Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TAKE ZUWAR WA MUTUM A RAYUWARSA* .

na lura kin rasa wanda zai faɗa miki gaskiya shi yasa kullum haukarki da Yarintarki suke ƙara jaanki , ki daina ganin yana yage miki baki yana sakar miki jiki ,Wlh daga ranar da ya gano cin kashin da kike mishi ba zaki kara jin dadin zama dashi ba, gwara ki zauna kiwa kan ki karatun ta natsu", ta fada tana wulla mata kayan da ta shigo dashi a hannunta.



Shiru tayi tana bin bayan Umma Jakadiya da kallo, sai taji kamar ta haƙura tabar konai sai taji bazata iya ba, tayi Alƙwarin gaskiya bazata ci gaba da zama dashi ba in kuwa ta zauba to sai dai su ci gaba da zaman da suke yanzu , dan bazata kara bari ko hannunta ya taɓa ba, dudduba kayan da Umma ta kawo mata ta shiga yi, duk da Express ne ɗinkin Amna ya yi kyau sosai, an mata su kamar na Amarya.



Guraren 1am Anty Rayhana tazo ta sameta zaune tana latsa waya, kallonta tayi tace "Anty!", "ba wata Anty sai gaskiya in da ni Antynki ce ai da kin yi abun da na sanyaki", shiru tayi bata ce komai ba.


"ni dai yanzu Anty muje amin lalle na, san kinsan gobe Sallah kuma tun yau zamu fara aiki", ta fada tana jaan hannunta, miƙewa tayi suka fito palo, nan suka tarar da su Zayn, "Zayn ko zaka siya mana Baƙin Lalle da jaa a Super market din nan ?", ta fada tana kallonshi, "ina ma da Jaan da nazo dashi", "to siyon baƙin", ta fada tana zama gefe.



"Amma fa kin san Yaah Shehi baya son Baƙin nan ko ?", Anty Rayhana ta faɗa tana kallonta, "ni badan shi zan yi ba ai", dariya ta dan yi tare da cewa "to dan wa ?" , "ni dan kaina zan", ficewa yy domin siyo mata.


Chan bai fi minti biyu da fitw ba ya dawo, kallonshi Sadiyyerh tayi tace "ina lallen ?", yana kallon wayarshi yace "Yaah Shehi ne yace , in na sake na siyo sai ya saɓa min", tsuka taja tare da cewa "ni ban san mai yasa yake son takurawa Rayuwata ba haaaba", ta fada cikin mugun takaicin da ya luluɓeta.
"Tun da yace kar a siyo nima bazan zanashi ba, yanzu dai dauko min Jaan a cikin Jakata a ɗaki ki kawomin A kwaɓa Lallan", ta fada tana gyara zamanta,ba tare da musu ba Sadiyyerh ta miƙe ta shige ciki, bata jima ba ta dawo hannunta dauke da wata babbar leda .


miƙawa Anty Rayhana Ledar tayi, "ɗibo min ruwan zafi", bb musu ta kara wucewa kitchen bata jima ba ta dawo da cup mai dauke sa ruwan zafi sai turiri yake, miƙawa Anty Rayhana tayi, ta zauna a gabanta, tana mai daura fararan ƙafafunta da suke tass kan wani babban pillow .


Anty Rayhana da kanta ta kwaɓa musu lallan , bayan ta gama ta fara zanawa Sadiyyerh Flowers masu kyau sosai, a hannunta , suna yi suna fira, amma Sadiyyerh tayi gum da baki ta sa boda haushin da take ji, ta kuma kuɗurta sai tayi baƙin, ko wani guri ne sai taje an mata sa boda ta ƙuntatawa Rayuwar Yaah Shehi in ya gani tunda shi baya so
.



sai da aka gama zama mata a hannunta, kamar Anty Rayhana tasan mai take tunani ta fara zana mata Jaan ma a bayan hannunta, kamar zata tsalla ihu kallonta tayi tana shagwaɓe fuska, dariya tayi ba tare da tace mata komai ba.



bayan an gama na hannun ta fara mata na ƙafa, bayan an gama aka sanya mata leda , tana zaune nan Anty Rayhana ta tafi gurin su Ayyana suna aikin Sallah, ita kuwa suna palo, gajiya tayi da shirun da bakintw yy kawai sai ta biyewa su Zayn suka ci gaba da firarsu, har sai da lallanta ya kama sosai ta cire, Maa sha Allah, lallan ba ƙaramin kyau ya mata ba, ta fito sosai, miƙewa tayi ta shiga kitchen bayan ta wanke, "Kaiiiii haka lallan nan ya yi kyau, gaskiya nasan Yau Yaaah Shehi har kyauta zai min in ya gani," cewar Anty Rayhana cikin tsokana, turo bakinta tayi tana ci gaba da aikinta, "baki ce komai ba ?", "Allah Anty zaki san har ya goge bai ganshi ba tom ", ta fada rana wani cin magani.


dariya kawai Anty Rayhana tayi va tare da tace komai ba, Ayyana ce tace "Rayhana gobe ki kitse mata kan nan nata pls , ya yi tozozo da yawa","Tom Ayyana", ta fada tana yanka flower din da take yanka cin cin.


"ni yanzu mai zan yi ?, naga Anty na yanka cin cin", ta fada tana kallon Umma Jakadiya, "Samosa dasauran aikin gobe ke zakiyi komai ", numfashi ta fesar, kafin ta fara haɗa flower din Somaso sai da ta gama , kafin ta ɗibo namanta a Fridge da wankeshi sosai, ta sanyashi a tukunya ta daura a gas, magi ta dan zuba, kafin ta koma kan carrot din da ra fiddo, wankewa tayi , ta fara yanyankashi ƙanana sosai, lokacin da ta gama , naman ya tafarfasa, tsameshi tayi ta mayar da carrot din shima ta dan dafashi sama sama.

lokacin da zata fama tafasashi ta gama daka namanta, kwashewa tayi ta ajiye a gefe, Fran fam ta daura kan gas ta zuba mai ba wani mai yawa ba sosai, Albasa ta dan zuba, sai da manta yy zafi kafin ta fara zuba namanta.
bayan ta gama ta zuba Carrot , magi da kayan kamshi ta zuzzuba , bayan ta gama soyashi sama-sama...........
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 21*




Bayan ta gama soyashi sama-sama ta kwashe ,Fran ta kara daurawa, ta matsa da kwaɓaɓɓan Fulawa dinta, brush masu taushi guda biyu ta samu daya ta sanyashi cikin bowl din da ta zuba mai, dayan kuma cikim robar fulawa.


na man ta dauka ta shashafa a cikin Fran din, bayan yy zafi ta dauki na cikin fulawar ta fara shasshafawa, yana dan fara soyuwa take daukewa tasa wani, ficewa duk suka yi , sakamakon gama aiyukansu da suka yi.


After 1 hourAnty Rayhana ta shigo, riƙe baki tayi tana kallon yarda take , "wannan ai baza kiyi sauri ba ke daya gashi da yawa, bari na taya ki", ta fada tana kunna dayan side din Cooker din, Fran ta daura ta fara tayata suna yi suna fira har suka gama.


yayyankaww suka fara , Anty Rayhana tana zuzzuba kayam haɗin tana liƙewa da kwaɓaɓɓiyar fulawa, tana yi Sadiyyerh na soyawa,sai gashi sharp-sharp cikin 2 hours suka gama, tattara komai suka yi suka adana.


"Sauran aikin fa ?", ajiyar zuciya ta sauke tana share zufar fuskarta tace "Ayya Anty wlh na bala'in gajiya ki bari in kika gama min kitson muka yi Sallah tum da lokaci yy sai na ƙarasa ", kallonta tayi kafin tace "kin san dai Yaah Shehi sai ya ci Abin ci zai fita ko ?", taɓe bakinta tayi, kafin tace "uhmmmm ban sani ba sai yanzu ", ta fada tana taɓe baki.


dukan kafadarta tayi tana dariya tace "zama ko sani ai yar Jakar Uba",A tare suka fice daga cikin Kitchen din.


kowa Bedroom dinshi ya nufa, Wanka Sadiyyerh ta fara yi dan har wani zufa-zufa take ji, Alwala ta dauro ta fito, ledar kayan da Yaah Shehi ya kawo mata ta jawo dubawa ta shiga yi, yatsina fuskata tayi, lokacin da ta fiddo wani black lass mai ratsin Ash da red , ɗinki Abuja Bubu da yy masifar fitowa da lass din an yi planting back din tun daga mazaunai har ƙasa, ɗinkin yy mata kyau ss.


fito dashi tayi, zip din rigar ta bude "Allahumma lakalhamdu anta kasautani hi, as'aluka min khairihi wa khairi ma suni alahu. wa a'uzubika min sharrihi wa sharrima suni a lahu" , ta furta ya yin da take saka kayan a jikinta, cif suka zauna cikim jikinta, tayi wani irin kyau, kanta ta gyara ta sanya dan kwallin a kanta ba tare da ta daura ba .


kalolin turaruka ta fesawa jikinta, wanda ita kanta ta gamsu da kamshin da jikinta yake yi ɗari bisa ɗari, plat shoe ta sanya , kai tsayevwaje tayi abunta.


tana fita waje wani kamshi ya daki hancinta, idanunta ta daga da sauri lokacin da taji saukar haɓɓarshi akan kafadarta, "wa'iyazubillah " ta furta a hankali tana lumshe idonta.


"Sadiyyatouh!", ya furta mata cikin kunnuwanta, ƙiris ya hana ta fasa ihu sa boda yarda tsiƙar jikinta yy wani mugun tashi
, idanunta ne suka fara kawo ruwa
, yunƙirin kwacewar ma da take kwana biyu yau bata yi ba, numfashi ya fara saukewa, yana manna lips dinshi da wuyanta a hankali ya furta "wai rigimar mene haka ?", ya fada yana lumshe idanunshi
, " ni ka sake ni", ta fada tana ƙoƙarin fisgewa, kara mannata da jikinshi yy yana shaƙar kamshi turaren jikinta da yake sanyaya mishi zuciya, jikinta yy wani mugun sanyi.


"uhmmm ni bazan sake ki ba", hawayen idanunta na zuba ta sanya hannu zata zame mishi hannunshi da yake kan jikinta, riƙe hannunta yy yana kallon lallanta da yy mishi wani irin kyau, hsnnun ya ƙara a bakinshi tare da bashi wata sumba mai kyau.


" ni ka sake ni, kar ka ƙara taɓani bana sonka , bana kaunarka mayaudari kawai", ta fada hawaye sharrrr na zubo mata, wani abu mai kama da mashi yaji ya soki ranshi, "bana sonka , na tsaneka!", ita ce maganar da ta ƙara dawowa dashi hayyacinshi bayan jin waccan maganar tata.


janyewa yy daga jikinta ya nufi hanyar sauka ƙasa, Haɓɓar Alƙyabbar jikinshi ta riƙe tana cewa ", nace maka ka sake ni Maleeq!", ta fada cikin wata kaurarriyar murya.


bai kulata ba ya ƙara nufar hanyar fita, cikin yar tsawa tace "Wlh sai ka rabu dani maha'inci", ta fada tana ƙoƙarin juyawa, wata fisga yy mata, wadda sai da kashinta yy ƙara, idanunshi da suka rine ya watsasu kan fuskarta, har wani ruwa-ruwa idanunshi yake tarawa , sa boda ɗacin maganar da tayi mishi.


Sosai ta firgita da irin kallon da yake mata, da yanayij yarda idanunshi suka sauya kala har ma da irin riƙon da yy mata.


bai iya ce mata komai ba, ya saketa ya wuce abunshi, da gudu ta faɗa bedroom dinta tana kuka sosai, bed ta fada, tana kuka , Addu'o'in samawa kai sauƙin ta shiga jerawa , amma bata jin komai har wata suya take jin kirjinta na mata, duk wani juyi da zata yi kan bed din kallon Yaah Shehi take rungume da wata , hannunshi kan cikinta "Yaaah Subhanallahi!", taya ma zata iya mantawa da hakan, da kamar wuya.


Zallar ɓacin ran da yake ciki ne ya hanashi ma zama cikin gidan gaba daya, garden ya nufa, yana tafiya a hankali.


tunda ya fara jin sanyayyiyar iskar cikin garden din sai hankalinshi ya fara kwanciya, bama kamar daddadan kamshin da yake fita daga furannin da suke gurin, numfashe idanunshi yy a hankali yana fesar da sanyayiyar iska mai cike da kamshin mouth freshener a hankali ya furta "Yaah Rab!", ya furta yana mai daura hannunshi akan sumar wuyanshi da tayi luf a bayanshi, ƙarasawa yy gurin wasu fararan kujeru masu kyau da suke gefe daya, ta gefen yana dauke da wasu ƙorayen filawowi da farare , kusa dasu kuna ga wani abu jan da yake zubo da rywa gwanin kyau.


Zama yy gefe, yana mai lumshe idanunshi da kyau, yanzu tunanin Yarinyar ya faɗo mishi a rai, shi ya dan manta ma da ita kwana biyu, ko yaje Asibitin baya zuwa gurinta, gashi lokacin aikinta na ta tahowa, jaaan gashin gemunshi yy, yana son motsa bakinshi ya bude, dakyae bakin ya bude a hankali cike da natsuwa yace "Astagfiroullah!", ya furta yana dan haɗe kafafunshi, muryan Zayn ce tasa ya dan ware idanunshi a hankali, sai da ya dam kalleshi kafin ya kara lumshe idanunshi ba tare da yace mai Uffan ba.


gurin ƙafafunshi Zayn ya zauna a ƙasa, a hankali ya dauki hannun Yaah Shehi ya daura akan sumar kanshi mai yawa, wadda ta kusan tarar da ta Yaah Shehi a yawa, "Hammana", ya furta a hankali, jij kiran da yy mishi ne ya tabbatar mishi da cewar akwai abun da yake so daga gareshi, shafa kanshi yy ba tare da yace komai ba, hakan kuma shine ya bawa Zayn damar yin mgn , "me ne ya samu Sister na sameta tana kuka ", ya fada a hankali, ba tare da Yaah Shehi ya hude ido ba, ba kuma tare da sanin cewar zai bashi Amsa ba yace "Rigima!'", yana fada ya tsuke bakinshi ba tare da yy mgn ba.


Shiru dukkansu suka yi, Zayn ya wani ƙara naba'a yy shiru yana sauraran kukan tsuntsayem da yale gurin wanda yake fitar da sauto mai dadi.


Kitso sosai Anty Rayhana ta yaryarawa Sadiyyerh na gani na fada yy kyau sosai, gashin nan ya sauka har gadon baya, girgizata daga gyangyaɗin da take Anty Rayhana tayi, zabura tayi tana kallonta , dariya de ta kwace mata tana nunata, "gaskiya ke kura ce, yanzu daga ɗan taɓa ki shine kika yi wannan Uwar zaburar ", ta fada tana dariya, cuno baki tayi bata ce da ita komai ba.


miƙewa duk suka yi daga gurin, Kai tsaye Sadiyyerh ta koma kitchen domin ƙarasa aikin da ya Rage mata, bata an ƙare ba taji alamun mutum a bayanta, da sauri ta juyo, tana juyowa ta faɗo kan jikinshi, ƙara ta fara ƙoƙarin kwallawa dan ba ƙaramin tsoro taji ba, gashi bata san cewar shi bane, da sauri ya jijjigata yaba kallon cikin idanunta, numfashi ta sauke tana zazzare idanunta a hankali ta zame daga jikinshi ta juya.


kanta da dan kwalinta ya zame yake kallo, "Alhamdulillah!", ya furta ba tare da ya bari ta ji mai ya furta ba, ƙara juyowa tayi da mug din coffee , jaaa baya tayi da sauri dan ra dauka ya fice tuni garin jaa da bayan da zata yi by mistake mug din ya kwaɓe daga hannunta, gaba daya ta wanke ƙafafunta dashi, "Allahumna Ajirni fiii Maseebati", ta furta tana sulalewa ƙasa, jikin Yaah Shehi har rawa yake gurin ƙarasawa gareta, da sauri ya ɗagota yana kallon ƙafar da lokaci daya tayi jaaajir .....



~BAN HAKURI DA CAPITAL LETTER .DON ALLAH KUMIN UZURI WLH HIDIMA TA SHA KIN KAII YANZU HAKA GAGANIYA HAKE DAKYAR NA SAMU NAYI, GASHI KUMA BB YAWA, PLS KUMIN UZURI KU YAFENI IN SHA ALLAH MUN KUSA KOMAWA, MUNA YI KAMAR DA~


LOVE YOU SO MUCH FAN'S🥰🫶
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.22*



Dafa Kafadarshi tayi da hannu bi-biyu ta dafe tare da daura fuskarta kan kirji shi ta murza hancinta a jikinshu, cikin muryar raɗaɗi azaba tace "Washhhhhhh Yaah Shehi, Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un!", ta furta lokaci daya zufa na wanke mata jikinta, da sauri ya ƙara rike yana kallon yarda take ƙoƙarin zameww daga jikinshi.


"Wayyo Allah!", ta furta tana lumshe ido , lokacin da taji ya daura tattausan hannunshi mai sanyi akan fatar ƙafar in da ta ƙone, ƙara dafashi tayi tana girgiza ƙafar Damarta wadda da Alamu tafi ƙonuwa duba da yarda tayi wani kuf-kuf alamar tashi kai tsaye, "Yaaah Shehi ka tofa min Addu'ah ", ta furta cikin sanyi da hawayem da suka cika mata ido.


jijjigashi tayi tana hawaye, a hankali kara bakinshi sautin ƙafar in da ta ƙone ya fara tofa mata "Qul na Yah Naara bardan wa salamun ala Ibrahim", daukarta yy chak zuwa ɗakinshi .


katon first Aid din da yake cikin wardrobe ya fiddo ya dawo gabanta, tun da taga ya fiddo Scissor , jikinta ya fara rawa, duba da yarda taga ƙafar ta wani tattashi tayi waji iri tasan fatar ƙafar yanzu zai ce zai taɓa .


Da sauri ta afka jikinta, ta kankameshi tana rike hannayenshi gaba daya
jikinta na rawa, ta rike hannayenshi taba cewa "pls kar ka cire ka bar min akwai zafi", ta fada tana zubar da hawaye sosai.


hannayenta ya haɗe gaba dayansu guri daya, ya kama ƙafar ,gaba daya in da ya tashi ya ɗaɗɗayeshi da Almakashi, bayan ya gama ya sanya mata magani a gurin.


kanta da ta soke a kirjinshi tun bayan da ya fara cirw fatar da ta ƙone ya ɗago, bata ko numfashi , jijjigata ya fara yi , dan ya lura da cewar suma tayi.


dakyar ya samu ta farfaɗo daga suman da tayi ta riƙeshi kam tana kuka, ta kasa sakinshi , janye jikinshi ya fara yi, cikin Azabar raɗaɗin ciwon da yake damunta, ta sanya yatsarshi a bakinta, ta sakar mishi wani annamimin cizo, lumshe idonshi yy a hankali ya furta "Subhanallah!", dan har cikin kwakwalwar kanshi ya ji zafin cizon.


"bana sonka ka matsa daga kusa da ni", ta fada tana kara kankameshi, mamaki fal zuciyarshi, gashi tana cewa ya saketa, gashi kuma yana ƙara kankameshi, kalmar *bana sonka* , tana mugun mishi Amsakuwwa a cikin kunnenshi gashi ita kuma taƙi ta gane hakan.


ta mayar da abun kamar Waƙa abu kaɗan tace bata sonsa, ta tsaneshi, har kuma Yau ya kasa sanin shin me ne ne taƙamaiman abun da yy mata har da take furta hakan a gareshi gashi kuma taƙi ta faɗa mishi me ne ne.


to yaushe ma suka samun kyaɓantaccen lokaci da gurin da zasu tattauna ma ?, bakinta ta kara budewa cikin kuka tace "bana son..........



~Wayyo ni Matar mijinta, don Allah kuyi hkr wlh ni kaina bana jin dadin dan gutsirin typing din da nake muku, amma ya zan ?, hidima ce ta riga da ta gama sha min kai wlh~
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 23*



Bakinta ta gude cikin kuka tace , "Yaah Shehi!", sai da ya kalleta kafin tace "Wlh bana sonka na tsaneka, Don Allah! don Sonka da Annabi ka sakeni, Wlh ji nake kamar zan mutu, matsawar na ci gaba da zama da kai", ta fada tana kuka izuws yanzu ya fara tunanin cewar mutananta ne suke sanya wannan abubuwan , idanunshi da suka yi jaaajir ya ɗago , da sauri ta sauke nata idanun ƙasa, dan bata kaunar haɗa ido dashi dama dai chan ba ɗabi'arta bace haɗa idon dashi, ballanta yanzu da ta tabbatar ya kalli Abun da yake cikim idanunta za'a iya samun matsala.


Tambayar kamshi ya fara yi, Anya ma Sadiyyerh ce wannan ?, to mai ya sameta ne lokaci daya haka ?, sai da ya gama tunaninshi gaba daya ya tsaya akan tabbas dai ba ita bace.


Miƙewa yy zai far gurin, da sauri ta fisgoshi, har sai da ya dawo kan bed din ya zauna, riƙeshi tayi tana cewa "mai yasa zaka min haka ?", Cikin rashin fahimta yy mata alama da mene ?, "ka yaudare ni ", Alama ya ƙara mata da tayaya , "ka ci Amanata, ka cuceni, ka zallunce ni, Yanzu har kana da Mata da Ƴa a wani gurin , amma ka mayar da ji shashasha Uhmmmm Namiji kenan, Namiji buhun ƙaya, Namiji ba dan goyo ba, duk yarda kasa ka goyashi karshe sai ka goyashin kafin ya gamtsara maka cizon da dole ka saukoshi", Alamar mamaki ce ta bayyana kan fuskarshi sosai, amma bai bari ta gani ba, kawai sai ya kaɗa kanshi ya fice.



Wani kuke ne mai toshe numfashi ya sarketa , komawa tayi kan bed tayi plate tana kuka kamar ranta zai fita, ita wallahi wani matsiyacij kishin mijinta take, dan Allah ya sani tana mugun sonshi da kaunarshi, dan haka bazata iya yin Sharing dinshi da ko wace mace ba sa boda kaunar da take mishi, zata iya haƙura dashi kawai.


Wani bedroom da yake kusa da nashi, ya shiga ganin lokaci na ƙurewa A gaggauce yy shirin tafiya Masallaci ya fito, bb kowa palo lokacin da ya fice, kai tsaye Masallaci ya wuce, lokacin da zai ƙarasa lokacin Sallar Subhi yy , ƙarasawa yy gurin Liman ya tada iƙama, Karatu ya fara yi cikin sanyin halinshi, sai dai duk da sanyin halinshi da natsuwarshi yau ka saurari karatunshi tabbas zaka fuskanci sanyinshi ya dadu, wanda hakan yake neman kawar da natsuwarshu, dan ma mutum ne, mai dakiya, juriya, matuƙar haƙuri dan ba lallai ka iya ganin damuwarshi kan fuskarshi ba.


A cikin wannan sanyim nashi aka yi Sallah Subh aka gama, dai-daita zamanshi yy a dai-dai gurin da yake zaune, ya fara karatu da rayuwarshi, yy karatu mai yawan gaske da lokacin da ya gama sai da yy mamakin karatun da yy, dan yy karatu sosai, ya karanta tuj daga Suratul Baqara har izuwa Ma'edah,cikin Abun da bazai wuce 2 hours ba.


sanyayan numfashi ya saukar , yana mai lumshe idanunshi , dan tabbas yasan da taimakon wasu Jama'ar a karatun nasa, yana juyowa ya tarar da gaba daya Ɗaliban karatunsa da wasu daga cikin Malamai zaune suna , suna jiran y gama, yy mamakin ganinsu sosai, a hankali ya juya ya fuskancesu yana mai lankwashe ƙafafunshi kamar yarda Sunnah ta tanadar, hannunshi ya daura kan gashin girarshi yana shafawa da yatsunshi, a hankali ya furta "Alhamdulillah", chan

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment