Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta daura kan gas ta dzn zuba Albasa ciki, kafin ta dawo kan markadadden Wakenta, a turmi ta zubashi, ta bugashi sosai, kafin ta fiddashi spices ta zuba, tare da jujjuyashi , Albasar da ta yanka ta zuba, ta ƙara motsawa kafin ta koma kan man da yy zafi, cikin natsuwa ta fara sanya ƙosan da ya sha kayan haɗi,
lokacin da zata gama su Amah sun gama fere dankali, har da yayyankawa, zubawa ta fara yi cikin man tana soyawa , bayan ta gama ta soya kwai, komai ta haɗa a cikin food flask , har zasu fita ta tuna da bata damawa Yaa Shehu kunun gyaɗarsa ba.


dafe kanta tayi, wanda ya fara mata ciwo, miƙawa Amatul-Azeez trayn cups tayi, ta miƙawa Amaturrahman plates, kallonsu tayi tace "A hankali kuje ku ajiye akan dinning ", ta fada tana juyawa, ficewa suka yi, ita kuma ta koma.


Shinkafar tuwo ta wanke ta zuba cikin tukunyarta da take kan wuta, juyawa tayi zuwa gurin wani fridge daban, niƙaƙƙen gyaɗa ta ɗiba kadan ba da yawa ba, shinkafarta na dahuwa, lemun tsami ta dan matsa, kafin ta fara zuba niƙaƙƙiyar gyaɗar tana jujjuyawa, har yy kauri , sai da ta dan bar sa yy dahu sosai, kafin ta sauke, cikin wani lafiyayyen flask mai kyan gaske ta zuba Kunun, fita tayi da shi, har ta juya zata wuce bedroom dinta, Amatul-Azeez tace "Anty Baki wa Uncle M Fruits Salad ba", ta fada tana kallonta, "Innalillahi!", ta furta cike da gajiya, sam ta manta da haɗa masa, "barsa Amah Wlh na gaji, An jima in zai sha sai na haɗa masa, dan lokaci ya ƙure sosai".


kafin tayi wanka ta shirya har an fara kiraye-kirayen Sallar Magrib , sauri-sauri ta shirya, Pray mat ta shimfiɗa tare da Kabbara Sallah.
turare ta fesa sama-sama , kafin ta fito palo, tana fitowa Amaturrahman ta miƙa mata, Dabinon Ajwa, peak ta mata a goshi tare da mata murmushi, zama tayi kan carpet .
Dabinon ta fara tattaunawa a hankali, gorar Zam-zam Amatul-Azeez ta miƙa mata mai dan rangwamen sanyi da cup, bayan ta gama shan ruwan sai jikinta yy lakwas , ta kasa cin komai.


sai Misalin karfe tara na dare kafin suka shigo cikin gidan a gajiye, Yaa Shehi ma cike da tsananin gajiya yake takawa izuwa cikin part dinshi, tana biye dashi a baya suka shiga cikin bedroom dinshi.
yana shiga ta juyo tare da fuskantar ƙofa, idanunshi akan Sadiyyerh tsareta yy da mayayatattun idanunshi , bata an kare ba ta ji ya zuba gaba daya hannayenshi a kan ......



Masha Allah ! .Alhmdllh !. yau muka cika shekara daya chif,munawa Allah godiya da Ya Azurtamu da samun ƙaruwa, kuma ya raya mn ita, wanda har yau takai shekara, ina fatan Allah Ubangiji y raya mn, Allah ya Azurta duk wanda bashi dashi, Alfarmar Annabi da Al-qur'ani.


masu tura min saƙon HBD ngd ss , Allah Ubangiji ya bat kauna🥰😍😘.


07033371851


DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR🧚‍♀️🧚‍♀️🧚‍♀️
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.16*



wanda yasa ta fara zabura , tana son kwacewa, sai da ya gama Jagwalgwalata da kyau kafin ya matsa gefenta yana sauke numfashi, itama numfashun ta shiga saukewa da sauri-sauri wanda yake sanadiyar dagawae kirjinta, haka ta ringa sauke numfashi da jan ajiyar zuciya mai karfi,sai da ya dai-daita tunaninshi kafin yamiƙe cikin natsuwa ya nufi bathroom dinshi, kungunshi har lokacin yana daure da ƙaton towel din da ya daura.
tsakiyar shower ya tsaya ruwa na dukan tsakiyar kanshi.


gaba daya ganshin kanshi ya kwanto mishi har kan fuskarshi , jikinshi na zubar da ruwa, wankan tsarki ya yi cikin Suffa ta kamala, kafin ya fito jikinshi na zubar da ruwa .
gently ya fito yana goge sumar kanshi da take sharkaf ruwa nata zuba,idanunta ta dagi a hankali ta zubawa kyakyawar fuskarshu da take sunkuye yana kallon kafafunshi, cikin natsuwa da ƙara kamewa yace "kallon fa ?", da sauri ta sunne kanta cikin blanket din da take bata ce komai ba.


bayan ya gama shirinshi cikin Caftain Jallabiya Ash colour sai kamshi yake buɗaɗawa, ganim bata tashi daga gurin da take ba har ya gama shirinshi yasa, ya kalli Agogon Bangon da, take manne jikin bango.


cikin gajiyayyiyar muryarsa yace "ke tashi ki tsarkake jikinki", ya faɗa murya a kame, dan baya son wasa da tsarkake jikin, musamman ma jikinta da ke da tulin gurin zaman mutane, dole sai ta ringa ƙiyayen tsarkinta, sa boda gudun matsala.
cikin natsuwa ta miƴe izuwa bathroom tana tafiya kamar zata faɗi sa boda tsawon yunwar da take dauke a hanjin cikinta.
dan tun jiya Uwar lokacin bata ci komai ba har lokacin, ganin kamar zata fadi sa boda yarda take tafiya yasa, ya kalli bayanta, cikin taɓe baki da basarwa kamar ba shine yy mgn ba yacr "ki kula fa tom", ya faɗa ba tare da ya ko ƙara kallon bayanta ba.


itama bata jiyo ba, sai ma ci gaba da tafiyarta tayi zuwa cikin bathroom.din, kamar yarda aka saba ruwan zafi ta tarar cikim bathtub ciƙe, sai kamshi yake, ga wasu furanni da tafi kauna kalar red kamshinsu da kamshin tiraren wankan da yake ciki da kamshin Soap din da take wankan da shi, ya haɗu ya bada wsni kamshi mai rugurguza zuciya da dadi.


luf tayi cikin ruwan tana jin yarda yake ratsa dukkan wata kafa da huda ta jikinta yana shiga, ga kamshin da ya hanata sukuni sai faman lumshe ido take kamar mai jin barci, wanda kuma azahiri kamshi ne da ɗumin ruwan ta haɗɗasa mata wannan yana yi.

bayan ta gama abun da take ma wasa ta shiga yi da ruwan da hannunta, ta jima sosai, har sai da Yaaa Shehi ta fara tunanin ko bb lafiya, cikin takun ƙasaita ya matsa gurin ƙofar tare da kwankwasa ƙofar bathroom din.
shiru bb wani sauti, hakan yasa ya tura ƙofar bathroom din jai tsaye.


idanunshi ne ya fada cikin nashi, laɓe baki yy ba tare da yy magana ba, ita kuwa kirjinta ta shiga kakkarewa da hannuwanta bata son ya gani, wani miskilin murmushi da ya haddasa lomarwa Beautiful point dinsa wanda ni ban taɓa gani ba, wanda kuma ya kusa haddasa min sumar tsaye sa boda yarda ya ƙara mishi kyau sosai, yatsarshi daya ya sanya cikin sumar girarshi mai yawa da ta dan yanka ta raba biyu, shafawa yy, tare da taɓe bakinshi.


kai tsaye ya juya bayanshi, sai da ya kusa rabin bedroom dinshi, kafin yace "ina jiran Abin ce ne fa", ya fada yana zama kan bed, idanunshi he ya hasko mishi gefen drawer in da wayar Sadiyyerh take, wanda ita bata damu da ita ba, dan tafi sati biyu ma ajiye akan drawer din, ba kuma ƙaramar mai tsada ba, waya ce babba, wadda ake ya yi Iphone 13 pro MAX , cikin natsuwa ya dauki wayar cikin hannunshi, jujjuyata ya shiga yi, yana mamakin yarda bb abun da ya sami wayar sakamakon da da take sakarwa su Amah suyi ta lalatawa, kusan duk bayan 2 to 3 months sau an chanja, amma yanzu ta kusa kai 5 months bb abun da ya sameta.


power wayar ya latsa, pics dinsu ne da su Amah ya bayyana sun yi murmushi,ba ƙara min kyau suka yi a pic din ba, gaba daya beautiful point dinsu ta loma, bama kamar Sadiyyerh.


Sama ya jaa, bai yi mamakin rashin password din wayar ba, dan shi kanshi baya son wannan password din,shima yasa bata sawa itama, nan kuma Pic dinshi ne shi , pic din ya ƙurawa ido sosai, tunanin inda aka yi pic din ya yi,bai wani dau lokaci ba ya gane, Ranar Eid din waccan Babbar Sallar ne, yana fitowa daga Massalaci Zayn-Maleeq yy mishi shi.
lokacin kuma aka yi katari da yy murmushi kumatunshi sun loma sosai.


kai tsaye Gallery ya nufa, pics dinsu ne kala-kala ya shiga gani cikin wayar wani nasu Amah wasu nata, wasu ita da su Amah, ga dai sunan da yawa, kusan 1k sai da ya gaji da kallo ma.


dubawa ya shiga yi, bb wani abu da ya saɓa shari'a cikin wayar ya kuma san ba zata yi makamancin hakan ba, dan ko WhatsApp bb cikin wayar, balle kuma wasu Abubuwan na daban, SIM ba iya numbers din yan Uwa ne take dasu ciki.


cikin natsuwa ta turo ƙofar bathroom din ta fito tana lullumshe idanuwanta, alamar ɗumin ruwan ya gama ratsa mata cikin jikinta, bata ƙarasa gareshi ba sai ta tsaya gaban mirror ta shiga mulke jikinta da turaruruka Humrahs da sauran kayan kamshi, bayan ta gama ta taje gashin kanta da yake da mugun yawa ga tsawo , ga baƙi , gwanin sha'awa, Wardrobe dinshi ta bude, hannunta ne ya sauka akan wata Tan Brown Jallabiya tashi, zarota tayi , dagawa tayi ganin tsawonta kamar zai mata yasa ta tura ba tare da tasa ko Under wares ba.


Hand dryer ta jona tare da fara busar da gashin kan nata, sai da ta tabbatar ta busar da gashin nata, kafin ta mulkeshi da man gashi mai kamshi, ribbon ta samya ta daureshi, tare da daukar dankwalin Abayarta ta sanyashi a kan nata, rolling din gyalen tayi, tare da tattare ƙasan rigar ta fara tafiya a hankali, zama tayi gefemshi ta daura kanta a kafadarshi, cikin sanyayiyyar murya tace "Uhn..uhn..uhmmmm Yunwa", ta fada tana kallon fuskar wayar da yake kallo, bai ko yi mgn ba ya miƙe tsaye, da sauri ta miƙe itama, jerawa suka yi suka fars tafiya, hannunshi daya na kan waist dinta.


suna ƙarasowa palon ya zame jikinshi daga nata, zamewa yy ya zauna kan kujera, ita kuwa kai tsaye ta wuce kitchen, noddle ta dafa da soyayyayen kwai, sai ruwan tea mai dauke kayan kamshi, sauri-sauri ta haɗawa Yaa Shehi Fruits salad, tana gamawa ta haɗo gaba daya kayan kan tray ta fito da su zuwa palo.


center table ta jaaa tare da ajiye tray din a kai, zama tayi kusa da shi,tare da daukar plate din Indomi dinta, pock ta dauka zata fara ci, da dauri ya riƙe hannunta, kallonshi tayi tana kwaɓe fuska.
shi kuwa bai ma kalleta ba, sai ma ci gaba da kallon abun da yake.


ƙin sakin hannunta tayi, ɗagowa tayi da niyyar yin mgn, wani kallo ya watsa mata, wanda yasa ta haɗiye miyau dakyar, dauke idanunshi yy daga kanta, sai lokacin ta tuna, cikin sanyin murya tace "Bissimillahirrahmanu rahim!", ta furta a hankali, bai ko kara kallonta ba ya sake mata hannunta.


jikinta a dan sanyayye ta fara cin Abin cinta, har ta gama bai kalli abun da ta kawo mishi ba, har ta gama komai ta tattara wanda ta gama amfani dashi ta wuce zuwa kitchen, sai da ta dauraye kafin ta fito, zama tayi kusa da shi, cikin murya mai dadi tace "Zauj ga Fruits Salad din nan fa ", ta fada tana cusa kanta ta hammatarshi ta shige jikinshi tana mai son ganin abun da yake yi.


dauke fuskar laptop din yy daga kan cinyarshi ya zubawa fuskarta ido, cuno baki tayi, tana ƙara gyara zamanta kan kirjinshi, hannubta ta sanya cikin gemunshi ta fara wasa da shi, shi kuwa a hankali ya dauki Bowl din fruits din, ya fara shaa a hankali idanunshi a lumshe.


sajenshi ta jaa, tare da cewa "Zauj!", bai amsa mata ba, kara jaan gemunshi tayi, wanda hakan ya tilasta mishi bude idanunshi, sa boda zafin da ya ziyarci cikin kanshi,idanunshi ya kafeta da su, ganin taki mgn yass ya dauke kanshi yana mai ci gaba da abun da yake, cikin shagwaɓa ta ƙara cewa "Zaujil khair!", cikin mgnarshi kamar ko da yaushe yace "wai me ne?", jaaan gemunshi ta ƙara yi.


da sauri ya riƙe hannunta, yana kafeta da gajiyayyun idanunshi, cikin kasalalliyar murya yace "Haah na kusa cire gemun nan ko zan huta da abun da kike mishi", ya fada yana zare hannunta daga cikin gemun.


kaɗa bakinta tayi cikin muryar Shagwaɓa tace "ai kuwa ba zaka yi kyau ba, komawa zaka yi kamar wani mutumin ɓoye, ai Namiji da gemu yake namiji , namiji bb gemu ya zama mace, Allah ya kiyasheni ma Babban Malami bb gemu ai sai ya zama abun faɗa", ta fada tana gyara kwanciyarta kan ƙafarshi.


murmushi mai haɗe da taɓe baki yy, kafin yace "Yau Allah y haɗani da mata, to naji dai koma mai zan koma cirewa zan, dan zan iya ba kullum kiyi ta cin zali na, "taɓe bakinta tayi kafin tace "dan ma ka samu ina taɓawa shine ma zaka ce haka ?, to ka ciren wlh mutumin ɓoye zaka koma ni ba ruwana", ta fada tana daura hannunta kan kirjinshi.


"kin san mutan ɓoye kuwa ?", ya fada yana riƙe yatsun hannunta, girgiza mishi kai tayi, "tom kar kiyi fatan ganin mai kama da su ma, dan zaki iya makancewa in kika gansu , ko ma tashin hankali yasa zuciyarki bugawa", ya fada cikin rashin damuwa.
riƙeshi tayi tana cewa "Yaa Shehi ina son zuwa Jaddi", ta fada tana wasa da gashin cikin Jallabiyarshi.


aikinshi ya ci gaba da yi ba tare da ya amsa mata ba,"Ina sin zuwa Jaddi", ta kara fada tana kallonshi still ya ƙara yin shiru bai amsa ba.


ƙara ta fasa mishi wadda ta dabura mishi lissafi gaba daya, cikin ƙaraji ta ƙara cewa "ina son zuwa Jaddi", hannunshi da ya dafe kanshi dashi ya cire, cikin ƙosawa rigimarta yace "na hanaki zuwa ne ? tashi ki tafi na ", ya fada yana shafa sumar kanshi, wanda ciwon kai ya dirae mishi, a rayuwarshi baya son surutu, shi yasa ya zaɓi da ya zauna a part dinshu, baya son shiga cikin mutane sai ya zame mishi dole.


hawaye ta fara tana kuka cikin rigima, take cewa "ni Jaddi zani!, ni ka kai ji gurin Jaddi, Wayyo!", ta fada cikin sakalci,cikin jadadda rigimarta da son ta da mishi zaune tsaye yace "Allahumma Ajirni fi maseebati", cikin kuka sosai tace "ni ce mamaseeban ko ?", ta fada hawaye na zubo mata sosai.



taɓe bakinshi yy cikin rashin damuwa da rigimar tata, idanunshi ma gaba daya ya rufe ba tare da ya kulata ba, dan yasan abun da take so kenan, baya son kukan mace ko kaɗan, yawancin lokutta kuma da wannan damar take amfanin gurin cin galaba a kanshi, "wayyo! wayyo!! Wayyo !!! Wayyo Allah", hannunshi yasa ya bige bakinta, ware eyes lashes din da hawaye ya gama jiƙawa tayi da sauri, shima ware mata manyan idanunshi yy , cikin kakkausar murya yace "tashi ki bani guri shagwaɓaɓɓiyar kawai", ya fada yana zameta daga jikinshi.


komawa tayi ta ƙara mannewa da jikinshu still hawaye da gunjin kukanta na nan, "kimim shiru", ya fada cikin kunnenta, yana fesa mata iskar bakinshi mai sanyi da kamshi.


tuni ta fara lumshe ido sautin kukanta na yin ƙasa, dan dama rigimar tata bata wuce ta barci ba, kamar yarinya kullum da drama din da zata dauko kafin barci,fuskarta ya zubawa gajiyayyun idanunshi, cikin cool voice yace "Sadeeyn rigima k...........
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.17*





"Sadiyyeeh Rigina, Allah y shirya min, ya Azurtamin ke da samun Zuri'a 'Dayyiba", ya fada yana sunbatar goshinta.
kamar ta ji abun da yake faɗa ta motsa tare da cuno baki gaba.


murmushim da bai fiye yi ba ya kara bayyana akan fuskarshi,bakinta ya kara sumbata kafin yace "bakin tsiwa da rigima", miƙa ta mishi tare da banƙare mai kirji, idanunshi ya lumshe a hankali yana mai furta "Subhanallah wal Hamdulillah,Allahu Akbar", ya fada yana gyara zamanshi, tare da gyara mata kwanciyarta tayi Balance a jikinshi.


hannayenta ta sanya ta zagaye waist dinshi, tare da manna lips dinta kan mararshi.
hannunshi ya daura cikin gashin kanta,a hankali ya shiga shafawa yana mata Addu'o'i , a hankali ta shiga sauke sanyayyiyar ajiyar zuciya.
kwanciya yy gefenta, yana kwanciya ta gangaro jikinshi ta manna jikinta da nashi sosai, kanta ta daura akan kirjinshi.


cikin barci da magagi tace "Zauj!", idanunshi da suke kan fuskarta ya kara budewa, kafin yy mgn ta kara cewa "Zauj!!'" cike da shagwaɓa, ware idanunshi yaƙara yi , "har a barcin ma ?", ya fada a hankali.


sanyayiyyar iska ta fesa mata akan fuskarta, Addu'o'i yy tare da tattofawa gaba daya kusurwuwin ɗakin, gyara kwanciyarshi yy, yana ɗaga kafarshi ta zura tata tsakankanin nashi, girgiza kanshi yy,rigimarta ba zata ƙare ba dai.


Barci suka yi mai cike da natsuwa , ni'imomi, da jin dadi, barci wanda zasu iya cewa sun dade basu yi irinshi ba, bama kamar Yaa Shehi da ba samun yin barci yake ba, amma yau yy barci sosai, dan bai ko farka ba cikin dare, sai gabanin Subhi kafin ya fara ware idanunshi a hankali cike da natsuwa, bakinshi dauke da Addu'ar tashi daga barci "Bisimikallahu amutu wa hayyana!", ya furta a hankali yana kara buɗe idanunshi.ganin time a Agogo, dan shi kwamciya ya dan yi, in lokacin tashn Darenshi yy ya tashi, amma bai tashi va sai guraren Asuba, kallon Sadiyyerh yy wanda take laluɓen in da zata jishi, a hankali ya gyara mata kwanciyarta, tare da sanya mata pillow madadinshi.


kafarshi ya sauko daga kan bed din da "Bissimillah", ya fara takawa, cikin kamalarshi, har ya shiga bathroom.
ruwa mai ɗumi sosai ya haɗa yy wanka , tare da dauro Alwala.


cikin kamala da nagarta ya turo ƙofar bathroom din ya fito, zaune ya sameta kan bed, dan tun shigarsa bathroom itama ta farka, bai ko kalli in da take ba ta ƙarasa gaban mirror, idanunshi ya daga ya kalli Mirror, wanda hakan yy dai-dai da facing din mirror da Sadiyyerh tayi.
kuma idanun Yaa Shehi ya sauka a kanta, abun yy mugun girgiza ni, dan a zahiri dai Sadiyyer ce zaune, Amma kuma Baɗini /jikin mirror suffa biyu ce, wato *MUTUM DA ALJAN*, rabi Fuskar mutum da jikin mutum amma sauran rabin kumurcin maciji ne baƙi ƙirin dashi.


Bai wani damu ba, har ya gams abun da yake, ya shirya cikin Jallabiya kamar kullum, fridge din bedroom din ya bude, zam-zam.da dabino ya dauka, kai tsaye gabanta ya ajiye mara, yana murza zoben zinarin da yake makale a karamar yatsar hannunshu, wanda ya karawa yatsae kyau da kyalle.


cikin natsuwa ta shiga tattauna Dabinon tana haɗiyewa, shi kam zam-zam kawai ya sha, yana gama abun da zai yi , ya dauki black din Alƙyabba mai ratsin gold a ƙasanshi , takalmi ya sanya, yana juyowa ya ga ta tsareshi da ido tana kallonshi, juya mata idanunshi yy alamar lpy dai?, hannunta ta daga mishi alamar yy kyau, murmushin gefen baki mai haɗe da taɓe baki yy , yana ficewa daga bedroom din, sanyayyan numfashi ta sauke cike da so da kaunar halittar da Allah y daura mata.


tun lokacin da suke fita zuwa Masallaci , taji alamun Azuminta ba zai kai ko ina ba, dan duk wasu alamomin Period dinta ta gama jinsu a jikinta, wasa-wasa har 10 aka gangara 11 sai guraren 1 , ta shiga yin Alwalar Sallah Zuhr , taji mararta ta murda mata, gabanta ya tsinke ya faɗi, saukar abu mai ɗumi ta ji cikin ƙafafunta, lumshe idanunta tayi tana sakin numfashi a hankali tace "Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un!",ta furta lokacin da taji wani abu mai nauyi cikin mararta.
a hankali ta sukale ta zauna, tana wata iriyar zufa, ai Bama Zuwan period din nata ba wahalar da take sha duk in ta fara.


dakyar ta samu ta fito daga bathroom tana dafa bango, kwanciya tayi kam bed tana jin yarda gaba daya gaɓɓanta suka dauki rawa , kyaf! kyaf!! kyaff!!! haka jikinta yake yibb wanda yasan tana ɗaki bb lafiya,gashi sun fara aikin Sallah sosai, san Yau sauran kwana biyu Sallah, ga mutane sun taru sosai a gidan, yan Masarautarsu Yaa Shehi da suka zo Umrah Azumi duk a gidan suka sauka, tun daga kan Mai martaba da Sauean Iyalanshi, aikin Abun buɗa baki ma aiki ne, shi yasa yau gaba daya Ayyana da Umma Jakadiya, har Ma da wasu *Bayin* da Matan Mai martava suka zo da su basu zauna ba.


"wai kam ni ina Sadiyyerh tun da ta fita yih Sallah bata dawo ba gashi lokaci ya fara ƙurewa, kuma yau za'a fita da abun sadaka", Umma Jakadiya ta fada tana Kallon Rayhana Matar Yayan Yaa Shehi wadda bama a ƙasar take ba ba kuma Nigeria ba, ita da mijinta da Yaranta biyu duka suna Ethiopia , "Umma kamar bata dawo ba , dama ina lura da ita tun ɗazun kamar bata jin dadi",Ayyana ce tace "Rayhana ajiye aikin ki dan duba min ita", ta fada tana nunawa wata Baiwa yarda zata yanka mata Kazar da ta fitar daga freezer.


"Tom Ayyana!", ta fada tana ajiye nadin Samosar da take yi.
itana fita daga cikin kitchen din su Yaa Shehi na shigowa da shi da Yayah Muhammad (Babban Yayansu Mijin Rayhana), da Zayn-Maleeq, Sayyid-Maleeq, Abdul-Maleeq, dukkansu fuskokinsu washe da murnushi ban da ta Yaaa Shehi da hakan sam baya cikin jadawalinshi, dan sai an kai ruwa rana zaka ga yana murmushi.
Rayhana na ganin Yaa Shehi ta fara Tsokanarshi , shi kuwa ganin su Mai martaba da.Jadda da take zaune rana ƙarewa gidan kallo, sai wani yatsina fuska take, wanda da Alama wani abu take kitsimmawa cikin ranta.


"Barka da hutawa Lamiɗo", cikin dan bada girma shima ya dan

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment