Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dashi, lokacin da,aka bashi Labiba har dako yake dauka duk dan yasamu yatara kudi masu yawa.

Kai yafara girgizawa, aranshi yace gara inrasa komai da inrasa Labiba, haka yayita sake sakenshi har Jafar yadawo, lokacin dayaga Abbas seda gabanshi yafadi, dan betaba ganinshi cikin irin wannan yanayinba,

Zama yayi yace Abbas lafiyarka kuwa? Tashi zaune yayi yace shikenan Jafar zan rasa Labiba, dan Allah muje asamu wanda zesayi filina Labiba batason shi, kuma kasan akwai manyan masu kudi da suke sonta,

Ni nasan saboda wannan matsalar zata iya hakura dani, kasan babu abinda Labiba takeso kamar hutu.

Jafar yace wai lafiyrka Abbas? Ka nutsu kafada mun abinda yake faruwa, share hawayenshi yayi nan yafada ma Jafar yanda sukayi da Labiba. Tsaki Jafar yaja daya gama jin labarin Abbas.

Cike da takaici, hade da tausayin abokinshi yace haba Abbas, kanka daya kuwa? Wai me kamaida mace ne arayuwarka? Shikenan kadauki son duniya kadorama Labiba,

Inaji ko Umma baka mata irin son dakake ma Labiba, ayanda kasha wahalar tara kudinka ninasan ko Ummace tace kasaida filinka bazaka yarda ba, wlh Abbas inajimaka tsoro akan son da kakema Labiba, duk da nasan itama tana sonka,

Amma bazata taba yimaka irin sadaukarwar da kake kokarin yimata ba,yanzu idan kasayar da filinka, ina zaka samu kudin dazaka cika kasayi wani? Ai ko Baba baze taba barinka karabu da filinka ba,

Shawarar dazan baka, idan har kanason ka mallaki Labiba dole ne kayi abinda zan fada maka, ai dasauri Abbas yace fada inji, zan dauka, inde hakan zesa insamu labiba.

Murmushi Jafar yayi yace lallai Abbas kayi nisa bakajin kira, to da farko de dole sekayi karya, abinda nake nufi ka gwada mata cewar ka saida filin kasayi wani, kuma ahankali zakayi gini me kyau,

Kuma inaso daga yau kada ka kara fada mata halin da kake ciki akan gininka ko kuma wani abu naka, hakan zesa kasamu sauki, idan kagama gininka ai bazata zo tagani ba, asalima se ankawota zata san gidan,

Kaga alokacin tariga tazama taka ko agidan bukka kasata zata zauna, inde tana sonka. Murmushi Abbas yayi yace kai amma nagode, harnaji dadi, shiyasa nake sonka, Allah yabarmu tare,

Yace amin, anjima sekazo muje ninasan mezan cemata, kasan mata se anayi masu karya, dariya Abbas yayi yace hakane, shiyasa takemun yanda taso kasanni ban iya karya ba, yanzu kai ya maganar Maryam?

Dariya Jafar yayi yace lafiya lau, gobe ma su Kawu zasu kai kudin neman aure, kasan nima acikin satin nan zanfara gini, Abbas yace to Allah yate maka, muje ka rakani induboma Umar jarabawarshi ance tafito,

Allah de yasa yasamu abun kirki, dan kasan Umar hankalinshi baya kan karatu yafison kasuwanci, Jafar yace ai da gaskiyarshi, tunda de yasamu na YES da NO ai yawuce komai,

Kaga ko ina ze iya shiga beda damuwa, dama amfanin mutum yasamu ilimi ko kadanne kafin yafara kasuwanci baza,a cuceshi ba, Abbas yace ai shikenan muje mugani idan basuyi kyau ba, kawai seya cigaba da kasuwancinsa.

Seda suka uba mashi, kamar yanda Abbas yayi zato haka suka samu. Daga Hausa se islamic kawai yakeda pass, Abbas yace shikenan Allah yabashi sa,ar kasuwancin.

Daga nan sallar magriba kawai sukayi suka wuce gidansu Labiba, bayan sungama gaisawa Labiba tace Jafar kwana 2 ka boye, dariya yayi yace naje unguwane, dazu nadawo, naje gurin Abbas shine yake fada mun wani abin alkhairi,

Natayashi murna dayace yasayi fili, amma yana fadamun unguwar daya sayi filin raina yabaci, Labiba tace yauwa kaima beyi maka ba ko? Jafar yace wane irin ma yi, haba yama za,ayi inbar Abbas yazauna a unguwar nan,

Aise abokanmu suyi mana dariya, kinsan Allah yanzu ma dande dare yayi da ayau za,a maida masu takardunsu subamu kudinmu,

Nifa tuni nayi mashi cigiyar wani fili a sallari kawaide tafiyar danayi ce tasa ban fada mashi ba, dariya Labiba tayi tace wlh Jafar har kasa naji dadi, ai dama nasan bada kai Abbas yasayi filin ba.

Jafar yace kibarshi kawai, gobe zamu maida masu, tace amma nagode sosai Jafar, yace ba komai bara inbaku guri, kallon Abbas tayi tana murmushi tace harnaji dadi wlh, murmushi yayi, yana tausayin kanshi duk ranar da Labiba tagane gsky.

Bewani dade ba yayi mata sallama suka tafi, ahanya yace amma gaskiya Jafar ka iya karya, dariya yayi yace kaide kazauna komai gaskiya, aikasan akwai karyar da mutum zeyi dan ya ceci kanshi.

Tun daga ranar hankalin Labiba ya kwanta, bakamar da Abbas yace ansayi wani filin, tundaga lokacin tadena yimashi maganar gida, haka sukaci gaba da soyayyarsu, alokacin Abbas yashiga shekarar karshe amakarantarsu,

Kasan cewar shekara 2 ce, ahankali yafara yin bulo na kasa shida Jafar da Umar sukeyi, sosai mahaifinsu yaji dadi ganin zasu fara gini, hakan yasa shima yarika tayasu kwaba kasa,

Hauwa ce da Labiba adaki suna fira, hauwa tace Labiba jiyafa aka kawo kayan sa ranata, Labiba tace kai da gaske? Shine ma baki fadamun ba seda aka kawo, Hauwa tace kiyi hkr wlh abunne yazo akure,

Bafa daniyar sa rana sukazo ba, kawai Abban mu yace asaka rana, kuma kinsan wata guda aka sa, Labiba tace amma naji dadi, wanene wannan me sa,ar? Hauwa tace wlh baya cikin samarina, bamu dade da haduwa ba,

Yanuna mun da gaske yake, amma yacemun a Dambatta yake kasuwanci yakeyi acikin kano, shine ma yakama haya a irin gidan gwamnatin nan yake zaune aciki,

To yace yanada gida a Danbatta, idan can nakeso akaini to, ai kinsanni da son gidan yan gayu, gidan gwamnati fa harda gurin sa dining table, ke bama wannan ba ya za,ayi ina cikin kano inyarda akaini kauye,

Shine nace mashi nafison nan toyanzu anan zaya ajeni. Dariya Labiba tayi tace kai amma kinburgeni, yama za,ayi akaiki kauye,ai ko cikin birni bazamu yarda akaimu unguwar talakawa ba, nan tabata labarin yanda sukayi da Abbas.

Hauwa tace kinmun dede ai yanzu ba soyayya ake ciba, kawai kasamu gidan hutu, Labiba tace a,a wlh kema kinsan ina mutuwar son Abbas, kawaide dan banason zama irin unguwar nan dabazan hanashi ba,

Amma nafison nayi auren soyayya akan na kudi, Hauwa tace tonaji nizan tafi, bikina baza,ayi anko ba, dan lokaci ya kure, idan kinsamu lokaci kishigo muyi sauran shirye shiryen.

Abbas ne zaune abisa kujera suna fira da Ummanshi, kallonta yayi yace wai Umma tundazu naga kamar akwai abinda yake damunki? Ajiyar zuciya tayi tace wlh Abbas tundazu nakejin gabana yana faduwa,

Murmushi yayi yace kila kishiya Baba zeyi maki, murmushi tayi tace tazo mana, kaga se kubar mata dakinku, dariya yasa, zeyi magana yaji ana sallama, amsawa yayi yafita,

Bayan sungama gaisawa, mutumin yace mashi dan sanda ne, anyi mashi kwatancen gidan nan amatsayin gidan Mal, Alee, Abbas yace hakane. Nan ne gidan, kuma nine babban danshi.

Mutumin yace to dama yasamu hadarine. Ahanyarshi tadawowa gidan wata mota tadaki adedetarsu, sede yafi kowa jin ciwo, wanda suke tare dasauki dan shinema yayi mani kwatancen gidan.

Cike da tashin hankali Abbas yace inazuwa, gidan yakoma yasanar ma Ummansu, tashi tayi tace zata bishi, yace kiyi hkr Umma shima amashin yake bari inje inga jikin nasu, ance Umar dasauki nashi, fita yayi, yabarta tana kuka.

Ko kafin suje asibitin har Babansu yacika, suna zuwa Abbas yazube akanshi yana kuka, da kyar aka cireshi daga jikinshi, nan akayi duk wani rubutu, sannan suka bada mota domin akaishi gida, dan wanda ya kadesu guduwa yayi.

Ummansu Abbas bakaramin tashin hankali tashiga ba, nan da nan gida yacika da mutane, dayake magriba batayi ba, hakan yasa aka shiryashi aka kaishi MUHALLINSHI na gaskiya. (Lallai MUHALLI YANADA DARAJA, SHIYASA HATTA GAWA SEDA AKA SAMA MATA MUHALLINTA. ALLAH KABAMU IKON CIKAWA DA IMANI AMIN).

Haka akayi zaman makoki harna kwana 7 kafin kowa ya watse, Abbas duk yafita hayyacinshi, Jafar ne, kadai yake lallashin shi, haka suka cigaba da zaman jimami, har suka hakura Abbas yacigaba da zuwa makarantarshi, Umar kuma yacigaba da zuwa kasuwa,

Ayanzu dole ginin Abbas yaja baya, saboda yanzu shine yake rike da gidansu, damma Ummansu tana sana,a shiyasa ba kullum suke aiki ba, shiyasa ma yakirawo me zanen gida aka fidda mashi ciki da falo se kitchen da bandaki, kasancewar filin ba babba bane hakan yasa gidan beyi wani girma ba, haka suka fara gini shida Umar, dan jafarma yana gurin nashi ginin, dande shi masu aiki yadauka.

Duk ranar da babu makaranta ranar agurin aikin gidan suke
wuni, dan shima Umar aranar baya zuwa kasuwa, abokanshi har magana sukayi mashi akan yasamu masu aiki su gina mashi amma yace beso,

Danshi aganinshi kudin daze biya masu aiki sun isa yayi wani abun dasu, gara yanzu suyi da kansu. Idan lokacin da zesa masu aikin yazo seya biya su karasa mashi.

Gulmar da abokanshi sukeyi ne yasa Jafar yace sudena zama agurinsu tunda basu da kirki, tun daga ranar suka dena zama gurinsu, acikin haka ne akayi bikin Hauwa,

Ranar da aka kaita gidanta shima Abbas yaje gurin Labiba da dare, tunda tafito take fadin gaskiya Abbas unguwarsu Hauwa ta burgeni, kalli gidajensu ba ruwan kowa da wani, kowa yana gidanshi,

Kalli kowace hanya akwai titi, damma bakaga cikin gidan ba, komai acikin gida yake, kai koruwan sama akeyi mutum bazesan anayi ba, dan babu ta inda ruwa zeshigo, basuda tsakar gida, ko rana mutum seya fito nan waje zesan anayinta.

Itakam Hauwa taji dadinta wlh, dama nice nasamu wannan gidan, tunda tafara magana Abbas yake kallonta, seda tagama sannan yace amma kuma gidanshi ne? Kai ta girgiza,

Murmushi yayi yace ai kinfita, tunda ke gidan daza,a sakaki gidan mijinki ne, itafa? Shekara tana cika idan be biya kudin haya ba, za,a iya korarshi daga gidan, bata fuska Labiba tayi tace aide nasan gidan dazaka gina mun baze kai wannan ba,

Kuma dade ace mutum yana irin gidanka ai gara ace haya yakeyi inde gidan hayar yana da kyau nide yafiyemun da,ace mallakin mutum ne, sakin baki Abbas yayi yana kallon Labiba, zuciyarshi yaji tana bugawa dasauri.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 85 🔱 90

Hannu biyu Abbas yasa yadafe kirjinshi, kanshi yaji yasara mashi, da sauri yadafe kanshi, yasamu guri yazauna, hankalin Labiba yatashi ganin yanayin da Abbas yashiga,

Dukawa tayi tana fadin, lafiyade Abbas ko kanka yake ciwo? Kai yadaga mata dan baze iya magana ba,wayarshi yadauko yakamo number Jafar yabata, karba tayi tace kiranshi zanyi? E yace mata,

Kira biyu Jafar yadaga, nan yaji muryan Labiba, tana fadin dan Allah Jafar kazo wlh Abbas beda lafiya ko magana yakasayi, Cike da damuwa Jafar yace kuna ina yanzu? Kwatancen gidan Hauwa tayi mashi, yace gashinan zuwa,

Adedeta yadauka suka nufi unguwar, fifita Labiba take tayima Abbas, se jera mashi sannu takeyi, shikam yama kasa amsawa, zufa kawai take fito mashi,

Adede lokacin Jafar ya iso, shida me adedeta ne suka kama Abbas suka sakashi adedetar, Labiba tace zata bisu, Jafar yace a,a tazauna dare yayi, kome kenan zasuyi waya,

Kuka tasaka mashi ganin zata bata masu lokaci kawai yace me adedeta sutafi, nan suka barta tana kuka, kai tsaye asibiti suka wuce, suna zuwa aka kaishi wani daki, likita aka kira yazo yayi mashi aune aune,

Sannan yasa aka kawo mashi allurai yayi mashi, aka saka mashi karin ruwa, nan take bacci yadaukeshi, likita yacema Jafar suje office,

Bayan yagama rubutunshi, yadago ya kalli Jafar, cire glass din idonshi yayi sannan yace, agaskiya wannan dan uwan naka jininshi ya hau sosai, nayi mamakin abinda yasa jinishi ya hau har haka,

Irin hakanefa zuciyar mutum take bugawa, gaskiya seyayi ahankali, bekamata ba, ace ashekarunshi yana gamuwa da irin wannan lalaurar,

Ajiyar zuciya Jafar yayi yace wlh, Dr, nima bansan abinda yake damunshi ba, ada de nasan yana cikin damuwar mutuwar mahaifinshi, amma daga baya ya hakura,

Amma kawai ina zaune sega wayarshi, ina dagawa naji wadda ze aura tacemun beda lafiya, inaji idan ma akwai wata matsala, to kila tsakaninsu ne, sede zan tambayeshi idan yafarka,

Likita yace to gaskiya kabashi, shawara yayi ahankali, kada yayi wasa da rayuwarshi, inde macece wlh zata kaishi tabaroshi, godiya Jafar yayima Likitan, sannan yabashi wasu magunguna yace yasiya,

Idan yafarka zasu iya tafiya, godiya yayi mashi yafita zuwa siyan magani, daga nan yaje yabiya sauran kudin, yakoma dakin da Abbas yake yazauna yana jiranshi, ganin dare yafarayi, yakira Ummansu Abbas yace ga Abbas nan agidansu

Yasha maganin mura ne kuma bacci yadaukeshi, ze kwana nan, Umman tace ai bakomai, Allah yabashi lafiya, kashe wayar yayi yacigaba da kallon Abbas,yana me kara jin tausayinshi, yasan irin son dayake ma Labiba, yanzu haka wani abun tayi mashi.

Segurin karfe 10 Abbas yafarka, sosai yaji dadin jikinshi, sam babu ciwon kan, nan wata nurse tazo takara dubashi sannan aka sallamesu, ahanya Jafar yafada mashi yanda sukayi da Umma, hakan yasa suka wuce gidansu Jafar,

Seda Abbas yayi wanka Jafar yahada mashi tea ya sha, sannan yasha maganinshi, kwanciya sukayi, anan Jafar yake tambayarshi abinda yafaru.

Ajiyar zuciya Abbas yayi yace Jafar inajin Labiba ita zata zamo ajalina, wlh bantaba jin tashin hankali irin na yau ba, bansan meyasa Labiba takeson ta canza hali ba,

Ni nasan Hauwa ce take zugata, inaji wata rana zan iya rasa Labiba, nide dan Allah katemakeni kada inrasa Labiba, Jafar yace yanzude kafadamun abinda yafaru,

Nan Abbas yabashi labarin abinda yafaru, Jafar seda yazubar da kwalla saboda bakin ciki, jiyake dama shine Abbas, da babu abinda ze hana berabu da Labiba ba, tuna irin Son da Abbas yakema Labiba yasa Jafar yashiga kwantar mashi da hankali,

Sosai yabashi shawara akan yanda zekara hakuri da ita haryasamu ya mallaketa, Jafar yace kasan duk abinda kakeso dole sekayi hakuri kake samunshi,

Kaima idan kayi hakuri wata rana komai ze wuce, Abbas yace shikenan insha Allah daga yanzu data fara mun irin maganar nan kawai zanyi mata sallama, hakan shi zekawo mani mafita, haka suka cigaba da tattaunawa har bacci yadaukesu. Labiba kam aranar kasa bacci tayi, jitake datasan asibitin da sukaje data bisu, hakade tayi hkr, har bacci barawo yadauketa.

Washe gari bayan sungama karyawa Abbas yayi wanka yasha magani, yace ma Jafar zetafi, sallama yayi ma Mamansu Jafar, se harararshi takeyi,

Dazasu fita tace ma Jafar idan ka rakashi kazo inason magana da kai, Jafar yace to, bayan yarakashi yadawo, yana zama tace bangane kwanan da Abbas yazo yayi agidan nan ba?

Nifa banason jaye jaye, Jafar yace wlh Mama beda lafiya ne, yasha magani shine bacci yadaukeshi, kinji abinda yasa ya kwana, amma kiyi hakuri baza,a sakeba, tsaki taja tace shikenan jeka, nibanga abinda yasa ka nacema Abbas ba, inbanda talauci babu komai ajikinshi,

Ga sauran abokanka nan, ka kyalesu kana biyema wancan talakan, tashi jafar yayi yana bata hakuri yafita, sam bayajin dadin yanda Mamanshi takema Abbas, idan shine yaje gidan su Abbas, Ummanshi kamar zata hadiyeshi dan murna, amma shi Mamanshi ta kasa gane irin son dayakema Abbas.

Abbas yana sauka kofar gidansu yaga Labiba zaune abisa dakali tabuga tagumi, idanunta har sun kumbura saboda kuka, dasauri yanufi gurinta har yana tuntube,

Tsugunnawa yayi kusa da ita, yace Labibata meyake faruwa na ganki anan? Saurin dago kai tayi jin muryar Abbas, wani kukan tasaki batasan lokacin data fata jikinshi ba,

Kasancewar atsugunne yake hakan yasa suka fadi kasa, tana samanshi, cikin sauri ya tureta ya mike tsaye hankali tashe, waige waige yafarayi, ajiyar zuciya yayi ganin babu kowa awajen,

Hannu yasa yatada ta tsaye, janta yayi suka shiga zauren gidansu, suna shiga yasaketa, ahankali yakara kiran sunanta, dagowa tayi tana share hawayen idonta,

Labiba kifadamun meyake faruwa naganki da sassafe haka, kuma ma ba gidan Hauwa kika kwana ba, amma naganki anan yanzu, kalli yanda fuskarki ta kumbura, dan Allah kifadamun abinda yake faruwa kinsan fa banda lafiya?

Idanu tazuba mashi, ahankali tace dan Allah Abbas kayi hakuri, ko baka fada ba, nasan maganar dana fada maka jiya ita tayi sanadiyar shigarka awannan halin, wlh nima daga baya nayi dana sanin abinda nafada maka,

Kayi hakuri bazan kara ba, kaji. Murmushi yayi, yana kallonta, yayin da soyayyarta take kara yawa azuciyarshi, hannunta yakamo yace bakomai, Labibata, nayafe maki, son danake maki baze taba barin zuciyata tayi fushi dake ba,

Akullum ni meyafiya ne, agareki, tundaga laifin da kikamun, harma da wanda zakimun nan gaba nayafe maki, fatana Allah yabani ikon mallakarki, murmushi tayi tace amin Abbas dina.

Sakin hannunta yayi yace muje ciki ku gaisa da Umma sekici abinci nasan bakici komai ba, turo baki tayi tace ni gida zantafi, bacci nakeji, jiya kasa bacci nayi, kuma Jafar yace zekirani yafadamun halin da kake amma bekira ba.

Dariya Abbas yayi yace ai naji sauki, kallonshi tayi tace wai meya sameka? Gira yadaga yace bakomai, kawai ciwon Son Labiba ne, yake neman halakani, duka takai mashi tana fadin bawani dan Allah kafadamun, kaga se inkiyaye idan laifin daga gareni ne.

Abinda likita yafadama Jafar shiyafada mata, rau rau tayi da ido tace tokayi hakuri kaji, insha Allah bazan kara bata maka rai ba, murmushi yayi yace Uhm Labiba kenan Allah yasa, tace amin,

Fita sukayi seda yarakata har gida yace zaki koma gidan Hauwa anjima ko? Tace e amma senayi bacci sannan, yace yauwa gara kihuta, banason kina wahalarmun da kanki, tace angama Abbas dina, gida tashige tana dago mashi hannu, murmushi yayi yawuce gida.

Haka sukaci gaba da soyayyarsu, babu abinda yakara hadasu, sosai Labiba take kiyaye duk wani abu dazesa Abbas bacin rai, hakan datakeyi bakaramin rura wutar kaunarta yayi ba, azuciyar Abbas,

Gininshi yayi tsawo dan har ankai linta, rafta kawai za,ayi asa kofofi da windors, ayi shafen siminti se fenti, ba laifi ginin yayi kyau, hakan yasa suka tsaya da ginin dan sungama nasu, saura namasu aiki, kuma seya hada kudin daze biyasu, saukinshi ma yagama siyan kayan aikin.

Sosai yakara dagewa wajen neman kudi, damma yanzu basa zuwa makaranta sosai, dan last semister exams zasuyi, tuni yagama project dinshi, hakan yabashi damar dagewa gurin zuwa kasuwa,

Yanzu ba sosai suke haduwa da jafar ba, dan shima yana zuwa gurin masu gininshi dan nashima saura kawai yarage,saboda nashi akwai kudi, dan yafi Abbas samu sosai, kuma mamanshi tanada kudi,

Idan kaga Abbas zakasan yarame, dan yanzu se yayi kwana 2 beji gurin Labiba ba,ga karatun exam, ga aikin kasuwa, ga rashin bacci, dan baya samun lokacin karatu se yadawo da dare, haka ze bata lokaci yayi karatu, duka baccinshi kadan ne.

Sosai ummanshi take tausayinshi, duk yanda taso yakarbi wasu kudinta datake tarawa akan yabiya masu aiki kin karba yayi, tace Abbas meyasa bakasan kowa yatemakeka akan gininka?

Murmushi yayi yace Umma inaso inyi alfahari da gidana kamar yanda Baba harya rasu yake alfahari da wannan gidan nashi, Baba yafadamun babu kwandalar kowa acikin gidan nan,

Gumin kanshi ne, shiyasa aduk lokacin daya kwanta yakejin dadi, kuma yake alfahari da wannan gidan nashi, to nima haka nakeso, shiyasa bana karbar kudin kowa, ranar nan ma Jafar yabani kudi inkara insayi langa langa amma wlh Umma koda na karba bansaya dasu ba,

Sune nasaya mana kayan abinci, daya tambayeni nasaya nace mashi e dan karyaji haushi, dan haka kema ki aje kudinki, zasumun amfani, idan nazo hada lefen Labiba.

Murmushin Jindadi Umma tayi, tace ina alfahari dakai da Umar, akullum ina godema Allah daya bani ku Allah, yayi maku albarka, kuma yabaku wadanda zasu yimaku abinda kuka mana, Abbas yace amin Umma.

Ayau ne, aka kai kayan saka ranar Labiba gidan Kawunta wani abokin Baban Abbas wanda tare sukaje neman auren Labiba shida Babansu Abbas,Kawunta yaji dadi sosai, yace toyanzu yaro shine yakeda hakkin aji daga bakinshi lokacin daya shirya,

Se asaka rana, anan suka tsaida idan Abbas yafidda rana zasu aikama sauran yan uwa, godiya sukayi, suka masu sallama,

Alokacin da Abbas yasamu labari, agurin Ummanshi yace to Umma kinga jibi zamu fara jarabawa, kuma bankarasa ginin ba, amma acikin week end damun gama jarabawa zasu fara aikin, kuma bazasu tsaya ba, dan natara kudi dayawa.

Seda idon Ummanshi yacika da kwalla tace Allah sarki Abbas, insha Allah wannan wahalar dakasha arayuwarka wata rana seta zamo labari, insha Allah seka daukaka, kalli, yanda ka koma saboda kawai neman na kanka,

Shima kwalla ne suka cika mashi ido yace amin, Umma, Umar ne, yayi sallama bayan sun amsa yashigo,yace Umma sannu da hutawa, tace yauwa sannu auta, zama yayi yace yaya sannu, yace yauwa autan Umma ya gajiya?

Yace lafiya lau, dama kasuwa zantafi, nace ko akwai wani aiki dazan maka? Murmushi Abbas yayi yace a,a bara inshirya mufita tare nima zanleka kasuwar, sallama sukayima Ummansu, tabisu da addu,a.

Kamar wasa ayau Abbas yagama jarabawarshi takarshe, yana fitowa seda yayi kuka, alokacin daya tuna kalaman Babanshi........ Abbas inafatan Allah ya nunamun ranar dazaka gama karatunka, aranar senayi maka sadaka, domin burinka yacika, tunkana yaro kakeson kayi karatu,

Aduk lokacin dana kwanta bacci, idan natuna nasaka amakaranta, nakanji farinciki tunda zancika maka burinka....... wani guri Abbas yasamu, besan lokacin da kuka meyawa yataho mashi ba, sosai yake kewar mahaifinshi awannan rana,

Seda yayi kukanshi yagaji sannan yatafi gida, ahanya ya tsaya yasayi dabino kwano daya sannan yawuce gida, wata makarantar allo dake unguwarsu yaje, bayan sungama gaisawa da malamin yabashi yace ayimashi sadaka ayima Babanshi addu,a.

Umma bakaramin dadi taji ba, alokacin da Abbas yadawo yace mata sungama lafiya, itama kosai tace zatayi na sadaka.

Acikin kwana 4 aka gama rufin gidan Abbas, anyi wearing, ansa kofa da windor, anyi fenti, sosai gidan yayi kyau, abandakin gidan harda broken tyles aka saka, kitchen din har kanta aka buga, sosai Abbas yayi kokari,

Gida dede na talakawa yayi kyau aranar da aka gamashi, Abbas kasa fita yayi aciki, haka yazauna yaketa kuka, saboda yatuna da Babanshi, dayanzu seyafi kowa farin cikin kammala ginin, domin yaci buri akan yaga angama gidan,

Jafar ne, yayi sallama dan yaje gidansu ance baya nan, hakan yasa yataho sabon gidanshi, dasauri yakarasa gurin Abbas, kafadarshi yadafa yace lafiyarka Abbas? Kallonshi yayi tare da goge idonshi yace lafiya lau, Jafar, kawai na tuna da Babane,

Allah beyi yana raye zan gama ginin nan ba. Jafar yace kayi hakuri Abbas, addu,arka Baba yake bukata, tashi muje. Kasan yau ne, zamuje gurin Kawun Labiba atsaida rana,

Tashi yayi yace muje gida inyi wanka idan munyi sallar magriba semuje, jafar yace amma bawani dogon lokaci za,a saka ba ko? Abbas yace gaskiya kam, dan dama wannan ginin ne ya tsayamun,

Yanzu abinda yaragemun kawai lefe ne, nasan inde akasaka bikin nan da wata 2 ya isa ingama hadashi, Jafar yace haka ne, nima zanso asa bikinmu rana daya, kaga semuhuta gaba daya,Abbas yace hakane, fita sukayi.

Bayan sunje gurin kawun Labiba aka tsaida ranar biki wata 2, bayan suntafi yaje gidan kakar labiba bayan sungaisa, yace dama nazo ne, infada maki zanje gurin su yaya infada masu za,ayi bikin Labiba kada suga anyi ba,a fada masu ba.

Kakar tace gaskiya ka kyauta, dama ba,abiye ta mutum,gara kafada masu, koma menene kafita hakkinsu, godiya yayi mata yatafi,

Kamar yanda yafada, washe gari yaje jigawa, ko kadan beji dadin yanda yasamu yan uwanshi ba, gaba daya rayuwa tafara juya masu baya, yayanshi har tsufan talauci yafito mashi, sede abinda yadaure mashi kai, yanda haryanzu basu sauko daga fushin dasuke dashi ba.

Duk yanda yaso ya fahimtar dasu amma sam sukaki saurararshi, yanaji yana gani haka yahakura yafito ranshi abace yanufi kano tare da alkawarin baze kara zuwa inda suke ba, zeje ko abokananshi sun isheshi yayi hidimar biki.

Haka bangarorin biyu suka cigaba da shirye shiryen biki, Abbas gaba daya bayada lokacin kanshi, kullum akasuwa yake wuni, dan burinshi yatara kudin dazeyima Labiba kaya masu kyau kada kawayenta su rainata.

Labiba ce take tafiya kakarta ta aiketa magana tarikaji abayanta anakiranta, juyawa tayi dan taga mekiranta, murmushi tasaki ganin abokin Abbas Buba, bayan sungama gaisawa yace amaryarmu bakya laifi koda kinkashe dan megida,

Dariya tayi tace Buba kenan hada zolaya, yace ai gaskiya nafada, ina mutumin naki kinsan yanzu yayi mana wahalar gani tunda yafara gini,

Kallonshi tayi tace ai nasan kuna haduwa amajalissarku idan yadawo kasuwa, gini kuma shida aikinshi kawai yabiya masu gini,

Dariya yayi yace haba Labiba,ai Abbas shine yakeda ruwa agini, mutumin dayake kwaba kasa da kanshi, yayi bulo nakasa sannan yahau shida kaninshi suyi gini ai shine keda aiki,

Cike da mamaki ta kalleshi tace wane irin kwabin kasa kuma? Abbas din daya sayi filinshi a sallari kuma yace ginin bulo da bulo zeyi yama za,ayi kace yayi na kasa.

Dariya yayi yace lallai da alama kece yamaida sallari, acikin unguwarsu fa yasayi wani kwatan fili, kuma tunkafin Babanshi ya mutu suka fara kwabin kasar dazasuyi bulo da ita,

Kuma koyanzu zan iya rantse maki da Abbas ginin kasa

Please Login or Register in order to submit comment