Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin damace karasa"
Ajiyar xuciya yayi yana saka key din motar jikin makunnin yace"ta riga ta wuce idan darabon kiji idan nasake samu may be zakisani"

"Shikenan yaya Abdoul nagode nima,amman karka manta da maganganun mu na baya akan alfarmar danake so kaimun,don Allah ka auri zakiyya domin tana sonka........."kekuma fa bakisona?"
Cigana tai batare data tanka ba.
"nibazan iya fadar irin son da take maka ba,nasan dai tayi nisa acikin duniyar kaunarka,kuma ta cancanta da zama matarka.........."ke kuma fah"

Runtse idonta tai tanajin kamar yana zaneta da dorina saboda yadda takejin kuna akan abunda yake fada,girman kai baxai barshi ya iya furta mata yana sonta ba,sai itace xata xubda kimarta da darajarta tace mashi tana sonsa,abunda batajin zata iya koda hakan nanufin kwanciyarta gadon asibiti.

"Koda ba aimun miji ba bana jin hakan zata faru tsakanin mu"

Cikin sauri yace mata"why"
"Saboda ban tsara haka araina ba,hasalima ni ba irinka nake mafarkin aure ba,kayi hkr"
Baitaba jin ta bata mashi rai irin hala ba,kasa magana yayi yatada motar yana jiran ta fita yafigeta yabar wajen ko zai samu saukin wannan ciwon da tasake jiwa xuciyarsa.
Saida tayi maganar taji bata kyauta ba,taji gabaki daya hankalinta yatashi.
Har hakan ya nuna ga fuskarta jiyowa tayi zatai magana.
Ya daga mata hannu cikin wata murya mai nuna bacin ransa yace"plzzz out"
Jikinta yayi masifar sanyi ta fice kuka nason kubce mata,kamar antada tiyagas haka Abdoul yatada kura wajen yatafi.
Aguje tashiga gida ko kallonsu mama dake tsakar gida batai ba ta hige dakinsu,adakin ma toilet ta rufe da kuba ta zauna kasa tana kuka mai taba rai..............

*don Allah kuyi hkr wlh yau kwance na yini banda lfiy,wannan ma karfin haline plsss kuyi mun uxiri lafiya na gaba da komi
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

πŸ…ΏοΈ.............52

"Kayarda da maganata babansu,wlh nayi imanin safiyya bazata taba bujirewa bukatarka ba saboda radin kanta,ta hango abunda mu bamu hangaba,anacewa abunda babba yahango yaro ko yahau rimi bazai hango ba,amman wannan karin maganar tasha banban da abunda yafaru,babansu ka godewa Allah daya baka yarinya tamkar da dubu safiyya nada hankali,tana da biyayya tana hangen nesa uwa uba hakurinta da kawaicinta,ta gaya mun cewa wlh bacin yadda taga yasmin ta shiga wani hali saboda jin abunda kayanke tsakanin safiyya da muhseen,da bazata taba nuna ma kowa bata sonsa ba,zata auresa kodan tayi maka biyayya tasan kuma bazata tabeba don kau mahaifinta ta yiwa abunda yakeso,kaduba kaga wannan zamani yadda wasu yaran suke jefa rayuwarsu cikin halaka saboda iyayen suna matsawa suyiwa yaransu auren dole,kanaji diyar yadikko harira har yau ba aganta ba saboda auren dolen da suke shirin yimata bata so,mafarin ta gudu kenan yau wata uku.sannan danginku kasan anyi haka diyar kawu shazali data yi yunkurin kashe mijin itama ta kusan kashe kanta,gobara ta saka agidan Allah ne kadai ya fiddasu basu mutuba suduka,saboda bata sonsa kuma yaki rabuwa da ita tagwammace sumutu suduka data cigaba da zama dashi,kaduba maganata babansu kuma kayi shawara da wani wanda kasan zai gaya maka gaskiya,idan kana ganin ni tawa ba komi bace"
Tatashi zata bar mashi wajen don iyakar kulewa takule,ganin yadda yake yunkurin aurar da diyarsa mafi soyuwa garesu ga wanda bata so,bacin ga wanda ke sonta kuma bazai amunce da hakan ba.
"Dawo nan mamansu"
Badan ta so ba tadawo don iyakad shekarun dasukai atare irin haka na jimawa bata faru tsakanin su ba.
Babu ma,auratan da basa samun sabani saidai ace na wasu yafi nawasu.
Dawowa tai ta zauna tana jiran abun da zaice.
"Inbanda ke wagareni dazai bani shawara irin wannan dakika ban?"
"Uhm babansu kenan na dauka kaima ai kayarda da maganar nan da akecewa mata tunaninsu kalilan ne,basu iya bada shawara ba"
Murmushi yayi yace"to aa banyarda da haka ba,don tawa matar tawice anan indai fagen hangen nesa ne da kuma tanadin abunda zai daidaita zaman takewar iyalinta,nakuma ji dadin wannan shawara kuma hakika nayarda uwata wajenki duk ta dauko wadannan halayen"
Sadda kai tai tana murmushi"uhm Babansu kadai fadane amman safiyya kam ai kaine gaba daya"
"Insha Allah zansan abunyi hakika da munyi kuskure babba,Allah ya kara rufa mana asiri."

Duk hirar da suke akan kunnen fiyah da yesmin wadanda basuyi bacci ba kowa da abunda yake damunsa,yesmin batasan Addarta batai bacci ba amman fiyah tasan yesmin idonta biyu.
Tun bayan data gama kukanta a toilet ta fito ta kwanta tana dana tasanin abunda ta gaya ma Abdul dinta.
Amman wani shashe na xuciyarta yana gaya mata gara ta ja ajinta gara ta nuna mashi ita din mai ajice hakan zaisake jansa ga kaunarta.don sun ganin su sunda abunda dole ma yarinya ta kware masu,wanda hakan yakeja wasu matan suna rasa darajarsu wajen maza saboda tun awaje kin xubar da kimarki........har ga Ko son Abdoul zai kashera baxata iya kallan idonsa tace tana sonsa ba,haba ina kunyarta take ai mama ma saita kusan dukanta saboda fada.haka taraba dare tana sakawa tana kwancewa,adduarta guda kada Allah yasa xuciyarsa tayi na,am da auren zakiyya domin tanajin tafafi zakiyya jin kishinsa axuciyarta,jitake muddin haka tafaru duk wani jindadinta yakau adoran duniya,kawai dai ita tana iya control din nata ne tana iya danneshi alokacin dayake sata abunda ba daidai ba......ta furta ya aureta ne don bata da wara mafita,don kuma zakiyyar ta dace dahaka tayi sadaukar da rayuwarta ne dominsa,bai dace ya wofintar da ita ba.ajiyar xuciya taja sosai har yesmin ta jiyo tace"Adda baki bacci ba kema"
Tama manta da yesmin wlh "aa nafarka ne keme ya hanaki bacci"
Kamar zatai kuka tace"Wlh Adda xuciyata wani iri take mun nakasa baccin tunani ya isan ni bansaba haka ba abun sai yake mun wahala"
Tausayi tabata don tabbas fadawa kogin kauna wadda ba,asan kanayi ba wahalane da ita,ba kowane zai iya jurewa ba sai mai tsananin hakuri da kauda kai,abune da kecin xuciya da ruhi abune dake taba dukkanin lafiyar jiki data kwalwa da xuciya ajiyar xuciya tayi tace mata"kije kiyi alwallah kizo ko raka,a biyu kiyi kidan karanta qur,ani ko sura biyuce zaki samu bacci mai dadi"
Babu musu tatashi ta shige toilet din,dafe goshi tai tana adduar Allah yasa kar so ya wahalar da yar qanwarta.
Komawa tai ta kwanta tana dasa tunanin nata,tabbas ayadda abdoul yafusata bata jin zaisake dawowa haka zalika zai nemeta,kuma zuciyarta tana raya mata abunda bata son,wani zafi taji ga kirjinta ahankali ta furta "bazan iya sharing dinka da kowa ba Yaya *NASSER* duk yadda xuciya ta kwallafa rai dakai dole xata barka,kishinka araina mai girmane bazai barni nazauna lafiya ba"
Saitaji kwallarta tana silalowa saitaji tana sakawa ranta hakuri dashi tun yanxu,tabbas tanajin ajikinta Abdoul zai dauki maganarta zaije ya daidaita da zakiyya,zai aikata abunda ta fada ba shakka hakan zata iya faruwa.......danasani ya shigeta yafi sau dubu na fadar abunda ta fada karshe dai wannan daren ya dade bai karema ta ba tana gani yesmin tayi baccinta hankali kwance itako saidai juyi,asubar fari baccin ya sureta tare da mafarkin *(ABIN CIKIN RUHINATA)*


motar Abdoul na fita ta su dady ta shigo cikin unguwar bin sa da kallo Abbi yayi yana cewa"Abdullahi motar Alfah ce naga tafita wlh shine Allah yasa gida yaxo Allah na rokeka Allah yasa hakane"
Murmushi dady yayi yace"Adduarka ba haka take ba,zance yaje. ga dukkan alamu kuma anbata ransa"
Hankalin Abbi atashe kamar zai kuka.
"Wlh tsakanina da mariya Allah ya isa Allah kadaukar mun mataki akan matarnan,ta cutar dani tana kan cutar da rayuwata data iyalina,mekake tunanin yafaru dashi Abdullahi"

"Kodai baisamu abunda yaje nema ba,kokuma mahaifinta ya ganshi ya dakatar dashi cikin daya biyu kokima duka"
Abbi muryarsa tana rawa yake cewa"duk duniya bayan iyayena damuka rasa banda abunso sama da Abdoulnasser,kuma saboda farin cikinsa babu abunda baxan iya ba,har kwamciya ina iyayi kasa malam kabir yabi ta kaina inhar zaibashi farin cikin dayake nema,inhar zai mallaka mashi yarinyar nanan,don naga kamar son ta yake kamar rayuwarsa"
Dady yace"rayuwar tasama bai adauketa da muhimmanci ba kamar safiyyah,shi kanshi baisan soyayyarta taimashi mugun kamu ba sai nan gaba tukun."

Har cikin compound din gidan yakai Abbi sojojin dake tsaron gidan wani yazo ya bude mashi kofa yana sara mashi,bama tashi yake ba.
Koke koke keta fitowa daga bangaren umma,cikin kuluwa yake tambayar sojan dasuke kula da bamgaren magana.
"Ubamme yafaru acan wajen suke wa mutane ihu"
Cikeda mamaki sojan daya kame don yasan baida magana mai dadi saita su umma,kullum daya zo zaice suna lafiya babu wani abu dai ko,amman yau sai yaji sabanin hakan.
Cikeda bala,i Abbi yace"dakai nake shege ka tsaya kana kallona"
Jikinsa yana bari yace"yallabai madam ce........itace......daman......dama......"dakai nake kana mun ina ina zan ci ubanka wallahi"
abbi ya daka mai uwar tsawa saida ya daskare,yana nuna part din yana cewa"itace ta......ta hauk.....ace......ta yayyaga kayanta tana iface iface,tayiwa haulat dukan tsiya har cikinta yaxube,yanzu haka zuwairat na wajenta ca asibitin,ta jiwa khadija rauni ga kai saida aka daureta aka rufeta adaki sannan,amman taki shiru itace keta wancen ihun,ankiraka yafi sau ba iyaka yallabai naka dauki waya ba kagafarcemu"
Murmushi yaga Abbi yanayi cikeda jin dadi yace"daddaden labari kana da kyauta ta dubu dari,ka tuna man da safe ban kuma ce uban kowa yashiga ba kunajina ya fada yana nuna sauran security din dake wajen.
Dady yace"karkayi haka yaya..........Abdoullahi idan baka son raina yabaci kaimun shiru kama hanya kuma ka nufi gidanka iyalin ka najiranka"
Ya wuce part din su Mami yanajin wata matsananciyar kewarsu ita da ni,ima.har tun tube yakw ya shiga jikinsa har wata tsuma yake,falon shiru sai karar Ac kallon falon yayi furniture's duk sun lalace,gabaki daya ma part din ya Lalace babu kulawa bawai rashin tsafta ba,aa komi ya lalace yana bukatar canji,wasu kwalla suka xubo mashi.
Sako da lungu na part din yake dubawa yana hawaye.
Motsi yaji kitchen ya leka mami ce keta kokarin sarrafa yar cus cus din data rage masu rabin leda tayi ma dady waya basuda abinci yace sai xuwa gobe.
Julluf tayi ta juye ga plet zata bar kitchen din don ni,ima ce keta amai bata lafiya dataci abu saita amayar dashi,mafarin ta yimata ita.
Juyowar da zatai taganshi tsaye bayanta yana goge kwallarsa,saboda tsorata sakin plet din tai kasa tana ja baya,don bazata iya tuna rabon data ganshi ba.......tsora ya kamata tuni hawaye sun wanke idon ta.


*_ABDOUL-NASSER_*

Ya na isa gida dakin zakiyya yayiwa tsinke................


*naga adduoin ku ina godiya sosai Sannan ina rokon Alfamar ku cigaba da man uxiri saboda yanayin jikina,ngd da nuna kauna*
[9/30, 3:43 PM] Mom Muhseen: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

πŸ…ΏοΈ..........53

Saida yashiga falon yaga baidace yashigo mata acikin yanayin dayake ciki ba,frig dinta ya bude ya dauko ruwa har zaikai bakinsa yatuna da dokarsa,saurin dakatawa maimakon yasha saiya fito waje da robar ya tuttulewa kanshi ruwan har xuwa ga fuskarsa,yana sauke ajiyar xuciya sanyin yana ratsa xuciyarsa yana sauke mashi duk wani zafi daya debo.
Jingina bayansa yayi da bango yana yin relax,saida ya kwashe minty biyar ahaka sannan ya samu sauki ya najin duk wasu makamai dake cunkushe cikin ransa suna sauka,duk da ba duka ba.
Har yanxu kunnensa yana sake jiyo mashi munanan kalamanta,wannan ya nuna cewar hasashensa akanta duk gaibune,yana tunanin yadda yakejin masifar kaunarta cikin ransa yazaji itama haka,koma fiye dahaka ashe haukan banza yake.yana bukatarta cikin rayuwarsa da zai dora agaba idan Allah yabashi iko,yana ma yaransa tanajin uwa da tagari da zata dorasi bisa daidai.yana mafarkin zamun hasken acikin rayuwarsa agaba,amman duk wani burinsa da fatansa ta rusa mashi su.
Saiwani nanata mashi maganar auren zakiyya take,ina ruwanta da aurenta da rashin auren ta dazai,amman yanaga wannan ce kurin damar shi.yadda ta nuna bata yi dashi duk maitarshi shima ya kamata yadaga mata kafa hakanan,karon farko yaji xuciyarsa ta raya mashi daidaitonshi da xakiyya,har xuwa sanda zai yanke shawarar data dace dashi.
Bedroom dinsa ya nufa kurin ya fada toilet ya saki ruwa ya jima yana sauka jikinsa yafito da Alwallah yayi sallar isha,i sannan ya canza kaya yaje ya hado tea marar zafi sosai,yana sha ya gama ya duba system dinsa sakonnin costomers masu son ganawa dashi,yayi accepting wasu wasu kuma yayi reject.
Haka yayita aikin da zai dauke mashi hankali daga tunaninta da bacin ranta,har dare ya tsala ya ajiye ta kwanta daker da sidin goshi baccin yayi nasarar daukarshi.

Muryarta cikin kuka kukanda duk wanda yaji saiyaji kamar ya tayata,tundaga kasan xuciyarta kukan yake tahowa,numfashinta har sama da kasa yake maganar ma bata fita sosai,don muryar ta dishe saboda kuka.
Yana rungume da ita cikin kirjinsa yana tayata kwallar shima,don shima kukan kurin zaiyi yaji ya samu saukin xucoyarsa.
"Na gode ma Allah da wannan jarabtar domin na yi imani dashi,hakan yana cikin kaddarar rayuwarmu nida yarana,kuma bazan butulce mashi ba zan gode mashi da har ya waiwayo maka da hankalinka akanmu.hakika wannan hukuncin sa ne ba na kowa ba.sai kuma sila da dalili,banda kamar wannan yarinya aduniyata hakika Allah zai mata kyakkyawan sakamako aduniya da kuma lahira,malam kabir daka tsana arayuwarka shine dalilin dayasa kake raye ahalin yanxu,haka diyarsa safiyya itace dalilin dayasa muka tsinci kanmu cikin wannan halin na farin cikin daidaituwar komi,idan baka nemi yafiyarsa ba Allah saiya tambayeka matayinsa na makocinka mai hakki akanka,amman kasa kowa ya tsanesa bada wata hujja ba Abbin ni,ima kadawo cikin hayyacinka idan baka gina lahirarka ayanxu ba yashe zaka ginata,kana da tabbacin kana da kwana ki dayawa arayuwarka..........rufe mata baki yayi yana kwalla harda shashsheka yace"insha Allah nai alkawarin gyara kura kuraina mamin ni,ima nai alkawarin dawowa mutumen da al,umma zasuyi alfahari dani kuma zan dage da neman tsari daga shaidan da makarrabansa,domin hada rashin kiyaye azkar yasa koma me mariya tayi mun ya sameni.amman na dauki hakan matsayin darasi da kuma hanyar gyarace Allah ya nuna man,hakika zan gyara alakata da malam kabir inhar yaban dama xuria zan hada dashi."
Jawota yayi suka zauna kan kujera yana rike da hannunta,yasoma bata labarin duk abunda ya sani ayau dinnan,kuka ta kamayi tana fadawa jikinsa yana sake godema Allah daya kawo silar fitarsu cikin wannan kangin.
Wannan dare haka Abbi ya rungume mami da ni ima ajikinsa har garin Allah ya waye.

*********

Yau da shirin koma wa wajen aikinsa ya tashi,tun wajen bakwai ya gam shiryawa yafito bai saka ran samun abun kari ba,don yasan irin wannan lokacin daga ita har malik basu isa tashi ba.
Amman sai yajiyo wani kamshi wanda ya ankarar dashi cewar tatashi,dandanan yaji yunwarsa ta ake yunkurowa.
Agogonsa ya kalla yaga ya kusan makara kuma yanzu haka mutanen da ya ansa zama dasu suna can har sun iso tun da asuba jirginsu ya sauka.
Hanyar kitchen din ya nufa yana dan daidaita fuskarsa.
Ta juya baya tana soya kwai ga dankali nan ta kwashe cikin gwagwa,saman gas din kuma farfesun yan cikine take idasa dafawa.ga placx nan komenene ta hada ciki kilan tea ne,inji xuciyarsa,
Rungume hannu yayi ga kirjinsa yana kallon bayanta,doguwar rigace ta bacci iyakar guiwarta amman mai kauri baka ganin jikinta,gyaran murya yayi wanda ya sata tsorata har tana yadda ludayin datake juya kwan dake cikin kasko.lumshe ido tayi tana ajiyar xuciya ta duka ta dauki spoon dinta tana juya tace"ina kwana"
Murmushi yayi ya ida sa shigowa sosai yana cewa"uhmmm wannan kamshi dakika bude gidan dashi haka,mekike aikata mana ne"
Banza tayi dashi amman kasan ranta murna ce fal kamar me.
"Don Allah ataimaka mun ahada mun cikin basket sauri nake kuma bazan iya jira naci ba,Allah yasa andafa dani"
Nanma taimashi banza ta gama soya kwan ta dauko kwandon da yaje xuwa office dashi da containers din da take xuba mashi,ta fara xubawa ko inda yake bata kalla ba.
Jinjina shariyar da take dashi yayi amman sai yaji hakan kuma ya burgeshi,hakika ballagazar mace marar aji batai ba ace kina mace Mai daraja kina watsar da ajinki da kimarki.
(Yan mata take not akula da kima da martaba,suna da matukar muhimmanci ga rayuwarki ko kau ga mijinki ne balle saurayi)
"Wai har yanzun fushin ake dani zakiyya"
Wani kallo ta jefa mashi ta dauke kai ta cigaba da aikinta kurin.
Dariya ya danyi kadan harta kalleshi don shidin bai cika fiddo dariya ba sai ta kama,gira daya ya daga mata ta dalla mashi harara.
Ta gama xubawar ta ajiye mashi gefensa tana tattara wanke wanken wanda zatayi yanzu.
Matsowa yayi kusa da ita kamar zai rungumeta muryarsa kasa kasa yace"I'm very sorry kiyya,nasan laifina yasa har yau kike fushi ko?"daskarewa tai awajen don gabaki daya jikinta ya dau wani sanyi,don abun yazo mata abazata.
"Idan nadawo zamuyi magana oky"
Daga kai kurin tayi yadauko abincin yafice sai lokacin ta sauke wani gauron numfashi.

************

Bayan fiyah ta dawo daga jarabawa yau wajen karfe shidda harda wani abu ma,tana shigowa gida akafara kiran sallar magruba.
Baba bai dawo ba saida aka gama sallar yesmin na kitchen yau ita ke shirya abincin dare,tuwon shinkafane miyar agushi baba ya siyo naman rago an xuba aciki (harnaji miyauna ya tsinke🀭)
Tunda fiyah ta dawo tana daki bata jin dadi ko kadan,don har wata masassara takeji.tana cikin tsananin kewarsa tana kan nadamar abunda yafaru,jitake inama ta fada mashi cewar soyayyarsa itace weakness dinta,itace farin cikinta da bakin cikinta.rashinsa gareta wani babban bigirene da bazata iya misalta shi da komi ba.
Mamace ta shigo dakin don yesmin tace mata tana daki kwance.
"Safiyyah lafiya kike kuwa"
"Bandai jin dadi ne mama kamar xanyi xaxxabi"
"Subhanallahi,ainace ku daura net kun kiya badole sauro ya cije kuba,bari dalha taxo saiya siyo maki ACT,kifito kici abinci harda yunwa ma kilan"
Babane yashigo yasa mama ta fita tana ansa sallamarsa.
Take gaya mashi abunda ke damun safiyyar,yaje shima ya dubata yace ta fito yasa mata tabarma tasha iska,saitaci abincin tasha magani.
Gaba daya suke cin abincin a tire guda,sun hirar su gwanin ba sha,awa,kallon safiyya baban yayi yace"bayan masassara akwai abunda yake damun ki uwata ko?"
Yake tayi tace"aa baba babu komi bayan ita,hada gajiya kullum ina kan hanya babu hutu shiyasa ma kila ta saukomun"
"Allah ya baki lafiya,muhseen ya kiraki kuwa"
Kanta yana kasa tace"eh ya kirani ina cikin jarabawa saida nafito na yasake kiraa"
Jinjina kai baban yayi yace"idan ya sake kira ka safe,kice ina son ganinsa idan ya samu lokaci"
Da to kurin ta bishi,tana jin dadin abunda zaifarun don tasan maganar yesmin zai mashi.
Dalha ya shigo da maganin nasha yafita,bai jimaba ya dawo yace ana sallama dani.
"Waye"
Inji baban.
"Kanen uncle yahya ne yazo"
"Kace ya shigo batajin dadi bazata iya fitowa ba"
Dadi ya kamani don kona fitar bansan me xance mashi ba.
Yesmin naga ta shige daki tana jin ance haka,murmushi nai nace araina makira tasan ta samu abunda takeso.
Sallama yayi mama ta ansa mashi baba na nuna mashi tabarmar dayakai.
"Bisnillah anan dana zauna"
Ya na murmushinsa na gado ya zauna yana gaidasu cikin girmamawa,hakika muhseen mijin aurene kawai dai ni banda ra,ayinsa ne shie kawai.
"Yaya muhseen ina wuni"
"Lafiya lau safiyya ashe bakiji dadi ba sannu Allah ya sawake"
Tace"ameen nagode"
Baba ya kalleta yace jeki ciki zamuyi magana dashi,kekuma mamansu xubo mashi tuwo karkace ka koshi zan dauka baka daukemu iyayeba"
"Zanci baba kayi hkr"
Mama tatashi taje ta xubo mashi ta kawo ta ajiye tana samun waje daga gefe itama ta zauna,yana ci baban yana janshi da hira kadan kadan har yaci dayawa yana ajiye spoon din.
"Na koshi mama ya isan haka nagode sosai kuma tuwo yayi dadi ba kamar tuwon jawaheer ba"
(kanwarsu dake bi mashi agida)
Dariya mama tai baban yana tayata tace"kadai raina nata ne amman ba dadine babu ba"
"Wlh mama karma ki hada da wanan nakin,don ita tuwonta kamar talge haka yake,kanaci zai ka nemesa karasa"
Dariya suke ita baba ta GB wuce ta kai kwanonin kitchen baban yace"wannan din kuma da kake yabawa qanwarka yesmin tayi ai"
Zaro ido yayi"dagaske,gaskiya ta yi kokari sosai zan turo jawaheer ta ringa koya wajenta.
Gyaran murya baba yayi yace "muhseen"
Jin yadda baban ya kirashi yasan maganace mai matukar muhimmanci,yadago yace"na,am baba"
"Magana zamuyi dakai mai muhimmanci,ina fatan zaka fahimce mu kuma xaka dauki abunda muke nufi da kai"
Jinjinakai yayi yace"insha Allah baba xanyi duk yadda kace"
Gyara zama baban yayi yace"ammm muhseen alokacin dana ansa maka kan maganar uwata ashe munyi kuskure kadan,wanda har hakan yake son kawo damuwa.
Inason nabaka hkr abisa abunda xance maka,don Allah ka hkr da safiyya ka nemi qanwarta yesmin.wasu dalilai suka nace haka saboda ganin cewar uwata batayi na,am da maganar ka ba kuma bata fadi cewar bata so ba,sainaga wannan zai iya kawo cikas ga zaman takewar ku maimakon kuji dadin zama da juna ana iya zamun akasin haka,saboda kaunar danake maka yasa naga bazan iya kyaleka ban maka tayin auren yesmin ba,ko ita za a mu dace amman idan kanaso bazan ta kuraka ba don bazan so wani ya cutu ba ya kagani,inbaka lokaci kaje kayi shawara agida kokuwa."
Ajiyar xuciya yasauke yana jin wani dan ciwo kasan ransa,hakika babu abunda yakai kaso akika amman kuma hakan yafiye mashi sauki daya aureta bata sonsa,bazaiji dadin zama da ita ba koda kau ta danne ta nuna bakomi,amma ita ai abun zai cutar da ita,sannan itama yesmin din baida tabbacin zata soshi balle har yayi saurin na am da maganar baban,hakika yana son safiyya so marar iyaka,amman hakan bazai sakashi yaso kanshi ba don haka ya hkr da ita maganar yesmin kuma itama dole yasan idan ita tanuna tana ra,ayinsa shikuma zayyi alkawarin kulawa da ita fiye da tunani kuma zai yi iyakar bakin kokarinsa wajen sakata cikin xuciyarsa,har Allah yasa mashi sonta.

"Kayi shiru muhseen,idan kaga akwai takura wlh babu tilasci kafafi ra,ayinka naji"

Ya sake sadda kanshi yace"baba hakika na fahimce ka kuma abunda ka fada gaskiyane,ban boye maka ba tun wancen lokacin inason safiyya,amman sonta bazai saka na cutar da ita ba,don haka na hakura da ita Allah ya bata wanda takeso nagari wanda yafini,sannan maganar yesmin.
Baba karku tilasta mata bazamu san meke ranta ba,kar axo ayi abunda zai kawo damuwa inhat yesmin bata da ra,ayina baba don Allah ayi hkr da maganar nan Allah xai bani wata makamanciyar safiyya"
Tausayinsa ya kama baba da mama,baban baiso fallasa yarsa ba baiso sanar dashi son da take mai ba,amman ya xama dole kodan ya samu kwarin guiwa,don harga Allag yana son yaron yanason sake hafa xuria da ahalinsu.suna da kirki da daddatako.
"Muhseen karka damu inhar akan haka ne,yesmin ta nuna mana kai takeso mafarin kenan uwata tazowa mamansu da maganar daba don haka ba,har ayi bikinku bazamu san bata sonka ba,kuma kaima nai imanin baxata nuna maka ba.amman saboda ta gano yar uwarta tana cikin wani hali akanka yasa ta yanke shawarar sanar damu,kaji dalilin zamanmu dakai.don haka kaje kayi shawara da mamanka ko dan uwanka,duk abunda sukace saikayi aiki dashi."

Murmushi muhseen yayi yana tuna wasu abubuwa dasuka faru ranar dayaje gano baba asibiti,da lokacin daya daukosu daga asibitin,sai randa ta biyosa ya kawo mama gida sanda fiyah bata lafiya,hakika tana da hankali da wayau tana sonsa bata bashi wata dama dazai gane ba,saidai zata ringa janshi da labari na ban sha,awa da dariya.bazaka taba ganewa ba,tabbas da matan wannan zamanin ne damarta tafarko data samu sanda ya daukota bayan sun ajiye mama alokacin zata barje kolinta ta gaya mashi,amman tana da kunya da kawaici ta danne saidai aka gane amman badai ita ta furta ba.
Murmushin yakeyi yanajin kaso sittin na amuncewa da ita yana saukar mashi,cikin sanyin murya yace"baba na amunce nima ina sonta,duk da haka zan sanar da su halin da ake ciki nasan bazasu ce aa ba,suma ai suna sonada daya daga cikinsu,Allah yasa hakan shiyafi alkairi"
Dandanan fuskar baba ta washe hakika yaron yana da hankali Albarka yayi ta samai shida mama,da zaitai ya ajiye masu dubu goma yafice,baba nacewa ya barshi amman bai dawo ba.

Fiyah na jinsu duk abunda ya wakana saitaji yabata tausayi,kuma ya burgeta hakika tana taya yar uwarta murnan zamun namiji irin muhseen,Allah ya samashi soyayyarta fiye da wadda yesmin take mashi.
Kallonta tai ta dunkule waje guda tana raba ido,dariya ta kwashe da ita tace"to mrs love tashi ankashe maki boss din saiki bani ladata"
Boye fuskarta tai tana dariya tace"nidai Adda kibari don Allah bana so"
Cikin tsokana tace"ehyy bakiso meye bakiso muhseen din kuma yanzu shine bakiso,innalillahi bari inje insanar da baba to ashe hasashena karyane........Wlh Adda ba haka nake nufi ba kiyi hkr"
Rike bakitai tana dariya tana kallonta,saida fada kuma kunya ta kamata ta soke kai tana dariya
"Adda don Allah kibari kunya kike bani"
"To nabari yar qanwata Allah ya tabbatar da alkairi yakuma kara kauna"
Kin ansawa tai da amin din.

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Umma dai direct gidan mahaukata aka kaita,saboda hauka take tuburan idan kasake kaje inda take saidai akwasheka ayi asibiti dakai,yaranta banda kuka babu abunda sukeyi Abbi kuma ya sakasu daki ya kulle yasa wani soja yayi masu dukan tsiya,har saida xuwairat da haulat suka suma.Amina ce

Please Login or Register in order to submit comment