Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tun da ya fara saukowa daga kan Stairs Sadiyyerh ta waji zuba mishi idanunta masu kaifi sosai tana kallonsji, har ya ƙaraso gurinta, a hankali ta furta "Maa sha Allah, Fa tabaraqallahu Ahssanun Qaliqin!, Allah yay halitta a gurin nan, Yaah Shehi ka gode Allah!.
dukkan wani abu da Bawa yake nema a gurin Allah!, Allah ya baka, kana da kyau, cikar zati, haiba, kamala da kwarjini, kana da kuɗi, ilimi both side Arabi da boko, Sarauta , da babban Ahli masu kaunarka." ta ƙarasa faɗa idanunta na tara kwalla.


Wayar da take kunnenshi ya cire dai-dai da ya zo gurinta, iskar bakinsa ya fesar, idanunshi a kanta yace,"Ooh See you! . ke mai kika rasa ? " ya fada cike da kamewa, "gaskiya na faɗa , Allah y baka Ahli babba mai Asali da tushe ga kaunar Yan uwanka da baka rasa ba , ka gode Allah", taɓe baki yay kafin yace "ke fa ?,kina da Mahaifiya!, miji! , Ƴa da soyayyarsu gaba daya,mai kika rasa kuma ?", ya fada yana kallonta.


"Uhmmm", ta faɗa ba tare da ta ƙara cewa komai ba, shima tsuke bakinshi yay ba tare da ya ƙara cewa da ita Uffan ba.


Sawwa da take zaune kan kujera hannunta riƙe da Chocolate da kuma cup cake , duk a hannunta ya kalla, tana sanye da wasu kalar kayan sanyi manya-manya masu bargo mai jikin mage, lingif suke, pink colour da su, sun yi kyau sosai kuma sun hau da jikinta, kamar Ƴar Turawa, hularta ta dan jaa baya sakamakon kusa rufe mata idon da tayi.


Sai safar ƙafa da take sanye da ita da wani fashion shoes , masu kyau da tudu.
A hankali yace "kina koyawa Yarinyar nan shan zaƙi da yawa", cuno baku tayi gaba kafin tace "aa fa kwara daya ne!", ta fada tana ƙoƙarin gyara mishi zaren Alƙyabbarsa.


tabe baki yay kafin yace "Uhmmm"hannunsa ya daura kan waist nata, tare da yin dan sama da ita, yarda tsawonta zai yi dai-dai da nasa, kasantuwar ya fita tsawo sosai , dan ba zata wuce kafadarsa ba.


"Yarinya ki ringa cin taliya ko kya samu ki ƙara tsawo", ya fada yana jaaan dogon hancinta, dan murmushi yay, ita kuwa taɓe bski tayi kafin tace "Arɗo!" shiru yay mata bai Amsa ba, "Shehi!", shima yay shiru, "Chubado!!!!!!!", ta fada cikin sigar shagwaɓa , tana kwaɓe fuska.


lumshe idonshi yat kafin yace "mene!", kallon kasan ido ta mishi kafin tace "kana jina dama ..!", taɓe bakinshi yay, kafin yace "barci nake . baki ga Alama ba ?", karkata kai tayi kafin tace "Uhmmmm!".


kai tsaye waje yay bayan ta gama gyara mishi zaren Alƙyabbar."come on Bongel am , kar Chubado yat jiranmu", ta faɗa tana miƙa mata hannu, sai da ta kalleta na tsawon minutes kafin ta miƙe zuwa gareta, kama hannunta tayi suka yi waje,kafin su fita Yaah Shehi har ya kame cikin mota, idanunshi sanye da wani siririn farin glasses mai kyau sa ya ƙara fitar da sahihin kyanshi.


Sawwa ta faea zama kusa da shi kafin Sadiyyerh ta shiga, zaune yake da laptop akan cinyarsa yana latsawa.
phone din Sadiyyerh ta fita, ta fara lallatsawa , ita kuwa Sadiyyerh titi ta zubawa ido, har suka bar cikin gidan kai tsaye titin Gombe suka hau.
tafiya suke cikin nishaɗi da jin dadi duk da ba wani fira suke ba, kowa da abun da yake , Shehi na lura da yarda Sawwa take shige da fice cikin wayar ta Sadiyyerh,mamakibya mugun kamashi, in da ya ga tana shiga shi kanshi bai san gurin ba, amma sai shige shige take.


Garin Gombe!.

gari mai tarin Albarkarai , da ni'imomi kama daga kan Noma .Kiwo kasuwanci da sauransu.
suna da Qabilu , sai dai Qabilar Fulanu sun fi yawa, daga su sai Hausawa, kafin kuma duk sauran Qabilu su ka biyo baya, ba wani babbsn gari bane sai Abubuwan Albarka na ban mamaki.


kusan yinu suka yi zungur dan tun 9am suka fito sune sai guraren 4pm suka shiga cikin garin Gombe, har Sallah a hanya suka yi, don Yaa Shehi baya kaunar jinkirta Allah saboda halin rayuwa.


Lokacin sa suka shiga cikin Masarautar. gaba daya garin Yay wani irin duhu aai iska ce take kaɗawa da ƙarfi , Alamar gab ake da tsugewa da ruwan sama sosai............
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 27*



Hannunta na cikin nashi tana goye da Sawwa suka fito daga cikin Hospital din, Motarsu suka shiga, Driver ya jaasu, Direct wani haɗaɗɗan guri mai masifar ƙayatarwa, wanda ya fi kama da gurin hutawa , sai dai gurin a mugun tsaro yake, sojoji Yan sanda, ko wane kalar Kaki na Ƙasar an zubasu a gurin,ga kuma wasu Yan Ubansun Motoci kala-kala wanda suka fi na Yaah Shehi Haɗuwa ma da wanda basu kai su ba.


A tare aka bude musu Mota suka fito, yana gaba ita tama baya , a hankali suke tafiya, itama kanta a ƙasa, wannan ƙaron har da Niƙaf dinta wanda ya ɓoye mata gaba daya fuskarta har idanunta, sai dai wani dan shararan guri take gani, hannunta ƙafarta jikinta, gaba daya yana lulluɓe dan Alƙyabbarta ma tayi bala'in mata yawa har jaan ƙasa take mata, ɗazun da suka je Asibiti sai dai dan ɗagata sama tayi, yanzu kuwa babu dama.


tun daga nesa , muka rinƙa jiyo wata zazzaƙa ɗaɗɗadar murya mai masifar dadi da sanyi tare da garɗi tana raira karatun Al-qur'ani mai girma,a cikin suratul Nisa'i , a hankali Sadiyyerh ta shiga lumshe ido karatun na ratsa mata gaba daya sassan jikinta, wani mugun shauƙi take ji, har suka ƙarasa gurin bata ɗago da kanta ba.


Cikin natsuwa da Kamala suka shiga keta taron mutanan da suke gurin suna shiga ciki, ba mutane bane sosai, bai fi mutum 50 ma maza da mata,sai dai da Alama gaba daya gurin Mata da Miji ne, bb Saurayi ko Budurwa, babu yawan Yara sai wanda suke shaan Maama , hakan yasa gurin bb hayaniya,domin duk wanda yake gurin ya mallaki hankalin kanshi, kuma sub san mai suke sun san Azabar wanda ake karatun Al-qur'ani yana magana, shu yasa gurin yg wani mugun silent bb mgn ko kaɗan ko tari bb, hakan yasa gaba daya karatun yale Amsa kuwwa a kafatanin gurin.


Gaba suka zauna, in da suna Zama Aka miƙawa Sadiyyerh Lund speaker, shiru ta ɗan yi, tana kallon gefe, tana kuma kallon Yaah Shehi da Ƙasan ido, ganin shima ya zuba mata idanunshi yasa ta ƙarɓa, da Bissimillah ta fara, kafin ta fara ƙaratunta cikin Suratul Ankhabut gaba daya gyara zamansu suka yi, suna ƙara jaddadda godiyarsu ga Allah, bb ma kamar Yaah Shehi da yaji karatun nata na Yau ya fi na ko yaushe dadi, ta sakin jikinta tana fidda dukkan wasu haƙoƙƙin haruffa da kalmomi,cikin taushin murya take karatun har ta idar, daga nan kuma Haleesa Aliyu Haydar Aliyu ce ta daura akan nata karatun.


bayan gamawa, aka daura da walima mai kayatarwa wadda Sarkin garin Makkah ne da kansa, ya shirya Walimar,bayan an gama ya bawa Yaah Shehi babbar kyauta, haka suka tattara guraren 5pm suka wuce gida.


A mugun gajiye suka shigo gidan, bb kowa a palo, hakan yasa suka yi sama, kowa ɗakinshi ya wuce cike da ɗinbin gajiya,bama kamar Sadiyyerh da take ta rugumniya da Sawwa da take ta barcinta abinta, zare Alƙyabbar jikinta tayi, tana mai fiffita da hannu sa boda zafin da take ji ga kuma zufa da take.


Gefe ta ajiye Alƙyabbar, tare da ƙoƙarin kwance goyon da yake bayanta,cikin gajiyawa ta sauketa, tana kallonta, ajiyeta tayi kan bed, tare da yunƙurawa zata miƙe , tarrr Sawwa ta bude idanunta wanda suka kasance manya-manya , har wani madara-madara cikin idon yake sa boda tsabar fari, fa kwanciyar wani mai-mai, kwayar idanunta ta kasance golden colour , wanda wani dan blue yy mishi da'ira, ya zagaye gaba daya Golden colour din.


hannu Sadiyyerh ta kai a wuyanta, tare da yin magana a hankali, kofar bedroom din ta sanyawa key kafin ta wuce ta shiga bathroom in da ta bar Sawwa ita ƙadai a zaune, bata jima ba sosai ta fito tana daure da towel jikinta sai ɗigar da ruwa yake, Sawwa da take in da ta ajiyeta ta kalla.


bata ko matsa daga in da ta ajiyeta ba, tana zaune ta haɗa hannayenta, sai bin ɗakin da kallo take, sai kace mai nazarin wani abu, Wuce wa gaban Mirror Sadiyyerh tayi ta shiga mulke gaba daya fatar jikinta da mayuka masu taushi da kamshi, sai da ta gama, ta sanya wasu Ɗamammun riga da wando wandon irin crazy din nan ya ɗameta sosai rigar ma top ce sun bala'in mata kyau, wata blue black din hula mai dan gashi gashi ta sanya, sai ta sanya fashion na ƴan kunnaye blue suma, sai ta dan murza white lips a bakinta.


daukar Sawwa tayi ta nufi Bathroom da ita, bata jima ba suka dawo hannunta riƙe da na Sawwa da take tafiya kamar tana tsoron taka ƙasa, tana daure da Dan towel ƙarami pink, jikinta nata turiri da kamshi shower gel , kan Stool din Mirror ta ajiyeta, ta dan shafa mata mai da turare kaɗan, ta mata sample kwalliya a fuskarta, sai dai Yarinyar tayi wani Ɗan jarababbiyar kyau da har sai da ta firgita, duk kyan da ake cewa tana dashi yarinyar ta takata kyau, bada ban kar tayi ƙarya ba da zata iya cewa ta ma fi Yaah Shehi kyau, sa boda kasancewarta na Ƴa mace, ga kwalliya da sauransu, ɗirarrar Yarinya ce da tun tana ƙarama kana kallon tsarin zubin Halittar da Allah yy mata, sai ka kara jadadda godiya gareshi, kana kallonta zaka san ta girma ba ƙaramin rush za'ayi a kanta ba.


komai nata jif-jif, kama daga kan yana yin tsarin halittarta, ita ba doguwa ba ba kuma gajera ba, fara tarr da ita, fari irin na Larabawa , mai sirki da na Turawa, tana da lallausan Baƙin gashin kai, mai yawan gaske da har bayanta ya sauko, tana da matsakaiciyar fuska, mai dauke da gashin gira mai yawan gaske, dara-daran idanu, zara-zaran eyes lashes , siririn hanci wanda ya kasance har baka, dan ƙarakin baki mai dauke da pink lips dai-dai sai dan kaurin da suke da shi ƙadan.



Cikin kaya irin nata sak ta shiryata, har takalmi iri daya haka ta sanya mata, Hijab ta zura mata ta dauki wayarta suka fito daga bedroom din.


Bedroom din Yaah Shehi suka fara shiga, suna shiga suka sameshi zaune yana aiki a laptop, da sauri Sadiyyerh ta cire hijab dinta ta ajiye a kan kujerar da take gefenshi, shigewa jikinshi tayi ta kwantar da kanta kan kirjinshi.


Miƙawa Sawwa hannu tayi kafin tace "Come My Dolly", ta fada tana ware mata hannu, a hankali ta fada jikinta, tare da kwantar da kanta itama kamar yarda ta kwanta kan jikin Yaah Shehi.


Firar Gurin taron Ɗazun Sadiyyerh ta shiga yiwa Yaah Shehi da son dauke hankalinshi daga aikin da yake, sai dai baya wani biye mata dan Amsa ma a gajarce yake bata ita.


gajiya yy da surutunta, kallonta yy kafin yace "Sadeey!", kallonshi tayi, "tashi ku koma palon ƙasa",tura baki tayi kafin tace "korar mu kake ?", kai tsaye ya gyaɗa mata kanshi, fushi tayi ta kams hannun Sawwa suka fice Abin su, sauke ajiyar zuciya yy kafin yace, "hakan shine ya fi min", ya fada yana mayar da kanshi kan aikinshi.



Duk a zaune suka tarar da su, su Amah na ganin Sawwa suka nufeta, cike da murna, kama hannunta suka yi izuwa gurin wasansu, bin su kawai take komai sai dai ta kalla suna yi, amma ita bata iya ba,ko magana bata iya ba sai dai gwaranci.


duk da zamanta cikin Yara da yarda suke jaanta, amma bata ko dariya ,sai in ta ƙure tayi murmushi.



Zama Sadiyyerh tayi kusa da Anty Rayhana da take shan Damammiyar Jalal Alawa da Madarar Peck tayi, "Anty Dan bani nasha Wallahi yunwa nake ji, yau yini nayi ban ci Abin ci ba", " baki ci Abin ci ba kuma ?, to ni dai sanin da nayi taron da kuka je Akwai Abin ci sai dai in kece baki ci ba", taɓe bakinta tayi kafin tace ", Ayya abubuwansu basu min ba".


"kin dai bawa Ƴar Abin ci ko?", dafe kai ta yi kafin tace "na manta itama bata ci ba", ta fada tana miƙewa da sauri, dariya Anty Rayhana tayi kafin tace "kun ji aikin hankali, Yanzu Ƴar taki ki manta da baki bata Abin ci ba ??, Lallai Sadiyyerh akwai gyara", ta fada tana kallon Yaran da suke wasa.


sai da ta haɗa mata komai akan tray ƙara mi, kafin ta fara kiran sunanta "Sawwa! Sawwa!! Sawwa!!! Sawwama!!!", ta fada tana zuba Drinks a cup.



cikin natsuwa ta ɗago luɗu Eyes dinta ta zuba in da take jin ana kiran sunan, dan izuwa yanzu ta san sunan ko na waye, "Came!", ta fada tana yafi tota.


gurinta ta nufa a hankali, tana tafiya tana lumshe ido,har ta ƙarasa gurinta, daukarta tayi ta daurata kan kujera tare da cewa "Say Bissimillahir rahmanur rahim!",ta fada tana kallonta, shiru tayi, sai da Sadiyyerh ta ƙalleta ta kara mai-maitaww kafin a hankali kuma a rarraɓe magana mai kama da ta mai in-ina tace "Bis..bi...Bissimillahi!", abun da taxe kenan ta tsuke bakinta, a hankali ta fara ɗibar abin cin,cikin natsuwa tace "Open your Mouth", bb musu ta bude bakinta in da Kyawawan haƙoranta farare tarrr wanda suke dauke da Teeth gave babba, suka bayyana .



Fara bata Abin cin tayi,duk in zata bata sai ta mata umarni da ta bude bakinta, har suka gama, suka dawo palon suna fira ita kuma tana gurin Yara.



A sati na biyu da yin Sallah gaba daya suka tattare suka taho Ƙasa Nigeria,a babban filin jirgin garin Abuja suka sauka, wato International Airport, kai tsaye Babban gidan Yaah Shehi da yake garin suka nufa, dan dama duk zuwa Nigeria ta nan yake sauka,sai ya huta na 2 days kafin ta wuce Masarautarsu.


Yaf-yaf haka ruwan sama yake sauka a garin, gashi ya wani lullume, yy duhu alamar hadari ne sosai a garin.


suna shigowa cikin gidan bayan sun zazzauna a palo , aka kece da ruwan sama mai ƙarfi sosai, gaba daya Sawwa sai ta fara jinta cikin wani yana yi na shauƙi, Yarinyar da bata cika walwala ciki mutane ba, amma ta fara doka murmushi, kamar mai.


wanda hakan yake nuni da cewa taba masifar son ruwan, kuma da dukkan alamu kamar Akwai wani abu da take gani a duk lokacin da ruwa yake sauka dan zata je ta ringa ƙoƙarin shiga ruwa sai Sadiyyerh ta dauketa.


bayan kowa ya natsu a palo, suna Addu'ar saukar ruwa, ita kuma ta sulale bb wanda ya ga lokacin da ta fice waje, tana fita ba tare da tunanin komai ba ta shige cikin ruwan tana dan jujjuyawa ciki.



ruwan ne ya duketa sosai, wanda ya haddasa mata shiga wata rayuwar ta daban, lokaci daya ta ji ƙafafinta na wani irin kwankwatsa, zamewa ta fara yi zata koma cikin palon, amma ina ƙafa ta riƙe, zubewa a gurin tayi, dan danan sai ga zazzaki mai zafin gaske, sai fisge-fisge, cikin abibaɗan da ba zasu wuce 10 ba ta fita hayyacinta,ko magaba bata iyawa, bata iya miƙewa ko rarrafe.


Miƙewa Sadiyyerh tayi zata haye sama, fara duddubata tayi, bata ganta cikin Yara ba, da sauri tace "Ina Dolly ?", gaba daya hankullansu ya dawo gareta, kowa yace bai ganta ba bb kuma wanda ya ga in da tayi.


kai tsaye tayi waje dan tasan zata aikata shiga ruwa, tana fita ta hangeta kwance ƙasa, da gudunta ta ƙarasa gareta, cikin hamzari, ta fara jijjigata tana mai kiran sunanta, da shiga Palon gaba daya, gaba dayansu suka yo kanta, hankali tashe ganin Yarda ta riƙota kamar marar rai.



jijjigata suka hau yi gaba daya, ai tuni su Amah suka ruɗe, a ruɗe Amatul-Azez ta wuce sama, tana kwaɗawa Yaah Shehu kira, "Uncle! Uncle!! Uncle!!!!", ta ƙarasa faɗa da karfi, dai dai ya fito daga wanka yana sanye da Ash din Jallabiya, yana tsaye gabcn mirror yana tsane kanshi da towel ta banko ƙofar Bedroom din.


jiyowa y yana kallonta, ganin yarda take kuka, tana kuma nufasa, yasa ya dakata da abun da yake yi, "Uncle Sawwa ce , gata chan ", ta faɗa tana nuna baya,yana yin yarda Yarinyar take kuka da shiɗewa ne yasa ya fahimci ba lafiya, da sauri ya zari key ya fito yana riƙe da hannunta.


tun kafin ya ƙara so palon ya gane Asalin abun da yake faruwa, cikin sauri ya ƙarasa gurin, yana zuwa yy sama da ita, ba tare da ya tsaya ba yy waje, duk mara mishi baya suka yi, Amma kafin su ƙaraso gurinshi, tuni ya jaa mota da kanshi yy waje.duk shishiga suka yi tare da mara mishi baya.


gudu yake tsulawa kan titin ta yarda yay musu rata, suka kasa cin masa, sai dai suka bi bayanshi, kai tsaye Asibitin da aka fara treating dinta nan ya nufa da ita,Cikin Sa'a kuma ya tarar da Wannan Dr din dai ne, cikin hanzari ya ƙarɓeta ya shiga da ita ciki
.



bayan hour 1 Dr ya fara fitowa daga cikin room din da aka shiga da ita, bayan fitowarshi Nurses suka fara tururuwan fitowa suma.


Yaah Shehi da yake zaune a kan wata farar kujera da take ajiye a gaban room din ya miƙe, yaba kallon Dr din, hannu ya bashi suka yi musabaha, kafin yace "muje Office", kallon su Ayyana yy kafin su wuce ciki.


Zama kan kujerar da take kallon ta Dr yy,ya naɗe ƙafarshi daya kan daya, yana dan kallon Dr din, numfashi ya fesar kafin yace "me yasa aka barta ta shiga cikin ruww bayan an sa irin Abubuwan da suke tare da ita, yanzu gashi Ammonia dinta ta tashi sosai , ya kamata a ringa kulawaa da ita sosai, duk da dai nasan kasan komai game da cutar amma gaskiya sai an ƙara kula sosai, dan wannan cutar tana da haɗari sosai a game da lafiyarta, musamman ma ita da take Yarinya Under age, gashi kuma bayan wannan cutar tana da wasu daban-daban h.......
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: SAI HKR DON WLH ZAKU GA TYPING ERROR DA YAWA, DAN BAN SAMU NAYI EDITING BA, YAU KUMA NAJI INA SON YIN TYPING NE KAWAI, SHI YASA NACE BARI MUDAN RAGE HANTSI DAN NASAN YANZU KUWA NA NAN YANA BIN INUWA😂


*P. 29*.



Da Bissimillah Shehi ya zura ƙafarshi daya waje, ta dan jima a haka kafin ya zaro dayar da gan-gan jikinsa gaba daya , rufe motar yay tare da bata baya, a hankali ya fesar da wani narkakken numfashu, a hankali ya furta "Alhamdulillah Yaa Allah! Alhamdulillah!", ya faɗa yana mai lumshe idanunshi, kusan two minutes suna haka kafin ya waresu Chan sama, ya jima yana kallon guri daya kafin ya dauke idanunshi daga kallon gurin, Sadiyyerh da Sawwa tuni sun wuce ciki, ya yin da shi kuma ya nufi Masallaci, dan lokacin Sallah ya gabato sosai , yaba zuwa ya tarar da ruwa ajuye cikij wata galleliyar buta fara tarr ko zane babu a jikin buta, gefe ya matsa ya zauna da bissimillah! a bakinsa ya jaawo butar ya fara Alwalarsa kamar yarda shari'a ta tanadar.

har ya gama tama zaune daga gefe cikin wasu kayan fulani na saƙa, farare tarr masu masifar daukar ido, fara ce tar in da farinta har wani rawaya-rawaya take, tana da dogon gashin kai wanda aka mata kalar kitson Fulani da yake kwantowa har gaban goshi, gashi nan baƙi siɗik , sai sheƙi yake , tana gashin gira sosai, da manyan idanu farare masu masifar daukar ido.
tana da dogon hanci mai kyau wanda tsarinsa ta dace da fuskarta, tana da ƙara min baki sosai, idanunta na kan Shehi har yay Alawar ya gama, tana zaune gefensa, shi kam abun da yake gabansa yake da dan sauri-sauri kuma cikin natsuwa kasantuwar yarda iska take kaɗawa kamar zata tafi da mutum, yana idarwa ya miƙe yay cikin Masallacin da sassarfa, yana zuwa gaba daya kowa ya matsa ya bashi guri ya shiga gaba.


cikim golden Voice dinshi ya tada Sallah, tare da fara rairo karatun Al-qur'ani mai girma a cikin Suratul Tahreem! , ƙuwwa da ihu tare da sowa ne ya fara fitowa daga sassan masarautar, ya yin da rugugin Hadari da ihun ya ƙara daukar cikin Masarautar har wani girgiza-girgiza take, lokacin da za'a tafi Sujjadar farko a lokacin ne kuma aka tsinke da wani kalar ruwan sama,mai masifar karfi da ƙara,wanda ya shafe tarihin gaba daya wasu koke - koke da iface-ifacen da ake yi cikin Masarautar bayan gama Sallah Asr din , ya gyara zamansa yana mai tasfihi ga Ubangiji Talikai , idanunshi lumshe ya jingina da bango , kai kace barci yake, Alhalin idanunshi biyu, shiru kawai yay yana saurarar ruwan da take sauka mai karfi da ƙara, An shafe 1 hour

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment