Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayarshi amma akashe, Umma tace muyi hakuri agama sallah kila tsayawa masallaci yayi. Labiba kam tade amsa mata kawai, amma jikinta yana bata akwai abinda yasamu Abbas dinta.

Su Alh, Bashir kuwa ana zuwa aka anshe komai nasu aka sakasu a cell aka kulle, Alh, Bashir se magiya yakema Ogansu akan yabari su sasanta ko nawa ne. Yayi alkawarin zebashi. Amma dayake ogan abokin Alh, Abbah ne, sam yaki amincewa da bukatarsu, haka suka zauna kowa da abinda yake damunsu.

Se bayan isha,i Abbas yadawo dede, alokacin leda 2 ta ruwa takare ajikinshi, yana tashi, Alh, yace sannu Abbas. Kai yadaga, yana kara kallon dakin, ahankali yace Alh, naji sauki mutafi gida, nasan hankalinsu atashe yake ganin bandawoba.

Alh, yace hakane, nima nayi tunanin haka, gashi banida numbernsu, naduba aljihunka kuma banga wayarka ba, kuma banaso intafi inbarka, shiyasa banje nafada masu ba. Amma bari inje gurin likita yazo yaga jikinka semutafi.

Bayan likita yagama dubashi ya rubuta masu magunguna yace zasu iya tafiya, bayan kwana 2 sudawo acire daurinda akayi mashi. Godiya Alh, yayi mashi, suka tafi, seda suka biya ta police station sukayi magana da abokinshi.

Alh, Abbah yace dan Allah kada kabada belinsu, abarsu, zuwa monday da gobe asabar munada zabe, jibi kuma lahadi babu aiki, inaso akoyama sauran mutane darasi, kotu zamushiga dasu ranar monday, nafiso alkali ya yanke masu hukunci, suje suji ya gidan yari yake.

Police din yace badamuwa Alh, koda wani ne, yasani wannan aikin zanyi, bare kuma nakane, gara akaisu kotun hakan zesa mutane dayawa su dauki darasi. Godiya yayi mashi, suka tafi.

Tun amota Abbas yakema Alh, magiyar kada yabari abashi wannan mukami dan gaba daya yagama tsorata. Murmushi Alh, yayi yace Abbas kenan, gashide kana da rikon addini, amma har yanzu ka kasa yarda da kaddara.

Kamanta dan adam mumuni baya taba samun abinda yakeso cikin sauki batare da Allah ya jarabceshi ba? To kaima hakan ne yafaru da kai, kuma tunda kaga Allah be kashe ka ba, to yanaso kayi wannan mulkin, dan haka banaso ka kara cewa bakaso.

Allah shine wanda yake bada mulki ga wanda yaso, kuma inaji ajikina kaine zakayi nasarar samun wannan matsayi, dan haka addu,a itace makaminka, dani gaba daya. Kai Abbas yadaga alamun gamsuwa yace nagode Alh.

Da sallama auka shiga gidansu Abbas, acikin rumfa sukaga su Umma sunyi tagumi, dakagansu zakaga tashin hankali kwance afuskarsu, ai Labiba mantawa tayi da kowa haka ta tashi da gudu idonta na zubar da kwalla ta nufi Abbas, tana zuwa ta rungumeshi.

Kuka tasaka tana kara shigewa jikinshi, gaba daya shikam kunya tagama rufeshi, ga Umma kuma ga Alh, Abbah. Ahankali yayi saurin zareta daga jikinshi, yakama hannunta suka zauna.

Umma kuwa tashi tayi tadauko ma Alh, kujera yazauna, bayan sungama gaisawa cike da damuwa umma takalli Abbas tace bade hadari kayi ba, naga andaure maka kai?.

Alh, ne yayi gyaran murya yace, umma ba hadari bane, wani tsautsayi ne, yafaru dashi, sede Allah yakareshi abun yazo da sauki. Anan Alh, yafada masu duk abinda yafaru.

Salati Umma tafarayi, tana kuka, Labiba ma Kukan takeyi, Umma tace Oh ni, shikenan dayanzu mummunan labari yazo mana, lallai mutane yanzu basa tsoron Allah, saboda duniya ka kashe mutum?.

Nikuwa Alh, idan har hakane, kawai ahakura da wannan zabe, kabar masu, suje su cinye, aide duk mulkin dazasu samu aduniya zasu barshi. Banaso inrasa dana, tunda yataso yake gamuwa da tashin hankali kala kala, narokeka kabarshi yacigaba da aikinshi agurinka ku hakura da wannan mulkin dan Allah.

Kuka ne, yaci karfinta tayi shiru, gaba daya jikin Alh, yagama sanyi, Abbas kanshi kuka yakeyi. Alh, yace Umma addu,arki bazata bari wani mugun abu yasamu Abbas ba, bashi kadai ba, harni dana rasa iyayena, nasan addu,arki tana tasiri ajikina. Dan Allah kada ki hana Abbas yakarbi wannan matsayi, wanda bamune zamu bashiba.

Allah shine yazabeshi kuma shine zebamu sa,ar cin wannan zabe, kicigaba dayi mana addu,a insha Allah wata rana se rayuwar Abbas tazama tarihi, duk da bansan komai agame da rayuwarshi ba, amma nasan Abbas yasha wahalar rayuwa.

Kuma nayi alkawarin temaka mashi da dukkanin karfina da dukiyata, tun lokacin dana fara ganin Abbas naji hankalina ya kwanta dashi, hakan yasa nayi saurin jawoshi jikina. Umma idan har kinyarda dani, kinyarda bazan taba barin wani abu yasamu Abbas ba. Idan har kinyarda nima danki ne, ina neman alfarmar kibar Abbas ya karbi wannan matsayi da za,ayi zabenshi gobe, wanda nakesa ran babu wanda za,a bama Chairman na WAPA se Abbas.

Idan har kinyarda da wannan abun dana fada maki, dan Allah ki amince da bukata ta badan na isa ba Umma.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 55 🔱 60

Ajiyar zuciya Umma tasaki, shiru tayi nawani lokaci sannan tadago kai ta kalli Abbas wanda tundazu idonshi yafara zubar kwalla, sakamakon tuno irin wahalar daya sha arayuwarshi ta baya.

Kai ta girgiza tace shikenan Alh, na amince, saboda nasan kai me son Abbas ne, bazaka taba barin wani abu yasameshi ba, mungode da irin kaunar daka nuna mana, Allah yajikan mahaifanka. Kuma Allah yabaku sa,ar wannan zabe da za,ayi gobe.

Murmushi Alh, Abbah yayi yace amin Umma, nagode kwarai, Allah yasaka da alkhairi, kuma insha Allah bazan bari wani abu yasami Abbas ba. Nadaukeshi tamkar kanina uwa daya uba daya, domin a zamanin nan duk mutumin da zerike maka amana bakaramin sonka yakeyi ba.

Wlh Umma ayanzu kodan uwanka baze iya rike maka amanar da Abbas yake rikemun ba, nasha gwada Abbas Umma batare daya saniba, amma bantaba samunshi da ha,inci ba, wanda tunda nafara wannan kasuwancin bantaba haduwa da merikemun amana kamar Abbas ba.

Shiyasa nadauki alkawarin shima zannuna mashi gata kamar yanda akema kowa, insha Allah watarana Abbas seyazama abun kwatance agurin mutane, zakiyi alfahari dashi Umma, fatanmu Allah yayi mana jagora aduk abinda zamusa gaba.

Umma tace amin, tashi yayi yace Abbas kasamu kayi wanka ga magungunanka nan kasha seka kwanta ka huta, Allah yakara sauki. Abbas yace amin nagode, hannu yasa a aljihu yaciro kudi masu yawa ya ajema Umma. Sallama yayi masu yafita, da addu,a tabishi tana masa godiya.

Umma tace sannu Abbas Allah yakara tsarewa, tashi kaje kayi wanka, haka tafita Labiba tahada mashi ruwan wanka yashiga.

Maman Jafar ce zaune tabuga tagumi tana kallon tukunya, tunda safe take jiran Jafar yakawo mata abunda zata dafa amma haryanzu shiru, da kyar tasamu aka samo mata koko na 20 tasha, ajiyar zuciya tayi tace kai wannan wace irin rayuwa ce, ace abincin ci ya gagari dan adam.

Nida ada har zubar dashi nakeyi amma yanzu insamu nazubarwa ma babu. Sallamar Jafar ce ta katse mata zancen zucin datakeyi, amsawa tayi tabishi da kallo, duk yarame yayi baki, zama yayi daga gefenta yana fadin Mama sannu da hutawa.

Bayan sungama gaisawa yace Kinjini shiru ko mama? Tace wlh kuwa Jafar tun safe kokon 20 ne kawai acikina, saukina ma daya banida yara da har bansan yanda zanyi da kaina ba. Jafar yace wlh Mama abubuwanne se ahankali, Allah ma yasoni Ummansu Abdul tana sana,a da bansan inda zansa kaina ba.

Tana iya kokarinta, wani kallo tayi mashi tace e dole kace haka tunda kai kasamu matarka tana bama yaranka abinci kaima kuma kanaci dole kamanta da Uwarka. Idan maganar gaskiya ce nima afitarmun da kwano daya arika kawomun mana.

Jafar yace wlh mama suma bawani abinci suke ciba, nikaina ba kullum nake karyawa ba, haka ma ba,a gida nakecin abincin rana ba, shiyasa nake kokarin kawo maki duk abinda nasamu, tunda naga ita tana sana,a zata iya rike kanta da Abdul.

Ya mutsa fuska tayi tace kwaji dashi, nide bani abinda kasamo inje insiyo abinda zanci. Hannu yasa a aljihu yaciro dari 500 ya mika mata yace gashi mama nasan zata isheki harzuwa gobe, idan yaso jibi se inyo maki cefanan kayan abinci sunfi da arika bada kudin.

Amsa tayi tace a,a ni banason wasu kayan abinci karika kawomun kudin nafi sonsu dan banason dora girki, Jafar yace shikenan zanyima Umman Abdul magana setarika dafawa dake arika kawo maki, dama can haka naso amma kikace kinfi son ki girka da kanki.

Tace ni banason akawomun abinci kabani kudi kawai insayi abinda nakeso, taya zanrika jira se lokacin da tagama abinci sannan za,a kawomun. Kai Jafar ya girgiza yace shikenan Mama duk yanda kikace haka za,ayi, nixan koma, tace to nagode agaida Abdul.

Washe gari haka WAPA tacika da mutane, kowa da jama,arshi, mutanen Alh, Bashir se zare ido sukeyi amma haryanzu basuga megidan nasu yazoba, wasu daga cikinsu tunjiya suke kiranshi amma bata shiga, har gidanshi sunje matanshi sukace bedawo ba.

Alokacin da Alh, Abbah da Abbas suka karaso haka jama,a suka zagayesu, da kyar suka karasa office, wasu manya daga cikin mutanan Alh, Bashir suka shigo, bayan sungaisa suke tambayar Alh, Abbah shiru megidansu bezo ba.

Murmushi Alh, Abbah yayi yace ai bazezo ba, yana police station shida abokinshi, mamaki ne yakamasu sukace kamar ya? Anan Alh, Abbah yaciro wayar shi ya kunna masu vedion da yayi masu jiya.

Kowa seda yayi mamakin ganin abinda Alh, Bashir yayi, babban cikinsu yace ai shikenan yajama kanshi, kuma ni bantaba sanin haka halinshi yake ba, da ban bata lokacina gurin tsayawa zabenshi ba, wayarshi yadauko yace atura mashi domin yanuna ma sauran jama,arsu kowa yasan halin da ake ciki, kuma yayi alkawarin shima yakoma bayan Abbas.


Gaba daya gurin ya yamutse da hayaniyar jama,a kowa da abinda yake fada, hakan yasa mutane dayawa suka dawo bayan Abbas, amma wasu dayake akwai kishi da kiyayya azuciyarsu cewa sukayi gara ayi asarar kuri,arsu dade su zabi Abbas, haka suka watse suka tafi gida.

Bayan komai yalafa wadan da zasuyi zaben suka iso anan aka fara gudanar da zabe, duk da haka akwatin Alh, Bashir seda aka samu wadan da suka saka mashi, sukansu jami,an zaben dasuka samu labarin abinda yayi basuji dadi ba, hakan yasa akama kulle akwatin zabenshi.

Bayan angama zabe agaban mutane aka kirga kuri,a inda Abbas ne yasamu damar lashe zaben Chairman na WAPA, mutane dayawa sunji dadin matsayin da Abbas yasamu, musamman abokan aikinshi, su Auwal da saddik suna daya daga cikin manyan yaranshi dasuka tsaya mashi akan zaben.

Bayan komai ya lafa mutane sukarika yima Abbas murna da fatan alkhairi,Abbas seda yayi kuka ya rungume Alh, Abbah yana mashi godiya, shima seda idanunshi suka kawo kwalla. Haka kowa ya watse suma suka nufi gida shida Abbas.

Koda sukazo shiga kwanar gidansu yaga Alh, ya wuce, kallonshi yayi, Alh, yace wani guri zaka rakani. Murmushi Abbas yayi, gaba da unguwarsu Abbas kadan sukaje, dede wani kwaton fili da aka zagaye aka samashi gate suka tsaya.

Fitowa sukayi Alh, yabude gate din suka shiga, babban filine babu komai cikinsa, shide Abbas kallon gurin kawai yake. Hannu Alh, yasa a aljihu yaciro wata bakar leda, wasu ta kaddu ya fiddo yamika ma Abbas, yace wannan filina ne, halak malak.

Kuma ayau ni Alh, Abbah Hassan Hala na mallaka maka shi halak malak, inaso kazabi irin ginin da kakeso nikuma daga gobe zansa afara zanenshi. Zankira sauran ,yan uwana infada masu suma su zama sheda, harma da hukuma zan sako suzama sheda saboda kasan yanayin rayuwa.

Shiru Abbas yayi yana kallon Alh, idanunshi suna zubar da kwalla. Murmushi Alh, yayi yace kada ka damu Abbas, idan ina raye zanmaka abinda yafi haka. Ka Kosan irin yawan dukiyar dana samu azuwanka office dina? Kasan yawan mutanen dasuka dawo gurina saboda aiki da kai?.

Tabbas haduwata da kai alkhairine, samun irinku aduniya bakaramin abu bane, shiyasa banajin kyashin yimaka duk wani abu na kyautatawa, fatana Allah yakaramana budi. Muje gida kada su Umma suga ka dade.


Rungumeshi Abbas yayi tare da sakin wani irin kuka, yace bansan da wane baki zan gode maka ba Alh, kayimun abinda Uba yake ma danshi, kayimun abinda wani dan Uwa baze iya yima dan uwanshi ba. Tabbas kazama babban jigo arayuwata.

Nasha matukar wahala arayuwata, sanadiyar rasa MUHALLI na danayi, nashiga damuwa sosai, mutane sungujeni aciki hada manyan abokaina, nayi yawon gidan haya wanda daga karshe seda aka kusa jamani sharrin Zina, Allah yakareni.

Nafitar da ran zankara mallakar MUHALLI nawa na kaina, amma gashi alokaci guda Allah cikin ikonshi yasake mallaka mun MUHALLI. Babu abinda zance maka sede fatan alkahiri arayuwarka, Allah ya tsareka da iyalanka aduk inda kake, yakara daukaka ka, yasa kafi haka.

Alh, yace amin Abbas, nagode nima da irin amanar da kake rikemun, sede idan bazaka damuba, inason duk lokacin da muka sami nutsuwa, komai yazama dede inaso kabani tarihin rayuwarka. Abbas ya goge kwalla yace nayimaka alkawarin zan baka labarina nida Labiba,Alh yace shikenan nagode, kuma inaso daga yau kadena kirana da Alh, zanfi jin dadi idan ka kirani da YAYA Abbas yace insha Allah Yaya. Murmushi yayi suka nufi gida.

Umma seda tayi kuka saboda farin ciki, Labiba ma haka, addu,a kam Alh, Abbah yashata, haka yabarsu suna ta murna, bayan yatafi Umma ta kalli Abbas tace tabbas babu abinda yakamata musakama Alh, dashi sede murika binshi da addu,a.

Yayi mana abinda babu wani dan uwanka dazeyi maka shi, amma gashi baka hada komai dashi ba, ya zama sanadiyar dauka karka,saboda haka inaso kamar yanda nasanka kada kabari wasu sushiga jikinka su canza maka hali.

Kasan tunda kake baka taba samun matsayi irin wannan ba, kuma mutane da dama suna canza hali alokacin da arziki yazo masu, bazan maka baki ba, amma inaso kayi kokari gurin yin yakida zuciyarka, domin idan kayi yaki da zuciyarka ko shedan yayi kadan ya kusanceka.

Kada kabari rudin dukiya ko zuciya sudebeka kazama butulu ga Alh, ko kuma kazama butulu ga mutanan dasuka zabeka, ka tsaya tsakaninka da Allah kayi aiki, babu ruwanka da karbar cin hanci, nasan akowane guri inde ance akwai shugaba dole za,a saka doka, to wadanda basa san gsky sukan bada cinhanci dan abarsu suyi abinda sukeso.

Nasan aduniya duk me gaskiya shine abin ki agurin wasu mutane, kuma yafi kowa samun makiya, dan haka bawai kasamu cigaba ba, kabari ibadarka tayi baya, ayanzu ne ma yakamata ka kara karfafa ibadarka.

Bacci beganka ba, amma zaka iya kwanciya da wuri kodan kasamu katashi cikin dare kanemi abinda kakeso agurin ubangijinka, kuma nima zantayaka, babu ruwanka da duk wanda zekawo maka maganin tsari, idan yana bada maganin tsari to yafara tsare kanshi.

Babu wani dan adam dayake iya tsare mutum se Allah, kanemi yarda da tsaro agurin Allah seya tsareka. Ka gyara mu,amalarka da ubangijinka seya kareka. Manzan Allah yace kaci moriyar kuruciyarka tunkafin tsufa yazo maka.

Kaci ribar lafiyarka tunkafin mutuwa ta riskeka, narokeka amatsayina na mahaifiyarka, kada kudi yasa kacanza halinka, kada kabari mutane su rabaka da Alh, hakan shine kadai hanyar dazaka iya saka mashi yaji dadi.

Kuka sosai Abbas yakeyi tunda Ummanshi tafara yimashi nasiha, itama seda taji idonta yacika da kwalla, Labiba kam itama kukan takeyi. Abbas yace naji duk abinda kikace Umma, kuma nayi maki alkawarin bazan taba bari wasu su canzamun halayyata ba, addu,arki itace garkuwa arayuwata.

Umma tace naji dadin hakan, Allah yayi maka albarka, yabaka ikon rike wannan amana da,aka baka, yakareka daga sharrin masu sharri, yace amin. Kallon Labiba tayi tace kema Labiba inaso infada maki wani abu.

Nasan baki manta irin abinda kika yima Abbas ba, wanda kowa yayi mamakin barinki danayi kika cigaba da zama da dana, kuma kema kanki kinsan bantaba yimaki magana ba, ko na canza maki fuska, wanda duk wata uwa bazata iya saka ido ta kyale wata tasaka danta cikin irin halin da kika saka Abbas ba.

Nayi haka ne, saboda shima ya dandana yaji yakuma gane da kanshi bakomai ne akema mace ba, nasan alokacin konayi mashi magana baze saurareni ba, saboda inasane da duk irin maganganun da mutane harma da abokanshi sukeyi mashi akanki amma yaki amincewa harseda yabi gurguwar shawararki, wadda daga karshe babu inda ta kaiku.

Kuma alokacin na kyaleki ne, saboda banason inzama kamar sauran iyaye mata dasuke tauye hakkin ,ya,yansu, kuma banaso nazama sanadiyar rushewar farin cikin dana, nasan kuna son junanku, alokacin dana rabaku nasan nashiga hakkinku, kuma kila dayanzu wannan babban rabon yazama ajalina.

Tunda Allah yarubuta rabo atsakaninku, hakan yasa nadanne zuciyata na hakura nabarku, dannasan koma menene tare zakusha duk wata wahala, kuma kece zakifi shiga damuwa, domin ke macece.

Alhamdulillahi yanzu komai yafara zama tarihi, nasan ayanzu kindauki darasi sosai, kuma kingane DARAJAR MUHALLI, koyazu zaki iya bama wasu shawara, kuma azamanku gidan nan yasa na fahimci kema kuruciya da son zuciya tare da biyema shawarar kawaye sune suka jaki harkika aikata abinda kika aikata.

Domin nafahimci kina da halaye masu kyau, kuma kina son mijinki sosai, dan haka ina kara rokonki kada kibari shedan ko wata kawa tazo jikinki ganin mijinki yasamu babban matsayi su saki ki kara canza hali.

Kiyi hakuri da duk halin dakike ciki, baruwanki da kawaye, yanzu duk wadda zatazo jikinki wai kuyi kawance wlh, ba masoyiyarki bace, dan duk wanda ze gwada maka so alokacin daka samu wadata karya yakeyi.

Lokacin da kake cikin wahala alokacin kake bukatar mutane, kizama me dora mijinki akan abu me kyau, kada kiyi amfani da son dayake maki kisashi ya aikata abinda beda kyau, wlh, kinji na rantse maki awannan karon bazan hakura ba, idan har kika sake maimaita kuskuren da kikayi abaya, koda zerasa ranshi idan narabaku sede yarasa.

Amma bazan bari Abbas yakara shiga matsala ba, inafatan kinfahimceni? Goge kwallan idonta tayi tace naji Umma, kuma namaki alkawarin bazaki sake jin makamanci wani abu irin nabaya yafaru tsakanina da Dadyn Ansar ba.

Murmushi Umma tayi tace naji dadi, kuma nagode maki, Allah yayi maki albarka, tace amin Umma.

Haka jama,a suka rika shigowa suna masu murna, harda wadan da suke gulmarsu ada, Umma de kallonsu kawai takeyi, dan tasan komai game dasu.

Washe gari haka Alh, Abbah yazo da mezanen gida Abbas yazabi irin fasalin dayakeso ayi mashi, sannan suka wuce, yadauko wasu yan uwanshi 2 suka nufi police station, anan yafada masu yabama Abbas filinshi, agaban abokinshi aka kafa sheda yayi rubutu kowa yasa hannu daga karshe officer yasa hannu. Godiya Alh, yayi mashi yace se sun hadu gobe akotu.

Washe gari aka shiga kotu dasu Alh, Bashir, bayan ankawo shedu kuma suka amsa laifinsu, Alkali ya yanke masu hukuncin daurin shekara 1 agidan yari, da tarar dubu 50 ga Alh, Bashir, sakamakon tashin hankalin dayasaka Abbas. kowa seda yayi Allah wadai da halin Alh, Bashir, shi kanshi kunyar mutane yakeyi, abokinshi se kuka yakeyi yana danasanin biye mashi dayayi, iyalansu se kuka sukeyi, haka aka tasa keyarsu zuwa gidan yari.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 60 🔱 65

Ranar monday Abbas yafara shiga office dinshi dayake cikin Wapa, sosai yake aiki saboda bakaramin aiki yasamu a office din ba, ga mutane dasuke shigo yimashi fatan alkhairi. Sosai Alh, Abbah yake kara nuna mashi abubuwan da suka shige mashi duhu.

Manyan yan Wapa se so suke suhada kai da Abbas, amma shi sam yaki sakar masu fuska, asalima yana karbarsu kamar yanda yake karbar kowa, abubuwan kyautatatawa har gida suna aika mashi dasu. Sukam su Auwal sunzama yan gaban goshi, se godema Allah suke daya shiryesu dayanzu suma sunzama yan kallo.

Sosai Abbas yakawo canje canje a Wapa, mutane marasa karfi sunji dadin wannan canji da Abbas yakawo, ayanzu duk wani canji idan kazo Wapa bakada matsala. Marasa gaskiya sosai abun yafara damunsu.

Haka Abbas yacigaba da gudanar da aikinshi hankali kwance, ta gefe guda kuma Alh, Abbah yana kokari gurin ganin an kammala ginin Abbas, gida ne, babba ake ginawa, part 3 ne kowane part yana dauke da falo da dakuna guda 2 hade da kitchen da toilet acikin kowane daki.

Guda daya ne kawai babu kitchen wanda yakasance bangaren Abbas ne, kuma yana hade da bangaren Labiba kofa ce kawai tarabasu, dayan bangaren kuma na umma ne, yana daga gefen na Labiba, daga gefe guda na gidan kuma boys quarters ne guda 2, ginin yayi kyau sosai, dayake anzagayeshi hakan yasa ba,a ganin irin ginin da akeyi daga waje.

Kwance Abbas yake saman kafar Labiba suna fira, kallonta yayi yace momyn Ansar wlh bakaramin farin ciki nake ba da Allah yasa seda wahalarmu tazo karshe Allah yabamu Ansar.

Sam banason dana yasha irin wahalar dana sha arayuwa,sede inaso inrokeki wata alfarma dan Allah kada kizamo irin mutanan dasuke sangarta yaransu akan dukiya, tabbas nasan ayanzu kudi sunfara zama ajikina, inaso Ansar yataso cikin kulawa da kyakkyawar tarbiya.

Ta yanda bazeyi alfahari ba, bare kuma yasamu damar raina na kasa dashi, kinsan halin da wasu yaran masu kudi suke ciki kenan, shiyasa nace aduk sanda kikayi sallah kirika yima Ansar addu,a hakan zesa Allah ya tsare mana shi.

Kinsan azamanin yanzu tarbiyar da namiji tafi wahala akan ta mace, kuma bawa be isa ya kare wani daga fadawa halaka ba, dole se yahada da addu,a Allah ne kadai yake iya shiryar da bawansa alokacin dayaso.

Dan haka kada kiyi sake da addu,a. Allah yayi mana jagora, tace amin Dadyn Ansar, nide tsorona daya murmushi Abbas yayi yakamo hannunta yace tsoron mekikeji?.

Baki ta turo tace aikaima kasani,dariya yayi yace to dana sani zan tambayeki. Dora kanta tayi saman kanshi sega hawaye suna zuba daga idonta, ai dasauri Abbas yatashi yakamota ya rungumeta yace Labiba meyafaru kuma?

Shiru tayi sema sautin kukan data kara, gaba daya hankalin Abbas yagama tashi, haka yayi ta lallashinta dakyar yasamu tayi shiru, yace dan Allah Labibata kifadamun abinda kikeso.

Share kwllanta tayi cike da shagwaba tace shikenan nasan yanzu zaka kara aure, dan nasan masu kudi basa zama da mace daya. Wata irin dariya Abbas yasaka yana kallonta hada rike ciki, ganin yamaidata abun dariya yasa ta tashi tadauki pillow.

Tashi yayi yana dariya suka fara guje guje, ganin takasa kamashi yasa tafadi tarike kafa tana fadin wayyo kafata, ai dasauri yakaraso gurinta yana fadin muga kafar, hannunshi takama tasa dariya tana fadin wana kama?.

Dariya yayi yajawota suka zube akasa, bayan sungama dariya ya kalleta ahankali yakira sunanta, kallonshi tayi sede bata amsa ba, hannunta yakara matsewa yace Labibata inaso kiyarda da duk wata magana dazan fada maki.

Wlh babu karya acikinta, kuma kinsan koni wanene, kudi ko mulki bazasu sa nacanza daga Abbas Alee dakika sani abaya ba, nasan talauci baya canza mutane kamar yanda kudi yake canzasu.

Ni nakine har abada, kidauka saboda ke kadai Allah yayini, kema haka, babu wata mace dazata burgeni ayanzu domin nasamu zabin raina, kinzauna dani alokacin da bani dashi.

Kinzauna dani alokacin da ake mana korar wulakanci agidan haya, kinyi hakuri dani wanda bakowace mace za,a samu awannan lokacin ba tayi irin abinda kikayi, idan har ban saka maki da alkahiri ba, banida wani amfani aduniya.


Duk wata mace dazata zomun da wata kalma ta so nasan yaudara ce, domin babu wani sauran so azuciyar mutane ayanzu, duk wanda zece yana sona ayanzu tamkar ya furta kalmar kiyayyace agareni. Domin basu soni lokacin danake cikin matsala ba.

Wlh Labiba banida burin zama da mata 2 arayuwata, kin isheni rayuwa, sede idan kincanza hali, hakan kadai zesa nima na karya alkawarin dana maki, inafatan kin fahimceni? Rungumeshi tayi tana murmushi tace insha Allah zaka sameni fiye da yanda kasanni abaya, nasan na cutar da kai, kuma kayi hakuri dani, bazan bari inkara maimaita kuskuren danayi abaya ba, fatana Allah yabani ikon yimaka biyayya akowane hali. Yace amin MATATA.

Bayan wata 4 dafara ginin gidan Abbas, ayaune Allah yasa aka kammala komai na gidan, babu abinda ba,a zuba aciki ba, na more rayuwa, tsayawa fadin kyawun cikin gidan kauyencine, amma iyakar haduwa ya hadu.

Hatta sutura seda Abbas yazuba ma Labiba da Ansar tamkar sabuwar amarya, dayan bangaren shine na Ummanshi itama kaya kala kala yazuba mata, sannan aka daukar mata me aiki, dazata rika yimata hidima, tundaga abinci, shara gyaran daki dasauransu.

Labiba kam cewa tayi me wanke wanke da shara kadai takeso, ita zata rika girkinta, sosai Abbas yaji dadin abinda tafada, kaninshi Umar a daya daga cikin BQ din gidan aka bashi daya, dan Abbas yace rushe tsohon gidansu za,ayi seya koma can kafin shima yayi aure.

Aranar da suka

Please Login or Register in order to submit comment