Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bangare na zuciyarsa yana tuno masa da wani sashe daya riga ya binne tun shekara shidda baya,saiyakejin kamar feelings na kauna da shauki na soyayya atare dashi,bawai yana yiwa wataba aa yanajinsa atare dashi yana bukatar wadda zai sharing wannan feelings din da ita amman wacece?kenan har xuciyarsa tayi sanyin da zai iya kallon mace da sunan kauna?Aa impossible nayi bikin binne soyayya shekara shidda baya,yana ma mace kallon namiji rabonda dayaji yana son mace kusadashi ko yaji yana bukatar kasancewarta garesa tun wancen lokacin,wanda yakejin kansa koda yaushe cikin shauki da mararin zamanta cikin rayuwarsa.
Yau lamarin ya canza masa,kasancewarta gefensa,kukanta sautin muryarta kalamanta sun ja hankalinsa ainun wajen juyoda lamarinsa baya,wani shauki daya danne tsawon lokaci yake niyyar tasowa,duk da yadda tariga ta bata ransa ta cusa haushinta hakan bai hana wannan abun tasiri akansa ba.
Mirginawa yayi yana runtse idonsa yanajin wani yanayi kamar zaiyyi kuka,amman ba kukan bane yanajin kamar yayi dariya amma ba dariyar bace,yanajin dukan jikinsa yana macewa,sannan tsikar jikinsa tana tashi salon numfashinsa yana canzawa.
Filo ya rarumo ya makalkaleshi yana jan numfashi,ya tattare jikinsa ya dunkulesa waje guda,jujjuya kansa yake yana jiyo wasu kalamai da suka shude suna mashi ansa kuwwa cikin kunne,baiyyi auneba yaji hawayensa suna silalowa suna bin kuncinsa idonsa arufe amman hawayen basu fasa fitanba.
Bakinsa ne yake kerma kamar zaifurta wani abu,amman kirjinsa yayi masa nauyi rubdaciki ya koma yana murtsike murtsike kamar mai ciwon ciki,saida bakinsa ya furta wannan suna ya samu sukuni.

*"ZAKIYYAH!!!"*

wani gauron numfashi ya sauke yana tashi zaune kansa yasa cikin kafafunsa yana zubar da kwallah.
Tun bayan barinsa gida yacireta aransa,daidai da rana guda baiyi tunaninta ba bai tuno komi nata ba,baya kallon mace balle ta tuna mashi da ita,shiyasa ya yiwa mata wata irin tsana.wadda har yau yakejin baidaina tsanar suba,don sune silar jefa rayuwarsa cikin garari da damuwa.
Amman yau anwayi gari shine yake magana da wata,yake hada jikinsa da wata yake daukar wata cikin motarsa.tsawon zamansa hakan bata taba faruwaba,ko dacan zakiyya kurin yake dauka duk da tarin bataliyar matan dake binsa.kusancinsa da yarinyar nan yau yasaka yaji komi na zakiyya yana dawo mashi..........cikin muryar kuka yace"why zakiya,why why me???."
Wannan dare dai Abdoul haka yagansa baisamu sukuni ba saida ya karanta qur ani,sannan yasamu salama har bacci ya daukeshi.

Itako fiyah kiri da muzu baccin yace baisan haka ba,tasha kukanta ta gode waAllah.don gabaki daya tarasa inda natsuwarta ta nufa,duk irin Abunda Abdoul yayi mata yau maimakon taji haushinsa kamar yadda ta dawo da abun,amman abun sai yagagareta data hangoshi sanda yake sunkuyowa yana bude mata kofa zataji gabaki daya hankalinta ya tashi,har lokacin tanajin gashinsa ga fuskarta..........mulmula kurin take agefe guda ga hirarta da zakiyya da irin alkawarin data daukar mata cewar zata mallaka mata Abdoul dinta zata dawo mata da soyayyarta.to taya?ta tanbayi kanta wata xuciyar tace ta yadda kika ansa mata ta haka zaki yi kihadasu ki sasanta su.
Ga haushin Anty ga na Alfah amman jitake na Alfah baikai na Anty girma ba,duk da kalamansa sun take na antyn girma da munu aman ta kasa ganin bakinsu ayanxu,sabanin lokacin dayake gaya mata su.
Tun daren fiyah ta gama hada akwatinta,don data gama abunda xatai saidai ta nemeta ta rasa shikuma wancen muhseen din ya gaji yabarta,inma don yabata wayace aiba rokonsa tayi ba bakuma zata bayar ba,kwata kwata baya cikin shirginta.
Zuciyarta tace mata"to saiwa yake cikin shirginki?badai Abdoul din dakika gama yiwa wata alkawarin hadasu ba?"
"Mtss mezan da dangiya nikau safiyyah,ai inajin ko maza sukenan shida muhseen bana son su bana aurensu gara na mutu ahaka."
Still xuciyarta tace"inkince Abdoul dan giya ne shikuma muhseen mezai hana kisoshi?"
Dirkowa tai daga kan gadon tana cewa"ohh ina ruwanki ne kirabu dani don Allah."
(🤣🤣🤣)
Zaman dirshen tayi kasa tana tagumi.
Tunani ta shiga yi daga sanda ya fito daga mota dawowar da yayi daga office,shigarsa tayi kyau rubutun rigarsa ya dauki hankalinta *ME&YOU* lumshe ido tayi tana silalewa kasa ta kwanta bia tayils din dakin.
"Nida kai ko,uhmmm saidai idan kaida zakiyya"
Idonta alumshe tana tuna sanda yake tsane mata hawayenta,kamshin turatensa mai shegen shiga kwalwa ya kasa barin hancinta.komi nashi mai tsadane.

_kuma duk dan iskan kwartonki daya biyoki nan gidan saina guntile mashi kafa alqur,an_

Ta tuna maganarsa sanda tace bazata bisa amotar sa ba,
"Wanan Kalmar ta kwartanci tana mata ciwo,wai shi baya ganewa ne meyasa zaimun wannan zargin,wlh Abdoul niba yar iska bace ban shigo rayuwarka don komiba saidon ina tausayinka,saidan na taimakeka ka koma cikin ahalinka,amman meyasa ka kasa fahimta. kenan da haka zaka saka mun.koda yake bana bukatar sakayyarka ladata tana wajen Allah,kuma duk abunda kayimun na yafe maka Allah yasani bana gaya maka wadansu maganganun don karan kaina kaine kakeja,kuma duk don in nuna maka cewar abunda kake babu kyau ba halin kirki bane shan kayan maye,addinin mu yayi hani,Haramunne akwai zunubi mai yawa ina maka fatan shiriya Allah yasa wahalata bata tashi abanza ba."
Afili duk take fadar haka kwallah na mata zarya afuska,ta rasa dalilin zubarsu.abunda tasani kawai shine tana tausaya mashi hakan rashin uwa da rashin uba da yan uwa dayake ciki,kowa daya sansa baya mashi kallon mutumen kirki.
Shafa kuncinta tayi inda ya mareta dazun cikin mota,
Lumshe idonta tayi amman kwata kwata bataji zafin marin ba,cigaba tayi da shafa wajen tana jin haushinsa yana bajewa cikin xuciyarta tausayinsa yana maye gurbin haushin nasa.duk ta duka takare tunda nayi alkarin bazan sake xuwa gidanku ba zangani idan inda rana kokuma banda ita.
Shin rashin ganina zai dameka ko bazai dameka ba tsaki taja jin wata xuciyar tana cewa "ke awa zai damu don bakizo bakenan kin saka wani abu aranki game dashi"
"Ohhhh niban saka komi cikin raina ba Abdoul na zakiyya ne nace maki ko"
(😄😄fiyah ta zare aradu)
Haka wannan daren ya kasance wa safiyyah har asuba,kuma kokadan ta nemi baccin tarasa tashi tayi taje tayi sallah sannan ta dora ma maijegon sanwar ruwan wanka,sannan ta koma daki tana karatun kur ani.
Sanda gari zaifara haske tashiga ta hada break miyar kwaice da kabeji tayi musu da ruwan tea mai na,a na,a da lemon grass sai citta da kanun fari kamshi kurin yake,ta soya dankalin turawa sannan ta hauda ferfesun naman kaza bata so aikin ya kaita ga takwas ba,shaf shaf ta yi nata break din tayi shara da mopping bata tsaya wanke wanke ba ta dauki akwatinta tayi get.
Karo sukai da muhseen ya shigo gidan,
Tsaki taja cikin ranta tana mitar "ko ubanme yazo yi tunda uwar safiya"
"Ah fiyah ina zuwa haka tun da farar safiya."
Yake tayi mashi tana gaidashi.
"Gida zanje na kai kayana anjima kadan zan dawo."
"Oky to muje na kaiki daman break nazo nayi wajenki tunda kuma baki nan shikenan"
Don dole take murmushin tace"ah wlh kashiga kayi ainariga na gama hadawa,bazama zanyi ba gidan"
Ansar akwatin yayi yana yin gaba yace"no muje kawai ai ganinki ma yasaka naji yunwar ta tafi idan na kaiki saina dawo nayi."
Ya zatayi da shi da alama wanan naci garai kamar magan disu.
Shiga tayi gaban motar tana yaba tsarinta da kyanta,gashi sai kamshi take.
Zagayowa yayi yashiga yatada suka dauki hanya.
Duk sai tajita atakure shikau jiyake yau kamar amashi bushara gashi ga safiyyan sa,cikin janta da fira yace"ko sannu da zuwa bakiyi mun ba safiyyah."
Saitaji bata kyauta ba cikin kunya tace"sorry pls andawo lafiya"
Murmushi yayi yace"no karki damu aike bakya laifi safiyyah,nayi hkrin kuma nadawo lafiya fatan kuma na sameki lafiya."
Ya ta iya dashi dole ta sake tana ansa mashi hirar tashi."komi lafiya yaya muhseen"
Cikin kwarewa yake jan motar yana sarrafa sikiyarin yace"Amman sanda na tafi Anty bata baki sakona ba"
Wayar hannunta ta kalla tace"wannan?"
Girgiza kai yayi yace"no ba wannan ba,i mean bata yi maki wata magana akaina ba"
Sai yanzu ta gane inda ya nufa,
Girgiza kai tayi tace"Aa gaskiya kilan ta manta"
"Kokuma kece kika manta ba,don munyi magana da ita sosai har idan muyi waya wani lokaci tace ashe muna waya dake ban gaya mata ba,to kasancewar nasan kingaya mata ne don kitsira daga masifarta yasa nima nake kokarin kareki,sai kawai nace mata eh munayi sosai ma.Aman tambayata anan safiyya itace meyasa kika mata karya."
Shiru tayi tana jin kunyarsa na kamata,hakika muhseen yana da kirki kuma duk wasu qualities da ake bukata ga namiji ya nadasu kawai dai kowa da nashi ra,ayin itadai bai mata ba batajin zatayi soyayya dashi balle aure.
"Kayi hkr"
Abunda tace dashi kenan.
"Ba maganar nayi hr bane kinsan me?nifa In my life duk abunda zanyi direct nake yinsa,kuma duk abunda yake raina ina fadarsa don idan nafadan ina samun saukin xuciya,don haka babu boye boye tsakanina dake inasonki kema kuma kinsan ina sonki kawai dai kilan ban maki ba shiyasa kiketa yimun hanya hanya,kin ban wuya.watana uku abuja ina godalan inganki muhadu in sabunta soyayyata amman kikakiya safiyya,aman saboda ina kaunarki bazan iya fushi dake ba gani na sake dawowa,don haka bazan koma ba sai kin gaya mun abunda kike nufi dani."
Gabanta yafadi gaskiya bazata iya kallon cikin idonsa tace masa bata sonsa ba,kuma bazata kwari kantaba tace tana sonsa bayan kuma ba haka abun yake ba.
Na bani yazanyi da shi.
"Karki damu kanki u have enough of time da zakiyi tunani don zan jima ban koma ba,amman kafin kigama nazarin nawa zan iya zuwa wajen baba don neman izinin zuwa zance?"
Wayyo tashin hankali ba,asaka mashi rana,muddin maganar taje ga baba shikenan bata da miji saishi,don inbazata manta ba haka akai da uncle yahya da Anty.

YAZANYI NI SAFIYYAH?

(TO FOYAH NA NEMAN MAFITA ALFAH FANS KU WARWARE MATA YADDA ZATAI,KO YAN ZAUREN MRS BB)

MRS BB CE
MOM MUHSEEN.
[9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........28

Tsare ta yayi da ido bayan da sukai parking kofar gidansu,sadda kai tayi tace"kaban lokaci zan yi tunani"
Relax yayi jikin kujerar yana shafa kansa yace"yanzu neman izinin zancen ma fiyah saikice sai kinyi tunani,gaskiya zaki wahalar da zuciyata,kenan bazan zo zance ba bacin ko awaya bama gaisawa."
"Aa yaya muhseen indan wannan zamu ringa waya amman kabar maganar zuwa wajen baba yanzu saina shirya don Allah."
Ajiyar heart yayi yac"shikenan na hkr amman gaskiya idan naji bazan iya jurewa ba saidai kiji sallama nazo zance."
Ansar no din ta yayi yana zuwa ya bude mata sannan yafiddo mata kayanta daga cikin but,godiya tayi masa ta wuce cikin gidan kadan yahana ta banki baba dake tahowa zai fita.
"Ah baba yi hkr ina kwana"
"Safiyya kece tunda uwar safiya haka,yo ya akai naganki da kaya kamar wacce tayo yaji."
Sadda kai tayi tana jin kwallah na zubo mata,ansar mata akwatin yayi yana cewa sushiga gida tau.
Shiga sukai mama dake shara cikin gidan kaji ta fito tana ajiye tsintsiyar,biyosu tayi cikin gidan yesmin na ganinta ta rogo ta rungumeta.
"Nayi kewark Addata,ya su Antyn ya kuma babyn."
Daker take ansawa yesmin ansoshinta baba yace"yanzu mukai karo zaure naganta da akwati natambaya kuma ta fara kuka,shine nace tashigo ciki tayi mana bayani."
Mama ta iso tana zama gefen fiyah dake matsar kwalla,ita masifar da Anty tayi mata ce tasaka tayo yajin,don baiyyuwa tana mata bauta amman bata iya mata uziri.
"Safiyya dake nake magana nace meya faru keda jamilar?"
Kuka ta saka tana gaya mata abunda yafaru jiya"mama Anty kullum bata canzawa da yaya muhseen bai saurin tareta ba duka na zatai fa,yanzu mama ban wuce duka wajen anty ba ai nai zaton zata tambayeni dalilin dadewata."
Baba ya shafa kanta yana lallashi yace"jamila bata kyauta ba kuma nima gara dakika dawo bazan yarda ana cutar mun da uwata ba,yesmin kaimun akwatinta daki ko sunan ba kizuwa."
Mama tace"Ba ayin haka babansu,komi jamila tayi wa safiyya ai kanwarta ce kuma yanzu saita baro gidan sunan tataho nan sabida Allah,idan banda yaya balaraba da yaranta wagareni dazan tura ya kama mata inaba dan safiyyar,komi tayi maki aibakin baro ta kitaho nan ba,kayi hkr anjima inta huta saita koma,kuma zanyiwa jamilar fada ita daman matsalarta kenan shegiyar xuciya da rashin uziri,haka dai yahaya yake fama nasani."
Kuka na saka ina murje murjen kafafu nace"nifa mama kiyi hkr,sokike inje tayita hantarata wlh Anty ta kara lalacewa da masifa duk hkr na yau ta kureni alqur an."
Murmushi baba yayi shida yesmin mama tace"haba Ansafiyyan mama kiyi hkr yanzu ma zan kirata nayi mata fada,aibakin barota ba kiyi hkr anagama hidimar ni daso nai ma kizauna har tagama wanka."
Kukana nake ina murzar ido yesmin sai dariya take mun.
Kafinma mama ta dauko wayar kira yashigo tace"kingani ma itace take kira."
"Wlh mama idan bata bani hkr ba bazan koma ba"
Bata kulata ba ta dauki wayar baba yace"zata baki uwata kwantar da hankalinki."
"Yanzu jamila sakayyar da zakiyi mun kenan?na turo diyata don ta ragemaki wahala shine kika saka hannunki mai albarka zaki mareta,bacin ba dagangan tayi ba"
Cikin rudewa jamilar tace"don girman Allah mama kiyi hkr wlh banyi da niyarr zalintarta ba hankalina ne yatashi har bayan magruba babu fiyah,shiyasa amman kiyi hkr bazan sake ba na tashi banganta ba naje har dakinta inlallasheta don nasan fushi tayi na iske bata nan,sai muhseen yake gaya mun shine ya kawota gida,kiban ita inbata hkr mama"
Dayake hands free wayar take kuma mama duk dan fiyah taji yasa tasaka,
Murmushi tayi jin za,a bata hkr baba dai daroya yayi yana cewa"uwata ko yar rigima kin iya rikici wlh,nidai natafi Saina dawo sukai mashi Allah ya kiyaye mama ta mikama fiyah wayar.
"Hello Safiyya,kina jina."
Cikin sunburar baki tace"eh Inajin"
"Haba yar kanwata kiyi hkr kinjiko,wlh rudewa ce ta sani haka tsoro naji kar wani abu yasameki,amman insha Allah bazan sake ba don Allah kidawo kingani ma ga inna balaraba nan duk sunzo suna tambayarki harda hasana da umaima"
Murmushi tayi tace"to zan dawo ya sunan princess dina"
Dariya jamilar tayi tace"uncle dinku yace bata cancanta da kowane suna ba sainaki safiyyah,don haka ina maki murna kinyi takwara."
Wani ihu ta buga tama tashi tana taka rawa "yeeee wlh naji dadi ngd Anty ganin zuwa yanzu zandawo wlh na huce wanan albishir ya wanke xuciyata mama kinji princess taci sunana yesmin kinjiko."
Kashe wayar jamila tayi tana dariya,rigimar safiyya sai ita.
Nan suka shiga murnan sunan yesmin tace"nikuma next sai asaka namu nida mamana(kasancewar sunan su guda hurairah)
Dariya mama keyi tana jin dadin yadda yaran nata suke son juna suke kuma yiwa junansu uxiri tare da fahimtar juna,Allah ne yabata don kam yaranta babu mai halin banza kullum takai goshinta addua take yasa ta aurar dasu fiyah lafiya.
Yesmin tace "ga yaya dalha can zai fita bari yatai dani idan natsaya jiranki Adda zan bata lokaci zanje na gano sabuwar Addata."
Dariya fiyah tayi tace"saina taho"tasige aki tana hayewa kan gdonu tayi missing din sa kwana biyu.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Tunda garin Allah yawaye bai iya fitowa daga dakin saba tunda yadawo sallar asuba,yau saboda farin cikin ganin Alfah masallaci malik har da kwallarsa,yana godewa ubangijinsa daya taimakesu har Alfah yafara daidaita,yasan ko ahaka sunci riba kuma suna godewa Allah yana kuma godewa fiyah.
Abdoul nacan yana mulmula akan gado yarasa meke mashi dadi,furucinta yake tunowa najiya.

_aidan kana ganina gidanka shiyasa kake cin zalina ko,to nida sake zuwa nan gidan har abadan abada_
Cusa hannunsa yayi cikin sumarsa yana ya mutsata huci ya furzar,baccinsa da yarasa jiya yakeson maidawa amman tazo tayi mashi tsaue bakin xuciya taki fita ita kuma taki shiga,
"Meyasa zakibar xuwa kiyi hkr bazan sake cutar kiba kidawo ga wanda kike xuwa gidan donshi nasan shima bazaiji dadiba laifin zai dora bisa kaina"
Saukowa yayi yana layi kamar yasha mutuniyar sa, ya shiga bayinsa ya sakarwa kanshi ruwa mai sanyi sosai.
Saida yaji sanyin ruwan har cikin ransa sannan ya kashe shower ya hada ruwan dumi ya shiga,lum yayi yana lumshe idonsa sai yatuna da wani lokaci sanda yake tashen barje soyayyarsa shida zakoyya.

_qalbina yanzun nafito wanka banga kiranka ba wlh sorry_

_murmushi yayi yace"karki damu nour dina,fatan dai kin wanku sosai"_

_dariya tayi tace"uhm qalbi mekake nufi?nifa tun ina yar shekara goma umma bata sake mun wankaba,kuma wlh ina fidda kaina sosai don baka ga yadda ruwa yake darewa ba shikanshi soap din saida yace kikyaleni haka zakiyya_

_dariya yayi sosai yace mata "gaskiyane nayarda ta tunda har soap dakanshi yayi magana,amman kinsan watarana dakaina an sabeki na nadoki cikin towel"_

_"qalbi kunya nakeji wlh kadaina_

Numfashi yasauke yana sake lumewa cikin ruwan,zafin zakiyya da yakeji bai hana jin wani tsohon mikin kaunarta ya taso mashiba.
"Kin cutar da rayuwata kiyyah,kin jefa rayuwata cikin qangin da bazan iya taba mancewa ba,bantaba tunanin zan iya dawowa irin haka ba,amman rana guda lokaci guda tashigo rayuwata shin mekike tunani zakiyya?inajin zafinki fiye da yadda wuta zata gona hannuna,haka inajin tausayin wannan yarinyar fiye da yadda nake jin tausayin kaina,ina son yimata sakayya akan sadauar da rayuwarta da lokacinta da jikinta akaina,amman banson wane irin sakayya zan mata ba..........nocking din kofar sa da ake ya kaste masa zantukan dayake yi afili cikin sassanyar lafazi da kwantar da amon muryarsa,inkaji zakai tunanin cewa yanantare da wani ko wata.
Wanke jikinsa yayi yafito yana daura towel ya fito.
"Lafiyarka Abdoul najika shiru baka fito ba gashi ankirani kanada baki office"...................


*fatan zakuyi mun uxiri,wlh saboda yadda naga kunayin book din nan yasa na takure kaina nayi maku wannan kuyi manage dashi zuwa gobe idan Allah yasa munkai da rai da lfy,ina alfahari daku 100% ngd da adduoin ku gareni*

Mrs bb ce
Mom muhseen
[9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........29

Kallonsa yayi na yan seconds ya dauke kai ya cigaba da tsane gashin kanshi dana fuskarshi,gaban mirrow din dakin nasa yayi burki yana dauko hand drayer ya jona yana busar da gashinsa,kamar ba mutun adakin bai niyyar cewa komi ba saida ya gama,malik ya zuba mashi ido yana kallonsa kafin murmushi ya kubce mashi.
"Yau kuma azumin magana aka tashi dashi?"
Mai yake shafawa ya kallai sannan yace cikin lallausar muryar shi "saidai idan azumin dole kake niyar tirsasani,tunda ko ruwa baka ban ba da safen nan,sai yanxu kake shigomun kana mun wani zance dabam."
Ajiyar xuciya malik yaja yana zama saman gadonsa yace"sorry sir,me kake bukata to"
Uffan ba ce mashi ba yaciga ba da abunda yake,kamar maijin tsoron fatar tashi haka yake shafa man.
Fita malik yayi yaje yadauko mashi break din daya ajiye masa a falo tun goma na safe.
Table yaja ya ajiye masa yana mashi nuni da break din.
"Gashinan ranka yadade"
Dan murmushi yayi kadan yace "tare dakai"
Kaya ya fiddo suit farar shet da farar coat sai black trozer wanke su yayi da turare sannan ya hau sakawa,yana satar kalon malik zuwa can yace masa.
"Karkaga wanan yarinyar bata zoba ta riga tace ba zata sake dawowa ba"
Cike da madaukakin mamaki malik yace"wani abun ka sake mata ahanya ko?"
Kafadarsa yadaga yace"daman nayi zaton haka zakace,toni ban mata uwar komi ba sarkin zargi"
Murmushi malik yayi yace"saika shirya anjima muje ban hkr"
Zaro kyawawan idanunsa yayi yana kallon malik yace"bcos?"
Murmushi malik yayi yace"bcos of u,u Abdul kaine kaja har tayi wannan furucin,safiyyah yarinyace mai hakuri da kauda kai,yadda kake tunaninta ba haka take ba,she is innocent girl kaine ka kure hkr rinta shiyasa tunjiyan zuwa yau banga kiranta ba,nasan arina don haka kashirya anjima tonight zamuje dakai har gidan antynta."
Dariya yaji Alfah nayi yana shan black tea har dariyar taso tea din ya zubar mashi ga kaya,ajiyewa yayi yana kallonsa kafin ya girgiza kai yace"u mean zan raka ka zance kome kake nufi,ina ruwana da zuwa bata hkr ainine ma zata dawo ba hkr saboda nitayiwa rashin kunya,imagine ta kallan tana furta mun Allah ya isa and nida Allah for what reason,inba sokake kasaka na zane ta cikin gidansu ba ajiye wannan maganar,suwaye bakin dake jirana office"
"Shikenan na ajiye maganar amman bada na barta ba,i don't know KO suwaye sai idan munje inson ma inje nagaida daddy kozaka"
Hararasa yayi yana cigaba da break dinsa.

Tare suka fita amman kowa cikin motarsa,malik ya wuce store don duba halin da yake ciki sanan suyi lisafi afidda albashin ma aikata na wannan watan.
Alfah kuma ya wuce company don haduwa da bakin nasa.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Suna yayi kyau mutane da dama su xo cikinsu kau harda momin feea takanas tataso daga katsina tazo sunan,don suna yi sosai da mama cikin estate din duka mutum biyu sukaje ma mama suna gidan Jamila.
Fiyah kau anacan ana hidima da baki bakinta har kunne tayi takwara,suna tare da hasana sa,ata ce baifi one year dake tsakaninta da fiyah ba,umaimaice suke d same years.
Dakinta suka sauka sunata hirar yaushe gamo,sai idan baki sun zo sufita su zuba masu abinci don ma ga inna balaraba da wata abokiyar wasansu da ta iso daga can garin su baba dutsi.inda mamanshi mai sunan fiyah take xaune.
Suna yayi kyau sosai anraba jakunkuna da hoton little safiyya,sunan da takwarar tata ta zaba mata kenan.
Zuwa magaruba kowa ya wuce gida sai su inna dasu hasana daketa faman gyaram gida,duk yinin yau fiyah zuciyarta bata da sukuni jitake matakin data dauka na daina zuwa gidan kamar bazata iya aikatashi ba,daga jiya zuwa yau wani irin yanayi take tsintar xuciyarta aciki,amman tayi iyakar kokarinta wajen dannewa,don ma gwamace wajen boye damuwa.
Wayarta duk yau nata kunna ta ba,balle ma malik ya kirata yayi mata dadin baki,saida gidan yazama need sanan su inna suka tafi,amman anbar hasana don washe gari su kama ayi soye.


💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Malik bayan yadawo daga wajen dady yayi mashi bayanin da zakiyya tayiwa fiyah,yace komi kenan in sungama tattaumawar idan da bukayar yashigo ciki sai yazo ya gaya mashi.
Office ya wuce wajen Abdoul don ya yi alqawarin koyanaso kobaiso sai sunje bikon fiyah,don yakira wayarta yafi sau goma amman anar gudace wayar kashe take.
Gaidashi ake tayi tunda yashiga company har ya samu isa office din Alfah,wanda saika rantse wata duniyace daban saboda yadda yatsaru iyakar tsaruwa.
Aiki yake kan compute ga bako kuma suna magana dashi,ciki ya wuce can cikin kiryar office din don har wani madaidaicin gado ke akwai.
Bayan ya sallame mutumen ya biyosa har cikin dakin ya samai yayi shame shame yana shan iskar AC.
"Ince dai lfy?"
Shan mur malik yayi ya cakude fuskarsa yace"zuwa nai na daukeka idan anyi sallar isha,i zamuje bikon safiyyah"
Tsaki yaja ya na juyawa zaifice b'igit malik yayi ya sha gabansa babu walwala afuskarsa alamun babu wasa yace"Alfah kabar wannan abun,dagaske nake saimunje dakai aikaine musabbabin komi yarinya tana maka abun alkairi........shiru yayi baison tona abun dasukeyi.
Kallonsa yayi yana shafa sumarsa zuwa kasumbarsa yace"metayi mani na alkairin?zagin nawa kokuwa rashin kunyar,aa kila kirana datake dangiya shine abun alkairin,kaga ABDOUL-MALIK karka janyo muyi rigimar da muka jima bamuyi ba nace bazanje ba final"
Ganin shan mur dinsa baiyyi nasara ba yasa ya saki fuskarsa don yatabbata idan ya matsanta zai rikice mashi ne.
"Kaga sorry Alfah,kayi hkr ka rakani to ba dole ma sai kunyi magana ba nizaka raka don Allah."
Cure hannunsa yayi daga kafadarsa ya fice yana tattara abunda zai dauka malik yafito ya daukar mashi jikkar system dinsa,yana cewa"muje yallabai ai kai hukumane saida lallashi"
Bashiri dariya ta kubce mashi ya jefesa da biron hannunsa,sukai dariya sannan suka fito sakatarensa ya rufe office din.
A mota guda sukatai Abdoul ybar tashi nan company,malik babu abunda yake mashi dadi irin canzawar Alfah lokaci guda,duk da yasan bazai taba dawowa kamar wancen lokacin ba,amman kaso sittin daga cikin halayensa sundawo saidai saurin fushin da ya zame masa jiki yanzu wanda ya hade da zafin xuciyarsa,shima nan gaba idan komi ya daidaita yana saka ran fiyah zata gyarasa,inhar Allah yasa suka daidaita kansu.
Shiyake ta mashi hidima tunda suka dawo tunda ga kan ruwan wanka tea dayake sha idan ya fito,kayan sakawa daddare jansa da hira yana sashi ariya baishirya ba.
Wasu riga da wando ne ya fiddo masu masifar kyau,don tunda yadawo daga Australia bai saka suba kuma suna daga cikin sabbin kayan sa daya dawo dasu.
Wandon ruwan kasa brown amman light,sai rigar coffee brown mai hannun links,ya feshesu da turare yana murmushi,tabbas yasan fiyah ta ganshi yau duk kauda kanta saita rude,don ba yabon kai ba abokinsa karshene wajen kyau da daukar wanka.
"Wai saikace wanda zaije zance?"
Dariya malik yayi yace aransa kacanko daidai amman afili sai yace"aa nidai zaka raka nayo bikon qanwata,nasan fushi tayi dani tunda har yanzu her phone is switch off."
"U hmm"
"Don Allah yallabai karkace bazaka rakani ba,nikadai ban iya zuwa,ban san gidan ba"
"Uh zanyi maka kwatance zaka gane"
"Ohhh rankayadade wlh nafison muje tare plsssss kaimun wannan alfarmar"
Kafada yada ga yace "is okay zanje"
Wata kara ya fasa yana daka tsalle murmushi Alfah yayi yana nunasa da hannu"u malik"
Fita yayi shima ya je yashirya suka fita sallar isha,i zanso kuga yadda kayan nan suka hau Alfah,kamshi kurin yake bugawa kamar wani sabon ango.
Bay

Please Login or Register in order to submit comment