Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni,ima sai malik din,zakiyya tana ganinsa tatashi tabar falon baice komi ba don daman yasan za,ai haka amman soon zata sauko idan yayi lallashi.
Duk abunda suka faru aketa bita wasu ayi kuka wasu ayi dariya,anan duk sukai dinner basu tashi hirar ba sai shabiyun dare.
Anan Abdoul yake tambayar ina su Amina Abbi ya bata rai yace "suna can shashensu yabasu sati biyu su fiddo mazaje duk ya aurar dasu idan ba hakaba wlh ya rantse saakarsu zai bayar.
Baice komi ba o aure ne shine ya dace dasu.
Mami da ni,ima sukai daki don bacci sukeji akabar malik da Abdoul da Abbi suna tattauna wa game da duk dukiyarsa da umma taso rabashi dasu,har wadanda yariga yasaka mata hannu amman baikai ga bata ba.
Nan suka tsara yadda abunuwanshi duk zasu dawo yadda suke basu tashi ba sai biyun dare.
Duk maitar shi akan jin muryarta hkr yayi don yasan tayi bacci.
Baisan fiyah tana can tana kuka ba,idan ta gaji tayi tagumi tana tunanin yadda zata rabu da Abdoul.
Yashiga jininta da bargonta tamkar fitar numfashinta takejin soyayyarsa,lokaci guda kuma baba zai mata haka.
Kashe wayarta tai don bazata iya ganin kiransa ta ki daga wa ba.
Washegari kamar marar lafiya ta yini don ma exam din sai yamma haka ta yini daki,saiga yaya jalal ya dawo Anty jamila kuma tazo.
Ranar yini tai tana surfa ma fiyah bala,i don taki muhseen shima yaya jalal din yana tayata.kuka kau idonta har ya kumbura,bata kara takaici da bakinciki ba saida maganar Abdoul nasser ta fasu duk suka sani ai kamar zatai tsuntsuwa tabar gidan haka taji.
Don yaya jalal yace wlh idan yasake ganinta dashi ko aka gaya mashi anganta dashi saiya balla mata kafafu.
Mama dai najinsu saida taga abun naneman zama hauka tace duk wanda ya sake mata fada akan haka saota bata mashi rai.miye laifin yaron kawai don anbata sunan sa shine kurin zaku tasanmata,to karta sakejin bakin kowa akan maganar.
Wanna ranar fiyah bata san ma meta rubuta ga exam din ba,tasandai ta yi tubutu amman bazata iya cewa daidai tayi ba ko akasin haka,har dare bata kunna wayarta ba Abdoul nacan duk ya rude ya fita natsuwarsa,saiyazo xaiyyi sallama gidan saiya fasa kasa zama office yayi don tashin hankali,maganarta tajiya yake tunawa kardai baban nasu ya dakatar da ita akanshi.inko hakane dole ne yau yaje ya fuskance shi............daga jiya zuwa yau fiyah ta fita natsuwarta bata iya cin wani abun kirki data fara zata ajiye ta shige daki......mama duk tashiga damuwa kuma har yanzu baban daure fuska yake don yasan zata ce mashi wani abu.............bayan salar isha,i yagama cin tuwon masara da miyar kubewa danya da mamar tayi,har lokacin fuaka abace duk gidan ya zama babu dadi saboda abunda yafaru.
Dalha ya shigo bayan ya gaida baban yace"kayi bako awaje yana son ganinka"
Kallon dalhan baban yayi yace"waye"
"Dan gidan Alh........katseshi yayi yace"cedashi ya shigo"
Fiyah na daki tana jin haka dandanan wata masassara tazo ta rufeta,kirjinta yana duka me baba zaice mashi innalillahi nashiga ukuna
Sallama yayi yashigo cikin wani yadi marar nauyi yayi kyau sosai,ya gaida mama dake bakin famfo ta asa cikin kulawa.
Kafin baba yayi mashi iznin zama ka tabarmar dayake bisa.
Yaya jalal ne yashigo yana ganinsa ya hade fuska,Abdoul bai damuba ya mika mashi hannu,Daker ya amsa mashi gaisuwar dayake mashi.
[10/11, 7:23 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

*kafin muci gaba zanyi wani bayani.akan masu ganin ban kyauta ba dan nasaka Alfah bai auri zakiyya ba,harda cewa ina nuna duk girman laifin mutun ana yafita yes duk girman laifinka idan katuba ga Allah yana yafe mana,haka zalika niban nuna cewar Alfah bai yafewa xakiyya abunda tai ba,tariga ta sanar dashi komi kuma yafahimceta yace ya hkr komi ya wuce,sannan badole sai Alfah ya auri zakiya ne hakan zai nuna ya yafe mata ba.abunda nakeson kugane nifa labarina gaba dayansa akan Abdoulnasser da safiyya natsara shi,duk wanda kukaji sunansa to daga jikin daya daga cikinsu ne,kuma nayi hakane don na nuna cewar ba komine kake nema ka samu ba.duk sonka da abu idan babu alkairi tsakaninku Allah zai iya hanaka,haka duk gujewarka da abu idan rabonka ne dole zai kasance.ita rayuwa haka take xuwa ku kalli yadda abubuwan suke faruwa ko a reality zakiga abunda kikeso bashine yake kasancewa ba,wanda bakinson shine alkairin ka akan kanki ma idan kika duba abubuwa dayawa dakikeso baki samesu ba kuma karshe wanda bakison shine alkairinki.don haka ina mai bawa masu challenging dina hkr akan cewar haka labarina yataho,haka zai cigana da tafiya idan anan anbata maka wani wajen ana faranta maka.haka rayuwar take idan nan kaji dadi ba dole can kaji ba,idan yau katashi da lafiya gobe ba lallai kajika normal ba.don haka kubarni na tafiyar da labarina ayadda yake,haka natsara haka zai tafi plzzzzz idan wata ta kullaceni har tana ganin ta yi asarar kudinta ina bata hkr,nidai don wata kodon wasu bazan fasaba bakuma zan canza idear ta ba ina godiya sosai da challenging wannan yanuna man cewar duk yadda kake faranta ma dan adam duk ranar daka kuskure mashi to hakan nanufin sauran daka faranta mashi zaimanta dasu ya gaya maka magana.ngd ngd sosai da hakan na sake samun experience ahakan,daman arayuwa bakowane zakaima daidai ba nabarku lfiy BISSALAM*


🅿️...........59

"Zauna sosai magana zamuyi dakai."
Baba yacewa Abdoul dake yakejin dukan kirjinsa yana karuwa.
"Meke tafe kai tukun karna katse maka hanzari"
Sadda kai yayi yanajin kamar ya tashi ya ruga amman muhimmancin safiyya arayuwarsa yafi gaban nan,wannace damarsa idan yara sata baisan ya zaiba.
Cike da ladabi yafara magana cikin natsuwa "baba nazo ne akan kaban iznin xuwa wajen safiyya,inasonta na yaba da halayenta nagari da hankalinta da natsuwarta don Allah baba karkace aa."
Yafada muryarsa tayi rauni tausayinsa ya cika xuciyar mama,jalal kuwa sai wani harararsa yake yaja karamin tsaki yace"kayaba da tarbiyyarta kaikuma fa,taka tayi daidai da tata kaga akwai tazara tsakaninku"
Dago jajayen idanunsa yayi ya xuba mashi su yaajin zafin xuciyarsa yana hauhawa,hakika da babu baba da ba agidan bane tabbas saiya xubar mashi da hkr,amman yaci albarkacin qanwarsa dayake so yaci albarkaci baban da kuma mama.
Cikin fada baba yace mashi"jalal tashi ana wajen,ina ruwanka dakai yake magana zan saba maka awajen ana oya fice man da gani"
Ya ta shi yafice kamar iska.
Kunya ce ta kama baban saboda yasan maganganun sunyi mashi zafi sosai.
"Kayi hkr bashida wayau ne,naji bayanin ka Abdoul-nasser kuma ada na riga na yanke hukuncin cewa alakarka da safiyya bazata yuwa ba saboda ganin nisan dake tsakaninku bayaga haka kuma ina duba wani abun bayan wannan,da zanyi anfani da matsayina na mahaifinta in dakatar dakai itama na hanata saurarenka Amman ya zu zan kirata idan har uwata tace mun ta amunce tana sonka zata aureka hakika bazan takura ku ba.don gudun shiga hakkinku"
Dadi Abdoul yaji ya kamashi duk wani haushin jalal yaji yana bajewa,yasan fiyah bazata kishi ba zatace ta amunce.
Kallon mama baban yayi yace"kiramun uwata"
Tashi tai tatafi tana kalon wannan lamarin,tabbas tasan fiyah babanta baya son hadin duk abunda baya so ko tanaso zata hkr,tasan wannan hanyace dayakeson korar Abdoul din batare daya kullace shi ba.
Jinjina kai take tanajin tausayin diyar tata.
Shiru dakin ko haske babu yesmin na waya da muhseen,fiyah na dunkule cikin bargo tana kuka can kasa.
"Safiyya kifito babanku yana son ganinki kisanyo abaya"
Fita tai don bata son ganita cikin wani hali zata sake karya mata xuciya.
Ahankali ta sauko daga ka gadon tana jawo abayarta ta saka tana goge fuskarta sannan ta fita,
Bata yarda ta kallai ba daga can gefen baba ta zagaya ta zauna cikin ladabi tace"gani baba"
Kanta kasa bata yarda ko kayan jikinsa ta saka ga idonta ba.
"Bakiga bakoba bazaki gaidashi ba"
Muryarta can kasa tace"ina wuni yaya Abdoul"
Wani abu yaji ya dirar mashi,kamar zai fashe dakuka don dajin muryarta kuka tamaga yi
Cikin kulawa yace"lafiya kau safiyyah"
Sukai shiru baban kanshi yanajin kamar bai kyauta masu ba,amma yana hangen abunda mutane zasuce akanshi zasuga kamar ya bayar da yarsa don ganin yaron nada kudi haka ubansa........."uwata ga nasser nan yazo kan batun neman aurenki,kina sonsa kin amunce zaki auresa bazan tauye ki ba"
Jitake har numfashinta yana sizing meyasa baba xaice haka,idan ya amunce ai ansamashi kawai zai basai ya sanyota ciki ba ita yanxu ya zatai zata ansa mashi ta bar abunda baban keso kokuwa yazatai.
"Kinajina uwata"
Muryarta tana shakewa tace"baba duk abunda ka yanke akai dashi zanyi anfani ka yanke hukunci kawai,duk abunda kace yayi"
Tatashi ta koma daki toilet tashige tana rushewa dakuka mai cin xuciya.........shikenan bata da sauran wani farin ciki baba ya rabata da burinta da walwalarta,waye zai iya maye wannan gurbin babu shi har abada kowaye zaice ta aura bazata tana sonsa ba,zata yi biyayya ta aureshi amman ba zata iya sashi cikin ranta ba har gaban abada.

Shiruce ta biyo baya sai yanzu baban yakejin bai kyauta ba,hakika safiyya yarinyace mai hkr dakawaici da kauda kai,yayi imanin duk abunda ya yanke akan alakarta da Abdoul haka xata karba tayi mashi biyayya,tausayinta ya cika shi har ya kasa cewa komi Abdoul din ya mike yana cewa"baba Allah ya bamu alkairi Allah yasa hakan shine Alkairinmu saida safe"
Yafice yana ganin bibbiyu don har wata juwa take daukarsa,metake nufi kenan ta bada damar da za,a nisanta shi da ita safiyya daman bata son sa bai sani ba,meyasa zata karya mashi xucya har haka daker ya iya gano get din gidansu yana shiga kau kamar jira ya yanke jiki ya fadi.........akan idon zakiyya ta fito daga sashen su khadija ta kaimasu abinci.....aguje ra karasa tana fasa kara tana jijjigashi dan da nan aka taru kanshi,sojojin dake waje suka daukai suka sashi mota,shigowar malik kenan yaga wannan tashin hankalin,kwana yayi yarufa masu baya don yasan asibiti za,aje dashi duk inda hankalinsa yak yayi masifar tashi don har yamance rabon dayaga Alfah cikin wanan hali,tabas abunda Abbi ya gaya mashi dazun akan maganar safiyyah da Alfah shine zai cosing wannan matsalar,kodai yaje gidan baban ya korai kokuma ya gaya mashi kai tsaye bazai bashi yarsa ba.
Mami da ni,ima kuka suka kamayi gashi Abi baikai ga dawowa daga wajen aiki ba,babu shiri mami ta kirasa ta gaya mashi ai yafi kowa rudewa da tashin hankali..............

Mama kanta tasha takaicin baba shiyasa ko saida safe batai mashi ba ta shige dakin ta kwanta,wane irin halin rikaune da babansu yana gani yaran nan suna son junan su amman saboda wani ra,ayi can nashi na daban zai cutar dasu da haushinsa ta kwana shikanshi yaga canji amman bai iyace mata komi ba.
Fiyah saboda kuka cikin dare zazzabi ya rufeta har hakoranta suna haduwa saboda kerma,hankalin yesmin ya tashi taita shafa mata ruwa saboda yadda jikin ya kidime baki daya banda kuka babu abunda yesmin keyi,fiyah kau bama ta cikin hayyacinta ganin dare yasa yesmin bata tado mama ba amman asubar fari dataga fiyahr har suma take agigice tafito tana kwalama mama kira cike da tashin hankali.
"Yesmin kanki daya baki iya salati ba kike ihu da kururuwa menene"
Tana shashsheka tana nuna dakinsu daker maganar take fitowa "Adda.......Adda ce gata can......su.....suma take tun cikin dare bata lafiya mama karta mutu...."
Tare suka karasa cikin dakin duk sun rude mama had jikinta rawa yake tana jijjiga fiyah amman bata numfashi..........rungumta tai tana kuka lokacin baba yaje masallaci dan danan mamar ta kira anty jamila don basu san wanda zasu nemi taimakonshi ba wajen mota idan ba su ba.
"Jamila kiceda yahya don Allah yayi hanzari yazo yakai safiyyah asibiti gata nan suma take"
Ai xunbur tai daga kan gado tana fitowa har bakin get tana jiran shigowarsa daga masallaci ta gaya mashi kayan baccine jikinta ta saka abaya suka taho agigice,tabar little fiyah ga mairenonta.

Sorry for d let update
[10/13, 12:32 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️............60

Ansamu nasarar daidaiton numfashinta amman bugu xuciyarta bai dawo daidai ba,saboda jininta daya dan hau shiyasa amman sunyi iyakar bakin kokarinsu akanta sunyiwa uncle yahya bayanin cewa zata tatashi insha Allah,damuwace zata haifar mata da masassarar kuma dama akwai maleria jikinta.amman yanzu da bukatar ta huta tasamu rest of mind da alama tana da matsala da bacci amman data farka tasha magunguna kuma ga ruwa yana shigarta komi normal insha Allah"
Godiya uncle yayi mashi yana komawa wajen baba da mama dasukai xugum xugum kamar masu zaman gaisuwa.
"Yaya dai yahya me likitan yace?Allah yasa ba wani mugun abubane ya faru da ita?"mamace cikin damuwa harda yan kwallarta take mashi magana.
"Ki kwantar da hankalinki mama safiyya zata tashi cikin koshin lafiya,ba wata matsala yamun bayani gamsasshe maleria ce da damuwa don har BP dinta yadan hau kadan amman yace data sha magani insha Allah normal,yamata allurar bacci data maleria karku damu abarta ta huta din kamar yadda yace"
Jinjina kai tayi tana zama kusada Anty jamila da tayi tagumi,inhar akan wannan mutumen fiyah take wannan ciwon gara abata shi hankalin kowa ya kwanta,yarinya da yan shekaru harta samu hawa jini.
Mama Ko kallon baba batai ba don har lokacin kule take da shi,ko magana ma batai mashi ba.
Baban da uncle suka ware gefe suna magana akan matsalar data faru uncle yana bada shawara da fadar yadda yadace.................haka aka bar mama wajenta yesmin zataje ta shigar mata exam don yau suke ta karshe tana adduar Allah yasa ta iya ansa mata question din daidai,don bata san me za,a tambaya ba.duk yadda baban yaso magana da mama kiyawa tai saidai ta kauda kai kurin dole suka wuce gida suka kyaleta.dalha ne zai kawo mata kalacinta,Anty jamila tace zataje tayo wanka sai tadawo tataya mamar zama.

*************
Duk inda hankulan iyalan Alh muazzam yake yakai kololuwar tashi,don kuwa ga Abdoul nan kwance gamar gawa baya numfashi,likitoci ukune kanshi suna bakin kokarinsu amman Abbi gani yake basu yin komi zarya yake bakin kofar dakin yana leke ta glass din kofar,daga can kuma mami ce dasu ni,ima zakiyya da malik kuka kurin suke,malik ne keta kokarin nuna dauriya.........dadyne ya iso shima cikin damuwa yake tambayar abi abunda yake faruwa kasa mashi bayani yayi yana kwalla,malik ne tace "dady duk ta kare yaje gidan su safiyya ne babanta ya korai kokuma kai tsaye yayi mashi iyaka da ita,abunda zai ita jefashi cikin wannan halin kenan don Abdoul yana ma safiyya soyayya mai zafi,rasata kamar yana barazanar shina rasa tashi rayuwar don gaskita cikin kwanakin nan inaganin canji sosai tare dashi,alamun sunriga sun daidaita da ita yarinyar gaskiya abunda nake zaton zai jefa shi cikin wannan yanayin kena"
Xunbur Abbi yatashi zaifice dady yarikoshi "ina zaka?badai koma wa zakai ba duk irin abunda ya gaya mana rannan"
Kamar abbi zai kuka yace"Abdullahi ina son rayuwar dana shekara nawa bana tare dashi,sai lokacin da komi ya wuce kuma wata matsalar xata shigo,zanje karo na uku na sake rokonsa kome yake son nai mashi inhar zaibarsu su auri juna wlh zan mashi,koda cewa yayi inkwanta ya bita kaina"
Ficewa yayi dadyn ya bi bayansa don yana iya cewa acikin wannan halin zaija mota.

**************
*****************

Fiyah cikin kwana uku tatashi ta samu sauki,ta dauki hkr ta sama xuciyarta amman fa ta rage walwala sosai da sosai don saita yini cikin daki bata fito ba idan ba wani abun xatai ba,zaka samu kowa tsakar gida amman ita tana daki babu yadda mama batai ba,babu irin lallashin da batai ba amman fiyah ta kasa dawowa daidai,abunda ya taba yesmin da mamar kenan shi kanshi baban yanajin babu dadi,shiyasa yaketa kokarin jawota jikinsa ko zata sake saidai murmushi kurin duk maganar da zakai mata idan har ba yazame mata dole ba bazakaji muryarta ba.tun Anty jamila na fushi da ita harta sauko tana jan yar uwartata jiki,jalal kau ko kallon inda yake batai ko ya mata magana uffan bata ce mashi.ana cikin haka aka saka ranar yesmin da muhseen alokacinne baba ya kira fiyah dakinsa da safe bayan angama karyawa.
"Uwata kinsan dai nine mahaifinki ko,kuma kinsan irin son danake maki bazan yi abunda zai cutar dake ba,duk abunda zanyi inayine don martabarki da kimarki yanzu ma wata alfarma nakeso daga gareki"
Dagowa tai tana kallonsa da fararen idanunta fuskarta ta saki daka kalleta kasan tana cikin damuwa don har wata irin rama tai.
"Baba ni banace kayimun ba daidai bane,kawai inakokarin ganin na manta da komi zan dawo daidai kuma komi kake son yankewa akaina baba basai ka nemi alfarmata ba kana da ikon yanke hukuncin duk da ka ga dama akan rayuwata"
Wani tausayinta yaji ya dirar mashi har kwalla ta cika idonsa "shikenan uwata Allah yayi maki albarka Allah ya albarkaci rayuwarki,wanine keson aurenki harna bashi dama ya turo iyayensa don harna yanke hukuncin saka rana guda keda yar uwarki,nan da wata uku idan Allah ya kaimu"
Wani irin bugawa kirjinta yayi dan danan kanta ya sara damn ciwo yake,daker take jawi numfashinta ta dake sosai tace"Allah ya sa haa shine mafi alkairi baba"
Tatashi tafice tabarsa yana binta da kallo,mamace ta shigo cikin tashin hankali take kallon baban "mekake shirin yi babansu?waikai bakajin digon tausayin yarinyarnan shin wace irin xuciya ce dakai babansu,inajin yaron nan har yau yana asibiti karshe dole aka fitar dashi kasar waje,duk da haka bazaka tausaya masu ba.har gida iyayensa suka zo suna magiya da roko amman vanji kace masu komi ba,gaskiya idan ka aurar da safiyya ga wani ba wannan yaron ba ka cutar dasu,kadaina ganin bata maka gardama Allah kadai yasan kuncin da kasasu baka tunanin Allah ya tambayeka.................ya i sheki nace ya isheki hakanan,ke zaki gaya mun abunda zanyi inace nima yatace,gaya maki kai ba nasonta?kinfini sanin daidai da ba daidai ba?to kinga daman kyaleki nake akan wannan abun,tunda akafara maganar nan kiketa mun wasu halaye marasa dadi safiyya dai yata ce kuma nine nakeda alhakin zaba mata miji wanda yake daidai da rayuwarta,don haka wannan yazama na karshe inajin kinji me nace"
Ya saka hularsa ya fice yabar gidan.
Tunda mma tazo gidan nan matsayin matarsa magana kwatan kwacin irin wannan mai zafi da daga murya baitaba mata ba,duk sabaninsu zasuyi abu su surufe sushirya babu wanda ya sani,kuma kullum suna cikin fahimtar juna daba juna uxiri,amman saigashi yazu da girmansu suke irin abunda baidace ba,har yaransu sunaji.
Kukan da mama ta manta batai ba shine take yi,suma can fiyah da yesmin kukan suke,don basu tabajin irin haka da iyayen nasu ba.
Fiyah naji nagani aka shiga shirye shiryen bikinsu itada yesmin,tun tana kuka tana damuwa tana kuncin,har ta shanye tazo ta zama kamar abun baya damunta,gidan koda yaushe da mutane yanuwan mama dana baba ana hidimar hada gara su cincin da dublan da alkaki da sauransu,shiyasa ma bata zama gidan tana gidan inna balaraba wajen hasana,ko tatai wajen feea.

Wannan kenan......


Tunda akaga ciwon Abdoul ya gagari likitocin na Abbi yayi visa suka tai suduka can Australia wajen dr Abdoul din da yataba dubashi,don sunce xuciyarsace ke ciwo duk sanda zata halba dole zai sume saboda bata da isassar lafiya.
Kuka kau mami sun shashi har idonsu ya kekashe,zakiyya tuni ta nemi fushin da take dashi ta rasa kullum suna cikin yi masa addua Allah ya tashi kafadarsa,sai ya zamana malik ne dan lallashi da nasiha da ban baki acikin sati ukun da sukai Australia sabo da fahimta ya shiga tsakanin zakiyya da malik,saboda shi ya ansa zai auri zakiyyarne don ya saukakama Abdoul matsala don tabbas yasan zai sabi fiyah akan zakiyya,shiyasa shikuma yaga yadace asamu mai lallashinta mai tausaya mata,don zakiyya ta cancanci wadannan abubuwan tarasa mahaifiyarta ta rasa masoyinta da tayi shekaru aru aru tana dakon sosan,amman zamanta da malik akai akai yana yawan yi mata nasiha da jawo hankalinta yana nuna mata cewar komi na rayuwa dan hkr ne,kuma duk abunda karasa arayuwarka ka dauka hakan alkairine,Allah yafimu sanin daidai da ba daidai ba,yana duba mana abunda zai zama alkairi arayuwarmu bisa ga wanda muka kwallafa rai.
Komi yafaru da bawa dama can rubutaccene kariga karubuto abunka tun cikin ciki,shiyasa kafi son duk abunda kagani to ka godema Allah kayarda da wannan kaddarar don yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau imanine...........da haka malik ya jawo hankalinta kanshi,duk da sudukan babu maijin son wani amman akwai kulawa da fahimta tsakaninsu,haka mami ma take yawan yiwa zakiyyar nasiha akan rayuwa da kuma alakarta da malik,don tagaya mata muddin ta rasa shi ba fata take mata ba samun irinsa zaiyyi wuya.
Ansamu cigaba ta bangaren lafiyar abdoul don ciwonsa na cikin ciki ya warke tas cikin kwana ashirin da dayan da aketa mashi treatment,xuciyarma kuma alhamdulillah bugunta ya daidaita don har yana farkawa yaci dan wani abu yasha magani,amman baya tankawa kowa maganarsa bata wuce eh,aa,yawwa ko idan zai gaida mami dasu Abbi zaice ina kwana atambayesa ya jikin zaice da sauki shikenan.
Malik ne kurin yake dan mashi hira yana tankawa shima idan yagaji yayi mashi banza.
Wani sabon miskilancine ya tsiro dashi aduk sanda yake sauraren maganar ta jiyake xuciyarsa tana kuna,har wata sa,in jikin ya rikice sai anmashi allurar bacci..........saida mami ta tusashi gaba da kuka tana ya sassautawa kanshi yaji tausayin kanshi da nasu,komi zaifaru yariga yafaru idan anhanashi safiyya bayana nufin karshen rayuwarsa ne yazo ba,akwai mata da dama Allah zai cire maka ita inhar ita din babu alkairin tare da ita,fada take mashi sosai har tasamu ya xubda kwalla ranar yini yayi baice komi ba,bayan kwana biyu kafin asallamesu dady da Abbi suka tai Nigeria saboda wani aiki daya taso anbar malik da su mami da ni,ima da zakiyya dai bayan sati biyu idan an basu sallama zasu dawo tare alokacin ne kuma Abdoul ya fara saukowa yana sakin jiki da yan uwansa zasuyi fira harda dariya shidai iyakarsa murmushi,ahakan ma sunajin dadi son da ai bama aiyin firar dashi.

Yau shi kadaine su mami basu kai ga zuwa ba don gidan Abbi dake nan kasar suke zaune malik ne yake kwana dashi,idan safiya tai yaje gida yayi wanka yayo break.
Xakiyya ce ta shigo da kwandon kalacinsa fuskarta da fara,a ganinsa zaune yana kallon tv dake cikin dakin nashi.
Murmushin shima yayi mata ta ajiye kwandon bisa wani table tana dauko brush din sa ta matsa mashi maclean tace"yaya ina kwana"
Muryarsa ta canza sosai tayi sanyi dakaji zaka san cewar yasha jinya.
"Lafiya lau kiyya,yau manta wa dani kukai har shadaya saura babu wanda yazo"
Murmushi tayi tace"wlh makara mukai yau,nice ma wai nai saurin fitowa sabida break dinka kayi hkr"
"Yazanyi daku"ya mika hannu ta bashi brush din yafara kokarin saukowa hannunta ta bashi ya kaa saan ya sauko yana cewa"thank you"
Murmushi tai tana bude mashi kofar bayin yashiga ta shiga tattara dakin tana gyara mashi gadin,duk dadai tun safe masu gyaran dakunan marasa lafiya suke shigowa su share.
Freshner ta fesa dakin ya kama kamshi komi yayi lafiya lau sannan ta zuba mashi break din ta ajiye kafin ya fito.
Kallon dakin yayi yajin jina kai kullum ita ke gayara mashi dakin yayita kamshi alamar jinjina yayi mata yace"kina kokari gaskiya da alama gidanku bazai kasance a datti ba ina taya abokina murna"
Hararar wasa tai mashi tana juyar dakai tana murmushi.
"Nidai bana so wlh"
Zaro ido yayi yana zama kasa inda ta shimfida mashi darduma yace"abokin naune bakiso kome?"
Itama zaro idontai tana rufe baki "nabani ni wlh ban ce ba karka jamun"
Dariyar da yajima baiba yau yayi yana kallonta ita kuma ta boye fuskarta tana juya baya.
Aransa yaji dadi da hakan ta faru,tabbas yasan duk wadda tasamu malik matsayin miji ta gama morewa,don shima gwanine wajen jawo hankalin mace akanshi,ya tabbata kokarinsa ne tasa har zakiyya take saurarensa kuma da alama tayi na,am da malik din.
Shine ya shi go da fara,a yana kallon Abdoul din "alhamdulillah jiki yayi kyau wlh daman nagaji da zaman kasarnan haka gara katashi komunje muji inda tamu maganar ta kwana ko yakikace"yafada yana kallon zakiyya jitake kamar zata nitse awajen tsananin kunyarsu takeji mikewa tai zata fice Ya tare kofar yana leken fuskarta Abdoul murmushi yake masu yana break dinsa.
"Ina zaki daga nayi magana shikenan tunda kunya kikeji na daina zoki zauna abunki,inkikatai ina zan iya zaman gadin wannan miskilin mutumen"
Dawowa tai ta zauna suka cigaba da hirar su gwanin sha,awa.
Har sadda su mami suka karaso.

**************
*nigeria*

Biki ya kankama don komi anriga da angama yiwa amaren,tundaga kan wani gyara da tsumi iyayen nasu sunyi bakin kokarinsu wajen yin hakan,idan kagansu zaka dauka cikin inji aka sasu aka wanke tass........damuwar da fiyah ke ciki itace ta shafi yesmin,duk yadda take murnar zata kasance da burin ranta idan ta tuna da cewar Addarta bata sanma mijin ba,saidai yakan kirata

Please Login or Register in order to submit comment