Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]


Bismillahir Rahmanirrahim.
Ina farawa da sunan Allah me Rahma mejinkai.

GARGADI....... Banyarda wani ko wata su juyamun littafina ko su canzamun sunanshi ba. Wannan labari kirkirarre ne, banyi dan wata ko wani ba, zanyi shine domin yazama darasi ga kai, ke,ni, su da kuma mu baki daya. Allah yasa yanda zanfarashi lafiya in gamashi lafiya amin.

Season 1 🔱 5

Zaune yake agefe guda yayi tagumi hawaye suna bin fuskarshi, idanu yazuba ma mutanen dasuke yi masu watsi da kaya.

Kallon dayan gefenshi yayi ganin yanda matarshi kuma abin sonshi, take kuka. Duk da itace sanadin fadawarsu wannan hali amma yana tausayinta sosai.

Kuma haryanzu duk da irin halin data sakasu bayajin digon sonta yaragu azuciyarshi. Wannan wulakanci na korarsu daga gidan haya shine na 3 tun bayan aurensu.

Goge idonshi yayi, wasu hawayen suka kara zubowa alokacin daya tuna magana mahaifiyarshi. Abbas kada kabiyema Son dakake ma wannan yarinyar, ze kai ka yabarokane, idan bazata iya zama da kai ayanda kake ba to kahakura da ita.

Kanshi yacigaba da girgizawa hawayen idonshi suna kara zubowa, yarasa inda zesa kanshi, gashi ta dalilin matarshi gaba daya sun bata da abokanshi, mutum daya ne, yarage mashi wanda yake temaka mashi.

Karar faduwar wani abu dayaji ne yayi saurin dawo dashi daga tunanin dayakeyi. Ihun matarshi yaji tana fadin dan Allah kuyi hakuri kada kuyi mana banna.

Saurin tashi yayi yanufi gurinta. Jawota yayi ya rungumeta yana bata hakuri, mutane dayawa yan unguwar harma da makota sun tausaya masu.

Wani daga gefe ne yace kai gaskiya abokina megidan nan beda mutunci, kamar ba musulmi ba, haba dan Allah yaza,a rika watsi da kayan mutane kamar besan darajarsu ba.

Abokin yace uhm abokina beda laifi, kama dena tausayin ABBAS ALEE, domin acikin rukunin unguwar nan mutane dayawa sun san halinshi,

Ace mutum beda tunanin kanshi sena matarshi. Haba wace irin rayuwace haka, ai so ba hauka bane, a iya sanina wannan shine gidan haya na 2 danasan ana mashi irin wannan korar wulakancin.

Kuma duk lokacin da aka tashi korarshi seyayi asara ba kadan ba. Yanzu kaduba kayansu, sekace wadanda suka shekara 10 dayin aure.

Duk sun kare ayawon haya. Wlh kaganni nan babu yanda za,ayi inyarda inyi aure batare dana mallaki MUHALLI na nakaina ba. Aishi MUHALLI DARAJA gareshi.

Maganar daya daga cikin mutanen dasuke masu watsi da kayan ne taja hankalin masu wannan maganar. Ina me tabbatar maku ko kukan jini zakuyi wlh kun gama zama acikin gidan nan.

Ai ko da kudin ubanku aka sayi gidan inde ance na haya ne, dole kubiya idan lokaci yayi, damma kunsami Oga mesauki ne har ya iya yafe maku na watannin da kuka kara.

Acikin kudinku na shekara har seda kuka kara wata 4, sannan duk da haka bakuga adalcin da megida yayi maku ba. Sa,a kukaci da besa aka daure kuba. Maza ku kwashe tsummokaran kayanku kubar kofar gidan nan.

Shide Abbas Alee yayi shiru bece komai ba, yana rungume da matarshi, yama rasa yanda zeyi, gashi ko sisi bashida ita bare yakira me mota yadaukar masu kayansu.


Yana kallo mutane yan kallo suka fara watsewa, da haka har gurin yazamto saura yara kanana, kama matarshi yayi yazaunar da ita gefe, tana ta faman goge kwallan datake zubo mata.

Aranta tana danasanin wannan hali nata marar kyau, da yanda tabiyema karyar zamani tasaka mijinta cikin wannan yanayin.

Matsawa yayi gurin kayansu yafara tattara akwatinansu yana kawosu gefe guda, sannan yakoma yahada sauran kayan daya bayan daya yatarasu suma agefe guda.

Kusa da ita yadawo yazauna, yace LABIBA dan Allah kidena wannan kukan haka, banason kina kuka domin kukanki yafi wannan hali damukeci, sakani cikin damuwa.

Kallonshi tayi tace dole inyi kuka Abbas, duk nice sanadiyar sakamu cikin wannan rayuwa, gashi yanzu duka shekararmu 4 da aure amma haryanzu babu gidan damukayi sama da shekara 1 acikinshi.

Tun muna zama gida me kyau, har muka fara zama marar kyau, yanzu gashi wannan dinma danake rainawa, shima ankoremu, yanzu kuma wayasan wane iri zamu samu? Kuka takara sakamashi.

Jawota yayi yace karki damu, Allah shine yasakamu acikin wannan halin kuma yana sane damu insha Allah bazamu tozarta ba, abinda nakeso dake ki kara hakuri dani aduk halin dazamu tsinci kanmu aciki.

Banason talauci yasa kijuya mun baya, nayi maki alkawarin zan zauna dake akowane hali nake ciki, inaso kema kimun wannan alkawarin Labiba.

Shan majina tayi takamo hannunshi tace nayi maka alkawarin zan zauna da kai koda acikin bukka zamu zauna matukar zan jika akusa dani, kuma nayi maka alkawarin insha Allahu bazan kara bijire maka ba aduk inda kasama mana domin muzauna.

Murmushin jin dadi yayi yakara rungumeta yana fadin nagode maki masoyiyata Allah yabarmu tare. Dafashi yaji anyi dasauri ya juya yana kallon bayanshi.

Murmushi yayi yace sannunku masoyan asali, wato kuna cikin wani hali amma kuna soyayya ko ABBAS ALEE?.

Murmushi Abbas yayi yace to abokina yakake so muyi, ai gara muyi soyayyar kozamu samu saukin abinda yake damun mu.

Zama yayi kusa da Abbas fuskarshi dauke da damuwa yace ina kasuwa ashago nasamu labarin abinda akai maku, hakan yasa na taho,kuma tundazu nasamu labarin.

Abinda yasa banzo dawuri ba, seda nabiya nafara sama maku wani gidan dazaku zauna sannan nataho da motar dazata dauki kayan.

Wasu hawayene suka zuboma Abbas dayaji bayanin babban abokinshi. Kallonshi yayi yace Jafar nama rasa dawane baki zan maka godiya, akullum bakada wani buri daya wuce ka kyautatamun.

Tabbas kai abokine nagari, Allah yayi maka albarka, yabaka duk abinda kake nema. Jafar yace amin. Dama kwana 2 banga kaje shago ba, shine naje gurin Alhajin na tamabayeshi,

Shine yake cemun wai ya sallameka, amma meyasa baka fadamun ba? Girgiza kai Abbas yayi yace haba Jafar yazanyi tasaka cikin damuwa, bayan kana kokarin temako na akowane lokaci.

Jafar yace koma menene yakamata kafadamun, ina da wani bayanka,ne? Kai wane irin temako,ne bakamun ba, seni yanzu inkasa temaka maka.

Wlh nayi bakin ciki da gidana be kasance me dakuna dayawa ba, da aciki zaka zauna har abada har kasamu naka nakanka, kai koda ace dakuna 2 ne, zan iya daukar daya inbaku daya.

Sede kash!!!, nima da kyar nasamu nagina ciki da falo da bandaki , kana ganin haryanzu kitchen dinma bankarasa ginashi ba. Abbas yayi murmushi yace Jafar ka godema Allah dayaba ikon mallakar MUHALLINKA na kanka.

Kuma babu komai, wannan abun ma dakamun kadai ya isa, nagode sosai, nima kaddara ce tafadomun harna rasa nawa MUHALLIN, se ayanzu nake gane DARAJAR MUHALLI.

Amma bakomai, tunda na tsira da abin sona hakan ma ya isheni. Girgiza kai Jafar yayi cike da tausayin abokinshi, yarasa wane irin sone yakema Labiba. Matar da itace silar shigarshi cikin wannan yanayin.

Kamar daga sama yaji muryar Labiba tace Jafar awace unguwa ka sama mana gidan, Allah de yasa tana da kyau, kuma babu kowa aciki?

Saurin kallonta Abbas yayi domin beji dadin maganar datayi ba, shiru yayi dan bayason yayi mata magana ranta ya baci. Jafar kuwa jiyayi kamar ya shakota.

Daurewa yayi yace acikin burget gidan yake, kuma abokina sede kuyi hakuri domin gidan dakuna 4 ne aciki guda 3 akwai mutane, dayan ne nakama maku, sede ciki da falo ne, amma babu bandaki aciki.

Yana waje, sede kuyi hakuri kafin Allah ya hore asamu wani se acanza maku, kasan yanayin da ake ciki, yanzu kasuwa tayi kasa. Abbas yayi murmushi yace haba abokina meye na bada hakuri sekace da kudinmu aciki.

Nagode sosai Allah yabar zumunci. Yace amin. Wata irin zufa ce tafara keto ma Labiba jin irin gidan da aka kama masu, yoko gidansu na da ai yafi shi daraja. Idonta ta kulle wasu zafafan hawaye suka zubo mata, tana kara tsanar kanta. Da haka aka saka masu kayansu acikin mota suka nufi sabuwar unguwarsu.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady )
08028525263
[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 5 🔱 10

Labiba tana tsaye aka gama shiga da kayansu cikin gidan, wani irin bakin ciki ne ya turnuketa, tunda taga sun shigo cikin unguwar, gaba daya layin beda fasali,

Ko acikin Burget dinma yana daga cikin kazaman layi, har cikinta seda taji yana yamutsawa saboda warin kwata, kara kallon gidan dazata zauna tayi,

Ko kofar kirki babu agidan, hatta da simintin gidan duk ya karce, kwalla taji ta cika mata ido, tunawa tayi alokacin da Abbas yakama masu wani gida kafin su zauna a wanda aka koresu,

Gidan yana da kyau, mace daya ce aciki kuma kowa da part dinshi, tsakar gida kadai ta hadasu, amma tace bataso ita bazata iya zama da kowa acikin gida ba.

Haka nan yanaji yana gani ya hakura da gidan alokacin har seda suka kusa yin fada da Jafar dan shine ya sama mashi gidan, ganin ran Abbas ze baci yasa Jafar ya kyaleshi.

Haka yaje ya kara samo masu wani gidan, wanda shine aka koresu aciki yanzu. Ajiyar zuciya tayi, setaji dama ta hakura sun zauna awancan gidan, tunda Jafar yace gidan dan uwanshi ne, yasan baze koresu ba, idan basu biya ba,

Segashi aranar da sukaki zama gidan aranar wasu suka karba. Hijabinta tasa tagoge fuskarta. Aranta tace oni Labiba, haka kuma ni tawa kaddarar tazo mani.

Allah yajikanku mama na da Babana, danabi shawarar ku da duk haka bata faru dani ba, segashi yanzu narasaku, banida mesona se mijina, dangin Babana ma sungujeni,


Dafata taji anyi, kobata kalla ba, tasan mijinta ne, hannunta yakamo yana fadin haryanzu bazaki dena kukan ba ko? Kiyi hakuri dan Allah, duk wannan abun wata rana ze wuce, kinji Labibata.

Haka yajata suka shiga gidan, mata 2 tagani atsakar gidan, wadda bawani fadi gareta ba, kowacce tana aikinta, babu wanda yadaga kai yakallesu, Abbas yayi sallama sannan suka dago suka amsa.

Da kallo suka bisu, har suka shige, dariya daya tayi tace wayyoni duniya, ke Laraba kina ganin wani sabon salo agidan nan yau, ke daganin yanayin kayan wannan mata ba amarya bace,

Amma kalli yanda yawani rungumota ita kuma tana kuka sekace wadda akama dole. Dariya wadda aka kira da labara tayi tace, uhm kede ganemun hanya Laure,

Inde gidan haya ne, ya isheka riga da wando, duk wasu masu kilibibi haka zasu kare, shewa suka saka harda tafawa.

Duk abinda sukeyi Labiba da Abbas sunajinasu, Jafar dayake zaune afalo bisa kujera yace dan Allah Labiba kada ki kula wadan can matan, kinsan gidan haya yagaji haka, saboda kowa yana takamar kudinshi yasa yakama gida, babu ruwanki dasu, kinga kece me zama acikinsu.

Shiru tayi tana ta kuka, haka sukayita bata hakuri hartayi shiru. Jafar yace abokina bara inje inkawo maku abinda zakuci tunda nasan bazata iya girki yanzu ba, kuma gashi yamma tayi har ankusa kiran sallah.

Kuma gobe inaso muhadu akasuwa ashagon danake kazo idan yaso se aduba maka abinda zakayi, bazaka zauna hakanan ba, amma sekayi hakuri kasan nima shagon banawa bane.

Abbas yace haba Jafar, wai meyasa komai zakamun seka bani hakuri? In badan kai ba, ayau ma bansan inda zamuje ba, kasande bazan tunkari Ummata infada mata halin danake ciki ba, dan itama gidan da take ciki ita da kanina bawani girma gareshi ba,

Saboda haka ni kowane irin aiki nasamu zanyi, matukar aikin halal ne, banida abinda zance maka sede Allah yakara daukaka. Jafar yace amin, bara inje sena dawo, yace to.

Tashi sukayi suka shiga daki suka kara gyara kayansu, Abbas ya bude tagar dakin, domin zafi yakeji dan dakin babu fanka ancireta, saukinsu ma akwai wuta, gaba daya kayan kitchen din Labiba adaki aka sasu, wasu kuma afalo bayan kofa.

Damma kayan bawani yawa garesu ba, duk ta saida wasu, kujerunta ma biyu kadai suka rage, alokacin dazasu tashi daga wani gida basuda kudi suka saida guda 2 manyan, hakan yasa falon be cunkushe ba.

Abbas yace Labiba ina ganin tunda falon yana da dan girma kawai musa labule daga can sekirika girki agurin banason kifita waje kina girki naga alamun matan gidan nan basu da kirki.

Murmushin jin dadi tayi, kamar yasan abinda yake damunta kenan, shima seda yayi murmushin ganin yasata farin ciki. Yace tunda muna da babbar robar zuba ruwa semu rika cikata, kinga babu ruwanki da fita waje debo ruwa,

Daya kusa karewa se azuba, bandaki ne, kadai zerika fitar damu, bakomai ai, ni dama fita inyi girkinne banaso, nagode, maganar bandaki kuma zan kula da lokacin da suke shiga se inkiyaye.

Abbas yace hakane, ko kuma kawai zansa alarm awayata kamar karfe 4:30 se murika tashi, muyi wankan mu muyi alwala kinga zamu samu saukin bin layi, dan naga alama akwai yara agidan.

Rungumeshi tayi tace gaskiya naji dadin wannan shawara taka, yace bakomai, Labiba, idan ban jiya maki dadi ba, wazan mawa? Nikadai kike dashi, kuma kinbani duk soyayyarki banida abinda zance maki, se fatan Allah yakara mani budi inmaki abinda yafi haka. Tace amin.

Jafar ne yayi sallama Abbas yace bismillah shigo, mamakine yakama Abbas ganin Jafar dauke da kaya, kama mashi yayi yasauke sannan yazauna. Abbas yace Jafar kaida kace zaka kawo abinci shine naganka da kaya haka?.

Murmushi yayi yace haba ai bakomai, kayan shayi ne, nasiyo maku da galan din kananzir, se kuma sabulai, ga kuma guga nan se kurika ajeta agurinku, kunsan gidan haya kowa da kayanshi,

Abbas yace mungode, anan yafada mashi dabarar dasukayi,Jafar yace gsky ne, hakan ma yayi tunda bawani yawa gareku ba, inafatan rishow din baya hayaki ko? Labiba tace a,a bayayi kaga tukwanena haryanzu basuyi baki ba,

Yace yauwa, Allah yabaki hakurin zama agidan nan,insha Allahu bazaku dade aciki ba, duk da kudin shekara na bada, amma idan nasamu hali zaku tashi idan yaso se yamaido mana kudinmu, dama nayi dashi ahaka.

Mikama Labiba cooler din abincin yayi yace abokina muje masallaci ko, yace to muje, Jafar yace to Labiba ni daga can zan wuce Allah yabaku zaman lafiya keda mutanen gidan, babu ruwanki dasu, kuma kada ki kyamace su,

Sede kar kije dakin kowa, amma inkinfita kirika gaishesu, hakan zesa kifisu, idan ma suna nufinki dawani abu, Allah ze kareki. Tace to Jafar nagode.

Abbas yace tashi kije ga bandakin can naga bakowa dauki pure water kizuba abuta kafin indawo se inzuba mana ruwa.

Jafar yace a,a bazaka fara jan ruwa tun yanzu ba, muje naga akwai masu ruwa se suzo suzuba, fita sukayi ita kuma ta dauki buta tanufi bandaki.

Tana fita wani yaro daya fito daga dakinsu shima da buta ahannunshi yarugo da gudu har yana shirin bangajeta, saurin bashi hanya tayi, kawai yashige bandakin yarufo.

Tsayawa tayi akusa da bandakin, ga wani irin wari agurin, wasu hawayene suka zubo mata na bakin ciki, yanzu idan wani babban uzuri gareta sede tayishi awando.

Share hawayenta tayi tace agaskiya bari Abbas yadawo acikin bokatai na, farare na fenti zan dauki daya inrika fitsari aciki, tunda de suna da murfi, idan yaso se inrika fitowa waje ina alwalar,

Gara inrika wahalar wanke bokitin dade irin wannan iskancin yaran gidan nan, ta dade atsaye kafin yafito, har wata yarinya zata shiga taji wata mata tace ke Zainab kitsaya ta fito tunda tarigaki,

Juyawa tayi ta kalli me maganar, dan alokacin da suka shigo gidan bataji muryarta ba, murmushi tayi mata tace nagode, ita murmushin tayi tace bakomai.

Bayan tagama sallah taji sallamar mace, tashi tayi tafita falo tana amsawa, fuskarta tasaki ganin wannan matar tadazu, tace a,a maman Zainab kishigo mana.

Bayan sungama gaisawa, maman zainab tace sannu da zuwa, wlh bansan kunzo ba, nade san ance za,a kawo wasu yau, dayake ina cikin daki bansan lokacin dakuka zoba.

Labiba tace ai bakomai, Maman Zainab tace ya sunanki? Tace Labiba, tace sannu da zuwa Labiba, kema Allah yakawoki gidanmu babu abinda zance maki sede ince kiyi hakuri da duk yanda kika tsinci kanki agidan nan.

Kinganni nan yau shekararmu daya agidan nan, diyata daya se mijina, akullum ina addu,ar Allah yakawo mana karshen zaman gidan nan. Zamane mukeyi kowa da mijinta amma yanda kikasan kishiyoyi haka ake wannan zama.

Agaskiya kafin insamu yanci agidan nan nasha wahala, shiyasa nayi alkwarin fadama duk wadda tashigo gidan nan halin yan gidan, bazanso acutar da itaba kamar yanda suka mani, domin anan nazo nasamesu.

Kin ganni nan nasha wahalar matan can guda 2, afarkon zuwana, dayake mijina idan yafita tun asuba baya dawowa se gurin 10, hakan yasa banida abokin fira, sede infita gurinsu.

Babu kalar wayon dabasu yimani ba, hatta girki kinga de mijina abincin dare kadai yakeci, mu 2 kawai zanma girkin safe dana rana ko, amma duk da haka sena dora babbar tukunya,

Haka zan gama abinci sena zuba ma kowace ita da yaranta, amma idan sune suka dafa abincin dazasu bani ko zainab yayi mata kadan,

Tun mijina baya maganar saurin karewar abinci har yafara, sede inbashi hakuri,dayake mijina mutum ne me hakuri haka ze kara kawo mani, nice share tsakar gidan nan, wanke bandaki,

Idan suka tashi rancen kudi agurina suke karba, idan aka tashi maido mani da 20, 50 haka za,a biyani, wani lokacinma rabi ake bani ace inyi hakuri, nikuma dan kawai insamu fuska agurinsu yasa nake bauta masu,

Kuma hakan be hana surika zagina, ga yaransu basuda kunya, kinsan idan akace mutum yazo cikin mutane 2 shine na 3 dole ya kwantar da kai, in bahaka ba, sede kulluma yayita zama shikadai.

Tun ina hakuri dasu, har nafara gajiya, wlh saboda su, nadena amfani da rishow, sede da gawayi, aikuwa wata rana yaron Laure yaduki Zainab, wai ni naga munzama daya shine nakamasu na dan dokesu nace sudena fada.

Kawai Laure da Laraba suna fitowa Laure ta daukeni da mari, cike da masifa tacemun meyasa zan dakar mata yaro, nace mata fada sukeyi ban idasa rufe baki ba, takaramun wani marin,

Ai bansan lokacin da nima nadauketa da mari ba, na jawota nadaga ta na maka da kasa, dama bawani kiba garesu ba, ganin haka yasa Laraba tayi baya, aiko nahau ruwan cikinta,

Haka nayita jibgarta nakoma kamar me aljanu, dakyar laraba ita dawasu suka kwaceta, akayita bani hakuri sannan naja zainab muka shiga ciki.

Tun daga ranar muka dena magana dasu, haka nasa mijina yazagayemun wancan kitchen din da kikegani da langa langa, nakai rishow na nafara girki aciki,

Komai nawa yana daki, hatta da rishow sezanyi girki nake daukoshi, ina gamawa indauke komai in kai daki, ko bandaki zanje sena kulle kofata, ko Zainab bana bari tsaron falo, waje nake fiddota.

Idan nafito mushiga ciki, bana basu abinci kuma bana zuwa gurinsu, gara inzauna adaki nida Zainab muyi kallo ko,karatu ko,muyi fira, ko yaran gidan nahanata wasa dasu.

Tundaga ranar nasamu lafiya, abincina yafara yimani auki, kuma inci abinda nakeso, domin agaskiya babu abinda mijina yarageni dashi, sede suyita gulma, nikam babu ruwana dasu.

Labiba tayi ajiyar zuciya tace gaskiya nagode dakika fadamun halinsu, kuma ni dama tunda mukashigo naji abinda suka fada kawai naji banyarda dasu ba, hakan yasa nima mijina yace anan zanrika girkina.

Maman Zainab tace shikenan kin huta, ai zaman gidan haya beyiba, barema ace irin wannan. Wlh nayi dana sanin ziga mijina, alokacin da aka raba masu gadonsu, to dayake shikadai ne, mahaifiyarshi ta haifa,

Kuma ta rasu, to da babansu yarasu akazo rabon gado, dama gaba daya yaranshi agidan suke zaune suda matansu, su 3, maza, 2 dakinsu daya, se mijina shi kadai,

Alokacin da aka raba gadon, kowa aka yankar mashi bangarenshi, kinsan wace shawara nabama mijina, dan kawai banason muzauna tare da matan yayyanshi?.

Cemashi nayi kawai ya saida masu nashi gadon, akwai wata mata a unguwar sallari, dama mu a Janbulo muke, nace mashi naji tace zata saida gidanta kwanaki, idan suka bashi kudin seya hada da nashi musiya hakan zefi.

Da farko yacemun a,a da kyar nasamu ya amince dayake yanada sonkin kai. Alokacin daya samu babban wansu da maganar, yabashi shawara yayi hakuri yazauna, ba,ason saida gidan gado.

Amma yace mashi shide kawai saidawa zeyi, ganin yaki yarda haka suka hada kudi shida kaninshi suka biya suka anshi kasonshi. Haka mukaje muka sami matar, setace ai bayanzu zata saida ba, sede idan munaso zamu siya mufara zaman haya na shekara 1.

Idan yaso daga baya seta saida mana da farko yace beyarda ba, haka nayita lallashin shi harya yarda. Haka muka fara zama agidanta, sauran kudin gadonshi muka rika cin dadi, da haka har suka kare.

Alokacin da muka cika shekara 1 tace idan zamu siya to mubata kudin domin tanaso tabar unguwar, anan muka fara zare ido domin ko kudin dazamu kara karbar haya bamu dasu bare na sayan gida.

Hakuri muka fara bata tabari musamu kudi amma tace batasan maganar ba, alokacin kuma wani mutum yazo ze siya, shine tace tabamu wata 1 musami gurin zama.

Kuka mijina yasakamun, yana fadin na cuceshi, hakuri nayita bashi, nace mu koma gurin yan uwanshi nasan zasu bamu gurin zama. Dayake mijina yanada zuciya yace wlh bazejeba, koda ace dakinsu daya, kuwa.

Haka yayita buga buga har yasamu wannan gidan muka dawo, kinji dalilin dayasa muke zaune agidan nan. Kuka sosai Labiba takeyi, jin labarin maman Zainab. Share hawayenta tayi tace lallai kunga rayuwa, amma inaji bakiga komai ba kan.......

Gyaran murya tare da sallamar Abbas ce tasata yin shiru, saurin tashi Maman Zainab tayi tana fadin kinga fira tasa bamuji kiran sallah ba. Gaisheda Abbas tayi tace Labiba seda safe ko.

Bayan tafita Abbas yazauna akusa da Labiba wadda haryanzu kuka takeyi, jawota yayi, yace haba Labiba ya isa haka, kuma na dade atsaye, naji firanku, abinda nakeso dake,

Ki koyi boye sirrinki, duk yanda kike da mutum kada kiga

Please Login or Register in order to submit comment