Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

babu labarinta, sauran yaran haryanzu suna gurin Ummarmu.

Innalillahi wa inna ilaihirrajiun shine abinda Alh, Bashir yake maimai tawa, idan kaga kayanshi kamar akwara mashi bokitin ruwa, duk da fankar datake aiki afalon amma bata isar shi.

Kai yadafe yama rasa abin cewa, abokinshi ne, yace hakuri zakayi kasan duk abinda Allah yaso ga mutum seya faru, dan haka kayi hakuri se Allah yasaka maka, shiru yayi ya tuna firar dasukayi da Alh, Bashir ajiya daren dazasu dawo.

( Zaune suke acikin dakin dasuke kwana, Alh, Bashir yace kasan kuwa ayanzu idan nakoma gida ina da kudin dazasu isheni kafin incigaba da kasuwancina? Dariya abokinshi yayi yace lallai Alh, ainasanka da dabara, nasan kayi ajiya acikin account dinka sosai, dariya Alh, Bashir yayi yace wane account? Ai tun sanda nabama Hajiya ATM dina narage saka kudi aciki, adakina nake ajiyarsu wani guri wanda babu wanda ya isa yaganosu seni.)

Ajiyar zuciya yayi alokacin daya gama tuna maganar dasukayi jiya, gaba daya tausayin Alh, Bashir yagama kamashi, duk wani buri nashi Allah yaruguza mashi. Maganar Alh, Bashir ce ta katse mashi tunanin dayakeyi.

Hannun Kasim Alh, Bashir yakama yana kuka yace Kasim tabbas wannan abun daya faru dani hada hakkin marayu dana danne, anyarda dani naci amana dan Allah kuyafemun, amtsayina na kanin mahaifinku ban iya rike amanar Allah ba, nine yakamata inrikeku amma senazamo mecinye maku abinda aka barmaku.

Idan baka mantaba, alokacin da Yaya yarasu, acikin account dina aka turo dukiyarshi datake kasar waje, nine nayi maku canjin kudin da kaina, wlh ko rabin abinda aka turo ban baku ba.

Haka na boye kudin nan acikin dakina segashi nima dayake ba hakkina bane ko kwandala banci ba acikin kudin haka suka kone gaba daya. Kai cona nayi asara natara dukiya da kudin haram duk kadarorina dana tara babu wanda babu kudin haram acikinsu.

Allah na gode maka dabaka bani ikon cin wannan kudi na marayu ba, dan Allah Kasim kuyafemun, yanzu ba se anjima ba zamuje inbama hajiya hakuri, wlh nayi nadamar abinda na aikata, yanzu ni Bashir ina zan dosa?

Kifa kanshi yayi yacigaba. Alh, kabar kuka, inde nine nayafe maka, sede muje gurin yan uwa na ka tambayi gafararsu.

Kuma kadena maganar inda zaka zauna, insha Allah bazamu barka ka tozarta ba,Allah ya yafe mana gaba daya, bara insa akawo maku abinci kuci. Alh, yace a,a muje gurin hajiya nafison innemi yafiyarsu. Tashi sukayi suka nufi gidansu Kasim, dayake Ummansu tana zaune agidan dasuka samu agadonsu.

Gaba daya falon kuka sukeyi dasuka gama jin abinda kanin mahifinsu yayi, yaranshi guda 3 suna jingine ajikinshi suma kukan sukeyi, haka yayita basu hakuri, anan kowa yace ya yafe mashi, godiya yayi masu.

Kasim ne yafara magana kasancewar shine babba, Kallon Ummansu yayi yace Umma inaso zantafi da Alh, gidana tunda akwai wani part seya zauna aciki, yaran kuma yabarsu anan tunda kince zaki rikesu.

Goge kwallan fuskarta tayi tace bakomai, Allah yayi maku albarka, kutafi tare nizan rike yaran, Allah yatayani riko, ita kuma hajiya abinda tayi itama zata hadu da dede ita. Godiya Alh, Bashir yayi tamata yana kuka, haka suka nufi gudan abokinshi suka saukeshi sannan suka wuce gida.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya ginin Abbas ba dare ba rana dayake akwai kudi, katanga daya ce amma part 2 akeyi aciki, komai iri daya, Alh, Abbah yadauka ma aure Abbas zeyi shiyasa bema tsaya tambayarshi ko nawaye dayan part din ba.

Sosai Jafar yake aiki a office din Abbas, suna samun cigaba a kasuwan cinsu, dan danan Jafar ya murje yakara kyau, su Alh, bukar duk sunzama abin tausayi basosai suke samun ciniki yanzu ba,

Damma Abbas yana tura masu mutane, hakan da yayi masu bakaramin dadi sukaji ba, kuma yakara sakasu jin kunyarshi, wani girma suke bashi tamkar shine babbansu.

Su Alh, Bashir har gida suka sami Abbas suka nemi gafararshi, anan yace masu bakomai, kuma zasu iya dawowa kasuwa suci gaba da aikinsu, kudi yadauko yabasu yace sukara jari, godiya sukayi mashi suka nufi gidan Alh, Abbah.

Shima kudi yabasu kuma yace ya yafe masu, da haka suka yanke shawarar su koma kasuwarsu kawai, koma me mutane zasu ce masu gara sunemi halak dinsu hakan zefi masu.

Sosai Labiba take aikama Hauwa da kayayyaki da kudi, duk yanda Hauwa taso tasan gidan Labiba abun ya gagara, hakan yasa ta hakura, dan tasan Abbas ne baya son sucigaba da kawancensu.

Sosai Hauwa ta murmure domin ayanzu tana cin abinda take so, danko girki bata cin nagidan, sunan tana zaune agidanne, amma abangaren mamarta take komai dama ita kadai ta haifa,

Bata fita tayi aikin gida hakan yasa matar babanta tahanata abinci, ko yaranta bata barin suje gurinta, amma ganin irin abubuwan da ake aikoma Hauwa, da irin girkin datakeyi yasa matar babanta tafara saukowa.

Dan wani lokacin idan yaranta sukaje gurin Hauwa idan tayi wani abu medadi tana basu, hakan yasa matar babanta tanemi gafararta kuma ta nemi suyi zaman mutunci.

Ba laifi su Alh, Bashir sunfara samun mutane, kuma suna ciniki, sede a dar dar suke zaune acikin mutanan gurin sunzama tamkar mujiya cikin tsuntsaye, ganin haka ne yasa Abbas yake jansu ajiki da kanshi yake tura masu mutane.

Zaune Abbas yake shida Jafar da Buba, bayan sungama jin bayanin Abbas Jafar yayi dariya yace amma wlh abokina ka iya tunani me kyau, wannan magana taka haka take, babu wani tsayawa shawara ni Jafar na bama Hauwa Buba.

Dariya Abbas yayi yace e lallai sannu da kokari, kabarima shi Angon yayi magana amma kai har kabadashi, kafadar Buba Abbas yadafa yana fadin na Hauwa kayi magana mana.

Hannun Abbas Buba yature yace dan Allah karabani da Hauwa, ni nasan babu wata shiryuwa datayi kawaide dadin bakine zatayi maka saboda tashiga yanayi, amma wannan matar irin abinda tayi maka ai bazan yarda na aureta ba.

Kude sake duba mun wata, ni wlh ko me tallar Awara ce inaso amma banda macen da idonta yabude sosai. Dariya Jafar yayi yace wai kai kana kallon masu talla wadanda basu waye ba ko? Ai inaji macen datake talla tafi macen datayi master's budewar ido.

Kaide kawai kayi addu,ar Allah yabaka tagari, amma maganar wadda idonta be bude ba, ma bata taso ba, karewar budewar ido seka auri karuwa kuma kuzauna lafiya, amma zaka iya auren macen da tunda ta taso agidansu bata fita.

Karatu ma acikin gidansu tayi, islamiya ma cikin gida, idan zata fita seda driver, batasan kowa ba, babu wanda yasanta amma wlh, idan ka aureta tsiyar dazata maka setafi me yawon duniya.

Ai yanzu kawai kadage kada ka cuci wani, kazauna da kowa lafiya, zuciyarka daya akan kowa, kamika al,amuranka agurin Allah, seya zaba maka abinda yafi maka alkhairi,

Amma wayonka, dabarar ka basu isa su zaba maka abinda kakeso ba. Zakaga akwai mutane dayawa suna aikata alfasha da yaran wasu, amma yaransu se su sanya masu matakan tsaro, waisu aganinsu hakan dabara ce.

Idan zanbaka shawara wlh, gara ka auri Hauwa, koba komai ansanta, munsan halinta, kuma duk wanda kaga Allah ya jarabta da irin abinda yasamu Hauwa, amma be tuba ba, to kadauka beda rabo agurin Allah.

Ni nasan yanda Hauwa taga rayuwa, kuma tayi nadama bazata kara barin ta maimaita makamancin kuskuren data aikata abaya ba, amma kaje kayi tunani kuma karoki Allah zabi akan lamarin.

Buba yace hakane, kuma nagode da shawararka, kuma harga Allah nayarda da zabinku, fatana Allah yashige mana gaba. Abbas yace yauwa ko kaifa NA HAUWA. Dariya sukayi.

Babu bata lokaci itama Hauwa ta amince alokacin da Labiba ta kaimata maganar Buba, tabata shawara sosai, kuma ta amince tace idan Babanta yadawo zasuyi maganar. Sallama Labiba tayi mata tawuce gidan Maman Zainab, dama Auwal ne yakawota.

Sosai maman Zainab taji dadin zuwan Labiba,dariya sukayi ganin su duka suna dauke da ciki. Maman Zainab tace Lallai mun dade bamu hadu ba, ashede da wuri za,ayima Ansar kani ko kanwa?.

Zama Labiba tayi tace wlh kuwa, Dadyn Ansar yace yana son yara, maman Zainab tace ai gara, ke dama kika dade baki haihu ba, ai gara kibari kisamu yaranki, domin sune abin alfaharinki.

Ina fatan de ana kula da megidan, yanzu wannan kunyar taki duk kincireta? Dariya Labiba tayi tace kai Maman Zainab, ande cire ta cirewa amma bazata ciru duka ba, kinsan Dadyn Ansar yana son kunya.

Maman Zainab tace e hakane gaskiya kunya tana karama mace kima agurin mijinta, amma kuma kada tayi yawa hartasa ki kasa yimashi abinda ze kasa kallon wasu awaje.

Yanzu ya maganar girkin,inafatan kina bin wadan nan littattafan dana kawo maki? Labiba tace sosai ma, kuma nashiga wani group ma na koyon girki, sosai nake karuwa, duk abinda ban sani ba ina tambaya.

Maman Zainab tace amma kin kyauta, Allah yakara yi mana jagora, anan Labiba tabama Maman Zainab labarin Hauwa, sosai ta tausaya mata.

Maman Zainab tace dama haka rayuwa take duk wanda ya cuci wani shima Allah seya tambayeshi tun aduniya, haka sukayita fira, har lokacin tafiyarta yayi, sukayi sallama ta tafi.

Alh, Bashir ya kalli Kasim yayi murmushi yace haba Kasim wannan magana taka ai bame yuwa bace, niyanzu nafiso inkarasa rayuwata haka yaran da nakedasu Allah yaraya mun su. Kasim yakara kasa da murya yace dan Allah Alh, wlh banyi wannan shawarar ba seda nafara magana da Umma.

Kuma ta amince, kai muke jira, nide gara Umma ta aureka da ace ta auri wani, dan danginta sun dameta da maganar aure, dama kuma tunbayanzu nake wannan tunanin ba, kawaide alokacin nasan bazaka yarda ba.

Banaso kannena suje agolanci wani gida dan Allah. Murmushi Alh, Bashir yayi yace shikenan Allah yasa haka yafi zama alkhairi. Dariya Kasim yayi yace amin, nagode. Dama nayima Kawu magana, shine yace idan ka amince wannan asabar din se a daura auren.

Alh, yace da wuri haka? Kasim yace tome za,a jira, Alh, yace naso insami gida sannan, Kasim yace haba Alh, mufa masu baka gida ne,tunda akwai gidanmu wanda Umma take ciki kawai kuyi zamanku. Alh, yace shikenan babu damuwa Allah yakaimu.

Ayau ne aka daura auren Hauwa da Buba, kuma yayi dede da aurensu Alh, Bashir. Mutane dayawa sunyi mamakin aurenshi da matar yayanshi, masu gulma sunayi, masu addu,a sunayi.

Aranar da dare aka kai Hauwa gidan su Abbas, wanda shine yadauki nauyin yimata kayan daki, Umar kuma yakoma bangaren Ummansu da zama.

Sosai Hauwa ta canza halinta, zamansu da Buba, shima yanajin dadin zama da Hauwa, sanin Abbas bayason tana shige ma Labiba yasa bata cika shiga part dinta ba, sunfi haduwa part din Umma.

Buba tare suke aiki da Umar a provision store din da Abbas ya budema Umar, aiki yake sosai babu ha'inci, kuma yana kokarin tara kudinshi, dan shima yaci burin siyan gida koda nakasa ne.

Zaune suke afalon Umma, Abbas yace Umar yakamata fa kafara tunanin aure,idan ma bakada budurwa to kanema, dan da muntashi zanyi maka aure. Dariya suka sa, Umma tace ai garade kayi mashi aure shima yashigo sahun manya.

Labiba tace yanama da ita, kawai mu ake jira, dariya Umar yayi yatashi yafita, Abbas yace idan nafito zamuyi magana, gara muje mu tambayo maka, kada suga kamar wasa kakeyi. Umma tace Allah yayi zabi mafi alkhairi.

Abbas ne da Labiba suka fita, gidan su Jafar sukaje da yamma, ahanyarsu ta dawowa suna tafiya Labiba cikin sauri tace dan Allah Dadyn Ansar ka tsaya, burki yataka yace waike anfada maki mota kamar keke take? Dariya tayi tace yi hakuri wlh, wata nagani kamar Laraba ta tsohon gidanmu.

Bude motar yayi yace ai seki fito idan kuma ba ita bace duka zansa tamaki, Aikuwa tana karasawa jikin shagon data ganta, sallama tayi hakan yasa Laraba tajuyo domin ganin me sallamar.

Cike da mamaki tace Labiba! Dariya Labiba tayi tace ashede kece dama zamu wuce naganki nace bara induba ko kece, Laraba tace amma wlh, kin kyauta, amsar abinda tazo siya tayi tace muje daga can.

Labiba tace oni Laraba ina kawarki Laure? Laraba tace wlh tana nan, amma yanzu ba gida daya muke ba, duk muntashi daga wannan unguwar, su sun koma Fage, ni kuma muna rimin kebe, yanzu ma da kika ganni anan gidan wata yayata nazo shine nafito zantafi gida na tsaya insayi wani abu anan.

Murmushi Labiba tayi tace Allah sarki ya rayuwa? Laraba tace Alhamdulillah gata nan munata shanta, yanzu kam munsami cigaba sosai dan nida Laure duk da munyi nisa amma muna kasuwanci sosai kuma muke samun alkhairi, sede haryanzu muna gidan haya, amma kuma mukadai ne agidan.

Yanzu kam mazajenmu gaskiya suna zuwa kasuwa sun maida hankali sosai. Kallon Labiba tayi tace ke kam koba,a tambaya ba, kunsami canjin rayuwa ko? Dariya Labiba tayi tace gaskiya sede mu kara godema Allah,

Muna cikin rufin asiri, ai muna haduwa da maman Zainab muna zumunci sosai, itama sunyi gidansu, Laraba tace Allah sarki, wlh naji maku dadi, muma Allah yahore mana, wace unguwa kuke ne?

Labiba tace agaban Darmanawa muke kadan, Laraba tace bade seyanzu zaki haihu ba, dan naga cikinki yayi girma? Labiba tace a,a na biyu ne, wannan akwai Ansar yana gida, muje kugaisa da Dadyn Ansar gashi can.

Laraba tace ashe tare kuke, nide ki gaisheshi wlh kunyarshi nakeji, hannunta Labiba takama tace haba Laraba yau shekara nawa ai komai yawuce, muje dan Allah ai zaman taren kenan.

Fitowa Abbas yayi yana murmushi yace ashede Larabar ce kika gani, risnawa tayi tana gaisheshi, bayan sungama gaisawa Abbas yaciro kudi masu yawa yabata yace ga wannan, ayima yara tsaraba,

Labiba tace Dadyn Ansar Laure ma ta tashifa, amma suna haduwa da Laraba, murmushi yayi yace Allah sarki to ki gaisheta, hannu yasa Aljihu yaciro wasu kudin yabata yace takaima Laure, har kasa ta duka tana godiya,

Haka sukayi mata sallama suka tafi, da ido Laraba tabisu cike da mamakin irin kyan motar dasuke ciki, jinjina kai tayi tace Allah sarki, rayuwa shiyasa kazauna da kowa lafiya yafi, da,ace sharrin da mukayi niyar jama Abbas yayi da shikenan yanzu bazasuyi mani kallon arziki ba, Allah na gode maka daka tsare bawanka.

Ayanzu Wapa tazama abun kwatence a garin kano, mutane basuda tsoron shiga gurin kowa suyi canji, zuwa yanzu Abbas Alee sunanshi ya daukaka agarin kano, mutane dayawa suna yimashi lakabi da mai gaskiya.

Gidan Tv, da Redio babu inda ba,a kiranshi ayi fira dashi kuma yabada shawara, yanzu Costomers dinshi daga ko ina yana dasu, fararan fata da bakake, ayanzu babu sauran zalinci a Wapa.

Abbas ganin ya kammala gininshi yasa aka rushe gidansu na gado akwai wani babban fili akusa dasu, siyenshi yayi yasa aka fara yimashi ginin bene dan yayi alkawarin seya gina gidan haya.

Bakaramin kyau gidan Abbas yayi ba, babu abinda ba,a zuba ba, komai ya kammala, hakan yasa Alh, Abbah yace dole se anyi walima abokanansu na Wapa sunzo domin kowa yasa albarka.

Alh, Abbah shiya dauki nauyin walimar da za,ayi, sosai yakashe kudi domin yanaso walimar ta kayatar, ranar lahadi aka sa walimar su kuma zasu tare asabar.

Abbas ne zaune shida Jafar agaban Mamansu Jafar sungama cin abinci, Abbas ya kalli Mama yace Mama insha Allah ranar asabar nida Jafar zamu tare asabon gidanmu.

Kuma hada ke zamutafi, dan nayi maki dakinki acikin gidansu Jafar. Mamaki ne dauke akan fuskar su Jafar, yama rasa bakin magana, mama kuwa kuka tasaka tana fadin ikon Allah,

Dama akwai ranar dazan zauna akarkashin inuwarka Abbas? Hakika abunda ka raina wata rana shine yake maka amfani, na wulakanta ka saboda MUHALLI, yau gashi kaine zaka bani gidan da ko a mafarki bantaba tunanin samun shiba.


Nagode Allah yayi maka albarka, yabaka abinda kake nema, kuma ina kara rokonka kayafemun akan abubuwan danayi maka. Abbas yace haba Mama babu komai, matsayin uwa kike agurina, Jafar kuwa dan uwanane na jini, babu abinda bazan iya yimaki ba.

Jafar matsowa yayi yakama hannun Abbas, idanunshi suna fitar da kwallah yace, Abbas bani da bakin magana, sede ince......hannu Abbas yasa yarufe mashi baki, yace bana son daga yau ka karamun godiya akan duk wani abu dazanyi maka.

Duk abinda zanyi maka baze kai wanda kamun ba, domin ayanzu ina yimaka ne, kana dashi, nifa? Katemakeni alokacin dabani dashi, dan haka kadena banaso, tashi muje kafada ma maryam, kaga gidanka seka sa yan haya, kema Mama wannan gidan yan haya za,a saka ciki,

Seki rika amsar kudin. Mama tace hakane, Allah yabiyaka, amin, yace suka tashi suka fita.

Alh, Bashir ne da Kasim suka fito daga kasuwar wambai, suna shirin shiga mota sukaji ana fadin bayin Allah kutemaka mani da kudin magani, juyowa sukayi suna kallon wadda tayi maganar,

Kallo daya zaka mata tabaka tausayi,hannunta guda daya ya kumbura ciwo ne, ajiki ga wani tsumma da,aka daure hannun dashi, se wani ruwa yake fita daga jikinshi.

Matar duk ta yamutse gwanin tausayi, kai Alh, Bashir ya girgiza cike da tausayi ya ciro dubu daya yamika mata, dayan hannun tasa zata karba, tsayawa tayi cike da mamaki tace Alh?.

Sake kallonta yayi yace baiwar Allah karbi sadakarki mu wuce, kuka tasaka tace ikon Allah Alh, baka ganeni ba? Sake kallonta yayi yace gaskiya banganeki ba, kallon Kasim tayi ta kira sunanshi tana fadin kaima baka ganeni ba?

Kai Kasim ya girgiza yace gaskiya kam, kuka tasaka tana fadin Alh, matarka ce uwar yaranka, Hajiya Binta ce fa. Saurin cire glass din idonshi yayi yakara kallonta, se alokacin ya ganeta, sede yanayin datake ciki bazaka taba gane taba inba fada tayi ba.

Kasim yace ikon Allah, Hajiya ina kuma kudin naki kika kare abara? Cikin kuka tace dan Allah Alh, kayi hakuri zan fada maku wlh nima banci kudinka ba. Kasim yace Alh, kada mutara mutane kaga kasuwa ce, mudauketa muje gida se ayi maganar acan.

Alh, kasa magana yayi se Kasim ne yabude mata baya tashiga, gaba daya seda kamshin motar yacanza, haka suka shiga suka nufi gida.

Seda Alh, yasa Ummansu Kasim ta nuna mata bandaki tayi wanka tabata kaya tasa sannan taci abinci suka zauna falon, balaifi harta fito datayi wanka.

Yaranta se kallonta sukeyi suna kuka, Alh, yace ke muke saurare. Goge kwalla tayi tace kamar yanda nayi maki sallama Hajiya akan zanje indawo, alokacin kudin account din Alh, da filinshi naje nasayar, kudin kuma na kwashe su duka.

Domin alokacin da gobarar takama ina daki, jin ana ihu wuta yasa. Bandauki komai ba, se jakata da gwala gwalai na, dama takardun suna cikin jakata.

Haka na hada kudina masu yawan gaske, kuma alokacin banyi tunanin insaka su a account dina ba, gani nake za,a iya rufeshi idan Kasim yagane na gudu, tafiya nayi gidan wata kawata da niyar inkwana acan washe gari inbar garin.

Ashe dana fada mata abinda nayi tayima mutananta waya, cikin dare muna kwance mukaji yan fashi, ba bugu ba zagi haka suka hada komai danazo dashi suka anshe, ko kwandala basu barmun ba.

Itama kudinta da gwal dinta suka ansa, ashe duk cikin shirinsu ne, haka muka kwana muna kuka, washe gari tacemun ita tafiya garinsu zatayi seta kwana 2 zata dawo, dama kuma bata da miji.

Nima haka nafito daniyar indawo, adede gidanmu daya kone, nazo wucewa naga Kasim da mutumin dana saida ma filin suna magana, ko ban tambaya ba nasan maganata sukeyi,

Hakan yasa naji tsoron zuwa gidan, juyawa nayi dasauri na rika tafiya, gashi banda kudi bare in hau adedeta, seda nayi nisa sosai, nazo zan tsallaka titi wani me mashi ya kadeni, ina faduwa kuma ashe akwai wani abayanshi shi kuma yatakamun hannu.

Haka aka kaini asibiti hannun yakare, ga ciwo ajiki, nan sukayi mani dinki ahannun suka mun allurai, sukace idan ciwon ya warke za,a gyaramun hannun, sannan sukace bayan sati indawo akwance dinkin.

Dama wasu ne suka kawoni masu mashin din sun gudu, magungunan da,aka rubutamun suka siyamun, anan suka bani dubu daya sukace inyi kudin mota, godiya na masu suka tafi.

Haka nafito narasa inda zani ga yunwa tana damuna naso intafi garinmu amma ganin kudin bazasu isheni ba, yasa nasayi abinci naci, nace idan nasamu kudin mota se intafi.

Haka nayita gararamba, bana wannan rumfa bana waccan, haka nakoma me bara karfi dayaji, dana fara tara kudin mota se sutafi asiyen magani da abinci, har sati yacika bankoma asibiti ba, haka nayita zama da hannun yana damuna.

Ganin yafara ruwa yasa nasa tsumma na daureshi. Dan Allah Alh, kayafemun, nasan hakkinka ne, yake tambayata, alokacin kana da kudi baka rageni da komai ba, asalima ATM dinka agurina yake, amma segashi nakasa zama inrike yaranmu, daga karshe ma naci amanarka,

Ta hanyar bin mazan banza alokacin da aka kulleka, har cikin gidanka nake kawo maza, yanzu ga karshena nan, kayafemun dan Allah.

Kowa seda ya girgiza dajin abinda Hajiya Binta ta aikata, wai bin maza. Cike da bacin rai Alh, Bashir yace bakomai Hajiya, kanki kika cuta, wlh da ace iyakar satar da kikamun kika tsaya babu abinda ze hana ban maidaki dakinki ba.

Amma wannan babban zunubin da kika dauka bazan iya cigaba da zama dake ba, na sakeki saki 3, sannan kuma nayafe maki abinda kikamun, domin kema bakici kudin ba, kuma dalilin yaran damuke dasu, zan kaiki asibiti, aduba hannunki, bayan kinwarke zan daukeki inmaidake garinku, Zamfara,

Wannan shine iya alfarmar dazan maki, saura kuma yarage keda ubangijinki. Kuka tasaka tana fadin nagode, yaranta ta kalla wadan da suke kuka tace kuma kuyafemun, hajiya nagode da rikon yaran da kikamun, kema kiyafemun.

Seda tabama kowa tausayi, haka Alh, da Kasim suka dauketa suka nufi asibiti, suna zuwa akace ai hannun ya rube dole ayanke shi, kuka tasaka Alh, yace kiyi hakuri hakan ne kadai zesa kisamu sauki idan ba haka ba, zama cikin mutane seya ga gareki, saboda wari.
Tanaji tana gani akayi mata allura aka yanke hannun damtsenta kawai aka bari, dressing akayi mata sannan suka nufi gida ita kuma aka bata gado. (Allah ya kyauta, karshen maci amana kenan).

Ayau ne su Abbas da Jafar suka tare asabon gidansu, Maman Jafar seda tayi kuka dan dadi, Umman Abbas kuwa cewa tayi abarta agidan Autan ta,Hauwa ma seda tayi kuka saboda zasu rabu da Labiba.(Nikam nace Allah yasa kukan iyakan nan ya tsaya).

Hada Maman Zainab cikin masu gyaran gida, sosai tayaba kyan gidan Labiba, iyakar tsaruwa ya tsaru, Abbas kuwa bakinshi ya kasa rufuwa saboda ayau ya mallaki gidanshi da guminshi ba nawani ba.

Washe gari haka aka kafa rumfuna aharabar gidan da kujeru, dan walimar karfe 4: 00 ce, komai na kayan ci da sha an tana da, masu abinci na musamman Alh, Abbah yadauko, kuma sune masu rabawa.

Walima ce wadda ta tara mutane dayawa, dan Alh, Abbah da kanshi yayi gayyata, din kunan dazasu saka shida Abbas da Jafar duk iri daya suka saka, sunyi matukar kyau,

Hatta da gidan Tv seda sukazo walimar, anci ansha, duk wanda yazo yasan an karrama kowa, Abbas har kuka yayi saboda farin ciki, haka aka gama walima kowa yarika zuwa yanama Abbas murna.

Bayan an natsu ne yan jarida suka fara yima Abbas tambaya akan yanda yakeji daya mallaki MUHALLINSHI? Tashi yayi nan mutane suka matso, masu dauka awaya suka fara seta Abbas.

Gyaran murya Abbas yayi tare da farawa da bismillah, godiya yafara yima mutanan dasuka halarci walimar, bayan yagama daya daga cikin yan jaridar yace Alh, Abbas wane irin farin ciki kake jin kanka awannan ranar daka mallaki MUHALLINKA na kanka,
duk da de mun sami labarin ba wannan bane gidan daka fara mallaka kusan ma ince shine na 3?

Murmushi Abbas yayi yace haka ne, wannan shine gida na 3 daya kasance amatsayin mallakina. Hakika ina cikin farin ciki marar misaltuwa. Rubutu yayi bayan yagama yace amma ayau kafi jin farin ciki akan sauran gidajenka.

Tunda wannan gidan shine yafi kowanne gida tunda ance da guminka ka ginashi kasancewar gorin da akace abokan adawarka sun maka? Abbas yace hakane, gidana na farko bantaba jin farinciki ba arayuwata ba kamar ranar da na kammalashi.

Domin shine gidan dana gina da zufata kuma da kudina nasha wahala kamar yanda masu gini sukeyi, na kwaba kasa da hannuna , nayi bulo kuma nadaukeshi akaina najerashi da haka har muka kai tsawon gini.

Agaskiya bazan taba samun farin ciki aduk gidan dazan gina kamar gidana nafarko, amma koyanzu ma ina cikin farin ciki, kuma inama Allah godiya.

Jinjina kai yayi yace Alh, Abbas kozaka iya fada mana dalilin dayasa karabu da gidan daka sha wahala kafin kagama ginashi, kaje kana yawon haya?.

Kai Abbas ya girgiza yace wannan nabarshi amatsayin sirrin rayuwata,kai ya jinjina yace hakane, to wace irin shawara zaka bama mutane agame da muhimmancin MUHALLI?.

goge kwallar data zubo mashi yayi yace hakika babu abinda yafi MUHALLI muhimmanci arayuwar yanzu, inabama duk wani matashi shawara yadage ya mallaki MUHALLINSHI, domin idan kanada MUHALLI duk wata matsala dazata taso maka me sauki ce.

Arayuwa da mutum yabaka kudi gara ya nuna maka hanyar da ake samunsu kaje kasamo aduk inda su, domin zasu iya karewa, amma idan kaine kake

Please Login or Register in order to submit comment