Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

crazy wanda har ana iya hango farar fatar cinyarta, sai riga body hug , da takalminta hill , ta yafa siririn mayafi a kanta wanda ko gashin kanta bai ƙarasa rufewa ba, hannunta riƙe da waye ƙirar IPhone 11pro MAX , suna gaba ita tana baya, bakinta dauke da chewing gum tana taunawa, lips dinta ya sha uban lipstick idanunta kuwa manne da Sunglasses , ga Ear piece manne da kunnanta, tafiya take a hankali cike da natsuwar da ta zame mata jiki.dududu ba zata wuce 16 to 17 years ba, amma girman jikinta, da yana yin halitarta zaka dauka tayi 20 years,ba wai bata da kyan jiki ba ko jikinta na saurin tsufa ne, aa tsabar jin dadi ne ya jiƙa bargon jikinta, wanda yasa tayi girma sosai , amma kana kallon idanunta zakasan yarinya ce ɗanya jaagaf.


ba wata doguwa bace sosai, fara cr tasss, tana da matsakaicin jiki mai kyau,har yanzu fuskarta babu abun da ta chanja kamar ta ta yarinta ita ce sak a jikinta, sai dai gaba daya illahirin surar jikinta babu in da baai fita ba, tana da diraran jiki tana da hips sosai wanda in dai baka santa ba, kana ganinta zaka ce tayi ƙari ne, sumar kanta kuwa har yanzu tana nan da yawa da sulɓi , ta ƙara yawa sosai, gaban goshin nan gashi ne luf wanda har ya haɗe, da na girarta, tana da saje mai kyau da ya ƙarawa fuskarta kyau sosai.


har suka shige ita bata yi wata tafiya mai nisa daga mota ba, tana tafiya tana dan yatsina fuska, don yunwa take ji sosai, ga rana da ake kwallawa, wanda yasa take zufa, gashi ita ba gwanar sauri ba balle tayi, cikin natsuwa tayi Sallama cikin palon,Ayyana da tale zaune ce ta Amsa mata,tana dagowa ta kalleta, suna haɗe ido tayi saurin yin ƙasa da nata,cikin dan shagwaɓa ta zauna a gefenta , sai kuma ta miƙe tayo side din Shehi, tun daga ƙofa take kwala mishi kira "Abieh! Abieh!! Abieh!!!! Abiehhhhh!!!!!", ta faɗa da karfi, tun fara jiyo muryarta ya bude idanunshi da ya lumshe, tare da zubawa ƙofar shigowa palon ido, tana shigowa ta mugun shagwaɓe fuskarta, tare da mayar da ita ta shagwaɓa,cikin ɗira ƙafa ta ƙarasa gareshi tare da zubewa kan kujerar da yake sai dai ita tana farko shi yana ƙarshe , sai dai guiyawunta suna gugar cinyarsa, cikin muryar shagwaɓa da gajiya tace "Abieh Yunwa nake ji!", ta faɗa tana kallonsa.


a fakaice ya kalleta, tare da cewa "ai gani ba sai ki cinye ba", ya fada yana lumshe idanunshi, "Abieh Wlh yunwa nake ji", ta fada tana riƙe hannunshi, ganin yay banza da ita ne yasa ta ƙwala ihu tare da cewa "ni yunwa nake ji!", da sauri ya sanya hannunshi ya doɗe kunnensa, kafin ya kalleta da gajiyayyun idanunshi yace, "ki daina damuna!", ya fada yana kallon face nata, ita kuwa sai ta ƙara shagwaɓewa tare da cewa "Yunwa nake ji", cikin jin haushi yace ki ci kan ki, wlh boarding school zan kai ki don na gaji da ciwon kan ki", ya fada , yana dafe kansa, kitchen dinsa ya nufa bai jima ba ya dawo da mug din tea,kan stool ya dangwarar mata da shi, kafin ya koma kan wata kujerar ya zauna, da sauri ta dauka mug , zafi-zafi take shan tea din bata ko bari ya huce ba, sai da ta shanye kafin ta ajiye mug din tana mai sakin sanyayiyyar gyatsa , kanta ta jinginar da jikin kujerar tare da lumshe idanunta, zufa ce ta shiga karyo mata.


"Jazkallahu bi khair Yaaa Abieh", ta fada fuskarta kame don fil azal dama ita bata dariya ko murmushi sai an kai maƙura take yi, ko da ta fito palo babu kowa, hakan yasa ya nufi ɗakinta don yin wanka, a kulle taji ƙofar bathroom din, tsaki ta dan jaa, haka ma ɗakin su Amah a kulle haka tayi ta bin ɗakunan duk da akwai mutane a ciki.


side dinshi ta koma tana kiranshi, "me ne kuma ?", ya fada lokacin da ta iso kansa, dira ƙafarta tayi kafin tace "wanka nake son yi", kallonta yay daga sama har ƙasa kallon harara kafin yace "to bari na zo na miki". "to ba waji ne ya shiga bathroom dina ba". yana kallon TV yace "shi kaɗai ne a gidan ?", jijjiga kanta tayi tare da cewa "duk akwai mutane a ciki, Abieh nayi a cikin naka ?",ta faɗa tana wucewa, yana mata magana amma inaaa bata san yana yi ba, "Yaaa Allah na gode maka daka Azurtani da wannan fitinanniyar Ƴar, Allah ka shirya min ita", daga chan tace "Abieh maganata kake ko?", juya kanshi yay ya kalli ƙofar bedroom dinsa ba tare da yace komai ba.


bata dau lokaci sosai ba ta fito sanye da Jallabiyarsa, kanta sai ɗigar da ruwa yake da alama kuma ciki bata sanya komai ba, don ga shaidar jikinta ana kallon komai, cikin dan ɗoki ta zauna tare da cewa "Abieh baka ce ya aka ƙare ba!", ta fada tana kwanciya kan kukerar ruf da ciki, gashin girarshi ya shafa da hannunshi , ba tare da yace komai ba, "Oxford England, kuma dai Subject din da na fi so aka bani Biology, abin dadin ma Masters ba Degree ba", ya faɗa tana dan murmushin da tun shigowarta bata yi ba,jinjina kansa yay cikin tsantsar kauna da kula yace "Allah yasa Albarka ", "Ameeen!" Zayn ne da ya ƙara girma sosai , ya zama babba yace "Uhmmmm Abieh's Gal ana nan gurin Abieh , ana shan fira", murmushi fal fuskarta tace "Your Highly Welcome Uncle Z", murmushi yay tare da cewa "Thanks Darling Daughter, a hankali tace " Uncle Sayyid da Uncle Abdul fa ?", mai zaki basu ?", tura baki tayi kafin tace "zan faɗa musu na samu gurbi a Jami'ar Oxford kuma Next Week zan tafi", ta faɗa fuska kadaran kadahan, fuskarshi ce ta washe da murmushi mai kyau cikin jin dadi yace "Eyyiiiiii kaga Ƴar Abieh, to wane cause kika samu ?", juya idobta tayi kafin tace "Biology!", "naci daban kuturu, ko da yake ai gado kikai", kallon ƙasa-ƙasa Shehi ya bankawa Zayn, da sauri ya kama bakinsa, sai kuna yace "Uhmmm za aje a fafata da botany, human biology, microbiology and zoology.kenan ", dariyar da ta bayyana fararan haƙorata tayi kafin tace "Sosai ma!", kafin ta rufe baki Sayyid , Abdul suka shigo palon, fira suka shiga yi gaba dayansu cikin jin dadi.


da Maraice Zayn ya shigo, kallonsu yay tare da cewa " ku shirya zuwa dare zamu je kowa na mishi shopping na kayan makarantarsa", cikin jin dadi duk suka Amsa, kallon Sawwa da take Latsa wayarta yay, kafin yace "Abie`s Gal ban ji kin ce komai ba ?", cikin dan yamutsa fuska da alamar miskilancinta ya tashi tace "To Allah y kaimu", ta fada bata dago ba, murmushi yay kafin ya fice.


9pm suka fito daga cikin ɗakunansu suka nufo palo, dukkansu suna sanye da Abaya's baƙaƙe da Niƙaf da safa saɓanin Sawwa da tashi ƙananun kayanta ta tsuke sosai har da belt ta sanya, ta zuge waist dinta hips dinta sun ƙara fitowa sosai.........
[4/29, 12:32 AM] salmeertsanisalman: *P. 35*



"Kirjina Abieh , wayyo zan mutu!", ta fada idanunta nayin kamar zata suma da sauri ya dagata daga inda take ya yi bathroom da ita, cikin jacuzzi ya sanyata, da sauri ya sakar mata ruwa mai sanyi ganin tana niyyar Sumar masa , doguwar ajiyar zuciya ta sauke , a hankali numfashita ya shiga dawowa jikinta, ƙarfaffan numfashi ya jaaa , kafin ya furta "Alhamdulillahi!", shi ya shiga taimaka mata har ta gyara jikinta, kasantuwar rashin ƙarfin jiki da take fama da shi, jingina ta ya yi da ƙafadarsa suka fito,lokacin da suka fito lokaci ya riga da ya ƙure,cikin hanzari ya shiryata, hijab ya sa mata, ya shiga gaba ta ba bayansa kaɗan, hala suka yi Sallar kamar zata faɗi, hijab ya sa mata, ya shiga gaba ta ba bayansa kaɗan, hala suka yi Sallar kamar zata faɗi, suna idarwa ta kwanta a gurin, da sauri ya jawota jikinsa, zafi sosai yaji jikinta.


*Washe gari*


Washe gari bayan an idar da sallan asuba ya had'a mata tea mai kauri ya bata tasha, bata jima ba kuwa bacci mai nauyi ya dauketa......



Ba ita ta farka ba sai wuraren goma na safe, wanka tayi ta shirya cikin simple abaya Wanda ya amshi D'an madaidaicin jikin ta, ya kuma yi mata kyau, babu komai a fuskarta sai gloss din data shafa wanda ya bawa lips din ta daman shining, hakan ko yasa fuskarta fitowa d'ass da ita, ta fito asalin fresher (waye ga JJC) direct school sukayi bayan ta d'an tab'a break-fast......





Basu samu wani tangard'a ba, ya gama mata komai saboda sanenne ne, hakan yasa basu bata lokaci ba, don har café sukaje suka biya na biya sukayi printing ma printing daga nan kuwa sukayi gida.......



***

D'agowa tayi ta bude idanun ta da suke lumshe tun dazu akan Zaid, Wanda lokaci daya ta fara masa kallon mai juyeyyen tunani ko kuma dai kawai ta ce Mara hankali, don yafi dacewa da hakan.




Cikin nutsuwar da Allah ya mata Wanda lokaci d'aya ya nemi gushewa saboda mamaki da kuma al'ajabin da maganganun Zaid suka haifar mata a lokaci guda ta ce.



"Amma dai kana cikin hankalin ka ba wai ka tabu bane? To kai ina ka taba jin ance maka akwai aure tsanani na da kai? Kana kanin mahafina? Kace kana so na? Uhmmmm lallai kam amma sai wallahi sai na gayawa Abieh, daga haka ta mike tayi cikin daki ba tare da ta amsa ko da kira d'aya cikin wadanda yake kwala mata ba, don ita Jin abun take Kaman mafarki, wai kanin mahafin ta ne zaice yana sonta so irin na aure,? ai gwara Abie yazo ta fad'a masa yasan me zai masa ko Dawanau ta kama ai sai a kaishi don wannan ba lafiya ba, da wannan tunanin ta tattara zancen ta wartsar tayi shirin baccinta......


Har ta kwanta, taji abun ya tsunkeleta, kwata tayi cikin jaan tsaki tace "Lallai ma Uncle Zayn din nan. ~SO~ , Aure Uhmmm", ta faɗa tana juya kwanciyarta , amma gaba daya abun duniya ya addabawa rayuwarta , da ta juya sai ta ji maganarsa tana mata Amsa quwwa, ta jima bata yi barci ba, sai da kyar ta samu ya dauketa.


Dadewar da tayi bata yi barci bane kuma ya haddasa mata, rashin tashi da wuri, wanda yasa Shehi yin tunanin ko ciwonta ne ya kuma tashi, cikin saurinsa ya tura ƙofar bedroom din, da sauri ya komaya juya bayansa, ya zamana bayanshi na kallon cikin ɗakin gabanshi kuma na kallon ƙofa, "Hasbunallahu wani'imal wakeen!"ya furta yana mai lumshe dukka idanunsa, cikin dan ruɗu, da sauri ya buɗe ƙofar ya fice, itama A diririce ta faɗa Bathroom don duk abun ta ɓata taɓa bari ya ganta a yarda ya ganta yanzu ba, "innalillahi!", ta furta tana mai sawa ƙofar lock ...



kasa fitowa tayi daga cikin bathroom din, ta kusa 1 hour , kafin ta fito duk a ɗarare, sauri-sauri ta shirya, tunani take ta yi,ya ganta a yarda take ko kuwa dai hasashe ne take da ya ganta, tunda dai ko idanunsa bai ɗago ba ya juya bayansa, in kuwa ya ganta da kunya mai zai yi tunani kenan ?, tayi sakacin da Mahaifinta har yaga surar jikinta a yana yin da bai kamata ba ko kuwa ?, tunane-tunane ta shiga yi, har da ta barsa akan bai ganta ba, nan take ta bar abun a inda ya faru, jin cikinta na kira mata ciroma ne, yasa ta fita palo, tana tafiya tana tattare gashin kanta da ya bazo mata, numfashi take fesar wa a hankali, tana shaƙar daddar iskar hadarin garin da ta haɗu da sanyin AC da aka kurewa gudi cikin palon ya dauki wani irin ɗari na musamman mai haɗe da kamshin turare mai dadin gaske, kanta a ƙasa har ta zauna kan kujerar dining, komai yana a shirye, duk kuwa da cewa babu mata a gidan, amma komai tsaf , kuloli kuwa sun fi biyar, da flask da abubuwa komai na shirye tsaf-tsaf gurin ,sai kamshi girki.


Cup ta dauka, ruwan zafi mai haɗe da kayan kamshi sai tashi yake ta zuba , wanda ta zuba bai fi rabin cup din ba, ta ajiye, madara ta bude da sugar da millo, zubawa ta shiga yi, bayan ta gama ta motsa , wata Ƙaramar kula ta dauka, budewa tayi, kyakyawan farfesun kayan ciki ne ya bayyana, yatsina fuska tayi, tare da rufewa ta matsar da kular gefe, wata ta ƙara budewa, farin mulmulallan tuwan danyar shinkafa ne , ya bayyana ya samu tuƙi mai kyau, an mulmulesa a leda, daya ta dauka, ta sanya akan plate din da yake gabanta, wata kula ta bude , haɗaɗɗiyar Miyar Egusi ce ta bayyana, ta sha Ogun da ganda ga kifi zuƙul-zukul , tayi wani irin kyau , ga mai ya kwanta a sama gwanin burgewa, tuni miyanta ya tsinke, serving Spoon ta sanya ta zuba miyar.


A hankali ta shiga cin Abin cin kanta a ƙasa, amma a jikinta take jin an tsaya mata a ka kuma ana kallonta, tun tana jin idanun basa damunta har ta fara jin idanun suna mata yawa a jikinta,cikin natsuwa ta dago ds kanta ta kalki direction din da take jin ana kallonta, tsaye ta gansa cikin shigar suits , ya kame ya yi wani irin kyau , sai kamshin Black Oud yake, cikin kamewa ya shiga takowa, fuskarsa a haɗe, alamar babu wasa, kallo daya ta masa ta dauke kanta, tare da ci gaba da cin Abin cinta cikin natsuwa kamar yarda ta fara.


ya Zauna a kujerar da take kallon nata, amma bata dago ba, cikin kamewa, ya fesar da iska daga cikin bakinsa, kana kallon idanunsa kasan bai samu isassan barci ba, ga kuma alamar kuka duk sun kumbura sun yi jaa.
kamar ba zai yi magana ba yace "jiya ina kiranki kika share ni ko ?", ya fada yana murza zoɓan Zinarin hannunsa.


Jiimmm ta dan yi, kafin ta cire spoon din da yake hannunta, ta dan kallesa, kamar yarda ya kame fuskarsa itama sai ta kame tata, cikin iya sarrafa harshe da salon magana, wadda zan iya cewa gadonta tayi, tace "Ayya Uncle Zayn, naga kamar baka cikin hayyacinka ne shi isa na baka guri ka dan dawo dai-dai", ta faɗa tana kurɓan tea din da yake gabanta, kafin ya ƙara yin wata magana ta tashi ta shige ciki.



Da Misalin karfe 11pm taji wayarta na ring, daga ring din da taji kawai ta gane mai kiran, cikin sauri ta dauki wayar, cikin shagwaɓa ta furta "Chuɓaɗo!', cikin dan gajiyawa, yace "ki shirya 11:30 kina da Lecture , zan tura miki sauran bayanan ta Gmail yanzu", yana faɗa ya kashe wayarsa, cike da murna ta miƙe ta faɗa banɗaki domin sake yin wanka, tana fitowa ta bude Gmail dinta , ai kuwa saƙonsa ya baɗo cikin wayar, da sauri ta fita tana ƙara duba abun da ya turo mata, sauri-sauri ta fito daga cikin palon gidan ta nufi parking space in da Driver yake jiranta, tana shiga ya jaata zuwa School din, tun da suka shiga farfajiyar makarantar take ƙarewa makaranta kallo, ciƙe da shauƙi, don zaƙuwa, suna zuwa tsakiyar makaranta tawa driver Umarni da ya sauketa, Umarninta yabi ya tsaya, fitowa tayi cikin shigarta ta yau da kullum dogon wando ta sanya, Royal Purple ya sha yanka (crazy) sai farar T-Shirt , sai kuma ta daura baƙar Falmara wadda ta zo mata har kusan guiwa, wani kyakyawan takalmi Royal Purple Benigna Paten Tuscany Leather da yay wa ƙafarta cif-cif gwanin kyau , ga wani ɗan Ubansu Legs Chain da tasa na zinari a ƙafarta daya.


ga wani mayen glasses No Respect da ta sha, gaba daya gashin kanta ya sha gyara da kalolin mayuka masu kyau, an yi oiling din ƙasan , yay wani macaroni-Macaroni gwanin kyau, daga chan sama kuma an yi fixing dinshi ya kwanta har gaban goshinta, siririn mayafine fari a kanta, sai Agogon Rolex na mata, mai kyau cif da tsintsiyar hannunta, sai zaɓɓan Zinarai masu kyan gaske, kyakyawar hand bag dinta, ya ƙarama tana maƙale a hannunta, sai kuma wayarta da take dayan hannunta. sanyayyiyar iska take shaƙa mai wadda tayi mata dadi sosai.


tafiya ta fara cikin natsuwa, gaba daya idanun Yan makarantar ne ya dawo kanta, da ace yau ta fara fitowa cikin mutane, ko yau ta fara shiga cikinsu, da zata mugun firgita da yanayin kallon da ake mata, kai in ma aka yi rashin sa'a da mace ce mai tsoro sai ta ringa jin fargaba ko ma ta ringa harɗewa, amma ita tsaf take takunta kamar yarda ta faro daga gida.


Tana tafiya tana duddubawa har taga Department dinsu, har cikin class dinsu ta shiga, sai dai babu kowa, dan zama tayi ko zata ga wani yazo, ta bisa izuwa Theater din da zasu yi Practical din da suke dashi amma shiru, har 12 tayi, ganin haka yasa ta fito tayi tana dube-dube amma bata ga Theater din ba, wasu Mutane biyu ta tare, da sauri suka daddare don dayawansu tunani suke ko Aljana ce don kyanta har ya zarta inda ake tunani, sam wani lokacin sai ka dauka ba mutum bace musamman in tana yin wasu abubuwan.



don kanta ta gaji da yawon da take ta zauna, a mugun gajiye, wayarta ta fitar daga cikin jakarta, kira ta danna masa amma tana ring bai dauka ba, sai da tayi masa kira biyu bai dauka ba, Innalillahi! kamar za tayi kuka ga yunwa da ta fara ƙwaƙular mata hanjin cikinta, tana cikin tunanin abun yi, taji kiransa cikin wayarta, da sauri ta dauka, tana kara wayar a kunnanta ta sakar masa kuka, numfashi ya fesar daga chan ɓangaren.


"Wayyo Allah na Chuɓaɗo!, gantalewa ta gama samuna ni kam", ta fada hawaye na zubo mata, "lafiya ?", cikin shagwaɓa tace, "uhmm uhmmm to ba na kasa gane Theater din ba, gashi kuma na kasa samun wanda zai kai mi, kowa ma tsorona yake", dan murmushi ya saki, don yasan za'a rina tunda Driver yaga ya masa yarda abun ya kasance .


"Me ?",
"Abieh Wlh kazo ka dauke ni," ta faɗa tana ƙara sakin kuka, "Okay¡ okay! gani nan", ya fada yana kashe wayar, anan ta ci gaba da zama har ya ƙira wayar....
[4/29, 9:15 AM] salmeertsanisalman: ```Assalamu alaikum!. fatan kowa yana lpy

ya kuke duka ?.

ya Aiki ?.

ya Ibada ?

ya shirye-shiryen Sallah ?.

ya kuma bankwana da wannan ƙasaitaccan watan mai Albarka ?.

to Ubangiji ya ƙarɓi Ibadunmu.

Allah yasa mun yi ibada karɓaɓɓiya.

Allah ya samu cikin bayinsa salihai yantattu.

Ubangiji ya gafarta mana.

ya shiga cikin lamurranmu.

shiryamu.

ya Shiri Iyalanmu.

yaji ƙan magabatanmu.

ya gafarta musu.

yasa Aljanna ce makomarsu .



Ameeen thamma Ameeen```







*P. 31*







"Ya dai ?", ya tambaya yana mai kallonsu duka, "Ammy ba lafiya!", ta faɗa tana goge mata Zufar da ta wanke mata fuskarta, ''mai ya same ta!", ya tambayi Sawwa yana mai ƙarasawa gurin da suke da tsantsar kulawa, gefen Sadiyya daga bayanta ya dan zauna kanta ya daura a kafaɗarsa tare da rankwafowa, yana mai duban fuskarta, wadda ta jiƙe da zufa, sai cizan lips take, ganin yarda take ne yasa ya kalli Sawwa tare da cewa "Maza kice wa Driver ya fito da motar nan", ya faɗa yana gogewa Sadiyya fuskarta.

kasa tafiya tayi daga gurin da take, tayi sagale tana kallonsu, "yi sauri", ya faɗa ba tare da ya ɗago ba, ganin dai bata tafi bane yasa ya ɗago kanshi yana kallonta , yarda ta tsaya abun ya basa mamaki sosai,cikin ɗan daka tsawa yace "bakya ji ne ?", riƙe hannunshi Sadiyya tayi, tare da jujjuya mishi kanta, da sauri ya dauketa zuwa waje, yana zuwa ya tarar da Driver ma a tsaye in da ya barsa bai tafi ba.





sanyayan numfashi ya fesar tare da furta "Alhamdulillah", da sauri ya shiga cikin motar tare dawa Driver nuni da ya shiga, "Mukhaifat hospital zaka kaimu", ya fada chan ciki, yana mai shafa kan Sadiyya da take ta murƙususu, 10minutes ne ya kaisu hospital din, suna zuwa bai jira nurses sun kawo gadon daukar marae lafiya ba ma ya dauketa zuwa ciki, kai tsaye labour Room (LR) ya nufa da ita, yana zuwa ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, nurses ne suka rufa masa baya, yana zuwa ya shimfiɗeta kan bed din.





Taimakon gaggawa suka shiga bata, amma inaaaa duk iya yinsu na ta haihu da kanta kasawa tayi, awa 2 chasss tayi ana abu daya, ganin ƙarfin ya ya kare ne gaba daya, gashi ta kasa haihuwa har ta fara alamun jijjiga ne , ga jini da ya wani ɓalle da karfin gaske kamar an ɓuɗe fanfo yasa Shehi kallonsu cikin ruɗu da tashin hankali yace

"Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un she can't give birth!, we need the surgery for her now, please arrange everything as soon as possible please!", ya fada cikin tashin hankali da kiɗima.





da sauri suka fice domin shiryawa, shima cikin sauri ya nufi wani room bai jima ba sai gashi ya fito sanye da kayan aikinsa, gurinta ya ƙarisa ya riƙe mata hannayenta yana kallonta ganin yarda bakinta ya mugun bushewa,cikin jin jiki ta fara bude idanunta, tana lumshewa a hankali, nurses din ne suka dawo tare da cewa "Sir Everything is ready!", jinjina kanshi yay tare da cewa "okay ina zuwa", ya fada yana gyara mata kwanciyarta, rigar tiyata ya sanya mata a jikinta,duk tana jinsa, bayan ya gama ya juyo zai gangara gadon zuwa Operation Room,da sauri ta riƙe hannunshi, A wahalce ta idanunta , cikin ƙasa da maganarta tace "Bana so! bana so!! bana so!!! kar ka bari a yankani", ta faɗa tana jijjiga kanta, shafa kanta yay tare da cewa "don mai ?,kiyi hkr samun sauƙin ki ne CS din, zai rage miki wani abun" riƙe hannunshi ta ƙara yi, cikin jin wani abu na danne numfashinta tace "na san bazan haifi cikin nan ba, don haka kar ku yanka ni," ta fada tana jujjuya kanta, bai saurareta ba ta bude room din zai fita da ita, "kar ku yanka ni bana so, ku barni naji da raɗaɗin fitar rai kar ku ƙara min wani a kansa, ku bar ni bana so", ta fada lokacin da taji yana gungurata izuwa dayan ɗakin.







lokacin da suka shiga ciki babu kowa sai kayan aiki da aka

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment