkiyarsa kenan Alfah shikenan Abdoul-naseer ya b'ace saidai Abbi kawai ke kiransa da ABDOUL-NASS,wlh fiyah Abdoul ya fuskanci bak'in ciki ta dalilin umma,don kau umma tun Abdoul yana cikin ciki take son ganin bayansa Allah bai bata dama ba,domin kuwa Allah yace sai yafito saiya rayu rayuwa mai kyau.Abdoul yana son y'an uwansa yayinda sukuma babu abunda suke son gani irin mutuwarsa,don mahaifiyarsu ta riga ta dasa masu tsamarsa tun suna y'an kususan su,haulat da Amina sunyi aure suna gidan mijinsu sai zuwairat da khadija da kuma zakiyya.
Ana cikin wannan hali fiyah Abdoul ya fad'a soyayya da zakiyya diyar umma agolarta data zo da ita gidan.
Wanda zakiyyar itace ta fara nuna mashi tana sonsa,don tunda tazo gidan Allah ya dasa mata kaunarsa,amman komi suke yi babu sanin uma,ab'oye sukeyin kaunarsu ni kadai na san da wannan soyayyar."
Sake katseshi tayi da cewar "yah malik ina kai banji taku alak'ar ba,nai tunanin kaima d'an gidanne."
Ruwa ya d'ansha sannan yace.......

Mrs bb ce
Mom muhseen.
*Comment and share it*
[9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........11

"Banda wata alak'a da Alfah sai abota ko nace amintaka,na had'u da Abdoul wajen dawowarsa daga taron siyasa ya wakilci Abbi wajen taron rantsar da wani minister.abunda kuwa ya had'a mu shine Richard card na waya,go slow ya tsayar dasu nikuma Ina bin layin layin motoci ina masu tallar wani sabon layi da kuma katin waya,Ina daidai motarsu naji drivern yakirani abunka da maison ciniki aguje na iso har ina ingije wani mai Babur,ya dunga antayo man zagi nibama tashi nake ba,cinikin da kekirana nake ma hanzarin isa gareshi.Ina shashsheka nace.
"Gani"
Driver yajuya baya yace"yallabai gashi nanawa zai mik'o."
Abdoul dake baya hakimce yasha wat a arniyar gizner yace"anso duka kona na wane."
Jinai kamar anmun gafara,don kuwa wannan cinikin yayi masifar yimun dadi Ina rawar jiki na ciroshi duka na mika mashi daman na 5k ne kawai.
Maimakon naga 5k fiyah sai naga 15k kankace me tuni idona yacika da kwallah,godiya zanyi Amman baibani dama ba yamiko min card dinsa yace on Tuesday inasamai maitama around 6:30 haka suka barni da farinciki kamar me,ranar har kukan dadi nayi.
Don ban tab'a samun kyauta makamanciyar irin wannan ba,na shigo Abuja cikin bakin talauci da rashin gata,nine buga can nine buga can,haka nake rayuwa.
Shago na Kama Ina za man haya,duk bayan wata uku nake biyan dubu goma sha biyu.
Aranar da ana gobe zanje wajensa, sai naga dare ya jima bai kare ba,har gajiya nai da kwanciya haka dai har gari ya waye,na fita buge bugen dana Saba,don wanan kudin bai hana ni fita nema ba.
Still titin na nufa na hanyar lugbe na had'a omona ina wankin glass Ana bani naira dari...........inata aikina har sadda lokacin tafiyata yayi shagona na koma na unguwar gwagwalada nashirya na hau taxi zuwa maitama estate.
Numfashi ya sauke idonsa akan na fiyah datayi shiru ta na saurarensa yace"kinga munsaki layin Maigida Abdoul-naseer mun Kama wani ko,inason na baki ansar tambayarki kafin mukoma ga asalin abunda ya zaunar damu kafin lokaci yayi."
Gyara zama tayi fuskarta duk tayi kalar tausayi tace"yah malik kenan duk hasashena akan alakarka da.....Abd...abokinka Ashe ba haka bane inson inji naka labarin rayuwar don har ciki xuciyata ahaka ma ya nuna mun kasha wuyar rayuwa."
Ruwa yasa Mata ya mik'a mata yana murmushi Mai kyau da tsari yace"abun kuma yayi mun yawa hajiya sofiyyah,kibari na karashe maki na mutumen mana tunda naji sunansa ma wuyar fada yake maki."
Dariya ta d'anyi tasha ruwan kad'an tace"uhm Ina jinka ka cigaba."
Cigaba yayi da cewa"sanda muka isa unguwar daker jamian tsaron dake area wajen suka barni na k'ara gidan,don card din daya bani duk address din naciki.
Sanda naga wannan daula ta gidan numfashina saida yaja,najinjina irin mahaukatan kudin da aka narkar wajen,maigadi nagaida yana tambayata wanake nema.
Kallon card d'in nayi nafada ma shi sunansa yace to nazauna nan bari yaje yasanar dashi aciki.
Inanan zaune yaje ya hadawo yace muje nakaika masaukin bak'i,haka nabisa baya Ina sake kalle gidan kamar Wanda yazo daga riga.
Haka

Please Login or Register in order to submit comment