Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motsawa yayi saidai Abbin da kanshi yazo ya rungumeshi yana kukan shima,wata irin kewar juna ce da tsananin kaunar juna ta kamasu.........bayan tsawon shekaru sai yau Allah yayi zasu sake ganawa,sai yau Allah ya bayyana sirrin daya boye sunsha kuka sosai suna rungume dajuna ni,ima da mami ma hawayen suke.
Daddy da umma salamatu banda hkr da nasiha babu abunda suke masu,hakika idan kagansu saika tausaya masu don kowa yayi kewar dan uwansa Abbi jiyake kamar ya bude kirjinsa ya saka Abdoul dinsa aciki.
Kira yake"kayafe mun yarona yafemun kaddararmuce tazo ahaka,babu wani tsumi ko dubara dole hakan zata faru,nayi kewarka har bansan adadi ba,nayi kukan rashinka har idona ya kafe da hawaye.............idan kanajin kalaman Abbi kai kanka saika zubar da kwallah,Abdoul yana shashshekar kuka yace"Abbi nima ka yafemun,xuciyata awancen lokacin ta gaza yardarmun cewar kana kaunata,xuciyata ta gayaman dama neman hanyar rabuwa dani kake,tunda har alakafa mun mummunan sharri irin wannan ka yarda tabbas kadaina sona,na yi iya yadda zanyi na koyama kaina tsanarka don ko sunanka bana son malik ya anbata mun,nayi rayuwa irinta dabbobi nayi abubuwa da basu dace dani ba,naso mutuwa lokuta dadama.nida kaina nake neman ta ninake kai kaina inda za,a bankeni.idan nai makaina rauni bana yarda naje asibiti don su dubani,malik yasha wuyata nayi masa abunda idan da wani dan uwana ne bazai iya zaman da malik yayi dani ba,Abbi nayi rayuwa cike da wahala kullum cikin kunci da bakar xuciya nake.xuwan safiyya rayuwata shine ya fara canzani,tasha wuyata ba yar karama ba idan na kamata kamar kato haka zan daketa,bana jin ko digon tausayinta.saboda lokacin babu wadda na tsana alokacin irin mace,bana kaunar ganinta idan har ta kusanto inda nake jinake tsaf zan kasheta..........nasha giya har babu adadi,kayan maye babu kalar wadanda ban sha ba,kafin malik da safiyya suyi nasara akaina.Abbi yanzu haka ina da illar da giya taimun,tayimun illar da bana tunanin zan warke,tamun tabo acikina wanda bazan iya shan ruwan zafi ba,haka bazan iya shan na sanyi ba.inko har nasha to gani can raina ahannun Allah.........rufe mashi baki Abbi yayi yana kwalla
"Ya isa haka ya isa Abdoul hakika na zama uba marar anfani,amman kayi hkr ba laifina bane mariya ta cuceni Allah ya isa tsakanina da ita ..........ka gaya mun duk abunda kake Abdoul komiye zan yimaka shi inhar bai take sharia ba,zan dawo maka uba fiye da wancen lokacin"
Ajiyar xuciya Abdoul yake yana kallon mahaifin nashi yace"Abbi safiyya nakeso,inason kaida dady kuje ga babansu kurukarmun shi ya bani aurenta,inasonta inajinta kamar raina idan ban sameta ni kaina bansan halin da zan shiga ba."
"Inhar don wannan ne insha Allah nida dadyn ka zamuyi iyakar kokarinmu muga mun samomaka ita,nima zanyi alfahari da ita matsayin sirikata.zan iya yinkomi don farin cikinka wanda bai take sharia ba,don haka Malam kabir ko cewa yayi na kwanta ya takani zanyi,don kuwa nasan nayi mashi abunda zai bukaci hakan"
Daddy ne yace"bama zai ce ba saidai wani abun na daban,to ita zakiyya fa Abdoul,kasan da cewar har gobe kai take so"
Sadda kai yayi yace"dady na sani amman tayi hkr bazan iya zabarta akan safiyya ba,zanmata addua Allah yabata wanda yafini".............ko bai bata wanda ya fika ba zaibata wani wanda xai jibanci lamurranta,wanda zai share mata kukanta wanda zai taushi xuciyarta akan rashinka datai,ni zan aureta inhar taba dama "
Daga bayansu sukaji wannan maganar,baki dayan su suka juya suna bin kofar shigowa da kallo,malik ne tsaye da zakiyya wadda idonta tuni ya gama lalacewa da kuka,da alamu taji abunda Abdoul ya fada.
Daddy ne yace"malik dagaske kake"
Riko hannun zakiyya yayi yajawora har cikin falon ya zaunar da ita gaban mami yace"dagaske nake Dady domin zakiyya mutuniyar kirkice,kuma inhar na sameta nasan nayi mata,saidai idan itace tace batayi dani"
Zakiyya jikin mami ta fada tana idasa kukanta Abbi yace"malik Allah yayi maka Albarka Allah yabaka abunda kake nema duniya da lahira,hakika kayi mana komi ka zama fitila agaremu Allah ya saka maka da mafifcin Alkairinsa."
Yana murmushi yace "Ameen Abbi nagode,maganar zakiyya fa anbani?"
Yafada yana sosa kai yana kallonta tana kuka jikin mami,
Duk saida suka mashi dariya Abdoul dai mamakin malik din yake,daman yana sonta kokuwa yanzu dayaji cewar ya fasa zaimaye gurbinsa aranta.
Mami tace"kubar mun diyata ta huce tukun,kubamu lokaci zakuji daga garemu kuma kai ta nuna Abdoul saika bayarda toshiyar baki,tunda kakimu don gidanki"
Sadda kai yayi yana murmushi,kunyar zakiyyar ma yakeji sosai amman ya ya iya da azalzalar da soyayyar fiyah kemashi.zai samu time ya lallasheta yasan zata huce.
Abbi ya shafa kanshi yace"yanzu ina zaka son"
Cikin wata irin kauna Abbin ya fadi shima ya shagwabe yana kwantawa jikin Abbin yace"office zanje in idaza ayyuka"
"Okay yaushe zaka dawo gida to"
Kalon malik yayi yana mashi alamar tambaya yaushe zai dawo.
Dari ya umma salamatu da dady sukai mashi shima malik din yana tayasu yace"ka tmbayeni yallabai"
"Shikenan xuwa dare daka tashi nan nakeson na ganka gida kajiko,kafinma ka dawo ankwaso maku kayanku tass za,a ajiye maku ana.amman abubuwan anfani kurim za,a dauko.kayan cikin gidan da gidan kanshi zanyi kyauta dashi.oky"
Jinjina kai Abdoul yayi yace"duk yadda kayi Abbi daidai ne,"
"Allah yayi maku albarka,kaje karka bata lokaci idan kadawo zamu sake tattaunawa."
Kowa kallonsu yake cikin jin dadi don ba tun yanzu wannan kaunar take ba,Allah ne dai ya kaddara sai haka tafaru.
Rungume Abbin yayi yana mashi kiss ga kunci yaje ya rungumi dady yana murmushi"nagode dady,thank you very much kayi kokari"
Wajen mami yaje itama ya rungumesu tare da ni,ima yana jin kewarsu sosai kallon zakiyya yayi wadda ta kauda kai bata son ganinsa.
Itama kissing goshinta yayi yace"thank you for everything kiyi hkr zamuyi magaa daga baya"
Tunkudeshi tai malik yana cewa"malam ya haka zaka wani shigema matata agabana,dalla wuce"
Tashi yayi guiwarsa tai sanyi yana masu saiya dawo.

***********

Yesmin ce keta kokarin hada sanwar dare sun hira da mama tana aikinta.
Shinkafa da miya zatai mamar ke yanka mata salad ita kuma tana soya miya don har ta kwashe shinkafar,dalhane yayi sallama.
"Aaha dalha ka dawo kenan"
Cewar mama "eh na dawi ko shagon ma ban budeba saiga muhsen yatsaya,yace in turo mashi yesmin."
Rudewar datai jin ance muhseen yana kiranta yasa ta yadda ludayin juya miyar tana zare ido,nashiga ukuna dawane idon zan kallai.daman kullum xullumin haduwarsu take.

"Yesmin miye haka?"
Muryarta tana rawa tace"ba komi mama faduwa yayi"
Murmushi dalha yayi yace"ya za,ace mashi mama"
Itama murmushin tai tace"kace tana xuwa yanxu"
Ya fita don sanar dashi
Mamar tashiga kitchen din ta ganta durkushe ta buga tagumi.
"Tashi like ki gyara jikinki ki fita yana jiranki"
Idonta yayi kwal kwal zatai kuka.
"Mama nidai don Allah"
"Banson shirme cinyeki zai ne kokuwa bakonki ne yau kuma,tashi karki bata mun rai."
Haka ta fito ta wuce daki kaya ta canza duk da basu jima jikinta ba,amma akwai kaurin girki.
Hijab tasaka kalar kayan data saka,ta fesa turare ta kalli kanta ga mirrow murmushi tai tana jin kunyar haduwar su,bata san dawane idon zata kallai ba.
Muryar mama tajiyo tana cewa"halan sai yayi tsiru a kofar gidan sannan zaki fita."
Dariya tai jin abunda mamar tace saida ta ga komi lafiya lau sannan ta fita.
Mama na mata dariya kunya kamar ta nitsar da yesmin.
Yana cikin motar amman kofar gefensa abude take yasha gayunsa don daman muhseen badai iya gayu ba.
Hangota yayi yadda take ta sunkuyar da kai,murmushi yayi lallai yana da aiki waccen kunyar kwarar sa zatai,yana son ta saki jiki yadda zasu saba shima har yafara jin kaunar tata.
Bude kofar wajen mai zaman banza yayi yana cewa"bismillah princess"
Kasa ansawa tai yabar kofar bude tadan zauna adosane.
Cikin natsuwa tace"yaya muhseen ina wuni"
Kallonta yake sai kauda kai take.
"Bazan ansa ba gaskiya tunda ma ko kallona baza xa ai ba yafada cikin muryar shagwaba kamar yaro.
Kasa kasa tai dariya kafin tace"kayi hkr yaya muhseen kunya nakeji"
"Yau kuma akejin kunyar tawa,to menayi har akejin kunyata"
Kasa ansawa tai tana wasa da yatsunta.
"Shikenan tunda bazaki fada ba,ya kike to yasu mama da baba"
Ahankali cikin natsuwa take anashi,har lokacin ta kasa kallonsa.

"Yesmin"
Yakirata cikin lumana don yana son ta bashi hankalinta.
"Na,am"
"Kallona nakeson kiyi"
Ahankali ta kalleshi ta sunkuyar dakai murmushi yayi yace"nasan kinsan komi daya faruko?"
Daga kai tayi"ba daga kai ba kimun magana nafison inajin muryarki"
Ahankali tace"eh yaya muhseen nasani"
"Yawwa fatan zaki ansheni hannu biyu kuma zaki bani dama na baje kolin tawa baiwar ta soyayya,bazan so kin dari dari dani ba, ban kuma ce kibar jin kunya ta ba aa kunya abune mai kyau ga diya mace,amman ki daukar kamar yaya jalal ki saki jiki kina mun fira kamar sanda muke abaya,zanso ace munyi rayuwa mai kyau da fahimtar juna.har mukai ga inda muke fata oky"
"Insha Allah Zan kokarta"
"Yawwa kokefa princess yau ranar gabatar da kai ce ba dogon surutu don haka anshi wannan"
Ya miko mata wata keda fashion harda dai kwalin waya aciki.
"Banson jin aa anshi kurin tunda dai na kusan zama miji ko ba haka ba"
Murmushi tai ta ansa cikin ladabi.
"Nagode yaya muhseen Allah ya kara budi"
Yaji dadin adduarta yace"thank you so much princess,kije gida magaruba ta gabato kisata caji anjima zamufara zance"
Dariya tai tana fitowa tace"ka gaida hajiya da jawaheer"
"Aikuwa kamar kinfada akunen su"
Sallama sukai ta shiga gida tana sauke ajiyar xuciya.

***********

Fiya basu fito exam ba sai karfe hudu da rabi agajiye suke feea daman ga rashin dadynta daka ganta kasan tana cikin damuwa matsananciya.duk ta rame ta zama so silent.
Fiyah ta lura da canjin yanayin kawar tata bayan sun fito suna zaune bakin block dinsu tace mata.
"Nikau feea mekedamun ki kinga wai yadda kika rame kamar wada ake dibar naman jikinta ana miya"
Yake tai idonta yana taruwa da kwalla tace"fiyah duk abun nan bakisan me yafaru damu ba"
Kallon mamaki take mata "ban gane ba,har wani abune yafaru daku wanda ban sani ba"
Kwallarta ta silalo tana gogewa tace"yau kwanan dady biyar kenan yana prison,fiyah dady baimana adalci ba dady ya cutar damu.ban tabaji tsanar ubana ba fiyah irin cikin yan kwanakin nan"
Tausayinta ya kama fiyah cike da damuwa ta rungumota cikin lallashi tace"innalilahi wa inna ilaihir raju,un.feea banji maku dadi ba dole zaki rame dole xaki shiga cikin halin damuwa,amman kidaina tsanarsa koma me dady yayi dai har gobe yana matsayin mahaifinki,don haka addua ce zaku ringa binsa da ita,kuna mashi fatan alkairi.hakika abun bai dadi ba amman ance hannunka baya rubewa ka yanke kayar,don haka kidanne xuciyarki harma kiringa tausar momi kuna binsa da addua har Allah ya kawo maku mafita."
Kuka take ajikin fiyah tace"fiyah hajiya mariya matar Alh muazzam fa...........karki fada kibar shi matsayin sirrinku feea,kuyi mashi addua kuma ku saka hkr da juriya Allah zai dafa maku."
Lallashinta fiyah tatayi tana sake kwantar mata da hankali har tasamu ta natsu,drivern ta yazo tace"bazaki bini mutai gida ba"
"Aa kije ina jiran wanine"
Haka tatai xuciyarta babu dadi.

Wayarta ta kalla taga tana haske dayake silent ta sata no dinsa ce,don ta riga tayi mata hadar da ko cikin bacci aka tambayeta zata karanto tsaf.
Tambayarta inda department din nasu yake yayi ta gaya mai ta sauke wayar tana bin cikin makarantar da kallo,duk yawanci antafi sai wadanda ke hostel ne keta shige da ficensu.
Mota ta hango wadda bata tabagani sa da ita ba,land rover ce fara fat,duk wadanda ke wajen tsura mata ido sukai,suna jiran wanda zai fito.kamar yasan haka yaki fitowa ya kirata.
"Inafa kallonki hajiya kitaso"
Hararar motar tai "kafi karfin kai kabiyoni ko,to bazan taso ba inbazaka fito ba wlh tafiyata zan"
"Basai kin gama rantsewa ba aike gimbiyace duk abunda kikace yi ake"
Yafada yana murmushi mai tsananin kyau.
Budo motar yayi yafito...........huking fiyah tai daga inda take zaune wata dankareriyar shaddace jikinsa tana maiko da walkiya black ce anyi masa dinkin harf jamfa hannun mai links akai mashi,hukarsa black haka takalman shi.kunsan farin mutun bakaken kaya suna masifar ansarshi,duk matan dake wajen tsayawa sukai suna kallonshi sake dabaki daga inda yake zuwa inda take da nisa amman ba sosai ba,tuni kamshinsa mayatacce ya gama karade hancinta.
Lumshe ido tai tana budewa wasu yan mata ne taga suna dosar inda yake.
Dan danan hankalinta yayi masifar tashi nadamar cewa yafito ta sameta,mema yasa tace yafito.
Hoto taga sunyi dashi sun wuce suna daga mashi hannu.........wani kududu yazo mata wuya kamar ta fasa ihu.
Tashi tai tun kafin ya karaso ta nufi hanyar barin wajen,ganin zata wuceshi din yaga fuskar murtik yayi saurin riko hijab dinta.
Yana murmushi"ya haka madam,nafito ban saba umurnin ki ba kuma zaki barni anan"
Kamar zata rushe da kuka tace"to yanzu kuma nace ka koma motar"
Kunshe dariyar sa kurin yake yace"angama gimbiya yar sarki"
Harara ta danna mai "ni ba yar sarki bace yar malam kabir ce"
Bude mata gaban yayi yace"yar sarkin kenan irinku ai sai mai sa,a" tashiga tana kubure kubure.
"Zamu iya tafiya rankishidade"
Tsaki taja tana jin bakin cikin hoton da suka dauka dashi wadannan yan matan.
Cike da masifa tace"idan bazaka tada motar ba wlh zan fita,saikake ka dauki wadamcen shashashun marasa aji dake daukar hoto dakai"
Baisan sadda dariyar tashi ta fito ba,babu shiri yayita kyalkyaka abunsa.sototo tai tana kallonsa bata taba ganinsa cikin irin wana farin cikin ba,duk dariyarsa iyakarta murmushi da sauti amman ba irin wannan ba mai kyalkyalawar haka.
Sai ta koma tana kallonsa yayi mata kyau sosai,har sada ya bar dariyar yana murmushi ya tada motar yajata ahankali.
"I'm sorry ina maki dariya,kedince kika tunxira dole nayi miye don sunyi hoto dani,kema inkinaso basai muyi ba"
Banza taimashi har suka fita daga makarantar.ahankali kamshin motar daya hade da turarensa ya saka mata wata irin natsuwa,taji duk haushin da takeji ya fice sanyin Ac yana shigarta wani yanayi yana bakuntarta,kallota yayi cikin canza murya kamar bashi ba yace"ina zamu"
Ta na jinsa ta rufe idonta ita batasan ma mezata ce ba.bata son wannan sabon yanayin ya gushe shiyasa ma batace komi ba.
Kida ne yajefita amotar batare da waka ba,sautin kidan mai ratsa uciya da ruhi,dan danan fiyah ta gigice da wata irin soyayya wacce bata san tanajinta ba sai yau.
Bai sake cemata komi ba yana kura da yanayinta wanda shima kanshi yana jin irin hakan,wani wajen shakawa ne ya kaisu wanda fiyah bata taba ganinsa ba,amman bata son fita amotar.
Shima kuma hakan yakeji shiyasa saiyayi parking kurin yana jingina bayansa da makarin kujerar yana sauke ajiyar xuciya ahankali.
Ba Wanda yace komi tsayin mintyna uku,har yagaji da shirun ya bude wata loka gabansa ya ciro wani hadedden xoben xinari,dan siririne mai design maikyau sai kyalli yake jirkitowa yayi yana fuskantar ta,ahankali ta bude idonta ta xuba cikin nashi wadanda suka canza kala suka dawo lovers color,kasa dauke idanunsu sukai su kansu basu san cewar suna ma junan su wani irin kallo ba,fiyah komawa tai kamar wata duluwa.ahankali ya jawo hannunta dake cikin hijab dinta yana kallonsa,kamar zai hadiyesa ya rike yatsarta guda ta wadda ake cema ring pinger na kusada na tsakiya,cikin salo da nuna kauna yake saka mata zobe cikin yatsarta,kallon yadda take saka xoben take tana bin yatsarta da kallo yadda tayi masifar yin kyau.
Yana gama sawa ya dago suka hada ido bata sanma ta lumshe su ba,ahankali ya kai hannun bakinsa cikin shauki yayi kissing hannun wanda yasa babu shiri ta bude ido tana kallonsa,girarsa ya daga mata fuskarshi na fidda wani annuri yace cikin wata swet voice di sa data sake rikita fiyah.

*"I LOVE U FIYHA,I REALLY LOVE U. I LOVE U FOR REVER AND EVER,PLSSS MY LOVE DID U MARRIED ME?"*

ahankali take anshe hanunta tana dunkukewa waje guda ibanda wasu abubuwa dake narke mata ga jiki babu abunda takeji,numfashinta yana sizen tunda take jin son Abdul da kaunarsa bata taba zaton sunkai haka ba,yau abun datakeji na dabanne shin mezata iyayi ita safiyya,zata ansa mashi bayan bata san ra,ayin mahaifanta ba kokiwa zatai rejecting har sai sadda baba ya amunce dashi.

*tau fiyah dai na neman shawara*

Don Allah kuyi hkr dani i sha Allah munkusan gamawa.ina alfahari daku.

Fatan na wanke xukantan ku yau ina jiran commentsπŸ˜‚πŸ˜‚
[10/10, 5:56 PM] Mom Muhseen: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

πŸ…ΏοΈ...........57

Jikinta gaba daya jitake kamar acikin frig aka fuddota,ta kasa kallon idonsa ta kasa motsawa daga cikin kujerar da take,hakika ta jima tana tsumayin kalaman nan tayi mafarkinsu har babu adadi,tabbas taji farin ciki taji dadi marar misaltuwa,amman ya zatai anya ansar soyayyarsa lokaci guda yadace da ita,anya bazatai kuskuren sadaukarwa da wuri ba?idan baba yazo yace bai yarda ba fa,bacin ta xurfafa kaunarta akansa hakan zaiyyi matukar tabata,zai girgiza xuciyarta don hakika Abdoul shine farincikin ta shine burin xuciya da ruhinta,tunda ta fara tunanin kasancewa matsayin mata awajen wani namiji dashi take hango rayuwarta,bazata iya daukar kalmar rabuwa daga bakin mahaifinta ba,babu tantama xuciyarta zata iya bugawa don ita kanta tana shakkar wannan ranar..............."safiyyah"
Taji muryarsa mai dauke da wasu alburusan shauki suna shigarta ta ko ina,daker ta iya dago kyawawan idanunta ta zubemasa su ga fuskarsa,lumshe mata ido yayi ya bude yana kallonta shima.cike da shauki da kauna daker ma kalaman suka fito.

"I need to say something plz"

Ajiye idonta tai tana sauke wata sassanyar ajiyar xuciya cikin muryarta silent ta fara magana wadda dan danan yaji ta hade mai tashoshi daker yake control din kansa yana saurarenta.

"Yaya Abdoul na gode da kaunarka gareni,domin banyi tsammanin zaka iya sona ba.duba da cewar nidin ba yar kowa bace face yar talaka bawan Allah mai neman rufin asirinsa akoda yaushe,sai kazo kaban mamaki tabbas nayi farin ciki dajin kalamanka wanda da zan iya fiddo xuciyata ka gani da kasha mamaki,Amman inason ka fahimceni yaya Abdoul inajin tsoro inajin tsananin tsoron abunda zai biyo baya,babana kaifi daya ne idan yace aa to mawuyacin abune yadawo yace eh,hakika kanada wani matsayi mafi girma acikin xuciyata,kayi nasarar cinye duk wani fili dake cikinta.kuma nima zan so ace na kasance...........shiru tai saboda kunyar furta kalmar dake bakinta.
Matsowa yayi sosai cike da kauna yana rage muryarsa kamar baison wani yaji yace"plzzzz ki fada inason naji,karki boye mun raina yabiya dasonjin me zaki fada plz love"
Kallon kasan ido take mashi kafin ya ganta ya daga mata girarsa guda,make kafadarta tayi cikin shagwaba tace"uhm uhm ba yanxu ba"
"Sai yaushe"
"Sai naje gida idan munyi waya"
"Shikenan nasan dai kinsan muhimmancin alkawari don haka basai na tuna maki ba,cigaba da maganarki ina saurarenki"
Numfashi taja tace"yaya Abdoul babana daban ne,inajin tsoron idan kaje mashi da maganata yace maka bai yarda ba kayi hkr,wannan kalaman sune suke tsorata ni"
Ta tsayar da idonta akanshi.
Shima kallon nata yake cikin low voice dinsa yace"meyasa kikekin tsoro"
Sadda kai tai cikin jin nauyin abunda zata fada.
*"Yaya Nasser banson in rasaka shiyasa"*
Cike da jin dadi yace"a u sure love?dagaske don Allah sake fada naji"
Dariya ta boye tanayi shima yana tayata kafin ya lauya murya kamar da yaro yace"bacin ma banji kince mun u love me ba"
Dariyar ta sake yi tace"ba yau ba sai naji daga bakin baba,kayi hkr ina hango mana abunda zai iya faruwa don haka idan kana iya wa kazo yau kawai kayi mashi maganar."
"Dagaske kike inje kuma ince kekika turoni"
Daga mashi kai tai cike da jin kunya murmushi yayi yace"yau din tazo mun cikin sa,a hakika ina fatan farincikin danake ciki ayau ya dawwama,ko kinsan bacin wannan dakika sani daman da kwarin guiwata nafito"
"Meyafaru to"
Ta tambayeshi lumshe ido yayi yana kanne mata ido guda yace"yau muka shirya da Abbina"
Xaro idanunta tayi masha Allah tana bube baki cike da mamaki da dariya tace"wow wow Alhamdulillahi dagaske kake amman naji dadi wlh,kamar ma nafika jin dadin meyasa tun daxun baka sanar dani ba"
Lakuce mata hanci yayi yace"haka kike kyau idan kina dariya,na gaza ganewa harara da kuka da dariya wanne yafi maki kyau duk wanda kikai sai naga yafimun kyau miye sirrin"
Hararar tashi tai tana dauke kai dariya yayi"wow I love it wlh plz karamun daya"
Dariya ta saka tana boyewa cikin hijab dinta,tana mamakin daman haka yake da barkwanci gaskiya ba karamin alhaki umma ta dauka ba.
"Nidai ka kaini gida kaga anfara kiran salla wani wajen"
"Idan da zamukai gobe anan love bazan gane ba don kuwa idan ina gabanki ba komine nake tunawa ba,kilaman idan kince mun whats ur name cewa zanyi safiyyah"
Wata dariyar ya sake bata haka suka cigaba da fira yana sata dariya har saida tadage yakaita gida sannan yaja motar,yana kallon kiran malik awaya yayi buris don karya bata mashi mode dinsa.

Motar muhseen na fita tasu tana shigowa,kallon motar tai tana murmushi da alama dai sun daidaita da yesmin.
Kofar gidan ya tsaya yana kallonta cikin kauna kamar xai cinyeta,
"Karkasa na kasa tafiya kallon yamun yawa fah"
"Don Allah ki gaya mun wani abu mai dadi karki tai kibarni"
Hararar so tayi mashi tace"take care of ur self"
Shagwabe fuska yayi "yamin kadan nidai"
Nidai budeni banson baba ya fito ya ganni cikin motar nan plzzz"
"Okay say something plz"
Kiss tayi ga hannunta ta hura mashi ta dauke kai tana kunshe dariyarta relax yayi cikin kujerar ya bude mata harta fita yakasa cewa komi,Allah kadai yasan yadda yakeji cikin jikinsa da xuciyarsa........saida tazo kofar shiga ta daga mai hannu by by.
Daker yaja motar ya isa bakin get din gidansu,yana tuno moments da dama dasuka wuce yana tuna ranar daya bar gidan,har ya isa yayi parking motarsa.

***********

"Safiyyah ya akai yau kikai dare"
Inji baba dake alwallar magriba zaije masalaci.
Sadda kai tayi don tana tunanin yaji saukar mota,amman bazata iya gane wa ba tace"baba jarabawar sai biyar muka fito sannan mundan tattauna da yan ajinmu kan exam din gobe,sannan na taho"
Jinjina kai yayi yace"yayi wuce kije kiyi salla"
Yafice masallacinsa.
Jiki sanyaye ta wuce daki tana rage kayan jikinta tana adduar Allah yasa baban baiji sadda aka ajeta ba.
"Adda sannu da dawowa"
Murmushi tayi tace"yawwa yesmin ya gidan"
"Gashinan ya exmas din,wai yaushe kuke gamawa"
"Wlh exams kam sai godiyar Allah i think sai jibi zamu karkare insha Allah,ina yaya muhseen dinki"
Murmushi tayi tana juya baya "daxun yazo bakinan har yaba waya da turaruka"
"Uhmmm soyayya dadi Allah yasa alkairi kingode,adai kula sosai yesmin kinsan yadda xamanin yake Allah yabar kauna"
Can kasa kasa taji tace"Amen Adda"
Dunguremata kai tayi"makira anaso anakaiwa kasuwa"
Shigewa toilet tai tabarta tana dariya.

Bayan sunci abuncin dare ne baba ya kalli safiyya yace"waye ya saukeki dazun awaje"
Kirjinta yabuga dan danan ta rude ta sadda kai tana murzar hannu Allah yasota ta cire xoben dazun.
"Dake nake kina jina"
Kwallata cika idonta tace"baba Abdoul ne"
Basai yatambayi wane abdoul ba don yau iyayensa sunje har wajen aiki sun samai.
"Bance maki karya sake xuwa nan ba,ina kuka hadu har daukoki kika biyosa"
Jikinta yana rawa tace "anyi wuyar abun hawa yau najima bakin titi saigashi yace inshigo ganin zanyi dare shiyasa nashiga kayi hkr"
Bata da zabin daya wuce haka tayi astagfirulla saboda tasan tayi karya kuma babu kyau.
"Inhar ba sokike musaka kafar wando daya dake ba karna sakeji karna sake gani,nace maki haka ne don ba sa,an aurenki bane wannan shine magana,don iyayensa sunje har wajen aikina yau sun mun magiya nace aa don haka idan kina son fushina kicigaba da tsayawa dashi."

Kwallarta ke xuba ga hannunta saukin ma babu nefa kuma babu haske sosai balle su gani,amman yesmin dake jikinta tana jin yadda jikinta yake rawa sai tausayin Addar tata ya kama ta har itama taji kwallartata tafito.
Ahankali tatashi ta shige dakinsu kan kujera ta zauna tana kuka kasa kasa,har kirjinta dagawa yake daman wannan abun takeji shi take tsoro tasan daman baba bazai huce daga abunda Alh muazzam yayi mashi ba,don inba haka ba inhar kan kudine da bazai bayar da anty jamila ga uncle yahya ba,tunda shima kudin garesu sosai.
Amman bazata iya ja da hukuncin mahaifinta ba,koda hakan na nufin dawwamar bakin cikinta.

Yesmin ce ta shigo ta zauna kusa da itana rungumota jikinta tace"plzzz Adda kibar kuka insha Allah baba zai fahimce abunda ke ranki insha Allah zai amunce dashi.tunda abunda ake zarginsa dashi karyane sharrine naji anafada rannan.kiyi hkr kiyita addua idan darabon ku kasance tare baba zai sauko zai hkr yabaki shi.zantaya ki addua kibar kukan Adda nima zaki sani"
Rungume juna sukai suna kukan tare,mama na tsaye bakin kofa tana jinsu,badai ta shigo ba tasan za,a rina tasan safiyyah tajima tana sin wani kuma tasan ba tun yanzu suka san juna ba.
Juyawa tai ta koma daki don bata ga fuskar yiwa baban su maganar komi yanzu ba.

***********

Mamaki yasha yadda aka canza komi na part din ya koma sabo,don yadda yaji bakin ni ima yau akai fenti aka saka sabbin komi na wajen rungumeta yayi yana jin dadin dawowa cikin family dinsa,gefe guda ga sahibarsa ta gama wanke duk wani datti dake xuciyarsa.
Shida malik gaba yau falon Abbi akai zaman fira ga mami ga Abbi ga

Please Login or Register in order to submit comment