Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din janbaki wanda ya sake fiddo ruwan kyanta kunsan fararen mata idan suka saka jan janbaki ko marrom sosai yake masu kyau.
Saida tasa taji kamar ta goge,amman ganin bata fuskarta zatai yasa tabarshi.gyalenta dan karami wanda iyakarshi rolling shita dauko ta nade kanta dashi bayan gashinta data gyara ta saki jelar baya,bata aka kallabin ba rolling din kurin tayi tana saka kwalli ta gyara girar idonta sannan ta saka turaruka dake jere akan mirrow dinta,kala waje biyar kowane da kalar kamshinsa.
Yar pos dinta milk da high hills dinta suma milk,ta saka masha Allah saita fito sak amaryarta tayi kyau sosai don fiyah bata taba kyau irin na yau ba,don ita kullum cikin hijab shiyasa baka gane dirin da Allah ya mata.
Ahankali take takawa tana barin dakin,ita kanta saitakejin ta wani iri jinta take kamar wata sabuwar halitta,tasha ganin mata abuja irin yadda tai wannan shigar,saitake ganin Allah ya sawake tayi wannan shigar tafita,saigashi yau tayi kuma tana ganin tayi kyau amman kunya takeji tafita haka kamar za,aita kallonta saboda bata sa abaya ba.
Falon ta koma tadora kafarta daya kan daya,tana kallon wayar da linder ta kawo mata.
Minty talatin yana cika aka danna dow bell cikin sassarfa wannan arniyar tazo ta bude tana risina wa.
Kalon kofar fiyah keyi tana kallon mutumen dake bakin kofar,bakinta taji yace"yaya mali"
Murmushi yayi mata yana sallamar linder dake sunkuye.
Hanya ya nuna mata da hannunsa yana dan rissinawa irin girmamawar nan,kamar sakara take binsa da kallo.ta kasa shigewa gaban kasa shanye mamakinta tayi karo na biyu tace"yaya malik kaine"
Murmushin yake yana shafa kanshi baice komi ba yace"plzzzz let's go"
Idonta yayi kwalkwal zatai kuka yagirgiza kai.
"Karki bata kwaliyarki mana muje"
"Bazanje KO ina ba saika yimun bayanin me ake boyewa man,ni nagaza gane wa"
"Sorry muje zaki fahimta yanzu lokaci yana kurewa"
Dole ta hkr ta shige gaba ya rufe kofar yana binta abaya har waje,wajen mota ya bude mata baya ta shiga ya shiga gaba shida driver suka dauki hanya.
Gaba daya tunaninta ya rabu kashi kashi,xuciyarta tayi rugurugu da tunani wai wata aura ne meyasa ma tun tuni bata damu da sanin waye ba,saiyanxu da take son sani ake ja mata rai.

Tafiya sukai wadda bata wuce minty goma sha biyar ba,suka iso wani plat din gida mai kyau shima tundaga kofar gidan zaka san an shirya wani gagarumin abu,docration ne akayi ta ko ina ga fitilu sun haske wajen saikace safiya ce,wani kafet ne aka malala tundaga bakin motar da zata fito har xuwa inda zata zauna acikin gidan,tsaye tai tana kallon malik shikuma yana mata murmushi mai kyau,kamar dazun yanzu ma risinawa yayi yana bata hanya jikinta yayi sanyi kalau ta kalli hanyar sannan ta fara kokarin binta ahankali kamar mai tausayin kasa kamar jira ake tafara tafiyar..........wasu flowers masu kyau kala daban daban suke sauka bisan kanta,tare da wasu kyalkyali masu daukar ido suna ta zubowa daga ko ina,kuma bata ga wanda yake xubo dasu ba.abun idan kagani saiyayi bala,in burgeka saiya baka sha,awa malik ke binta abaya har cikin babban tangamemen falon da shima ya gaji da haduwa,anyi mashi kwalliya fiye da ta wajen ga high tabke can anjera lemuka sunkai kala takwas,ga cups biyu da katon cake dogo mai hawa hawa,anmashi kwalliya kalar kayanta.
Wutar Wake ta dauke sai dumlight dake haskawa yana walwalin kaloli daban daban.
Tsaye tayi tana kallon malik high table din ya nuna mata yana ta murmushi mai kyau,jiki asalube ta hafa hawan steps din har ta karasa wajen kujerun ta zauna tana zama ta nemi malik ta rasa awajen,hankalinta tashe kirjinta bugawa yake sosai cikin second dabaikai biyuba tag walau haske ya bayyana ta ko ina wannan kyelkyelin yana tashi kamshi ta ko ina kida mai sanyi da sanyaya xuciya yana tashi awajen,kafin waka mai dadi tafara fitowa da turanci tana jin wata kalma cewa *HAPPY MARRIAGE LIFE FOR UR'S*
kafin taga mutane sunfara fitowa daga ko ina daga cikin wanna aba falo,suna bin wakar happy marriage life din dake tashi jitai anrufe idonta daga baya ta bi hannun tana tabawa bazata iya gane kowaye ba,amman kamar macece ahankali ake zare hannun tayi saurin jiyowa tana bin mai rufe mata idon ta kallo.
Zaro idonta tai bakinta yana furta.
*"ni,imah"*
Dariya take kyalkyalwa tana riko hannunta tana ta dariyar,bata gama shan mamakinba taji runguma daga bayanta cikin sauri ta dago tana sake dararo idanunta tubarkallah.
*"zakiyyah,mami"*
Dariyar suke mata suma dandanan tafara fara,a kwallah na fitowa daga idonta,zakiyya ta share mata tace "surprise again"
Cikin tsananin farin ciki tace"again zakiyya"
Daga mata kai tayi tace rufe idonki kadan to babu musu ta bude jitai ta saka hannunta cikin wani tattausan hannu mai kama da auduga,sannan tana jin wani sassanyan kamshi mai narkar da xuciya numfashi taja tana neman susucewa,ahankali zakiyya take zare hannunta daga idonta tana dariya tace "see ur husband"
Kamar mai ciwon wuya take jiyawa ahankali take kallon gefenta tanajin numfashinta yana neman guduwa saboda rikita.
Idonta ya nitsa cikin nashi wanda daga ita harshi saida numfashin kowa ya nemi guduwa.
Bakinta abude idonta da kwallar farinciki nunashi take, tana kallon su zakiyya daketa masu dariya ita dasu mami da ni,ima ga malik rike da hannun zakiyya suna ta sakin murmushi.
mutane kuma sunata kallonsu gwanin ban sha,awa.
Labbanta rawa suke suna kerma hakoranta suna bayyana tsantsar farincikinta tace.

*"yaya Abdoul kaine,dagaske kaine"*

Naga Adduoin ku ngd sosai insha Allah mun kusan kawo karshen wanan book kuyi man fatan kammalashi lafiya.
[10/17, 10:42 AM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️...........63


Baice komi ba illa kyawawan idanunsa dasuke ta kallonta kamar yauce rana tafarko daya fara ganinta.
Malik da zakiyya suka iso wajensu zakiyya tariko hannu fiyah shima malik ya riko na Abdoul suna kallon juna,photographer ya yi masu kyakkyawan hoto sannan kiyya ta jawo fiya malik ya jawo hannun Abdoul suka hade hannayensu waje guda,suduka bin hannuwan nasu sukai da kallo kafin su dago mai hoton ya daukesu,nan fa yacigaba da kashe masu kala,wani dayayi kyau sun kurawa juna ido su kansu basu san ma hakan tana faruwa ba,don baki daya abun yazo masu acikin bazata.
Kafin akaimasu baki daya na family,dady da Abbi ne kurin babu sai gobe zasu iso.
Kafin sujuya baki dayansu,wajen zamansu suka nufa suka zauna amman gabaki daya fiyah gani take kamar mafarki take,saita kallai ta sadda kai shima saiya kalleta ya dauke kai.fuskarsa bazaka ce yana murmushi ba haka bazakace yasha mur ba,kadaran kada han yake itace dai kallo daya zakai mata kasan cewa tana cikin farin ciki,kidan ya cigaba da tashi masu rawa nayi masu shan drinks nayi,fiyah kallon zakiyya take yadda duk inda malik yayi tana biye dashi,kuma hannunsu cikin najuna.kuma bata ga wani ya nuna hakan wani abu bane,mami ce ta iso wajenta ta dafa kanta.
"Diyata mekikeson ci"
Sadda kai tayi tana murmushi cike dajin kunya tace"aa mami ba yanzu ba"
Kallon Abdoul tayi tace"son kaifa"
Dage girarsa yayi yace"ba yanzu ba"
Murmushi mamin tai tana cewa oky ..........bayan wani lokaci kuma akazo za,a yanka cake wukar tana hanunta saiya dora nashi hannun bisan nata suna yankawa tare,mai hoto yanata daukarsu.
Cirowa tayi ta kai bakinsa ya tsura mata ido yanata kallonta,baidace komi ba yajima idonsa kamar zaifado saboda kallonta sannan ya bude bakin yagutsira,haka shima ya bata sannan sukabi kowa suna saka mashi ga baki.sune har karshe shabiyun dare anata abuguda,karshe har nafara hamma hakan da mami ta gani yasa tacema malik atashi hakanan kowa yaje ya kwanta,ai angode Allah ita dama bada son ranta aka hada partyn ba duk zakiyyace da ni,ima.
Hanuna cikin na mami tajani har dakinta daya gaji da haduwa komi yayi gwanin sha,awa.
Zaunar dani tai bakin bed dinta ta shiga toilet ruwan wanka tahada mun daga inda nake inajiyo kamshin turaren wankan da take xubawa,don inajin ma ba daya bane gaskiya.
Fitowa tai da towel ga hannunta ta bani.
"Shiga kiyi wanka kifito saina rakaki dakinki,abincin ki yana can yana jiranki"
Cikin jin kunya tace ansa da to mami,sannan ta shiga toilet din tajima tsaye tana kare mashi kallo,kamar wani wajen shakatawa gaka bayin yake komi gwanin kyau da burgewa.
Kayan ta cire ta shiga cikin komin tana lunshe ido,ruwa mai dumi mai gasa jiki ga kamshi na gaske dake tashi,tabbas wanan zai jima jikinta bai fita ba.
Akallah ta dauki minty goma sha biyar kafin ta iya fitowa tana tsane jikinta sannan ta dauro towel din,ta fito.
Wasu kayan bacci ta gani riga da wando dogon wandone har kasan guiwa,sai rigar mai gajeran hannu kayan masu tsananin kyau da taushi.lotion ta shafa sannan ta fesa turare tasaka farar powder kasan da lipstick,ta gyara gashinta ta daure da ribon ta saka hular kayan.
Tayi kyau Sosai da sosai har saida tayi murmushi,wata natsuwa takejin tana shigarta ta daban,jitake yanzu bata da sauran damuwa baba ya riga ya gama mata komi illa ta dawwama tana mashi fatan Allah ya biyasa da aljanna.
Mamince ta shigo ta bata hijib kamar tasan bazata iya fita ahaka ba murmushi tai tana sada kai ta ansa ta saka.
"Kibar jin kunyata har haka safiyya kamar ni,ima nake kallonki don Allah karki doraman nauyinki nima nafison muna yin abu irin na diya da uwa,kinjiko ki saki jikinki nima kamar mamanki ce"
Tana wasada yatsunta tace"insha Allah mami zanyi yadda kikeso"
"Yawwa Allah yayi maki albarka muje na rakaki"
Tafiya suke har xuwa wani part din na daban,shima ba baya ba wajen kyau komi ya hadu har bakin bed room ta rakani tace"akwai abinci nanan an ajiye maki kici kisha ki kwanta saida safe"
"Nagode mami mu kwana lafiya"
Ta ansa mata cikin kulawa sannan mamin ta juya tatafi,fitowarsa wanka kenan yana shiryawa cikin kayan baccinsa hankalinsa kwata kwata baya tare dashi,abubuwa sun cunkushe mashi kai!wai suna nufin anyi aurensu da safiyya how comes tayaya bacin tace bata yinsa kuma babanta yace bazai bashi ba,duk ciwon dayayi akanta hakan baisa ya ce ya amunce ba su dady da Abbi babu irin zaryar da basuyi wajensa ba ya rufe idonsa to shine kuma bayan ya warke anga bai mutu don itaba aka daura auren.uhmmmmm tabbas sun bashi surprise kuma yagode don baiji koda daidai da kwayar zarra na sonta ya ragu ba,amman saiya rama abunda tai mashi.ya ajiye duk girman kanshi da ajinsa ya furta mata yana sonta yaringa zarya gidansu,amman ita anbata zabi tarufe ido tace bata san haka ba.murmushi yayi bai taba zaton cewa zai sameta ba,ba kamar dayaji labarin aurenta wajen malik...........turare yake sawa yaji anbude kofa jiyowa yayi yana kallon kofar,don yasan kowa ya kwanta saboda gajiya tun kwana biyu basu zauna ba sai hidima suke yasan dai an daura auren malik da zakiyya,duk tunaninsa hidimarsu ce ba tashi ba.
Tsura mata ido yayi kamar yadda ta tsura mashi nata.jikinsa mutuwa yayi irin mutuwar da baitaba ji ba har saida ya runtse ido sannan,ya ajiye kwalbar turaren tana rungume hannuwa sadda kai tai tana murzar yatsunta cikin abayar,bata dauka daki daya zasu kwana ba aida bata shigo ba.
"Lafiya malama,ko kinyi batan hanya ne"
Kallonsa tai da mamaki jin abunda yace girarsa ya daga yace"ehy,waye yace nan ne dakinki"
Kamar mai koyon magana tace"mami ce ta rakoni niban sani ba ai,kayi hkr"
Tana jiyawa tanufi fita.
"Wait"
Ta tsaya tana jin gabanta yana faduwa ga duk alamu Abdoul fushi yake dan ita,kuma tasan hakan zata faru don abunda tai ita kanta ya dameta amman bata da yadda xatai da baba alokacin.
Bayanta ya tsaya yana rungume da hannayensa yace"ina kuma zaki,bakince mamice ta rakoki ba its oky shigo ki kwanta"
Jiyowa tai tana narai narai da ido ta girgiza kai"kabarshi zanje falo kayi hkr pls"
"Okay kijamun abun magana ko,to ban amunce ba nace ki wuce halan ma wancen abin ba nau bane shiyasa kiyya har take rawar jiki waje jerawa"
Ya nuna wani table da aka jera kuloli masu kyau da lemuka.
Jujjuya kai tayi cikin sanyin jiki tace"ban sani ba ance dai abincin yana nan"
"Okay muje ki dan sanmun yunwa nakeji"
Ya wuce wajen table din tana biye dashi baya,kallonsa take kamar ancanza shi yayi rama sosai kuma ya kara haske da kyau.gashi ya sake barin gashi afuska saiya kara mashi kyau,dakin sai kamshi yake.
Kujera yaja guda biyu dake zagaye da table din ya zauna itama ta zauna kan guda,shiya bubbude kulolon ferfesun kifi sai faten Irish yasha ganyenyaki,kaza gasassa da lemuka masu sanyi.
Kalonta yayi yaga duk ta takure ya dauke kai,ya zuba nashi ya hauci baibi ta kanta ba,yana gama wa yaje ya haye gadonsa ya juya mata baya.
Duk abunda yake na karfin haline,ba har xuciyarsa ba yana son dai ta gane cewar shi Santa yake da xuciya guda ba wani abu yake nema ajikinta ba.
Hawaye suka silalo mata tashare,tatashi ta kwanta kan kafet din dake malele adakin tana dunkulewa cikin hijab dunta,me hakan yake nufi me yakesin nuna mata,wanan daren daga shi har ita basu runtsa ba saida ya tabbatar tayi bacci ya daukota ya sata gabanshi,tusata yayi kamar tv yana kallo haka asubar fari taxo mashi


Kuyi hkr zuwa anjima zan sake wani postinig din kkda read more biyune
[10/17, 4:57 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️............64

Tsintar idonsa tai cikin nata daidai zata juya kenan taji kamar kiran salla,kuma acikin dakin take jiyosa
Kamar alam ne akasaka mai kiran salla idan time yayi,dauke kai yayi daga kallonta yasha mur.
"Meya kawoki kan gadona,harda wani shishshigeman cikin jiki keda bakisona miye na kwakwata kuma"
Zaro duka idonta tayi tana kallonsa tana kwalkwal da ido cike da son yin kwallah cikin muryarta ta bacci tace"wlh nibana kwakwarka kuma bani na hau gadon ba,Allah ma ya sani ni akasa na kwanta saidai idan..........tsura mata ido yayi yana kallon lips dinta sun mashi kyau sosai ya karkace kai yace"saidai me?saidai idan ni nine na daukoki ko saboda ina kwakwarki zanbiki har kasan kafet na daukoki,to inmaki me?"
Harara ta watsa mashi tana tashi zaune taja blanket din xuwa kirjinta saboda babu hijab ajikinta,hakan yasa ta tabbayar shine ya daukota zai rena mata wayau.
"Nafa gajii da halin da kake nuna mun daga jiya zuwa safiyar yau,wai ce maka akai nima damuwa dakai nai don Allah ka sallamani inhar dole akai ma"
Tatashi tana saka abayarta ta shife toilet tayi fitsari tayi alwalla tafito,tana shan mur.
Danne murmushinsa yayi yace"ke nida dakina zaki yimun rashin kunya,Wlh zan turaki falo duk sanyin dake can yakare kanki daga an rufa maki asiri"
Wata hararar ta danna mai tana neman abun salla,"kaga banda lokacinka"
Ta nufi inda taga an killace shi donyin salla saidai kuma wandonta bai kai mata har idon sawuba,kuma abayar itama bata wuce guiwa ba.
Kauda kai yayi yana dariya can kasan makoshi,yaga yadda xatai sallar ai dole dai yakawo wani taimakon.satar kallonsa tayi taga ya juya baya yana kashe alam din daketa ki faman kiran sallah.
Ganin bata ita yake ba yasa ta dan waigo "don Allah........"
Mikewa yayi ya nufota dan danan kuma gabanta ya fadi,runtse ido tai tana adduar karya iso inda take amman adduar bata ci ba daf da ita ya tsaya har yana goga goshinsa anata dan danan ta mamuke jikinta tana runtse ido.
"Kaga fa salla zanyi lokaci yana tafiya kuma bacci nakeji"
Kuncinsa ya dora bisa nata idonsa rufe kamshin dake jikinta yakeji yana sashi wani yanayi,don baisa ma meyake shirin yi ba.
"Ban hanaki ba ai,kiyi sallar ki"
Kamar zatai kuka tace"ai ka tareni ko"
Murmushi yayi yana jaye abayarta ahankali ahankali har cinyoyinta suna bayyana ya dora hannunsa akai.........numfashinta taja tana rike hannunsa "ahaka zaki sallar xindir"
Kasa ta silale tana soka kanta cikin cinya tana jin kunyar duniya tana rufeta,har yanzu jitake hannun nashi yana cinyarta.
"Tashi na baki kayana kisa"
Babu shiri ta dago tana kallonshi cike da zare ido.
"Allah ya kyauta nasaka kayanka"
Dariya yayi yana nufar wadrop din kayansa yana budewa.
"Yanzu kuwa zaki ga ikon Allah"
Kallonsa take ita duk gani take kamar bashi ba,duk ya canza gaba daya tashi tai tsaye tana raba ido ita kam yau taga haza harda haxihi.
Jallabiya ce ya dauko fara kal sai kamshi take,kuma zata shigeta saidai tsawon ne zai mata yawa.
Mika mata yayi daga ina take"zoki ansa kisaka kokuma yanzu kiga ikon Allah"
Babu musu tataho tana rabewa gefe ita wlh duk ta takure ita yau wata irin kunyarsa takeji,kamar ta bace ko tashige cikin bango.
Mika hannu tai zata ansa taji yajata dakarfi xuwa jikinsa ya matse...............abun yazo mata bazata gaba daya jikinta ya dau rawa,dan danan kuma taji ta nemi natsuwarta ta rasa mutsu mutsu kurun take tana son kwacewa amman yayi mata riko bana wasa ba.
"Zaki saka ko ni nasa maki,gardamammiyar yarinya kawai daga yau idan nace ga abunda zakiyi banson musu just do it kawai."
Daga kai take kamar kadangaruwa tana kermar baki"to kasakan wlh zansaka Allah zan saka"
Murmushi yayi ya tallabo face dinta yana kallon yadda ta rufe dukan idanunta,saiyaji sha,awar ya sunbaci idon nata.
Ahankali ya matso da bakinsa ya mata sunba kan kowane idon nata,sannan yace "oya open ur eyes"
Girgirza kai tayi ahankali kuma saita fara budewa tana zube mashi idon nata akan fuskarshi,gira ya daga mata yace "are u oky"
Daga kai tayi yace"oky bari muyi jam,i zakiyi dani ko"
Nan ma daga kai tayi ya saketa yana nufar bayin shima.
Wata nannauyar ajiyar xuciya ta saki tana nufar inda ake shiga asaka kaya taje ta cire na jikinta tana sauri karya zo ya sameta,fadin ya yi mata yawa amman daga kasanta hips dinta sun cika kasan,sai tsawon daya mata yawa shima.
Kalon kanta tai ga mirrow din dake wajen taga kuma tai mata kyau,saidai saman ne ya mata yawa Allah yasota bata cire bra ba da kirjinta yawo zaitayi aciki.
Jin anbude kofar toilet din yasa ta fito tana sanye da abayar,kallonta yayi yana murmushi ya je shima ya canza kaya xuwa jallabiya yajasu sallar,karatunsa gwanin dadi kamar ya daina ashe daman ya iya qira,a haka aikuwa nan gaba idan komi ya daidaita zairinga mata kari don ita inda yake jawowa ma bata kawo nan ba.
Suna sallamewa kowa yaja gefe yana azkar dinsa,amman kadan kadan sun saci kallon juna.
Idan ya kamata tana kallonsa sai yayi mata murmushi kawai,idan itace ta kamashi yana kallonta saita watsa mashi harara jinjina kai yake ya rabu da ita ahaka har suka gama,zaman cin tuwo yayi yana kallonta yace"good morning love"
Sadda kai kasa tai tana jin yana kashe mata jiki,ashe dai darabon zasu sake ganawa ashe dai darabon su mallaki juna,aduk sanda ta tuna saitayi wa baba addua marar iyaka.
Ahankali tana wasa da hannunsa da yasha kunshin biki tace"ina kwana"
Jingina bayansa yayi da abun gado yana ajiyar xuciya yace"bani nafara gaidaki ba"
Murmushi ya kubce mata ta sake boye fuskarta tace"ai babba baya gaida karami inko har karamin ya ansa to ya cika marar sanin girman na sama dashi"
Dadi yaji ya kamashi yace"oky to as from 2 day damun gama salla inason gaisuwarki ta fara shiga kunnena,are u hear me"
"Insha Allah"
Shiru sukai kowa da tunanin dayake hannunta hake kallo kunshin yayi masifar daukar hankalinsa,kamar ya kamashi yayita lasa.kamar kurame haka suka zama,jawo system yayi yana dannawa bakuma don yasan me zai ba,kawai dai yana son ya dauke hankalinsa daga shagala da kallonta basu ankaraba
Alam ya buga karfe takwas,xunbur tatashi taje ta cire jallabiyar ta ajiye mashi gefen gado ta nufi kofar fita.
"Ina zaki"

"Wai kitchen naga time yana wucewa koba ku break da wuri anan"
Baisan meyasa gangar jikinsa takeson rusa mashi plans ba,runtse idonsa yayi sannan yace"xonan"
Ahankali take dawowa ta rabe gefensa ya ajiye computer ya matso kusada ita,kamar zai rike hannunwan saiya fasa yace"keda kike amarya waye yasaki shiga kitchen?"
Soke kai kasa tai batace komi ba.
"Ko kin manta amaryace ke?"
Girgirza kai tayi yace"halan kurma kika koma"
Shagwabe fuska tai bata san ma tayi ba tace"to ni ai nasaba agidanmu ko"
"Ai yanzu tattalinki ake idanma mami ta ganki kitchen nabani ai"
Kallonsa take cike da tambaya "to miye"
Zaro ido yayi yace"ai ita yanzu ma duk tunaninta kinan kwance babu lafiya me zai iya fiddoki"
Har lokacin kwalwarta bata bata komi ba,kallonsa take yadda yake murmushi tace"nifa ban gane ba,mezai sameni to bacin na warke"
Matsowa yayi yarage murya kamar wani yana jinsa yace"kin manta kenan,ina nufin ai kowa gani zai na angonce yau kinga ai zasuga kinan kwance ina..........bata san sadda ta tashi ta shige toilet ba ta rufe kofar.
Me zai inba dariya ba rabonsa da dariya irin wanan bazaie ga lokacin ba.
Knocking din kofar falon yaji anayi ya tashi ya fita yaje ya bude,ni,ima ce da kaya ga hannu tace"yaya ina kwana"
"Lafiya lau wadannan kayan fa"
"Anty safiyya mami tace akoma wa"
Bata hanya yayi tashigo ta ajiye su bisan kujera tace"mami tace karfe tara kufito ayi break su Abbima har sun iso"
Jinjina kai yayi yana daukar kayan yana wuce wa dasu ciki.
Har lokacin tana toilet din ya ajiye ya isa bakin kofar yace"ki budemun na shigo wanka zayi idan ke bakiyi"
"Don Allah yaya Abdoul katai falo idan na gama saika shigo nidai wlh kana sani jin kunya don Allah karka kara"tafada cikin muryar kuka har da kwallarta.
Dariya yayi yace"oky kiyo wankan bazan sake ba natai falon ina jiranki"
Ya haye gado yana dariya kasa kasa wankan ta tube ta shiga yi da ruwa mai dumi,tayi anfani da kayan wankanshi ta jima kafin ta fito daure da towel dinsa tunda yace mata yana falon,ko kadan batai tunanin yana nan ba,kanta tsaye ta fito bata kali gadon ba ta nufi kayanta tana dubawa ta dauki karamin towel taa tsane gashinta...........sakarai ya koma ya saki baki da hanci yana karewa halittarta kallo,bata ankara ba saida taji kamar motsin mutun sakin karamin towel din tai kasa tafasa kara don har ga Allah ta tsorata bata dauka da kowa ba aguje ya sauko ya riketa tamau yana rufe mata baki
"Keee karkitara mana mutane"
Shiru tai ajikinsa yarungumeta suna sauke ajiyar xuciya tare,shafa kanta yake ahankali yana bubbuga bayanta ahankali har yakaita bakin mirrow.ya zaunar da ita,
Kwalla sharrrr suka xubo mata saboda tsabar kunyar da taji tama rasa mezatai.
"Shiiiiitt kukan me kike"
Fashewa dakukan tai "nace maka katai falo meyasa ka zauna ehy,nidai don Allah karabu dani inshirya da kaina katai kaban waje"
Juyawa yayi kurin with out say anything,sai taji bata kyauta ba koba komi dai mijinta ne yanzu.
Amman kuma idan ba haka taiba bazata shirya cikin kwanciyar hankali ba,shiryawa take cikin natsuwa tasan fushi yayi bazai dawo ba.
Doguwar rigace irinta indiyawa tayi masifar hawan jikinta komi fito masha Allah,sai dan mayafin rigar pich color be da dark pink rigar sai style din ya sake fiddo kyan rigar da wadda ta saka ta.
Simple make up tayi don kayanda ni ima ta kawo harda kayan shafa tasan dakin namijine ba lallai asamu irin kayan shafe shafen mata ba.
Tasa turarensa kadan don karya ringa tashi dayawa,
Tafita falo jiransa shima baijima ba ya fito cikin suit yaa rike da rigar saman baikai ga sawa ba,sai farar dake cikin kawai sai agogo da bakaken takalma yayi kyau amma ta kasa fada wuceta yayi tabishi baya suka isa cikin main falon gidan kowa ya hallara su daman akejira daga nesa take hango zakiyya tana mata dariya,duk saitaji kunyarsu ta kamata kowa zai mata kallon sunyi wani abu bacin ba suyi komiba
[10/18, 5:00 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️............65

Bayan angama break dady yajawo hankalin kowa anan yafara nasiha da nuna karfin kaddara da kuma rabo,duk inda kake inhar abu rabonkane saiya tadda ka yabada misali da auren fiyah da Abdoul yake cewa.
"Har Saura sati daurin aure bamusan da cewar babanki zai bamuke ba,mun riga mun hkr shima kuma ya hkr kwatsam saiga kira daga maigadin gidan yaya(watau baban Abdoul kenan)yace malan kabir yana neman mu agaggauce,cikin hanzari muka samu visa bamu sanar dasu ba nan mundai ce kirane daga wajen aikinmu.
Alokacin yake gaya mana yana son mubada sadaki da komi sati mai xuwa za,a daura auren tare da kanwrki,amman yace muyi shiru soyake ya maku bazata abun yayi bala,in yi mana dadi Abbinku kamar zai mashi sujjada din jindadi,haka muka bayar da kudi da komi sanan nayowa maminku waya cewar zan turo salamatu ta tayata hada lefe kala biyu,don mun yanke hukuncin harda na malik za,ahada rana guda ayi.
Kuma ranar na zagayowa aka daura danaku dana malik da zakiyya,malik din kadai na sanarma wa saboda hidimar zuwanki don haka kudauki wannan matsayin darasi,inhar rabonka ne abu to kocin rami saiya bika saidai idan rabon yana nesa zaijima baizo ba.
Don haka ina mai jawo hankulanku daku zauna da juna lafiya,kuyi hakuri da juna duka rayuwar bakomi ke isarbawa ba sai hkr,zamane bana yau ba bana gobe ba anafatan mutuwace zata raba,don haka ku matan kuzama masu biyayya ga mazanku sannan kukuma kuxama masu adalci da kyautatawa garesu,don haka ina maku fatan alkairi garayuwar

Please Login or Register in order to submit comment