Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya motsa laɓɓansa alamar Amsa Sallamarta, ƙasan ƙafafunsa ta zauna , cikin ƙasa da kai tace "Barka da Safiya Abieh!", cikin tsantsar kauna da kulawar da yake mata yace "Kin tashi lpy ?", a hankali ta furta "Alhamdulillah!". "Maa sha Allah!".Gyara zamanta tayi, ta dunkule guri daya, shi kuwa gyara zamansa ya yi , tea mai dan kauri ya haɗa ya fara sha, har ya gama sha tana gurin da take ko motsi mai karfi ba tayi ba, sai da ya gama ya juyo gareta, dan ware idamunsa ya ƙara yi akanta, ganin fuskarta sharƙaf da hawaye, sosai yaji babu dadi ganin hawayenta, hannunshi ya miƙa mata, a hankali ta miƙa hannunta ta kama nasa, jaawota yay ta zauna gefensa har jikinsu na gugar juna, kanta ta daura a ƙafadarta ta shiga shasheƙar kuka, ɗagota ya fara ƙoƙarin yi, amma ta manne da jikinsa ta riƙesa sosai,numfashi ya sauke a hankali kafin ya fara cewa"na miki Nasiha ?", ya fada yana dan murmushi, idanunta da suke ciƙe da hawaye ta zuba masa, da sauri ya dauke idanunsa daga cikin nata, cikin iya sarrafa harshe ya fara cewa "_Hulu Allah, joga hore ma, heftu a Debbo, Debbo ma mo Dongal nabbi dowmun, mi Andi mi wala seko a dow mad'a, sai dai hentun a dow nane, ko dun wadantama fu ta jabu hokku horema dow god'd'un, joga Allah hanun tan! Joga salatu Annabijo, ko gonda fu jangu deftere lelare, gam d'un magante, dun magante naugol, ta jabu tokku atal gal na da gal Jomirawo e juldamku, to a fijir wor6e, banda yire ji'en be gala hakkilo, horu hakkilo ma dow jande, ko nastan ma nyimre fu `yamu Abienki gam on don gondi._(kiji Tsoron Allah ki riƙe mutuncinki, ki sani ke ɗin mace ce, macan ma mai rauni da kuma nauyi a kanta, duk da nasan bani da shaƙƙu akan yarda kike ƙoƙarin riƙe mutuncinki, amma ki ƙara akan yarda na sanki, komai za'a miki kar ki sake ki bada mutuncinki sa boda wani abu, ki ɗayanta Allah daya,ki riƙe kaunar Ma'aiki da Salatinsa, sannan duk halin da kike ciki ki kasance mai yawan karatun Al-qur'ani domin shi din waraka ne, sannan mai kore damuwa, ki kula akwai nauyin da yake kan ki, kar ki yarda ki take hukuncin Allah da ya gindaya miki, ki kare mutunci , ban da wasa da maza, ban da kawayen banza, ki mayar da hankali sosai akan karatunki, duk abun da ya shige miki duhu ki tambayi Abienki don yana tare da ke........



[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 34*


Girgiza kanta ta fara yi, cikin kukan da ya kwace mata, ta faɗa jikinsa ta mugun kankamesa, tare da cewa "In sha Allahu Abieh!", lumshe idanunshi yay da Azabar karfi, jin tana niyyar ƙassara mishi rayuwarsa, chan ciki yace "Yaaah Allah! so kike ki ƙasssara Abien naki ya kasa aiwatar da komai ne", ya fada yana ƙoƙarin zameta daga jikinsa, amma inaaaa ta mugun riƙesa, dole bb yarda ya iya ya kyaleta, sai da ta gaji da kukan kafin ta sakesa, kallon fuskarta yay, sai da ya dan yi murmushin gefen baki kafin yace "kin gama ne", tura baki tayi bata ce komai ba, miƙewa yay ya shige bedroom dinsa bai jima ba ya fito cikin shigarsa ta yau da kullun wadda take mugun masa lyau take kuma ƙara fito da zallar ƙuruciyarsa,haiba,nasaba,kamala da kwarjininsa a fili, voile ne black mai sharara wanda har ana iya hango farar singlet dinsa ya sa, sai kuma Alƙyabba fara tas mai digon baƙi-baƙi a jiki, sai kuma baƙin rawanin Maluntakarsa da ya zauna daram a kansa, idanunsa sanye da wani siririn farin glass mai kyau, hannunsa sanye da Agogon Rolex na Azurfa wanda ya mugun yiwa tsintsiyar hannunsa kyau, sai kuma takalminsa ƙirar
White Cipriano Wove Italian Leather , idanu ta zuba masa, tana kallonsa har ya ƙaraso gareta, hannayensa yasa ya tallafe kumatunta, a hankali ta ce "Abiena kayi kyau!", murmushi yay a cikin zuciyarsa ya furta "Ƴar Abieh farin cikin Abienta", a zahiri kuwa cewa ya yi "Uhmmm", ganin ya nufi waje yasa tayi saurin mara masa baya suka fito hannunta cikin nasa.


tun da suka fara saukowa ƙasa Zayn-Maleeq da yake zaune cikin shigar ta Alfarma ya zubawa hannayensu da suke saqale da juna idanu, har suka ƙaraso idanunshi na cikim hannunsu, dai-daita tsayuwa tayi a gefensa, a dai-dai kuma lokacin ne Shehi yake wa Ayyana magana, "An gama fita da kayan dama kai ake jira", jinjina kansa ya dan yi kafin yace "muje to!" gaba daya waje suka yi, a chan wajen suka tarar da su Sayyid suna gaban motocin da zasu yi tafiyar dasu, kallon idanunta Sayyid ya yi, a hankali yace "idanun nan kamar sun yi kuka", kallonta duk suka yi ita kuwa sai ta kalle Shehi, tare da jingina kanta a jikin kafadarsa, ta shagwaɓe masa fuska, dariya duk suka yi kafin suce "Yarinya ta zama Daddy's Gal", kwaɓe baki tayi kafin tace . "Uhmmm", ta fada tana dan matswa jikin Umma Jakadiya, "kin ga Uncle Sayyid ko ", ta fada tana riƙe hannunta, murmushi tayi tana cewa "ai dole ace haka, kullum kina liƙe da shi, ko da yake laifinsa ne da ace ya yi Aure an sama mike ƙanne da duk ba kiyi hk ba", da sauri ta saki hannun Umma Jakadiya, ta komai gefe, shi kuwa shan kunu yay , bai ce komai ba, don ba tun yanzu suke ta damunsa ba ita da Ayyana, don ita Ayyana ma da ta ishesa da magana ce mata yay " itama sai ta fito da miji tayi Aure ko zata daina takura masa", dole tayi shiru dan taji yana shirin dauko mata Dala ba gammo.


Agogon hannunsa ya kalla, kafin ya dan yi tsaki ciki yace "lokaci na ƙurewa fa", ya fada yana wucewa gurin motarsa da Sawwa ta tsufa a ciki, duk shishiga suka yi suka tafi.


direct Airport suka nufa, lokacin da suka isa bai fi sauri 10 minutes jirginsu ya tashi ba, don har an fara cigiyar passengers , Sallama tawa kowa, tana zuwa gurin su Amah ta haɗasu gaba daya ta rungumesu, sai kuma ta saki kuka, ta riƙesu kam, lallashinta suka shiga yi, amma taƙi ta daina kuka taƙi kuma ta saki su Amah, duk sai ta basu tausayi, Ayyana da Umma Jakadiya ma hawayensu suka shiga sharewa a ɓoye don kar su kara karyar mata da zuciya, su kuwa su Amah ai kuka har da majina, dakyar Shehi ya rabata da jikinsu, jikinsa ta faɗa ta ci gaba da kukanta, "nan yafi cancanta da ki zubar da hawayenki dama",Ayyana ta furta a hankali, kallonta Zayn yay kafin yace "But Why ?", da sauri ta kallesa don bata san maganar ta suɓuce mata ba, cikin dan daburcewa tace "tsananin kauna da shaƙuwar da take tsakanin Uba da Ƴa!", taɓe bakinsa yay kafin yace "oh!" ,jinjina kanta tayi.



"bari muje", ya fada yana jaanta, baya Zayn ya mara masa, sai da yay taku biyu ukku ya juyo yana kallonsa da alamar tambaya , pass port din hannunsa ya nuna masa, bai ce komai ba ya ci gaba da tafiya, A hankali suke taka steps din jirgin har suka shige ciki, VIP side Zayn ya zauna, su kuwa a Special side suka zauna.


kanta ta daura akan kafadarta, ta lumshe idanunta, kamar yadda taga ya yi, 3 hours cif ta isar da su England daga Saudi, ƙofar jirgin ce ta fara buɗewa, cikin natsuwa passengers din da suke cikin jirgin suka fara fitowa , sai da kusan duk mutanan da suke jirgin suka gama fitowa kafin suka fara takowa izuwa fitowa, yana gaba tana bayansa, tafiya suje cikin natsuwa sosai, kanta na ƙasa, shi kuwa nasa suna cikin glass, sassanyar iska suke fesarwa.


a hankali ya ci gaba da wawware idanunsa yana kallon cikin gurin, idanunshi ya ƙurawa Zayn da yake gaban wata tamfatsetsiyar baƙar mota ,suna fitowa , wasu tsala-tsalan motoci biyar suka shigo gurin, baƙaƙe biyu a gaba biyu baya, sai farar mota ƙirar Benz a tsakiya , sai walwali motocin suke, har gabansu suka tsaya, cikin sauri aka buɗe musu motar da take tsakiya, ita ce ta fara shiga sai shi, rufe motar aka yi driver ya jaaa, a tsare motocin suke tafiya, kan lafiyayyan titin ƙasar , babu cikowar wucewar motoci sosai.
, nasu na gaba ta Zayn na baya, shima drivet ne yake jaansa cike da natsuwa , a haka suka shiga wata katafariyar Anguwa mai kyau da tsari, titin Anguwar ma kansa abub kallo ne, don gaba daya gefe-da gefen titin flowers ne masu kyau a jere, an wani irin yalwata gurin dasu, Anguwar tayi kyau sosai, gashi ko ina a kulle, babu kuma yawaitar mutane masu wucewa a gurin.



tunda suka shiga wani layi da yafi ko wane layi da suke cikin Anguwar, suka rage speed din motocin , suka koma tafiya slowly, har suka ƙarasa kofar wani gida na Alfarma , horn aka yi, a take get man din gidan ya bude ƙofa ya leqo ganin masu gurin ne, yasa da saurinsa ya bude musu ƙofar, da gudu motocin suka sulala cikin farfajiyar gidan mai girman gaske.


sai da suka ƙarasa babban parking space din cikin gidan kafin suka yi parking, da sauri aka bude musu motar, kasantuwae akwai gajiya a tattare da su yasa basu tsaya wata-wata ba suka fito daga cikin motar cike da muguwar gajiya suna fesar da numfashi, gaba Shehi yay ita kuma tana biye da shi, kafin Zayn ya ƙaraso tuni sun shige ciki, har Upstaira suka hau, nuna mata wani bedroom da yake kusa da wanda ya shiga ya yi, shigewa tayi da sauri, don tun tashinta yau bata jin dadi ga kuma alamar zuwan baƙonta da take ji, gashi kuma ma taji kamar zubowarsa, da saurinta ta shiga bathroom din da yake cikin bedroom din, sauri sauri ta cire kayan jikinta, gabanta ne ya faɗi "Subhanallahi!" ta furta lokacin da idanunta suka hasko mata , period dinta da ya zubo a pant dinta.


cikin rashin karfin jiki da kalasa, ta fara wanke fatar jikinta tana sakin sanyayiyyar iska daga bakinta, sauri-sauri ta gama wankan ta daura babban towel ta fito, da gudunta ta nufi Bedroom dinsa, tun daga ƙofa ta fara kwala masa kira "ABIEH! Abieh!! Abieh!!!", ta ƙwala kiran da ƙarfi lokacin da ta shiga bedroom dinsa, a tsaye ta samesa gaban mirror yana taje sumar ƙansa , a baƙin ƙofar ɗakin ta tsaya, ta cikin mirror ya hango yarda ta wani yi rau da idanunta, juyawa yay gaba daya ya kalleta, alama ya yi mata da me ne ne ?, hawayen cikin idanunta ne suka zo, lips dinsa ya dan tsotsa a hankali yana kallon fuskarta da ta koma wani iri .


"Abieh wlh kuwa ni bana son Abun nan, kawai a ɗinke min gurim yinsa na huta", ta fada tana turo baki, dan ware idanunsa yay, alamar da hankslinki kuwa, chan ciki ya furta "Chappp!", " kullum in yazo cikin fargaba da ciwo nake, yanzu haka jin marata nake kamar zan mutu", ta fada tana dafe cikinta, "Zo!" ya furta chan ciki.



A hankali ta fara takawa gurinsa, tana zuwa ya ware mata hannayensa, shigewa tayi cikin jikinsa ta rumtse hannayenta , sanyayyan numfashi ya fesar, tare da dan lumshe idanunshi, turo ƙofar da yaji ne yasa yay saurin saketa tare da mayar da ita bayansa ta yarda ba'a iya hangota.


Zayn ne ya turo ƙofar bedroom din ya shigo, daga chan baƙin ƙofa yace "Hamma bari na dan fita", jinjina kansa yay alamar to, ficewa yay, sai da yw fita ya matsa daga gabanta yana fesar da iska, a hankali ta furta "Abieh da buƙatar na gyara jikina", ta fada tana kallon ƙafafunta , miƙewa yay ya jura Alkyabbarsa cikin natsuwa ya furta "ki jirani anan", ya fada yana ficewa.gefen bed dinsa ta zauna.



bai jima sosai ya ba ya dawo, hannunsa riƙe da manyan ledoji guda biyu, saman carpet da yake gwfen gado ya ajiye ledojin, da sauri ta matsa gurinsu dan ta matsu ta gyara jikinta, ledar farkon ta fara dubawa, ta ko yi sa'a pad din Besense Sanitary pads , mai guda 30 - 30 guda ukku ne, sai set din pants masu jikin net, kala-kala masu kyau , da tsada, da sauri ta zari dai-daya ta shige bathroom din da sauri
.



sai da ta ƙara gyara jikinta kafin ta shirya cikin wata Abaya mai masifar kyau da ya siya mata, tsaf ta fito cikin kayan, sai dan ramewar da tayi , tana fitowa tace "Abieh yunwa", harararta ya dan yi kafin tace "ai gani. sai ki cinye ni", ya fada yana dan danna ƙaramar wayarsa, "A...." bai bari ta ƙarasa ba ya nuna mata dayar ledar da ya shigo da ita, da sauri ta nufi ledar,budewa tayi, kamshin lafiyyan Abin ci ne ya bugi hancinta, lumshe idanunta tayi tare da furta "Yummy!", da sauri tayi bissimillah ta fara cin Abin cin cikin natsuwa, yarda take tauna Abin cin ma kansa abun kallo ne, komai cikin natsuwa take yinsa, tana yi tana lumshe idanunta, ta ƙasan idanunsa yake kallonta, bata ci da wani yawa ba ta tsame hannunta tare da furta "Alhamdulillah!", kallon Take away din Abincin yay ya kuma kallonta, a yatsine yace "mai kike nufi ?", langwaɓar da kanta ta dan yi ta dan yi luuuu da idanunta, cikin natsuwa da muryar shagwaɓa ta furta "na ƙoshi", ta fada tana dan lasar lips dinta da harahenta, da sauri ya dauke idanunshi daga kallonta, numfashi ya fesar, da sauri ta je jikinsa ta zauna, da sauri ya ware idanunsa, zameta yay daga jikinsa,cikin dan ruɗu yace "mai yasa bakya jin kunyar hawa jikina ne ? ke baki san kin girma bane ?", ya fada yana haɗe ƙafafunsa tare da baza, Jallabiyar jikinsa, ta bude sosai cuno baki tayi gaba cikin sakalcin da shi daya take iya yiwa, maganar ma bata damu da yi da kowa ba, amma a gabansa Zabiya take komawa
, "ni kam ban girma ba, ko yaushe a gabanka Ƴar Jaririya nake jina, kuma nasan ba zan taɓa girma ba, ba kuma zan ji kunyar hawa jikinka ba ko a gaban wa", jijjiga kansa yay cike da tarin mamakin Yarinyar, chan ciki Ya furta "Allah y shirya!", da sauri tace , "Ameeen", gyara zamansa ya ƙara yi yana duba litattafin Hisnul muslum, da yake hannunsa.


Kwance yake kan Gado idanunsaca lumshe, bakinsa bai gusa da Ambaton sunan Allah ba, ɗira ƙafarta tayi cikin shagwaɓa tace "Abieh ina zan yi barci ?", bayanshi ya nuna mata, ba tayi tunanin komai ba, ta afka kansa, tare da kwanciya luf a bayansa, "Yaaah Ilahi! Yaah Allahu!! , Yaaa Ar-rahman raheemin!", ya furta lokacin da yaji saukar ta akan jikinsa, jikinsa na wani irin rawa, ya zameta daga jikinsa, da sauri ya yi waje, miƙewa tayi tana kallon bayansa da ya shige, watsa hannayenta tayi.



Bedroom din da ya nuna mata ya shiga, bai tsaya ciki ba, bathroom ya shige cikin mugun kiɗima, kanshi ya sakarwa ruwa, lumshe idanunshi yay yana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya, masu zafin gaske, "Wayyo Allah!", ya furta chan ciki, yana mai sanya hannayensa cikin sumar kansa ya bazata, ta zubo har bayansa gaba daya ta liƙe masa a bayansa da gaban goshinsa, yana haɗa hanya ya fito daga bathroom din, bed ya faɗa, cikin minutes din da basu shige biyar ba wani zazzafan zazzafi mai masifar zafi ya rufesa, abu kamar wasa ƙaramin Alamari ya fara zama gaske.


A hankali ya fito daga bedroom din da ya kwana, yana tafiya yana baza Alƙyabbar jikinsa, kamar mai san ɓoye wani abu, idanunshi da suke muci-muci ya ware sosai, lokacin da ya fara buga ƙofar Bedroom din da take, chan ciki ta furta "Abieeeeeeeh!", ta furta chan ƙasa cike da mawuyacin hali, da sauri ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, ɗurkushe ya ganta gaban bed, tayi amai duk ta ɓata jikinta, gaba daya jikinta babu ƙarfi, da sauri ya ɗurkusa gabanta, faɗawa jikinsa tayi, wasu hawaye na zubo mata, jijjigata ya fara yi yana dan dukan bayanta a hankali jin tana ƙara yin kakarin Amai, hannunta ta riƙe, muryarta na shaƙewa ta furta "KIRJINA ABIEH zan mutu , K........
[4/29, 12:32 AM] salmeertsanisalman: *P. 35*



"Kirjina Abieh , wayyo zan mutu!", ta fada idanunta nayin kamar zata suma da sauri ya dagata daga inda take ya yi bathroom da ita, cikin jacuzzi ya sanyata, da sauri ya sakar mata ruwa mai sanyi ganin tana niyyar Sumar masa , doguwar ajiyar zuciya ta sauke , a hankali numfashita ya shiga dawowa jikinta, ƙarfaffan numfashi ya jaaa , kafin ya furta "Alhamdulillahi!", shi ya shiga taimaka mata har ta gyara jikinta, kasantuwar rashin ƙarfin jiki da take fama da shi, jingina ta ya yi da ƙafadarsa suka fito,lokacin da suka fito lokaci ya riga da ya ƙure,cikin hanzari ya shiryata, hijab ya sa mata, ya shiga gaba ta ba bayansa kaɗan, hala suka yi Sallar kamar zata faɗi, hijab ya sa mata, ya shiga gaba ta ba bayansa kaɗan, hala suka yi Sallar kamar zata faɗi, suna idarwa ta kwanta a gurin, da sauri ya jawota jikinsa, zafi sosai yaji jikinta.


*Washe gari*


Washe gari bayan an idar da sallan asuba ya had'a mata tea mai kauri ya bata tasha, bata jima ba kuwa bacci mai nauyi ya dauketa......



Ba ita ta farka ba sai wuraren goma na safe, wanka tayi ta shirya cikin simple abaya Wanda ya amshi D'an madaidaicin jikin ta, ya kuma yi mata kyau, babu komai a fuskarta sai gloss din data shafa wanda ya bawa lips din ta daman shining, hakan ko yasa fuskarta fitowa d'ass da ita, ta fito asalin fresher (waye ga JJC) direct school sukayi bayan ta d'an tab'a break-fast......





Basu samu wani tangard'a ba, ya gama mata komai saboda sanenne ne, hakan yasa basu bata lokaci ba, don har café sukaje suka biya na biya sukayi printing ma printing daga nan kuwa sukayi gida.......



***

D'agowa tayi ta bude idanun ta da suke lumshe tun dazu akan Zaid, Wanda lokaci daya ta fara masa kallon mai juyeyyen tunani ko kuma dai kawai ta ce Mara hankali, don yafi dacewa da hakan.




Cikin nutsuwar da Allah ya mata Wanda lokaci d'aya ya nemi gushewa saboda mamaki da kuma al'ajabin da maganganun Zaid suka haifar mata a lokaci guda ta ce.



"Amma dai kana cikin hankalin ka ba wai ka tabu bane? To kai ina ka taba jin ance maka akwai aure tsanani na da kai? Kana kanin mahafina? Kace kana so na? Uhmmmm lallai kam amma sai wallahi sai na gayawa Abieh, daga haka ta mike tayi cikin daki ba tare da ta amsa ko da kira d'aya cikin wadanda yake kwala mata ba, don ita Jin abun take Kaman mafarki, wai kanin mahafin ta ne zaice yana sonta so irin na aure,? ai gwara Abie yazo ta fad'a masa yasan me zai masa ko Dawanau ta kama ai sai a kaishi don wannan ba lafiya ba, da wannan tunanin ta tattara zancen ta wartsar tayi shirin baccinta......


Har ta kwanta, taji abun ya tsunkeleta, kwata tayi cikin jaan tsaki tace "Lallai ma Uncle Zayn din nan. ~SO~ , Aure Uhmmm", ta faɗa tana juya kwanciyarta , amma gaba daya abun duniya ya addabawa rayuwarta , da ta juya sai ta ji maganarsa tana mata Amsa quwwa, ta jima bata yi barci ba, sai da kyar ta samu ya dauketa.


Dadewar da tayi bata yi barci bane kuma ya haddasa mata, rashin tashi da wuri, wanda yasa Shehi yin tunanin ko ciwonta ne ya kuma tashi, cikin saurinsa ya tura ƙofar bedroom din, da sauri ya komaya juya bayansa, ya zamana bayanshi na kallon cikin ɗakin gabanshi kuma na kallon ƙofa, "Hasbunallahu wani'imal wakeen!"ya furta yana mai lumshe dukka idanunsa, cikin dan ruɗu, da sauri ya buɗe ƙofar ya fice, itama A diririce ta faɗa Bathroom don duk abun ta ɓata taɓa bari ya ganta a yarda ya ganta yanzu ba, "innalillahi!", ta furta tana mai sawa ƙofar lock ...



kasa fitowa tayi daga cikin bathroom din, ta kusa 1 hour , kafin ta fito duk a ɗarare, sauri-sauri ta shirya, tunani take ta yi,ya ganta a yarda take ko kuwa dai hasashe ne take da ya ganta, tunda dai ko idanunsa bai ɗago ba ya juya bayansa, in kuwa ya ganta da kunya mai zai yi tunani kenan ?, tayi sakacin da Mahaifinta har yaga surar jikinta a yana yin da bai kamata ba ko kuwa ?, tunane-tunane ta shiga yi, har da ta barsa akan bai ganta ba, nan take ta bar abun a inda ya faru, jin cikinta na kira mata ciroma ne, yasa ta fita palo, tana tafiya tana tattare gashin kanta da ya bazo mata, numfashi take fesar wa a hankali, tana shaƙar daddar iskar hadarin garin da ta haɗu da sanyin AC da aka kurewa gudi cikin palon ya dauki wani irin ɗari na musamman mai haɗe da kamshin turare mai dadin gaske, kanta a ƙasa har ta zauna kan kujerar dining, komai yana a shirye, duk kuwa da cewa babu mata a gidan, amma komai tsaf , kuloli kuwa sun fi biyar, da flask da abubuwa komai na shirye tsaf-tsaf gurin ,sai kamshi girki.


Cup ta dauka, ruwan zafi mai haɗe da kayan kamshi sai tashi yake ta zuba , wanda ta zuba bai fi rabin cup din ba, ta ajiye, madara ta bude da sugar da millo, zubawa ta shiga yi, bayan ta gama ta motsa , wata Ƙaramar kula ta dauka, budewa tayi, kyakyawan farfesun kayan ciki ne ya bayyana, yatsina fuska tayi, tare da rufewa ta matsar da kular gefe, wata ta ƙara budewa, farin mulmulallan tuwan danyar shinkafa ne , ya bayyana ya samu tuƙi mai kyau, an mulmulesa a leda, daya ta dauka, ta sanya akan plate din da yake gabanta, wata kula ta bude , haɗaɗɗiyar Miyar Egusi ce ta bayyana, ta sha Ogun da ganda ga kifi zuƙul-zukul , tayi wani irin kyau , ga mai ya kwanta a sama gwanin burgewa, tuni miyanta ya tsinke, serving Spoon ta sanya ta zuba miyar.


A hankali ta shiga cin Abin cin kanta a ƙasa, amma a jikinta take jin an tsaya mata a ka kuma ana kallonta, tun tana jin idanun basa damunta har ta fara jin idanun suna mata yawa a jikinta,cikin natsuwa ta dago ds kanta ta kalki

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment