Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shehi.


Zaune ya sameshi, ya tanƙwashe ƙafafunshi, idanunshi a lumshe yana ta Istigifari , da Sallama a bakinshi ya ƙarasa gaban Yaa Shehin da ya lumshe idanunshi, a hankali ya amsa Sallamar Zayn chan ciki, wanda in ba ka saurara da kyau ba ba zaka ji sadda ya amsa Sallamar ba.


gaban Shehin ya ƙarasa tare da ajiye tray din a ƙasa, yace "Sannu da hutawa Yaa Shehi..!", bai bude idanunshi ba, kuma bai Amsa mishi ba. gefenshi Zayn_Maleeq ya zauna ya nannaɗe ƙafafunshi ya dan jaaa numfashi, yana kallon Shehi.


kusan 10minutes Yaa Shehi bai bude idanunshi ba,bai kuma yi mgn ba, kallonshi yy yace "Yaaa Shehi Yunwa",ya fada yana dan yatsina fuska,bude idanunshi yy tare da jaan tray din, ya fara bude plate tare da ajiyewa a ƙasa. wormers din ya fara bubbudewa, Tuƙaƙƙen Tuwon shinkafa da ya haɗe jikimshi yana daure a leda ya bayyana, daya ya dauka tare da budewa ya daura akan plate, dan bowl ya dauka, tare da bude ƙaramar Wormer kalar babbar Wormar din da ya fiddo tuwon.


buɗe Wormer din yy lafiyayyiyar miyar Kase ce ta bayyana,sai kamshi take ta ji name zuƙul-zuƙul sai turiri yake, hannu Yah Shehi ya dauraye cikin wata yar tasa, tare da gutsiro tuwon, ya sanya cikin miyar ya fiddo tare, da nufar bakin Zayn_Maleeq, da sauri Zayn ya gyara zamanshi, ya dawo gaban Yaa Shehi sosai, bude bakinshi yy, cikin soyayyar Yan Uwantaka ya fara bashi tuwon yana ci, har ya cinye leda daya, kallonshi yy tare da mishi lamar ya ƙoshi girguza kanshi yy .


hakan yasa ya kara bude wani, tare da gutsirowa, jin da zafi yasa ya dan busa mishi da iskar bakinshi, ya ci gaba da bashi,zufa ce ta fara tsatsafowa Zayn_maleeq na ƙoshi, sanyayyiyar gyatsa ya saki tare da cewa " ```Alhamdulillahi Ala kullu Halin ...!``` ", ya fada yana dan jaaa baya, sanyayyayen Lemun Kwakwa da yaji madara Yaaah Shehi ya zuba mishi , dauka yy ya sha, yana lumshe ido sa boda sanyin da ya ratsa maƙogwaronshi.


baya ya Jaaa tare da jingina kanshi da jikin kujerar da Yaa Shehi yake zaube ya fara sauke numfashi, tuwon shima ya ci kaɗan dan ko loma biyar bai yi ba, duk kuwa da cewar yana jin yunwa dan tun Coffeen safe bai ƙara cin komai ba.

Amma kasantuwarshi na ba ma'abocin cin Abin cin mai nauyi bane, musamman in zai kwanta bai iya cin Abin cin ba.


bayan ya gama ya tattara komai cikin tray din ya miƙawa Zayn_Maleeq , ba tare da yace komai ba, ganin ya miƙa mishi gabanshi yasa ya dauka yy Downstairs domin mayar da kayan abin cin.


bayan ya ajiye ya zauna gurin Sayyid da suke zaune suna kallon ball....


sai guraren 11pm kafin ya miƙe yy Sama suma bin bayanshi suka yi, yana zuwa ya tarar da Yaaa Shehi na Bathroom hakan yasa suka kwanta akan bed dinshi, sai da suka yi Addu'o'i kafin su rufe idanunsu, suna Tasbhi kamar yarda Yaa Shehi ya koyar da su dan basa barci matsawar basu yi Tasbhi ba, barcin ma gaba daya baya zuwa amma da sun fara sai ya daukesu.


har suka yi barci bai fito ba, sai da ya ɓata kusan 1 hour kafin ya fito, cikin Jallabiya Maroon da tayi mishi masifar kyau, idanunshi da suke cike da gajiya da barci ya dan jaanye tare da lumshesu, ƙarasawa yy gurin bed din, sai da ya sake musu wata Addu'ar ya shafe musu jikinsu, ya jaaa musu duvet kafin ya kwanta a gefensu, kashe glove yy tare da fara karanta "```SUBHANALLAHIWA BI HAMMADIHI SUBHANALLAHIL AZEEEM```", haka ya ringa mai maimatawa, hae barci mai dan nauyi ya daukeshi.


```Washe gari```



wannan book din na kuɗi ne, ki dage ki siya domin karantawa, dan na tabbarar zaki fa'indantu da wani abu.


07033371851


Wanda ya shirya siya kawai pls.


DAGA TASKAR ƳAR LELE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼



*DAGA ALƘALAMIN*


SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️.


```SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA . SADIYYA ABBAKAR MARU(ƳAR GATAN ROYAL STAR🌹🌹)```



*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*



*P. 6*



``` Washe gari```


Gurin 9am Yaaa Shehi ya fara takowa daga Upstairs zuwa Downstairs , sai baza kamshi yake, har kullum yana sanye da Alƙyabbarshi ruwan ƙasa ciki kuma ya sanya wata Milky din Shadda Gizna sai wani irin maiko take, yana tafiya yana barbaza Alƙyabbar jikinshi.


Umma Jakadiya ce ta dan tsareshi da idanunta, tana dan murmushi tace "barka da hantsi Shehin Malamin mu..!", ta fada cikin bada girma, dan kallonta yy tare da jinjina kai, sai da ya kusan ficewa kafin ya tsaya cikin Yar daga murya yace "Umma kin shirya ?", cikin girmamawa tace "da izinin Allah", jinjina kanshi yy tare da ficewarshi.


A hankali cikin natsuwa da ciƙar kamala yake tafiya, bakinshi kuma na motsi, dan saurarawa nayi, sai da nayi dan shiru kafin naji yana cewa " ```SUBHANALLAHI WA BI HAMMADUHI ADADU KHALƘIHI```" haka yake ta maimaitawa har ya fito wajen Masarautar
, Jerin Gwanon Motocinshi duka suna parker a ƙofar shiga part dinshu, wanda kuma duk shi suke jira,wannan jaron 4Matic GRL 350, aka bude mishi.


shiga yy tare da hakimcewa, ya baza Alƙyabbar jikinshi, Sayyid-maleeq Abdul-maleeq da Zayn-maleeq kuma suka shiga motar bayanshi, wadda itama ta kasance 4matic din sai Motar bayansu kuma ita Ummu da wasu Kuyangu Ukku suke ciki,a hankali motocin suke tafiya, har suka fita daga get din Masarautar.


bayan fitarsu daga Masarauta Abuja road suka nufa direct dan sai sun koma ta chan jirginsu zai tashi, fira ce ta barke tsakanin Zayn da Yan uwansa, dan dama in kaga firar su Sayyid to da Zayn ne ko kuma Shehi ko Yayarsu Babba da Yaranta.

haka suke fira har suka ƙarasa cikin garin Abuja, basu zarce ko ina ba sai wannan Asibitin dai. A mota duk suka tsaya Shehi ne kawai ya fito daga motar zuwa cikin Asibitin, Office din Dr din ya nufa direct,bayan gama Yan maganganun da zasuyi ya miƙe ya fito , Dr din na bayanshi har suka fito daga cikin Asibitin, direct gurin motarshi ya nufa, sai da suka ƙara yin musabha da Dr din kafin ya shiga motarshi suka wuce International Airport din da yake nesa kaɗan da Asibitin.


lokacin da suka ƙarasa bai fi saura 10 minutes jirginsu ya tashi ba, hakan yasa suka shishiga suka zauna zaman jiran tashin shi, lokacin tashin jirgin nayi, ya fara tafiya, tare da lulawa sama.
Lumshe ido Yaa Shehi yy yana fesar da sanyayiyyar iska daga cikin bakinshi.


tasbhi ya fara tare da kirari wa Mahaliccin Sammai da Ƙassai , har zuwa wani lokaci, VIP side.
Umma Jakadiya ma idanunta lumshe suke kamar mai yin barci, Zayn-maleeq na gefenta kunnenshi manne da Ear pie, yana sauraron karatun Al-qur'ani mai girma , sai su Sayyid-Maleeq da suke kujerar gefensu, kowa ya natsu yana abu mai muhimmanci.


4 hours chif ta saukesu, a cikin birnin garin Madina, bayan sauƙar jirgin da wasu mintoci, aka bude ƙofar jirgin, a hankali ciƙe da gajiyawa da zaman cikin jirgin mutane suka fara fitowa daga cikin jirgin, kowa fuskarshi washe da murmushi,kusan sai da kowa ya gama saukowa kafin Yaa Shehi ya fara taka Steps din jirgin a hankali cikin natsuwa da kamalar da ta zame mishi jikinshi, kanshi a ƙasa, yana baza Alƙyabbar jikinshi mai kyau da tsari, har ya gama saukowa daga kan Steps din, yana diro da ƙafarshi daga kan steps din, Yan Jaridar Ƙasar Madinah suka mishi Caaaaa, a kanshi,lafiyayyu kuma firgitattun idanunshi masu dauke da kwarjini tare da zallar haiba ya watsa musu, yana ci gaba da tafiya a hankali.


Ciƙe da murnar dawowarshi suke mishi tambayoyi, Amma ya gagaraa Amsa musu ko Tambaya daya, su ma kansu sun san halinshu ba mutum bane mai yawan magana, in kaga maganarshi to Karatu yake, mafi aka sarin maganarshi da ido yake yinta ko da hannu.


"Fatan Yaa Shehi ya sauka lafiya..?" , duk suka dauka bakin dayansu, gentle ya lumshe idanunshi, tare da dai-daita kyawawan lips dinshi masu taushi da sheƙi, ya furta "Alhamdulilah..!", ya fada chan ciki, wanda sai kayi dagaske zaka iya jin mai yace, sai dai motsin kyawawan lips dinshi ne zai nuna maka alamar mgn ya yi.


jinjina kansu suka yi cike da tsananin gamsuwa tare da kaunarshi, haka suka rakashi har gurin manya-manyan motoci kirar Benz da aka zo daukarshi da su, Zayn-Maleeq ne ya bude mishi ƙofar motar.


ciƙe da dattaku tare da zallar natsuwa ya kimtsa kyakyawar fuskarshi, shi bai saketa ba, shi kuma bai daureta ba, yana yi mai wuyar fassarawa, wanda ba kowa ne ke iya fassara irin wannan fuskar ba, sai wanda ya karanci ilimin Halayyar Dan Adam.


dai-daita zamanshi yy tsakiyar nack site din, tare da jinginar da kanshi jikin kujerar ya lumshe idonshi, a hankali ya furta, "Subhanallah wal hamdulilah wa laa'ila ha illalahu wallahu Akbar", ya furta yana dan jaan igiyar wuyan Alƙyabbar jikinshi, ya sassauta matsewar da ya mishi.


Zayn-Maleeq da Umma Jakadiya motar bayan Yaa Shehi suka shiga, ya yin da Sayyid_Maleeq da Abdul-Maleeq suka shiga ta bayan tasu Zayn, bayab tasu motar akwai biyu toyota a bayansu, da kuma ukku gaban motar Yaa Shehi, wanda gaba dayansu Escort dinshi ne a ciki.


a jere motocin suja fara tafiya a hankali har suja fita daga tafkeken Airport din wanda ya zama International Airport , kan titi suka hau, tare da fara tafiya cikin wani kalar speed , a hankali Yaa Shehi ya gyara zamanshi, tare da dan gyaran murya.


gane nufinshi yasa Driver da ya kasance Balarabe sanye da baƙin rawani ya fara sai-saita gudun motarshi, ganin hakan yasa gaba daya sauran motocin suka shiga taitayinsu, tare da dai-daita tafiyarsu, dan Yaa Shehi bai fiye son gudu da mota ba , sakamakom in ana gudu sai yaji kanshi na juya mishi.


har suka shiga cikin garin Makka yana lafe jikin kujera idanunshi lumshe, har suka zo cikin gari ss.
Hanya ce ta rabu ukku, daya wadda zata kai ka Massalacin Makkah, daya gidan Sarkin Makkah dayar kuma cikin gari, hanyar cikin gari sauran motocin suka yanke suka bi, ta Yaa Shehi kuma direct hanyar da zata sadasu da gidan Sarkin Makkah suka nufa, dan suna da babban taro na Manya-Manyan Malaman. da Limaman garin Makkah.


bai ko motsa ba sai sa suka ƙaraso tafkeken get din gidan, da Jami'an Tsaro suka daddaɓe suna zagayanshi ko da zasu ga wani abuj cutuwa, tsayar da motar Yaa Shehi suka yi, ko da suka leqa ta win door suka ganshi, da sauri suka basu hanyar wucewa, dan Yaa Shehi sananne ne a cikin Ƙasar har ma da kewayenta
.


Kai tsaye Driver ya shige da motar cikin gidan, sai da ya dai-daita Parking a cikin manya-manya motocin da suke tsakiyar gidan , sai da ya fito ya budewa Yaa Shehi nota, kafin ya juyo ya kalli Yaa Shehi da idanunshi suke lumshe yace "Mun ƙara so..", ya fada a hankali .


bude idanunshi ya bude tare da fesar da numfashi a hankali, ya zuro zara-zaran kafafunshi waje, kusan 5 minutes kafin ya zaro gangar jikinshi daga cikin motor, ya fito baki dayanshi, yana dai-daita zaman Alƙyabbar jikimshi ya bazata.


A hankali ya fara takawa, yana fesar da numfashi, har ya ƙarasa wani tafkeken ƙofa, da wasu manya Sojoji suke tsaronta, ganinshi yasa suka wangale mishi ƙofar shiga, a hankali ya zare Cover shoes dinshi na Alfarma, kafin ya zira kyakyawar ƙafarshi cikin palon da Bissimillah akan harshenshi, a hankali ya furta "Assalamu alaikum..!", ya furta yana dago da zara-zaran Eyes lashes dinshi, da manyan kyawawan idanunshi farare masu dauke da nau'in blue din eyes ball.


ciƙe da tsantsar mutunta juna suka Amsa mishi, da dan murmushi kan fuskokinsu, "Haaaaa..!", ya furta a hankali ba tare da bari sautin ya fita ba.


ƙarasawa cikin palon yy , hannu ya fara binsu daya bayan daya yana basu suna musabha, tare da side hug na al-adar larabawa, ko da ya ƙarasa gurin Sarkin Makkah sai ya dan risinar da kanshi alamar ban girma, murmushi yy , yana son Wannan girmamawar da Yaa Shehin yakw mishi, shi yasa yake ƙara kaunarshi, domin shi mutum ne mai son mai girmamashi tare da girmamashi shima.


Kujerar da take kusa da Sarkin ya nuna mishi, tare da cewa "ga gurin Zama Yaa Shehi Maleeq..", kallon kujerar yy , tare da mishi dan godiya da murmushi, kafin ya zauna.
gaba daya Sauran Limaman kansu daurewa yy , dan su sun dauka kujerar ta Sarki ce, domin dukkansu, bb wanda ya zauna a irinta sai shi.


A hankali, Sarkin ya shiga Gabatar da Abun da ya tarasu a kanshi, bayan gama maganarshi , suka dan yi maganganu da suka danganci Azumin watan Ramadan, bayan gama tattaunawa ne , aka zaɓi wanda zasu gabatar da Sallar Tarawidhi, an Zaɓi mutane da yawa wanda aka tabbatar da Babu wani Babban Uzuri a kansu lokacin, bayan gama zaɓarsu aka zaɓi wanda zasu gabatar da Sallah Ƙhiyamullal . shima aka zazzaɓa Yaa Shehi dai na Zaune ban da yamutsa fuska bb Abun da yake, dan ya ƙaragara a tashi taron Sa boda gajiyar da take ɗawainiyya da gangar jikinshi.


Bayan gama komai, kowa ya Natsu domin Sarki zai fitar da wanda zai zama Special Imam, wanda shine mai Jaan Sallah sai dai in da wani Babban Uzuri kafin wanda aka zazzaɓa su maye gurbinshi, ba Tarawidh kaɗai ba har Ƙhiyamullal, manyan Limamai duk sun Natsu , kowa na fatan Zama wannan Imam din, sai dai Yaa Shehi ko a jikinshi ma, dan idanunshi a lumshe suke yana ta kirari ga Allah, wanda in ba ka lura da yarda yake sauke numfashu ba zaka rantse barci yake.


Azahiri kuwa duk Abun da suke yana sauraransu, yana kuma kallonsu ta ƙasan Ido, sai dai Uffan bai ce da su ba, tun bayan gama gaggaisawa da suka yi, ya zauna,bai ce komai ba.


kallonsu gaba daya yy, kafin yace "A wannan shekarar Yaah Shehi Arman_Maleeq ne zai zanto Shugaban Limamai, shine zai dunga fitar da tsare-tsaren da za'ayi Amfani da su, sannan shine Special Imam, muna roƙon Allah ya taya shi Riƙo", ya furta idanunshi akan saurarn Imam's din.


kallan-kallo sukawa junansu, kafin su taya Yaa Shehi da idanunshi suke lumshe murna, bayan gama taya murna, Sarki ya musu kyauta, kafib suyi Sallama su fice, sai da duk suka fice kafin Yaa Shehi ya sauke nannauyar Ajiyar zuciya, kallon Sarki Tajjudeen Abdulgaffar Ya yi, tare da cewa "Shukran laka Yaa Sayyadi", ya faɗa yana mai fadada fuskarshi, sai dai ba murmushi bane akan fuskar.


Dukan Kafadarshi yy, kafin su miƙe, yana dan mishu Jawabai , ga mai da shirye-shiryen, bayan gama maganganunsu, aka ƙara mishi Escort da motoci, Sannan aka bashi lafiyayyiyar mota, Kirar Campanyn Audi, tare da kyautar babban gida a kusa da Babban Masaalacin Makkah wanda bazai mishi wahalar zuwa ba daga Masallaci.



godiya Sosai yawa Sarkin kafin ya wuce, direct ........



NA KUƊI NE, DUK MAI SO ZATA IYA MIN MGN SAI NA TURA MATA ACCOUNT DETAILS.


07033371851


IN KIN SAN BAKI SHIRYA SIYA BA PLS KAR KI MIN MGN MU BATA LOKACINMU.


DAGA TASKAR ƳAR LELEN ROYAL STAR.

RUWA NE KAWAI YAKE MAGANIN ƘISHI🤙🏾
[2/22, 5:33 PM] ƳAR LELEN ROYAL STAR CE🧚‍♀️🧚‍♀️: 🌼🌼ARMAN MALEEK🌼🌼


*DAGA ALƘALAMIN*


SALMAJI ƳAR LELEN ROYAL STAR CE 🧚‍♂️🧚‍♂️🧚‍♂️



SADAUKARWA GA AMINIYATA MASOYIYATA, SADIYYA ABBAKAT MARU (ƳAR GATAN ROYAL STAR CE🌹🌹)


*🌟ROYAL STAR WRITER'S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*



*P.7*



Godiya yy sosai, kafin ya wuce tulin Escort dinshi na binshi a baya,kafin ma ya ƙarasa gurin Moto din shi an buɗe mishi mota, yana zuwa ya shiga da Bissimillah, rufewa aka yi, kafin suma duk suka shige motocin da suke bayan tashi da gaban tashi, a hankali suka fara tafiya cikin ƙwarewa.


Asalin gidanshi da yake babbar Anguwar Shara-Mansir da take cikin Makkah suka wuce da shi, idanunshi na lumshe har suka ƙarasa tafkeken gidanshi da yake cikin Anguwar, gida ne babba na gani na faɗa,gaba daya gidajen da suke kewayen Anguwar gidan shine the number 1, z gurin kyau da tsari, har da wasu akwakun fitilu , masu kyau sai kaloli suke badawa.


Sun danno kai gurin gidan gaba daya get din gidan mai kyau da tsari ya yaye yy sama, cikin natsuwa suka sulala da motocin cikin gidan , sun dan yi tafiya mai dan nisa kafin su iso Asalin cikin gidan wanda shima take dauke da wani get din, hon suka yi , wanda yasa da sauri Get man din gidan ya rugo ya bude musu get din.


sulalawa suka yi ciki, suna shiga wani babban parking alot mai kyau da tsari wanda yake cike da motoci masu kyau kala-kala ya bayyana, gaba daya motocin a wajen parking alot din suka tsaya motar Yaa Shehi ce kawai ta samu guri cikin parking alot din.


bayan Driver ya dai-daita parking a cikin parking alot din, aka bude mishi mota, a gajiye yake sosai, hakan yasa bai ɓata lokaci ba gurin fitowa daga mota, A hankali ya fito yana baza Alƙyabar jikinshi, cike da tsantsar gajiya yake dan lumshe gajiyayyayun idanunshi, tare da fesar da sanyayyiyar iska,haka har ya zo daf da ƙofar shiga cikin palon part din.


tsayawa yy na yan mintuna, sai da ya ji takun Driver din shi kafin ya juyo, tattausan hannunshi ya miƙa mishi, brief case din shi ya miƙa mishi, karba yy kafin yace "Jazakhallahu bi khair..!", yana fadar haka ya juya ya shiga ciki.



chan ciki yy sallama cikin muryarshi sanyayyayiya mai dauke da zallar gajiyawa, "Wa'ailaika Salama..!", wata Babbar Mace da zata iya kai wa 29 years ta furta cikin sanyin hali, idanunshi ya sauke akan fuskarta mai dauke da murmushi, ta gefenta ya wuce yana sauke numfashi, bata yi mgn ba har ya haye Upstairs.


A hankali ta miƙe, kitchen ta nufa, bata jima ba ta fito da madaidaicin flask , da Ƙananan Cups sai kwalin Sugar da Tea spoon, saman ta haye, ƙofar farko ta kwanlwasa tare da tura ƙofar , haɗaɗɗen palo mai kyau da tsari ya bayyana, sanyayyan kamshi tare da sanyi ACn cikin palon ne ya haɗu ya gauraye Palon tare da bada wani ni'imtaccen kamshi mai sanyaya zuciya, tare da sanya natsuwa.


kan daya daga cikin royal chair din palon ta zauna, tare da jaawo Center table ta daura tray mai dauke da flask da cups, jiranshi ta shiga yi, ganin an share 1 hour, bai fito ba yasa ta miƙe ta fita, tana fita ba da jimawa ba, ya turo ƙofar bedroom din ya fito, yana ta baza kamshi, yana sanye da Jallabiya fara tass da wando, kanshi yana luluɓe da hirami red da ɗigon fari, hannunshi zube cikin Aljihun Jallabiyar , sai zuba kamshi turaren huge boss yake, fuskarshi na fitar da wani Annuri da haske mai daukar hankali , yy wani fitinannen kyau , yana tafiya kanshi a ƙasa, yana tasbhi da baya rabuwa da bakinshi.



zama yy kan kujera yana fesar da numfashi, jinginar da kanshi yy , tare da zame lips dinshi na kasa ya zamana yana cikin bikinshi, a hankali ya fara tsotsa cikin wani salo na musamman, wanda za'a kiranshi da Sexy moment , shi kuwa zallar gajiya da yunwa ce ta sanyashi yin hakan, dan rabonshi da abin ci, tun jiya war haka.


Wayarshu ƙirar Iphone 13 pro, ya dauka a hankalin tare da daddana number, ring daya biyu a na ukku ta dauka cike da natsuwa tace "Assalamu alaika..!", "Wa'alaiki salam..!, Yunwa", ya furta da daddare.


Yana ajiye wayar ta shigo sanye da hijab dark Blue , ta ziro siraran hannunwanta ta cikin hannun hijabin, fara ce sosai, sai dai tana da dan jiki ba laifi a shekaru ba zata gaza 16 years ba, colour ba Hijab din shi ya fidda Asalin kyan fuskarta, zagayayiyyar fuskarta ta fito rass ta cikin dan wuyan hijab din, tana tafe tana fitar da kamshin humra mai masifar kamshi.


Sallama tayi,chan ciki ya amsa mata ba tare da ya bude idonshi ba, tana ƙarasowa tsakiyar palon ta cire zunbuleliyar hijab din jikinta, ta ajiye akan kujera 1 sitter, kyakyawar surar jikinta mai kyau da tsari da ta gama haɗewa cikin ɗamammum kayanta, masu kyau.
sanye take da riga fara body hug , sai black din wando skin tight ya bala'in dameta shima iya cinya.
gaba daya surar jikinta da ta kasance coca-cola a bayyane, jikinta sai glowing yake.


ƙarasawa tayi kusa da shi, tare da dan zama ta shige jikinshu, a hankali ta furta"Shehi..!", idanunshi ya dan matse a hankali ta daura yatsun hannunta da suka sha jaan lalle akan fuskarshi tana bin sajenshi da yatsunta, tare da jaa

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment