Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayi sallah, dama fuskar ce kawai bazan iya shedawa ba. Murmushi mutumin yayi yace gaskiya nagode da wannan abun dakamun.

Domin azamanin nan bakowane ze tsinci babbar waya ba ya mayar ma me ita, kai koma karama ce, yanda ake cikin talaucin nan babu wanda ze maido maka. Nagode sosai, gaskiya, kuma hakan dakayi ya nunamun kanada amana. Idan bazaka damuba intambayeka mana?

Ya sunanka? Sunana Abbas Alee, murmushi yayi yace da kyau, amma kai bakone ko, naga kace bakasan shagona ba? Abbas yace hakane, nibakone, amma agurin nan, dan agarin nan nake amma bancika shigowa nan ba, yauma neman aiki ne yakawoni nan tunda safe, amma gashi har la,asar takusa bansamu ba.

Hakan yasa nayanke shawarar tafiya kwari kozan dace,to wannan wayar dana tsinta ce tasani zaman jira, gashi ansa key bare ni inkira. Jinjina kai mutumin yayi yace Allah sarki, ni sunana Alh, Abbah Hala.

Kuma ina aiki anan Wapa, shagona yana daga nan baya, ina canjin dala ne, gaskiya naji dadin haduwa da kai, kuma nayaba da hankalinka, ayanzu duniya ta lalace, kana zaune da mutane, amma suna maka bakin ciki shiyasa bazaka iya gane dawa kake tare ba.

Abbas yace tabbas hakane Alh, nikaina ayau zaman danayi agurin nan nakara fahimtar mutane, anan yabashi labarin abinda mutanen gurin suka mashi, jinjina kai Alh, yayi yace Abbas zaka iya nunamun shagunan mutanan?.

Kai ya girgiza yace kabarsu kawai Alh, yafi kyau mutum beson makiyanshi ba, da,ace yasansu, hakan zefi mashi dadin rayuwa, amma duk yanda akace kasan makiyinka kuma ace kuna zama guri daya dashi, tabbas ko bakada niyar mashi wani abu shedan ze iya rinjayar zuciyarka har yasaka maka wani mugun tunani.

Kuma nima idan har nafadesu tabbas nazama annamimi me hada fitina, domin bansan meze faru ba, bayan nafada. Kayi hakuri kawai, kamar yanda kake zaune da kowa lafiya to kayi kokarin zama dasu da zuciya daya.

Hakan zesa Allah yate makeka akan makiyanka, kuma kadage da addu,a da neman tsari daga sharrin masu sharri. Tsayawa Alh, yayi yana kallon Abbas cike da burgewa, hakan dayayi seya tuna mashi babban yaron shagonshi, akullum beda wani aiki se son yakawo mashi gulmar mutane da son ya bakanta wani agurinshi, shi kuma yasamu shiga.

Maganar Abbas takara ankarar dashi abinda yaronshi yakeyi kenan badede bane, murmushi yayi yace, nagode Abbas da tuna tarwarka, hakika samun masu zurfin ilimi irinku, kuma ace suna aiki dashi ayanzu akwai wahala, dan zaman danayi da kai yanzu, nakaru da abubuwa dayawa, inaga ace nazauna da kai har abada?

Idan bazaka damu ba, nizan daukeka aiki ashagona, ina fatan zaka rikeni da dukiyata bisa gaskiya da amana? Abbas besan lokacin daya kai goshin shi kasa yafara sujjadar godiya ga Allah ba.

Hakan da yayi bakaramin burge Alh, yayi ba, seda yayi addu,a sannan yadago yafara yimashi godiya, haka suka jera suka nufi shagonshi.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 30 🔱 35

Mamaki ne ya rufe Abbas ganin sun nufi shagon daya fara zuwa wannan yaron ya koreshi. Tunda suka shiga mutane suke yima Abba Hala sannu, fara,a dauke a fuskarshi yake amsa masu.

Auwal, shine sunan da Abba yakira bayan yazauna, yayi ma Abbas umarni daya zauna, daga waje wanda aka kira da Auwal yashigo, shima mamaki yayi ganin wanda ya kora dazu amma yanzu gashi agaban megidansu.

Alh, Abbah yace yauwa Auwal munkara samun sabon ma aikaci, sunanshi Abbas, kuma nizan bashi aiki da kaina, ba daya yake da sauran ma aikatan gurin nan ba.

Dan haka inaso kuzauna dashi lafiya, daga yanzu shine PA na, dama haryanzu kasan tunda wancan PA yarasu ban sake dora wani ba, duk da nace kaine zan bama, amma naga alamar gara inbarka matsayinka na mekula da ma,aikata.

Wani bacin raine ya rufe Auwal, ya dade yana jiran wannan ranar, tunda tsohon PA yarasu yake jiran anadashi, amma gashi yanzu daga zuwan wannan mutumin yabashi, kuma da alama besanshi ba.

Murmushi Auwal yayi yace ai bakomai Alh, Allah yahada kanmu, kallon Abbas yayi yamika mashi hannu yace abokina kayi hakuri da abinda yafaru dazu. Murmushi yayi yace haba ai bakomai.

Alh, Abbah yace dama kasanshi ne? Auwal yace wlh dazu yazo neman aiki, nikuma nakoreshi, kasan yanzu duniyar ta baci. Alh, Abba yace haka ne, amma duk da haka banaso kuna wulakanta duk wanda zezo nemana.

Koma wanene kubashi dama yaganni, domin ba,a taru akazama daya ba, bakasan darajar da Allah yayi ma wanda zaka kora ba, sekaje ka kori wanda shine nagari, idan nabanzan yazo kuma ka karbeshi.

Yanzu gashi nan, kayi mashi ranshin kyautawa dazu, cikin ikon Allah kuma yanzu Allah ya dauka kashi har yafika matsayi agurin aikinka, kaga yanzu kaji kunya ko? Kai Auwal ya sosa yana fadin ayi hakuri megida.

Yace shikenan ya wuce, ka kiyaye gaba,jeka zan nuna mashi duk abinda yakamata. Fita Auwal yayi yana cizon hannu, wato aikin ma, megida da kanshi ze nuna mashi,

Amma ada shine yake kula da komai, to kode wannan mutumin wani abu yayi ma Alh, ne? Gaskiya da sake, dole insaka mashi ido, baze yuwu yazo yafini fada agurin megida ba.

Anan Alh, Abbah yadauko file yarika nuna ma Abbas yanda komai yake, dayake Abbas yayi diploma akan accounting, shiyasa abun yazo mashi da sauki.

Sallar la,asar kawai ta tadasu, suna dawowa suka cigaba da aiki,seda misalin karfe 5, sannan sukayi shirin tashi. Alh, yace bakomai naga kana da saurin fahimtar abu, nan da wani lokaci zaka kara sanin komai.

Idan Allah ya kaimu gobe se mucigaba. Ina wayarka insa maka number ta? Wata Nokia Abbas yamika mashi, Alh, yace lallai Abbas gobe zantaho maka da babbar waya, saboda dole zaka bukaceta.

Abbas yace godiya nake Alh, yace bakomai, atare suka fito, yana rike da jakarshi, har bakin motarshi yarakashi, Alh yace wace unguwa kake ne Abbas? Yace anan Darmanawa nake can gurin gandun Sarki gaba da primary alayin wanzamai.

Murmushi yayi yace kace muna kusa, nima kusa daku nake, muje se in ajeka ko? Abbas yace badamuwa, haka suka tafi, suna zuwa Abbas yace ya ajeshi akwai abinda zeyi abakin titi. Dubu 5 Alh, yabashi, haka Abbas yayi tamashi godiya yamashi sallama.

Seda ya tsaya yasaya masu lemu da kankana sannan yahau adedeta yanufi gida, se kara godema Allah yakeyi da wannan nasarar daya samu ta yau, lissafin yanda zefara gininshi kawai yakeyi.

Hamdala yayi tunda yasamu aiki, kawai zesa malam Musa yasamo wani wanda zetayashi aikin se Umar yarika kula dasu, tunda beda lokaci kuma yanason agama dakin dawuri.

Da fara,arshi yashiga gidan, bakinshi dauke da sallama, abakin murhu yasamu Labiba tana kokarin dora tukunya, saurin aje tukunyar tayi tanufeshi fuskarta dauke da murmushi.

Tana zuwa tafada jikinshi tana fadin sannu dazuwa, rungumeta yayi yana fadin yauwa Labibata, sannu da kokari, ina Umma ne? Tace tashiga bandaki, yace shiyasa ai naga kinshige jikina, nasan intana daki bazakiyi ba.

Hannunshi taja suka nufi falon Umma tana fadin Abbas daga ganin bakinka akwai alkhairi, yace sosai ma Labiba, kede muje in kimtsa kusha labari,

Ruwa takawo mashi yasha, sega Umma tafito, fita waje Labiba tayi tahada mashi ruwan wanka, Umma tace Abbas kadawo? Yace wlh kuwa Umma, zama tayi tace tundazu bakina yakasa dena maka addu,a Allah yasa kasamu narasar fitar?

Yace sosai ma Umma, ai sede kawai muyima Allah godiya, bari infito wanka kusha labari. Umma tace Alhamdulillah, Allah shine abin godiya,jeka fito.

Bayan yagama wanka ya nufi masallaci, bedawo gida ba, seda akayi isha,i, akofar gida yahadu da malam Musa, bayan sun gaisa yayi mashi maganar ginin daki, malam musa yace ai babu damuwa akwai wanda zankira semuyi tare,

Abbas yace muje kaga filin inaso idan ze isa ayi mana hada bandaki aciki, kasan bandaki daya beda dadi agida, sbd matsuwa ake gudu. Tare suka shiga gidan, yadauko fitila ya haska masu.

Malam musa yagama dubawa, sannan yace kwarai kuwa za,a samu bandaki, Abbas yace yauwa amma naji dadi, yanzu agajiye nake, gobe ana fitowa asuba zan nemeka, tunda bamu fita kasuwa se 8 semuji yanda za,ayi.

Malam Musa yace shikenan babu damuwa, yanzu idan nafita zansamu me zanen infada mashi, abokin aikina ma zan fada mashi. Abbas yace nagode sosai, sallama yayi mashi yatafi.

Bayan sungama cin taliyar da Labiba tadafa masu, suna zaune afalon Umma, anan Abbas ya basu labarin duk abinda yafaru, kuma yafada masu gobe za,a fara ginin dakinsu.

Sosai sukayi farin ciki da labarin Abbas, suma suka fada mashi abinda yafaru da bayanan, sosai yaji dadi, dajin irin canji daga gurin Labiba. Umma tace babu abinda zamuyi ma Allah se godiya, dan haka ayau inaso muyi kokari mutashi muyi godiya ga Allah.

Domin duk abinda kasamu daga Allah yana da kyau kayi wata ibada wadda zata nuna godiyarka agurin ubangijinka. Allah yatemakeka, ya kareka daga sharrin masu sharri. Dole Abbas ka kara dagewa da addu,a domin Allah ya kaika gurin da dole saka dage da addu,a.

Gashi kaje gurin asa,a kashiga gaban mutane dayawa, dole ne suji haushinka, amma kaide babu ruwanka da kowa, kazauna da kowa lafiya, Allah ze temakeka akan makiyanka.

Abbas yace insha Allah Umma, bari inje inkwanta nagaji dayawa, Umma tace gaskiya kam, nima bari inleka gidan Zulai indubata. Abbas yace Umma bata da lafiya ne? Tace lafiyarta kalau, kawai zanshiga mugaisa ne.

Abbas yace amma Umma naga har 9 takusa, mikewa tayi tadauki mayafinta tana fadin aikuma sekayi fita waje tayi batare data kara kulashi ba.

Dariyar da Labiba take boyewace ta fito, Abbas yace wato ma dariya kikemun ko? Matsowa tayi takwanta saman kafarshi tace kaima de Abbas naga alamar bakaje ghana ba, aini tunda Umma tace zataje gidan Zulai nagane abinda take nufi.

Amma kai ka tsaya ka isheta da tambayoyi, bakinshi yarufe yana zaro ido yace kai hakanefa, gakiya Umma tana da kula, tashi muje kidanmun tausa inji duminki kafin tadawo, Allah sarki Ummata, muma munkusa komawa dakinmu. Infada maki hada bandaki nasa ayi mana.
Labiba tace da gaske? Yace da gaske mana, kara rungumeshi tayi tana fadin nagode sosai Abbas, dariya yayi yadauketa suka shiga daki.

Washe gari kamar jiya haka su Labiba suka fara aikinsu da wuri, yau harda kunu sukayi, dan mutane sunce arika hada masu da kunu. Shikam Abbas tunda suka dawo sallah suka nufi gurin ginin, bayan me zane yazo haka aka kiyasta komai, tundaga kasa, ruwa da sauran kayan gini, haka yadauki kudin yabama Umar, yace yarika kula dasu.

Bayan yagama wanka ya karya sannan yayi masu sallama yafita, haka jama,a suka rika shigowa suna shiyan kosai da kunu, kafin wani lokaci tuni sun kare.

Abbas kuwa yana zuwa shagonsu yafara aiki, haka mutanan shagon suka rika shigowa suna gaishe shi, sosai yaji dadin abinda sukayi mashi, Auwal kam yama kasa zama agurinshi, gani yake kamar idan baya kusa za,ayi wani abun..

Se karfe 10 sannan Alh, Abbah ya iso, bayan sungaisa yamika ma Abbas sabuwar waya akwalinta, infinix hot 4 lite, sosai Abbas yaji dadin wayar, haka yayi ta mashi godiya.

Auwal kuwa kamar ze hadiyi zuciya dan bakin ciki, Abbas ya mika mashi wayar yana fadin katayani godiya, Auwal yayi murmushin yake yace gaskiya waya tayi kyau, angode megida.

Kallon Abbas yayi yace ai seka bani tsohuwar taka, Abbas yayi dariya yace wannan ai se Labibata. Dariya Alh, Abba yayi yace bama zaka bashi ba, shima yana da ita, Alh, yace Abbas tashi muje banki akwai wasu kudi dazamu ciro,

Haka suka fita Auwal se bata rai yakeyi, tunda wancan tsohon PA yarasu dashi ake zuwa bank amma yanzu shikenan yakoma dan tsaron shago. Fita yayi yakira wani abokinshi kuma amininshi yace abokina zokaji babbar magana.

Anan yafada mashi duk halin da ake ciki, Saddik yace lallai dole musan abinyi, kai dolema yabar shagon nan wlh. Dariya Auwal yayi yace yauwa abokina haka nakesonka, wlh be isa yazo yasamemu yace ze nuna mana kano ba, zamu gwada mashi mu yan asalin Fage ne. Muje zuwa.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 35 🔱 40

Haka Abbas yacigaba da aiki a shagon Alh, Abbah Hala, sosai yake kara gane takan aikin, Auwal da abokinshi akullum kokari sukeyi su sami hanyar dazasu kullama Abbas sharri. Sede idan Allah ya tsare bawansa babu wanda ya isa yaja dashi.

Labiba da Umma sosai san,arsu take cigaba, aduk sanda suka dafa sesun saida, acikin sati 2 aka gama ginin dakin Abbas, ba laifi yayi kyau, duk da ko fenti ba,ayi ba, amma anyi shafen farar kasa.

Bayan sati 1 da gama ginin suka koma, sosai sukaji dadin komawarsu domin bakaramun takura sukayi ba adan zaman dasukayi, haka suka cigaba da sana,arsu. Acikin haka ne ciki ya bayyana ajikin Labiba, bayan sunje asibiti akace wata 3.

Sosai Abbas yayi murna da samun cikin Labiba, yakara godema Allah da seda yasamu gurin zama sannan Labiba tasamu ciki, haka Umma tahana Labiba aiki sosai, itace takeyin girki.

Jafar kuwa tunbayan rabuwarsu da Abbas bekara ganinshi ba, akullum yana son yanemeshi amma yana tuna maganar Mamanshi, hakan yasa yake hakura, sede kullum yana mashi addu,a kuma shima yanzu samunshi yayi kasa sosai,

Yarasa dalilin dayasa yanzu ko kudi yasamu basa zama, abu kadan zesiya zasu kare, ko mamanshi dayake daukar dawainiyarta yanzu yafara kasawa, tun tana fada hartafara gajiya, domin ba kullum yake kawo mata abinci ba, shima gidanshi wata rana so 2 suke ci, dan ma matarshi tana yar sana,a.

Sosai arzikin Alh, Abbah yake karuwa, tunda yafara aiki da Abbas yake ganin budi, dan Abbas yakawo mashi cigaba aharkar canjinshi, hatta abokan kasuwancinsa sunajin dadin harka da Abbas, inhar Alh, Abbah bayanan basa ganin kowa se Abbas, hakan bakaramin batama su Auwal rai yakeyi ba.

Wata rana Abbas yakarbo ma wani baturen mutum abokin Alh, canjin Kudi daga bank, dala ya canza mashi, kudin zasukai million 10, bayan sunyi waya da mutumin yace yakai mashi office dinsu anjima zezo ya karba.

Abbas yafadama Alh, Abbah yanda sukayi da baturen, suka kirga kudin, se Alh, yace shikenan ka aje mashi, nizanje gida akwai inda zanje amma anjima zandawo. Cikin office din yashiga ya aje mashi kudin ta yanda babu wanda zesan anyi ajiya.

Ashe duk maganar dasukeyi Auwal yanajinsu. Lokacin da aka kira sallah, kamar yanda Abbas yamaida tsarin office din inde ankira sallah babu abinda za,a kara jira za,a kulle office atafi sallah, kuma hakan yana daya daga cikin cigaban dasuka samu akan kasuwancinsu.

Haka yau ma Abbas yafito yace masu akulle office atafi sallah, dama akwai wani yaro shine yake kulle office din kullum kuma ya bude, tare da Auwal da Abbas suka jera suka nufi masallaci, bayan kowa yafita yaron ya kulle kofa shima yanufi masallaci.


Bayan sundawo ne, wannan baturen yazo karbar kudinshi, haka Abbas yadauko jakar inda ya ajeta, kara fitar da kudin yayi zekirga, baturen yace a,a inde yasan sun cika yabashi kawai, Abbas yace a,a ka,idar kudi anaso arika kirgasu,

Baturen yace shifa sauri yakeyi yabashi ai yasaba harka da Alh, kuma betaba samun failure dashi ba, haka Abbas yadauki jakar kudin yabashi. Auwal ne, yashigo yace kaga nagaban goshin megida.

Dariya Abbas yayi yace, Auwal baka rabo da tsokana, ai kowa yasan kafi kowa kusanci da Alh, Auwal yace ada kenan, amma yanzu kaine babba, mukam munzama yan kallo, murmushi kawai Abbas yayi yacigaba da aikinshi.

Da yamma bayan Alh, Abbah yadawo office, yana zama sega wannan baturen yashigo, bayan sungaisa yacema Alh, yayi mamakin ganin kudinshi basu cika ba,Alh, yace kamarya baku kirga bane kome? Yace ai yasaba dashi hakan yasa betsaya ankirga ba,

Anan Alh, yace nawa ne, babu? Yace mashi 2 million. Mamaki ne yakama Alh, tunda yafara aiki da Abbas ba,a taba samun haka ba, anan yakirashi yafada mashi abinda yake faruwa, wata irin zufa ce, tafara ketoma Abbas, Innalillahi Wainna ilaihirraji,un kawai yake fada.

Hankalinshi yagama tashi, dan tundazu dama yakejin faduwar gaba, Alh, yace Abbas kayi magana mana, naga duk hankalinka yatashi, ka kwantar da hankalinka, ninasan akwai abinda yafaru, kamun bayanin yanda abun yafaru tunbayan ka aje kudin.

Ajiyar zuciya Abbas yayi, harseda kwalla tazubo mashi, anan yafada masu yanda akayi, sallah kadai sukaje. Alh, yace akira mashi yaran office din gaba daya, danshi ba,a taba samun irin wannan a office dinshi ba.

Yade san yasha aje kudi a office idan yazo dauka seyaga sunrage, dayake becika kirga kudi ba, hakan yasa baya sanin konawa ne, amma kuma tunbayan zuwan Abbas bekara ganin hakan ba, amma ace wani customer yazo karbar kudi yadawo yace basu cikaba, shine abinda ba,a tabayi a office dinshi ba.

Shiyasa abin yadaga mashi hankali. Bayan kowa yazo, anan Alh, yafara bayanin abinda yafaru, sosai kowa hankalinshi yatashi, anan guri yacika da surutu,kowa da abinda yake fada, shikam Abbas yana gefe guda, inbanda kuka babu abinda yakeyi.

Baturen yace, Oga inaganin wannan yaron daya bani canji shine yacire wani abu aciki, bantaba harka dashi ba, se yau, kuma gashi ayau nasamu failure, kawai kabarni dashi zan kiramashi police, idan yaje can zeyi bayanin inda kudina suke.

Auwal yayi saurin fadin hakane yallabai, mude tunda muke aiki ba,a taba samun matsala ba, amma gashi ayau antaramu ana tambayarmu kudi. Saddik yace gaskiya megida kabari kawai afitar da bara gurbi acikinmu, hakan zesa asamu zaman lafiya, nidama tuntuni banyarda dashi ba, tun lokacin daya kawo dokar dole se antafi sallah atare.

Idan aka tafi kuma seya riga kowa dawowa, tun daga nan nafara zargin shi, kuma gashi ayau gaskiya tafito. Wani daga cikin yaran yace amma kuma koda muke tafiya tare yake riganmu dawowa, ai bashine yake kulle office din ba, kuma bashine yake kullewa ba.

Idan har akace shine yadauki kudin ba,a mashi adalci ba. Wani yace kaga malam dalla kamana shiru, ni aganina ba,a cikin office din nan aka dauki kudin nan ba, domin babu wanda yabishi bank, shikadai yaje, dan haka babu wanda yasan lokacin daya dauki kudin. Haka kowa yarika kawo uzurinshi,

Tebur Alh, yabuga yace ya isa hakan bankiraku nan danku yanke hukunci ba, nakiraku ne saboda acikin office dinnan aka dauki kudin nan, dan lokacin daya karbosu nidashi muka kirga kuma dede muka kirga, dan haka zanyi maku tambayar karshe, idan har babu wanda yadauka nizan biya kudin, amma kusani duk ranar da aka gane wanda yadauki kudin nan wlh, nikadai nasan abinda zanyi mashi.

Kunyi shiru, babu wanda yadauka? Auwal ya hadiyi muyau da kyar, zufa tana zubo mashi yace megida to sede atambayi dan Bala, domin shine me kulle office din nan, kuma kowa yasan shine muka bari akarshe, kuma tare suka dawo da Abbas.

Kallon dan Bala Alh, yayi yace tsakaninka da Allah bakasan inda kudin nan suke ba? Kai yashiga girgizawa hawaye suna zubo mashi, yama kasa magana. Baturen yace Oga kana batamun lokaci, zantafi dasu duka 2, idan ansamu wanda yadauka seya biya.

Alh, yace a,a nizan biya kudin kayi hakuri, idan katafi nizan gano wanda yadauka da kaina, wata durowa yabude yakirgo 2 million yabashi, anan yafita. Alh, yace kowa yatafi gurin aikinshi.

Kallon Abbas yayi wanda yaketa kuka yace kayi hakuri Abbas, ninasan bakai kadauki kudin nan ba, kasan arayuwa idan akaga mutum yana samun cigaba, yafi samun makiya, kada kadamu, nizance naji dadin daukar kudin nan da akayi, domin insha Allah zamu gano makiyanmu.

Bazanyi kasa aguiwa ban zanyi kokarin nemo wanda yadauki kudin nan, kodan inrabu dashi. Abbas yace shikenan nagode Alh, nima insha Allah ayau zan dage da addu,a harse Allah yatona asirin wadanda suka dauki kudin nan.

Haka kowa yarika kallon Abbas amatsayin wanda yadauki kudi, gaba daya yakasa samun sukuni haka yacema Alh, zeje gida, shikanshi Alh, yatausaya ma Abbas, hakan yasa ya kyaleshi yatafi.

Koda yaje gida daki kawai yawuce ya kwanta, domin kanshi ciwo yake mashi sosai, ganin hakan Labiba ta tashi tabi bayanshi, tana zuwa tazauna kusa dashi tare da dafa kanshi tace Abbas lafiya naga kadawo gida da wuri?.

Wahaye ne, suka sake zubo mashi, cike da tashin hankali takamoshi tace Abbas kowani ne yarasu? Shiru yayi bece mata komai ba, tashi tayi takira Umma, atare suka shigo, anan suka cigaba da tambayarshi.

Da kyar yatashi yafada masu abinda yafaru, sosai hankalinsu yatashi, Umma tace ammade ai ba,a koreka daga aikin ba ko? Kai yadaga mata, jinjina kai tayi tace dama nafada maka, yanda Allah ya daukaka ka alokaci guda dole kasamu makiya, nagode Allah dayasa shi Alhjin yake da hankali har ya iya yanke wannan hukuncin.

Kayi hakuri Allah yana tare da kai, insha Allah babu wanda ya isa yayi maka wani abu, kuma dole karika zuwa gurin aikinka, addu,a kadai ta isheka kariya duniya da lahira, kuma insha Allah za,ayi walkiya Allah zetona asirin wanda yadauki kudin nan. Da haka suka lallashi Abbas har yasamu ranshi yayi dadi.

Cikin dare Abbas, Labiba da Umma suka tashi sukayi nafila suna rokon Allah yatona asirin wanda yadauki kudin nan, se asuba sukayi sallah suka kwanta.

Washe gari haka Abbas yatashi ranshi yayi tas, babu abinda yake damunshi haka yayi masu sallama yatafi office, koda yaje office besamu Auwal ba, Alh, ma bezo ba, daya tambayi dan Bala yace bezo ba, kuma da kyar idan zezo, haka yacigaba da aikinshi har Alh, yazo.

Bayan sun gaisa yace ina Auwal fa? Yace shima yazo besame shiba, ya tambaya ance bezo, murmushi Alh, yayi bece komai, ba, yazauna yafara duba wasu takardu, yace Abbas akwai abinda nake zargi amma insha Allah komai zezo karshe.

Godiya Abbas yayi mashi yace Allah yasa adace nikaina inaso Allah yatona asirin wanda yadauki kudin nan, kodan insamu nutsuwa araina. Alh, yace karka damu akwai Allah.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:10 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 40 🔱 45

Mukullin mota Alh, Abbah yadauka ya kalli Abbas yace muje karakani wani guri, fita sukayi anan ya tambayi wani ina Saddik, yace ai shima bezo ba.

Murmushi yayi yace shikenan bara muje bank mudawo,suna fita Abbas yace wai Alh, ina zamuje? Murmushi yayi yace Fage zaka rakani. Shiru Abbas yayi suka tafi.

Adede majalissar su Auwal suka tsaya, fitowa sukayi, wani abokin Auwal da yasan Alh, Abbah shine yayi saurin tasowa yana gaishe shi. Bayan sungama gaisawa yace yau banga abokinka ba agurin aiki shine yasa nazo inji ko lafiya?

Mamaki abokin yayi, dan sunyi sallama da Auwal yace mashi yatafi gurin aiki, kallonsu yayi yace aikuwa tundazu mukayi sallama dashi yace yatafi aiki, har nake cemasa yau kafita dawuri, shine yace wai aiki garesu sosai.

Mamaki Abbas yayi, shikam Alh, dama yasan za,ayi haka, kallon abokin yayi yace nagode,dama munzo muji ko lafiya tunda mutum yana zuwa kullum kuma mukaji shiru ai dole mubiyo.

Wani ne yazo wuce wa shima abokin Auwal ne, bayan sun gaisa dayan yace mashi megidan Auwal ne, yaga shiru bezoba shine yabiyo yaji ko lfiya. Yace aikuwa tare muka shiga adedeta dashi dazu, harmuka dauki wani abokinshi awancan layin shima inajin gurin aikinsu daya.

Amma dama ni Fam Center zanje kuma suma can naga sunnufa. Alh, yace shikenan nagode bara mutafi, haka suka nufi mota Alh, shikadai se murmushi yakeyi.

Abbas ya kalli Alh, Abbah ganin yadauki hanyar Fam Center yace mezamuyi acan kuma? Yace kaide kayi addu,ar musamesu acan, domin zuciyata tana kara sakamun wani abu. Shiru yayi sukaci gaba da tafiya.

Suna isa kai tsaye suka shiga wani babban layi inda ake saida manyan wayoyi suka nufa, cikin sa,a sunzo wuce wani shago Alh, yaga Auwal yana kirga wasu makudan kudi daga aljihunshi.

Tsayawa yayi tare da kamo hannun Abbas yayi mashi nuni da Auwal, sosai yayi mamakin ganin yanda yake zaro kudi daga aljihunshi, can daga gefe sukaga Saddik shima yana zaro nashi.

Cikin sauri Alh, yanufi gurin Auwal, dama ya aje wayar daya siya akan table yana kirga kudi, hannu Alh, yasa ya dauki wayar yana fadin kai abokina kaga wata hadaddiyar waya kuma daga ganinta zatayi tsada.

Saurin dagowa Auwal yayi jin

Please Login or Register in order to submit comment