Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fada tana yin rau da ido.


jawota ya yi jikinshi, dingure mata kanta ya yi, yana cewa "ban san ranar da kika koyi rigima har haka ba", cuno baki tayi , tana langaɓar da kanta gefe.


"ranar da zan ƙara aure ban san yarda zamu kaya ba", wani kallo ta mishi kafin tace " sai dai in na mutu, amma madamar in da rai da lafiya, Wallahi Yaaah Shehi baka isa ka Ƙara aure ba", ware ido ya yi, cikin muryarshi mai zaƙi yace, "da raina da lafiyata, Allah ya horemun abun da zan rike mata fiye da daya, in ma dari ake zan iya yi na riƙesu da Abun da Allah ya wadatani amma kice ban isa ba ?, ki dai roƙi Allah kar na hango wata", ya fada yana linketa cikin Alƙyabbar jikinshi.


budewa tayi ta fito, " ka kaddarawa rayuwarka duk ranar da zaka ƙara aure ranar zan bar gidanka", taɓe baki yy kafin yace "ki koyi kishi Irin na su Naanah Aysha mana , masu kishi gurin farantawa Mijinsu, ba kishin mata zamani ba, kishin da ake rige-rigen farantawa miji, wanda ake kishin aga daya ta fi kyautata miji, A tsarina bana da tsarin zama da mace daya, bana kuma da tsarin saki a ciki. so you should take care !" ya fada yana lulluɓa mata Alƙyabbar da ya dauko mata, wadda ta kasance irin tashi komai-da-komai banbancin kawai nashi na namiji nata na mace.


Zare Alƙyabbar tayi ta fice fuskarta a kumbure, wani munafikin murmushi ya yi, kafin ya biyo bayanta hannunshi riƙe da Alƙyabbar da ta bari a hannunshi sai da suka zo tsakiyar palo, kafin ya tarar da ita, miƙewa tayi zata kara wucewa, da sauri ya riƙo hannunta, ta faɗo jikinshi.


ido cikin ido suke kallon juna , a hankali ya zura mara hular Alƙyabba, zaren Alƙyabbar ya fara ƙoƙarin daura mata, hannu tasa ta tare, hakan yasa ya riƙo kugunta yana kallonta, itama kallonshi take, sharrrr hawaye ya zubo mata, wani kill smile ya sakar mata, basu anƙare ba sai ƙarar tashin pics suja fara ji.


tsorota Sadiyyerh tayi, da sauri ta kalli inda karar ke tashi, gaba daya Ahlin gidan ne, har ma da wasu daban, suna dauke da manyan cameras , suna daukarsu pics masu kyau.


da sauri ta fara ƙoƙarin zame jikinta daga na Yaaah Shehi, riƙe ƙugunta ya kara yi, yana kallon kirjinta da ya bayyana ta saman rigar jikinta, tsaye yake ƙiƙam shi ba motsa ba, shi bai saketa ba.


suna tsaye a gurib wasu flower red and blue suka fara zubowa a kansu, gaba daya yan cikin palon suka haɗa baki gurin cewa "Happy 5years Anniversary Yaah Shehi and Sadiyyerh Arman-Maleeq Abdul-azeez Shehi Arman-Maleeq ", da sauri Sadiyyerh ta kalli Yaah Shehi.


gira daya ya ɗage mata,hannunta ta dafa kan kirjinshi, tana mishi kallon ƙasan ido, a tare suka saki wani sanyayyan murmushi mai mugun narkar da zuciyar masoya, a hankali ta furta "love you more My Husby!", lumshe idonshi yy ya kara budesu tarr akan fuskarta.



gaba daya Ahlin suka matsa garesu, shi kuwa bai matsa daga in da yake ba sai da ya daura mata igiyar Alƙyabbarta, Photographer ne ya cs su zauna zai musu photo, zama Sadiyyerh tayi, shi kuwa gogan sai ya tabe baki tare da nufar hanyar waje, da sauri Zayn - Maleeq ya riƙe hannunshi, yana mishi baitin Waƙar Abdul D One na *ALAQA* gaba daya Sayid da Abdul suka dauka.


"Mu Qullah Alaqar gaskiya ita ke ware yan hayaniya.!
sannan Alaqar gaskiya, ita kesa Maraya Zuciya.
kyakyawan zato shi kaɗai ke kan ja duniya!, duniya!! duniyaaaaah.....!!!🎤🎤

Mu Qullah Alaqa!🎤

Mu Qullah Alaqar gaskiya!!🎤

Mu Qullah Alaqar gaskiya!!!🎤

Mu Qullah Alaqaaaaa!🎤


Alaqa! Alaqa!!🎤


ita Qullah Alaqar gaskiya kafin tare akwai wuya , komai wahala muna tare tamkar daurin tsintsiya ...!!🎤🎤"dafe kanshi yy dai dai lokacin da suka zaunar da shi kusa da Sadiyyer da take zaune.


ido suka haɗa dashi, da sauri Anty Rayhana ta kwantar mata da kanta akan kafadar Yaah Shehi dai dai kunnenshi, a bisa Umarnin Photographer , a hankalin ta fara furta

"Uhmmm ka ganni na sha kitso!. nayo kwalliya domin in burgeka !!!.🎤


ga kyan jiki har diri kamar yarda ka fadamin ra'ayinka ...!!!🎤🎤 .


ba wanda zan bai wa lokacina ko bayan idanunka !!!...🎤🎤🎤


kamin karatun da duk sakanni dole in tunaka..!!!🎤🎤." ɗaga gira daya yy kafin yace , "ce min za kuyi gaba daya gidan Yaah Shehi ya koma na Mawaƙa, tom nima ba za'a bar ni a baya ba", ware ido Sadiyyerh tayi, hore mata idon yy kafin tayi magana ya fara cewa .


"


DON ALLAH KUYI HKR DA WANNAN, JIYA WAYATA BA CHARGE , YANZU KUMA INA CIKIN CHAT AKA FAƊA MIN RASUWAR YAYANAH PLS KU MIN AFWA😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P. 25*



To bari na sanyaku a farko, wanda kuka min gaisuwar Rashin da muka yi, dama wanda basu min ba , Na gode sosai ,Allah ya saka da Alkhairi, Yaah Ubangiji ya bar kauna 🫶🏽🥰.



"Duniya da dadi..!🎤🎤.

mafi dadi na dadin...!!!🎤🎤.

ka samu mace mai kyan hali da bata ɓarna...!!!!🎤🎤.


komai yana gushewa, amma ka gane cewa ita gaskiya guda dai ce bata chanja suna...!!!🎤🎤.

Allah ina da mata.! Allah Akwai Ɗiyata.! Allah ka basu kariya Allah na dare da rana...!!!🎤🎤🎤.


Ubangijin Muhammadu ranar rabon takardu, kasa na ƙarɓi tawa da dama na samu Jannah...!!!🎤🎤🎤", ya fada yana sakar mata light kiss a lips, a hankali ta cuno baki, cikin ƙasa da murya kamar yarda yy mata baitikan waƙarsa tace, "Laaa'ilah Yaah Shehi da waƙa!", ta fada tana rike baki.

dan yatsina fuska yy kafin yace "Shehu Sahabi ne ? ko Annabi ne ?, baiti daya biyu ukku, wanda zai sanya Iyalinka farin ciki ba'a hana ba, dan ko Malam sai dai yace babu kyau, ba dai yace babu dadi ba, ko baki ji dadin ba?", ya fada yana dungure mata kai.


murmushi tayi, kafin tace "Yaah Shehi Wlh muryarka tayi dadi sosai da Waƙa dama ka ringa raira min kullum", ta fada tana daura hannunta kan yatsun hannunshi, taɓe baki yy kafin yace "uhmmm nawa zaki biya to , kin san gwamnati ta hana Aikin banza ", ya fada yana kallon Agogoj Rolex din da take hannunshi.

"kasan ?", ta fada tana kallon ƙafarshi, "me ne ?", ya fada idanunshi akan wayarshi da yake duba muhimmun abu, "takalmin nan sam bai hau ba ", ta fada tana kallonshi, "chanjan wasu to", ya fada bai ko kalleta ba.


miƙewa tayi tayi sama, bata jima ba ta dawo hannunta daNavy Cipriano Woven Italia n Leather Shoe , har ƙasa ta ɗuka ta ajiye takalmin, cikin natsuwa ta shiga warware Ƙafarshi daga cikin Takalmin da ya sanya, cikin natsuwa ra zura mishi takalman a ƙafafunshi, ko da ta gama zaune tayi akan ƙafarta, zufa ce ta fara yanko mata, mararta na mata wani irim ciwo da lokaci daya abun ya zo mata, ƙasa dagowa tayi daga in da take.


A hankali ya fara fahimtar halin da take ciki, cikin natsuwarshi da cikar Haibarshi, ya ɗago haɓɓarta da yatsunshi, a hankali ya zuba mata idanunshi masu matuƙar hankali, cikin natsuwa ya jujjuya mata idanunshi, alamar "lafiya?", kasa amsa mishi tayi sai hannunshi da ta riƙe tana dan nishu a hankali kamar mai shirin haihuwa.


Miƙewa tsaye yy, kafin ya ɗago ƙafadarta gaba daya ya tarairayota jikinshi, ya karata yana kallonta, bai ko kalli mutanan da suke palon baya nufi hanyar fita waje da ita, da sauri Zayn ya tare gabanshi yana cewa "Hamma Yaah Shehi bafa a gama ba", wani kallo wanda yasa da sauri Zayn fa matsa daga gabanshi yana sunkuyar da kanshi yy mashi.


direct suka fice waje, Hannunshi na kan Ƙugunta, kanta na kan kafadarsa ta wani langwabar da shi, idanunta a lumshe ga zufa na yanko mata ta ko ina, hannu ya nunawa tunin Escort da drivers dinsa yy, da sauri suka shishiga mota suka ƙaraso gurinshi, sai da ya fara sanyata cikin motar kafin shima ya shiga, jin ginar da ita ya yi a jikinshi, ya daura kanshi akan a bayanta da ta kifa akan cinyarshi.


zufa ce shima ta shiga karyo mishi, duk kuwa da sanyin AC da take cikin motar amma Zufa yake, a hankali ya shiga ciza lips dinshi, haƙoranshi na rawa sosai, "Shehi ina zamu je ?", chan ciki ya faɗa mishi sunan Hospital din , suna hawa babban titin da zai sadasu da Hospital din ta wani irin riƙeshi da karfi, tana jin saukar wani abu mai ɗumin gaske, tare da raɗaɗin azaba ya zubo mata daga cikin jikinta.

riƙe Yaah Shehi tayi sosai, tana jin wani raɗaɗi na Azaba wanda tun da take rayuwarta zata iya cewa bata taɓa jin Azaba irin haka ba, gaba daya cikinta ya ruɗe ya haɗu da mararta yake wani irin ciwo, wanda ya haddasa mata ringa fusgar numfashinta da take niyyar ficewa daga jikinta da karfi.


Kirjinshi ne yy wani mugun duka, wanda yasa a hankali ya fara bude idanunshi, yana kallon gefe, abun da ya gani yy mugun girgizashi, cikin ranshi ya furta "Yaah Mujibudda'awati! Yaah Zilzallalu wal Ikram! Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allahumma Ajirni fee museebati!", ya fada kansh na sara mishi, kafin su kai Asibitin idanunshi sun yi jaajir , jijiyoyin kanshi sun fito raɗo-raɗo.


ko da suka ƙaraso dakyar , ya bude motar ya fito, ɗaga wayarshi yg, ba tare da yy magana ba, bayan minti 2, sai ga nurses sun fito da gudu da keken tura marasa lafiya, shi da kanshi ya dauketa ya daurata akan gadon yana ganin yarda jini yake malala daga ƙasanta, wanda abun ya wuce ace na period.


bin bayansu yy suka nufi cikin Asibitin, suna shiga ya bi wata hanya ya yin da su kuma suka wuce da ita gurin yin Scan , bayan tabbatar da abun da yake zargi ne aka wuce da ita Labour room , suna shiga aka fara tattara kayan da zasu buƙata.


kafin su gama haɗa kayan, aka bude wata ƙofa daga gefe aka fito, sanye yake da Kayan likitoci ya sanya face mask a fuskarshi, ya luluɓe kanshi da hular likitoci wanda har tulin sumarshi gaba daya ya zubata ciki, sai hular tayi kamar acuci maza.


hannunshi na sanye da safar hannu, yana shigowa, suka shiga gaisheshi, " Profectional Doctor kuma Invigilator da kansa", cewar wasu nurses , "what do you means ?", wata daga ciki ta tambaya "i means Yaah Shehi Arman-Maleeeq Abdul-azeez Sarki our Invigilator and Profectional Doctor in a Hole Countries", wawware idanunsu suka yi, suna masu ƙara kallonshi gaba daya, "kai Amma fa Guy din ban ya haɗu", cewar wata daga cikinsu, "kwalelan kare kuwa da Hantar kura, kina Shaddar Kasuwa mai zai da ke ?", iya Shaqa Kafiffah tayi.


bata kara cewa komai ba , amma a ranta ta Roqa , abun da bb wanda zata bari ya sanshi daga ita sai Rabbassamawati wa rabbul Arshil Azeem, kuma ta ƙudurta zata basu mamaki.


ganin suna ɓata mishi lokaci da surutun banza, wanda suke yi ƙasa ƙasa, amma shi kamar cikin kanshi suke yi, yasa ya nuna musu hanyar waje ba tare da yy magana ba, jikinsu sukuku suka fice waje.


Allurae Barci ta fara bankawa Sadiyyerh sai da barcin ya daukarta, kafin ya fara aikinshi cike da natsuwa, yana yi har wata kwalla-kwalla take taruwa cikin idanunshi, jijiyoyin kanshi suka ƙara wani irin tashi, kallo daya zaka mishi kasam yana cikin damuwa, sai dai duk da haka bakinshi bai gushe da Ambaton Allah ba, Ambatonshi yake sosai, wanda kuma hakan yasa gaba daya natsuwarshi ta fara dawowa jikinshi ya ƙara samu kuzarin yin aikinshi.


After 1 hour.

Cike da Ƙasaita ya fito yana sharce zufar da har zuba take daga jikinshi, hankalinshi a dan tashe, dan ya bala'in tsorata da abun, yana fitowa ya samu su Ayyana a tsaye hankulansu duk a tashe, da sauri Anty Rayhana tace "Maleeq ya jikin nata ?", ta fada tana kallonshi, "she's good!", ya fada yana komawa da baya.


wani Office ya wuce yana fesar da numfashi cike da damuwa, a hankali ya kwantar da kanshi kan kujerar Office din, yana tunanin wai yau da kanshi , shine ya ƙarasa yin flushing din gudan jininshu, wanda yake sa ran ganin a rayuwarsa, wanda yake burin gani a rayuwarsa, a hankali ya furta "Alhamdulillah Yaah Allah, Astagafiroullah! Subhanallah!, Hasbunallahu wa ni'imal wakeem Innalillahi wa inna ilaihi raju'un!, Allahumma La sahala, illa ma ja'altahu sahala, wa anta taja'alul hazna ila shi'ittassalaha", ya furta a jere .


Cije Lips dinshi yy, a hankali Ayyana ta turo ƙofar Office din ta shigo, zama tayi a gabanshi, kafin tace "Maleeq!" a hankali ya ware idanunshi da suka mishi jaa suka ƙanƙance, tsabar ciwon da kanshi yake mishi, ga kuma rashin jin dadi.


"me ne yake faruwa wai ?" ta fada taba kallonshi, sai da ya cije lips dinshi na ƙasa kafin yace "Miscarriage!", ya furta kamar zai fashe da kuka, "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un , hasbunallahu wa ni'imal wakeen, Ubangiji ya bata lpy, ya kuma bayar da wasu masu Albarka , Ashe ba banza ba nake ganinta sukuku kwana biyu , Allah dai ya bata lpy" ta fada tana jinjina hikima irin ta Allah, duk yaushe daren yy ma bare gari ya waye, Allah yasa dai Yaah Shehi shi mai saurin Haihuwa ne, amma Zuri'arsu basu cika haihuwa da wuri ba, mahaifiyarsu sai da tayi shekara 10 da aure kafin ta samu ƙaruwarsu, dan ita ma sai da ta shekara 20 cif da Aure Kafin Allah ya bata su Amah Yan Biyu kyautar Allah , bayan su kuma Mijinta ma Ya rasu tub suna Tsumna kuma bata ƙara Aure ba.



tsantsar damuwar da ta gani akan fuskarshu, tare da Son hutu yasa ta fice, gurin Ɗakin suka tsai tsaya, suna hangota chan kan bed, tayi lame-lame fuskar nan tayi wani irin sharrr kamar irin wadda bata da jinin nan , ta rame lokaci daya, duk wanda ya kalleta dole ta bashi tausayi.


"Mai yake damunta ne ?", Anty Rayhana ta tambaya, "Miscarriage tayi", gaba daya suka maimaita "Miscarriage!", ban da Umma Jakadiya, da tun tuni ta gano Yaron ciki danye jaagab da yake jikin Sadiyyerh, "Allah Ubangiji ya mayar da Alkhairi , ita kuma Allah ya bata lpy"suka faɗa cikin tausayawa, duk Amsawa tayi tana zama gefen Umma Jakadiya.


Miƙewa tayi tana cewa "to ni bari na shige" ta faɗa tana miƙewa, da sauri Ayyana tace " ba zaki bari ta farka ba ?", girgiza kanta tayi tana mai cewa "a'a bari dai ba je, in yaso sai na haɗa muku Abin ci a kawo muku", jinjina kai Ayyana tayi dan tasan Umma Jakadiya ba zata tsaya ba, Zayn ne yace "Umma Mu je na kai ki gida", ya fada yana miƙewa, Yaah Muhammad ne yace "bari na shige gurin Abie , Sayyid da su Amah suka ce "mun tafi gurin Babyn Abba!" (Yaah Shehi), jinjina kai Ayyana ta musu , suka tafi.


ita kuma da Anty Rayhana sai suka shige ciki, zama suka yi a gefe da gefwn Bed din da Sadiyyerh take , suna kallon Drip da blood din da aka sanya mata gefe da gefen hannuwanta.


2 hours Left.


Da wani Annamimin ciwon ciki mai gigitar da tunani, mai sanya mutum cikin matsanancin hali ta tashi, suma ta ringa yi, kafin Ayyana ta kira Yaah Shehi tayi suma kusan 5 , sa boda tsananin Azabar ciwon ciki.


cike da mugun tausayawa ya shigo cikin Room din, kai kace kuka zai mata tsabar tausayi , a rayuwarshi ko ba Yar Uwarshi ba ko va Matarshi ba, baya son mace ta ringa shan wahala.


"Ayyana sai dai a mata Wankin ciki fa", ya fada cikin damuwa, idanunta da suka cika da hawaye ta zuba mishi tana cewa "a mata in dai zata samu sauƙin ciwon nan " ta daɗa kwallar idanunta na zubowa, cikin ƙanƙanin lokaci aka fara mata wankin ciki.


"Yaah Ilahi!" Abun da Yaah Shehi ya furta a lokacin da ya gama wanko mata wasu Abubuwa kwara ukku ras masu , manya-manyam gudan jini, wanda suka yi kama da an fara Halittar abu amma bai fara ko girma ba, haka yy mata komai guiwa a sake ya gama.


shi ya zauna da ita har wayewar gari,da safe ta farka bb ciwon cikin sam sai dai ciwuwukan da ba'a rasa ba, bayan gama bata wasu treatment din suka koma gida, har lokacin Sadiyyerh bata san mai yake damunta ba, dan ta dauka It's just a period pain da ta saba yi duk ending month shune ya zo mata a haka yanzu.



*bayan kwana biyu*



tana kwance kan damtsen hannun Yaah Shehi, tana wasa da gemunshi, shi kuma yana duba littafin Al-akdhari , a hankali tace "Zauj!", chan ciki ya Amsa mata, "wai mai ya same ni ne tun da muka dawo daga Hospital ake ta min sannu, kuma ba muje Nigeria din ba fa ", ta fada tana gyara kwanciyarta a jikinshi.........



sorry pls🫶🏽🌚😒
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.26*


Tana gyara kwanciyarta a jikinshi "Kece baki da lafiya", ya bata Amsa kai tsaye, tura baki tayi kafin tace "to me ya same ni ?", a hankali ya ƙara cewa "Ɓari!", cikin rashin fahimta tace "mai na ɓare ?", cikin ƙosawa da tambayarta yace "gudan jinin Yaah Shehi!", jim tayi kafin tace "ni ban gane ba", ba tare da ya kalleta ba ya ce " ni na gaji da tambayar" , ya fada yana shagwaɓe murya.


dariya ta danyi kafin tace "to mai yasa na daina jin zafi da ƙullewar da marata take 2 days ?", kai tsaye yace "sa boda bb komai a ciki", shafa marar tayi kafij tace "babu komai fa ?", jinjina mata kai ya yi, "ina koman yake to ?", dafe kaii yy kafin yace "Haleesa Aliyu Haydar Aliyu part 2", taɓe baki tayi kafin tace "Abun da ma ni bata taɓa zuwa min ba, nima ba zan kara zuwa ba,sai dai ba ringa turawa ana dauko min Haala", taɓe baki yy kafin yace "Amma kin san bata cika zama Ƙasar ba", taɓe bakin tayi kafin ta watsa hannayenta alamar ko a jikinta, "Shehi Ɓarin mai nayi wai ?", ta kara tambayarsa Unexpected .


jim ya san yi kafin yace "Yaran Yaah Shehi", da sauri ta kalleshi sai kuna ta taɓa cikinta, kafin tace "to a ina suka zauna kenan", cike da zallar mamakin ƙuruciyarta ya daura hannunshi kan mararta ya dan shafa kaɗan.
"to ai ni ban ji lokacin da suka zaunan ba" Ajiye Littafin yy gefe, kafin yace "dama ke taya zaki ji ?", kaɗa bakin ta kara yi kafih tace "Amma kai ka ji", jinjina kanshi yy, kafin yace "Sosai ma", "to ni mai yasa ba zanji ba", ta fada tana kifa hannunta kan cikinta.


da teeth dinshi ya kama lips dinta na ƙasa ya dan ciza kafin yace "ƙuruciya da Wauta!" tura baki tayi kafin tace "kuma fa nayi period, bayan kuma an ce in mutum na da ciki baya yi", ta fada cikin alamun daure kai.



"Waya faɗa miki ?", ya fada yana tsareta da ido, a hankali tace "ji jayi ", "a ina ?", kallonshi tayi kafin tace "Tunanin ne ya zo min" , jinjina kanshi yy, yana gyarw kwanciyarshi.


cikin natsuwa ya gyara kanta da yake kan hannunshi, sai da ya ƙara kallon cute face nata kafin yace, "to ai kowa da irin hallittarsa, sannan kowa da irin baiwarsa, mata kala-kala ne, akwai macen da bata Al-ada ma sai tana da ciki, akwai wadda bayan ta samu take, akwai wadda kwata-kwata ma bata yi, akwai wadda da zaran ta samu ciki ta daina yi kwata-kwata, wanda mafi rinjayen mata haka suke, da zaran sun samu juna biyu basa kara yin Al-ada sai kuma sun haihu, hakan ba wai damuwa bace baiwa ce ta Allah so hakan kar ya ɗaɗaki da ƙasa lafiyarki lau" , numfashi ta sauke a hankali.


kafin ta bude ido ya daura lips dinshi kan nata, a tare suka saki sanyayan numfashi, a hankali ta shigar da leɓanshi na kasa cikin bakinta ta fara tsotsarshi, tana lumshe ido a hankali, ga wani sanyayyan numfashi da take saukewa.


idanunshu na kan fuskarta yana kallon, tsari da zubin Halittar da Allah ya mata, a hankali take zare zara-zaran lashes dinta, lokacin da ta ji ya kama gaba daya haɓɓarta ya kara karkarar mata da kanta, ƙara haɗe bakinsu yy cike da wani irin salo,cikin natsuwa da sanyinshi ta fara kisses din Bakinta, yana lumshe

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment