Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ana wannan ruwan kafin ya dan fara tsagaitawa,lokacin kuma ne ya fara tunanin Sawwah dan yasan in ba wani iko na Lillahi ba to tana chan ciki ruwa, duk kuwa da tasan Lalurarta amma ita dai tana kaunar ruwa, wanda har ya rasa gane wacce irin soyayya ce tsakaninta da ruwa, anan ne ra'ayinsu ya mugun banbanta, dan shi mutum ne mai kyankyami da rashin son ruwa, baya son ruwan sama ya taɓa jikinshi sam
.


sai Bayan Magrib kafin ruwan ta tsagaita, amma duk da haka garin bai daine walƙiya ba, bai kuma daina cidaba ba da rugugi, bai fita ba yana nan har bayan Isha' kafin ya fito a hankali yana fesar da sanyayiyyar iska daga bakinsa, yana tafiya yana dan lumshe ido, gajiya ce a jikinshi ga wata ja'irar Yunwa da take damunsa dan rabonsa da Abin ci tun daren jiya, dan ko da safe bai ci komai ba.


A sanyaye cikin siririyar murya Yay Sallama cikin palonshi, Sawwa da take tsaye gurin kujera tana zazzare ido tayi karfin halin karɓa masa Sallamar gaba daya jikinta na dan cira alamar sanyi ya fara ratsa bargon jikinta, yana yin yarda tayi magana kawai da sanyin da muryarta tayi, ta tabbatar mishi da ta shiga cikin ruwan, kuma da Alama sai da ta faki ido kafin ta shiga dan babu kowa cikin palon, jinjina kanshi ya dan yi, yana mamakin wace iriyar Yarinya ce da bata jin magana, sam bata jin maganarsa in zai sa doka so dubu zata karya , ya hanata shiga ruwa ba daya ba, ba biyu ba amma taƙi dainawa.


Haka kawai Zuciyarsa ta raya masa, ya dan barta yau da halinta taji yarda ciwon jikinta yake sosai, in taji taji yarda abun yake may be ba zata kara bari ruwa ya tareta a wani gu ba balle ta shiga ciki, anan cikin palon ya barta ya hayewarsa sama dan dama bai ko kalleta ba , tun bayan shigowarsa.


zamewa tayi in da take tsaye ta zauna tana jin ƙafufunta na mata wani mugun kwankwatsa, ƙafafunta ta riƙe da hannayenta gaba daya naman jikinta na wata iriyar rawa na ban mamaki.
kamar saukar Aradu haka ciwon ya mamaye jikinta gaba daya yana wata kwankwatsa da cira kamar zai zazzalo ƙasa, a hankali hawaye suka shiga silalo kata akan kumatunta, gashi ita dai irin Silent killer din nan ce, ko abu zai kasheta ba zata yi magana mai karfi ba, miskilancinta da izzarta abun mamaki ne sosai, dan irinyarda take tafiyar da lamurranta sai du'a.


ta dade sosai a gurin tana cikin mawuyacin hali, hawaye nata silali mata daga cikin idanunta.
A hankali yake saukowa daga kan upstair yana sanye da Jallabiya Ash colour da tayi masifar hawa da fatar jikinta, ta mishi kyau sosai, gashin kanshi ya sauko har gaban goshinshi, cikin sanyin hali yake tafiya, ga jikinshi da yake fitar da wani sihirtaccen kamshi mai sanyaya zuciya, ƙafarsa sanye da slippers mai kyau da taushi.


idanunshi a kanta ya fara saukowa daga saman, yana dan jijjiga kanshi, har ya sauko, numfarfashi yaji tana fitarwa masu kama da dafarar mutuwa, hakan yasa da dan sassarfa ya nufo gurinta, yana zuwa ya ɗagota da hannayensa, tare da saɓeta akan kafaɗarsa, bai ko tsaya ba yay sama, da ita.
Yana zuwa bedroom dinsa Bathroom ya shiga, kai tsaye ya shamfiɗeta cikin zazzafan ruwan da ya sarki masu zafi sosai.


numfashi ta dan jaa a wahalce, tana mai lumshe idanunta, ta jima sosai cikin ruwan kafin ta fara jin jikinta yana dan saki, hannayenta da suka lallakwashe suka sassaki, ba tare da damuwar komai ba, ya fitar da ita a ruwan ya cire mata kayan jikinta da suka jiƙe, ya sake haɗa wani ruwan ya wanke mata jikinta sosai ya ƙara gasata, kafin ya fito da ita, sauri-sauri ya shiryata cikin wasu fararen kayan sanyi masu kauri sosai ,har da safar ƙafa da hannu ya sanya mata, sai da ya gama, kafin ya nufi fridge dinshi, sachets din magunguna ya fitar da wata allura da ruwa mai dan rangwamen sanyi, tun da ya fito da Magungunan da Allurar Zuciyarta ke ɗatace, tayi kicin-kicin da fuskarta, yarda kasan an aiko mata da sakon mutuwa.


takowa ya shiga yi gurinta, kallo daya ta mishi ta dauke kanta daga kallonsa, wani gamsasshen murmushi yay ta gefe daya, wanda yay sanadiyar lomawar Beautiful point dinsa, ganin kamar zata juyo yasa yay saurin mayar da fuskarsa yarda take yama ƙara haɗeta , cikin natsuwa ya fara ɓallar magungunan har ya ɓaɓɓali wanda zata sha, sun kai guda goma Cikin glass cup ya tsiyaya ruwa mai rangwamen sanyi, ya miƙa mata , juyowa tayi ta kallesa kamar za tayi kuka, dauke kanta tayi, "riƙe!", ya furta yana ƙara miƙa mata, sulalewa tayi ta kwanta kan bed dinsa, kafin a hankali ta furta "Ci Abin ci"dan kallon inda take ya yi, kafin ya ajiye Komai kan stool .fita yay daga bedroom din, bai dade ba ya dawo hannunshi dauke da dan madaidaicin Plate.


jaan stool din yay ya kwashe komai , ya ajiye gefe ya zauna, ajiye plate din yay a ƙasa kafin yace "tashi!", a hankali ta miƙe tana kallonsa, nuna mata Abin cin yay yace "Ci . kizo ki sha" ya fada yana daukar laptop dinshi, wadda take charge a gefe, operating dinta yay, ya fara dan dudduba wasu abubuwa da suka shafi aikinshi.
A hankali ta shiga cin Abin cin kamar mai cin magani, tana ci tana gyangyaɗi , wanda ita ta ƙirƙirarwa kanta barcin duk dan kar ya mata Allurar ya kuma bata magani, dan sam bata so.


bai Ankare ba sai da ya gama abun da yake kusan 10pm yana juyowa yaga har ta gyara kwanciyarta a inda ta kwanta tana barcinta cikin kwanciyar hankali, girgiza kanshi ya yi, Allurar ɗazun ya mayar cikin fridge ya fito da wata daga cikin wani dan kwali, tayi sanyi sosai , haɗata ya yi, ya zuƙa a Syringing , dagota yay, tare da zame Wandon kayan jikinta , da *"BISSIMILLAH"* ya daura tsinin Allurar a jikinta, ya tsira mata, a firgice ta farka , tare da sanya kuka, sai da ya juye mata gaba daya ruwan Syringing kafin ya zarw mata Allurar a hankali, yana zamewa ya mayar da hannunshi kan gurin da ya mata Allurar ya shiga murza mata gurin a hankali, yana jin yarda kukan nata yake ratsa gaba daya kunnuwanshi.


cikin gajiyawa da kukan da take, ya saukota daga kan kafadarsa, yana kallonta, idanunta na lumshe , amma a haka take yin kukan , ga hawaye nata zuba, a hankali ya sanya tafin hannunshi mai laushi da tsantsi ya shiga goge mata hawayen idanun nata,a hankali ta shiga jaan ajiyar zuciya,har ta tsaya da kukan nata sai dai ajiyar zuciya.


zameta yay ya ajiyeta gefe daya, bathroom ya nufa, bai jima sosai ba ya fito yana goge gashin kanshi da yake linkif da ruwa, a hankali ya zame ƙaramin towel din da ya sanya a fuskarsa wanda yake goge ruwa,in da yake jin motsi yabi da idanu, zaune ta ganta tsakiyar bed dinshi, ta nannaɗe ƙafafunta, ta bowl a hannunta, tana shan kankana da madarar da ta haɗa, tana yi tana kallon laptop dinshi da ta sanya cartoon ,murmushi ne kan fuskarta.
ƙarar bude bathroom din da taji, ne yasa ta dago idanunta, ido biyu tayi da Yaah Shehi, da sauri ta sauke kanta ƙasa tana sanyayyan murmushi .


taɓe bakinshi ya dan yi,ƙafin ya wuce gaban mirror yana ci gaba da goge kansa, Abun busar da gashi ya jona , ya fara busar da gashin kansa, sai da ya gama tsaf kafin ya mulke gashin kan nasa da mayuka kala-kala masu ƙara taushi da ƙamshin gashi, lotion dinshi ya shafa, kafin ya bi da turarenshi na Huge Boss, wani ɗan ƙofa ya bude ya shiga, bai jima sosai ba ya dawo da wani kayan barci farare masu taushi da santsi sun mugun lafewa a jikinsa, zagayowa yay ta gurin da take zaune, laptop din gabanta ya dauke tare da kallonta da lumsassun idanunsa, A hankali yace "baki gaji ba ?", ƙifta ido ta dan yi, kafin ta gyara Zamanta kan bed din da take zaune, tana mai wasa da hannayenta tace "a'a!", watsa hannayensa yay alamar bai damu ba.


Kai tsaye ya wuce gurin Ibadarsa, tankwashe ƙafafu yay , tare da daukar Al-qur'ani mai girma ya fara raira ƙaratun Al-qur'ani mai girma , da muryarsa mai dadin sauraro.
Gyara kwanciya Sadiyyerh tayi tana mai sauraron karatun nashi wanda kai tsaye yake huda dukkan wata ƙafa ta jikinta yana shiga, ji take kamar a kanta ake karatun , hakan ne yasa ta lumshe idanunta tana mai sauraronsa.
har bata san lokacin da barci ya dauketa ba, sai guraren 2am kafin ya tashi daga gurin da yake zaune bayan ya yi.


Addu'o'i sosai, idanunshi ya kai in da ya kwantar da Sawwa da take barcinta hankali kwance sai fitar da sassayan numfashi mai cike da zalar ciwon da yake nuƙurƙusar gabbanta take,miƙewa yay, bai tsaya ba sai wuce in da take, hannayensa biyu yasa ya dauketa.
A hankali ya bude ƙofar da zata sadashi da palonshi, durum palon yake babu yawaitar haske kasantuwar gaba daya na'urorin cikin palon a kashe suke, ta tsakiyar kujerun da suke zube a palon ya bi, tare da ƙarasawa wani ƙofa da yake kallon ƙofar bedroom dinshi, buɗe ƙofar yay ya shiga, kamar dai palon shima ɗakin bashi da yawaitar haske sosai amma akwai blue light , wanda ya dan haska ɗakin.


ta cikin wannan ɗan hasken da Ya rage cikin ɗakin na shiga ƙarewa Ɗakin kallo, babban ɗakine sosai, mai dauke da royal bed, wardrobe daga bango har bango, side drower mirror , stool da dai sauran kayan karikitai, wasu manya manyan Elagement ne na pics din wata ƙyaƙyawar Yarinya ,mai kyan gaske kamar Aljana, tana cikin wani ɗan gadon Yara hannunta a bakinta, alamun tana tsotsa, tana sanye da light blue din kayan sanyi na Yara masu kyau, hatta da showel dinta ma light blue ne.
dayan Elagement din kuwa, tana cikin showel ne a lokacin ba zata wuce 2 months ba, gashi ne linkif a kanta, ta kanannaɗe fuskarta da hannayenta,wanda yasa ba'a iya ganin komai na fuskarta daga lips dinta sai siririn karan hancin kawai ake iya gani.


Sauran pics din kuma a mabanbantan gurare aka mata shi, wasu a park wasu a garden , wasu a mall -mall wasu super market duk dai pics din babu wanda Yarinyar tayi sama da 3 years , kuma daga yarda aka zazzagaye pics din da kalolin fure da abubuwa zaka gane kaunar Yarinyar ga mamallakin ɗakin, a hankali ya ƙarasa gefen bed din da yake lulluɓe da light blue din bedsheet ya kwantar da ita, Addu'o'i ya shiga mata sai da ya gama kafin ya jaa mata duvet ya rufeta , manysn labulayen ɗakin ya gyara mata,ya ƙara gyara mata windoors , ajiyar zuciya ya ji ta jaaa.
idanunshi da suke a narke ya daga tare da ɗan kallonta na seconds kafin ya fice yana , fesar da sanyayan numfashi.kulle mata bedroom din yay tare da wucewa nasa.


yana tura ƙofar bedroom din ya hangi Sadiyya zaune ta tankwashe ƙafafunta hannayenta akan cikinta tana dan yatsina fuskarta.
jin ƙarar bude kofa yasa ta dan dago tare da zuba mishi idanunta, haɗa idanu suka yi, cikin gaggawa ta zare idanunta daga cikin nasa.
cikin bedroom din ya shiga takawa, yana sob iso bed din, zama yay gefen bed din yana mai nazartar yana yin da take ciki don kallo daya yay mata ya gane akwai abun da yake damunta.


Kan bed din ya hau dakyau tare da nannaɗe ƙafafunsa yana mai binta da kallo.
jaawota yay kusa da shi tare da kama kafaɗunta yasata yarda zata fuskancesa, haɓɓarta ya dago don ta kallesa, amma sai ta sun kuyar da kanta, domin matsawar ta kalleshi to fa sai idanunta sun fallasa masa Abun da ke damun zuciyarta har ma da gangar jikinta.


numfashi ya fesar, tare da kishingiɗa daga zaunan da yake, ya lumshe idanunshi, ba tare da ya kulata ba, ganin ya basar ne yasa itama.........



Isanatu tace a muku Addu'a😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂😂
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 30*



Ta kwantar da kanta akan kirjinshi, cikin hikima ta zura hannunta cikin rigar jikinshi tare da murza kwantaccan gashin kirjinshi da yake fitar da wani sihirtaccan kamshi mai mugun sanyi da kwantar da hankali, kafaɗunta ya dago tare da tsurawa fuskarta da tayi wani jaa lokaci daya ido, cikin hikima da baiwar da Allah ya masa yake nazartar ta, cikin sa'a ya samu nasar sanya ƙwayar idanunshi cikin natajuya narkakkun idanunshi yay cikin nata, kai tsaye ta gane Abun da yake nufi na tambayarta" ya ya dai!", kwaɓe fuskarta tayi tare da manna fuskarta da faffaɗan kirjinshi wanda ya bayyana sakamakon bottom din rigar da ya dan zare, gaba daya hannayensa ya nutsa cikin tufkakkiyar sumar kanta da take fitar da wani sihirtaccen kamshi, sai sheƙi take, a hankali ya shiga zaro hannunshi wanda hakan yay sanadiyar warwarewar tufkar gashin da tayi, zare hannunshi yay dai-dai da warwarewar gashin nata ya bazu har kam fuskartagaba daya gashin ya bazu ya rufe mata fuskarta.


yatsunshi yasa ya shiga tattare gashin da ya rufe mata fuskarta, tsam ya rugunmeta a jikinshi, yana shaƙar kamshin jikinta mai dadi da kwantar da hankali.
ɗagowa tayi gaba dayanta ta afka jikinsa, kumatunshi ya tallafe tare da karkatar mishi da kanshi kamar yarda tayi, ba zato yaji ta manna lips dinta kan nashi tare da ziro harshenta tana lasar lips dinshi, a hankali ya lumshe idanunshi, tare da sake mata ragamar rayuwarsa gaba daya, ita kuwa cikin tsantsar buƙatuwa ta ci gaba da bidasa.


kusan 10 minutes tana sarrafa mishi jikinshi,kallonta kawai yake , ganin duk jikinta yay sanyi ne yasa ya saki wani ja'irin murmushi, baya yay da ita tare da binta ya fara sarrafata , cikin salon burgewa da kwantar mata da hankali, har sai da ya tabbatar mata da samun natsuwa kafin , yay wata iriyar Ajiyar zuciya mai tattare da jaan numfashi mai ƙarfi.


numfashi ta shiga saukewa,tare da jaaan bargo ta rufe jikinta da shi, shi kuwa mikewa yay ya shiga bathroom domin tsarkake jikinsa, bayan ya fito ya umarce da itama ta je ta tsarkake jikin nata, kafin ma ya gama shiryawa wasu daga cikin masallatan cikin gari an fara kiraye-kirayen Sallah Asuba, hakan yasa cikin sauri-sauri ya gama shirinshi cikin wata farar jallabiya ya daura Alƙyabbar da ta zamana kamar Ibada sanyata, turare ya faffesawa jikinshi, tare da zura slipper dinshi yay waje da sauri, don lokaci ya yi mugun tafiya


sosai.Sannu! Sannu.....!

haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin dadi da ba dadi ba, lokaci ya tafi sosai rayuwa tana gudu sosai, in da abubuwa suka shuɗe da dama.


Cikin Ikon Allah kuma Sadiyya ta ƙara samun wani cikin, wanda yake mugun wahal da ita, bata ko iya magana bata cin Abin ci, bata iya aikatawa kanta komai, sai kwanciya.
kamar kullum Yau ma kwance take, tayi ruf da ciki, tunanuka ne birjik a ranta, wanda har bata ji shigowar Yaaah Shehi ba da yake bakin ƙofa ya naɗe hannayensa yana kallon yarda wasu hawaye suke zubo mata.
a hankali ya taka ya shiga cikin bedroom din , har ya zauna a gefen bed dinta bata sani ba.


hannayensa yasa ya jawota gareshi, tare da daura kanta akan cinyoyinsa, sai a lokacin ta ji shigowarsa, nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke, tare da kara ƙanƙame hannunshi da ya raɓa a gefen wuyanta, cikin sarƙaƙƙa murya yace "Kuka! kuka!! kukan dai har yanzu!..?", ya fada yana mai zuba mata idanu, kafin tai magana Sawwa ta shigo cikin ɗakin, cikin shigar riga da wando masu kyau da suka dan kamata, an mata kalaba ƙanana ta zubota kan ta babu ko dan kwali, tayi wani kalar girma sosai in ka kalleta zaka yi zaton ta kai 10 years ma, gefenshi ta zauna tare da daura kanta akan kafaɗarsa ya zamana Sadiyya ta daura kanta a cinyarsa ita kuma ta daura a ƙafaɗarsa, a hankali tace "Abie wai Ammyna mutuwa za tayi ?", jim ya dan yi kafin yace "waya faɗa miki ?", jiki a mugun mace tace "kullum tana faɗa min wai rayuwarta ba mai tsayi bace ta kusa ta tafi ta bar mu", ta faɗa kwalla na cika mata idanunta, riƙe hannuta Sadiyya tayi, kafin tai magana Shehi yace "aa wasa take miki" ya faɗa yana dan mayar da idanunshi kan Sadiyya, kallonshi ta dan yi kafin tace "Uhmmm a jikina fa nake jin hakan, ina jin rayuwata ta kusa zuwa ƙarshe , mutuwa zan yi !", ta faɗa tana dan murmushi tare da shafa cikinta da ya fito sosai , a ido ma kawai ka kallesa kasan zai iya yin 8 months dan yay girma sosai har ya fara sauko mata.
"tana kan kowa", ya faɗa cikin dan rashin damuwa, murmushin da ya bayyana kyawawan haƙoranta wanda kamar an ƙara musu fari tayi tare da cewa "ba zaka gane hakan ba sai bana nan, fata na dai ka riƙemin Amanata , ka bata kulawar da ni ban samu ba a gurinka, ka tarairayeta, Amanarmu ce", gashin girar shi ya dan shafa kafin yace "ki tafi da ita kawai man", ya faɗa cikin dan gatsali, murmushin takaici tayi dan gaba daya sam ta lura bai fahimci mai take ji bane, kuka Sawwa ta sanya tana cewa "bana so ki tafi! Abieh ka faɗa mata man" , ta faɗa tana girgiza mishi hannunshi.


A hamkali ya bude kyawawan idanunshi, tare da dan kwaɓe fuskarsa yace "bata jin maganar Abieh ai", ya fada yana shafa kan Yarinyar, ana cikin haka Umma Jakadiya ta shigo cikin ɗakin, da sauri ta ƙarasa gurinsu, tana kallonsu tace "halan kai ma ta faɗa maka soki burutsuta, " jinjina kanshi yay alamar "Eh", numfashi ta jaa kafin tace "tun da ta samu cikin nan dai bata da magana sai ta mutuwa kullum sai tace wai ta ji take kamar Ajalinta take dauke dashi, ni ban san mai take ji da gani ba da har take wannan maganar", ta faɗa idanunta a ƙanƙance, girgiza kanta tayi tare da cewa "Uhmmm Umma ba zaku gane mai nake ji ba, wlh ni kaɗai nasan mai nake ji da gani, wannan cikin bazan haifesa lafiya b....", da sauri ya bige bakinta, cikin ƙanƙance ido yace "Falyakul khairan !", kwaɓe fuskarta tayi ta mata wani abun tausayi, "Shehi jinginar da ni", ta fada cikin halin gajiyawa da kwanciyar ga Aban cikinta da yake gaba.


da Sauri Umma Jakadiya ta sanya mata pillow a jikin gado, cikin dubara ya zaunar da ita a gurin, Sayyid ne ya dan leqo kanshi yana kiran Shehi, da sauri ta yafito sa tana cewa "kuzo kuma na bar muku taku wasiyyar", ta faɗa tana dan cizon lips dinta.


dariya yay daga chan bakin ƙofa yana cewa "Adda Sadeey kullum maganar kenan, kullum wasiyya ni dai yau ba zanji wasiyyar nan taki ba bari dai na kira miki su Zayn", ya faɗa yana dariya tare da ficewa a Bedroom din , idanunta ne suka cika da kwalla, ganin kowa yana watsi da maganar da ta faɗa masa, "shi kenan ai tunda duk baku dauki maganata da muhimmanci ba kallon mahaukaciya kuke min, duk ran da na mutu zaku yi takaicin kin tsayawa ku saurare ni", dan tsareta da idonshi yay, kafin ya miƙe yana baza Alƙyabbar jikinshi, yace "Umma a kulla da ita", ya fada yana ficewa yana riƙe da hannun Sawwa, zama Umma tayi gefenta tana nazartar kalaman da take faɗa kullum a bakinta.


kama hannun Umma tayi tare da cewa "na san ke Mahaifiya ce, zaki iya fahimtar abun da yake damun Ƴarki Amma Umma sam kin gaza fahimta ta", murmushi ta dan yi, tare da cewa "kin ga Sadiyya bana son wannan sakalcin naki, in dai ciki ne da Izinin Allah lafiya zaki haifesa, in sha Allahu zaki riƙa abun da kika haifa", ta faɗa tana shafa kanta, dai dai lokacin da cikin ya mata wani irin juyi, wanda hakan ya tilasta mata dafe cikin da hannu bi-biyi tana lumshe ido tare da cizan lips dinta.


"Innalillahi wa'inna'ilaihi raju'un! Hasbunallahu wa ni'imal wakeen!!", ta fada a hankali wata zufa na tsatsafo mata, da sauri Umma tace "Sannu! Sannu!! juyi ne", ta faɗa tana goge mata gumin da ya wanke mata fuskarta , a hankali taji gaba daya abun ya bari lokaci daya, numfashi ta sauke tare da cewa ,"Alhamdulillahi Yaaah Allah!", ta furta tana dan ƙara jingina da in da take don ta ƙara jin dadin kwanciyar tata.


Tasbihi da ya zame mata Abokin rayuwa tun bayan Samun Cikin ta ci gaba da yi idanunta lumshe, har barci mai nauyi ya dauketa, numfashi Umma ta sauke, cikin natsuwa ta miƙe tare da fara kakkaye mata bedroom din nata, wanda ya ke fes sai dai yan wasu kaya da ta dan ajiye gefen bed.


Ta jima sosai tana barci, kafin ta farka bakinta dauke da Addu'ar tashi daga barci, cikin natsuwa ta dan muskuta, tana kallob Sawwa da take barci a gefenta cike da natsuwa, a hankali ta tashi tana dafe da cikinta ta shiga bathroom wanka tayi , tare da daura towel babba , ta fito tana tsane kanta, da sauri Sawwa ta dago ta kalleta tare da cewa "Ammyna kin warke ?", jinjina mata kai tayi, tattausan murmushin da ba ɗabi'arta bane ta saki tare da cewaa "Alhamdulillahi Rabbie naji dadi sosai", ita ma murmushin tayi, tana ƙarasawa gaban dressing mirror, shiri tayi cikin wata doguwar rigar Abaya mai kyau , ta yane kanta da gyalen Abayar, kama hannun Sawwa tayi suka shiga bathroom din wanke mata fuskarta tayi ta manta wanka, cikin shiga irin nata ta shiryata, kama hannunta tayi suka fito palo.


A zaune suka samu kusan gaba Dayan Yan gidan, hakan yasa suma suka zauna a cikinsu suka fara fira, Umma Jakadiya ce , ta shiga kitchen bata jima ba sosai ta fito hannunta riƙe da wani dan tray , tana zuwa ta miƙawa Sadiyya , karɓar trayn tayi tare da cewa "ngd Umma", ta faɗa tana daura tray din aka cinyarta, tuwon danyar shinkafa ne da ya tuƙu yay kyau sosai, da miyar kase da tayi wani irin kyau, wanda da alama har a baki zatayi dadi sosai, murmushi ta dan yi tare da furta "Favorite!", ta fada tana gyara zamanta, A hankali ta shiga cin tuwon

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment