Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gobe Abdoul zai dawo Anty jamila ta haihu ansamu baby girl.
Fiyah ta shirya kayanta itace yar zaman bakwai,har rigima sukai da yesmin akan ita zata fiyah tace"keda kin cika lalacin tsiya me zaki tsinana mata dallah matsa mun."
Mama tace"Ato nidai ai bazan tura ku kudu ka ba kamar wata wadda bata da hankali,kume ke safiyyah ai ga makaranta da hkr kikai tunda ita ta gama zaman banza take."
Silalewa kasa tayi tana dirje dirjen kafafu don yau rigimar takeji bilhaki da gaskiya "wallahi mama dama nasan saikin kware mun baya,kullin saikin nuna ni baki goyon bayana tsakani da Allah nida nake babba ai ni zakice intai."
Yesmin tace"kiyi hkr Adda wlh ni daman janki nake don inji me zakice."
Ta fada tana dariya mama na taya ta kallonsu take tama kasa cewa komi mama tace"kinji kunya wlh safiyyah kullum ke bakida wani girma saina jiki."
Ranar da daddare bayan sallar magruba ta shirya kayanta zata wuce,baba yace yaya jalal ya raka ta ta samu abun hawa."don kin matsa uwata ai da bari akai saida safe,wlh ni bana son fitar dare."
Yaya jalal din yace "yo baba sai abuna take so don gidansu,ke maza maida wannan akwatin saida safe zakitai,don ubanki kamar wacce ake cizo cikin gidan ko ker mar ubanme take."
B'are baki zatai ta wage da kuka yafaske bakin "kisake inji sautin numfashinki sa niyyar kuka kigani."
Daki na koma nayi kuka na bakuma komi yasa nakeson fitar ba munyi sa malik zaiso bakin titi ya wuce dani baban najiyosa yana cewa"kayi hkr Abdoul jalal barta tai kila itama jamilar tana can jiranta take."
Kwala man kira nai nafito hararata yayi yace"kina iya wucewa muje ai,fitinanar wofi ke ko kunya baki kiji ga yar kanwar ki nan bata addabi kowa ba saike katuwar wofi."
Haka ya tusani har bakin titi sai sababi yake shida Anty jamila insuka fara fada kamar bazasu barka ba,koda ya tari taxi din cewa yake"wlh kika bari naji labarin kin kai saurayi gidan nan zaki gaya masu."
Yabiya mai taxi din mukatai.
Wayata keta haske alamun kira na Ake don silent take kar akirani gabansa inshiga uku.
"Yaya malik yayane ta tarar mun taxi kaganni nan ma mun tafi kabarshi mun hadu gobe ai inada lectures."
"Aa yar qanwata gani nan bayanku fa"
Zaro ido tayi tana lekawa aikuwa shine saurin tsayar da mai taxi din tayi tace"daka ta malam saukeni anan yi tafiyarka."
"Amman hajiya kinajin kashedin yayanki."
Cikin masifa tace"dallah can niba kudin zan ansa ba mak'olo kuma ina ruwanka da shiga sabgar da babu kai."
Hkr yabata sauka tai ta shige motar dariya yake mata yace"haka kike masifa qanwata."
Murmushi tayi tana cewa"yaya malik naga zai kawo mun raini."
"Toya kike kinsan kuwa nayi kewarki."
Jin kalamar nayi kewarkin tayi bala,in sata shock har ta kasa kallonsa kauda kai tayi gefe,yana lura da ita yasake cewa.
"Na saba kullum ina ganinki kwana hudun nan jinsu nake kamar na shekara,koke bakijin yadda nakeji."
Shirun ta sake yi masa dariya yayi kasa kasa yace"tunda baki magana gaya man sunan unguwar."
Daker ta lalubo abun fad'a tace"gwarunfa"
Hira yake mata amman ta kasa cewa komi don yau da wani salo yaxo dashi wanda ya sata shiga shakku.........sakin maganar yayi ya kama wata "kinsan kuwa zakiya aure zatai in the next 4 weeks"
Sai lokacin ta bashi duk kanin hankalinta tace"dagaske!kashhh banji dadi ba amman ya zamuyi yanzu."
Karka ta wa yayi yasa hannu ga Aljihun wandonsa na baya,ya zaro wata pos mai shegen kyau ya mik'o mata.
Ansa tayi tana binsa da kallon karin bayani.
Hankalinsa na kan tuk'i yace"ta yarda ita ne bakin bank,ina gefen hanya nazo shigar da kudi,Allah yasa ni kadai na gani nai saurin dauketa,duba ciki kiga akwai information din duk da mukeso jikin wami card nan,phone number,address da sai sairansu to duk ciki dai ba kamar phone no din itace abu mai muhimmanci,gashinan na bar maki sauran aikin."
Alamar jinjina tayi mashi tama smile dinta mai kyau da gigita wanda ake mawa.
Ajiyar xuciya ya sauke yace"gobe 12:00 na rana zai sauka zakimun rakiya."
Tana rik'e da card din data fiddo tana kallo tace masa"ni kau mezan yo."
Murmushi yayi yace"kece da abunyi kau,zaki je tarbarsa ne harma da guzirin flower."
Dariya tayi tana girgiza kai tace"kaima yaya malik da neman magana kake to miye na wani zuwa da wata flower saika ce wasu lovers."
Rage gudun yayi yana kallonta asace wanda hankalinta yana kan card din dake hannunta,kauda kai yayi ya cigana da tukinsa.
"Ba dole sai masoya ke haka ba,kawai zakiyi masa ne don muga action din dazai bada."
Rausayar dakai tayi tana kallonsa kadan kafin ta kauda kai tace"oky let me see"
Sun iso unguwar lafiya yayi parking bakin get din ya ja kofa taki budewa,juyowa tai ta zuba shi ido kamar yadda ya zuba mata nashi masha Allah..........kasa jura tayi ta janye idonta ta rasa wadannan sale salin da malik yake mata ko namiye......."kin ga"
Daker ta oya sake juyowa don wlh yadda bai tunani bata son hada ido dashi,tana jin kunyar kallon da yake maka mata.
Lumshe ido yayi ya jawo wani d'an gift daga bayan motar an nadesa da irin ledar nan da ake nade gift da ita.
Kasa ansa tayi tana kallonsa tace"na miye yaya malik?"
Ajiyar xuciya yaja yace"just for u,na gani ne yayi mun kyau nace zaifi dacewa da hannunki."
Tunda suka fara muamala yaune ya taba bata abu,don haka bata jin zata bashi kunya cikin sanyi ta mik'a hannu ta ansa.
"Thank u so much yaya malik."
Hannunsa yasa gefen kansa yayi mata salute alamar sara wa.
Murmushi tayi tana masa saida safe.
"Karki manta fa zanzo nan natai dake kizama cikin shiri."
Daga masa kai tayi tana shigewa cikin gidan.
Dora kansa yayi saman sikiyarin motar yana magana can kasa,bazan iya juyo meyake fada ba,yajima wajen sannan yaja motar yabar unguwar.

Da saukin mutane gidan don makociyarta ce kadai sai wasu mutun biyu dangin uncle yahya,ta gaidasu tana isa ga jaririyar ta dauketa cike da jin sonta.
"Welcome to d world my princess Allah yayi maki albarka ya raya ki bisa sunna,amman don Allah karkiyo fadan Anty wlh bata wa zamuyi."
Dariya duk suka saka masu itama fiyar tana dariyar,tace"Allah kuwa dagaske nake,dama dama ma inkika biyoni da naji dadi."
Nan ma dariyar sukai Antyn dake shigowa dakin tace"kice dana shiga ukuna wlh,aiban mance masifar da kika gana ma mama ba,sannan kice ta biyoki aa ban lamunta ba."
Hira suka ringa sha yaka junan su da kuma mutanen cikin dakin,saida dare yakara sannan duk sukatai,nan suka bude sabuwar hira saida uncle din ya dawo sannan tayi masu saida safe ta wuce dakin da zata sauka,komi akwai bata bukatar komai shirin bacci take tayo wanka hade da alwalla tayi ksha,i da shafa,i da wutri sannan ta saka kayan baccinta ta haye gado wannan gift din ta dauko tana warwarwa,wani box ne ya hadu sai daukar ido yake ya budesa ............wow wow masha Allah kawai take furtawa zobene yasha kyau,dan karami kuma sannan yazauna daidai kan yatsarta ta kusada ta tsakiya,dan danan ya haske mata hannun damabgata da dogayen yatsu da doguwar akaifa......bata fita cikin shaukin zoben ba kiransa ya shigo.
"Fatan kin kwanta."
Cikin annashuwa tace"ina zan iya bacci yaya malik."
Cikin rashin gane kan maganarta yace"ban gane ba."
Ajiyar xuciya ta sauke tace"shaukin zoben nan ya kawar da baccin,wlh yayi kyau sosai baka ga yadda yayi kyau ga hannuna na ba,kuma daman ni mutunce mai son ring."
Wani dadi yaji jin abunda take cewa,murmushi mai sauti yayi yace"daman ina ganin sa nace bai dace da hannun kowa ba sai yatsar qanwata safiyyah."
Kwanciya tayi tana kallon hannun bace komi ba,wannan damar ya samu ya sanyaya muryarsa yace"ya kikeji."
Murmushi kan fuskarta tace"i'm feeling happy yaya malik har na mance rabona da zobe."
"Karki damu indan wanan,fatan zaki kasance cikin farinciki har waye war gari,zanso inga yadda fuskarki take Annashuwa,kinsan duk sanda kike cikin farinc ciki duk kan wani kyau daAllah yayi maki safiyyah yana fitowa,kamar misali kinga inkikai dariya wushoryarki tana bayyana,yayinda take kara fiddo annurin face naki,and than kywawan hakoranki wadanda ake kira da hakoran kyau suna fitowa su haskeke fuskarki,bayan wannan ma kina da abu mafi soyuwa dayake kara mun ganin kyanko shine dumful dinki left and right,ta ko ina Allah ya baki ki gode masa."
Tunda yafara magana tayi lub cikin bargo,idonta arufe yake ruf,kunnenta ne kawai yake sauraren kalaman malik,da take jinsu amar acikin bacci shin idan ta dorasu bisa ma,aunin tunninta anya atayi gaskiyaa abun da take zargi,meyasa haka to ko dai shi haka yake salonsa saika ce wamda yake cikin soyayya........wata zuciyar tace aa ba haka bane malik bazai soyayya dani ba,aini bana soyayya yanzu ban ma iyaba wata kuma tace mata"bakison sa kenan,meyarasa duk abunda kake bukata ga namiji ya mallaka.....runtse idonta tayi tana ciro wayar taga kodai shirmene na tunani ban gaskiya ba,amman still yana online.
Muryarta kamar wacce aka shake tace"zan kwanta saida safe."
Ta kashe wayar ba wai don wulakanci ba aa bata san dai abunda za tace masa ba,daker tayi addua ta kwanta amman baccin ya jima bai zo ba.

Mrs bb ce
Mom muhseen.
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........22

Tunda tayi asuba bata koma ba ta fito ta kama gyaran gidan,don tana da lectures around 8:00 yau suke covering lectures din don week mai zuwa exams ne zasu fara biyowa baya,dolene ta bama kanta hutu kodan exams din nata.kafin mai aikin tazo fiyah ta gama shara da goge goge duk wani lungu da sak'o ta share ta gyara,sannan ta gogeshi tas kamar kasunkiya ka lasa don tsananin yadda ta goge tayils din,dama gashi fari sai ya sake haskawa.
Ta bud'e ko ina da turarukan wuta dakin Antyn ne kurin bata gyara ba.
Saifa bangaren uncle yahya shikuma sai ya tashi kilama saita dawo ta gyara,duk da tasan Anty da kokarin tsafta take ba ma lallai yayi wata daud'aba.
Falukan biyu da extra rooms din ta gama dasu da daining room.
Kitchen ta wuce ta duba abun da suke dashi tahau hada kalaci,tana yi tana ankare da time.
Kunun alkama tayi mai hade da markad'ad'dar gyada yasha madara sai daukar ido yake.sai ta dumama wani ferfesu data gani cikin frig,sannan ta fere doya ta tadafa ta sannan ta daketa tayi sakwara daman akwai kayan miya tayi greeting dinsu ta yi yar sos mai hade da kwai da vegetables........dan danan k'amshi ya karad'e gidan.
Wainar fulawa ta hau soyawa bayan tasaka mata albasa mai lawashi da cabbage,sai kwai data xuba aciki da magi.......kafin takwas da rabi harta gama da wanna fannin ta wuce tashiga wanka.
Duk abunda takeyi kalaman malik na jiya suna mata yawo cikin kai,ta rasa wani waje zata ajiyesu duk inda ta duba taga basu da waje amman kasancewar malik mutunne mai mutunci da dadin zama,saitaji bai dace da wofintar waba koba komi sun saba kuma aduk hasashen irinsa take yiwa kanta fata.
Wanda ba dan kowa ba bai kuma da jijidakai irin na masu shi,wanda yasan girma da mutuncin iyaye wanda zai girmama mata nata,wanda bai dauki duniya da abunda ke cikin ta ba.wayayye mai fara,a da boye bacin ransa akowane hali.
A iyakar zaman su ta karance shi duk haka yake,malik yana da kudi don kuwa zaman sa da Alfah ya samu kudi da shi kansa baisan yawan su ba,amman bai dauki kansa bakin komi ba bai kuma kalli kudin matsayin masu darajar da zai iya yin komi dasu ba.
Yana yin komi yadda ya dace da ace wani ne yadda yake kokarin ganin ya faranta mata,to zaiyyi anfani da dukiyarsa don yana ganin ai kodan ita zata saka yasamu duk abunda yakeso.
Sai akai sa,a shima malik din ya ganeta yaga kudi da wasu kyalekyale na duniya basu gabanta,iyayenta sunyi kokarin gina mata tarbiyya da duk wanda yazauna da ita ko ta zauna dashi zayyi sha,awart.
Fitowa tayi tana tsane jikinta bakin gado taji budewar kofar juyawa tai taga Anty ce.
Murmushi tayi tace"Anty maijego barka da tashi ga ruwa can baya an kwashe maki karya huce,ya kwanan princess."
Cikin jin dadin kulawar yar uwar tata ta idasa shigowa tace"princess dinki bata da kirki jiya bata barni nayi bacci ba wlh sai biyu da rabi,nikau in tace ke zata biyo wlh na bani uku na safiyyah."
Me fiya zatai ba dariya ba tana lakuto mai tana bin jikinta dashi tace"Allah yayi wa princess albarka ai kema mama tace kin mata kuka har taji da ana bayarwa data samu maiso ta bada saboda kukan ki."
Murmushi tayi tace "aigashinan kau ana rama mata,ke wai kinji yadda take kuka saboda wulakanci wai kar a kashe wuta kuma karna zauna kiji min yarinya ita nan har tasan wani zama da wani haske ita da tazo shekaranjiya."
Fiyah shafarta take tana dariya tace"Ato sai kushirya don aradu akwai aiki."
"Uhm Bari kawai,fiyah duk ke kai ayyukan gidan nan,gaskiya kin kyauta Allah yabiya ki yabar ki da muhseen."
Dam taji kirjinta yace ita wlh ta ma manta da babin wannan gayen,tunda ta anshi wayarsa bata taba yunkurin kiran sa ba.
Tabdijam ashe anty nanan kan bakanta nashigesu yazan yi,don wlh ni ban ra,ayinsa ya cika yanga wlh.
Yak'e take tace"uhm Anty kenan."
"Kamar ya anty kenan badai baku waya ba,mekike nufi fiyah?"
Bata bari sun hada ido ba tace"kai anty shidin ya ce maki bamu waya?"
"Ban sani ba"
Dariya take ciki ciki tace"sorry kwantar da hankalin ki muna waya amman ba kullin ba gaskiya."
Sai lokacin ta washe baki "koke fa yar qanwata,wlh ina maki sha,awar muhseen yaron kirki ne baida wata matsala."
Uhm kawai fiyah tace ta shiga saka kayanta juyo mata bata tayi "mak'ala mun Anty."
Cikin haushi tace"tirr da ke shekara ashirin da biyu baki iya saka bra ba,ba doke yesmin take maki dariya ba."
Ya mutsa fuska tayi "Anty hannuna ne fah bai kaiwa,nidai ki makalan mun sauri nake in da class."
Makala matan tayi tana nufar kofar fita"ga kudinki can bisa frig kitchen,nasan sadda zaki fito ina wanka ga kaya can da za asaka mata idan za,ai mata wanka."
To tace mata sanan ta fice ita kuma ta idasa saka kayan ta murza farar powder da libstick bata sa kwalli ba fiyah irin mutanan nan ne da zaka ga koba su saka kwalli ba sai kaga kamar sunsa,haka idonsu yake daga Allah ne.
Hijab har kasa ta zuba bayan riga da siket din data saka don inhar ta sasu tofa bata saka karamar hijab,saboda duk shap dinta bayyana yake tubarkallah.

Saida ta tabbatar ta yi abunda Anty tace sanna tayi break sama-sama ta dauki kudin har 1k ta jinjina kokari irin na uncle yahya. tasan shine zai dauki nauyin zuwa makarantar ta har ayi suna.
Karo sukai da feea zata shiga itama shan mur fiyah tayi tana wuceta feea na gama parking har sauri take ta iske fiyah karta shige aji........"fiyah,fiyah magana nake fa don Allah kitsaya."
Juyowa tayi tana kallonta "lafiya wannan kira haka kamar makauniya."
Numfashi ta saue tace"hkr nake ta son inbaki akan abunda yafaru rannan,kar kiga laifi na wlh iya gaskiyata na fada maki akan Abdoul,amman tunda naji bayanin ki na dauki hkr na sama raina,damuwata guda zakiya da Abba zai aura wlh kau don Allah kiyi hkr mushirya bana jin dadin shariyar da kikemun."
Tunda ta anbaci zakiya wani irin dum taji tana sake ware duk idonta akan feea kafin taja hannunta tace"feea kin tabbata ita zai aura."
Jinjina kai tayi "wlh kau fiyah kinga ma invitetion nan."
Ta zaro ta nuna mata gashinan zakoya muazzam and Alh jamilu badaru (kwangila)
Cikin tsananin mamaki ta kalli feean tace"insha Allah baza ai auren nan ba,karki damu zan taimakeki ki kwantar da hankalinki"
Zakiyya!zakiyya!!
Abunda take nana tawa kenan tana da tarin tambayoyi sosai amman zakiyar kawai ce zata ansa mata su,kallon ajinsu tayi babu malami ta kalli feea sannan tace"kije class ga shi can inajin ma last test zakuyi,zamuyi magana kicire komi aranki."
Haka suka rabu fiyah ta shiga class dinsu ta samu waje ta zauna tunani ta shiga yi.
"Zakiyya na son auren ko aa,in har bata so wane dalili ne yasa zata aureshi wanda ya haifeta sau uku ko hudu.kai bama yarda zai zakiyya ta so auren sa,lokaci guda bai isa ta manta da nasser ba har tayi wani auren..........haka akai wannan lecture daker taba da constretion dinta ga abunda ake masu tana yi tana jotting,ganin abunuwan suna da amfani sosai kuma tasan shi tsaf zai iya makosu cikin questions din exams.
Tayi mashi tambayoyi sosai tana yi tana rubuta duk abunda yake sake mata bayani.......sai sha daya suka fito waje ta samu ta zauna koda taga sakon malik share wa tayi.don ba shine gabanta ba bata ma duba shi ba,
No din zakiyya da tayi save tun jiya ta shiga lalubowa ta kasa kunne taji kozata shiga,cikin sa,a ta shiga tana ta ringing saida ta kusan katsewa sannan ta dauka .
"Hello,wake magana"
Ajiyar xuciya ta sauke tace"Sunana safiyyah,don Allah ina magana ne da zakiyya muazzam."
Cikin tabbatar wa tace"yes I'm zakiyya,who is safiyya mekikeso."
Fiyah tace"no tukunna dai yanzu dai magana nake son nayi dake amman ba awaya ba,ki saman time sai nazo na kiyi mana wajen da xamu hadu,maganar is very important awajen ki.bayan haka pos dinki da kika yar a bakin bank tana wajena."
Cikin dokantuwa tace"plss ina Central park kizo mu hadu yanzu don Allah saboda banda isasshen time ina hidimar bikine."
Fiyah tace"no yanzu ina makaranta kuma kona tashi banda time akwai ayyuka da zanje nayi kisamu lokaci kedai,inkin yanke time kikirani sai anjima."
Ta yanke wayar tana jin insha Allah komi zaizo da sauki,don naga alamar bata da zafin kai irin na yaran masu kudi.
Sakon malik ta shiga dubawa tana jin kirjinta yana bugawa,bata son ganin kalaman nan nashi wlh tada mata hankali suke.
Ilai kuwa sune _Kyakkyawa acikin kyakkyawai fatan kin tashi lfy,jiya kin gudu kin barni da jimami Allah yasa dai kalaman malik basu hanaki bacci ba_
Runtse ido tayi tana fita daga cikin text app din.
Tana tsogumin wannan sabon salon na shi,wata qawarta ta iso tana cewa
"Fiyah ana nemanki wani guy ne gashi can bakin department."
Zaro ido tayi tana binta abaya aikuwa malik ne hararar sa tayi shikuma yana mata dariya,
"Amman meyasa bak kirani ba zaka zo har nan baka san yanzu mutun ake kiwo ba ba dabba ba.idan wani yaje ya kai labari ga baba ko yaya jalal fah."
Kama kunnesa yayi duka biyun zai durk'usa tai maza tatare shi har suna karo danjuna.
"Meye haka yaya malik,don Allah ka daina muje idan magana ka keso dani amman ba nan cikin mutane ba wani dan sa idon yana can yana gulmata fiyah tsaye da namiji."
Dariya yake yana shigewa gaba tana bin bayansa wai gowa yayi yace "wai tsoron aganmu tare kike?"
Bata kalleshi ba tace "yaya malik kenan don baka san yan sa ido ba,to yanzu wani nacan yana cewa ashe dai safiyya el-ladan ashe daman musulmar karya ce kuganta can tare da saurayi bayan bata tsaya wa da kowa duk makarantar nan."
Me malik zai banda dariya kallonta kurin yake yace"Ashe dai qanwata ba wasa har tsoron tun kararki ma ake,to miye idan anganni dake ba sai kice yayanki bane."
Jinjina kai tayi tana rik'e haba tace"uhm yaya malik kenan wlh wata ko wani nacan suna mana kallon masoya raba kanka da mutane."
Daidai isowarsu bakin motarsa ya juyo yana rungume da hannun sa ga kirji ya zuba mata mayatattun idanun sa.
Shiru tayi tana neman hanyar buya daga idonsa dake mata wannan kallon da bata so,yasha gabanta yana murmushi mai sauti leko fuskar yayi yana son su hada ido dariya yayi ganin ta runtse idonta.
Motar ya bude mata yana cewa"bismillah gimbiya safiyyah."
Wannan suna ya shigeta har saida ta kallai cike da mamaki,shi kuma ya kanne mata ido guda tai saurin shigewa motar tana jan numfashi.
Dariya yayi yazaga yashiga suka bar makarantar.
Don ma kar yayi anfani da yin shirun ya sake yi mata abunda bata so yasa tace.
"To da bangama lectures ba fa"
Hankalin sa naga tukin uace"ai dayake ma nayi sa,ar kun gama."
Rausayar dakai tayi tace"ina zamu yanzu to."
Kwana yayi yana cewa"siyen flower,wace kala ce tafi yi maki kyau cikin flower."
"Yanzu wannan flower da tsiya sai ansiyeta, don Allah nidai kabarta kasan halinsa yanzu haka muna isa karshe kila ma dani da ita zaiyi watsin ala tsine damu cikin mutame."
Dariya yayi yace "karki damu Allah bazai maki ba."
"Hum to idan yayi manin fah"
"Saki rama kaina"
Dariya tayi "da haka kace sai kiyi hkr,inbanda abunka ina ni ina iya bugunka ai saidai kabarni da ciwon hanu."
Hirar su suke har suka isa wani waje da flowers din kawai ake siyarwa zalla,gasunan gwanin sha,awa sai wadda ka keso........tunda suka tsaya ta hango wata pitch color and dark pink color,dance danan taji ta burgeta inda take kalla yabi da ido yayi murmushi yafita yabarta.
Inama ace mutumen kirkine zata ba kuma in ta bashi ya ansa cikin jin dadi da annashuwa,wanda tasan har abadan bazai yada ba saidai idan yabarta inda zata bushe,da tace ya dauko wadda ta gani don tayi bala,in burgeta Amman bazata so taba wanda baisan mutuncin mutame ba,banda yunkurin kisa bai iya komai ba saifa zafin ran banza.
(Nikau nace uhmmm gaba dai gaba dai ansafiyyan malik😊)
Dawowa yayi da ita rik'e ga hannu,an sakota cikin wata fation leda mai zanen flowers din.
Banda kamshi babu abunda take duk ta cika motar da kamshi,mamaki da al,ajabi ya rufeta ganin wadda dai taketa santi itace ta siyo baki bude take kallonta
Kasa cewa komi tayi murmushi yayi yace "baki ce tayi kyauba."
Kauda kai tayi gefe"yaya malik ba kyau ake nema ba ai,fatan da ake abashi ya ansa cikin girmamawa shine kawai bawai kyau ba."
Kunshe dariyar sa yayi yaja suka bar wajen.
Tunda suka tunkari airport din kirjinta ke amsa wa,tunda take tunda tafara wannan aikin wahalar bata tabajin faduwar gaba irin ta yau ba,duk sai taji ta diririce tun ma kafin suyi ido hudu dashi...........kallon sa tayi cikin raurau da ido don har gobe bata mance wahalar da ya bata tace"yaya malik nidai bazan iya fita ba kaje kai dai wlh ni tsoro nake ji wlh."
Ajiyar xuciya yaja yace"relax safiyya,karki saka tsoro nace maki bazai maki komi ba ai yadauki fada na"
Ajiyar xuciya ta sauke tana sake jin gabanta yana faduwa.
Fitowa sukai daidai sana akafara sanarwar saukar jirhin.duk atsorace take kamar ace kes ta ruga da gudu.........ahankali mutanen suka fara saukowa duk wanda yaga nashi sai ya je ya tare sa,har zuwa sanda idonta yakai ga wani balarabe yana saukowa yasha suit dinsa bakake,amman ya cire ta saman yana rake da ita ga hannu,sai side bag dinsa idonsa da bakin glass bayansa wasu mutane guda biyune suna dauke da akwatinsa biyu.......saukowa yake cikin jarumta da natsuwa iya haduwa nasser ya hade tau,sai yasake yin fresh gashin fuskarsa sai daukar ido yake,haskensa ya karu tunda ya sauko idonsa ya kai ga su malik,iska ya shaka yafesar yana sake dire idonsa akanta.......ayadda yake kallonta yagano tsoro da shakku atare da ita,baisan ma wani killer smile ya kubce masa ba.......yana ayyana wa aransa cewa"yarinya zaki gaya masu."


Mrs bb ce
Mom muhseen.
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........23

"Masha Allah laquwata illa billah,gaskiya Abdoul ya karo kyau zuwan sa Australia,baki gani ba fiyah?"
Malik ya Sanar da ita yayinda ta tabbatar wannan balaraben da take ta faman yaba wa cikin ranta she Abdoul dinne,babu hassada kam yakaro kyau da haske wannan idan ya shiga cikin larabawan ma bazaka tantance sa ba idan ba hausa akaji daga bakin sa ba.
Amman da yake bata haushin sa da tsanarsa yasa taja tsaki tace"idonka dai bai gani daidai ba yaya malik,ina abun yake wai maye yaci jariri."
Dariya yayi yana mik'o mata flower yace"banda dai jealous ansafiyya kifadi gaskiyar abunda yake ranki."
Gabanta ya fadi karfa ya gane ta yaba kyansa,sake shan mur tayi tace"mts Allah na tuba koni dai nafisa kyau."
Ganin yana tunkaro su yasa baice mata komi ba,nan fa gabanta yaci gaba da lugude,ta rasa da fuskar da zata anshe sa.
Rungume juna sukai shida malik,yayinda fuskarsa ta sake ba kamar yadda tayi zato ba,hannunta banda rawa babu abunda yake kallon flower take tana jin bakin cikin mik'a masa ya yi watsi da ita,runtse ido tayi tana karanta duk adduar data zo bakinta sannan ta bude,tana saka dauriya aranta ta fara takawa zuwa garesa,tayi jarumtar saka kyakkyawan smile mai kyau a fuskarta........jerowa sukai shida malik yana rike da side bag dinsa daya ansa,duk idonsu akanta yake amman haka ta maze tana sake sakin murmushi,hakoranta suna bayyana kallonsa ta soma yi aslowly tun daga kasa zuwa sama,tana yi tana juya idonta ta sigar kallon banza,sanna cikin siririyar muryarta data

Please Login or Register in order to submit comment