Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........14

Wajen da ya sauketa wancen lokacin nan ya sake saukarta,bayan ta zauna yadan rusuna yace"hajiya me zakisha."
Murmushi tayi tana waigen nayanta tace"rufan asiri kaganni ko airport ni ban tab'a zuwa ba,amman karka damu kanka wlh bana son komi nidai kayi ka idasa mun infece kafin wannan boss din naka ya dawo."
Dariya yayi yana jan kujera ya zauna yace"kinga can gashi can cikin d'akin exercise yana ta faman G-ming kawai dai abunda zakiyi ya taimakeki fiyah shine jajircewa,da fitar sa tsoro acikin ranki koda kinajin tsoron karkibari ya fito kan fuskarki kisha mur kuma duk abunda ya fada maki kiyi kokarin maida mashi wadda ya gaya maki,koma fiye da haka ki fetsare idonki gabanshi,shine zaisa ya sassauta maki kuma hakan zai baki damar shiga jikinsa kuma duk abunda kika zomashi dashi zai yarda."
Murmushi tayi tace"uhmmm yah malik kenan nidai ina jinka kawai aman ina ni ina mayarwa da wancen gagaren magana."
Dariya yayi ya cigaba da sanar da ita cewa.
"Alh kwangila ne yace ma Abbi Alh muazzam zaman wannan yaron cikin iyalinka masiface babba,kamar yadda hajiya umma tace ka korai tokuwa hakan yafi dacewa,ka rabashi da kai ka ahalinka wannan shine mafita inba haka ba............cikin zafin rai da kunan zuciya Alfah ya shak'oshi iyakar karfinsa,ya ringa naushi ga fuska har hakorinsa ya fita,kuka yake yana cewa muryarsa duk ta dishe don kuka karya kake munafuki wlh baka isa ba kana gudun na fallasa.......kafin ya idasa abunda yakeson fada Mutanen wajen suka ringa janshi suna raba shi da Alh kwangila,daker aka rabasu inkinga yadda kirjinsa yake d'agawa saikin zata xuciyarsa fitowa zatai.Abbi ne ya iso wajen yana huci ya fizgoshi bai diresa ko inaba sai gaban mami wadda sai lokacin ta samu hawayen yin kuka,cikin kakkausar murya yace"zan fad'a gaban kowa kuma gabanki,daga rana mai kamar ta yau babuni babu Abdoulnasser na yafeshi daga cikin zuria ta,na barshi har abadan abada sanan wlh wlh wlh duk wanda na kama cikin yaran gidannan yana muamala dashi aboye ko azahiri wlh zaibisa,yadda na korai shima haka zaibisa.ba ga yara ba harke ushe muddin kika bibiyesa ko awaya ko zahiri daga ranar abakin aurenki,kidauka koda ban gani ba to ranar zakibar gidana..........yanzu ba sai anjima ba nakeson ka tattara komatsanka da wancen yaron da ka kwaso ka kawo mun agida,waya sani koshine ya koya maka kufitar mun agida yanzu,kuma karka bari ink'arayin arba da bakaken fuskokin ku,inba haka ba wlh sawa zanyi adaureku har tsawon rayuwarku........bazan anshe duk abunda ka samu daga jikina ba don wannan nayi makane domin Allah da wahalar da dakakemun........muryarsa tayi rauni sosai fiye da lokacin da ya fara magana.........bakayi mun Adalci ba Abdoulnasser ba ka kyauta ma rayuwata ba,duk cikin zuria ta babau wanda nakeso kamar ka,babu wanda ke kyautata mun kamarka,shine zaka yimun haka dole zaka ar jikina kuka Abi yake kamar yaro,kai idan mai hankaline zaka san cewar abun anfi karfinsa ne baida wata mafita........barin wajen yayi yana shashshekar kuka.ina daga can jikin bango ina nawa kukan,inajin inama ace mafarki nake ba gaske bane wannan wace irin bakar rana ce.umma kau tana ganin tafiyar abbi ita dasu haulat mezasuyi ba darinba,har gaban mami tazo tace to sai abi wani sarkin don yaudai tauraron gidan nan haskensa ya dishe har abadan abada mamman shine zai maye mana gurbinsa.
Mami tana durk'ushe gaban Abdoul tana kuka ita da ni'ima bata maida kai ga umma ba.
Cikin karfin hali da danne ciwon da yakeji ga xuciyarsa yace ma mami"mamina kuta shi kubar nan wajen wannan kukan da kuke bazai canza komi ba,kunfi kowa sanin waye Abbi baya magana daya don haka ni da ya fidda zan fita ba ka zan sake bari fuskata da tashi ta hadua sai in munje lahira sai Allah yayi mana hisabi."
Ta shi yayi yana yafitoni akan inzo muje mu hada kayan mu,
Alh kwangila da wani amininsa murmushi suke suna magana k'asa k'asa ba zan iya jiyo kome suke tattaunanwa ba dariya sukai suka fice daga gidan,yan jaridar suka rufa masu baya don da gani sune suka kirasu.
Har mun fara nisa da barin filin wajen saiga zakiya ta rugo da gudu ta rungumeshi ta baya,tana wani irin kuka kar ramta zai fita tana cewa"yah Naseer wlh banda yadd.........wata irin fizga yayo mata daga bayansa,yayi mata wani kalar rik'o kamar ya rik'e doki ko wani k'ato girgizata yayi iyakar karfinsa harsaida numfashinta ya kusan fita,kokarin kwatar ta nake ua daka man wata tsawa da tun da nazo duniya banji irinta ba,ban tab'a ganin Alfah cikin irin wsnnam condition din ba,cikin tsawa da hargagi yake mata magana still yana rik'e da shoulder dinta "uban me zaki gaya man,mekike dashi da zaki gaya man,ashe daman kaunar banza kike mun ashe daman soyayyar cin amana muke nida ke,ahada kai dake acimun mutunci a wulakanta ni wannan tozarcin ya isheki ko da saura,jijjigata yake yana sake cewa nace ya isheki ko da saura to bari kiji zakiya wlh nai nadamar amuncewa dake arayuwata,natsaneki zakiya na tsaneki ban kaunar sake ganin fuskarki gabana,kuma kin ban darasi kin nuna man halinku na mata ashe duk haka kuke wannan ma ya isheni kibarni da wannan jeki kibar nan wajen.
Yayi jifa da zakiya gefe saida kanta ya bugi wani tudu dandanan wajen ya fashe,yaja ni muka shiga tattara kayanmu muka bar gidan fiyah tunda ga wannan ranan har yau ban sake shiga maitama ba,bamu sake hada ido da wani daga cikin yan unguwar ba sai fah Alh kwangila da abun nan ya faru.ko mami bama waya da ita,saboda ranar da zamu taho ta kirani tana kuka kamar me duk ta tashi hankanlinta tana cewa kakula man da Abdoul malik ka kula man dashi,daga shi sai ni'imah nake dasu don Allah karka bari ya illata kanshi,Abdoul yana da zuciya xuciyarma kamar ta mahaukata muddin akaimashi abunda yafi karfin tunaninsa zai iya aikata komi akan shi,na rokeka karka barshi shikadai duk abunda zai maka don Allah malik karka barshi ya cutar da rayuwrsa,ta ban wsu iyayen kudi nikaina lokacin bansan adadinsu ba ina kuka tana kuka haka ma ni'ima tanayi muka baro gidan,lokacin daddy bai gari abun yafaru daga baya ya nememu yabamu hkr tare da cewa duk abunda muke so muzo mu samai.
Amman lokacin Alfah sai ya kwana uku bai gidan nan,yana can club wajen wasu abokansa tun suna secondary,wanda sukaita kokarin ganin sun jawoshi cikinsu amman abun ya gagara sai yanzu da ya idasa rikicewa dafari har wiwi yakesha.
yasha shisha duk wani abu da kikasan d'an maye yana sha Abdoul yasha abuguda ce baisha ba,itace sigari taba kenan.
Nasha bak'ar wuya kafin na iya samo kanshi yana zaman gida,sannan nafara yak'in ganin ya daina shan sauran kayan mayen amman har yau Allah baisa giya ta barsa ba,nasha wuyar Alfah koma ince ina cikin shanta.kinji waye Malik sannan kinji waye Abdoulnaseer Alfah.yanzu zan bar maki wuk'a da nama sai d'an abunda ba arasa ba da zan kama maki dashi"
Tana dafe dakai tasha hawayenta ta gode ma Allah.
Cikin sanyin murya tace"yah malik wlh labarin ku yaban tausayi,yatab'a man zuciya nama rasa sanin ta ina zan fara kama abun,don akwai abubuwan tambaya aciki da basu da iyaka,amman kaban lokaci inyi tunani sosai akwai bukatar inkulla kawancen dole da zakiya,inhar Allah baisa tayi aure yanzu ba."
Gyara zama yayi yace"zakiya nanan batai aure ba mun tab'a had'uuwa a store din Alfah tazo itada wasu kawayenta,taso muyi magana mai tsawo amman muna tare da alfah idan yasan intare da ita zamu samu matsala,tabbas hangen ki yayi daidai tunda bata sanki ba zaki iya bugar cikinta kisan gaskoyar komi kafin musan yanhar da zamu bayyana ta ga kowa.na jinjina karfin tunaninki wannan ma alamace ta kinda tsananin kokari makaramta."
Dariya tayi tana duba wayarta alamar kamar sak'o taga har hudu tayi,
"Yah malik inga zan wuce sai munyi waya kome kenam zamu tattauna."
Ta shi yayi shima yana taka mata suna hira da dariya afuskarsu,kamar daga sama suka ganshi gabansu fuskar nan banu alamun rahma akanta ko miskala zarratin........fiyah jitai kamar zata saki zawo cikin wando har saida cikinta yabada sautin kulululu........tunkarota yake yana daure da fuska bata yi kokarin matsawa ba amman fah cikin xuciyarta k'es za ace mata ta ranci na kare.
Ga wayar ta yah jalal nata faman kira babu halin dauka.

Fiyah anshigo komar Alfah koya dramer zata kasanceπŸ˜‚


Mrs bb ce
Mom muhseen.

09034722970

Karku manta sanyin idaniya Abin cikin ruhina return,yana nan bisa hanya akan farashi mai tahusa darin ki biyu kacal ta nisha dantar dake,labarin mai tafe da rikita zuciya da d'okantuwa zuwaga ainahin inda zamuje.labarin yana dauke da salo salo da zaisaka mai karatu nishad'i da kuma d'okin jin yadda Ayman da sanyin idaniyarsa zasu kasance.
Ku kasance da mom muhseen domin nishadantar da masoyanta.
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........15

Wani irin kerma kafafunta ke mata amman iyakar dauriya ta aro ta yafa akan fuskarta,malik kau gefe yaja yana kallonsu yana jin tsoron abunda zaije yazo.
Saida ya kusan shigewa jikinta sannan yaja burki idonsa akanta,wanda ta kasa cigaba da kallonsu saboda tsabar abunda yake fitowa daga cikinsu.
Cikin kakkausar murya wadda kaushinta bai hanata fitar da wani sauti mai dadin amo ba,runtse ido tayi saboda har sautin maganarsa yana sauka akan fuskarta.
"Kee ubanwa ya kawoki nan gidan,bai gaya maki sak'ona ba cewar idan na sake ganin bakar fuskarki saina kasheki.to in bai sanar dake ba yanzu kinji,don haka wlh in na sake hada ido dake ko ahanya ne saina kwalkwale idonki idiot stupid girl oya get out wawuya village girl dake."
Sai lokacin ta d'ago dara daran idonta tubar kalla masha Allah farare tas kamar takarda ta zuba mashi su,idan da yasan yadda xuciyarta ke masifar bugawa da baikai ga gaya mata irin wannan zafafan kalaman ba,amman baka tab'a gane hakan akan fuskarta wani dak'ik'in kallo take watsa mashi,tana juya kwayar idonta kamar ba tata ba,kafin taja baya tana dad'e hanci da baki kamar taga kashi ko wata k'azanta.bacin salon nata kenan don dai kawai itama ta rama dizginsa da wulakancinsa,ja baya tayi tace cikin wata siririyar murya mai dadin saurare "dallah malam matsa ya zaka wani matsoni kana wannan smelling d'in,ka kuwa ji yadda kake tashi da alamar hancinka baya jin kamshi balle wari,aida kai kanka ka kyamaci kanka.har kake kirana stupid akwai wani stupid bayan ka,dubeka don Allah a haka kamar duka kenan,yo taya ma mutane zasu rab'eka kana warin giya mts!!! Move me kana wani tsaye bisa kaina."
Dalalo idanu yayi kamar yaga sabuwar halitta,yana jin kalamanta kamar sukar mashi cikin kirjinsa juya wa tayi tana sauri don ta fice kafin ya kai ga saka mata kafa ya tad'oyeta,banda bugawa babu abunda kirjinta yake,har wani fitsari takejin yana taho mata bata wani buri daya wuce ta ganta tabar unguwar.........saidai kashhh tunaninta bai ci ba jitai anyomata wata irin fizga kamar zaitai da hannun nata.
Afirgice ta ganta zube k'asa gabanshi fuskar nan ta sake rinewa cike da zafin xuciya ya daga k'afarsa zai taka mata hannu,cikin zafin nama malik ya karaso yajanye ta cike da b'acin rai yace mashi.
"Mekake shirin yi Alfah,ina ruwanka da ita gunka tazo kokuwa ta kula da lamarinka banson cin zalin kaga kawuce kabarta tunda dai kaine ka fara tada wannan fitinar."
Wata ingiza ya yiwa malik yace"karka gaya man nonsense malik,meye hadinka da ita miye alakarta da nan gidan,wallahi inka bari ta sake takowa nan yafada yana doka kafarsa da k'asa cike da mazan taka yacigaba da cewa to billahil azim za,a kwashi gawarta."
Malik xai magana ta rigashi cike da tsiwa da rashin kunyar data aro babu jimawa tace"ni kuma saina zo,nan gidan dai ko to kadauka kamar gidan ubana yake haka xan mayar dashi,kwana ne kurun bazan ba kama hangoni gani can har dakin baccin ka,angaya maka kowa sakaraine da zaka ringa yiwa mutane hauka,yo waye bai iya haukan ba dallah can da kai mtsss!!cike da bala i yace"ke don ubanki ni kike gayaa magana tun kararta yake yana zaro ido tatare siket dinta tayi zata baza aguje don idan ya kamata ta bani ta lalace.......kotaki guda batai ba ya cabko hannunta ya dage cicin karfinsa ya watsata gefe tayi wata kalar fad'uwa har tana gurje guiwa..........ta fashe da kuka bakinta bai mutu ba tace"Allah ya isa na mugu Azzalumi macuci.......faske mata baki yayi yana huci "don kutumar ubanki tashi kifita shigiya mayya."
"Kaine maye azzalumi macuci kuma sai Allah ya sakaan mugu mashayin giya.......tana fadar haka ta rarumi jikarta ra ranta cikin na kare......shima ya rufa mata baya aguje malik shima yabisu yana son yin dariya amman halin yinta bai zoba sai yaga yar mutane ta bar unguwar sannan.
Cikin sa,a tama fita taga taxi ta tareta tashiga cikin azama.
Tace"maza muje karka tsaya muje muje maitama estate zamu."
Shashsheka kurin take ta leko ta danna mashi dak'uwa tana mashi gwalo.
Zubewa malik yayi bakin k'ofar yana kwasar dariya harda rik'e ciki,don wannan wasan yayi masifar burgesa,koba komi fiyah zata ringa saka Alfah magana ta wannan hanyar zafin ransa zairagu tun yama biyeta wataran dole zai dawo hankalinsa idan yaga tana niyyar mayar dashi cikekken mahaukaci.
Huci kurin Alfa keyi yana jin bakin cikin rashin kamata da baiba kallon wulakanci yayi wa malik cike da haushi yace"kana sane kayi haka ko,don ka b'ata man rai to kayo nasara amman kasani bataci lallai ba zanso ta sake zuwa zakaga abunda zai faru,saina cire mata kafar baya alokacin zata gane ko waye ni don ubanta."
Ya wuce malik yana dariya gaskiya fiyah ta mamesa baizaton haduwar farko zatayi irin wannan karfi halin ba.

Tana isowa gida taji kafarta ta rik'e sai yanzu faduwar da tayi takejin ciwonta,daker ta fito daga taxi ta salamesa ta nufi gidan cikin karfin hali.........mama tafara cin karo da ita zaune tsakar gida tabuga tagumi,ga yesmin gefe tana ta kuka......dandanan taji ciwon ya b'ace ta isa garesu cikin tsananin damuwa bakinta har kerma yake tace"mamana lafiya meya faru,naganku cikin wannan yanayin....yesmin daina kuka gani sanar dani don Allah meya faru."
Mama kasa tankata tayi tana share hawayenta yesmince ta iya kallonta tace cikin kuka"Adda sofiyyah babane........sai kuma ta fashe da kuka ai fiyah najin ance baba ne cikinta yayi wata irin katsawa cikin rikicewa tace"sanar dani kanwata daure ki sanar dani meya samu baban yana ina babu dai abunda ya samai ko kigaya man don Allah."
Tuni itama idonta ya fara zubar da kwallah ta tashin hankali komawa tayi wajen mama dake sharen hawaye tace"haba mama kunbarni cikin duhu don Allah kusanar dani ahalin da yake ciki,don Allah xuciyata bugawa take."
Mamarce ta iya cewa cike da raunin xuciya "safiyyah babanku ne aka kama yana police station,tun bayan fitarsa ashe yaa can suka kamashi,kuma sunk'i fadar ainahin abunda yayi kuma sun hana belinsa,tun shabiyu jalal yake can shida dalha amman babu magana ingantatta da sukafada,hardai korarsu sukai cewa kozasu kwana anan bazasu canza umurnin da aka basu ba."
Zaman dirshan fiyah tayi tana zubar da kwallah cikin kid'ima ta riko hannun mama tace"innalillahi wa inna ilaihir raju,un mama waye yasa aka yiwa baba haka,meyayi mashi wlh mama inada yak'inin baba bazai abunda ba shine ba waye shi wane macucinne azzalumi."
Cikin jan majina tace"Alh muazzam ne bansan abunda ya hadashi dashi ba,amman daman ai yana cike dashi yanada wani kudiri aransa tsawon shekaru,kullum hanya yake nema dazai wulakanta shi allah bai bashi ba sai yau tsotsai nasan komi ma yafaru wlh babanku bada niyya zai ba,saidai tsotsai da rabon wahala."
Hawaye take sharewa cike da jinjina magamar mama,Alh muazzam yasa aka kama baba,kenan banu wanda ya isa yasaka asakesa idan har ba shine yaga dama.........yanzu ya zasuyi wagaresu waye zai tsaya masu dazai ceto masu mahaifi.
Cikin hawaye tace"yanzu kenan mama babu wanda zai taimakemu waye zaitsaya mana mama bamuda kowa daya wuce yah jalal,shikuma ba wani abin hannune dashiba sai rufin asirin Allah......mama haka zamu zuba ido baba yayita zama can."
Itama cikin halin k'unci tace"Allah shine gatanmu sofiyyah,shine zai taimakemu shizamu kaiwa kukanmu kutashi kuyi Alwallah ga magruba can anfara kira mukaiwa Allah kukanmu don Alh muazzam baida wani mak'iyi cikin unguwar nan daya wuce mahaifinku,bai shiga gonarsa ba ma ya ya iya dashi balle yashiga,muje musanar da Allah kukanmu shine zai share mana hawaye.
Daidai sallamar yah jalal kenan shida dalha maitsaron shago.

*kuyihkr yauda kullum ce sai Allah*

Mrs bb ce
Mom muhseen.

I really proud of u fans Allah ya kara mana kaunar juna.
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........16

Duk idonsu akan su suna jiran ganin baba ya shigo suka ka shiru,zama jalal yayi cikin damuwa dalha kuma ya dauki buta ya zuba ruwa yafita don yin Alwallar magruba.
Cikin zak'uwa da sonjin halin da akeciki fiyah ta dawo gabansa ta rik'o hanunsa cikin damuwa "yaya mesuka ce kenan can baba zai kwana,yaya ya zamuyi bamuda wani matakin dauka kenan."
Shima muryar sa cike da damuwa yace"me zamu iya yi sofiyyah,kawai kuyita mashi addua itace kawai mafita,munyi iyakar yinmu amman mutanem nan sun runtse idonsu akan baza su bari ma muganshi ba,Allah shine maganinsu shine kawai."
Mama na gama jin haka ta wuce taje tayo alwallarta tashige d'aki shima tashin yayi yafita.
Kuka yesmin da fiyah sukeyi sosai daker sukai sallar magruba,rokon Allah kau sunyisa kamar me akan Allah ya kawo masu mafita ya kuma saka ma baba.
Ranar abincin kirki ma babu wanda ya iya sawa ga baki,anayin isha,i kowa ya wuce masaukinsa don ko hirat da suka saba yi bayan sallar isha,in yau babu natsuwar yinta.damuwar da suke ciki tafi karfin hirar.
Bayan yesmin ta kwanta saida fiyah taga tayi bacci sannan tafiddo wayarta ta kunna,ta shiga kiran malik.
Suna tare da Alfah yana mashi bayanin kudaden sa zasu fitar don yin tafiyar dasuke so,sai shan mur yake daker yake maida mashi ansa,don tundazun abun da yafaru bai wuce mashi ba,jiyake inama yasamu damar karya shegiya.
Daker suka gama tattaunawar sun tsayar da lokacin tafiyar wayar malik tashiga ringing,kallon Alfah yayi yana murmushi yace"mutuniyarka ce kozaku gaisa."
Wani jakin kallo ya watsa mashi ya tashi yabar falon,dariya malik yayi yana daukar wayar.
"Yadai matsoraciya."
Cikin halin kunci tace"yah malik inaciki tsananin tashin hankali."
Cikin mamaki da rudewa yace"kina lafiya dai ko badai yaji maki mummunan ciwo ba."
Cikin zubar kwallah tace"Aa ba Abdoul bane mahaifinsa ne ya kama mana babanmu,yana can caji office sun ma hana ganinsa balle aji ta bakinsa,suma kuma basuce komi ba sunce kuma bayanxu zasu sakeshi ba."
Kuka take k'asa k'asa.
Cikin tausayawa yace"yi hkr fiyah,daina kukan insha Allah baba zaidawo yanzu kinga dare ne kiyi bacci zuwa safe saimuyi magana.ai kinada class gobe ko."
Cikin shashshekar kuka tace eh ina dashi 9:00am to 12:00am imfact sai hudu zan dawo gida kila."
Yace"don't worry kisa ma xuciyarki natsuwa kiyi bacci insha Allah xantai makamaki zuwa gobe."
Godiya tayi mashi yace"Abdoul dai baiji maki rauni ba ko?"
Tace"targade ne amman zan gasa dasafe inshafa magani."
"OK sorry Allah ya sawake muhadu goben ki kwantar ma da mama hankali babu abunda zai faru."
Haka dai yayita lallashinta da tausarta sukai sallama tayo Alwallah tayi nafila sannan tayi karatun qur ani ta kwanta.
Washe gari kowa sukuku daker ma yesmin tasha koko taci waina gira sannan jalal ya bata kudin taxi tatafi jarabawar ta.don ma xuwa jibi suke gamawa.
Ta riga fiyah tafiya ita saida ta gama ayyukanta tanayi tana tausar mama,tana kara bata hkr da kalamai masu sanyaya zuciya har ta samu tayi kalaci don cewatai azumi tatashi dasi d'ore.
Jalal da fiyah suka tilasta mata ta ajiyesa don zata sha wahala tunda batai sahur ba,ga damuwa kuma har saida fiyah ta ragewa mama ayyukan gidan,har jajjagen kayan miya tai mata ta gyara shinkafa ta dora mata ruwan zafin wanka.
Albarka kawai mama ke samata don sofiyyah badai kokari ba,tana da tausayi fiyeda sauran yarata.

Don saida ta makara ma don wajen tara da kusan rabi ta samu tafiya bayan ta gasa k'afarta ta shafa magani.
Fuskarta yau babu walwala sosai daka kalleta kasan bata da walwala sosai,makaranta ta wuce taci sa,ar malamin baida zafi yabarta tashiga,rabida kwatar lectures din ta yau basu shigeta ba yadda ya ka mata,haka dai ta samu ta silale duk da yadda feea ke son yin magana da ita,amman ta sace ta barta don abunda ke gabanta yafi tattauna wa da feea muhimmanci.

Bata ma sanar da malik cewa tana hanya ba,kawai dosar gidan tayi saida tazo bakin kofar shiga abunda ya faru jiya itada Alfah ya fad'o mata arai.
Turus tayi kirjinta yana dukan tara tara,wayarta ta fiddo ta maka mashi kira tace"Allah yasa wannan tafasheshshen abokin naka baya nan,don wlh inhar yana nan baxan shigoba ya idasa karya mun k'afa."
Yar dariya malik yayi yace"oh matsoraciyar kanwata to baya nan kina iya shigowa."
"Aa yaya malik karkamun wayau kamar jiya."
Dariyar yake yace"Allah I'm serious he is not here"
Ajiyar zuciya tayi ta shiga da bismilah don bata shirya wata hayaniya dashi yanxu ba,har saita ga baba ya fito.
Yana cikin main falon su akan computer yana aiki daga shi sai singlet.
Kunya taji ta kamata ta d'an juya baya,murmushi yayi ya jawo rigarsa dake gefensa ya saka yace"to sarkin kunya kina iya juyowa yanzu."
Idonta ak'asa ta idasa shiga falon tana yabawa da tsarinsa zama tayi kan oneseater tana kallon wani chanis films da sukeyi wata tasha.
Gaisawa sukai yana jajanta mata akan abunda ya faru dasu,taji dadi sosai malik yana da kirki,kuma ya iya mu,amala da mutun kallonsa tayi tace"ina wannann mugun yake."
Shafa sumarsa yayi yana idasa aikinsa kanan ya rufe computer yace"yau Alfah yaje supervision na store d'insa da company,yau ya tashi da rigima daker idan bai kori wasu ba,don ni banma san fitar sa ba saida nakira drivern sa yace suna tare."
Tab'e baki tayi kurin tana wasa da yatsunta kamar ba ita ta tambayesaba.........mukullin mota ya dauko yace "zomuje akwai inda zamu yanzu,kash ko ruwa ban baki ba sorry don Allah."
Tashi tayi tana smile dinta kamar yadda ta saba tace"no karka damu yaya malik banga tashan ruwa ba tukun,muje bana jin k'ishi bare yunwa."
Fita sukai yaja motar suka bar gidan,wata unguwa suka nufa maidan nisa,sanan suka tsaya bakin wani get aka bude masu suka shiga,gida ya had'u sosai do fiyah irin wadannan gidajen ba bak'inta bane don duk irinsune a unguwarsu.
Bai bata halin tambayar inasuka zo ba.ta bisa abaya suka shiga kofar da xata sada su da cikin gidan,duk jami ai sun kewaye gidan da alama dai babban mutunne ubangidansu.
Babban falone mai kujeru royel set biyu sai k'amshi yake,zama sukai yana danna wayarsa zuwacan yakafa ga kunne yace"eh Daddy munzo muna nan main falo."
Daga haka ya kashe wayar kallonta yayi cikin tsokana yace"wajen yankar kai na kawoki mai cire kan yana zuwa yanzu."
Duk da ta san wasa yake hakan bai hanata jin faduwar gaba ba,yak'e tayi tace"uhm yaya malik kenan,zatonka zanyi tunanin wani abu ko?ai yardar dana maka ba raguwa bace na yarda dakai 100% don haka duk inda zaka ce muje bazan maka jayayyaba,don nasan bazaka iya salwantar da ran kanwarka ba."
Kalamanta sunyi masifar faranta mashi har ya kasa cewa komi ya dora mata idanunsa yana kallonta,murmushi akan fuskarsa.
Kawarda kai tayi gefe kafin suji alamun shigowa,wani kukune d'auke da tire na wasu kuloli masu kyau da plax da cups.
Ajiyewa yayi yabar falon yama gaidasu still har lokacin idonsa akan fiyah,wadda takejin duk ta takure saboda kallonda malik yake mata,fitowar Daddy ya ceceta daga kallon da malik yake jefanta dashi.
Duk saukowa sukai daga kan kujerar suna gaidashi.......cikin fara,a da karramawa yake ansa masu yace sukoma su zauna amman suka k'iya dole ya k'yalesu.
"Abdoulmalik bakuci komi ba naga."
Kansa akasa yace "Daddy nidai i'm oky wlh."
"To ai ka yi serving din ta ita ko."
Fiyah cikin ladabi tace"Aa daddy wlh nima na k'oshi kayi hkr."
"Shikenan tunda kun k'icin abincin gidana,malik naji duk abunda ka sanar dani jiya abunda yasa nace kazo mun da yarinyar don naji ta bakinta."
Malik yace"fiyah ki sanar dashi abunda ya faru yadda zai fahimta."
Cikin natsuwa ta fada masa iyakar abunda tasani wanda taji bakin mama,katseta yayi cikin mamaki yace"kardai kice mun mahaifinki malam kabir El-ladan."
Colin tabbatar wa tace"eh Daddy shine tun jiya yana wajensu anyi anyi su sakesa sunk'iya kuma sunk'i fadar abuda yafaru,jiya bamu samu isashshen bacciba."
Jinjina kai daddy yakeyi cike da gamsuwa da kuma jimamin abun.........yace"am ya sunan ki diyata,cikin ladabi tafada masa ya ciga ba da cewa "sofiyya wannan lamarin tsohuwar gabace tsakanin mahaifinki da yayana wato Alh muazzam.zan iyacewa tun

Please Login or Register in order to submit comment