Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana yi tana lumshe ido, tana kuma jin yarda wata Azababbiyar yunwa take taso mata sosai, don rabonta da cin Abin ci ta manta, Sawwa da take shan choculate ta kalla tare da cewa "ba zaki ci Abin cin bane ?", jijjiga kanta tayo alamar ta ƙoshi.


jinginar da kanta tayi ta ci gaba da cin tuwon , sai da tayi rabin Abin cin kafin ta saki sanyayyiyar gyatsa , tare da furta "Alhamdulillahi Yaa Allah", ta faɗa tana ƙarɓar cup din da Umma Jakadiya take miƙa mata, sanyayyiyar Gangariyar Madarar shanu ce, a cikin cup din, tuni yawunta ya tsinke don tama masifar son madarar shanu, kafa kanta tayi ta fara sha, sai da ta shanye tass kafin ta daga kanta akan cup din.


gaba dayansu mamakin irin cin da tayi suke, ci kamar na karshe, sai dai babu wanda yay magana.


tun daga ranar bakinta ya bude tana cin Abin ci sosai, don har mamakin cin Abin cinta suke, har cikinta ya kulle 9 months.


*Ranar sati*.

kasantuwar ranar ta kasance Weekend ranar ba babu aiki yasa dukkansu suna gida, hayaniyarsu tai yawa sosai, hakan yasa bata iya samun yin barci mai yawa ba, 12 pm gaba daya gidan ya daɗe babu kowa sai ita daya sauran gaba daya sun tafi Asibiti dubo Abieh, itama don Shehi ya hanata fita da da ita zasu tafi.


Cikin sanyi sosai take aiwatar da komai ranar, kasantuwar jikinta da yay wani irin sanyi, tun bayan tashinta, wani sukuku take jinta, sai dai fuskarta tayi wani Annuri sosai, goshinta sai ƙyalli yake, gaba daya gaɓoɓɓinta sun wani washe sai haske suke, a haka ra nufi part din Yaah Shehi, duk da part din A share yake a goge sai ta tsinci kanta da son ƙara gyara mishi, duk da da bata iya komai ko ɗukawa bata iyawa, amma yau sai ta ji zata iya gyara mishi, hakan yasa ta zage ta gama gyara mishi komai, palo ta koma tana mai shaƙat daddaɗan kamshi mai tattare da sanyin iskar AC , a hankali ta fara jin wani yana yi na daban na sauko mata , hakan yasa ta kwanta kan carpet tare da yin rigingine.


Suna Shiga Hospital din ana fito da Gawar wata Mata da ɗakinta yake kusa da Ɗakin Abieh , matar sun santa sosai, suna mutunci, kuma kusan tare aka kawota Asibitin da Abieh hakan yasa hankalinsu ya dan tashi, ko da suka shiga ciki Sawwa kasa zaune da tsaye tayi, ta damu su tafi gida, har da kukanta, hakan yasa Ayyana kiran Driver don ya mayar da ita.


tun da ta shiga cikin palon gidan take kwala mata kira Amma shiru bb motsinta, bedroom dinta ta shiga nan ma babu ita babu dalilinta, da sauri ta nufi part din Shehi don tasan har in bata ganta anan ba to tana chan side din , , a kwance ta sameta ta riƙe cikinta , idanunta a lumshe, zama tayi a gefenta tana kallon fuskarta , A hankali tace Ammy! Ammy!! Ammy!!!", ta faɗa sau ukku, a hankali ta shiga bude idanunta har ta waresu akan fuskarta, "bakya da lafiya ne ?", ta faɗa tana taɓa wuyanta, jijjiga kanta tayi a hankali, tana mai ƙara Lumshe idanunta, "Ayya sannu!", ta faɗa cikin tausayawa, jijjiga kanta ta kuma yi .


A haka Yaa Shehi ya shigo palon ya samesu a zaune.....



Barkanmu da Asuba!.
fatan kowa ya tashi lpy ?

[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 34*


Girgiza kanta ta fara yi, cikin kukan da ya kwace mata, ta faɗa jikinsa ta mugun kankamesa, tare da cewa "In sha Allahu Abieh!", lumshe idanunshi yay da Azabar karfi, jin tana niyyar ƙassara mishi rayuwarsa, chan ciki yace "Yaaah Allah! so kike ki ƙasssara Abien naki ya kasa aiwatar da komai ne", ya fada yana ƙoƙarin zameta daga jikinsa, amma inaaaa ta mugun riƙesa, dole bb yarda ya iya ya kyaleta, sai da ta gaji da kukan kafin ta sakesa, kallon fuskarta yay, sai da ya dan yi murmushin gefen baki kafin yace "kin gama ne", tura baki tayi bata ce komai ba, miƙewa yay ya shige bedroom dinsa bai jima ba ya fito cikin shigarsa ta yau da kullun wadda take mugun masa lyau take kuma ƙara fito da zallar ƙuruciyarsa,haiba,nasaba,kamala da kwarjininsa a fili, voile ne black mai sharara wanda har ana iya hango farar singlet dinsa ya sa, sai kuma Alƙyabba fara tas mai digon baƙi-baƙi a jiki, sai kuma baƙin rawanin Maluntakarsa da ya zauna daram a kansa, idanunsa sanye da wani siririn farin glass mai kyau, hannunsa sanye da Agogon Rolex na Azurfa wanda ya mugun yiwa tsintsiyar hannunsa kyau, sai kuma takalminsa ƙirar
White Cipriano Wove Italian Leather , idanu ta zuba masa, tana kallonsa har ya ƙaraso gareta, hannayensa yasa ya tallafe kumatunta, a hankali ta ce "Abiena kayi kyau!", murmushi yay a cikin zuciyarsa ya furta "Ƴar Abieh farin cikin Abienta", a zahiri kuwa cewa ya yi "Uhmmm", ganin ya nufi waje yasa tayi saurin mara masa baya suka fito hannunta cikin nasa.


tun da suka fara saukowa ƙasa Zayn-Maleeq da yake zaune cikin shigar ta Alfarma ya zubawa hannayensu da suke saqale da juna idanu, har suka ƙaraso idanunshi na cikim hannunsu, dai-daita tsayuwa tayi a gefensa, a dai-dai kuma lokacin ne Shehi yake wa Ayyana magana, "An gama fita da kayan dama kai ake jira", jinjina kansa ya dan yi kafin yace "muje to!" gaba daya waje suka yi, a chan wajen suka tarar da su Sayyid suna gaban motocin da zasu yi tafiyar dasu, kallon idanunta Sayyid ya yi, a hankali yace "idanun nan kamar sun yi kuka", kallonta duk suka yi ita kuwa sai ta kalle Shehi, tare da jingina kanta a jikin kafadarsa, ta shagwaɓe masa fuska, dariya duk suka yi kafin suce "Yarinya ta zama Daddy's Gal", kwaɓe baki tayi kafin tace . "Uhmmm", ta fada tana dan matswa jikin Umma Jakadiya, "kin ga Uncle Sayyid ko ", ta fada tana riƙe hannunta, murmushi tayi tana cewa "ai dole ace haka, kullum kina liƙe da shi, ko da yake laifinsa ne da ace ya yi Aure an sama mike ƙanne da duk ba kiyi hk ba", da sauri ta saki hannun Umma Jakadiya, ta komai gefe, shi kuwa shan kunu yay , bai ce komai ba, don ba tun yanzu suke ta damunsa ba ita da Ayyana, don ita Ayyana ma da ta ishesa da magana ce mata yay " itama sai ta fito da miji tayi Aure ko zata daina takura masa", dole tayi shiru dan taji yana shirin dauko mata Dala ba gammo.


Agogon hannunsa ya kalla, kafin ya dan yi tsaki ciki yace "lokaci na ƙurewa fa", ya fada yana wucewa gurin motarsa da Sawwa ta tsufa a ciki, duk shishiga suka yi suka tafi.


direct Airport suka nufa, lokacin da suka isa bai fi sauri 10 minutes jirginsu ya tashi ba, don har an fara cigiyar passengers , Sallama tawa kowa, tana zuwa gurin su Amah ta haɗasu gaba daya ta rungumesu, sai kuma ta saki kuka, ta riƙesu kam, lallashinta suka shiga yi, amma taƙi ta daina kuka taƙi kuma ta saki su Amah, duk sai ta basu tausayi, Ayyana da Umma Jakadiya ma hawayensu suka shiga sharewa a ɓoye don kar su kara karyar mata da zuciya, su kuwa su Amah ai kuka har da majina, dakyar Shehi ya rabata da jikinsu, jikinsa ta faɗa ta ci gaba da kukanta, "nan yafi cancanta da ki zubar da hawayenki dama",Ayyana ta furta a hankali, kallonta Zayn yay kafin yace "But Why ?", da sauri ta kallesa don bata san maganar ta suɓuce mata ba, cikin dan daburcewa tace "tsananin kauna da shaƙuwar da take tsakanin Uba da Ƴa!", taɓe bakinsa yay kafin yace "oh!" ,jinjina kanta tayi.



"bari muje", ya fada yana jaanta, baya Zayn ya mara masa, sai da yay taku biyu ukku ya juyo yana kallonsa da alamar tambaya , pass port din hannunsa ya nuna masa, bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya, A hankali suke taka steps din jirgin har suka shige ciki, VIP side Zayn ya zauna, su kuwa a Special side suka zauna.


kanta ta daura akan kafadarta, ta lumshe idanunta, kamar yadda taga ya yi, 3 hours cif ta isar da su England daga Saudi, ƙofar jirgin ce ta fara buɗewa, cikin natsuwa passengers din da suke cikin jirgin suka fara fitowa , sai da kusan duk mutanan da suke jirgin suka gama fitowa kafin suka fara takowa izuwa fitowa, yana gaba tana bayansa, tafiya suje cikin natsuwa sosai, kanta na ƙasa, shi kuwa nasa suna cikin glass, sassanyar iska suke fesarwa.


a hankali ya ci gaba da wawware idanunsa yana kallon cikin gurin, idanunshi ya ƙurawa Zayn da yake gaban wata tamfatsetsiyar baƙar mota ,suna fitowa , wasu tsala-tsalan motoci biyar suka shigo gurin, baƙaƙe biyu a gaba biyu baya, sai farar mota ƙirar Benz a tsakiya , sai walwali motocin suke, har gabansu suka tsaya, cikin sauri aka buɗe musu motar da take tsakiya, ita ce ta fara shiga sai shi, rufe motar aka yi driver ya jaaa, a tsare motocin suke tafiya, kan lafiyayyan titin ƙasar , babu cikowar wucewar motoci sosai.
, nasu na gaba ta Zayn na baya, shima drivet ne yake jaansa cike da natsuwa , a haka suka shiga wata katafariyar Anguwa mai kyau da tsari, titin Anguwar ma kansa abub kallo ne, don gaba daya gefe-da gefen titin flowers ne masu kyau a jere, an wani irin yalwata gurin dasu, Anguwar tayi kyau sosai, gashi ko ina a kulle, babu kuma yawaitar mutane masu wucewa a gurin.



tunda suka shiga wani layi da yafi ko wane layi da suke cikin Anguwar, suka rage speed din motocin , suka koma tafiya slowly, har suka ƙarasa kofar wani gida na Alfarma , horn aka yi, a take get man din gidan ya bude ƙofa ya leqo ganin masu gurin ne, yasa da saurinsa ya bude musu ƙofar, da gudu motocin suka sulala cikin farfajiyar gidan mai girman gaske.


sai da suka ƙarasa babban parking space din cikin gidan kafin suka yi parking, da sauri aka bude musu motar, kasantuwae akwai gajiya a tattare da su yasa basu tsaya wata-wata ba suka fito daga cikin motar cike da muguwar gajiya suna fesar da numfashi, gaba Shehi yay ita kuma tana biye da shi, kafin Zayn ya ƙaraso tuni sun shige ciki, har Upstaira suka hau, nuna mata wani bedroom da yake kusa da wanda ya shiga ya yi, shigewa tayi da sauri, don tun tashinta yau bata jin dadi ga kuma alamar zuwan baƙonta da take ji, gashi kuma ma taji kamar zubowarsa, da saurinta ta shiga bathroom din da yake cikin bedroom din, sauri sauri ta cire kayan jikinta, gabanta ne ya faɗi "Subhanallahi!" ta furta lokacin da idanunta suka hasko mata , period dinta da ya zubo a pant dinta.


cikin rashin karfin jiki da kalasa, ta fara wanke fatar jikinta tana sakin sanyayiyyar iska daga bakinta, sauri-sauri ta gama wankan ta daura babban towel ta fito, da gudunta ta nufi Bedroom dinsa, tun daga ƙofa ta fara kwala masa kira "ABIEH! Abieh!! Abieh!!!", ta ƙwala kiran da ƙarfi lokacin da ta shiga bedroom dinsa, a tsaye ta samesa gaban mirror yana taje sumar ƙansa , a baƙin ƙofar ɗakin ta tsaya, ta cikin mirror ya hango yarda ta wani yi rau da idanunta, juyawa yay gaba daya ya kalleta, alama ya yi mata da me ne ne ?, hawayen cikin idanunta ne suka zo, lips dinsa ya dan tsotsa a hankali yana kallon fuskarta da ta koma wani iri .


"Abieh wlh kuwa ni bana son Abun nan, kawai a ɗinke min gurim yinsa na huta", ta fada tana turo baki, dan ware idanunsa yay, alamar da hankslinki kuwa, chan ciki ya furta "Chappp!", " kullum in yazo cikin fargaba da ciwo nake, yanzu haka jin marata nake kamar zan mutu", ta fada tana dafe cikinta, "Zo!" ya furta chan ciki.



A hankali ta fara takawa gurinsa, tana zuwa ya ware mata hannayensa, shigewa tayi cikin jikinsa ta rumtse hannayenta , sanyayyan numfashi ya fesar, tare da dan lumshe idanunshi, turo ƙofar da yaji ne yasa yay saurin saketa tare da mayar da ita bayansa ta yarda ba'a iya hangota.


Zayn ne ya turo ƙofar bedroom din ya shigo, daga chan baƙin ƙofa yace "Hamma bari na dan fita", jinjina kansa yay alamar to, ficewa yay, sai da yw fita ya matsa daga gabanta yana fesar da iska, a hankali ta furta "Abieh da buƙatar na gyara jikina", ta fada tana kallon ƙafafunta , miƙewa yay ya jura Alkyabbarsa cikin natsuwa ya furta "ki jirani anan", ya fada yana ficewa.gefen bed dinsa ta zauna.



bai jima sosai ya ba ya dawo, hannunsa riƙe da manyan ledoji guda biyu, saman carpet da yake gwfen gado ya ajiye ledojin, da sauri ta matsa gurinsu dan ta matsu ta gyara jikinta, ledar farkon ta fara dubawa, ta ko yi sa'a pad din Besense Sanitary pads , mai guda 30 - 30 guda ukku ne, sai set din pants masu jikin net, kala-kala masu kyau , da tsada, da sauri ta zari dai-daya ta shige bathroom din da sauri
.



sai da ta ƙara gyara jikinta kafin ta shirya cikin wata Abaya mai masifar kyau da ya siya mata, tsaf ta fito cikin kayan, sai dan ramewar da tayi , tana fitowa tace "Abieh yunwa", harararta ya dan yi kafin tace "ai gani. sai ki cinye ni", ya fada yana dan danna ƙaramar wayarsa, "A...." bai bari ta ƙarasa ba ya nuna mata dayar ledar da ya shigo da ita, da sauri ta nufi ledar,budewa tayi, kamshin lafiyyan Abin ci ne ya bugi hancinta, lumshe idanunta tayi tare da furta "Yummy!", da sauri tayi bissimillah ta fara cin Abin cin cikin natsuwa, yarda take tauna Abin cin ma kansa abun kallo ne, komai cikin natsuwa take yinsa, tana yi tana lumshe idanunta, ta ƙasan idanunsa yake kallonta, bata ci da wani yawa ba ta tsame hannunta tare da furta "Alhamdulillah!", kallon Take away din Abincin yay ya kuma kallonta, a yatsine yace "mai kike nufi ?", langwaɓar da kanta ta dan yi ta dan yi luuuu da idanunta, cikin natsuwa da muryar shagwaɓa ta furta "na ƙoshi", ta fada tana dan lasar lips dinta da harahenta, da sauri ya dauke idanunshi daga kallonta, numfashi ya fesar, da sauri ta je jikinsa ta zauna, da sauri ya ware idanunsa, zameta yay daga jikinsa,cikin dan ruɗu yace "mai yasa bakya jin kunyar hawa jikina ne ? ke baki san kin girma bane ?", ya fada yana haɗe ƙafafunsa tare da baza, Jallabiyar jikinsa, ta bude sosai cuno baki tayi gaba cikin sakalcin da shi daya take iya yiwa, maganar ma bata damu da yi da kowa ba, amma a gabansa Zabiya take komawa
, "ni kam ban girma ba, ko yaushe a gabanka Ƴar Jaririya nake jina, kuma nasan ba zan taɓa girma ba, ba kuma zan ji kunyar hawa jikinka ba ko a gaban wa", jijjiga kansa yay cike da tarin mamakin Yarinyar, chan ciki Ya furta "Allah y shirya!", da sauri tace , "Ameeen", gyara zamansa ya ƙara yi yana duba litattafin Hisnul muslum, da yake hannunsa.


Kwance yake kan Gado idanunsaca lumshe, bakinsa bai gusa da Ambaton sunan Allah ba, ɗira ƙafarta tayi cikin shagwaɓa tace "Abieh ina zan yi barci ?", bayanshi ya nuna mata, ba tayi tunanin komai ba, ta afka kansa, tare da kwanciya luf a bayansa, "Yaaah Ilahi! Yaah Allahu!! , Yaaa Ar-rahman raheemin!", ya furta lokacin da yaji saukar ta akan jikinsa, jikinsa na wani irin rawa, ya zameta daga jikinsa, da sauri ya yi waje, miƙewa tayi tana kallon bayansa da ya shige, watsa hannayenta tayi.



Bedroom din da ya nuna mata ya shiga, bai tsaya ciki ba, bathroom ya shige cikin mugun kiɗima, kanshi ya sakarwa ruwa, lumshe idanunshi yay yana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya, masu zafin gaske, "Wayyo Allah!", ya furta chan ciki, yana mai sanya hannayensa cikin sumar kansa ya bazata, ta zubo har bayansa gaba daya ta liƙe masa a bayansa da gaban goshinsa, yana haɗa hanya ya fito daga bathroom din, bed ya faɗa, cikin minutes din da basu shige biyar ba wani zazzafan zazzafi mai masifar zafi ya rufesa, abu kamar wasa ƙaramin Alamari ya fara zama gaske.


A hankali ya fito daga bedroom din da ya kwana, yana tafiya yana baza Alƙyabbar jikinsa, kamar mai san ɓoye wani abu, idanunshi da suke muci-muci ya ware sosai, lokacin da ya fara buga ƙofar Bedroom din da take, chan ciki ta furta "Abieeeeeeeh!", ta furta chan ƙasa cike da mawuyacin hali, da sauri ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, ɗurkushe ya ganta gaban bed, tayi amai duk ta ɓata jikinta, gaba daya jikinta babu ƙarfi, da sauri ya ɗurkusa gabanta, faɗawa jikinsa tayi, wasu hawaye na zubo mata, jijjigata ya fara yi yana dan dukan bayanta a hankali jin tana ƙara yin kakarin Amai, hannunta ta riƙe, muryarta na shaƙewa ta furta "KIRJINA ABIEH zan mutu , K........
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P .32*


Numfashi mai dauke da tsantsar tausayi da tashin hankalinsa a fili, karo na farko a tarihin rayuwarsa da ya kasa tsayar da kukansa sai wasu hawaye suka fara zubo masa cikin tsananin tausayin Yarinyar da yarda yake jon tana yin kuka,da dukkan gaskiyarta, shi kanshi ya fahimci kallar kukan da take, kallar kukan da har idan mutum bai yi ba to zai iya zamar masa matsala,kanta ya shiga shafa cikin natsuwa yana hura mata iskar bakinsa, na tsawon lokaci ya dauka yana mata hakan da Addu`o`i.
tuni barci ya dauketa, shi kuwa jingina kanshi yay da Allon gado, yarda yaga rana haka yaga dare, kiran Sallar fari, ya tashi daga in da yake zaune, ya nufi bathroom, wanka ya yi sosai, ya dauro Al'wala da towel daure a ƙugunshi ya fito daga bathroom din, direct gaban mirror ya nufa, yana goge jikinsa, a hankali ya fara shafawa jikinsa lotion , turare ya sawa jikinsa, ya nufi gurin wardrobe Jallabiya mai taushi ya dauka milk mai kyau, zurawa yay tare da zame towel din jikinsa, bathroom don ya mayar dashi tare da saƙalashi a jikin hanger, yana fitowa ya isa gaban bed din, a hankali ya fara dan bugun pillow da take kwance kai, a hankali ta dan bude idanunta, tare da dan zuba mishi, kawar da kanshi yay tare da cewa "tashi!", ya fada yana tsareta da ido, a hankali tayi sanyayyoyar miƙa ,shi kuwa gaba yay abun shi.


bayan ta gama komai ta fito palonsu,a zaune ta tarar da Mutane, a hankali ta raɓa gefe, ta zauna ita dai sam bata yarda ta mutu ba, ganin abun take kamar shirin film ko kuma a mafarki, Amatullah ce tace "ina kika kwana , na duba ɗaki bakya nan ?", dan shiru tai kafin tace "Ɗakin Abieh", tana fadar haka ta tsuke bakinta, haka ranar aka yini karɓar gaisuwa, washe gari ma, ana yin na kwana ukku , Shehi yace "to ya isa haka, tun da an yi ukku kowa ya tafi", hakan ce ta kasance ranar da Aka yi huɗu babu kowa gidan, daga su sai su, dama daga Nigeria Lamurɗe ne kawai yazo, bayan shi babu wanda yazo, daga chan kuma bangaren su Jaddi babu wanda yazo don sun kasa samun VISA hakan yasa basu zo ba.


Zaune take tayi tagumi hawaye sai zuba suke daga cikin idanunta, da alama ta shiga duniya tunani sosai, cikin natsuwa yay sallama cikin palon, har ya shigo ciki babu wanda ya Amsa, idanunshi akan fuskar Umma Jakadiya har ya iso tsakiyar palon, cikin kamala yace "Umma!", a firgice ta dago don maganar a Sama ta jiyota, da sauri ta share hawayenta tana cewa "Na'am Shehi!", cikin natsuwa ya zauna a gefenta tare da cewa "kina lafiya kuwa ?", jinjina mishi kanta tayi, tare da cewa "Alhamdulillah!", "Maa sha Allah!", ya fada yana mai barin gurin ya nufi in da zai sadashi da side nashi, har ya kusa shigewa, ya hango Sawwa tana tafiya kamar zata kifa, gaba daya ta rame , da al`ama ma bata cin Abin ci ,da hannunshi yay mata Alama da tazo.


A hankali ta biyo bayansa, ba tare da tayi magana ba, har suka isa palonsa tana binsa a baya, kan kujera ya zauna, ita kuwa gefen kansa ta tsaya, lumshe idanunshi yay kafin chan ƙasan maƙoshi yace "Tashi a kai na", tura bakinta ta dan yi tare da matsawa ta koma gabansa, still dai tana tsaye, a hankali ya fara bude idanunshi, idanunta na kallon fuskarsa kamar mai sob ganin wani abu a fuskar tasa, sai dai a Zahiri bata san mai take kallo ba kawai dai tana kallonsa ne.


"Bude Fridge!", ya fada ba tare da ya kalleta ba, sai da ta ɗan tsaya kafin ta nufi fridge din, kallonsa tayi bayan ta bude, alama yay mata da ta dauko abun da yake ciki, daukowa tayi tazo ta ajiye a gabansa, show glass ya nuna mata alama ta dauko cup, daukowa tayi ta kawo masa , karɓa yay ya zuba mata, tare da miƙa mata, ƙarɓa tayi tana kallon Sanyayiyyar madara , yamutsa fuska tayi don sam bata son ci ko shan wani abu makamancin hakan, "Abieh ban sha", ta fada kai tsaye, kallonta yay yana ƙara nazartar halayen Yarinya gaba daya ita bata jin komai don tayi musu dashi, sam bata jin komai don ta gardama masa, abun da kuwa take so shi ake mata, idanunshi ya dan fidda waje, cikin cool voice yace "mai kika ci ?", murya chan ƙasa itama tace "babu!'', wani kallo ya manna mata kafin ya furta "babulo come on dauki ki shanye kafin na ƙirga ukku", ba don tana so ba ta fara sha a hankali idanunta cike da kwalla, sai da ta shanye ta tas kafin ya fice tana mai sakin sanyayyan kuka, shi kam lumshe idanunshi yay yana mai fara since zaren Alkyabbar jikinsa.



*After 3 Years*

A hankali suke tafiya cikin natsuwa, biyu suna sanye da kayansu kala daya hatta takalmansu da gyalansu kala daya ne, dayan kam kayanta daban bama shigarsu kala daya ba, tana sanye da dogon wanda da yay tight dintw sosai, ya sha

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment