Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma seda Alh, Abbah yashirya walima, mutane da yawa suka samu halartar walimar, anci ansha, kowa ya yaba da gidan Abbas Alee, da masu gulma damasu tsegumi duk sun halarci gurin.

Anan Alh, Abbah yayima Abbas kyautar wata mota me tsadar gaske, wasu daga cikin mutane har cewa suke kode asiri Abbas yayima Alh, dan suna ganin kyautar dayake mashi tayi yawa, wanda agurin Alh, yana ganin beyi mashi komai ba, idan akayi la,akari da irin halarcin da Abbas yayi mashi.

Bayan kowa ya watse Alh, dasu Umma suna zaune afalo, Umma se godiya take ma Alh, yace Umma bakomai dannayima Abbas wannan ai bawani abu bane, Allah yakara hada kanmu, tace amin. Abbas kuwa seda yayi kuka, haka Alh, yayi masu sallama yatafi.

Aranar kasa bacci sukayi, saboda tsananin murna, hakan yasa Umma tace kowa yaje yayi alwala suyima Allah godiya abisa sauyin rayuwar dasuka samu. Haka suka raya wannan dare da ibada, Labiba gani take kamar amafarki ne abun yake faruwa, akowace addu,a seta roki Allah yasa kada Abbas yayi mata kishiya.

Nikam nace Allah yasa LABIBA

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 65 🔱 70

Zamansu gwanin dadi suna cikin farin ciki, hankalinsu ayanzu akwance yake, acikin sati 2 da dawowarsu gidan harsun murmure.

Labiba da yaronta tubarkallah yaro yayi girma kyanshi se kara fitowa yakeyi, Abbas kuwa duk wanda yasanshi awatannin baya idan yaganshi yanzu baze iya ganeshi ba,

Umma ita kanta jikinta yayi kyau, batada wata damuwa, komai yimata akeyi, Umar kuwa Abbas yabude mashi wani babban shago abakin titi ya zuba mashi kayan provision hakan yasa yadena zuwa kasuwa yakoma zaman shago, shiyasa Umma tace bazata iya zama bata komai ba, shiyasa tafara yin cincin da zobo na roba tana bama Umar yana tafiya dashi.

Zaune Abbas yake shida Auwal a office suna lissafi, kasancewar Alh, Abbah yabama Abbas Auwal dan yace yasan takan aiki kuma sundade tare gashi kuma yacanza hali, zefi jin dadin aiki dashi akan yasamu wani.

Hakan yasa Auwal yadawo office din Abbas shi kuma Saddik ya zauni matsayin Auwal, kuma sosai Abbas yakejin dadin aiki da Auwal, dan yanzu tsakani da Allah yake zaune da kowa.

Kallonshi Abbas yayi yace Auwal ina ganin abar lissafin nan haka, kaje ka kai wadannan kudin bank, idan kadawo anjima akwai wanda yace zezo karbar canjin dala, shine Yaya yahadani dashi, idan kadawo se ahada mashi.

Auwal yace angama megida, murmushi Abbas yayi yace Auwal baka rabuwa da abin dariya, sallama sukaji abakin kofa, hakan yasa Auwal yayi surin rufe jakar kudin datake hannunashi.

Amsa sallamar Abbas yayi yace bismillah shigo, wasu manyan mutane ne suka shigo irin Alhazawan nan, da sauri Abbas yatashi murmushi dauke afuskarshi yace a,a Alhaji Kallah sannunku dazuwa.

Gurin zama yanuna masu yace ga gurin zama, bayan sun zauna yakarasa kusa dasu yamika masu hannu suka gaisa, Auwal ma hannu yabasu suka gaisa se bata fuska yakeyi, dan yasan kosuwaye acikin Wapa.

Bayan Abbas yazauna yace Alh, inafatan lafiya ko? Gyara babbar rigarshi yayi yana murmushi yace eto lafiyar kenan, tunda kaganmu munzo office dinka adede wannan lokacin ai kasan akwai dalili.

Abbas yace haka ne, to meke tafe daku? Wanda aka kira da Alh, Kallah yace agaskiya Abbas bamajin dadin irin wannan canji damuka samu tunbayan hawanka wannan kujera.

Kasuwancinmu banda karyewa babu abinda yakeyi, kasan halin dan kasuwa, akullum munfison ace kaya suna tsada akasuwa bawai karika kokarin sauko dasuba, ayanzu dala tafadi, bama samun komai idan munyi ciniki.

Kullum cikin bacin rai muke, sabanin nakasa damu wadanda akullum suke cikin farin ciki, gsky muna ganin ayi hakuri akara mana koda kaso 20 ne acikin 100, idan akayi hakan muma ante makemu.

Kaga kaima zaka samu, muma musamu, idan kabiye ta talakawa wlh damu da kai bazamu taba samun abinda mukeso ba, kuma kaga wannan kujerar taka lokaci gareta, idan kayi sake babu abinda zaka tara.

Ni kaina dana rike irin matsayinka danayi irin abinda kayi ai da lokacin dana sauka nazama abin dariya agurin mutane, amma gashi haryanzu ina cikin wadan da suke damawa.

Amma gashi ayanzu daga hawanka arzikina yafara sauka, jiya dana duba account dina bakaramin tashin hankali nashiga ba, harseda hawan jinina yakusa tashi.

Nasaba kudi basa yanke mun, hakan yasa nadauki ATM dina nabama Matata, amma jiya dana duba kudina bakaramin fadawa sukayi ba, gaba daya abinda ke ciki baze wuce million 30 ba, jiya ko bacci kasa yinayi, kamata ace 30 million ne a account dina.

Gashi yanzu mutanan danake harka dasu sunfara barina, shiyasa nace muzo gurinka ayi mana wannan temakon, ko ba haka ba Alh, Bukar?.

Wanda aka kira da Alh, Bukar yace kwarai ma kuwa Alh, wannan itace maganar gaskiya, damu akayi zabe, mune muka amince aka zabeka dan haka dole muma ayi mana abinda muke so.

Murmushi Abbas yayi yana kare masu kallo, Auwal Kuwa jiyake kamar yarufe su da duka, babu abinda yafi bata mashi rai kamar wai sune suka tsaya aka zabeshi, kuma su suka zabeshi, wanda yana sane akwatin Alh, Bashir suka sama kuri,arsu.

Abbas yayi gyaran murya yace hakane, naji duk abinda kukace, amma zan maka gyaran magana daya Alh, Bukar, ni babu wani daga cikinku wanda ya tsayamun nasamu wannan matsayi, asalima ni bansanku ba, inba yanzu ba, dan magana ta fatar baki bata taba hada muba.

Garama Alh, Kallah, shi inajin labarinshi, kuma nataba ganinshi so 2 amma akoina zanfito da babbar murya infada cewa Alh, Abbah Hassan Hala shine mutumin dayayi sanadiyar hawana wannan matsayi, dan haka kadena ikirarin kuntsaya mun.

Abu na 2 kuma Alh, kallah naji korafinka, sede ina mamakin mutane irinka, kanada kudi har million 30 amma kake fadin wai baka da kudi, har hawan jininka zetashi, kana cikin katon gida, babbar mota, amma duk da haka kake fadin bakada kudi.

Inaga wanda yakeda iyali sama da mutum 10 agidanshi, be aje ko kwarar masara ba, balle kudi agidanshi, haka kullum yake tashi beda ko kwandala kuma ga nauyin mutane akanshi haka zetashi yafara tunanin abincin karyawa.

Daga nan yafita neman abincin rana, shi beda burin ma yatara agidanshi, burinshi inde zesamu abinda iyalinshi zasuci alokacin zeyima Allah godiya, na tabbatar idan aka bude store dinka na kayan abinci ya ishi wani yabude karamin shago dasu.

Talaka fa? Wanda dayawa azamanin nan sede suyi awo bade su siyo abincin yau da gobe ba, yakake ganin idan muka kara farashin dala, wane hali mutane zasu shiga? Akullum kada kayi tunanin kanka, kayi tunanin nakasa da kai hakan ze kara maka karfin imani.

Mu muna kokarin muga yanda Dala zata kara karyewa domin talakawa su samu saukin rayuwa kana sane da idan dala ta tashi komi seya tashi, amma ku kunaso akarata, so dayawa ba daga sama komai yake tashi ba, wani lokacin laifin yana garemu yan kasuwa.

Kullum burinmu tayaya zamu samu karuwa, babu ruwanmu da sauran bayin Allah, to agaskiya ni bazan iya daukar wannan maganar taku ba, kuma kamar yanda muka zauna da sauran manyanmu aka tsayar da farashin Dala.

Kuma aka kafa doka duk wanda aka samu da laifin yakara akan afarashin da akasa ze fuskanci hukunci, to haryanzu doka tana nan, babu wanda zezo yakawo mana wani bakon al,amari, inafatan kunfahimce ni?

Gaba daya zufa da bacin rai sun gama wanke fuskokinsu, Alh, Bukar ne yayi karfin halin dauko wata jaka dasukazo da ita, share zufa yayi, yace haba Yallabai, ai abun be kai nan ba, muma bamuzo ba, seda muka shirya,

Amma laifinmu ne, kamata yayi mufara baka wannan kafin mufadi bukatarmu, ga wannan bayawa, million 2 ne, asa mai, sauran bayani kuma daga baya zakaga sako insha Allah har gida, dora jakar yayi saman table din Abbas.

Cike da bacin rai Abbas yatashi tare da dukan table din wanda har Auwal seda ya tsorata, dan betaba ganin Abbas cikin bacin rai kamar haka ba, idanuwanshi har kankancewa sukeyi saboda bacin rai.

Cikin bacin rai yace Bukar kutashi kubarmun office daku da cin hancinku, kuma wlh, wannan shine karo na farko kuma na karshe dazakuzo office dina da magana irin wannan, idan kuma bakuji ba, tabbas zakuyi dana sani, zannuna maku waye Abbas Alee.

Cike da bacin rai Alh, kallah yatashi yakalli abokinshi yana huci yace dauko jakar mutafi, kallon Abbas yayi yace kaine, matsiyaci, wanda begaji arziki ba, shiyasa zakayi watsi da kyautarmu.

Murmushi yayi yace kodayake ba laifinka bane, kai sabon shiga ne acikin arziki, domin dama talaka be iya samun guri ba, duka yaushe kafara farfadowa daga talauci?

Ko kamanta in tuna maka, kadauka bamusan komai akanka, ba? Sanin ko kai waye yasa muka hana abaka wannan kujera, domin bama son abama talaka marar arziki yazo yanuna mana halin naku.

Segashi tukafin ayi nisa munfara gani, aini atunanina yanda kasha wahala arayuwarka bazaka taba bari wata dama ta arziki tashigo maka batare dakayi amfani da ita ba.

Ko kamanta ko wata 1 bakayi da mallakar MUHALLINKA ba? Kodayake bazakji ciwon wannan ba, saboda bada guminka ka ginashi ba, kasan duk wani dan halak yakanyi kokari yaga yagina MUHALLINSHI da gumin kanshi.

Hakan zesa aduk lokacin daya kwanta zerika alfahari da abunshi, amma kana gefe anmaka gini ansamaka komai kashiga ta yaya zaka iya alfahari dashi?

Tambayarka nake ka amsamun idan har kasan da gaske abinda na fada badede bane? Wasu zafafan hawayene suka fara zuboma Abbas, kasa yayi da kanshi, murmushin mugunta Alh, kallah yayi dan yasamu abinda yake so, hakan yasa yacigaba.

Idan zaka fadi tsakaninka da Allah, alokacin da aka koreka daga gidan hayarka na karshe, kadawo gidanku, dakin daga gina da guminka, ranar daka fara kwana acikinshi kozaka iya fadamun wane irin farin ciki kayi aranar?

Shin zaka iya hada farin cikin ranar da wanda kayi aranar da ka kwana agidan da babu ko sisinka aciki? Uhm kobaka fadamun ba, nasan bazaka iya hadasu suzama daya ba.

Idan kamanta bara intuna maka, tunda kake arayuwarka baka taba kwanciya a karkashin inuwar data kasance guminka ne, kayi bacci me dadi aciki ba se ranar daka kwana acikin dakin daka gina na gidanku.

Ko kamanta gidanka daka gina dazakayi aure, hakanan kasha wahalar banza amma ko zaman. Yini guda bakayi aciki ba, bare kuma ka kwana aciki?

Uhm Abbas kadena yaudarar kanka, MUHALLI koda kudin haram ka ginashi inde daga aljihunka suka fito, seyafi daraja akan adauki sadaka abaka,nasan zakayi mamakin yanda nasan waye kai ko?

Karka damu, siyasar kenan, munbarka lafiya, duk lokacin daka shirya tafiya damu kofa abude take, asha inuwar gidan SADAKA lafiya, dariya Alh, Bukar yayi yadafa kafadar Abbas yace semunjika, haka suka fita suna dariya.

Zubewa saman kujera Abbas yayi yana wani irin kuka wanda betaba yinshi ba, tunda yazo duniya, ze iya cewa koda mahaifinshi yarasu beyi irinshi ba, hatta da Auwal seda yayi kuka jin irin bakaken maganganun dasuka fadama Abbas, koshi dasuke tare betaba sanin labarin Abbas ba, amma saboda yashiga harkar siyasa yau anzo har office dinshi ana mashi tonon asiri.

Shiru office din yayi, banda sautin kukan Abbas babu abinda akeji, Auwal ne, yagoge kwallanshi yamatso kusa da Abbas yadafashi yace yallabai dan Allah kayi shiru haka nan,

Kada kadamu da irin maganar dasuka fada maka, dama ita siyasa tagaji haka, dole se mutum ya toshe kunnanshi sannan ze iya zama lafiya, kuma maganar gidan da Alh, yabaka dasukeyi karabu dasu,

Bakin ciki kawai sukeyi,da sune aka bama gidan karba zasuyi, kuma ai kafisu, suda suke zaune akarkashin inuwar haram, kaifa? Kyauta aka baka gidan, kuma kowa yasan yazama mallakinka halak malak.

Dago kai Abbas yayi, yashare hawayenshi yana murmushi wanda yafi kuka ciwo, yace a,a Auwal, basuyi karya ba, tabbas farin cikin dana tsinci kaina aranar dana mallaki dakin dana gina agidanmu, yafi wanda na kwana agidan da yaya yabani kyauta,

Bantaba lura da haka ba se ayau da akamun tuni, aranar dana kwana asabon gidana, naji dadi, amma wlh be kai dadin danaji ba, aranar dana kwana adakina. Goge kwallan idonshi yayi yace haka ne Auwal,

Kyan MUHALLI ka ginashi da guminka, sekafi farin ciki da alfahari, sede nayima Allah alkawari ba zan taba bari haram tashigo cikin dukiyata ba,amma naji dadin wannan tuni da Alh, Kallah yayi mun,

Kuma insha Allah zan dauki shawarar daya bani, duk da agurinshi yana gani cin fuska yamun, ni kuma nayi alkawari, inaso kazama sheda, insha Allah nan dawani lokaci zanyi kokarin gina MUHALLI na da gumi na, kuma acikinshi nakeso incigaba da rayuwa, nasan tabbas MUHALLIN daka gina da guminka yafi DARAJA akan wanda kasamu daga sama.

Nasan yaya zeji ba dadi amma zansameshi inmashi bayani, nasan ze fahimceni. Uhm Alh, kallah, inaso kasa aranka wata rana zakaga cin fuskar dakamun alkahirin dazata janyo mun. Dan ayanzu nafika sanin DARAJAR MUHALLI.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 70 🔱 75

Dukar da kanshi Abbas yayi yacigaba da kuka me tsuma rai, Auwal duk tausayin shi yagama kamashi, turo kofar da,akayi ne yasa Auwal saurin kallon kofar,

Alh, Abbah ne yashigo fuskar shi cike da damuwa, harya zauna Abbas besan yashigo ba,seda Auwal ya gaisheshi sannan Abbas yayi saurin dago kanshi.

Hannu yasa yana goge fuskarshi, yana fadin sannu da zuwa Yaya, kai Alh, Abbah yadaga yace sannu Abbas, shiru yayi ya dukar da kanshi.

Alh, yace Abbas kayi hakuri da duk wani abu dayake faruwa akanka, da kuma wanda zefaru nan gaba, dama haka siyasa ta gada, naji duk abinda yafaru,

Tundaga shigowar su Alh, Kallah, alokacin nataho zanzo gurinka naga sun shigo nan, hakan yasa na tsaya abakin kofa, duk abinda yafaru akunnena naji komai,

Alokacin dazasu fito nayi saurin boyewa, sanda suka fito basu san inajinsu ba, Alh, Bukar yace yaji dadin abinda Alh, Kallah yayi maka, dama shiyasa suka saka akayi masu bincike akan rayuwarka,

Domin susami hanyar dazasu daga maka hankali, Alh, kallah yace ka kyaleshi tunda nafara mashi maganar naga tashin hankali da bakin ciki a idonshi, dan haka ta wannan hanyar zamu bullo mashi, da kanshi seya nememu,

Kaga semuci karanmu babu babbaka, dariya suka sa suka wuce, nazo zanshigo senaji kuna magana da Auwal. Karka damu, ni kaina raina bakaramin baci yayi ba, da irin wannan cin fuska da sukayi maka

Amma ka kyalesu, suna ganin kamar sun cimaka fuska, naji dadi sosai da kadauki wannan mataki, dama kuma haka akeso ga duk wani dan halak, kuma namiji me kishin kanshi yayi.

Kuma banaso kasaka wannan abun aranka har kowa yafahimci kana cikin damuwa, hakan zesa suji dadin abinda sukayi, kuma zasu samu damar hanaka aikinka, dan idan har mutum beda kwanciyar hankali to komai nashi yana ja baya ne,

Narokeka kosu Umma da Labiba
kada kabari suji domin suma hankalinsu zetashi musamman Umma kasan ayanzu hankalinta akwance yake, dan haka kamar yanda kake addu,a kacigaba insha Allah makiyanka sede subiyo bayanka.

Maganar gida kuma banaso ka kara tada hankalinka saboda abinda suka fada, nide harga Allah bada wata manufa nabaka wannan fili ba, kuma lokacin da aka fara gini babu wanda yasan nine nake gina maka.

Kai ko yan uwana babu wanda yasan cewar nine nayi maka wannan ginin, kuma ina me tabbatar maka suma basani sukayi ba, sunde san nabaka fili agurin mutane. Amma sunfadi haka ne, kawai dansu kara daga maka hankali,

Kuma naji shawarar daka yanke, Abbas bazan hanaka ba, domin kowa zeso ace ya mallaki MUHALLINSHI da gumin kanshi, idan har yana kishin kanshi, kuma naji dadi daka zamo daya daga cikin irin masu kishi,

Bakomai, wlh raina be baci ba, na fahimceka, kuma ko nine matakin daka dauka shizan dauka, sede inaso kasani, banaso saboda wannan maganar kadaga hankalinka kafara ramewa abanza,

Kasan zafin nema baya kawo samu, kabi ahankali insha Allah zaka mallaki gidanka, wuyar abun ace mutum bayada abunyi, alhamdulillah yanzu kawuce tunanin me tunani, nasan ko ayanzu cikin account dinka za,a samu kudin dazasu saya maka fili, babba har kafara gini menisa,

Dan haka kabari abi komai asannu, kuma ko kagama gininka bayarda kabar gidanka ba, sede kabama Umar shima yayi aure hakanan, sesu zauna agidan, Allah yamana jagora aduk abinda mukasa gaba, kada kabari makiyanka surika gane fushinka afuska,

Kowane irin bacin rai suka saka ka, kayi kokarin dannewa, hakan zesa karika kona ransu. Kallon Auwal yayi yace kaje ka kai kudin bank, idan kadawo se ahada ma wannan mutumin kudinshi, kuma abinda nakeso da kai,

Inaso kasaka ido akansu Alh, Bukar, inaso musami kwakkwarar shedar dazatasa mu fallasa su agaban mutane, kowa yasan halinsu, kaga dakansu zasu daure kansu, zaman Wapa seya gagaresu.

Tashi Auwal yayi yadauki mukullin motar Abbas yatafi, anan Alh, Abbah yayita lallashin Abbas harseda yaga yasaki ranshi, Har Auwal yadawo yana nan, suna gama hadama mutumin kudinshi yakirashi yazo, bayan sungama yayima Abbas da Auwal kyauta me tsoka, dan bature ne mutumin,

Bayan sun gama yayi masu sallama tare da alkawarin zekawoma Abbas sauran abokanshi suma zasu dawo gurinshi dayin canji, sosai Abbas yaji dadi, anan sukayi musayar number, hakan yasashi yamanta da bacin ran dayake ciki, dama kuma shi bame riko bane.

Jafar ne, yake ta sauri yasamu yakaraso kofar gidan mamanshi, dan tun daga nesa yahango dandazon mutane akofar gidansu, hakan yasa yayi saurin karasowa.

Da kyar yasamu yakutsa ciki, mamanshi yagani tayi dammara da mayafi se ruwan bala,i takeyi ita da wata mata, mutane se hakuri suke basu, yana zuwa dayar matar tana kwashe mamanshi da mari.

Besan lokacin daya daga hannu yakai mata naushi afuska ba, nantake tazube asume, gaba daya mutana gurin suka dau salati, ga jini daya fara zuba ta hancinta, ashe shima danta yaiso gurin akan idonshi Jafar ya naushi Babarsa,

Ai kamar walkiya shima yafado cikin filin, anan ya cakumi wuyan Jafar suka fara dambe, hankalin mutane yakoma kansu, nan aka shiga kokarin rabasu, ganin fadan yaki karewa yasa wani mutum yayi waya yakira yan sanda,

Da kyar, aka samu aka rabasu, duk sunjima kansu ciwo, anrikesu sosai amma kowa soyake yakaima dan uwanshi kafa, wasu ne suka dauko ruwa suka rika zubama dayar matar data suma.

Adede lokacin yan sanda suka karaso, nan akayi masu bayani, hakan yasa suka tasa keyar Jafar da abokin fadanshi, da Mamar Jafar, harma da dayar matar, wadda bata dade da farfadowa ba, hancinta duk jini,

Gaba dayansu abayan motar yan sanda ka sasu, Jafar da dayan ansaka masu ankwa suka ja motar, maman Jafar se kuka takeyi, yau gashi adalilin son zuciyarta tajama danta zuwa police station, mutane se magana sukeyi dan wadanda abun yafaru agabansu sun san Mamar Jafar ce bata da gaskiya.

Adede inda ake bada hannu motar dasu Jafar suke ciki ta tsaya, mutane se kallonsu sukeyi, gaba daya kunya tagama kama Jafar, abinda tunda yake arayuwarshi betaba yin fada ba, amma gashi yau shine hada ankwa,

Dukar da kanshi kawai yayi kwalla tana zubar mashi, abokin fadanshi banda harara babu abinda yake aika mashi, dama kuma can bawani shiri sukeyi ba, dan wancan irin yan zafin kan nan ne, kuma Jafar ma ya girmeshi.

Zaune Abbas yake agaban motar Alh, Abbah dan tare suka fito, motar Abbas kuma Auwal ya tukata, tsaye suke suma a inda ake bada hannu, kamar ance Abbas yajuya, karaf idanunshi suka sauka akan fuskar maman Jafar abayan motar yan sanda, kara gyara zama yayi, yana kara kallon motar, kawai yaga Jafar hannunshi daure da ankwa, ga fuskarshi duk jini,

Mamaki da tashin hankali ne suka bayyana afuskar Abbas, kafin yayi magana aka bada hannu, besan lokacin dayace Yaya dan Allah kabi waccan motar yan sandan, Alh, Abbah yayi saurin kallonshi cike da mamaki,

Abbas yace dan Allah Yaya, girgiza kai Alh, Abbah yayi yabi bayansu Jafar,gaba daya hankalin Abbas baya jikinshi, kallon Jafar kawai yakeyi, Alh, Abbah ne, ya kalleshi yace Abbas wai lafiyarka kuwa?

Meya hadaka da motar yan sanda, kasani sebin bayansu nakeyi kuma kai bakamun bayani ba? Kallonshi Abbas yayi yace Yaya wlh wani aminina ne da mahaifiyarshi nagani abayan motar yan sandan kuma ga ankwa ahannun shi, kalli fuskarshi duk jini, rabona dashi mundade seyanzu dana ganshi awannan halin.

Kabari muje idan mundawo zakaji komai agame dashi, Alh, Abbah yace to Allah ya kyauta, haka suka rika bin bayansu, har suka isa bakin station,bayan sunshiga suma su Abbas sukabi bayansu, kai tsaye office din DPO aka yidasu,

Da sallama su Abbas suka shiga, gurin wani dan sanda sukaje, bayani sukayi mashi, yace sujira yafito, bayan minti kadan yafito yace sushiga, atsugunne suka samesu, maman Jafar se kuka takeyi,

Bayan sungama gaisawa da DPO yabasu guri suka zauna, Abbas yace Jafar, ai dasauri Jafar yadago kai ya kalli wanda yakira sunanshi, cike da mamaki yace Abbas, ita kanta Maman Jafar seda tadago kai tabi Abbas da kallo, mamaki dauke akan fuskarta.

Alh, Abbah yace yallabai munzo ne, muji meyafaru da wadannan bayin Allah, muna tafiya muka hadu da yaranka sun kamosu, shine muka biyo muji ba,asi.

DPO yace to nima de yanda kagansu haka aka shigo mun dasu, yanzu ko bayaninsu ba,ayi mani ba kuka shigo.

Kallon dan sandan daya kawosu yayi yace kai muke sauraro. Gyara tsayuwa yayi yace yallabai muma waya aka mana aka fada mana ana fada, shine mukaje, koda mukaje wani yayi mana bayanin wannan, yanuna Jafar, shine yadake waccan matar harya sumar da ita, shine itama danta yakamshi suka fara fada,

Toshine muka daukosu duka muka taho nan dasu, semuji daga bakinsu. DPO yakalli Jafar yace kai kafada mana abinda yake faruwa, da har baka kalli girman wannan matar ba ka iya ware karfinka kamar zakayi fada da sa,anka har ka sumar da ita.

Jafar yayi kasa da kanshi yace wlh yallabai tsautsayi ne, nima zuwana unguwar kenan na hangi mutane kofar gidanmu, dasauri nakarasa gurin, zuwana yayi dede da wannan matar tadaga hannu ta kwashe mamana da mari,

Ni kuma idona yarufe, bansan lokacin dana nausheta ba,shine ta suma, ashe danta yana gurin shine yarufeni da duka muka fara fada. Jijjiga kai DPO yayi yace kai kuma fa? Yace nima zuwana kenan gurin nasamu Jafar yakaima Ummana naushi, agabana naga ta suma shine nima nakai mashi duka.

Murmushi DPO yayi, yace atakaice de kuduka babu wanda yasan abinda yahada fadan, kawai de kowa yashigarma Babarsa? Kai suka daga su duka, DPO yace amma gaskiya kun kyauta, ko nine abinda yakamata inyi kenan, musamman idan akace nine aka sumar da Babata.

Murmushi Alh, Abbah yayi yace habade yallabai, yace emana, ai Uwa batafi Uwa ba ko? Alh, Abbah yace hakane, ammade ayi hakuri muji abinda yahada fadan, kasan mata.

Kallon iyayen DPO yayi yace kowa ta matsa kusa da danta, bayan sun matsa, yace yauwa, ayanzu nagane wadda aka sumar, dan haka zan fara da ita, baiwar Allah meya hadaki fada da waccan matar?

Gyara zama tayi tace yallabai, wannan matar kowa a layinmu yasan halinta, akwaita da karbar bashin mutane, ta dade tana karbar bashin kudi ko kayan amfani agurina, ayanzu haka inabinta dubu biyar, bayan kudin sabulu da omo datake amsa, wanda akalla zasu kai, dubu biyu.

Tun ina hakuri da ita har nagaji, ayau naje gidanta karbar kudina shine tarufeni da masifa, wai ita batada hanyar samun kudin dazata bani, ganin tanamun masifa nace to zan kaita gurin yan sanda, shine taci dammara ta turoni waje tana ta fada,

Nima sena biye mata muka cigaba da rigima, nan mutane suka taru, abinda yafi bani haushi yanda agaban mutane take fadin wai nice naci mata bashi naki biyanta shine kawai na mareta.

Amma wlh banyi niyar fada da ita ba, kowa yasan irin zaman danakeyi da kowa a unguwar nan, DPO yace naji bayaninki, kallon maman jafar yayi yace kefa? Kuka tasaka tace wlh hakane duk abinda tafada babu karya,

Kaichona banzama Uwa tagari ba, Allah yabani yaro nagari, me zuciyar imani, da son temakon wanda bedashi, amma nayi amfani da damar da Allah yabani amatsayina na Uwa na tauyeshi,

Segashi tun lokacin dana hanashi aikata aikin alkhairi nima Allah yajarabceni, gaba daya samun da Jafar yake dashi ada yanzu babu, kunga laifina yashafeshi, Abbas ka gafarta mani, tun daga ranar dana sa Jafar yarabu da kai, nasa aka koreka daga gidan hayar daya kama maku,

Wlh tundaga ranar kome yashigo hannuna baya albarka, shima Jafar haka kasuwancinsa yafara lalacewa, abincin ci seda yafara gagararmu, duk da Allah yabani sirika tagari, amma

Please Login or Register in order to submit comment