Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jinjina kanshi yace "Sannu Barkiɗo ya aiki ?", cikin dan gajarcewa yace "Alhmdllh!", ya fada yana haurawa Sama, bin bayanshi Anty Rayhana tayi tana ci gaba da tsokanarshi, har ya taka steps daya biyu ya dan tsaya, har ta ƙaraso gurinshi bai ce komai ba, kallonta ya dan yi , cikin yin ƙasa da murya da marairaice ta yace "Ayya tsokanar ta isa haka Anuty, " dariya sosaj tayi tace ,"wato dai Sadiyyerh ta koya maka rigima da shagwaɓa", murmushi yy yana shafa gemunshi yace "Zama da madaukin kanwa.?", dariya ta ƙara yi kafin tace, "ooooh wato shi ke kawo jaan kai, lallai Yaaa Shehi wai ni yaushe ma kayi baki ?", ta fada tana kallonshi.


girarshi ya shafa kafin yace "uhmmm dama chan ni da bakina, ko ku bakwa ganinshi ?", ya fada yana takawa a hankali, "uhmmmm lallai kam ai yanzu na gani, amma dai da alama Sadiyyerh ce ta koya ma wannan surutun", ta fada tana yin hanyar Ɗakinta, har ta tura ƙofar yace "ki dan tura min ita", yana fada shima ya shige bedroom dinshi.


kwance ta sameta jikinta na ta rawa, da sauri ta ƙarasa gareta, tana cewa "lafiya dai ?", ta fada tana taɓa wuyanta, zafi zau ta ji jikinta, "baki da lafiya ne ?", ta fada cikin tausayawa, bata iya amaawa ba sa boda yarda mararta take mata, "Ayya sannu, Yaa Shehi na nemanki", ta fada tana kallonta.


jin Shehi na nemanta yasa ta yunƙura, a hankali Anty Rayhana ta taimaka mata ta miƙe, tare suka fita tana taimaka mata, har suka zo ƙofar palon Yaa Shehi, wucewa Ƙasa Anty Rayhana tayi, ita kuma ta tura ƙofar palon.


tana shiga taji hawaye suj fara taruwa cikin idanunta, dakyar ta iya zuwa bedroom dinsa, tana hangosa ta rushe da kuka, tare da ƙarasawa gareshi ta riƙe hannunshi tana kuka sosai.


A hankali ya fara ware idanunshi da suka mishi nauyi sosai sakamakon rashim barcin da baya samu, riƙeshi sosai Sadiyyerh tayi tana kuka sosai.


Zuba mata idanu yy yana son ya ji dalilin kukan, ita kuma sai kukan take taki tayi mgn, ganin ba zata ce komai ba , yasa yace "me ne?", ya faɗa yana zubawa fuskarta da ta jiƙe da hawaye ido, hannunshu da ta rike ta daura kan mararta tana ci gaba da kuka cikin shagwaɓa.


jikinshi ta shige tana kuka, shu kuwa a hankali ya fara yawo da hannun nashi kan mararta yana mata Addu'a tare da mammatsa mata kaɗan-kaɗan, a hankali kukanta ya fara ragewa yana yin ƙasa, sanyayyan numfashi take, fitarwa tana lullumshe idanunta.


a hankali barci ya fara fusgarta, yana fesa mata iskar bakinshi mai sanyi da dadin kamshi akan fuskarta, tana yi tana jaaan ajiyar zuciya har barci mai dan nauyi ya dauketa.


shi kam yana mai mamaki wannan ciwon marar da yake damunta tsawon lokacin da ta fara alada duk month sai tayi ciwon cikin , ya yi bancike amma ya kasa samun maganin ciwon kai tsaye sai dai na rage raɗaɗi, fesar da numfashi yy, kafin a hankali yace "uhmmm sai mun fara neman na hausa kenan", ya fada a hankali, yana mai mugu mugun tausaya mata sosai.


fuskarta da har ta fara faɗawa ya kalla, a hankali ya sa tattausan hannunshi ya shafi fuskarta.
gyara zama kwanciyarta yy a damtsen hannunshi yana mai lumshe idanunshi shima, dan so yake yy barci ko da na 30 minutes ne, sa boda ya rage nauyin idanunshi.


idanunta ta sauke akan fuskarshi tana kallon yarda yake barci cike da natsuwa, a cikin ranta ta ayyana, komai nashi mai kyau ne tattare da natsuwa,dan ko barcin ma cikin natsuwa yake yinshi, tun daga kan girarshi mai yawan gaske da ta yanka biyu har i zuwa kan lulu eyes dinshi da suke lumshe.


zuwa zara-zaran eyes lashas dinta, zuwa dogon hancinsa mai dauke da siririn karan hancinsa, zuwa ƙofofin hancinsa masu kyau da tsari, izuwa lips dinshi yan ƙanana masu kwauri da kyau , red colors da su.


ji tayi tana son sumbatar lips dinshi da a kullum suke kara kyau da sheƙi, a hsnkali ta matsa da fuskarta kusa da rashi fuskar, wanda haka ya haddasa haɗewar numfashinsa da na shi, cikin sanyi ta ci gaba da yin sama da fuskarta izuwa kan tashi fuskar.


cikin kamala ta manna mishi light kisses akan lips dinshi, saukar kisses din ne yasa ya fara bude idanunshi a hankali har ya saukesu kan kyakyawar fuskarta da ta rame na lokaci daya, ware idanunshi yy , cikin yar tsokana yace "kina son karyan Azumina ne ko ,?" ya fada yana mai duban fuskarta, cuno baki tayi tana shafa gemunshi, a hanksli tace "ni na isa karya Azumin Yaaa Shehi", gefen fuskarta ya shafa kafin cikin cool voice dinshi yace "har ma kin yi yawa", ya fada yana kissing forhead dinta, "ta ya ya ?", ta fada a hankali, cikin kasalalliyar murya yace "kina son sani ne?", gyaɗa mishi kanta tayi.



cikin natsuwa ya fara yin ƙasa da kansa sai da ya kai dai dai ........
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.18*



Cikin natsuwa ya fara yin ƙasa da hannunshi, sai da ya daurashi kan waist nata kafin ya matso da ita jikinshi sosai, ta yarda jikinshi yake gugar nata , numfashinsu na sauka akan fuskar juna, a hankali ya fara matsowa da duskarshi zuwa gareta.


sai da ya kusan haɗe lips dinshi da nata kafin tayi maza ta matsa daga kusa da shi ta koma gefe chan ta kwanta tana kallonshi, lumshe idanunshi yy kafin yace "Yarinya kin ceci kan ki", dariya ta yi kafin tace "Yaaa Shehi kai ne ka ceci Azuminka fa, da yanzu yy rugu-rugu" ta fada tana dariya.
fuskarta da tayi haske ya ƙara kallo, yana mamakin irin gasken da take in tana period kamar mai bleaching .


miƙewa tayi ta nufi fridge dinshi, tana neman abun da zata sawa cikinta, idanunta ne ya sauka akan Tuffar da take ciki, dauka tayi sai da ta kalleshi kafin tace "in ci ?", ta fada tana kao wa gurin bakinta, girgiza mata kai yy kafin yace "a'a kar ki ci", kwaɓe fuskarta tayi tace "yunwa fa nake ji", taɓe bakinshi yy kafin yace "gyandiya bata Azumi ta zama toton masara", tura bakinta tayi tana gatsa Tuffae tace ",Allah ne ya hutassheni ai ", ta fada tana kallonshi.


dauke idanu shi yy kafin yace "salon in kinzo ramuwa kuma kizo kina gwagwallomin idanu, " da sauri tace "ai ba zan yi ba ", kallonta yy kafin yace " mai ?", yana gwaggwalo mata idanunshi, hannunshi kuma na cikin gemunshi yana shafawa.


"Azumin", "kiyi saurin tuba ma Yarinya dan ramuwa bb fashi, dan gidan Babban Malami ba'a shan Azumi sai da lalura, lalurarar ma in aka sha sai an rama, ko su Amah ba zasu ƙara shan azumi ba, balle ke aure bana haihuwa faɗi kisha kice bazaki rama ba", turo baki tayi kafin tace "kaiiiii Yaa Shehi" , kallonta ya dan yi kafin yace "ki tsaya wasa ki ga", ya fada yana miƙewa, bathroom ya shige bai saurari maganganun da take zuba mishi ba.


ganin ya shiga ciki yasa ta miƙe, kai tsaye gaban wardrobe dinshi ta nufa, tana budewa ta fara tozali da Tan Brown Jallabiya sabuwa dal , da sauri ta zarota, boxer da Singlet ta daukar mishi tare da feshesu fes da turarenshi na Huge Boss.


Ajiyewa tayi a gefen bed kafin ta nufi gurin takalmanshu da sun kai kala Arba'in kala-kala ,wasu ma sababbi ne ba'a taɓa sanyasu ba designs kala-kala companies ma daban-daban.



hannunta ne ya sauka akanGray Joaquin Italian Leather half Shoe sababbi dal dasu, sai sheƙi yake, gurin Agogunanshi ta nufa, in da suma suke kala-kala Zinariya Azurfa da sauransu Boston white silver , ta daukar mishi sai daukar ido take, kafin dai ya fito ta haɗa mishi komai da zai sanya.


gently ya fito daga Bathroom din jikimshi na ɗigar da ruwa , towel ne a hannunshi yana tafiya yana goge gashin kanshi da gemunshi da suke ɗigar da ruwa, sai gashn jikinshi da ya ƙara yin luf a jikinshi, da sauri ta matsa domin taimaka mishi, da sauri yace "sha zamanki ki huta zan", ya fada yana ƙarasa goge ruwan da yake jikinshi ya ajiye towel din a gefe.



sauri-sauri ya shiga shiryawa dan lokaci ya fara ƙurewa, bai wani sau lokaci mai yawa ba ya gama komai da zai, yana gamawa ta nufeshi da Alƙyabbarshi Brown sa torch din baƙi, itama tana ta zuba kamshi turare.


kanshi ya dan karyar tare da dan dukawa ya rage tsawonshi izuwa nata, a hankali ta sanya mishi Alƙyabbar , tana mai daure mishi igiyoyinta sai da ta gama ta daura mishi kiss a checks dinshi cike da tsantsar kulawar mata zuwa ga miji.


cikin natsuwa tare da nuna tsantsar kulawa shina ya ɗago kanta tare da manna mata kiss a goshnta da kumatunta, cuno baki tayi taba kallonshi, alama yy mata da me ne ne kuma, lips dinta ta ƙara turowa kafin tace "nan ba'a mishi ba", ta fada tana daura hannunta akan lips dinta, dafe kanshi yy, ganin tana neman sanya mishi ciwon kai yasa ya manna mata light kiss, yy gaba abunshi.



har ya kusa zuwa waje ta juyo cikin sanyinshi yace "ki shirya zamu kasuwa An jima", ya fada yana ficewa ba tare da ya jira jin Amsarta ba, biyo bayanshi tayi , yana gaba tana binshi a baya, bb wanda kuma ya cewa dan Uwanshi Uffan.


suna shigowa cikin palo Jadda tace "Uhmmmm Juya !, juya wato ke dai sai dai kici kiyi ƙaton kashi shine kawai aikinki, amna ko zuciya ba zakiyi ki haihu ba", Sadiyyerh na iya baƙin ƙoƙarinta gurin ganin ta bawa kowa girmanshi, amna Jadda irin tsaffin nan ne marasa kamun kai, masu hassada da ƙyashi hakan yasa bata biyata, amma yau ta mata abun da ta ji haushi sosai.


bata ko kulata ba tayi gaba, cikin isgili tace "dake fa nake Ƙabuwa ina magana kina shareni , an samu dukiya an yi ƙane ƙane, ke da uwarki bb gori bale nagode , yan cin Arziki kawai", Ya ilahi kar kuso ku tona zuciyar Sadiyyerh tayi baƙiƙƙirin, cikin zallar ɓacin rai ta juyo , idanunta har wani ruwa-ruwa suke, cike da rashin ƙyaliya tace "ya fa isheki, ina ce kema baki da Ɗa baki da Ɗan jika, baki taɓa haihuwa ba, kuma ina da labarin cewar Dattijai ma ke daya suka haifa da kika tashi fitowa sai kika yi baƙin kashin da daga ke basu ƙara ba, to me ne ne na ɗaga hankali da magana dan ban haihu ba, mijina bai damuna ba, Yan uwan mijina ina tare dasu lafiya, amma ke kinon rusawa.
kuma da kar ki manta Asalin wance itama Baiwace baiwa ma ƙasƙantacciya, Allah ya daga su to kuma ai ƙarshen talauci kenan", ta fada tana daura ƙafarta daya kan daya.


ciƙe da zallar ɓacin rai Jadda tace "ke! ni kike fadawa magana ?, kamar ji da nayi sa'an kakarki amma har kike budar baki ki faɗa min mgn,lallai baki da kunya Yaa Shehi bai yi dacen mata tagari ba, gayyar na ayyaro gayyar marasa kunya ", dariya Sadiyyerh tayi kafin tace "to ai in babba bai ji kunyar hawa jiki ba, to jaki ma ga zai ji kunyar ɗirkashi da ƙasa ba, marasa kunyar na da yawa", ta fads tana lallatsa wayarta.



basu Zayn da suke ganin ikon Allah ba har Yaa Shehi yy mamakin yarda Sadiyyerh ta uya fadawa Jadda wannan maganar haka, duk kuwa da cewar sun ji dadin hakan da ta mata, amma kuma bai dace ba magamganun sunyi sauri sosai da Sadiyyerh ta faɗesu ko akan wani balle kuma Matar Kakansu .
ko da yake ita tajaa sa boda bata son zaman lpy da kowa, yarda ta tsani Yaaa Shehi da Yan uwanshi kamar ta kunna musu wuta take ji.


"shegiya marar kunya , sai naga karshen ki tunda baki da mutunci, tsiyar talaka fa kenan ka daukoshi ka sanyashi a daula ya wulaƙantaka in ya tashi," ta fada tana kyaɓɓe baki gefe.



Sadiyyerh ta bude baki zata yi mgn Umma Jakadiya tace "tak kika ƙara cewa ban yafe b ", dole ta kulle bakinta, tana jin duk irin baƙaƙen maganganun da Jadda take mata.


daga ƙarshe ma shigewa tayi ta bar Jadda da yi.
da misalin 8pm gaba dayansu suna zaune kan Dining suna buda baki, har da Yaa Shehi wanda shu daban yake Buda baki amma yau duk tare suke.


Jadda ta kwaɗawa Sadiyyerh da taci kwalliyarta tana jiran su gama sa boda fotar sa zasuyi da Yaaa Shehi harara, kaɗa baki tayi tare da cewa "Ka Auri mara tarbiyar Yarinya, bata ganin Uban kowa da gashi, kowa ganinshi take tamkar dan iskan Lagas , gashi bb Ɗa bb Ɗan jika, amma kaj a haka kake son zama da ita, ? .
wallahi dole a chanja zama dole ka ƙara Aure, in ma shanyeka suka yi sai na ji", ta fada tana wullawa Umma Jakadiya harara, ita kuwa murmushi tayi, cikin kaifin baki irin na Sadiyyerh tace "dadinta ma ba ni aka farawa kishiyar ba sa boda ban haihu ba, kafin amin an wa wasu da yawa, to me ne abun ɗaga hankalina, Dan Allah Yaaa Shehi in ka tashi Aurowa ka ƙaro ukku mu zama huɗu, chan ta matsewa Yan hassada wlh ni ko a liƙon Slippers dina", ta fada tana kurɓar sanyayyan lemun Abarba.


maganar da tafi ƙonawa Jadda rai kenan, wato nufinta , ita aka farawa kishiyar sa boda rashin haihuwa kafin ita ?, gaskiya tayi sake da yarinyar nan tasan Asalin tarihinta.


nunawa Sadiyyerh hannu tayi cikin zallar ɓacin rai tace "mara kunya bake ba ko Uwarki Jakadiya ta isa tamin rashin ɗa'a ?, to ki kiyaye harshenki ko kuma ki gane kurenki", ta fada tana nuna mata hannu, ko kallonta Sadiyyerh bata yi ba, dan taga Irin kallon da Yaa Shehi yake aika mata dashi, wanda yake nuna zallar rashin dadin abun da tayi.


Jadda zata ƙara mgn Shehi ya ɗaga mata hannu, cikin kakkausar murya yace "ina zaune qlau da Iyalaina bazaki zo ki haɗa min husuma ba, bana son hassada", ya fada yana miƙewa, ya bar gurin.


gaba dayansu tashi suka yi suka bar wa Jadda gurin ita daya, tsabar takaicin da ta shiga ji tayi kamar ta dilmiye ƙasa , sa boda tsabar haushi da takaici wai yau ita wannan Yaran sukewa haka, a bayyana tace "barin su da nayi suna shaƙar iskar duniya shine yasa suke faɗan magana yarda ransu ya musu, za ku kuwa yi ta rayuwarku, dan wlh bazan lamunta ba, " ta fads tana buga dining din tare da ci gaba da mugun kulli ciki zuciyarta.


Dama Gyalan Abayarta da Niƙaf dinta na hannunta, tana ganin Yaaa Shehi yy waje, tabi bayanshi tana rolling din Gyallen da daura Niƙaf dinta a kanta, sak ta fito Asalin matar Yaaa Shehi, tayi shiga irin ta Larabawa, farar fatarta da zallar kamarta da Fulani yasa har ta fara ɗibar kama da Larabawa.


kafin su isa gurin mota har an bude musu, suna shiga aka rufe ƙai tsaye motocin Ƙirar Bentley flying spur, a hankali suke tafiya har suka karasa babbar kasuwar Makkah, sai ma da suka Zo Yaaa Shehi ya ji ba zai iya fita ba, a hankali y rike hannunta, kallonshu tayi sukawa juna kallon ido cikin ido kafin yace " ki je ki dauki duk abun da kike so, kuma ki kula " yana fada ya zare hannunshu daga nata.



"Kai kuma fa?", ta fada kai tsaye ba tare da ta kalleshi ba, kallonta yy na yan tsurarun minutes kafin yace " bana bukata", bata ce da shu kimai ba ta fice daga cikin motar, gaba daya masu tsaron lafiyar Yaaa Shehi suka take mata baya izuwa cikin babbar kasuwar da ake ta hada-hada kamar rana.


Kai tsaye shagon kayan siyarwa suka nufa, shago ne babba sosai na gani na fada shagon yana cike da kayan sawa na Kasae dama na sauran kasashe, a hankali ta fara bin layin lass dan ita tafi son lass a cikin kaya, kays ta shiga diba ba tare da duba tsadarsu ba, dsn tasan Allah y hore musu Abun da zasu biya,bayan ta gama zazzaba sai ta bi layin Abayas ba laifi suna ta dan diba.


Shoes da bags kuwa har ba'a magana dan har sun fi kayan da ta siya yawa, sai kusan 11pm ta fito daga shagon a mugun gajiye, sai hamma take bugawa, tun daga nesa ya hsngo yarda take tafiya alamar ta gaji, sauran guard na dauke da manyan jakunkunan da aka zuba musu kayan a ciki, mai tambarin Al-azee store.


Bude mata motar aka yi ta shiga , tana shiga tawa kanta masauki akan jikinshi tana fesar da sanyayyan numfashi, idanunta akan fuskarshi tace "Uhmmm na gaji, gashi ba'a siyo Hijab's ba", ta fada tana lumshe idonta.


" mai yasa baki siya a nan ba ?", ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba, cuno baki tayi kafin tace " na gaji ni . barci nake ji", ta fada tana rufe idanunta ruf, " bakya azumin amma kika gaji ?" , kallon fuskarshi tayi, sai da ta shagwabe fuska kafin tace "Wlh ko kai baka kai ni gajiya ba, yau aikin da nayi sai Allah", ta fada tana daura kantw kan kirjinshi," na ga alama" ya bata amsa kai tsaye.


Suna nan gurin Yaa Shehi yawa Telanta magana, akan ta zo ya samesu anan gurin ,ba'a dau lokaci mai tsawo ba sosai sai gashi ya zo, farin Balarabe dashi dan baya ma jin Hausa.



Cikin harshen Larabci Yaaa Shehi yy mishi mgn, tare da bada umarnin a bashi kayan ya tafi da su, har ya juya ya kara kiran sunanshi, sai da ya juyo kafin yace "gobe nake so ", ya fada cikin muryar gargadi, murmushi yy tare ds jinjina kanshi, yana barin gurin suma suka bar gurin.


Lokacin da suka karaso gidan palo bb kowa ,kowa ta kwanta, a hankali Sadiyyerh take tafiya tsna layi kamar zata fadi, suna zuwa tsakiyar palo tayi luuuu zata fadi saboda barcib da ya dibeta, da sauri ya manna hannayensa kan waist dinta, ya karata da jikinsa sosai gudun kar ta fadi, cikin natsuwa suke takawa har suka fara haura steps .
Kanta ta manna kan faffadan kirjinshj ta rikeshi, idanunta lumshe.


Suna shiga bedroom ta zame ra kwanta , girgiza kanshu yy yaba wucewa Bathroom yana mai kara jadadda magagin barcinta, wanka hade ra alwala yy kafin ya fito, a hankali jikinshi na digar da ruwa, shiri ya chanja zuwa wata Jallabiyar fara sai daukar ido yake.
Agogo ya duba , lokacin da idanunshi suka sauka akan agogo lunshe ido yy, kafin ya sauke idanunshi akan Sadiyyerh.


Zaunar da ita yy, kafin ya fara zuge zip din rigar jikinta, har y gama yin kasa da rigar bata sani ba, zame rigar ga fara kokarin yi, da sauri ta rike hannunshi tana mai ware manyan-manyan idanunta masu cike da barci, shima ware nashi idanun yy , bakinta ta bude zata yi mgn, toshe mata bakin yy, kafin ta gama banbance abun da ta rufe mata bakin dashi taji hannunshi na yawo cikin r.........
[4/27, 9:07 PM] salmeertsanisalman: *P.19*


Zaunar da ita yy, kafin ya fara zuge zip din rigar jikinta, har y gama yin kasa da rigar bata sani ba, zame rigar ga fara kokarin yi, da sauri ta rike hannunshi tana mai ware manyan-manyan idanunta masu cike da barci, shima ware nashi idanun yy , bakinta ta bude zata yi mgn, toshe mata bakin yy, kafin ta gama banbance abun da ta rufe mata bakin dashi taji hannunshi na yawo cikin rigar jikinta.
Da sauri ta wartsake idanunta ta mike tana kallonshi.



Rike mish hannunshu tayi taba kallon cikin idanunta, da suka wartsake kamar bata tab'a kwanciya barci ba, "me zaka min ?", ta fada tana rike hannunshi, d'aga idsnunshi yybya watsesu cikin nata, da sauri ta dauke kanta dan ko kad'an bazata iya kallon cikin idanunshi ba, wanda tun tana ƙarama ya horeta da hakan, bama shi daya ba idon ko wane babba bata iya kallo, domin an horeta da cewar kallon cikin idanun babba kamar raini ne, hakan yasa bata iya haɗa idanu dashi.


cikin muryarshi da tayi ƙasa yace " ni da halalina kike tuhumata?", ya fada yana tsareta da manyan idanunsa, ƙasa da kanta tayi tana cuno baki tace "Ayya Yaa Shehi ", ta fada cikin sanyin mgn, ɗago da haɓɓarta yz yi yana kallom fuskarta.
rumtse idanunta tayi gaba daya dan ta fuskanci so yake su haɗa idanu, "Yaa Shehi.!", ta furta cikin shagwaɓaɓɓiyar muryata, mai narkar da shi, "Sadiyyerh!", shima ya furta cikin sanyin

3 Comments On ARMAN MALEEK
avatar
batula-yahaya

1 year ago

Reply

08139693951

avatar
daiy

1 year ago

Reply

Replying to batula-yahaya

Me yasa kika ajjiye nambarki kuma

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to daiy

Thanks for tuni

Please Login or Register in order to submit comment