Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nace muzo mugaidaki.

Bayan sungaisa Abbas yace bari yaje yakarbo wani abu, Kaka tace to kada kadade kasan zakuyi baki yan ganin dakin amarya, yace to kaka.

Yana fita Labiba tafada mata duk abinda yafaru, salati kaka tafarayi takaima Labiba duka tana fadin ammade anyi yar banzar yarinya wlh, aini dama tuntuni wannana yarinyar Hauwa bata kwanta mun ba,

Ashe seda tasaki hanyar banza hankalinta yakwanta, ke kuma dayake 'yar fari ce kika biye mata tamaki wayau, bakisan bakin ciki take maki ba, ke naki mijin gidan kanshi zesaki, ita kuma gidan haya ne, hakan yasa tasaki kika aikata wannan shirmen.

To bara kiji,wlh kanki kika cuta, baki cuceshi ba, domin shi namiji ne, kowace irin rayuwa, tazo mashi ze iya daukarta, kefa? Macece wadda batasan wahalar rayuwa ba,

Zakiyi kuka da idanunki wata rana, da kinyi hakuri da wannan gidan wata rana daukaka zata iya zo maki, domin kowa da haka yafara, wasu ma da gidan kara suka fara arzikinsu,

Amma ke kinsamu kikayima Allah butulci, to wlh kobayan raina zakice nafada maki, wata rana sekin nemi gidan da bekai wanda kika raina ba, amma yafi karfinki,

Labiba idan har kinaso kisamu rayuwa medadi, tabbas sekin koma ga Allah kuma kinsake wannan rayuwar da kika dorama kanki ta karya, sannan Allah ze kalleki. Kuka Labiba takeyi sosai,

Kaka tacigaba, MUHALLI da kike ganinshi wlh kona tsumma ne, daraja gareshi musamman idan mutum da gumin kanshi yayishi,kinko san irin farin cikin da mutum yake tsintar kanshi aciki aranar daya mallaki MUHALLINSHI? kina ganin ko mahaukaci beyarda yazauna awaje ba, koda icce da tsummuna seyayi kokari yahada gidanshi, amma ke kinsamu me daraja kika wulakanta.

Hakuri tashiga bama kakarta, da kyar ta hakura dan ranta bakaramin baci yayi ba, shawara tayita bata, Abbas ne yayi sallama, yashigo, shima nan Kaka tarufeshi da nashi fadan, tace,

Kabani kunya da har ka iya biyema mace, kuma meyasa ma ni baka fadamun ba? Hakuri Abbas yayita bata, tace ai shikenan ku kuka sani, kutashi kutafi, Allah ya kyauta gaba, haka suka fito suna mata godiya.

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya suna cin amarcinsu cikin jin dadi, Abbas duk abinda Labiba takeso shiyake mata, ko girki batayi sosai, sede yasiyo masu, soyayya kawai sukeyi,

Ko fita yayi baya dadewa zedawo, hatta kasuwa ba kullum yake fita ba, Jafar yayi maganar harya gaji, Abbas ganin Jafar ze matsa mashi yasa yabar kasuwar dayake zuwa shida Jafar da Umar Kwari, ya koma sabon gari.

Da Jafar yamashi magana Abbas yace yasamu wani ubangida kuma yamafi samu acan, sosai Jafar yaji dadi, dan yanason Abbas yarika samu, Umma ma taji dadi da Umar yafada mata.

Ganin babu wanda yake matsa mashi hakan yasa seyaga dama yake zuwa kasuwar, dama kuma babu wani uban gida daya samu, idan yajema dako yake danyi, daya samu yan kudi zetashi yakoma gida.

Sauran kudinshi daya aje sune yake dauka suna cin dadi dan kullum seya sayama Labiba kaza da madara, sosai sukayi kyau, bakamar Labiba, hutu ya karbeta.

Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya, sannu ahankali suka cinye kudin Abbas duka, saukinsu ma sunada abinci dan ba kullum suke girki ba, ganin beda kudi ahannu Labiba tace yasaida mashin dinshi se yayi jari.

Babu gardama ya amince da shawararta, kayan gwanjo yasaro yafara saidawa, sosai yake ciniki sede kudin basu azuwa ko ina, kafin wani lokaci kudin suka kare.

Zaune suke afalo suna cin abinci, wayar Abbas ce tayi kara, yana dubawa yaga kawun Labiba ne, bayan sungama gaisawa yafada mashi Allah yayima kakar Labiba rasuwa tunda dare, sakamakon ciwon ciki seda safe aka balle kofar akaga tarasu.

Salati Abbas yayi yace gasunan zuwa, yana fadama Labiba tasa kuka, haka sukatafi, lokacin dasukaje har angama shiryata, sosai Labiba take kuka dan sun saba sosai da ita,

Bayan anyi mata sallah aka kaita gidanta na gaskiya, haka akacigaba da karbar gaisuwa, dangin baban Labiba mutum 2 sukazo, sosai Kawunta yaji dadi, dan bedauka zasuzo ba, daya fada masu.

Bayan sadakar 7 kowa ya watse, sosai Abbas yakara dagewa gurin bama labiba kulawa,saboda bakaramin tausayinta yake ba.

Rayuwa tafara yimasu zafi domin yanzu se Abbas yaje kasuwa amma da kyar yake samun dari 500, aciki ze cire kudin mota yadawo gida, gashi koyaya yasamu kudi seya sayama Labiba abun dadi, wani lokacinma shibaya ci, sede sam bebari Jafar yasan halin dayake ciki ba, duk sanda suka hadu yana gwada mashi yana tara kudi a asusu, Jafar kam dadi yakeji idan yaji haka.

Lokacin da shekara tacika akazo karbar kudin haya, nan suka fara zare idanu, dan Abbas beda ko dubu 500 bare yasamu dubu dari 200 kudin haya, hakuri yafara bama megidan, amma yace idan basu da kudi kawai su fita dan yanzu haka akwai meson kama gidan, dan haka yabasu nan da sati daya sufita, nan yabar Abbas zufa tagama jikashi.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 100 🔱 105

Tagumi Abbas yayi hannu 2, hawaye ne kawai suke sintiri a idanunshi, Labiba tana zaune gefenshi itama kukan takeyi, tanaso tayi mashi magana tsoro takeji, dan gaba daya tasan koma meyafaru laifinta ne.

Sallama yaji akafor gida, sanin muryar wanda yayi sallamar ne, yasa gaban Abbas faduwa, domin kobe fita ba yasan Jafar ne, shiru yayi yakasa tashi, kofar da aka rika kwankwasawa ce tasashi saurin tashi ya goge idonshi.

Akofar gida yasamu Jafar karasawa yayi yace Jafar sannu dazuwa, hannu yabashi suka gaisa yazauna kusa dashi, kallonshi Jafar yayi amma sam Abbas yaki bari su hada ido, Jafar yace Abbas lafiyarka kuwa, kode bakada lafiya ne? Kai ya girgiza.

Ai duk wanda yaganka yasan akwai damuwa atare da kai. Shiru Abbas yayi bece komai ba, dafashi Jafar yayi yace kamun magana Abbas, kasan de baka da wani wanda yawuceni, wanda zaka fadama damuwarka,

Ko Umar sunan yana kaninka ne, amma bakomai kake fadamashi ba, saboda haka kafadamun damuwarka, ashirye nake inmaka koma menene inde befi karfina ba. Kwantar da kanshi yayi saman kafadar Jafar yasaki wani irin kuka me ban tausayi.

Cikin tashin hankali Jafar yadagoshi, yana tambayarshi lafiya? Kasa cewa komai yayi inbanda kukan dayakeyi, hakan yasa Jafar yarabu dashi yasan kila kukan ne zesa zuciyarshi tayi sauki.

Yafi minti 5 yana kuka kafin yadago kanshi yana goge fuskarshi, se ajiyar zuciya yake saukewa kamar wani yaro. Kallon Jafar yayi wanda shima tuni hawaye sun fara sauka afuskarshi, hannunshi yakamo yace,

Shikenan Jafar abinda Baba yake gudarmun yafaru, Labiba ta cuceni, narasa gatana, daga yau zuwa wani lokaci zan iya tozarta agaban mutane, banda komai Jafar, megidan hayarmu yabamu lokaci mubiya komutashi.

Kuka yacigaba dayi, Jafar yashiga bubbuga bayanshi yace dan Allah kayi shiru Abbas, inde ina raye bazaka taba tozarta ba, Allah yana tare da bayinsa masu gaskiya da hakuri, kayi shiru musan ta inda zamu bulloma wannan matsalar, kaifa namiji ne,

Idan kana kuka Labiba tace me? Kama dena cewa Labiba ta cuceka, duk da tana da laifi, amma kadauka kawai wata jarabawa ce Allah yayi maka, kayi hakuri ka rungumeta se Allah yasaka maka da abinda yafi alkhairi,

Kafadamun gaskiyar abinda kake boyemun, tunbayan barowarka kasuwarmu? Tashi Abbas yayi yafara fada mashi duk gaskiyar abinda yafaru azamansu da Labiba. Ajiyar zuciya Jafar yayi,yace gaskiya Abbas bazan boye maka ba,

Wlh, Son da kake nunama Labiba yayi yawa, ba,ace kada mu nunama matanmu soyayya ba, amma wadda kakeyi tawuce misali, taya zaka dorama kanka abinda yafi karfinka duk dan kawai kafaranta ma matarka rai?.

Kasan sufa mata basu san wanda yake masu ba, wlh, duk yanda kake kyautata masu duk ranar da bakayi masu ba, se sunnuna maka bacin ransu, garama karika nuna masu zafi wani lokacin, zakufi dedetawa dasu.

Amma yanzu mubar wannan maganar, abinda nakeso da kai zannema maku wani gidan, sede kayi hakuri ba,a wannan unguwar ba ne, kasan nima bawasu kudi gareni ba, zanyi kokari insama maku gida mesauki a burget,

Acan za,afi samun gidan dazaku zauna ku kadai mesauki, dan gaskiya banaso kuzauna da wasu, ammafa sekunyi hakuri, ba dadi kunsaba zama anan kuma yanzu kusake wani gida.

Murmushi Abbas yayi yace haba Jafar, niyanzu ko gidan bukka nasamu ai wlh, zama zanyi sede idan Labiba bazata zauna ba, ai namafi son musami kaskantaccen gida kodan yazama darasi agareta.

Nasan yanzu kowane gida nasamu zata zauna, domin nine gatanta, da ace kakarta tana raye nasan bazata yarda tabini ba, to kasan bata shiri da yan uwan babanta, kawunta kuma baze taba goya mata baya ba.

Nayarda kasama mana duk inda kaga zemaka saukin biya, kada kadamu dani Jafar, kasan ni namiji ne, zan iya kowace irin rayuwa ce, nasan inason Labiba amma zanyi kokarin dannewa domin itama ta gyara halayenta.

Amma dan Allah Jafar kada kafadama Umma wannan abun daya faru, nasan Umma tana da kawaici, bata zuwa gida na, kawai zance mata munsake gida saboda inaso intara kudi wannan gidan kudin sunyi yawa,

Nasan zataji dadi sosai. Jafar yace karka damu, babu wanda zesan anyi wannan magana,zanje anjima da yamma zandawo seku fara hada kaya, rungumeshi Abbas yayi na fadin nagode Jafar tabbas kai abokine nagari, Allah yabani abinda zan saka maka dashi na alkhairi, tashi Jafar yayi yace kada kadamu, sena dawo.

Gida Abbas yashiga yana me cike da farinciki, hankalinshi kwance, akwance yasamu Labiba tana kallo, dariya da tausayinta ne zuka kamashi, kusa da ita yazauna, yace tashi zakiyi mufara hada kaya,

Ai kamar ya watsa mata ruwan zafi haka ta tashi zaune, kallonshi tayi tace Abbas yanzu babu yanda za,ayi asamu kudin hayar dole semun,,,,, wani kallo yayi mata hakan yasa takasa karasa maganarta,

Kasa tayi da kanta tace awace unguwa zamu koma? Daure fuska yayi yace ai nadauka tambayata zaki farayi inda nasamu kudin kama wani gidan, amma zaki faramun wannan maganar banzar,

Labiba kisan ina sonki, kada kibari kifara batamun rai, koma menene ai kece sanadi, dan haka kiyi abinda nikeso idan har kinason zama dani, ayanzu bamu da wani zabi, duk abinda yazo mana dole mu karbeshi hannu 2, koda kuwa acikin kango ne, dole muyi hakuri muzauna.

Kuka tasa mashi me bantausayi, gaba daya seyaji be kyauta ba, tausayinta yakamashi,saurin kamota yayi yace yishiru mana, kallonshi tayi tace dan Allah Abbas kada ka kara cewa idan inason zama da kai,

Kasan ayanzu bani da kowa se kai, da kawuna, idan muka rabu ina kakeso inje? Kuka tacigaba, rungumeta yayi, seyaji sam be kyauta ba, lallashinta yacigaba dayi, yace naji kiyi hakuri nima wasa nake maki, aikinsan bazan iya rayuwa babuke ba.

Amma kema kimun alkawarin duk inda nasamu gurin zama zaki bini kuma ranki baze baci ba? Kai tadaga mashi tace namaka alkawari bazan kara maimaita kuskuren danayi maka abaya ba, yace yauwa Labibata, tashi muje kada Jafar yazo yajiramu, anan yafada mata komai,

Jafar yana zuwa sungama hada kaya, dama da mota yazo, haka sukarika kwasar kayan har suka gama, Labiba kasa shiga makwafta tayi don suyi sallama, haka Abbas yaje yakaima megidan mukullin gidan suka tafi.

A unguwar burget wani karamin gida suka tsaya, ciki da falo ne, bandaki atsakar gida, se kitchen din langa langa, sosai Labiba tayi bakin cikin gidan, hakanan tadanne kada sugane halin datake ciki.

Kayan suka sanya aciki, sauran kayan kitchen dinta aka sasu daki, kayan ruwanta aka saka wasu bandaki, wasu awaje, Jafar yakira me ruwa yazuba masu, dan sun saba inda suka baro akwai famfo, seda suka gama shirya komai Jafar yace zetafi,

Gobe su hadu kasuwa yasama mashi wani aikin, godiya sukayi mashi Abbas yarakashi, bayan yadawo sukayi wanka dama Labiba ta dafa masu abinci acan gidan sukaci, Abbas yace naga abincin gidanma yakare ko? Labiba tace E.

Shiru yayi dan yasan beda kudi, Labiba tace kawai kadauki kujerun nan kanana guda 2 kasayar semu sayi kayan abinci, Abbas yace nagode Labiba, tace kadena godemun nice silar komai.

Washe gari seda ya saida kujerun yasiyo masu kayan abinci sannan yanufi kasuwa, sede aikin daya samu bekai wanda yakeyi ada ba, haka Jafar yayita bashi hakuri yace yacigaba dayinshi nan gaba zesamu wani.

Bayan suntashi kasuwa gidansu yawuce dan yagaida Umma, bayan sun gaisa tace Abbas meyake faruwa da kai naga duk karame? Cewa yayi bakomai Umma nayi rashin lafiya ne, tace Allah ya kyauta,

Nan yafada mata suntashi, amma yanuna mata soyake yatara kudi shiyasa suka tashi, Umma tace to Allah yate maka, amma kaima seka rage kashema matarka kudi sannan zaka iya tara abin arziki, Abbas yace to Umma, tashi yayi yatafi.

Da kallon tausayi tabishi, dan tasan akwai abinda yake damunshi, kawai baze fadaba, amma tayi alkawarin yimashi addu,a.

Haka rayuwar su Abbas tacigaba datafiya, yanzu samunshi yayi kasa sosai, dan ba kullum yake samu akasuwa ba, gashi Labiba tasaba da cin dadi, hakan yasa tafara saida kayan kitchen dinta suna siyen abinci.

Wasa wasa haka shekara takare Abbas betara wasu kudi ba, domin koyatara Labiba zatasa su cinyesu saboda hidimarta, ada ma yadauka ko ciki gareta shiyasa yake siya mata duk abinda takeso.

Duk wasu abokansu yanzu sungujeshi, hatta Buba baya kulashi, dan kowa yanada rufin asiri, Jafar ne kawai yake temakonshi, alokacin da kudin hayarsu yakare alokacin matar Jafar ta haihu.

Ganin hakane yasa Abbas yacema Labiba baze iya yima Jafar maganar kudin haya ba, hakan yasa Labiba tace su saida kayan kallonsu da sauran kayan falonta se su biya, alokacin daya saida kayan dubu 30 yasamu,

Kuma gidan dasuke ciki dubu 45 ne, hakan yasa yashiga neman wanda bekaishi ba, da kyar yasamu wani gida irin masu yawan nan, amma yace bayason zama da mutane,

Hakan yasa megidan yace akwai wani part amma zaka kara dubu 500 asama danshi nazagayeshi daki daya ne se bandaki awaje, dubu 25 zaka bada, Abbas yace bakomai yayi,

Zuwa yayi yaga gidan, dakin babbane, haka yabada kudin aka bashi makulli, me kura yasamu suka rika daukar kayan dayake abayan layinsu gidan yake, haka suka gama kwashe kayan yakaima megidan makullinshi.

Labiba seda tayi kuka dataga gidan, haka sukaci gaba dazama aciki, langa langa Abbas yasamu akayi mata kitchen, saboda ruwa, ga dakinsu inde ana ruwa zuba yakeyi.

Alokacin idan kaga Labiba zakasan rayuwa ta canza mata, duk tarame, damma Abbas yana kokarin yimata abinda takeso, hatta da wayarta tasaida danyanzu batada wata kawa, Hauwa ma sunrabu tunda suka taso bata kara nemanta ba,

Kiran datake mata ne, yasa tasaida wayar, dan bataso tazo taganta agidan datake, alokacin da Jafar yasamu labarin suntashi fada yayi tama Abbas, shikam hakuri yayita bashi yace Jafar kaima fa hidima tayi maka yawa, ga haihuwa anmaka,

Badamuwa yanzu ma muna cikin farin ciki, Jafar yace duk da haka Abbas banajin dadin ganinka cikin irin wannan rayuwar, wlh da ace gidana yanada dakuna dayawa can zaku koma.

Abbas yace bakomai Jafar, ni inajin dadin wannan rayuwar kodan saboda Labiba, inaso takara sanin DARAJAR MUHALLI, kaga duk sanda Allah yaye mana wannan matsalar bazata kara maimaita kuskuren datayi abaya ba.

Jafar yace shikenan, amma meze hana tunda takardunka sunyi kyau muje kasami ko makaranta ce nasan zasu baka ko dubu 10 ce, Abbas yace a,a niyanzu kasuwanci yafiyemun komai.

Nasan aduk rana zan iya samun kudi, aikin gwamnati fa? Dole se wata yayi, kabarshi kawai ina jindadin halin danake ciki nasan kaddarata ce haka wata rana komai zewuce. Jafar yace Allah yasa.

Haka suka cigaba da rayuwa, tausayin Labiba da kuma soyayyarta sune suke sa Abbas yana kasa tara kudi, bayajin ze iya hanata wani abu inde yanada kudi, wannan itace babbar matsalar data hana Abbas tara abun kanshi,

Haka suka rika cinye kwanakinsu batare dasun tara komai ba, har lokacin biyan kudi yazo, da kyar suka samu aka kara masu sati 2, Abbas duk hankalinshi yatashi, yarasa yanda zeyi, gashide gidansu daki daya ne cike da falo kuma na Ummansu ne,

Gashi basuda sauran abinda zasu saida se gado da kujeru 2, kuma yace ma Labiba baza,a saidasu ba, ranar da sati 2 suka cika tunda safe masu karbar kudi sukazo suka fara masu wulakanci,

Jafar yafito kasuwa yahadu dawani dan unguwarsu Abbas, shinema yake fada mashi abinda yake faruwa, gida yakoma yadauki wasu kudinshi dayake tarawa zesayi mashin, bekoma gurinsu Abbas ba seda yaje fage yakama masu gida,

Sannan ya samo mota suka nufi unguwarsu Abbas, suna zuwa suka samesu awaje ankulle gidan kayansu awatse, shine Jafar yadaukesu yakaisu gidan daya kama masu me mutane 3.

WANNAN SHINE ASALIN LABARIN ABBAS ALEE DA LABIBA.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 105 🔱 110

CIGABAN LABARI.

Kuka sosai Abbas yakeyi alokacin daya gama bama Alh, Abbah labarinshi, shima Alh, seda yazubar da kwalla, bakaramin tausayi Abbas yabashi ba.

Gyara zama yayi yace kayi hakuri Abbas, tabbas kaga rayuwa wadda bakowane namiji bane ze iya jureta, ko kuma yacigaba da zama da Labiba ba.

Tabbas duk wanda yaji labarinka dole ya tausaya maka, Allah ya jarabceka kuma kayi sa,a kaci wannan jarabawa domin bakaramin me imani bane ze iya haye wannan jarabawa.

Jafar ba abokinka bane kadai, yazama dan uwanka najini, azamanin nan kafin asamu irinsu gaskiya za,a sha wahala, yayi maka abinda bakowa ne ze iya yinshi ba.

Kai intakaice maka wlh ko dan uwanka ciki daya bakowane baze iya yimaka abinda Jafar yayi maka ba,kuma ayanzu ne, kaima zaka temaka mashi kamar yanda kayi addu,a Allah yabaka damar dazaka temaka mashi wata rana.

Gaskiya Abbas kayi namijin komari da har ka iya cigaba da zama da Labiba, duk da itama tana sonka, dan bako wace mace bace zata iya yin abinda tayi, itama ya cancanta a jinjina mata.

Kuma banga laifinka ba, idan kace bazaka iya yimata kishiya ba, duk da itace silar duk wata wahala daka sha amma itama tabada gudummuwa sosai arayuwarku.

Kuma ayanzu ne nima zankara baka goyon baya wajen ganin ka mallaki MUHALLINKA da guminka, domin kacikama Baba da Umma burinsu, kuma kanuna ma su Alh, Bukar cewa kai dan halak ne.

Bazamu bata lokaci ba, kafadi a unguwar da kake so kayi gininka ni kuma zan nema maka kuma zan baka dama kayi gini da kudinka kodan kasamu farin cikin da kowa yake samu alokacin daya mallaki gidanshi da guminshi.

Goge ido Abbas yayi yace zanso insamu fili akusa da kai, idan har akwai Yaya, domin kaima kazama daya daga cikin yan uwana, murmushi Alh, Abbah yayi yace badamuwa ni kaina zanfi son hakan,

Zan nema maka insha Allah, sede akwai wata shawara danakeso inbaka agame da yan uwan matarka, duk da sune suka yada zumunci zanso ka tsaya mata wajen ganin ta aikata aikin lada.

Kashige mata gaba kuje ku sasanta tsakaninta da yan uwan mahaifinta, domin sune abun ado ga kowa, kuma ayanzu dole zasu karbeta kodan arzikin datayi, shima Kawunta kuje hadashi.

Abbas yace insha Allah Yaya zanyi yanda kace, Allah yasaka maka da alkhairinsa, yabaka abinda kake nema duniya da lahira, Yace amin,nizanzo intafi, labarinka yasa nayi dare agidanka. Abbas yace Yaya ka tsaya muci abincin dare mana.

Tashi yayi yace a,a naci na rana kanaso inyi laifi agurin uwar gida ne? Kasan bakowace mace takeso mijinta yaki cin abincinta ba, nagode tunda naci., tashi Abbas yayi yace nima nagode muje inraka ka.

Sauke ajiyar zuciya Labiba tayi, fuskarta ta jike da hawaye, ita kanta Maman Zainab kuka takeyi, ada tadauka tafi kowa shirme datasa mijinta yarabu da gidan gadonsa, segashi ayau taga wadda tafita wauta.

Kallon Labiba tayi tace lallai Labiba ayau naji labarin daya bani tausayi da kuma tsoro, ada inaganin kamar babu wata mace data fini wauta, amma ayau na jinjina maki, dole zakice labarinki yafi nawa.

Gaskiya ki godema Allah daya baki miji nagari kuma mesonki, wlh da ace wanine da tuni kun rabu, gaskiya bakaramin wauta kikayi ba, da har kika iya daukar gurguwar shawarar Hauwa.

Kodayake idan Allah yariga yarubuta abu zefaru dole seya faru, bawa baya iya kaucema kaddararshi, amma ina fatan wannan yazama darasi agareki, bakowace shawara ake dauka ba ta kawa.

Duk wata wadda zata baki shawara kifara tsayawa ki kalleta kiga shawarar data baki ita tana binta kokuwa kawai son zuciyane, dan wlh dayawa yanzu kawaye basa bama kawayensu shawara tsakaninsu da Allah.

Kawai dasun duba sunga kafisu wani abu, ko kuma zaka daukaka shikenan se sufara bakin ciki, to itama Hauwa abinda tagani kenan har tabaki wannan shawarar, ita meyasa bata bama mijinta shawarar yasaida gidanshi na danbatta ba?

Ashe kenan tana sane har tabaki wannan shawarar, saboda taga ke acikin gari zaki zauna, itafa? Akoda yaushe zasu iya komawa garinsu, kuma kilama karya tayi maki babu wani gida da mijinta yake dashi, kawai dan ta yaudareki ne, Kiyarda da ita.

Amma bakomai kanta tayi mawa, yanzu gashinan Allah ya daukaka ku, dama hausawa suna cewa hassada game rabo taki ce, nasan ayanzu Labiba kin dauki darussa da dama, domin ko babu Hauwa kema kina da naki halin.

Amma yanzu da kikaga duniya na tabbata kinkoyi darasi? Share hawayenta tayi tace haka ne Maman Zainab, wlh ayanzu nadauki darasi meyawa arayuwata, nasan idan Hauwa tana da laifi nima inadashi,

Na cutar da Dadyn Ansar sosai, kuma yayi hakuri dani, shiyasa ayanzu banida wani buri wanda yawuce insan duk wata hanya dazan faranta mashi, koda rayuwata zata kare gurin bauta mashi, bazan damu ba, inde zeyi farin ciki.

Ayanzu babu abinda yake damuna kamar yanda nake yawan mafarkin Babana, aduk sanda nayi mafarkinsa yakan cemun Labiba ina yan uwana, haka kawai yake cemun seya bace,

Kuma kinga ai banida laifi ko? Murmushi Maman Zainab tayi tace haka ne, bakida laifi amma manzon Allah yace duk wanda ya yarda zumunci aranar lahira idan ze tsallaka siradi igiyar zumunci seta kamoshi,

Dan haka idan har bakiso kizamo daya daga cikinsu kidage kinemi yan uwanki, koda zakije suna jifarki kada ki hakura, harse idan abun yayi yawa to wannan zaki iya kyalesu domin Allah yaga zuciyarki.

Labiba tace insha Allah zanyi kokarin ganin mundedeta tsakaninmu da yan uwana, nagode sosai da shawararki kuma zanzo domin ki kara koyamun yanda zan kula da mijina,

Domin ayanzu shine abinda ke gabana, dan yanzu Allah yabamu duniya, saura nikuma indage innemi aljannata agurin mijina. Maman Zainab tace karki damu, yanzu ma ga wasu littatafai nan nakawo maki kibisu daya bayan daya,

Inda baki ganeba ki kirani zan maki bayani. Amma kada kiyi sake da abincin mijinki, kinga de mijinki dan kasuwa ne, ba kowane dan kasuwa bane yake iya dawowa gida suci abinci rana ba.

Amma kidage ko direba ne kisa mijinki ya aje maki, kirika dafa mashi abinci yana kaimashi, hakan bakaramin kara maki daraja zeyi ba agurinshi, kuma sauran mazaje ma zasuyi sha,awar hakan har susa matansu suyi koyi dake.

Sannan duk wata kunya kicireta kirike mijinki, kingade yanzu yayi kudi yakara zama dan gayu, mata dayawa zasu rika kawo mashi kansu, kema sekin dage, shigar kananan kaya, kwalliya, sarrafa magana duk sekin koya,

Ke duk akwaisu acikin littafin nan, zaki sami komai, ada nasan bakiyima Abbas komai najin dadi ba, dan haka yanzu kidage, hakan zesa mijinki yadauke idonshi akan kowace mace, ba boka ba malam zaki siye zuciyar mijinki.

Labiba tace nagode sosai Allah yabar zumunci, insha Allah zanyi yadda kikace, zakisha mamaki na, shiyasa yanzu nima nadage kallo da karance karance bakaramin karuwa kuma nakeyi ba.

Maman Zainab tace bara inkira Baban Zainab, kinga dare yayi, waya tadauka takira mijinta yace aigashinan ma yakusa zuwa, dariya tayi tace sekazo abin alfaharina. Kallonta Labiba tayi tace maman Zainab manya,

Tace sosaima aiyanzu soyayya bata tsufa, duk wadda kikaga takoma baya agurin mijinta ita taso, dariya Labiba tayi ta tashi tace inazuwa to.

Sabulai da turaruka tahado mata, tana fitowa sukaji sallamar Abbas, amsawa Labiba tayi, zungurarta Maman Zainab tayi, murmushi tayi bata tashi ba, harara tasakar mata ahankali tace bazaki tashi ba?

Murmushi tayi ta tashi taje ta rungumeshi tana fadin sannu dazuwa megidana na kaina abin alfaharina, kara matseta yayi yace yauwa amaryata, kallonshi tayi tace yaude anboyemun kai,

Sakinta yayi yakamo hannunta suka shigo yana fadin ashe Maman Zainab tana gidan nan, yanzu mijinta ya tsaya kofar gidan nan, seda yafito naganeshi, shine yake cemun ai nan gidan yazo daukar matarshi.

Nace mashi ai gida nane, bakaramin mamaki yayi ba, yanzu haka yana falona, nace bara inzo inkirata, zama yayi, yana fadin sannu dazuwa Maman Zainab, tace yauwa Dadyn Ansar, mun wuni lafiya, yace lafiya lau,

Nan tayi mashi murna

Please Login or Register in order to submit comment