Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

narufe idona dole sede Jafar yakawomun kudi inyi girkina,

Tun yana samu akullum har yadena samu, gashi duk abinda nace haka yake kokarin sama mani, duk kokarin dayake akaina be hanani cin bashi ba, wanda bansan menake dasu ba,

Segashi ayau ta sanadiyata yarona yazo gurin yan sanda, kayafemun Jafar, nasan na cutar da kai, kaima Abbas haka, kayafemun, narabaka da abokinka, narabaka da aikinka, gashi tunkafin aje ko ina Allah yanuna mun shine kadai yake iya azurtawa kuma ya talauta,

Ko baka fada ba, nasan baka cikin talauci, dan girman Allah kuyafemun, Talatu kema nasan nacutar dake, kinmun rana daga karshe nayi maki butulci, kuka tasaka, wanda seda tabama kowa tausayi, Abbas da Jafar kuwa tuni suke kuka.

Shiru gurin yayi nawani lokaci, sannan DPO yace tabbas baiwar Allah baki kyauta ba, kinzamo uwa marar tausayin danta, kuma kin zamo mace marar kyautatama makotanki,

Kisani Allah yabama iyaye amanar ,ya,yansu kuma ranar gobe kiyama zetambayesu wane irin riko suka masu, kamar yanda iyaye suke da hakki akan ,ya,yansu, haka ,ya,ya suke da hakki akan iyayensu, be kamata iyaye surika amfani da damar da Allah yabasu ba, suna cutar da ,ya,yansu, musamman iyaye mata.

Ki godema Allah daya barki da ranki harkika samu damar neman afuwa agurin wadanda kika cuta, dan haka yanzu wata dama Allah yakara baki, idan kinso kiyi amfani da ita gurin gyara lahirarki,

Idan kuma kinso zaki iya yin yanda kikaso, sbd haka niyanzu abinda zance, yarage tsakaninku da wannan mata, kibiyata kudinta, sauran kuma idan tayafe shikenan, dama mu aikinmu shine sasanci.

Alh, Abbah yace hakane yallabai, kallon matar yayi yace baiwar Allah nawane kike binta? Matar tace dubu biyar ne, wanda nasan nabata adunkule, sauran kuma kana nane, agaskiya abazan iya fadinsu ba, namanta, tabani dubu 5 din nayafe mata sauran.

Mamn Jafar tasa kuka tace nagode Allah yabiyaki, Alh, Abbah yaciro dubu 10 yabata yace tarike, godiya tayi masa, yakalli yaronta yace kaikuma kayi hkr da abinda akayima mahifiyarka,

Kasan duk da nahalak bazeso yaga anwulakanta mahaifanshi ba, kayi hkr, yace shikenan ya wuce, Jafar yamika mashi hannu suka gaisa, nan DPO yabasu takarda suka cike yasallamesu, Alh, yaciro kudi yabashi suka fito.

Amotar Alh, suka shiga su duka, har kofar gida suka kaisu, anan Abbas yakarbi number Jafar yace mashi zasuyi waya, godiya sosai Jafar yayimasu, Alh, yaciro kudi yabama maman Jafar, shima Abbas yabata, yakuma bama Jafar, hada kukanta tana kara fadin kayafemun Abbas,

Haka suka nufi gida, amota Alh, Abbah ya kalli Abbas, yace agaskiya yau dinnan naji ina matukar son inji labarinka, na dade inaso kabani labarinka, dan nasan dole akwai abubuwan ban tausayi aciki,

Musamman ayau danaji kadan daga tarihinka, Abbas yayi murmushi yace bakomai Yaya insha Allah ayau zakaji labarin rayuwata, Alh, yace yauwa bara inkira gida infada masu bazan dawo da wuri ba.

Labiba tana zaune afalo tana kallo, Ansar da metayata aiki suna zaune akasa tana yimashi wasa, daga kofar falo, sukaji sallamar megadi, Labiba tace yashigo, bayan sun gaisa yace hajiya dama wata matace tace gurinki tazo, shine nace ta tsaya inyi mata iso.

Labiba tace to Baba kace tashigo, yana fita segashi sunshigo tare dasauri Labiba ta tashi tana fadin Maman Zainab, tace na,am momyn Ansar,

Dariya sukayi suka rungume juna, bayan sungama murnan ganin juna, Labiba tasa aka kawo mata lemu da abinci, zama tayi tafaraci,suna gaisawa.

Maman Zainab tace ikon Allah se kallo, naje gidanku akacemun kuntashi, gashi wayata na manta ta agida, Allah yatemakeni nasamu wanda yasan nan, shine yarakoni,

Kobaki fada ba, nasan Allah yakawo maku sauyin rayuwa kamar yanda yakawo mana, tabbas ba karamin farin ciki nayi ba, alokacin dana ganni agaban gidan nan kuma akacemun nakune,

Labiba tace wlh kuwa maman Zainab kinga yanda Allah yakawo mana sauyi cikin kankanin lokaci, koyanzu nakoyi babban darasi arayuwata, ya Lagos ban tambayeki ba muntsaya labari,

Maman zainab tace wlh lafiya lau, ai zuwanmu Lagos bakaramin nasara Baban Zainab yasamu ba, Allah yahadashi da megida nakirki, yau watanmu guda da dawowa,

Kinsan wani abin farin ciki? Tunkafin mudawo Baban Zainab yazo yasaya mana gida akusa da tsohuwar unguwarku, amma mu a gandun sarki muke, wlh bakiga gidan ba, babba gsky babu abinda zamuce sede muyima Allah godiya,

Ayanzu har mota muke da ita, gaskiya arziki kam yazauna mana, saboda karatun Zainab yasa muka dawo nan, dan Babanta yace yafison tayi karatunta anan kano,

Nima kuma nagaji dazama cikin yare, bansan kowa ba, ai gida yafi komai dadi, koba komai zakaga yan uwa da abokan arziki, labiba tace gaskiya kam, ni kaina na kosa kidawo, dan akwai abubuwa dayawa danakeso agurinki.

Dariya maman zainab tayi tace nikaina kina raina, amma insha Allah babu inda zamu kara zuwa, koma zamuje wani guri sede idan Zainab tasamu hutu, yanzu de ba wannan ba, nifa yau nazo acikamun alkawarina,

Wlh har kosawa nayi mudawo, na matsu inji labarinki, musamman danaji kince labarinki yafi nawa. Labiba zatayi magana wayarta tayi kara, tana dauka Abbas yace momyn Ansar gamu nan afalo tare da Yaya,

Akawo mana abinci, tace to yallabai, murmushi maman Zainab tayi tace e lallai nafara ganin canji, dariya Labiba tayi tace ba dole ba, ai naji dadin shawararki,

Baride indawo kisha labari, ammade Baban Zainab zezo daukarki ko? Tace e nama yimashi kwatancen gidan tunda nazo yace yagane, idan mungama zezo yadaukeni, shima yana gurin abokinshi. Dariya Labiba tayi tace to bara indawo kisha labarina da Abbas.

ASALIN LABARIN ABBAS ALEE DA LABIBA.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 75 🔱 80

ASALIN LABARIN ABBAS ALEE DA LABIBA.

Abbas Alee su 2 ne, agurin iyayenshi, shida kaninshi Umar, mahaifiyarsu ita kadaice agurin mahaifinsu, Abbas shine babba, mahaifinsu Mal. Alee bawani arziki gareshi ba, kasuwa yakezuwa yana kasuwanci,

Duk da rashin wadatarshi behana yasa yaranshi makaranta ba, Ummansu Abbas tana sana,ar cikin gida, kasancewarta mace me kirki batada nuna kyashi akan abun hannunta,

Idan har yaranta suna bukatar wani abu na makaranta inde befi karfinta ba, ita take basu, alokacin da Abbas yagama secondary school haka mahaifinshi yasashi gaba suka rika zuwa kasuwa, kafin takardunshi su fito,

Abbas mutum ne, me ladabi da biyayya, gashi da hakuri, da juriya, akullum maganar mahaifinshi daya ce, Abbas aduk lokacin dakasamu kudi kada kabari ka kashesu abanza, kasamu kasayi fili kobaka ginaba wata rana zeyi maka rana,

Kana ganin yanda na dage nagina wannan gidan damuke ciki, nasan bawai yana da girma ba, ciki da falo ne, kawai nasamu na gina se bandaki, haka muka rayu da Ummanku,

Se bayan an haifi Umar ne, naga dakin baze ishemu ba, shine nasamu nayi maku wancan dakin azaure, Abbas shi MUHALLI dakake ganinshi daraja gareshi kafin insamu nawa nasha wahala nida Ummanku,

Hakan yasa lokacin da mahaifina yarasu, aka raba mana gado, dama ni daya ne agurin mahaifiyata, kuma dama dana auri Ummanku agidanmu muka zauna, bayan anraba mana gado sauran yan uwana sukace basu yarda abar gidanmu ba, sede asayar abama kowa kudinshi,

Da mutane sukaga abun ze zama rigima shine aka kaimu gurin megari, bayan anyi bayani masu rabon gado sukace gidan baze tsagu abama kowa ba, se megari yace shikenan ayima gidan kudi shize siya,

Bayan yabada kudi aka raba kowa ya anshi nashi, megari kuma yabamu kwanaki mubar mashi gida, haka nadauki wannan kudin na kama mana haya, sauran kuma nasaro kaya dasu nafara saidawa,

Cikin ikon Allah kasuwan cina yafara yawa, haka narika tara duk wata riba dana samu, bama cin abinci medadi, haka Ummanku tayi hakuri dani, har Allah yasa kudina suka taru nasayi fili,

Ahankali nacigaba da tara kudi, wannan ginin da kake gani, da hannuna na ginashi, akwai wani abokina shine kadai nasan ya temaka mun agurin ginin, aranar dana gama gina gidan nan, aranar aka haifeka,

Bakaramun dadi naji ba, farin cikina yazamo biyu, seda akayi sunanka sannan muka koma sabon gidanmu, acikin yan uwana haryanzu babu wanda ya mallaki gidan kanshi,

Shiyasa aduk sanda na kwanta nakejin wani farin ciki yana rufeni idan natuna wannan gidan nawa ne, da gumina na ginashi, shiyasa nayi alkawarin tsayawa akanku inga nabaku ilimi wanda zaku dogara dashi,

Dan haka Abbas kaga yanzu girma yafara zuwa maka, koyanzu zaka iya yin aure, tunda sa,anninka biyu sunyi aure, shiyasa daka gama makaranta nace murika zuwa kasuwa da kai, nafiso tun daga yanzu kafara tara kudin siyan fili,

Bazanso ace zakayi aure bakada MUHALLI, idan kasamu naka, nasan ko bayan raina zaka iya kula da kaninka, Abbas yace insha Allah Baba zanyi kokari in mallaki gidan kaina,

Wannan labarin daka bani kadai ya isa yazamo darasi akan kowa, fatana Allah yabani ikon samun takarduna, kaga idan nagama karatuna nasamu aiki zantemakeku sosai, murmushi Babanshi yayi yace Abbas kenan,

Allah yatemakeka, amma kasani banaso ka dogara da wannan karatun, nafiso kabada karfi akan kasuwan cinka, dan kasuwanci yamun abinda har in mutu bazan manta ba,

Inda ace nima karatun nayi kaga dole senajira nagama, sannan inzo inyi zaman jiran samun aiki, kafin infara daukar albashi inyasi gida, dan haka koda kasamu shiga makaranta nafiso ka cigaba da kasuwancinka,

Kaga seka hada biyu, Abbas yace shikenan Baba zanyi yadda kace, tundaga ranar Abbas yakara dagewa akasuwa, duk kudin daya samu Babanshi baya karba, asusu yasaya mashi,

Akullum yake zuba kudi aciki, ana cikin hakane wata rana yahadu da LABIBA tafito daga gidan kakarta, tunda Abbas yaganta yaji sonta yashiga zuciyarshi,

Alokacin suna zaune shida abokanshi, Jafar yana kusa dashi, hakan yasa yayi saurin tabo Jafar yace abokina kasan waccan yarinyar? Jafar yakalli inda Abbas yake nuna mashi,

Dariya yayi yace gaskiya ban santa ba, daya daga cikin abokanshi yace ai Labiba ce, bata dade da dawowa nan unguwar ba, agurin kakarta take, Abbas yace Jafar gaskiya inasonta,

Dariya suka saka daya daga cikinsu yace haba Abbas, duka yaushe ka gama secondary da har zaka fara maganar soyayya? Daure fuska Abbas yayi yace amma naga nida Usman shekararmu daya amma shi haryayi aure,

Jafar yace rabu da Buba kasanshi da tsokana, kabari anjima zan rakaka gurinta, bade munsan sunanta ba, kuma munga gidansu ba, murmushi Abbas yayi yace yauwa abokina, dama nasan kai kadai kake goyon bayana,

Aranar Abbas da Jafar sukaje gidansu Labiba, bayn tafito Jafar yayi mata bayanin abinda yake tafe dasu, itama tunda taga Abbas taji ya kwanta mata, babu bata lokaci ta amince mashi,

Sundade kafin suka tafi, tundaga ranar soyayya me karfi tashiga tsakaninsu, abokanshi babu wanda besan suna soyayya ba, kakar Labiba tasan Abbas, kamar yanda Ummanshi tasan labarin Labiba,

Sede koda tafadama Babansu yakira Abbas yace mashi, Abbas naji wani labari agurin Ummanku, bazan hanaka abinda kakeso ba, amma shawara daya zan baka, idan har yarinyar tana sonka, to tayi hakuri kasamu gidan kanka,

Wannan shine babban burina arayuwa, bazan so ace kayi aure bakada MUHALLIN dazaka zauna ba, Abbas nasan ciwon rashin MUHALLI, hakan yasa duk wani wanda zeyi aure nake mashi sha,awar samun MUHALLINSHI,

Wlh gara ace bakada abincin dazakaci, bakada sana,aryi da ace bakada MUHALLI, duk wadan nan abubuwan dana lissafo maka, masu sauki ne, idan kanada MUHALLI koda bara kakeyi kuna samun abinci kasan de akarshe gidanka zaka dawo ka kwanta,

Kuma idan kafita bara dole kasamu wani yabaka, amma idan bakada MUHALLI, babu wanda ze dauki gida yabaka, ko kuma yarika biya maka haya,

Yau ko nine nake biya maka haya wata rana dole ingaji, bare kuma ace wanine wanda baka hada komai dashi ba, sannan idan bakada sana,a hankalinka zefi kwanciya idan katuna babu wanda zezo yace kabiya kudin haya,

Wannan ma bakaramin abu bane, dan haka nide bazance kada kayi aure ba, amma nafiso ka mallaki gidan kanka, idan har kanason yarinyar, nizanje innema maka aurenta, amma da sharadi,

Nafarko seka gama ginin gidanka sannan za,ayi aurenku, kuma idan har kasamu makaranta zaka cigaba dazuwa, idan har kayarda da haka, ni kuma zanje insamu iyayenta muyi magana.

Abbas yasauke ajiyar zuciya yace bakomai Baba na amince, nidama ba ina nufin inyi aure yanzu ba, kawai ina tsoron kada wani wanda yashirya aure yazo yacanza mata ra,ayi, kasan mata sunfison da sunsami saurayi suyi aure.

Murmushi Babanshi yayi yace Abbas shifa rabon mutum baya taba wuceshi, duk abinda kaga mutum yasamu ba wayonshi ko dabararshi bace tasa yasameshi ba,

Idan har Allah yarubuta seka auri Labiba, to kozakayi shekara nawa baka aureta ba, babu wanda ze aureta se kai, dan haka ka kwantar da hankalinka, banaso kasaka wani abu aranka wanda zekawo maka matsala arayuwarka,

Kuma ka dage da addu,a idan Labiba alkhairice agareka Allah yabaka ita, idan kuma babu alkhairi atsakaninku Allah yayi maka canji da mafi alkhairinsa. Abbas yace amin Baba,kuma naji dadin wannan shawara,

Insha Allah zandage gurin ganin na mallaki muhallina na kaina, Babanshi yace Allah yasa, anjima zamuje gidansu nida abokina semuyi magana, Abbas yace ai agidan kakarta take dazama,

Babanshi yace to idan munje setayi mana bayanin inda zamuje, sosai Abbas yaji dadin maganar Babansu,

Bayan magriba sukaje gidansu Labiba, dayake Labiba tafadama kakarta, hakan yasa ta aika aka kirawo kawun Labiba, koda sukazo sun sameshi,

Bayan sungama gaisawa sukayi bayanin abinda yake tafe dasu, kawun Labiba yace ai babu damuwa, tunda yara suna son junansu, mu namu addu,a ce, kuma duk lokacin da yaro yashirya, babu damuwa se adaura auren,

Naji dadin abinda kukace, kuma dama duk wani Uba me kishin danshi, bazezo ace suna zaune agidan haya ba, mutane ne basa ganewa ka mallaki MUHALLINKA Yafi kaje kana biyan kudinka awani guri, Allah yayi mana jagora,

Sukace amin, anan suka bada kudin neman aure, sukayi addu,a sannan suka tafi, da Abbas yasamu labarin abinda yafaru rasa inda zesa kanshi yayi saboda farin ciki,

Tundaga ranar soyayyarsu da shakuwarsu takara yawa, kuma kullum yake zuwa kasuwa, sosai yakara dagewa gurin saka kudi a asusu, ada koya saka seya ciro idan yaji bayada kudi,

Amma ayanzu gara yazauna beda ko sisi daya taba kudin asusunshi, sede yaje Ummanshi tabashi, duk wani kayan kyale kyale ya hakura dasu, shiyasa acikin abokanshi yazamo baya agurin gayu, har tsokanarshi sukeyi, amma baya nuna damuwarshi,

Duk da abun yana damunshi, dan wata rana suna zaune zakaga kowa yana siyan abu sunaci, sede suyi mashi bismillah, sam baya cin abunsu, sede idan Jafar ne, Yabashi,

Ganin abun nasu yana kona mashi rai, hakan yasa yarage zuwa majalissarsu, sede su hadu da jafar, ana cikin haka yasamu admission a poly sunbashi fannin kasuwanci,

Bakaramin dadi yaji ba, sede babban tashin hankalinshi yasan dole yataba asusunshi, tunda Babansu bawasu kudi gareshi ba, alokacin da kyarma aka samu rabin kudin registration din, ganin dole seya taba kudin asusunshi yasa yace yafasa karatun.

Babu yanda Babanshi beyi dashi ba, akan yadauka aciki zekara samun wasu, amma yace ya hakura, lokacin da Jafar yaji abinda Abbas yace, hakan yasa yadauko wasu kudinshi dayake tarawa, be bari Mamanshi tasani ba,

Haka yakawo ma Abbas yace yaje yabiya, Abbas yace bazan karba ba, haba Jafar, kai meze hana kabiya ma kanka kaima kayi karatun, nimafa inadasu, kawaide nasan idan natabasu zan iya rasa damar auren Labiba,

Nikuma da inrasa Labiba gara na hakura da karatun, wanda nayi ya isa, zan cigaba da kasuwancina, mutane nawa ne, sukeda kudi ta hanyar kasuwanci,

Wasuma ko aji basu taba shiga ba, dan haka nima na hakura, jafar yace haba Abbas, kasande nine banida ra,ayin wucewa makaranta, shiyasa nabaka kudin, ni nafison kasuwanci,

Kaifa nafi kowa sanin dole ce tasaka kake zuwa kasuwa, tun muna makaranta nasan bakada ra,ayin kasuwanci, kawai kana bin umarnin Baba ne, dan haka ka anshi kudin nan, kuma ni kyauta nabaka, banaso kafada ma kowa nine nacika maka kudin, kawai kace asusunka ka fasa,

Abbas yace Jafar, wlh ada ne, banason kasuwanci, amma yanzu haduwata da labiba inason kasuwanci sosai, domin ta dalilinshi gashi ina tara kudin dazan samu Labiba,

Ayanzu nagane cewar kasuwanci abune me daraja, dan haka kabar kudinka, jafar yace naji, amma bara kaji, wlh, idan har baka anshi kudin nan ba, babu ni babu kai,

Juyawa yayi zetafi, dasauri Abbas yarikoshi yace yi hakuri abokina, naji zan amsa, nagode sosai da kulawarka, tabbas kai abokine nagari, Allah yabani ikon yimaka koda rabin abinda kake munne,

Murmushi Jafar yayi yace amin, rungume juna sukayi, washe gari Jafar ne. Yarakashi sukaje sukayi komai, bakaramin dadi Baban abbas yaji ba,alokacin dasuka fada mashi sungama komai,

Aranar monday Abbas yafara zuwa makaranta, daya dawo da yamma kuma yawuce kasuwa, yana dawowa yanufi gurin abun sonshi.

WACECE LABIBA?

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 80 🔱 85

WACECE LABIBA?

Labiba yar asalin kano ce, ita kadai iyayenta suka haifa, tayi primary da secondary, babu laifi iyayenta suna da rufin asiri, mahaifanta suna sonta sosai,

Duk wani abu najin dadi suna yimata, akusa da gidansu akwai wata kawarta, mesuna Hauwa, tare sukayi karatunsu, komai zasuyi tare sukeyi, kawayene sosai,

A unguwar sallari suke dazama, mahaifinta dan jigawa ne, kasuwanci yakawoshi kano harya hadu da maman Labiba sukayi aure, alokacin Labiba tana aji 3 asecondary school,

Sosai mahaifinta yake kaita gurin yan uwanshi ajigawa, kasancewarshi su 2 mahaifiyarsu ta haifa tarasu, dagashi se kanwarshi, sauran duk ubansu daya,

Kanwarshi agurin haihuwa itama tarasu, hakan yasa yadawo beda wata yar uwa makusanciya, sede yan uba, yana sane da irin bakin cikin dasuke nuna mashi, amma hakan besa ya yanke zumunci dasu ba,

Idan Labiba tasamu hutu, yakan kaita tayi ko sati 2 ne, duk da mamanta bataso amma hakanan take hakuri dan tasan yanda mijinta yakeson yan uwanshi,

Acikin kannanshi mutum daya ne, yabiyoshi kano shima yafara kasuwanci, shine Labiba take kira da Kawu karami,shi beda irin halin sauran yan uwanshi,

Hakan yasa yake zaune da yayanshi lafiya, ahaka yasamu yasayi gidanshi yayi aure anan kano, lokacin da Labiba tayi J,S,C,E tasamu dogon hutu,

Hakan yasa Mahaifinta Alh, Lawal yakaita jigawa gidan yaynshi tayi hutu, alokacin har kuka tayi dan batason zuwa gidanshi, kuma bataso arabata da kawarta Hauwa,tace mashi yabarta taje gidan kakarta acan darmanawa, yace tayi hkr idan tadawo setaje,

Seda tayi sati 2 sannan iyayenta suka shirya zuwa daukota, akan hanyarsu ta zuwa jigawa sukayi hadarin mota, babu wanda yarayu, lokacin da labari yasami yan uwanshi bakaramin tashin hankali suka shigaba,

Labiba kuwa sumanta 3, da kyar aka samu tasamu sauki, anan jigawa akayi zaman makoki, acan kano kuma iyayen mamar Labiba sukayi nasu zaman makokin,

Bayan sati daya da rasuwarsu, Kawu karami yace abashi Labiba yatafi da ita gidanshi, tunda bata gama karatunta ba, sam babban yayansu yace beyarda ba, ayanzu shine yakeda hakkin rike Labiba,

Domin shine babba, makaranta seta cigaba anan, Kakarta ma tace abata ita amma yaki yarda, haka tayi hkr tabarta, Labiba kuwa kuka tasa tace ita tafiya zatayi, dan tasan halin Kawunta,

Sam beda kirki, shida matarshi, hakade yadage dole seda aka barmashi ita, shida kanshi yasa akayi rabon gado, bayan angama yace yaza,ayi da na Labiba? Sauran yan uwanshi sukace ai shine zerike mata,

Tunda shine marikinta, murmushi yayi, aranshi yace nasan za,ayi haka ai, shiyasa nadauki rikonta. Da kanshi yasama mata makarantar gwamnati, bakaramin haushi Labiba taji ba,

Dan kawai babu iyayenta shine za,a maidata makarantar gwamnati, aranar tasha kuka, hakanan ta hakura tafara zuwa makarantar, data dawo gida kuma tayi aiki,

Sam kawunta baya bata kudi, na makaranta ma kudin zuwa kawai yake bata, nadawowa kuma ta dawo akafa, acikin lokaci kadan kamanninta suka canza, haka tacigaba da hakuri, harta shiga aji 5,

Alokacinne tace bazata koma makarantar ba, saboda wahalar datake sha, aranar tafita makaranta kawai ta gudu zuwa kano, koda taje kakarta har kuka tayi ganin yanda jikarta ta koma, hakan yasa tasa aka kira kawunta karami,

Shima ranshi bakaramin baci yayi ba, yacema kakar tarike Labiba zeje yasamu yaynsu kome sukayi ze fada mata.

Alokacin daya samu Yayansu da sauran yan uwanshi da maganar, kowa ranshi yabaci, gani sukeyi yanaso yacima yaynsu fuska, ya goyi bayan bare,

Yayansu yace shikenan, yayarda ze barma kakar Labiba ita, amma da sharadi, babusu babu ita, kome za,ayi mata kada anemesu, kuma maganar gadonta tariga data cinye abunta,

Tundaga kudin makarantarta harzuwa abincin dataci, dasauran kayan daya siya mata, dan haka yanzu babu ko sisi nata agurinshi, Kawu karami har kuka yayi, dayaji bayanin yayansu,

Jiyake inama ace mamansu daya da mahaifin Labiba ba yayansu ba, yanaji yana gani ancinyema yarinya kudinta, goge kwallanshi yayi yace shikenan yaya, amma inaso infada maka kaji tsoron Allah,

Duk wanda yaci kudin maraya wlh wuta yacima cikinshi, kuma insha Allah zamu rike Labiba, domin mahaifinta yayi mani gata, harma daku kanku, amma zaku saka mashi da sharri,

Saukar marin dayaji ne yasashi yin shiru, Yayansu yana huci yace banason sakarci, tsakanin Lawal dani wanene makusancinka, da harzaka rufe ido kana fadamun abinda kaga dama, to kaima bara kaji, kada insake ganin kafarka agidana, kaje kacigaba da zama akano.

Tashi Kawu karami yayi ranshi abace yace naji Yaya, bazaka kara ganina ba, kuma insha Allahu yarinyar da kuka cuta wata rana setazamo abin alfahari acikin al,umma,

Haka yafita, ranshi bace, koda yafada ma Kakar Labiba abinda yafaru itama har kuka tayi, tarokeshi akan yabar mata Labiba, yace shikenan amma dan Allah duk wani abu daya shafeta arika sanar dani,

Nayi alkawarin zan zame mata Uba, kuma maganar makarantar ta zata cigaba, sosai Kakar taji dadi, bayan yatafi Labiba tashigo Kakar tabata labari, itama kuka tasaka,kakar tace bakomai kanshi ya cuta, nide Labiba kobayan rai na, kada kiyarda kawunki, aduk yan uwan mahaifinki babu mesonki kamarshi.

Bayan kwana 2 kawu karami yasamo mata makaranta, haka tacigaba da zuwa, nan suka cigaba da kawancensu da Hauwa,

Labiba tana da hankali, sede tana da saurin yarda da shawarar kawayenta, hakan yasa batada ra,ayin kanta, kome zatayi seta tambayi Hauwa,

Ita ko Hauwa, tana da wayo sosai, shiyasa kome zatayi tafiso itama Labiba tayi irinshi, ahaka har suka gama makaranta, sede Labiba ba ruwanta da kula samari, sabanin Hauwa, ita akwai kula samari,

Duk wani abun bukatar ta samarinta suke mata,ita kuma seta bama Labiba, dan tanaso itama tafara kula samari, Labiba duk abinda tanema kawunta yana mata hakan yasa tasaba da jindadi. Ana cikin hakane kuma suka hadu da Abbas.

CIGABA..........

Sosai Abbas yake gane karatunshi, ga kasuwanci yanayi, alokacin da Babanshi yasashi yabude asusunshi sun sami kudi masu yawa, hakan yasa yaje yayi mashi cinikin wani fili kwata ne acan kasan unguwarsu,

Sede gidanjen gurin duk na talakawa ne, shiyasa fili yake arha agurin, sosai Abbas yaji dadi aranar da akasiya mashi fili, hakan yasa yanufi gidansu Labiba da murnarshi.

Zaune suke afalon baki bayan sungama gaisawa Abbas yace Labibata albishirinki, tace goro, murmushi yayi yace yaude Allah yanufa na mallaki Fili da kudina,

Dariya tayi tace da gaske Abbas? Yace da gaske, kinga ma takardun filin, abinda yaragemun yanzu infara gini, Labiba tace amma gaskiya naji dadi sosai, awace unguwa kasayi filin? Allah de yasa unguwar yan gayu kasamu.

Saurin kallonta yayi yace Labiba kenan, kinsan banida kudin dazan iya siyen fili a unguwar masu kudi, wancan ma dana siya kwata ne, ko rabi be kaiba, kinga yanzu dana kara samun kudi se infara mana gini koda na kasa ne, se inyi mashi shafen siminti,

Bata fuska Labiba tayi tace haba Abbas, wato gidan ma ba,a unguwar yan gayu ba, sannan kuma ginin kasa zakayi mana, haba ai sekasa kawayena suyi mani dariya, nide ina ganin kawai kasaidashi kaje wata unguwar kasiya mana wani.

Wata irin zufa ce yaji tafara zubo mashi, kallonta yayi yace haba Labiba, banzaci wannan maganar daga bakinki ba, tashi tayi tace shikenan, sekayi yanda kakeso,

Saurin rike hannunta yayi yace yihakuri, haba Labibata, daga magana zakiyi fushi, shikenan zanje induba kinji abinso na, murmushi tayi tace tonaji, haka sukayi sallama gaba daya ran Abbas abace yake.


Kai tsaye gidansu Jafar yawuce, harwani jiri yake gani saboda tashin hankali, yasan Labiba tana sonshi, amma akan wannan gidan zata iya rabuwa dashi, dan tasha fada mashi,

Tana son rayuwar yan gayu, tana son gida mekyau, hakan daya tuna bakaramin tashin hankali yaji ba, yana zuwa dakin jafar yasameshi akulle, kasan cewar yana da mukulli hakan yasa yabude, yana shiga ya kwanta,

Wasu zafafan hawayene suka fara zubo mashi, jiyake kamar yarasa Labiba yanzu duk irin wahalar daya sha kafin yatara kudin fili yanzu haka ze hkr

Please Login or Register in order to submit comment