Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haɗa babu abun da babu wanda ya danganci fiɗa, baya ya bata yana aikinsa, awon bp ya fara mata, wanda shi ake farawa wanda za'awa CS don ba'a yanka mutum alhalin bp dinsa ya hau, "Alhmdllh!."

ya furta lokacin da yaga jininta dai-dai bai hau ba, haɗa wata ƙatuwar Allura ya shiga haɗa zai mata.





ya gama yana ɗagowa da niyyar yi mata, ya dan jaa baya idanunshi a dan warwaje, yana kallon yarda jikinta yake wani mummurɗewa , tana kanannaɗewa kamar macijiya, cike da wahala take nannaɗewa har ta daɗe jikinta sosai ta koma ƙaton mesa(Babban Maciji), cikin wannan sabuwar suffar tata take ta gumurzu cike da wahala da zafin naƙuda.







shi kuwa Shehi tsaye yay yana kallon ikon Allah, ta fi 10 minutes tana mummurɗa jikinta, tana ta halainiya kafin ya fara riƙidewa zuwa mutum dai kamar da, lokacin da zata t koma normal Sadiyya , fuskarta tayi wani irin fari tarrr , numfashinta na fita da sauri sauri, wanda ya fita baya dawowa wanda ya shiga baya fita, kirjinta yana wani irin ɗagawa, maimakon cikin ya sauko ƙasa sai yay wani irin hayewa har kan kirjinta, ganin tana dafara ne yasa ya matsa kusa da ita sosai cike da tsantsar madarar tashin hankali da take kwarara a cikin jikinsa,matsawa yay sosai gurinta, tare da riƙe hannunta, itama riƙe hannunshi tayi sosai, a hankali ya fara faɗin "Laa'ilaha illalahu! Muhammadurrasulillah!" , ya shiga maimaita mata, cikin kunnanta, A hankali ta fara maimaitawa har Allah y bata ikon yinta gaba daya, kanshi ya jinginar da gadon yana kirariwa Rabbassamati wa rabbal Arshil Azeeem!, har lokacin da Rai yay halinsa.





kanshi ya ɗago daga sunkuyarwa da yay, yana jin kamshi na tashi cikin natsuwa, nurses ne suka shigo, ganin yarda take kwance jikinta a sake yasasu fahimtar rai yay halinsa, cikin sauri-sauri suka gyarata tare da damka masa gawarta, da kanshi ya gungura gadon nata zuwa waje.





Ambulance aka haɗa masa domin kai gawar gida, shigar da ita akai sukai gida.





Suna zaune a palo, suka fara jiyo ƙarar Ambulance , Ayyana ce tace "kamar ƙarar Ambulance nake ji a layin nan" ta faɗa tana dan ƙara saurarawa, "Anya kuwa ?", Zayn-maleeq ya faɗa, Umma Jakadiya da zuciyarta take ta tsinkewa tun tashinta yau tai shiru tana sauransu.

Sayyid-Maleeq ne ya shigo cikin palon da sauri yana cewa "wai mai yake faruwa ne ?, ga Ambulance ta shigo gidanan ", ya fada yana kallonsu.





A tare suka miƙe, tare da yin waje domin gasgata maganarsa, suna fitowa barandar part din Ambulance na tsayawa a gaban part din,cike da mamaki duk suke kallon Ambulance din har aka budeta, nurses biyu ne suka fara fitowa, wasu da suke ciki suka gangaro da gado, kamawa suka yi aka fito da gadon,ana fitowa da gadon wata iska mai karfi ta kaɗa wadda tayi sanadiyar kaɗawar tsirran da suke gurin , hakan kuma yasa farin ƙyallan da aka rufe fuskarta dashi ya yaye.





baya Umma Jakadiya tayi, da sauri Ayyana ta tarota ganin zata faɗi, sai dai inaaaa sai da ta kai ƙasa cikin hali na rikicewa, kafi wani yay yunƙuri motar Shehi ta shigo cikin gidan, bai ko jira an bude masa ba ya fito da kansa, fuskarnan tayi jaaazir , duk da tsananin tashin hankalin da yake ciki amma ba zaka iya ganin hakan akan fuskarsa ba.





cikin rashin kuzari yake tafiya, a hankali tare da wa nurses din alama da su dauko gawar, haka suka shiga ciki yana gaba suna biye da shi a bayansa da kuma gawar, su kuwa yan waje gaba dayansu babu mai ruwan jikin iya tafiya gaba daya guyawunsu sun yi wani irin sanyi, ba kamar Zayn , da Ayyana, su Amah kuwa tuni kuka suke.





dakyar Ayyana ta iya tashin Umma Jakadiya suka shiga ciki, sai dai dukkansu sun kasa kukan , sai kukan zuci wanda yafi na fili ciwo,Shehi ne da kansa yawa gawar wanka tare da kimtsata, sai dai komai da yake cikin mugun karfin hali da jarumta yake yinsa, bayan ya gama mata wankan ne ya dauki Likafani zai fara shiryata, likafanin ne ya zame a hannunsa ya fada kan fuskarta.

" Uhmmm Wannan Likafanin gwanin kyau, kama Asawa mutum shi" yaji yo Amsakuwwa muryarta a ranar da aka ɗinko likafanin na Maza da na Mata.

kan kirjinta ya daura kansa, yana sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, kirjinsa kamar zai bude wani abu mai nauyi yake jin yana taso masa tun daga kasa har samansa, dakyar yake fusgar numfashi.





A hankali ya dago kansa, tare da fara sanya mata likafanin, yana yi yana jaan ajiyar zuciya har ya gama,bayan ya gama ya dauki wani oud mai masifar kamshi,wanda ita ce ta siya masa shi da kanta, ya shiga sanya mata, tuni wani irin sirihittance kamshi ya fara tashi a jikinta.

yana gama kimtsata ana kwankwaso ɗakin don lokaci ya tafi sosai gashi mutane sun haɗu sosai, bai iya magana ba, sai da Zayn ya gaji da kwankwasarwa ya bude ƙofar ya shiga,jingine da gado ya gansa yana jaan tagwayen Ajiyar zuciya, A hankali yace "Hamma Al-umma sun gama haɗuwa ga kuma Makara an kawo", ya fada yana bawa su Sayyid da suka taho da makara guri suka shiga ciki.





shi da kansa ya dauketa ya sanyata cikin makarar, daya bayan daya aka ringa kiran Yan uwanta suna mata Addu'o'i , har da Sawwa da idanunta a ƙame suke tama ko kasan yin kukan, sai walwala idanunta take yi, sai da kowa ya shigo kafin gaba dayansu suka kama gefe da gefe suka dagata sama , suka fitar da ita, ko da suka fito gaba daya mutane sun haɗu sosai, har Sarkin Garin Makkah yazo da Limamai da dukkan wani da suke zaman mutunci dashi sun hallara, A gaba aka ajiye Gawar, Baya Shehi ya tsaya tare da nunawa Sarkin Makkah gaba, yace "Bissimillah" cikin dan jin dadi da nuna karamcin da yay mai, ya jinjina kansa tare da shigewa gaba, shi ya limanci Sallatar gawar, har Aka idar, mota aka sanya gawar, kafin daga Bissani suka shishiga suma don Makabartar tana da nisa sosai daga gidansu.





lokacin da zasu ƙarasa an gama dukka abubuwan da suka dace, Sheykh Aliyu Hydar Aliyu ne, ya fara musu Nasihohi da Addu'o'i tare da neman rahmar Allah, kusan 1hour yana ta Nasiha game da mutuwa da jin tsoron Allah, kafin ya nunawa Shehi guri, matsawa yay, Zayn da Sayyid da Abdul ne suka dauketa tare da miƙa masa ita, karɓarta yay a hannunsa " ```Bissimillahi wa ala Sunnati Rasulillahi```". ya fada a lokacin da ya shigar da iya cikin ramin kabarinta wanda shine gidanta na gaskiya, bayan sanyatan ma sai da aka yi Addu`o`i kafin a sanya mata duk abun da ya dace, Shehi ne ya fara zuba mata ƙasa, kafin daga bisani aka zuba mata aka rufeta, bayan an gama ne Shehi ya hango wata yar ƙofa kadan da ba'a kulle ba, A hankali ya ɗibi ƙasa da hannayensa ya zuba a gurin tare da tattoshe duk in da yaga wata kafa," ```Allahumma`gfirlahu Allahumma Sabbithu``` " gaba daya suka Amsa da "Ameeen y Rabbal Alameen". bayan ya gama ne, wasu siraran hawaye masu ɗumi suka zubo masa, sai kawai ya sulale a gurin ya zauna akan kafafunsa, akan kabarin ya daura kansa, bai san lokacin da kuka mai ƙarfin gaske ya kwace masa ba, A ranshi ya fara raya ```Yanzu duk kaunar da take tsakaninka da mutum haka zai mutu kazo ka rufesa da ƙasa, har ma in kaga wani guri bai rufu ba kasa hannunka ka ƙara rufewa, wai kuma ma wannan ce tsananin kaunar da kakewa mutum``` "Yaaah Subhannalillah! Innalillahi wa`inna`ilaihi raju`un! Hasbunallahu wani`imal wakeeen! Astagafiroullah!!³ laailaha illah²! " ya furta a bayyane, yana mai jin damuwa a ransa, Zayn ne ya riƙe hannunshi, tare da girgiza masa kansa idanunshi cike da kwalla, Sayyid ne ya ƙara dafasa, a hankali suka fara rarrashinsa, Sarkin Makkah ne ya riƙe hannunsa suka fito daga cikin Makabarta, motocinsu suka ƙara shiga suka nufi gida, kafin su koma an shimfiɗa wasu manya-manyan carpets na Alfarma

, jeep - jeep ne na Alfarma suka fara shigowa cikin gidan, duk girman gidan amma har sai da aka yi parking motoci a waje, gaba daya suka fito suka nufi kan carpets din, zama suka yi sai lokacin ne mutane suka ringa zuwa gurin Shehi suna masa gaisuwa, hannu Sarkin Makkah ya miƙa masa, ganin yarda fuskarsa take ne yasa yace " ```Innalillahi ma`akhaza, wa lahu ma`aatda`wa kullu shai in indahu bi Ajalim Musamma```" (Hakika Abin da Allah ya dauka nasa ne, haka ma wanda ya bari ma nasa ne, kuma kowa ne abu a wurin shi yana da Ajali ).



jinjina kansa yaytare da cewa "```Shukran laka! Jazkallahu bi khair```!" , ya fada yana miƙa masa hannu, musabaha suka yi, kafin ya tafi.





haka suka yini suna ƙarɓar gaisuwa, sai bayan Isha ya shiga cikin gidan yana fesar da sanyayyiyar iska mai cike da kasala , yana tafiya yana tasbihi har ya ƙarasa shiga cikin palon part dinsa, kwance ya samu Sawwa idanunta lumshe, kamar mai barci, fuskarta tayi wani sawai-sawai tayi haske, babu alamar damuwa akan fuskarta , dan kallonta yay, kafin ya shiga ciki bedroom dinsa, komai need ya tarar a kimtse a gyare , kai tsaye bathroom ya wuce, jikinshi ya fara tsarkakewa domin tun tashin da yay wanka lokacin bai ƙara yi ba, wanka yay wa jikinsa na tsarki da kuma wankan soso da sabulu, bayan ya gama ne ya fito daure da towel, kimtsa jikinsa yay cikin wata tattausar Jallabiya mai taushi da tsantsi, turarensa na Huge Boss ya feshe dukkan jikinsa dashi,kafin ya zura bedroom Slippers dinsa ya fita, a in da ya barta nan ya sameta, yana yin fitar numfashinta ne ya tabbatar da barci ya dauketa, daukarta yay zuwa Bedroom dinsa, kan bed ya shimfiɗar da ita kafin ya wuce , gurin glover Switched dinshi yay daga on zuwa Off kafin ya wuce gurin Ibadarsa, Sallah raka'a biyu yay,kafin ya fara karatun Al-qur'ani cikin suratul Lukman , karatu yay sosai , har guraren 2 a hankali ya fara jiyo sautin kukan Sawwa da dan surutanta, chan ƙasa, cikin natsuwa ya fara yin ƙasa da karatun da yake, kafin ya miƙe cikin kamala ya nufi inda take din, kwance ya sameta idanunta lumshe amma wani irin kuka take mai ban tausayi, kukan da yafi kama da na rashin jigo, ko in ce kukan da yay kama da na rashin wani makusanci masoyi,mai tsayama a dukkan wasu harkokin rayuwa, kukan irin wanda ake yi sau daya tal a rayuwa,kuka irin na fita Hayyaci, kukan da daka gani kasan ma'abocin yinsa baya cikin cikakkiyar natsuwarsa da tunaninsa.





tsakiyar bed din ya hau tare da jaawota jikinsa ya jingina bayanta da kirjinsa, ya sanyata a jikinsa, cikin wani irin rauninsa da ya bayyana, ya fara jijjigata da magana a hankali, wadda tafi kama da raɗa-raɗa a hankali chan ciki, idanunta ta shiga budewa, juyowa tayi garesa tare da kankamesa, wani wahalallan numfashi mai dauke da t.......
[4/29, 9:25 AM] salmeertsanisalman: P. 33*







Tana riƙe da ƙaramar hand bag, da kuma gyale ta rataya sa a kanta, da kadan ya rufe kanta, "muje ko ?", Zayn ya faɗa yana yin waje, da sauri suka tashi suka bisa, ita kam sai da ta gama shan iskarta kafin ta biyosu a baya, tana tafiya kamar bata son taka ƙasa, cikin natsuwa da ta game mata dukkan jikinta take tafiya har ta ƙaraso gurin motar, duk suna baya, Zayn ne kawai a gaba, tana zuwa ta bude baya ta shiga, kallon Juna suka yi, kafin suce "ke fa zaki shiga gaba", shiru tayi bata kallesu ba, haka bata tanka musu ba, sai ma wayarta da ta shiga dannawa, tana dan tauna chewing gum cike da natsuwa, "Mtswww Allah y yaye miki wannan halin naki", ko a jikinta don ko alamar ta damu da maganar tata bata nuna ba,balle ta mayar da martani.





Amatullah ce ta bude bayan ta fita ta koma gaba, shi dai Zayn yana sauraransu bai ce komai ba, sai kallon Sawwa da yake, ta cikin mirror din gaban motar. "Bissimillahi!", ya furta yana mai yiwa motar key, a hankali ya fara tafiya da motar,har suka fita daga gidan, suna shan kwanar fita daga layin Motar Shehi yana shigowa, motar tasu ya dan bi da kallo, wayarshi ya dauka tare da karawa a kunnansa.





Wani tashin kiɗa mai dadi ne ya fara tashi a wayar, idanunta ta dagw tare da kallon Screen din Wayar "Abieh!" ne rubuce a jiki numfashi ta sauke, kafin ya dauki wayar, A hankali ta furta "Chuɓaɗo!",shiru ya dan yi kafi yay magana a hankali, tura baki tayi kafin tace "Super market fa!", ta fada tana kallon hanyar da suka dauka, "uhmmm!", ta furta kafin ta kashe wayar, Labari suka shiga yi, some times Zayn yakan sakota cikin firar sai dai bata biyawa daga "uhmmm! sai uhummm", shi kenan maganar tata.

har suka ƙarasa Khaira Super Market, bb wanda tacewa ci kan ka, ko da suka ƙarasa duk fita suka yi, Zayn ne da kansa ya zagaya baya ya buɗe mata ƙofar motar tare da cewa "Chuɓaɗon Abieh sauko", ya fada yana dan matsawa baya.





sai da ta shaƙi iska kafih ta sauko da ƙafarta daya,dayar ma ta jima a ciki kafin ta fito da ita, gyara zaman gyalen kanta tayi ta daura jakarta a kafaɗa, ta gyara zaman eyes glasses din idanunta da kyau, ta gama kallon komai da yake gurin kafin ta fara takawa cike da izza da haiba da wata irin kamala ta musamman, cikin natsuwa take taka ƙafafunta a ƙasan gurin idanunta a ƙasa, tana motsa bakinta a hankali, suna gaba tana biye da su a baya, har suka shiga cikin super market din.

bayan sun shiga ciki ne , ya kallesu a hankali yace "kuje ku zaɓi abun da kuke so", dan kallon Sawwa tay yace "ke kuma muje na zaɓa miki", dan kallonsa tayi ta ƙasan ido kafin ta yi gaba yana binta a baya, haka ya ringa siya mata kayayyaki, na kwalliya , Performs , kayan ciye-ciye da lashe-laahe har kayan sawa, layin Abaya's suka bi, haka ya ringa ɗibar mata, ita kuwa sai taɓebaki take, dan sam ba kalar kayan sawar ta bane.





sai guraren 12am suka fito daga cikin Super market, din kowa a gajiye, cikin natsuwa take takawa idanunta a ƙasa tana tafiya tana dan fitar da hucin gajiya, idanunta har wani lullumshewa suke yi, da sauri ta ɗago dara-daran idanunta ta zubawa, wanda suka gabza uban karo da shi,kyakyawan gaske ne sosai fari tasss dashi Alamar hutu ya ratsa jikinsa dakyau, wani kallon raini yay mata ya sa kai zai shige, jaawoshi yaji an yi,kafin ya juyo yaga aikin waye yaji, saukar wasu tagwayen maruka,masu Azabar zafi da gigita kwanya, kafin ya dawo hayyacinsa ya duba yaga aikin waye gurin ba kowa, da sauri ya juyo yana waiwayen bayansa, jikin mota ya hangeta tana mishi wani kallon ƙasƙanci mai cike da wulaƙanta,bata da raina babba,bata da wulaƙanci da raini, amma ta tsani a wulaƙantata ko a rainata, duk wanda ya nemi cin zarafinta za tayi iya bakin ƙoƙarinta taga ta wulaƙantasa kafin ya wulaƙantata.







idanunshi da sukai jaajir ya watsa mata cikin tsananin tsantsar tsana, cikin harzuƙa yay kanta, zai mareta , riƙe hannunshi tayi ta saukesa ƙasa kafin ta furta "ƙusƙure mafi muni da zaka aika a rayuwarka kenan", ya fada tana watsa hannayensa, kafin ta sakar masa wani murmushi mai bawa wanda akawa haushi, tana juyawa ta shige mota ranta a mugun ɓace.

maganar duniya suka mata tai banza da su tana kallon yana yin gari da yake ta haɗa wani irin hadari, kafin su ƙarasa gida hadarin ya yo sama, sai iska mai karfi ce take kaɗawa .





ko da suka ƙaraso gida, kowa ya fita a motar Amma ita tana in da take bata ko motsa ba,buɗe mata Zayn yay tare da cewa "to fito!", in motar da take cikinta ta yi magana to itama tayi,bata ko kallesa ba , idanunta na tsaye guri daya, ba yarda ya iya da ita ya shige, ita kuwa tana gurin, a hankali ruwan sama ya fara sauka a garin mai daraja, tana fara jin saukar ruwan ta fito daga motar a hankali take tafiya tana sauke zazzafan numfashi mai zafin gaske

, garden ta nufa, kan wasu kyawawan kujeru ta zauna, tana sauke numfashi , zama tayi ta nannaɗe ƙafafunta kanta a sama idanunta a buɗe, ruwa na dukan fuskarta.





A hankali ya fara saukowa daga Upstairs yana sanye.

da Jallabiya fara , sai wando baƙi har ƙasa, slippers ne sanye a ƙafafunsa, yana tafiya yana fesar da numfashi a hankali, har ya kai step din ƙarshe, wanda suke zaune a cikin palon yake ƙarewa kallo daya bayan daya.





yaga kowa amma ita bai ganta ba, taune lips dinsa yay, kafin yace "Zayn where is she ?", cikin kula yace "tana mota", wani kallo yay masa kafin yace "Mota! amma kana sane da hadari a garin", shiru Zayn yay bai ce masa komai ba, gyaɗa kansa yay ya waje, cikin sassarfa ya nufi gurin motar, babu kowa a ciki sai veil dinta da yake yashe a

gurin, harshenshi ya dan ciza, kafin ya nufi hanyar garden, tun daga nesa ya fara hangota tana zaune, fuskarta na kallon sama, idanunshi ya tsura mata, har ya ƙarasa gurin da take, kanta ya tsaya yana kallonta, a hankali ya sanya hannayensa ya dan mari fuskarta, a hankali ta mayar da idanunta gareshi,numfashi ta sauke da ƙarfi kafin ta lumshe idanunta sa sauri, bai mata magana ba sai hannunta da ya riƙe suka yi ciki, ta ƙofar baya ya nufa da ita izuwa side dinsa, ita dai tana biye da shi a naya bata ce masa komai ba har suka shiga palonsa, bedroom suka shiga,kai tsaye ya nuna mata hanyar bathroom, cikin sanyi ta wuce ciki, shi kuwa palo ya koma, kai tsaye kitchen ya nufa, gas ya kunna ya sanya tunkuya ruwa kaɗan ya zuba, da sugar sai Lipton ,wani dan guri ya ƙarasa, budewa yay , nan danan wasu yan robobi masu kyau suka bayyana kusan guda bakwai ko wacce a rube da murfinta daya, bayan daya ya dunga budewa yana diɓar abun da yake ciki yana zubawa, sai da ya gama tass ya rife tunkunyar ya mayar da komai.





matsawa gefe ya dan yi, 3 minutes tsakani tukunyar ta fara tafasa, tuni kamshin kanunfari, citta, masoro, kimba, tafarnuwa da sauran kayan yaji suka fara tashi sosai, sai da ya bari ya ɓarka sosai(tafasa) kafin ya sauke, tacewa yay a cikin wani dan flask , kashe gas din yay, ya dauki ƙaramin tea cup ya koma palo, zama yay tare da jawo stool ya ajiye a kai, green tea din ya zuba a cup ya fara sha a hankali, sai da ya sha cup biyi yaji ƙarar bude ƙofar bedroom,bai dago da idanunta ba har ta ƙaraso gurin da yake, gefensa ta zauba tare da dan zamewa jikinsa ta daura kanta akan kirjinsa, hannunta ya daura kan nasa hannun da yake kan cinyarsa.

gajiyayyun idanunsa ya dan lumshe cike da zalar gajiya, "Chuɓaɗo!", ta furta cikin sanyi sosai muryarta har tana dan rawa, lumsassun idanunsa ya bude ya kalleta cike da tsantsar kulawa.





zameta yay daga jikinsa ya ajiyeta akan kujerar,yana kallonta ,idanunta yaga sun yi jaaa, yatsun hannunta ya kama da nasa, ya dan murza a sannu, tare da cewa "me !. ?", kallonshi ta danyi, hawaye ne suka fara ƙoƙarin taruwa a idanunta, da sauri ta kifa kanta akan cinyarsa, ta kasa cewa komai ganin bata ciki mood din da ya kamata ya tirsasa mata yin magana tunda bata so yasa yay shiru yana mai cusa yatsun hannunsa cikin tsakiyar fatar kanta tana dan sosa mata kaɗan -kaɗan.





Green tea din ya tsiyaya mata a cup, ya miƙar da ita tare da cewa "sha kafin kija min", ya fada yana daura mata cup din a baki, zafi da kamshin tafarnuwar da suka bigeta ne yasa tai saurin bude bakinta da sauri ya fara zuba mata tea din, sai da ta shanye tass kafin ta cire kanta, tana mai jin tafarnuwar na taso mata.





Zufa ce ta shiga karyo mata daga dukkan sassan jikinta, duk kuwa da iskar da ke da akwai cikin palon amma har fiffita take da hannayenta, a hankali ya fara fesa mata iskar bakinsa mai sanyi da dadi, lumshe idanunta ta shiga yi alamar natsuwa ta fara saukar mata a cikin jikinta, a hankali take sauke numfashi kanta a ƙafadarsa, a hankali tace "Ni!", sai kuna tai shiru, cikin kasa fahimtar mai take nufi da ita din yasa ya zura mata idanu, ya fuskanci akwai abun da take son faɗa sai dai da alama abun yana mata ɗaci ko tunawa tayi yana mata zafi.





ganij yarda take ne yasa ya shafa kanta tare da cewa "cool your mind down!", ya fada yaba dan dukan bayanta, numfashi ta ci gaba da saukewa mai dan zafi+zafi da kuma sauri-sauri,kusan 10minutes kafih ta daina,gyara zamanta tayi kamar yarda ya yi, a hankali yace "Faɗa min!", fesar da lumshe tayi kafin tace ", Chuɓaɗo mai yasa wasu mutanan suke abu kamar Dabbobi ?", zuba mata idanu yay, "ya bugeni naji by mistake hakan zai iya faruwa, amma how dare he is , da zai wuce ko hkr bazai ban ba", shiru y dan yi kafin yace, "ki daina haɗa Dan Adam da Dabba domin Allah ma ya ƙarrama shi, sannan akwai banbance - banbance sosai tsakanin Dan Adam da Dabbobi , ki dai na , sannan kows da kalar yana yinsa, mai zai sa ki damu don bai bace miki kiyi hkr ba, nasan sai ya girme miki sosai" tura baki ta dan yi kafin tace, "to kai kuma Chuɓaɗo goyon bayansa kake ?", ta faɗa tana juya ba, taɓe baki yay kafin yace "ki kula dai bana son kinawa mutane rashin kunya dan sam ba tarbiyar da na baki ba kenan", ya fada yana daura ƙafarsa kan stool.





shiru tayi bata ce komai ba, gyara zamansa yay, tare da zubawa TV idanu, ita kuwa miƙewa tayi zata fita, da sauri yace "Ke!", juyowa tayi tana kallon bayanta, "wuce ki sa kaya", ya fada ba tare da ya kalleta ba, diddira ƙafarta ta fara , cikin shagwaɓa tace "to ai ni zafi fa nake ji", ta fada tana zuwa gabansa, "Chuɓaɗo!", wani kallo da ya mata sai da yasa ta sha jinin jikinta, a hankali jikinta a sanyaye ta wuce bedroom dinsa,bata jima ba sosai ta fito, sanye da jallabiyarsa brown , ta naɗe kanta da gyalle, bata mishi magana ba ta fice tana tura baki, shima lumshe idanunshi yay, yana magana a ziciyarsa.





*TUESDAY*





Tun Asuba gidan yake fama da hayaniya, kasantuwar Ranar ne ranar tafiyar Sawwa England , cikin shiri gaba dayansu suka fito palo, anan suka yi break fast, bayan sun gama ne Ayyana ta dubi Sawwa cikin kula tace "ga Break fast din Abienki ", ta fada tana nuna mata tray din da yake gefe, cikin sanyi jiki ta dauki tray din tayi hanyar part dinsa, a hankali tayi sallama cikin palon , raɓar sa palon ya dauka ne ya ratsa dukkan jikinta, a hankali ta lumshe idanunta ta kuma buɗewa akan fuskarsa da tayo wani fresh sai Annurin da Hasken Musulunci take fitarwa, gashi tayi wani sahihin kyau, sakamakon Aski da gyaran fuskar da aka masa, wanda ya fito da fuskar sosai, ba tare da ya bude idanunsa ba,

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment