Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a sunyi sallar isha,i masallaci sannan malik yafiddo wata jibgegiyar car,wadda sai Alfah yayi wata bai hauba,daman suna dawowa yasaka maigadi ya gogeta don ma rufe tae ba kura tayi sosai ba.
Sanan suka dauki haya Alfah na son fesin cap ita yasaka bisa kansa,ya rufe idinsa da ita,imagining yake yadda haduwar tasu zata kasance,zaiso yaga wadannan idanuwan nata kamar anzuba oil aciki suna daukar ido yaga ya zasuyi,murmushi ya kubce mashi kodawace fuska zata anshesu,yasan shidai mai laifine bama lallai ta kallai ba,amman bazaije yadawo bai saka idonsa cikin nata ba.
Malik kamar anzuba mashi kankara cikin rai ganin yadda aminin nasa yake cikin annashuwa,alamar dai fiyah ta samu wani waje ta zauna aransa.

Munata fira bayan mungama ayyukan mu Anty na can itada umcle yahya suna kallo falo,nida hasana da princess dina muna dakina muna ta hira da daroya,amman har cikin kokon raina banjin dadi,wata irin kewa nakeji wadda banson menake ma kewar ba.saina dauko wayata da niyyar kunna wa saina fa saboda nasan yaya malik zai neman.ikuma so nake na nuna mashi nayi fushi suduka susan babu wani abu cikin raina balle in har nabar zuwa inda suke wani yazargi bzan iya hakanba.princess dake mamulan hannu na kalla hasana kuwa ansa waya take,saukowa nai na nufi falon don anata mama tasha.
"Anty little yunwa takeji,tun dazu fa baki tua da ita ba"
Ansarta tayitana cewa"keta gado shegen tsotso,don haka da wuri zan fara bata cerelac ko priso."
Uncle yahya dake ansa waya ya harareta naji yace"ok Abdoul saika iso"
Kashe wa yayi duk sai naji na zargu wane abdoul din kenan,koda yake ai basu san juna ba kuma bata zaton zai iya zuwa yadda yake jida kansa........"safiyya wanda ya bankeki shekaran jiyane zaizo dubaki jeki gyara falon saukar bakin don Allah."
Wucewa nai jikina yana wana irin sanyi,xuciyata banda zillo babu abunda take,ni narasa wannan sabon yanayi nawa.Anty naji tana tambayarsa"waye kuma haka uncle,badai da biyu xaizo ba don ni nariga nayiwa kanwata miji"
Dariya yayi yace"inma da uku yazo jamila miye naki,ita mace ai Allurace cikin ruwa mairabo yake dauka,kuma shi abokinane sosai rabuwarmu tun school yasa abotar ta rushe,banda wani good friend banda shi,kuma dashi da muhseen babu wanda nake ma bakin cikin samun safiyya,don kuwa duk wanda yasameta zanyi murna su duka duk nawane,kuma kowane babu na banza cikinsu abunda zakiyi mata kawai shine addua da fatan alkairi"
"Uhm,shikenan amman ni gaskiya ina bayan muhseen kuma zan cigaba dayi mashi canpen"
Wucewa nai inajin zuciyata tana karkarwa,wai waye yace dasu wannan arrogant din yana sonta,shi wannan wacece ma zata soshi inbanda zakiyyar,yadda yake dashegen miskilanci da fadin raiAllah yasawake mun auren dangiya.

Mrs bb e
Mom muhseen.
[9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........30

Gyaran falon tayi cike da rashin kwarin jiki,bawai don gajiya ba,eh to akwai gajiyar ma amman kuma zuwan Abdoul wajenta shine dalilin dayasa jikinta duk ya mace murus.
Turaren wuta ta saka ta kuma kunna tsintsiyar kamshi,saida hayajin ya gama bud'e dakin sannan ta dauko freshner ta sake sawa,ta gyra labulbulun falon yayi lum gwanin sha,awa ga hasken kwan nefa farin haske da blue sai red green dake haskawa.fitowa tayi ta iske su cikin falon uncle yana rike da little fiyah suna hira da Anty.
"Kishiga ki tanadar masu abunda zasu ci ko hakanan xasu zo sutai."
Ya mutsa fuska tayi tace"Anty ruwa ma kadai ya ishesu"
Harararta tayi uncle yace"haba dai fiyah,bakonka annabin ka jeki falona akwai snacks din da muka rage dazun da friends dina suka zo,basu ci daya wa ba sai ahada masu da lemo ko"
Ba yadda ta iya haka ta juya taje ta dauko taje kitchen ta zuba su cikin wasu bowls,Anty tace akwai ferfesun yan ciki data saka akai mata dazun,tace ta dibar masu .
Kamar zatai kuka tace"wai Anty saikace wani shugaban kasa ne zai zo"
Kallon banza tayi mata tace"dalla banson sakarci,mutun baitaba zuwa inda kake ba yau zaizo kuma sai bazaka tarbeshi da kayan motsa baki ba,ni indan tanine wlh bamson zuwansa,don inajin kamar da biyu zaizo yana iya amshe ma muhseen kunerarsa.
"Anty wai ance maki muhseen dinma wani sonshi nake,nifa wlh kawai don ba yadda zanyi dashine,nifa ba yanzu zanyi aure ba"
Dungure mata kai tayi tana wucewa tabara.
Bayan ta gama shirya masu abun da zasu bukata ta koma daki,samun kanta tayi da yin wanka hasana tace"bako zakiyi ne fiyah"
Shafa take yi cikin mutuwar jiki "Wanda ya kadeni rannan zaizo dubani"
"Kice daya kadeki sai kuma yayi wuf da xuciyarki"
Murmushi tayi tace"waye yace maki,shi baya soyayya ai"
Dariya hasana tayi tace" naga waliyyi,karewar baya soyayya bari dai mugani ni nasan badubiya kawai zaizo ba harda banruwa zaiyiwa flower sa."
Dariyar da bata shirya ba tayi tam cigaba da abu da take.
Uncle ne yafita jin karar mota gaisawa sukai sosai da Alfah da malik,sun jima a harabar gidan kafin yyi masu iso.hira suke da malik kamar sun saba,indai malik ne badai iya hira ba koya kahadu dashi zakaga ya jaka ajiki dandanan zaku saba baida bakunta.
Anty ta wuce can ciki.
har cikin falon ya sauke su suka cigaba da hirar,sai daga baya ya fito don kiran safiyyan.
Simple make up tayi powder da lipstick sai kwalli,tasaka rigarta coffee brown da zanen milk color ajikin rigar,sai tayi rolling da milk din gyale tana fesa turare.
"Safiyya kifito haka nan sun iso,hasana ki rakota saiku gaisa ko"
"To uncle insha Allah"
Kasa motsawa tayi ita wai dawace fuskar zata tarbi wannan mutumen,kuma ma dame yazo ne wai.
"Kika zauna kuma ko gabanki yake faduwa ne?"
"Kice bashi kadai ya kamu ba ace kema yayi carab dake,"
Murmushi tayi tana mikewa tace "muje"

Tana tafiyar gabanta yana faduwa har xuwa bakin kofar shiga,togewa tayi hasana ta jata suka shiga da sallama..............idon malik akan su yana cikin kujera,hasana cikin fata ta nemi waje ta zauna tafara gaisa malik.
"Kece yar rakiya kenan,ya kike yagidan"
"Lafiya lau wlh anzo lafiya"
"Alhamdulillah ansha suna Allah yaraya me akasamu"
Dariya tayi tace tana nuna fiyah"gata nan itace aka samu"
Cikin murmushi d mamaki yake kallon fiyar yace"iyye qanwata ashe takwara akayi,"
Murmushi tayi mashi bata ce uffan ba,hasana ta juya ga Alfah tana gaidashi,banyi tunanin zai kar mata fuska su gaisa ba.
"Lafiya lau ya kike kunsha suna Allah yaraya"
Cike dajin dadi ta ansa tana tambayarsa aiki.
Malik ya ce"qanwata baku gaisa da abokina ba"
Kamar karta kallai suna ta hira da hasana cike da wayewa da sanin makamar zance,kallonsa tayi sosai taga irin yadda yayi mata masifar kyau,har ta shaga da kallonsa saboda yadda kayan suka ansheshi,ga hasken dakin dake haskawa sai hakan ya karawa fuskarsa kyau.
"Kinga yar uwarki zata cinyeni da kallo bacin ko gaidani batai ba"Alfah ya cewa hasana.
Dariya duk suka saka mata wadda jitai kamar ta nitse don kunya,wai garin yaya ma har ta shagala da kallonsa haka.
Sadda kai tayi tana murzar yatsunta hasana tace"kinji to fiyah,baki gaida bakon naki ba."
Kasa magana tayi wai meza tace mashine itafa bazata gaidashi ba,malik yace"qanwata harni ma din bazaki a magana ba"
Bata kallai ba balle ta tanka,hasana tace"kila fa kunyata takeji,kinga bari nabaku waje sai anjimanku fa mun gode"
Sallama tayi masu ta wuce,malik yace"tunda ko ruwa baza,abani ba nibari nayi karanbanin dauka insha."
Sai lokacin tayi saurin tashi tana ajiye wayarta ta matso da tabke din gabansu tana bude kwanukan tare da zuba lemukan acikin cups sannan ta zuba ruwa shima,dauka tayi ta ba malik cikin sanyin murya tace"kayi hkr yaya malik ga ruwan,don Allah kudan taba wadannan don ku Anty tayi"
Ansa yayi yana cewa"ainayi hkr qanwata kece za,aba hkr don nasan fushi kike damu,tun jiya wayarki akashe meyasa?"
Satar kallon Alfah tayi taga idonsa akanta ya shige cikin kujera yasaka yatsa guda yana sosa girarsa.
Dauke kai tayi tace"ba haka bane yaya malik kawai dai nayi hakane don a barku kuhuta don naga alamar xuwa wajenu danake ysa ake cin xalina ake yimun ugunta ana gaya man aganganu babu suger"
Malik yakalli Alfah yaga har lokacin fiyah yake kallo kamar zai hadiyata.har cikin ransa tayi masifat yi mashi kyau,amman bakinsa yayi nauyin da bazai iya furtawa ba,bayajin ma koda wasa zaiya furta hakan amman yadda tayi mashi yasa yaji wani abu yatsaya mashi ga makoshi,babu sannu da zuwa babu ina wuni babu karramawa.malik ne yace
"Kiyi hkr to insha Allah baza akara ba,,ga Abdoul nan ma yazo taya ni baki hkr ko Alfah"
Yajuya yana kallon Alfahn.
Tashi yayi zaune yace"hakurin me zan bata bacin nida ba,a dauka da mutunci ba ko ruwan ba,a bani ba bae nasaka ran zan samu sannu da zuwa kaga kuwa zuwana baida anfani,kaida keda mutuncin da har za,a kulaka kana iya zama zanjira fitowarka."
Ya mik'e ransa ab'ace don har cikin karshen ransa fiyah ta kuntata mashi,badan yaso yataho ba amman shine zai samu wannan tarbar.
Dandanan taji hankalinta yatashi,haushin kanta ya kama ta bazata so yatai da fushinta ba koba komi bakonta ne,tara sa gane kanta zuciyarta rawa take inhar tana sauraren muryarsa,idaniyarta bata hutawa inhar yana mata wannan kallon,takaza control din kanta akan wannan sabon yanayin data kejin kanta,cikin sanyin muryarta tace ma malik.
"Yaya malik kace yayi hkr yadawo wlh niban wulakanta shiba"
Murmushi malik yayi yace "aa aibani nayi mashi laifi ba qanwata kece don haka kibishi kibashi hkr kafin ma kidawo bari naci wannan yana jawo kwanon snacks."
Jikinta amace zuciyarta ta cushe bata son yatai da fushinta harga Allah bata so ransa yabaci ba,
Kallonta yayi yace"kije mana"
Kamar Mai tausayin asa tatashi tafara nufar kofar fita,dariya yake son yayi amman baison tagani.
Waigowa tayi kamar zatayi kuka tace"yaya malik karya dakeni,karya zuciya ya mun tsawa."
Girgiza mata kai yayi yace"bazai maki haka ba kidai bashi hkr kisamu yadawo ya ci wannan garar don wlh yamun dadi sosai maza jeki"
Haka ta bude kofa ta fita aikamar jira yake ta fitan ya dunga kwasar dariya,lallai tarkon nan yayi kamu sosai,insha Allah komi zaizo da sauki.
Yana cikin mota ya kwantar da kujerar zaman banza ya kwanta ya rufe fuskarsa da fesin cap di sa.
Jikinta wani irin sanyi yayi ahankali ta kwankwasa glass din window din,tunda ta tsaya kamshinta ya iskoshi jiyai xuciyarsa na mashi kai kawo,ahankali ya sauke glass din baiyi magana ba baikuma dago ba,lawallar kuda ta kamayi tarasa abun cewa bakinta rawa yake wana mutun yana ata kwrjini cikin kwana biyunnan.
"Sauro yana shigo mun inbakida abun cewa plss zan rufe glass dina"
Bakinta yana kerma muryarta kamar zatai kuka tace"pl....s kayi hkr.....karka tafi kadawo don Allah"
Wani sanyi dabai san daga inda yake ba yaji yana sirarowa cikin ransa,amman sai yayi shiru yana adduar Allah yasa ta sake bashi hkr karta tafi.
Bata san dalilin hawayenta ba muryar na rawa tasake cewa"plssss kaji,im sorry........"maganar ta katse sanda kukanta yake fitowa
Wani suka yaji ga kirjinsa jin muryarta na fidda sautin kuka,ahankali ya tashi jiyake kamar anzare mashi duk wata lakka daga jikinsa muryarsa kamar tafito daga cikin frig yace"come in"
Ahankali ta zagaya wajen zaman driver ta shiga kanta akasa hawaye na bin fuskarta,tunda yake rayuwarsa bai tabajin kwatan kwacin irin halin dayakeji yanzu ba.koma wa yayi ya kwanta yanajin wani irin yanayi na sake bin gabbansa.
Ahankali take sharar kwallah,inza,a yankata bazata iya cewa ga dalili ba.
Hanky taga ya miko mata babu musu ta ansa tana kaishi ga fuskarta,wani kamshi ne ta shaka daya saka taji duk wani kunci na xuciyarta yaya yaye,ahankali take share kwallar har ta samu kwallar ta tsaya.
Sannan ta mika mashi bai ansa ba yace"nabar maki"
Tanajin yadda xuciyarta take bugawa numfashinta kanshi ya canza salon fita,
Kamar mai koyon agana tace"kazo muje kayi hkr ko lemun kasha don ku akai"
"Danshi dai,ni awa za,ayi abu danni daman ban saka ran samun tarba daga gareki ba saboda baki daukan mutun ba"
Juyowa tayi duk da ba ganin fuskarsa take a tace"amman ai nabaka hkr ko"
Murmushi yayi yace"baimun ba kije kawai ngd kin baroshi shimadai bacin dnke yazo"
Kamar zata rushe da kuka tace"plsss mana kayi hkr to"
Malik ne yafito shida uncke suna hira cikin fara,a duk sai taji ta kunyata.
Fitowa Alfah yayi itama ta fito tana jin kunyar uncle tasan dole zai dauki wani abun,tunda gasu acikin mota su biyu.
"Tunda kunya ta hanaka cin kayan tarban bakon Abokina gashinan na saka an yimaka takeaway dashi,don Allah karkace bazaka ansa ba tasha wuya fa wajen hada maka"
Duk uncle ne yake wannan maganar.
Kanta akasa malik ya isa inda take cikin kasa da murya yace"qanwata kuka kikai mashi"
Tabe fuska tayi kamar zatayi kuka tace"kai yaya malik shine fa........kasa magana tayi tana sadda kai"
Dariya malik yayi yace"qanwata gaya mun meyayi maki yasaki kuka"
Kasa ansa shi tayi don bata san ma me zata ce mashi ba.
Hanyar shigewa tayi zata shige gida uncle yace ah safiyya bakiyi sallama da bakon naki ba,xokuyi sallama aimun gama maganar."
Sake musabaha sukai dasu yakoma cikin gida yana cewa maigadi idan ta shigo arufe gidan.
Malik tuni ya shige mota yana jiransu kasa motsawa tayi daga inda take saidai shine ya isa inda take,ta juya baya ya tsaya daga bayanta.
Tsayuwarsa yasa taji kamar ta koma kankara saboda wata irin mutuwar jiki tasame ta.
"Goodnight amman karki manta banyi hkr ba,zan tai da cewar nazo kin wulakanta ni saboda..........juyowa tayi kadan yahana ata fda kirjina ba tayi saurin dan ja baya,
"Don Allah..........lumshe idonsa yayi yana girgiza kai wanda kadan yahana numfashinta bai kare ba.
"Goodnight"
Haka yabarta kamar anshuka ta har motar tabar kofar gidan sannan ta samu karfin guiwar daga kafarta tashige.

Wannan dare xukatan mutane biyu basu huta ba.

Mrs bb
Mom muhseen.
[9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........31

Washe gari da wuri suka gama soyen raguna uku,zuwa karfe biyu na rana sun gama dan ma Suna da dan yawa kuma kasko uku sukai,duk yadda fiya take kwari kwari saida Inna balaraba da Anty jamila sukai mata magana ko bata da lfiya,saboda yadda duk ta zama sukuku,bacin sun santa da kazar kazar da yawan magana wani bin.
Tun safe take tsammanin wayar zakiyya amman shiru kuma ta kirata bata samu ba,duk saitaji gabanta yana faduwa Allah yasa ba wani abunne zai faruba,haka taita tsammanin kiranta har karfe uku na rana.
Daker ma taci abincin rana kadan kadan ta duba wayarta taga ko zata ga misscall amman shiru.
Saida akai sallar la,asar ta sallame kenan taji karar wayar zunbur tayi ta jawota
Kosallama batakai dayi ba taji muryar zakiyya tana magana cikin tsananin tashin hankali,
"Fiyah........kina ina fito yanzu fito don Allah ki saman hanyar shoprite.......babu lokaci kifito don Allah akwai babbar matsala"
Jikinta ya dauki karkarwa tace"ganinan zakiyya kiyi kokarin boyewa biyoki akai ne"
Muryarta da alamun kuka take tace"eh biyoni sukai gasu nan bayana ina cikin mota na samu waje na lab'e kiyi sauri bari na turo maki inda zaki saman."
Kashewa tayi tatashi zunbur ta canza abayarta ta suri wayar tafito falon.
Anty na kitchen ta sameta tace"Anty don Allah zan fita bazan jimaba,result dinmu na islamiya zan ansa feea tace yau ake rabawa kuma basu bada na wani,don zasu tantance wadanda zasuyi musabaqa"
Kallonta take kamar zata karyata ta amman kuma bata hujja,
"Shikenan,amman safiyya don girman Allah kiyi kokari kidawo da wuri,banson kiyo dare nafison kina kusadani"
"Insha Allah bazan ba"
Fita tayi cikin hanzari saita dawo ta duba jikkarta tadauki kudin taxi ta sake ficewa cike da fargaba.
Duba kwatancen tayi tasanar da mai taxi din ya karya kwana ya nufi wajen,suna shiga wani lungu ta hangi mota tsayw wajen,tunaninta ta zakiyyarce don bata sanar da ita kalar motar da take ciki ba.
Sauka tayi ta sallami mai taxin ta nufi motar,kwankwasa glass din tayi aka sauke shi idonta akan wani bakin mutun fuskarshi babu kyan gani,shikadai ne cikin motar ja baya tayi tana rawar murya tace"kayi hkr nai zaton yayana ne yace mun yana kusa da nan"
Kallonta yake yana zaro ido yace"bar nan kafin ina farka cikinki"
Babushiri na yanki hanya amman jikina yaban akwai wani abu,labewa nai wani sakon gida ina leken motar wani katon mutun yafito daga wani gida hannunsa da wata jikka ta mata,yana fitowa daga gidan na hangi faduwar mukulli baisan ya fadi bama shi,shiga motar yayi ya jima sannan sukaja suka bar wajen.
Saida na tabbatar sunyi nisa sosai na dawo da sauri na dauki key din,nashiga kofar da zata sadani da gidan don kofar babu marfi.
Mukullin nasakana shiga bude gidan jikina ko ina rawa yake,daker ya bude na shiga gidan da gani andade babu kowa cikinsa.
Kiran wayar zakiyar nayi tana ringing bata dauka hankalina yasake tashi,sako da lungu na gidan nashiga kewaye wa Allah baisa naga kofa mai irin mukullin hannuna ba,fitowa nai nayo hanyar fita naji alamun tsayawar mota jinai fitsari zai kubcemin.........wata mota da take ajiye ta lalace na kurda kasanta na kwanta gabana banda faduwa babu abunda yake,zuciyata kamar zata fito waje haka nakeji.
Motace aka shigo da ita daga baya naga an fizgo mutun abayan motar idona akan kafafun mace,hankalina yasake tashi don tabbas raina yaban zakiyya ce.yadda take nishi da gurnani daji bakinta suka dade..........rawa kurin jikina yake bakamar jin danai wani yace"da alamun fa wani yashigo mu jefa shegiya can dakin muduba mugani."
Dayan yace"nifa wannan yarinyar ban yarda da ita ba duk zargina tare suke"
"Aa ban tunanin haka kamota mugani,shegiya zaki yi magana ne inkikaji ukuba,saikin fadi inda kika ajiye memory din nan"
Wani daki dake bayana suka bude suka sata suka jawo suka rufe da kwado.
Dube duben gidan kawai suke Allah bai basu sa,ar ganina ba,sannan suka fita nabada tsawon lokaci sannan nafito ina rawar sanyi duk da ba sanyin nakeji ba.
Leka wa waje nayi naga basunan na koma ina b'ab'are na samu katon dutsi naringa bugun wannan kwad'on yana waigen bayana karsu dawo su saman.
Nasha wuya kafin na samu nasarar balle kwadon.
Shiganai dasauri itace kau kwamce daker take numfashi,cikin sauri na cire plaster da aka rufe mata baki,ashe bayan ma plaster saida suka cusa mata soso cikin bakin.
Tari takamayi tana rike da wuyanta,
"Tashi maza zakiyya bamuda lokaci,koda ace munyi asarar memory yazama dai ke bamuyi asararki ba,"daker tatashi muka fito janta nake daker muka fito duk arude nake,karar motar da mukaji abayan mu bayan fitowar mu daga cikin yasa ina juyawa muka hada ido da daya daga cikinsu,zakiyya tace cikin nishi "muruga fiyah yaya mamman ne karmu tsaya,idan suka kamamu bazasu barmu da rai ba."
Tunkafin na idasa jin mezatace na fizgeta muka fara falfala gudu,yayinda suka rufa mana baya don insukace su shiga mota zamu bace masu.
Gudu muke wanda tunda nake bantaba irin saba,zakiyya tun bata iyawa har ta zage itama damun ga sun kusa cin mana saimu sake himma...........wani gida dake bude muka fada muka labe bayan kyauren kofar,muna lekensu suna dube duben wajen.
Jinake fitsari zai kucce man zakiyya durkushewa tayi kasa tana rufe bakinta,don nishi take take sosai karsujimu.
Sun jima sosai wannan wurin har muka sadakar da bazasu tai ba sannan suka tafi.
A gajiye suka fito suka yanki titi kamar zasu fadi kowa cikin su ya gama galabaita,zubewa sukai bakin titin suna maida numfashi.
Xakiyya numfashinta sama sama yake daker tae fizgoshi,riko hannun fiya tayi daker take iya magana tace"fiy....ah.......kikira wani yazo ya taimakemu ina......buk...atar asibiti ga wannan mcard din ta ciroshi cikin breziyarta,ki adanashi....ko..namut..u foyah ki idasa wannan aikin........sumewa tayi nan wajen.
Saida fiyah ta saki kara tana girgiza zakiyyar amman bata motsi,agigice take sosai.
tafara tarar mota neman taimako amman babu mai tsaywa duba da yadda taimako yanzu yayi wuya,durkushewa tayi gaban zakiyyar tana kuka,kamar anzungureta tatuna da malik ta rarumo wayarta hannunta yana karkarwa ta shiga kiransa.
Harta tsinke baidauka ba ta sake kira karo na biyu,nan ma haka jitake kamar zata haukace"kadauki waya yaya malik ina bumatar taimakonka"
Runtse ido tai tana sake kira cikin sadakarwa saikuma taji andaga,bata bari yayi magana ba tace cikin kuka"yaya malik don Allah kataimakeni kazo ka taimake mu........kuka yaci karfinta ta kasa cigaba da maganar.
Jitai ance"kina iya"
Bata cikin natsuwar da zata iya tantance muryar waye amman tasan bata malik bace.
Fadar inda suke tayi cikin dimaucewa da gigita,saidai shican ya kashe wayar.
Kuka ta tisa zakiyya gaba tanayi idan zakiyya ta muti ya zatayi da rayuwarta.
Babu jimawa taga mota tsaye inda suke saidai wanda yafito daga motar ne yasa hankalinta dawo jikinta,bakinta ne taji yafurta.
*yah Abdoulnasser* kallon zakiyya tayi dake kwance kamar gawa sannan ta dago ta kallai,shikanshi wadda ke kwance kasan kusada fiyah ganin ta ya gigitashi,idonsa dan danan yayi jajawur yasha mur matuka bai sake dago kai ya kalli fiyar ba yayi kwana zaibar wajen batare da yunkurin yin wani abuba.
Aguje tatashi ta bishi tana hawaye ganin dagaske koma wa zaiyyi. idan yatai yabarsu anan komi zai iya faruwa dasu wata kila zakiyya tana iya rasa ranta.
Jiyai kurin ta rike hannunsa cikin rawar murya tace"karkayi haka plsss narokeka karka tai karka tai kabrmu a,inhar katai zamu iya rasa ranta bata camcanci haka ba kome katuna akanta baidace kabarmu ahaka ba......narokeka plsss yah Abdoul plssss.........ingijeni yayi na fadi agefe cikin fushi da na jima banganshi cikin sa ba yace"ina ruwana da mutuwarta ko rayuwarta,baishafan ba data mutu kotai rai karkisake zuwa inda nake balle kimun mganar wanna abar."
Ya wuce kamar kububuwa yabar ni awajen.....zaman dirshen nayi ina kuka nashiga ukuna ni safiyya yau naga bala,i dagaske Alfah tafiya yayi wace irin xuciyace dashi haka,ya zanyi da zakiyya ni kau yau.nafi karfin minty talatin wajen babu wanda ya kulani kowa yazo wucewar sa yake.........kamar wasa saiga motarsa tasake dawowa wajen,inda muke lokacin naci kuka nakoshi har muryata bata fita,koda naga kiran anty kasa dauka nai namata sakon cewa naje gida amman zan dawo yanzu.
Ko kallonsa banba banza nai dashi yana zuwa ya sungumeta yaje yasata baya yarufe,yayi tsaye baimun magama ba alamun intaho mutai,yadda ya bata mun rai bana jin ko kallonsa zan sake yi ahalin yanzu,tashi nai daga durkushin danake na kakkabe jikona na share fuskata na nufi tiri kurin,inajin xuciyata na zafi kamar garwashi.
Madam bata lokaci kafin taxi ta tsaya nashiga nabarsa nan shida zakiyyar nasan dole zaikula da ita ko dawowar dayayi nasan xuciyarsa ce taji bazata iya barinta ta rasa rayuwarta ba bayan yana da damar kaita asibiti,can kukarata kaida ita wani abu yazo mun wuya ya tomare kuka nakeson inyi inba haka ba azai wuce ba,kukan naitayi wanda har cikin raina nakejinsa har mai taxin yana ban hkr ,ban ma sauraresa ba saida nayi na koshi sannan ya mikomun ruwa na wanke fuskata dashi bayan nafito daga taxin.na sallamai na shiga gida.
Anty na ganina tace"kina lafiya fiyah?kuka kikai me akai maki"
Wani kukan ya haomun nace"Anty yanzu don Allah sun kyauta mun kenan,inazowa na biyu amman suka ban na biyar wannan karon,har hakan yaja baza asani cikin musabaqa ba,wlh Allah ya isana"
Dariya Antyn tayi tace"lallai safiyya har yau dai da sauranki,to waye yace maki kullum ake kwana bisa gado" ganin haka karyata ta ansu yasa nashige daki naci gaba da kukana.

Don't share it plssss and plss
[9/17, 3:39 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........32

Tunda na shiga daki kuka naitayi ni bazan ce ga abunda nake ma kuka ba,kawai dai nabarwa raina cewar yadda ya banzatar dani awajen bacin yaga irin halin da muke ciki,shine dayaga cewar masoyiyarsa zata zata rasa rayuwarta yadawo............saida naji kaina yafara ciwo sannan na hakura,m.card din da zakiyya tabani na ciro daga cikin aljuhun doguwar rigata na kura mashi ido,zanso jin abunda yake ciki amman ba yanzu ba sai tare da yaya malik,cikin jikkata naje nayi mashi kyakkywar ajiya sanan ta nufi bayi,don jikinta duk tsami yake mata.
Gyare jikinta tayi tsaf sai kamshi take fitowa tayi don cin Abinci yunwa takeji.
Sallamar muhseen ce tasaka ta juya shikadai ne daga bayansa kuma saiga uncle ya shigo shima,hira suke ta kwallo sai muhawara suke shi uncle dan arsenal ne shikuma muhseen dan Manchester united ne,sai gardama suke.
Anty ta fito tana cewa"aifa kun fara halinku ko,wai meyasa baku gama duk gardame gardamen ku acan waje sai dole kunshigo mun gida da hayaniya."
Fiyah dai na kan dining tana tsakurar tuwon shinkafa da miyar agushi taji zallar naman kaza.
Uncle bai kula Antyn ba sai muhseen ne yake bata ansa suna ta fadansu itada shi dasuka zaba,
"Safiyya babu magana"
Yake take tace"uncle naji aikuna ta magana ne sannuku."
Muhseen najin ankira sunan ta yai saurin juyawa yana washe baki,cike da jin dadin ganinta barin Antyn yayi yana nufar wajen da fiyah take.
"Aa ah ashe kina nan nazo da yamma bakinan"
Ta na Kai cup din ruwa bakin ta tace cikin sanyin murya"ina wuni yaya muhseen"
Murmushi yayi yana shafa kanshi yace"lafiya lau ya kike,nayi kewarki yau zuwana biyu bana samun ki"
Idan dayasan

Please Login or Register in order to submit comment