Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tare da cewa "Sannu Sarauniyar Sa ido", ta fada tana cewa, bin bayanta Ayyana tayi tana murmushi.


Sakinshi Zayn yy , yana sakinshi ya juyo cikin natsuwa ya fara tafiya zuwa komawa cikin gidan, bin bayanshi suka yi gaba dayansu, ko da suka shigo cikin palon bai tsaya ba sama yy Abunshi.
yana shiga palo ya kalli Dining dinshi, ciƙe ya ganshi da food flask kala-kala da flask na ruwan zafi, cikin bedroom dinshi ya koma , har lokacin tana kwance ƙ.........
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.13*



Ƙudundune, tana fitar da numfashi sama-sama, A hankali ya yaye blanket din da ta rufa da shi, zafin zazzabin da ya bugi fuskarshi ne yasa ya dan lumshe ido, ko bai taɓa jikinta ba yasan tana jin zafin zazzaɓin nan,idanunshi ya bude tare da zufasu akan fuskarta, jikinta da yake rawa har fatar idanunta kawai zai sa ka gane yarda take jin zafim har cikin ƙashin jikinta.


iskar bakinshi mai sanyi tare da kamshin mouth freshener ya fesa mata a kan fuskarta, wanda yasa ta fara ware manyan idanunta da suka ƙara fitowa sun yi jaaa har wani ruwa-ruwa yake kwanciya a ciki sa boda tsabar zafin zazzaɓin da yake jikinta, suna haɗa ido ta maza ra rufe dan bata son ganinshi ko kadan , tsoro yake bata, "lokaci na ƙurewa", ya fada a hankali, yana kallonta, yasan ba lallai ta iya yin Azumin ba, Amma kuma ta wani fannin yasan tana da juriya.


gurin fridge din da yake chan gurin ƙofar fita ya nufa, budewa yy , packet din Dabino Ajuwa ya dauka da ruwa mai rangwamen sanyi, yasan bata wani cin Abinci da Subhi dama sune abun Sahur dinta.
gefen bedside drawer ya ajiye mata, tare da juyawa ya fice.
bayanshi ta bi da kallo.


A gaggauce ya fara yin Sahur dinshi dan lokaci ya kusa ƙurewa , bayan ya gama ta koma bedroom din, kai tsaye bathroom ya wuce , wanka ya fara yi yy brush kafin ya fito daure da bathrobe mai tsayi da ta rufe mishi jikinshi, yana tafiya yana dan ɗigar da ruwa , har ya ƙarasa gurin mirror, shi ba ma'abocin kyalkyal bane sosai, in ya shafa lotion ya taje sumarshi da gemunshi sai turare sune kawai abubuwan kwalliyarshi.


gaban Wardrobe ya koma, ta dan jima yana kallon tulin kayanshi da suke cikin wardrobe din kafin ya zaro Alƙyabba Milky colour, gefe ya ƙara matsawa ya bude, Jallabia's ne jere gurin kala-kala gwanin burgewa, Whitening Jallabia ya dauka, bathroom ya koma, dan duk da sun zama daya bazai iya bari taga Tsiraicinshi ba, yana da matuƙar kunyar jikinshi, zai iya rantsuwa da Allah tun da yy hankali bb wanda ya taɓa ganin damtsen hannunshi ma balle a kai ga sauran sassan jikinshi, haka yake rayuwarshi.


Gently ya turo ƙofar bathroom din ya fito, kallona na mayar gareshi,Masha Allah !.
yy wani sahihin kyau, fuskarshi na fitar da wani irin ƙyalli da Annuri irin na wanda ya Angwance, sai zuba kamshin turaren Huge Boss yake, ga Alƙyabbarshi sabuwa dal,sai sheƙi take, ƙafarshi na sanye da takalmi White Adrian Italian Leather Slippers sababbi fil, komai nashi sabo, ya fito a real Ango dinshi,.


Cikin kamilalliyar muryarshi mai taushi yace "Sadiyyerh !. Sadiyyerh !!", sai ya dan jinkirta da kiran sunan nata, bata Amsa ba, amma yana yin motsin da tayi ya tabbatar mishi da tashinta, hakan yasa yy waje Abinshi.


ba suji ƙarar taƙun takalmimshi ba, sai kamshin turarenshi na Huge Boss, shine ya fara musu Sallama, duk a tunaninsu kamshin da ya riga ya zauna a cikin palon ne suke ji, sai da ya iso daf da su kafin su san da zuwanshi, idanumshi a ƙasa ya cewa Umma Jakadiya "Sabahul Noor !", murmushinta mai kyau ta mishi kafin tace "Sabahul Khair Yaa Ustaza !", ɗan kallonta yy da gajiyayyun idanunshu, tare da juyasu akan fuskarta.
kallon su Zayn yy gane Abun da yake nufi yasa suka miƙe,har yy taku daya biyu ya juyo, Ayyana ya kalla, bai bari sun haɗa ido da ita ba ya dauke, chan ciki yace "Su Amah fa ?.", Umma Jakadiya ce tace "She's too Young . suka yi Azumi ai sai an rimga zuba musu ruwa" , kaɗa kanshi yy , ba tare da damuwa ba yace "ku tashesu" Umma Jakadiya, zata yi mgn, yy waje Abunshi ba tare da ya ko juyo ba.


girgiza kanta tayi tana mamakin wannan halin na Yaaa Shehi, Ayyana ce ta miƙe, ta nufi wani ƙofa.
ba'a jima ba ta dawo hannunta na riƙe da hannayensu, cikin sauri-sauri ta haɗa musu Celeriac , cikin natsuwa suka ringa sha har suka gama, jan hannunsu Ayyana tayi suka shiga ciki, Umma Jakadiya ma ciki tayi.


bayan kamar 20 Minutes , ƙamshin turaren Arebian Oud ya cika gaba daya palon, kafin daga bisani na fara jiyo ƙarar takalmi, cikin natsuwa da zazzaɓin da ya rufeta ga tafiyarta da take da kyar, ta fara tako Steps dim zuwa ƙasa, tana sanye da red turkey Abaya , sanya Hijab half , tasha takalminta
Silver Romina Tuscany Leather Mid Heel, ta yane fuskarta da niƙaf , jajayen dara-daran idanunta da ta sanya musu Sunglasses kawai ake hangowa ta ciki.


tana ƙarasowa tsakiyar palon suma suna fitowa cikin shirinsu kusan kalar nata, dan duk Abaya's din ne suka suka sa, kallon takalmin kafarta Umma Jakadiya tayi, kafin tace "Anya ba zaki sanya takalmi Plate ba ?", ta fads tana kallonta, girgiza kanta tayi, ganin bata so , yasa ta kyaleta, hannun su Amah ta riƙe suka fara tafiya a hankali, su Ayyana na gaba su kuma suna baya, har suka ƙaraso Massalaci.


Ta ƙofar mata suka shiga, Nafilfili suka fara yi kafin lokacin Sallah yy a ƙabbara, ba su fi 20 minutes ba, aka fara Sallah, Yaa Shehi ne Liman, cikinn natsuwa da zaƙin murya yake karatun Al-qur'ani, wanda gaba daya garin Makkah ya dauka, kasantuwar Abun sautin maganar da aka lillika a ko wane sashe da yake cikin garin Makkah, cikin natsuwa yake har aka idar, bayan idarwa mutane suka fara tattafiya, wasu kuma suna nan zaune cikin Massalacin, kamar dai su Ayyana basu ko motsa daga in da suke ba, sai tasbhi suke da, kiran sunan Allah.

Gyara zama Shehi yy, da nufin ci gaba da karatunsu na jiya, sauran jama'ar da suke gabanshi ma duk gyara zamansu suka yi, suna son su ƙara shan madarar ilimi daga garesa, Cikin Lankwasa harshe yace " *HADARIN DAKE CIKIN CIN DUKIYAR MARAYA*

Maraya, shi ne wanda mahaifinsa ya rasu kafin ya balaga, ya yi hankali. Ma’aikin Allah ya ja kunnen al’umma sosai da sosai.
a kan kulawa da hakkin maraya da tausaya masa. da yin fadi-tashi kan
al’amuransa, kuma ya bayyana falalar yin hakan a wurare da dama.
To, amma abin takaici sai a wayi gari, dan abin da Uba ya mutu ya bar wa Ƴaƴansa, sai wani/wasu su bi ta kan wannan abin da aka bari, kafin dan lokaci a neme shi a rasa. Allah Madaukakin sarki
Yana cewa dangane da masu cin dukiyoyin marayu da zalunci.


‘’Lallai dukkanin wadanda suke cin dukiyoyin marayu da zalunci, abin sani kawai, suna cin wuta ne a cikinsu, kuma da sannu za a kona su a wuta wacce ake rura ta.’’ Suratun Nisa’i, aya ta:10.


*HANYOYIN CIN DUKIYAR MARAYU*


Akwai hanyoyi da dama da mutane suke bi wurin cinye wannan dukiya ta maraya.

Wasu idan suna hulda da mutum, sai ya zama akwai wasu kudadensa ko filayensa ko ma dai wasu kadarori da ya
san ba wanda ya sani sai shi, sai kawai ya yi shiru a kan su, ya ki fito da su. In kuma ya ga suna da yawa ko za a gane, sai ya dan tsakuro wasu daga ciki sauran kuma yayi shiru akansu.


Ana samun masu irin wannan mummunan hali cikin Matan Mamacin ko Ƴaƴanshi ko Abokanshi ko Abokan Cinikayyarsa da sauransu.


Wannan haramun ne ko tantama babu, kuma duk wanda ya yi irin wannan hali, sai ya amayar da abin da ya ci a ranar alkima a lokacin da hakan ba zai yi amfani ba.

A wasu wuraren kuwa hukumomin yankin ne –masu unguwanni da dagatai da hakimai (wadanda ake kira masu kasa) su ke wadaka da
abin da aka bar wa magada, sai dan abin da aka sammusu, gonaki ne ko fadamu ko ma dai me aka bari.


A wani lokacin kuma shi malamin da ka kira domin ya raba gado shine wanda zai kamfaci wani kaso mai tsoka ya ce wannan na masu rabo ne, ko kuma a zaga ta baya a hada baki da shi don ya kara wa wani. Wai fa wanda zai yi fada akan wannan mummunan hali, shine kuma zai zama ja-gaba. Allah Ya sawwake.


A wani jikon kuma ’ya’ya mata da matan mamacin su ne za a yi rabon gado, amma kwata-kwata ba su san me aka raba ba, ko dai ‘yan uwan mamacin su yi watsi da su, ko kuma ‘ya’ya maza su yi watsi da ‘yan uwansu ‘ya’ya mata. Ko kuma, duk ba wannan ba, wacce ta fi ‘ya’ya, sai ta yi zamanta a kan dukiyar. Ka ji! Don rashin jin tsoron Allah, wai ana cewa ba a raba gado da mara ‘ya’ya. Sau da yawa wata irin kazantar da ake yi a wurin rabon gado, kare ba zai ci ba.


A wani karon kuma shi wanda aka ba dukiyar marayun ya kula da ita, bayan an gama rabo shi ne zai hau ta da casa, kafin kiftawa da bisimillah, ya hallaka dukiyar baki dayanta.


Bai halatta a danka wa yara kanana dukiyarsu ta gado ba, sai bayan sun cika sharudda guda biyu:

(1) Balaga: Dole kai da aka ba dukiyar mamaci ka ci gaba da rike ta, kana jujjuya ta, ba za ka danka masa ba, sai ya balaga. Ita kuma alamar mutum ya balaga, alama ce kamar haka:

(A) Mafarki: A lokacin da yaro ko yarinya ta yi ko ya yi mafarkin ya sadu da mace ko macen an sadu da ita kuma mani ya fita, to daga wannan lokacin hukunce-hukuncen shari’a sun hau kan shi ko kan
ta, mala’iku za su dinga rubuta musu ayyukan da kowa ya yi, mai kyau ko mara kyau, sun yi aure ko ba su yi aure ba, domin babu wanda ya ce sai ya yi aure sannan za a bude masa fayil a wurin Allah. Ko kuma maniyyin ya fita a farke, ba wai sai a bacci ba kadai.



(B) Bayyanar Gashin Mara: Haka nan idan gashin mara, mai kaush-kaushi, ya bayyana a gaban ’ya mace ko da namiji.

(C) Jinin Al’ada: Haka nan daga lokacin da mace ta ga jinin al’ada to daga wannan lokaci ta balaga; hukunce-hukuncen Allah sun hau kanta, a nan nake cewa dole ne iyaye su tashi tsaye wurin kula da
‘ya’yansu.

(D) Cika shekara 15: A lokacin da da namiji ya cika shekara 15 ko 17 ko 18, kamar yadda malamai suka kara wa juna sani, to lallai ya balaga.

Wadannan alamun balaga kowacce daya cin gashin kanta take yi, ba lallai ba ne cewa sai sun bayyana duka, a lokacin da daya ta bayyana shi ke nan. Ya zama dole iyaye da masu riko, su kula sosai da sosai, domin sai ka ga yaro ko yarinya sun sha azumi, amma kwata-kwata
ba maganar ramawa, wai an dauka sai an yi aure sannan mutum zai dinga cika ibadarsa.

(2) Sharadi Na Biyu, Wayau: Ko da yaron da kake kula da dukiyarsa ya balaga, to bai halatta ka ba shi dukiyar ba
sai ka jarraba hankalinsa da dabararsa da wayonsa. Idan ya natsu,sai ka danka masa, idan kuwa bai natsu ba, to bai halatta ka ba shi ba.
Wadannan sharudda guda biyu su ne aya ta 6 cikin Suratun Nisa’i ta yi bayani. Allah Madaukakin sarki Yana cewa: “Kuma ku jarraba
marayu, har idan suka isa aure, to idan kun tabbatar da wayonsu, sai ku ba su dukiyoyinsu. Kada ku ci ta (dukiyar) da barna da gaggawa kafin su girma (komai ya kare). Duk wanda yake mawadaci
ne, to ya kame, wanda ko fakiri ne (marashi ne) to ya ci gwargwadon wahalarsa. Idan za ku danka musu (dukiyar), to ku kafa musu shaida,lallai Allah Ya isa Mai lissafi a kan komai”.

Wannan babbar aya ce a kan abin da ya shafi kulawa da dukiyar maraya a tsari mai cike da adalci da tausayawa da ba kowa hakkinsa.
Da farko dai ayar ta yi nuni da a dinga jarraba su marayun, har
idan aka ga sun cika wadancan sharudda biyu, sai a ba su dukiyarsu.
Sannan ayar ta ja kunnen masu kula da dukiyar da kada su tasa ta a gaba da ci ham-ham, kafin yara su girma babu komai. Sai ayar ta bayyana hakkin mai kula da dukiyar, idan shi mai kula da dukiyar
maraya da ma mawadaci ne yana da harkokinshi, to ya ci gaba da kulawa, amma ya kame daga cin wani abu na dukiyar.
Idan ko talaka ke kulawa da dukiyar marayan, ta shagaltar da shi daga nashi fadi-tashin, to ya dauki gwargwadon wahalarsa. Ma’ana, in da wani
ka dauka aiki yake kula ma da dukiyarka, nawa za ka ba shi, to abin da ka san za ka ba shi, haka za ka dauka. Sannan ayar ta nuna mana cewa idan lokacin damka wa maraya
dukiyarsa ya yi,kada ku kunshe kanku a daki, a’a, ku kafa shaidu.
To ke nan ma a lokacin da za ka karbi dukiyar maraya, ka tabbatar an sa shaidu kuma a rubuta adadin abin da ka rike. Kada ka yarda a ce, ‘ai ba sai an rubuta ba, ba danka ba ne’? Sau da yawa mutum bazai raka ka ba, ya ce dare ya yi ma. Wasu su za su zugo marayun,
bayan sun girma, ace ‘babanku ya bar muku abu kaza da abu kaza’, a nemi a hada ka fada da ‘ya’yan kanenka ko yayanka.

Allah Ya sawwake!
Sannan wurin shaidun, ba lallai ba ne a ce sai dattijai, a hada da matasa, wadanda suke da wayau. Allah ne dai kadai Ya san gawar fari.Sai Allah Ya rufe ayar da: ‘Ya isa ya zama mai lissafi’. Wannan yana nuna mana cewa a tsaya a yi lissafi mai kyau lokacin karba da kuma lokacin bayarwa. Za ka lissafa duk abin da kake kashe wa marayan da ke hannunka, kamar kudin makaranta; kudin koyon sana’a; domin zaka tsaya ne ka kula da tarbiyyarsa. Lokacin muzurai, a yi mishi muzurai; lokacin fada, a yi mishi fada; in ya yi abin duka, a doke shi, amma ba duka mai tsanani ba. Domin sai an runtse ido ake shan magani, musamman a irin wannan lokaci da tarbiyya ta sukurkuce. Ka sa shi makarantar Islamiyyah da ta boko da koyon sana’a, sai ka ga ya girma ya zama natsattsen mutum kamili. Ga
kuma irin wannan dimbin lada da ka samu, domin duk wadannan al’amurra da kake wa wannan maraya kana da lada ta musamman a wurin Allah.
Ayoyin Alkur’ani sun zo da bayanin kada ku yi kusa da dukiyar maraya sai da abin da yake shi ne mafi kyau. Saboda yadda ayoyi suke magana a kan dukiyar maraya, sai da ya kai wasu sun nemi su ware dukiyarsu da ta maraya, ba tare da sun hada ba, ko da jinsinsu guda, kamar dabbobi; kayan gona; kudi da sauransu.
A Suratul Bakara aya ta 220, Allah Madaukakin sarki yana cewa:
“Kuma suna tambayarka dangane da marayu, ka ce: Kyautata musu shi ne daidai, har idan kuka hada dukiyarku da tasu ai ‘yan uwanku ne (ba komai), Allah Ya san mabarnaci kuma Ya san mai gyara”. Kuma ya kamata al’umma su tsaya su yi karatun ta-natsu a kan marayu! Bai gagara mutum shi ma ya mutu ya bar nashi yaran kanana, ai shi ma ba zai so abin da ya bar musu wani ya yi wandaka da shi ba. Saboda haka lissafa cin dukiyar maraya ba-gaira-ba-sabab da Ma’aikin Allah ya lissafa shi cikin abubuwa bakwai masu halakarwa,
ba karamin tashin hankali ba ne.

Allah Ya kara shiryar damu, Ya bamu ikon fin karfin Zuciyarmu.Ameen !.
Kadan daga cikin Haɗarin cin Gadon Marayu kenan", ya fada yana dan lumshe gajiyayyun idanunshi da suka ƙara yin ciki kaɗan sa boda rashin barcin da bai samu ba."Jazkallahu bil khair Yaa Shehi !", daya daga cikin Manyan Malumman da suke gabanshi yace.


ware idonshi ya dan yi, chan ciki yace "Uhmm Ya Mu...........



Fatan muna lpy .?
Ya Zaɓe ?
Wa kuke ga Alamar Zai lashe zaɓen bana ??

Allah Ubangiji ya zaɓa mana Alkhairi dai🥰😍
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.15*


Gaba daya hannayensa ya zubasu akan ƙugunta, tare da matsowa da ita gabanshi sosai, kanshi ya daura akan kafadarta gemunshi na gugar fatar kirjinta, a hankali ya daura lips dinshi akan fatar wuyanta ya mata wata sihirtacciyar tsotsa mai tsuma jiki, da sauri ta rumtse idanunta, fatar idanunta na wani irin rawa, hancinshi ya daura a fatar gurin tare da fara murzawa, cikim rasa yarda zata yi da abun da ya girmewa tunaninta, itama ta zuba hannenta kan ƙugunshi, sama ya shiga yi da hayyanensa har ya daura kan fatar cikinta da take a bayyana sanadiyyar kayan da ta sanya a jikinta.


yatsun hannunshi ya zuba cikin ramin cibiyarta mai dan zurhi, a hankali ya shiga mata tafiyar tsutsa, yana sanya hannun ciki yana fitarwa, tunaninta ne ya fara son kwacewa, cikin rawar murya tace "Y..Y..Ya..Yaaa ...Sheeeeeeeeeehi", ta furta da dan sauti , tana daura hannayenta a kanshi, tare da ƙoƙarin zame mishi kan nashi daga cikinta.
idanunshi da suke lumshe ya fara budewa a hankali, kamshin jikinta na mishi dadin shaƙa sosai.
kallonta yy, kafin ya zame lips dinshu ns ƙasa zuwa cikin bakinshi, a hankali ya fara tsotsa yana kallon fuskarta da har lokacin idanunta na lumshe.


Zamewa yy ya zauna kan bed, yana zameGray Joaquin Italian half shoe din kafarshi, zubewa tayi a ƙasa tare da cewa, "barka da shan ruwa.!", tsayawa ya dan yi da abun da yake, ya mata kallo na yan seconds kafin ya dauke kanshi ba tare da ya amsa ba , har ya gama abun da yake a gurin bai yi mgn ba.


cikin natsuwa ya miƙe zuwa Bathroom, yana shigewa itama ta fice abunta, bai jima da shiga ba, ya fito cikin wata Jallabiya mai saukin nauyu kalar Ash , sai baza kamshin turaren Huge Boss yake, slippers dinshi ya zura zuwa palo, dan cikinshi har dan kuka -kuka yake mishi.


Kan 3 Sitter ya zauna , tare da jinginar ka kansh jikin bayan kujerar, hannunshi ya daura akan dogon gemunshi yana dan jaaa a hankali, bitar karatun Al-qur'ani yake, wanda yake son cikin kwana ukku ya sauke, san Aƙalla yana sauka cikin Azumi fiye da goma, turo ƙofar palon tayi a hankali, muryarta ciki tayi Sallama kwata-kwata bata yi tunanin zai ji ba, kuma bai nuna mata alamar ya jin ba, tsareshi da manya-manyan idanunta tayi, tana kallon zubin Halittar da Allah ya zuba mishi.


Kamar daga sama yace "baki san ni bane ?", ya fada ba tare da ya bude idonshi ba, kallon gefe-da-gefenta tayi kafin ra ƙara kallonshi, dan sam bata ga lokacin da ya bude ido ba, ta yi imanin kuma bai ji shigowarta ba, to ko dai Aljani ne ?, in ba Aljani ba ya yayi yasan da shigowarta, Al halin bai bude ido ba bai kuma ji motsinta ba, "kar ki bari na ƙara mgn", ya fada fuska a tsuke, a hankali cikin kasala take takaww izuwa cikin palon, cikin natsuwa ta jaanyo center table gabanshi ta ajiye tray a kai, zama tayi a gefen kafarshi , cikin ɗari-dari.


gently ya bude idanunshi , bowl ya jawo tare da sanya pork , yakoma ya jin gina.
ƙafafunshi ya daura akan cinyarta, kallonshi tayi ,amma idanunshi a lumshe, tura baki kaɗan tayi tare da sanya hannayenta da gumi ya baibaye, ta fara mammatsa mishi ƙafafun, ɗumin da yake jikin hannunta na ratsa ƙafafun nashi.
cikin natsuwa kuma yake shan yankakkun fruits dinshi, bai ci komai ba shi kawai ya sha , janye ƙafafunshi yy daga kan cinyarta, numfashi ta sauke a hankali san dama ta gaji.


nuna mata kusa da shi yy , cikin natsuwa tamiƙe daga in da take zaune ta zauna a in da ya nuna mata, zame kanshi yy ya daura akan cinyarta,tare da kamo gaba daya hannayenta ya cusa cikin gashin kan nashi.


lumshe idanunta tayi,sakamakom zafin da ya ratsa yatsunta,wanda hakan na mata nuni da cewar ciwon kai mai tsanani yake, a hankali ta fara cusa hannayenta chan cikin gashinshi,har ta samu nasarar taɓo fatar kan nashi, "Du'a zaki min", ya fada idanunshi a lumshe, itama rufe nata idanun tayi, bata kamun kai Amma ya ta iya tun da shine ya sa ta mishi, cikin natsuwa ta kama gaban goshinsa, tare da fara tofa mishi Addu'o'i cikin kwarewa,da sanin Addininta.
tana gama mishi kamun kan, ta rumtse idanunta da azabar ƙarfi, bakinta ne ya fara rawa, dan danan tsikar jikinta ta tashi,naman jikimta ya fara wata kalar rawa, dan danan ƙafafunta suka fara ƙaƙƙamewa, duk abun da take, yana jin ta Amma yy shiru kamar bai sam mai yake faruwa ba.


dauke kanshi yy daga kan cinyarta, yana daukewa ta miƙe da gudu tayi waje, cikin hanzari ya bude idanunshi da suka sauya kala,miƙewa yy cikin Azama ganin ta nufi waje.


Da sauri ya biyo bayanta, yana mai ƴara sassarfa , sanadiyar ganin da yy zata fice Compound gashi ko suturar kirki bb a jikinta, kafin ta fito har ta doshi babban get din gidan.


ƙoƙarin fara bude get ta fara, da sauri get man fa riƙeta, wani kalar runtse ido Yaa Shehi yy lokacin da ya ga Get man din y damki hannunta , ji yy kamar an soki zuciyarshi da wani abu, kishinta mai tsanani ya luluɓeshi, yana ƙarasawa gareta, ya zura mata Alƙyabbar da ya gani a palon ƙasa, tare da jaaan hannunta , tana turjewa da komai haka ya riƙe mata hannu izuwa cikin palon gidan.
tsaitsaye ya tarar da su suna shirin fitowa waje, "Mai yake faruwa da ita ne ?",Ayyana ta tambaya tana kallonsa.


"Kamun kai...", cikin fada ta fara cewa "Amma ai kasan ba'a sanyata yin kamu ko ?,kasan matsalar da hakan yake jawowa ", bai ko saurari

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment