Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muryar megidanshi, ai besan lokacin daya saki kudin hannunshi ba, dukawa Abbas yayi yakwasho mashi yana fadin hankali kana zubar da kudinka.

Saddik kam yadauko wayarshi yataho gurin Auwal yana fadin abokina nifa nariga natsaya anan, kalla kagani idan tayi inbashi kudin dubu 250 yace ze saidata, nide ina........... Ai be karasa maganar ba ganin megidansu akusa da Auwal.

Gaba dayansu zare ido suka farayi, dan Auwal jiyake kamar yasaki fitsari agurin, sosai suka tsorata, basuyi tsammanin ganinsu anan ba, shiyasa ma Auwal yace suzo wannan kasuwar dan yasan babu abinda zesa suhadu da Alh, dan baya shiga irin wannan kasuwar.

Murmushi Alh, Abbah yayi yace Saddik ashe kaima kana nan, ni hankali na, duk yatashi yarana basuje aiki ba, ashe kuna nan kuna shagalinku, to muma munzo ayi damu.

Shiru sukayi, dan gaba dayansu zufa ta wanke masu fuska, maganar meshago ce tadawo da hankalinsu, yace dan Allah kabani kudina sekucigaba da maganarku kabarni inajira.

Alh, yace kabashi kudinshi tafiya zamuyi dama wani abu mukazo dubawa kuma munsamu zamu wuce muka ganku shine mukazo, idan kungama kuzo muwuce office ko?.

Hawaye ne, suka fara zuboma Auwal, cike da nadama yakalli Alh, yace dan Allah kayi hakuri karufa mana asiri wlh zanyi maka bayanin amma kada katona mana asiri acikin jama,a.

Alh, yace dan Allah kayi shiru, niban tambayeka komai ba, kabashi kudinshi mutafi, kallon meshagon Auwal yayi yace dan Allah kayi hakuri mun bata maka lokaci, munfasa sayan wayar kayi hakuri dan Allah.

Meshago yace bakomai, tunda bakutafi ba, shima Saddik jin haka yasa yajuya yamaida ma meshagon wayar shi. Murmushi Alh, yayi yaja hannun Abbas suka nufi mota, yace kuzo mutafi.

Kamar munafukai suka bi bayansu kowa sedafe aljihu yakeyi, haka suka zauna acikin mota kamar kurame, wani guri daban sukaga Alh, yanufa ba hanyar office ba.

Kuka Auwal yasa yana fadin dan girman Allah megida kayi hakuri kada ka kaimu police station, wlh zanyi maka bayani, kuma kudinka ko kwandala basuyi ciwo ba, yanzu haka muje gida indauko maka sauran, dama dede na wayar muka dauko nida Saddik, dan Allah kayi hakuri.

Murmushi Alh, yayi yajuya kan motar suka nufi Fage, suna zuwa Auwal yafita segashi yafito da wata leda, yana zuwa suka tafi, sede duk da haka Alh, be nufi office ba, can wani guri suka nufa wani filinshi acan yayi parking, yajuyo yana kallonsu, yace Auwal inajinka banason boye boye kafadamun komai.

Ajiyar zuciya Auwal yayi yace wlh lokacin da Abbas yashigo Office dinka da kudin,duk maganar da kukayi naji hakan yasa na labe har seda naga inda Abbas ya ajiye kudin.

Alokacin da yafita yace akulle kofa ankira sallah, alokacin nayi saurin dibar kudin, kuma cikin sa,a har na dauki million 2, anan nayi saurin fita mukatafi masallaci tare da Abbas, kuma sanda muka idar da sallah narike Saddik mune karshen dawowa office din.

Dama agaskiya nida Saddik mun dade muna so muga mun kullama Abbas sharrin dazesa akoreshi daga aiki, amma bama samun nasara akanshi, ninasan mundade muna maka sata a office, kuma baka taba magana ba.

Dan Allah kuyi hakuri, ni nayarda ka koremu a aiki amma dan Allah kada ka kaimu gurin yan sanda, wlh nasan Babana tsinemun zeyi, tun ranar dana samu aikin nan kullum idan zanfita seyace kada inbari inyi wani abu dazan jawo mashi magana, idan har hakan tafaru, wlh bazan yafe maka ba.

Dan Allah kada kabari mahaifina yaji wannan maganar, nasan inde aka kulleni dole yasamu labari. Saddik yace dan Allah megida kayi hakuri, tabbas munyi kuskure amma wlh, wlh, wlh, kaji nayi maka rantsuwa 3, daga yau mundena aikata duk wani abu marar kyau, amma karufa mana asiri bazamu kara ba.

Abbas kuwa kuka kawai yakeyi,Alh, yace shikenan yanzu hadamun kudin kabani, kuma inaso kusani nibazan koreku ba, zamu cigaba da aiki tare, kuma insha Allah kamar yanda mukayi maganar nan mu 4 babu wanda zejita se idan kune kuka fada.

Kuma banaso afadama kowa angano kudin, nida kaina zanyima sauran bayani, nide tagurina nayafe maku, amma inaso kuji tsoron Allah, bawai zanbarku kucigaba da zama dani bane sbd ina tsoronku, nayi hakane kawai dan in nuna maku ba,a kyamar mutum dan yayi wani abu marar kyau.

Nasan idan nakoreku zaku iya shiga wani hali, kaga anyi ba,a yiba amma idan har halinku ne, wata rana zaku kara sede alokacin wlh ba mutanan office kadai zasu jiba, kotu zan kaiku yanda kowa zesan halinku.

Yanzu seku nemi yafiyar Abbas, dan kun cutar dashi. Kallon Abbas sukayi sukace yayi hakuri. Abbas yace bakomai shi yayafe masu, haka suka nufi office cike da kunya.

Suna zuwa Alh, yatara duka yaranshi anan yace masu dazu abokinshi baturen nan yasameshi da wadannan kudin yamaido mashi yana bashi hakuri ashe acikin motarshi kudin suka zube, shine yamai domin wanda nabashi kuma yace abaku hakuri da Abbas yaja maku bacin rai.

Hamdala kowa yafari, anan wadan da sukace abinciki Abbas suka fara bashi hakuri, shikam mamakin irin halin kirki na Alh, yakeyi, sukansu su Auwal sunyi mamakin abinda yace. Anan kowa ya yafi kowa aka koma aiki, sede haryanzu su Auwal sunkasa sakewa, ganin haka yasa Alh, yace idan baku sake ba,


Zakusa kowa yafara zarginku, haka suka saki jikinsu, sede tsakaninsu da Alh, da Abbas sun koma tamkar surukai, Auwal kuwa yaran shagon sunfara mamakin canjin dasu kagani daga gareshi sam yadena masu fadan dayake masu, yakoma tamkar bashi ba.

Bayan Abbas yadawo gida yafada ma su Ummanshi abinda yafaru, sosai sukaji dadin abun, Umma tace ai Allah baya bacci inde kadage kamaida al,amuranka gareshi tabbas zekareka. Allah yakara karemu daga sharrin mahassada.

Haka Abbas yacigaba da aiki agurin Alh, hankali kwance,yakara samun daukaka akan mutane, yaran office dinsu sosai suke bashi girmanshi dan yakawo cigaba sosai a kasuwar.

Haka suka cigaba da renon cikin Labiba kuma arzikinshi sosai yake karuwa dan albashi metsoka Al, yake bashi, hakan yasa asusun dayakeyi yakaru, itama Labiba tana asusu, sam yanzu tayi hakuri darashin cin dadi, sede cikin datake dashi yasa akullum Abbas seya siyo mata nama da kayan marmari.

Alokacin da cikinta yacika wata 9 duk wata siyayya Abbas yayi mata, hatta da ragon suna yasiya ya turkeshi, duk wani abu daza,a nema yasiya, dan ayanzu yahana Ummanshi yin abincin saidawa sede duk wani abu da ake amfani dashi ya saro masu, ita da Labiba.

Umma da kanta taraba masu kowa da abinda zerika saidawa, idan akazo siyan wani abu idan Umma kesaidashi ita zata basu, idan kuma Labiba ce gurinta za,aje. Sosai sukejin dadin zamansu, dama shi Umar kasuwar kwari yake tafiya.

Saboda yawan Customers da Abbas yake dasu hakan yasa Alh, yace yanaso shima yabude mashi nashi office din, Abbas yace a,a Alh, kabarni incigaba da aiki akasanka, hakan ma ya isheni inajin dadin zama da kai.

Alh, yace ai ba rabuwa zamuyi ba, inaso nida kai mukara daukaka kasuwancinmu, karka damu wlh na daukeka tamkar jinina, kana da amana, karka damu akwai wani zabe ma daza,ayi mutane dayawa suna son infito amma ni kuma nafison intsaidaka, danni bana son mulki ko kadan,

Kuma gaka bana zama sosai. Abbas yace amma Alh, ina tsoron mutanan gurin nan kalli fa yanda suke nuna maka kiyayya afili, nide ina tsoro wlh. Murmushi yayi yace kada kadamu, banayin abu da ka, aduk lokacin dazanyi wani abu, sena fara neman yarda daga gurin Allah, dan haka nabaka nan da sati 1, kaje kafara tsayuwar dare, nima zan tayaka, danni bazance banasa amun rokon Allah ba.

Ina sawa amma gaskiya nafiyi da kaina domin nine me neman bukatar, dan haka mudage muyi wannan istaharan idan har akwai alkhairi aciki insha Allah zamu gani, amma banaso kafadama kowa, senan da sati 1. Godiya Abbas yayi mashi sannan suka tafi.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
( Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 45 🔱 50

Bayan sati daya dayin maganarsu shida Alh, Abbah suna zaune a office wasu manyan mutane suka shigo office din, abokanan kasuwancin Alh, ne kuma suna daya daga cikin wadan da suka fito zaben daza,ayi.

Bayan sun gaisa daya daga cikinsu yakalli Abbas yace bawan Allah idan bazaka damu ba kabamu guri zamuyi magana da megidanka. Har yatashi Alh, yace karku damu PA nane, zaku iya maganarku.

Abbas yace a,a Alh, bara inje dama akwai abinda zamuyi nidasu Auwal, Murmushi Alh, yayi yace shikenan. Bayan yafita yajuyo gurinsu yana fadin inajinku.

Gyara zama,sukayi daya daga cikinsu yafara magana. Dama bawani abu bane yakawo,mu gurinka, munsan de kasan nida Alh Bashir munfito cikin wadanda zasuyi takara, wato ta chairman din Wapa.

Kuma inaso Alh, Bashir yasamu shiyasa na barmashi sauran jama,ata kaga zesamu kuri,a. To munsamu labarin kaima ba kaine zaka anshi mukamin ba, sede haryanzu bamu san wanda kake tayawa ba.

Shine mukazo muroke ka kabarma Alh, Bashir mutanenka ko nawa ne zamu baka. Murmushi Alh, Abbah yayi yace tonaji bayaninku, sede inaso kusani niba saboda kudi nace zanyi wannan zaben ba.

Kuma shima ba saboda kudi zerike mukamin ba, kawai nazabeshi ne saboda can cantarshi. Dan haka ina ganin babu kudin dazasu saka inbama wani kuri,ar mutane na. Inafatan kun fahimci abinda nake nufi?

Shiru sukayi gaba daya ransu yagama baci, babu kamar Alh, Bashir dama shi beyi niyar zuwa ba, hakanan yabi shawarar abokinsa sukazo, tashi yayi yana huci yakalli abokinshi yace katashi mutafi, dama ai nafada maka Alh, Abbah baya cikin irin mutanan dazaka nemi alfarma agurinsu.

Fita yayi abokin yabishi abaya. Murmushi Alh, Abbah yayi, dan ya riga yasan wanene Alh, Bashir, waya yadaga yakira Abbas, yana zuwa yafada mashi yanda sukayi, gaba daya jikin Abbas yagama sanyi.

Kallon Alh, yayi yace wlh dama nafada maka ni bana son wannan mukamin, kawai kabar masu, banason ina zamana nida iyalai na wani abu yazo yasame mu, wlh Alh, bakasan irin wahalar dana sha arayuwata tabaya ba, shiyasa yanzu dana samu wannan aikin nake jin dadi sosai, kuma ina alfahari dashi.

Banaso sanadiyar wannan zaben nazo narasa aikina gaba daya, ko kuma wani abu yasameni. Murmushi Alh, yayi yace karka damu Abbas, insha Allahu babu abinda ze faru, kada kamanta kafin mufara wannan zaben seda muka nemi yardar Allah sannan.

Banaso kasaka tsoro acikin ranka, idan har mutum yana neman wani abu, kuma yamika al,amuranshi agurin Allah, to abinda yafi kawai kayarda cewa babu wanda ya isa yayi maka wani abu se Allah.

Idan kuma har kaga bamu sami wannan mukami ba, to kadauka daga Allah ne, kada kayi zargin wani dan adam ze iya baka ko ya hanaka. Ka tsaida zuciyarka aguri daya Allah yana tare damu.

Ajiyar zuciya Abbas yayi yace shikenan nagode Allah yashige mana gaba. Wayarshi ce tayi kara, yana dagawa yaga Ummanshi ce, saurin dauka yayi, bayan sun gaisa take fada mashi yazo asibiti ankawo Labiba zata haihu.

Yana ajiyewa Alh, yace yade Abbas naga kamar akwai matsala ko? Kai yadaga mashi yana fadin wlh Labiba ce akace ankaita asibiti zata haihu. Saurin tashi Alh, yayi yace to ai semuyi sauri muje kada anemi wani abu.

Sallama sukayi ma su Auwal suka tafi, koda sukaje harta haihu, anma kaisu dakin hutu, suna zuwa suka sameta ita da danta cikin koshin lafiya.

Sosai Abbas yayi murna ganin Labibanshi ta haifa mashi yaro me kyau, yana kama dashi sosai, atare suka shiga da Alh, shima yatayashi murna, Abbas yadauki yaron yayi mashi huduba sannan yamikama Alh.

Addu,a shima yayi mashi yacema Abbas suje gurin likita subiya kudaden da aka biyosu. Bayan sungama da likita yace ai zasu iya tafiya tunda dukansu suna lafiya.

Haka suka hada kayansu suka nufi gida amotar Alh, amota Umma se godiya takema Alh, Abbah akan irin abinda yakema Abbas, addu,a kam yashata, sosai yaji dadi, har seda kwalla tazubo mashi, daya tuna mahaifiyarshi wadda ta dade da rasuwa.

Har kofar gida yakaisu, sosai ya tausaya ma Abbas, ganin irin gidan dasuke zama, kamar daga sama yaji Umma tace Alh, kashigo mana, haka yabi bayan Abbas suka shiga.

Bayan sun shiga gidan zuciyarshi takara tsinkewa da tausayin su, afalon Umma suka zauna, ita kuma Labiba Umma tace suje dakinta, ganin sun nufi dakinta yasa Alh, yagane nan dakin Umma ne.

Yadan jima Umma takawo masu abinci, bayan sungama yace ma Abbas ze koma. Dubu hamsin ya ajemasu, sosai sukayi godiya yace seya dawo anjima da iyalanshi suma suzo ganin jariri. Har mota Abbas yarakashi, yana fadin anjima zezo. Alh, yace a,a yabari se gobe.

Da yamma haka Alh, Abbah yazo da iyalinshi motarshi cike da kayan abinci sosai su Umma sukaji dadin zuwanshi, itama matarshi dubu 20 tabama Labiba, haka sukayi tamasu godiya, suka tafi.

Ranar suna Abbas yasama yaron sunan Alh, Abbah na gaskiya wato Hassan, ana kiranshi da Ansar, sosai Alh, Abbah yaji dadin karar da Abbas yayi mashi, haka yasiyama yaron kaya masu kyau, shida mamanshi, hatta Umma seda yasiya mata kaya, Abbas kuwa kudi yabashi dubu 100.

Yan gurin aikinsu ma kudi suka hada dazasu zo ganin jariri suka kawo, Abbas yaji dadin abinda sukayi mashi. Haka ya hada masu kayan suna yabasu. Ba laifi sunan yayi taro, yan uwan Labiba ma sunzo. Maman zainab itama da yamma sosai tazo sunan, domin Labiba tafada mata. Labiba sosai taji dadin zuwanta haka suka shiga daki.

Bayan sungama gaisawa Maman zainab take cemata ai suma suntashi. Labiba tace Allah Sarki inasu Asabe da Laraba? Maman zainab tace wlh tun bayan tafiyarki suka koma abin tausayi, sosai muke shiri dasu, baki gani ba sunkoma makarantar islamiyya duk wannan halin banzar sun dena, sede matsala daya su duka suke fuskanta.

Daga gurin maza jensu, kinsan dama yan kasuwa ne, ranar kawai sega mijin Laraba yadawo gida abuge, haka yakamata yayi mata shegen duka, da kyar aka kwaceta. Da safe tazo tana fadamun ita gidansu zata tafi haka nayita bata hakuri, nace idan ta tafi ya, yanta kuma batasan wadda zatazo tarike mata suba.

Da kyar nasamu ta hakura, bayan kwana biyu kuma aka kama mijin Asabe yashiga dakin wata mata abayan layinmu, ashe dama sun dade suna aikata masha,arsu, aranar Allah yatonu asirinsu.

Seda aka kulleshi da kyar aka bada belinshi, itama tace zata tafi haka mukai ta bata hakuri. Alokacin Baban Zainab ya hada kudin gidanshi, haka nayi masu sallama se kuka sukeyi, ni kaina seda nayi kuka, haka muka rabu.

Yanzu kam Alhamdulillah babu laifi arzikin mijina yafara dawowa, shiyasa duk wata hanya danasan zata kawo mashi cigaba nake nema mashi, domin nice sanadiyar shigarmu halin da muke ciki.

Yanzu haka nadage da sana,a kudi komin kadan dinsu, bana kashewa ina ajiye wasu a asusu. Wlh, Labiba nakoyi darasi sosai arayuwata, duk yanda kaga mijinka yana da abu kada ka rainashi, kayi kokarin tayashi son abun, se Allah ya buda maku nan gaba. Da banyi rashin hakuri ba, da yanzu arzikin mijina yafi na yanzu.

Amma gashi nan yanzu munkoma baya, ina addu,ar Allah ya kara karemu daga zaman Haya. Labiba ta goge kwallan dasuka zubo mata tace amin. Maman Zainab tace Labiba kince duk ranar damuka hadu zaki bani labarinki.

Murmushi Labiba tayi tace, kiyi hkr, kinga yanzu akwai mutane, kuma dare yafarayi, nasan Abbas yakusa shigowa. Inaso infara tambayar Abbas idan har ya yarda duk ranar da kika kara zuwa zanbaki labarina nida Abbas.

Maman Zainab tayi murmushi tace bakomai, amma akwai gyaran danakeso inmaki, haba Labiba kamar ba auren soyayya kukayi keda mijinki ba, kuma gashi de ku yan zamani ne, bare ace mutanan da ne. Ai yakamata ki canza ma mijinki suna, tunda kukayi aure yakamata ace kindena kiranshi da Abbas.

Idan kuma kun haihu se ki kara canza mashi suna kamar yanda kikaji ina fada ma Baban Zainab. Kinga dayawa mutane yanzu zakiga ya,yansu suna kiran iyayensu da sunansu, kuma hakan yana samo asali tundaga gurin iyayen.

Yanzu tunda kun haihu yakamata kirika kiran Abbas da Abban Ansar, kinga idan ya girma shima da Abba zerika kiranshi, kema kifada mashi yakiraki da Momyn Ansar ko kuma wani suna. Hakan zesa yaranku surika kiranku dasunan dakuke fada.

Labiba tace nagode Maman Zainab inasha Allah zan gyara kuskuren danayi, ada nadauka badole bane seka canza ma mijinka suna ba, wlh kunya nakeji shiyasaya nakasa canza mashi suna.

Murmushi Maman Zainab tayi tace lallai Labiba naga akwai abubuwa dayawa daya kamata ace kin sansu amma kuma gashi ina ganin baki sansu ba, ai ita rayuwar aure tasha bam bam da rayuwar gida, duk min son da mijinki yake maki dole sekin bada taki gudummuwar sonki zekara shiga zuciyarshi.

Amma bakomai, insha Allah namaki alkawarin duk sanda nasake zuwa zan kawo maki abubuwa dayawa wadan da zakiji dadinsu, kuma zan sawo maki littatafai kamar su Gyara da kanki, Sirrin Mijina, harma da na koyon girki, domin girki shine mace.

Kada kiga kin iya miya, tuwo, dafa shinkafa da iya saka magi amiya kice kin iya girki, akwai sauran girke girke daya kamata ace kinkoya, kada kice wai bakuda hali, yanzu kam mijinki nasan shima duniya tafara canza mashi.

Bakisan meze zama nan gaba ba, ke koma bakuyi kudi ba, zaki iya sarrafa maku abinci masu rai da lafiya, mata dayawa suna kuskure suna ganin dole semasu kudi ne, zasu iya yima mazajensu kalar abinci me dadi.

Ko Fulawa kadai kike da ita zaki iya sarrafata, yanzu in tambayeki, dame dame kika iya na Fulawa? Sosa kai Labiba tayi tace ito na iya cincin, wainar fulawa se dan waken fulawa. Dariya Maman zainab tayi tace lallai kam, kinada aiki.

Kin ganni nan, bawai seda nayi aure na iya abinci ba, tun kafin nayi aure nake zuwa gidan wata makwabciyar mu, dayake mijinta yanada hali, hakan yasa nake zuwa, inde naga zata shiga kitchen ina rokonta tabarni inbita.

Da farko taji tsoro, amma dataga inason koyon girki ne, hakan yasa tajani ajiki tarika koyamun girki da yanda zan gyara jikina, alokacin da zanyi aure, bakiga irin littattafan data bani ba, duk da nasan ba me kudi zan aura ba, hakan besa na zubar dasu ba.

Amma kibari yanzu magriba tayi, duk ranar danazo zakisha mamaki na, amma matsala daya ce, bazan dawo nan kusa ba, saboda Baban Zainab yace wannan karon idan yaje Lagos ze dade sosai, megidanshi yace zasuyi yawo shine yace yataho da iyalanshi akwai boys Quarters dinshi semu zauna.

To gaskiya bansan yaushe zamu dawo ba, amma ai akwai waya, kome kenan zakiji. Sosai Labiba tayima Maman Zainab murna, kuma taji dadin shawarar data bata, haka tahada mata kayan suna sukayi sallama, har kuka seda sukayi.

Bayan suna da sati daya aka tsaida ranar zaben su Abbas, sosai hankalinshi yatashi, musamman daya tuna kashedin dasu Alh, Bashir sukayi mashi, dan tuni sungano cewar shine Alh, Abbah yake nemama kujerar, hakan yasa sukayi mashi kashedi, sede Alh, Abbah yace kada yadamu.

An tsaida zabe ranar asabar, duk wanda yaga Abbas yasan baya cikin natsuwarshi, abinci ma baya iya ci sosai, duk yarame. Bawai mulkin yake tsoro ba, barazanar dasu Alh, Bashir suke mashi ce take damunshi. Ana gobe zabe Abbas yadawo daga office, dan yau batare da Alh, suka taho ba, yana cikin adedeta kawai yaga me adedetan yawuce hanyar unguwarsu.

Kallonshi yayi yace malam bakaji menace maka ba? Darmanawa nace amma naga kawuce, waigowar da me adedeta zeyi kawai ya hura mashi wani abu afuska, nan take Abbas yafara ganin dishi dishi, anan ya kwanta asume cikin adedeta, dariya me adedata yayi yakira waya yana fadin Alh, nagama aikina, gashi nan zankawoshi inda kace. Shiru yayi sekuma yace e akwai mukulli agurina. Kashe wayar yayi yana dariya.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 50 🔱 55

Cike da mamaki Alh, Abbah yabi adedetar da Abbas yake ciki da kallo, saboda alokacin da Abbas ya hau adedeta shi kuma Alh, yafito yana bayanshi, har suka hau kan titi yana binsu abaya.

Lokacin da akazo kwanar daza,a shiga da Abbas ta Gandun Sarki, shi kuma Alh, ze wuce gidanshi dayake can gaba dasu, ganin adedetar bata shiga kwanar ba, ta wuce shine abun yabashi mamaki, gashi de yaga yamma tayi.

Aranshi yake fadin Abbas ko wani guri zeje? Haka yabi bayansu har sukazo kwanar dazata sadashi da gidanshi, seyaga sun wuce, har yashiga kwanar tacikin madubi yaga kamar Abbas akwance yake acikin adedetar.

Jikinshi ne, be bashi ba, hakan yasa yayi saurin juya kan motarshi yabi bayansu, mamaki ne yakara kamashi ganin yanda me adedetar yake wani irin gudu gashi yasauka daga titi yadauki hanyar wani guri.

Ganin abun yaki karewa yasa kawai Alh, yadauki waya yakira police, anan yayi masu kwatancen inda yake, yace zerika fada masu duk inda yayi, kashe wayar yayi yacigaba dabin bayansu.

Mamakinshi be karuba seda yaga sunshiga wani gate wanda da kaganshi kasan fili ne, aka zagaye ba,ayi gini ba. Matsawa yayi daga gaban gidan yayi parking.

Zuwa yanzu hankalinshi yagama tashi, waya yakira yakarayi masu kwatancen inda yake, yana gamawa yaga wata bakar mota tazo gaban gidan, budewar gate din keda wuya yaga anshiga da motar.

Wata zufa ce tafara fitoma Alh, aranshi yake tunanin kode yan yankan kai ne? Shiru yazauna azuciyarshi se addu,a yakeyi akan Allah yakare Abbas daga dukkan sharri.

Adede lokacin motar yan sanda ta iso, fita yayi, yasa mesu, anan yayi masu bayanin abinda yagani, ogansu yace karka damu insha Allah zamu kamasu.

Anan ya raba yaranshi suka zagaye gidan, shikuma shida wasu mutum 3 suka bi bayanshi, Alh, cike da fargaba shima yabi bayansu. Kwan kwasa kofar ogan yayi, anan megadin yafito.

Yana ganin yan sanda cikinshi ya kada, da sauri yayi niyar komawa ciki, anan wani dan sanda yayi saurin cafkoshi, se zare ido yakeyi. Murmushi ogan yayi yace kana tunanin guduwa ne? Kai yashiga girgizawa.

Ogan yace ina megidanka yake? Yace suna ciki, dan Allah kuyi hakuri, tasa keyarshi sukayi yashiga nuna masu hanya. Mamaki sosai sukayi ganin katon filin dayake zagaye.

Abbas kuwa bawan Allah suna zuwa Alh, Bashir yasa aka daureshi jikin wata bishiya, ruwan sanyi yasa aka dauko mashi amota, tundaga kan Abbas yafara zuba ruwan me bala,in sanyi.

Cike da firgici Abbas ya farfado, gaba daya jikinshi rawa yakeyi, begama wartsakewa ba yaji saukar wani katon icce akanshi, nan take jini ya wanke mashi fuska. Dariya Sukayi, Alh, Bashir yace da kadauka wasa nakeyi maka?

Uhm, kai yarone, kuma bako acikin harkar canji, shiyasa bakasan koni waye ba. Ayau zakayi asarar mahaifiyarka matarka da kuma danka. Kana tunanin bansan komai akanka bane? Da farko mahaifiyarka naso indauke da danka harseka yarda kabarmun matsayin danake nema sannan insake su.

Amma daga baya senayi tunanin gara indauke ka gaba daya daga duniyar, hakan zesa nadena ganinka gaba daya, dan nasan ko kabarmun wannan matsayin nan gaba Allah ze iya dagaka.

Amma idan ka mutu, nasan banida sauran fargaba. Kallon wani kato yayi wanda sukazo tare dashi, yace gama dashi, banason yakara ko minti 5 aduniya. Matsowa yayi hannunshi rike da igiya.

Yana zuwa yashake wuyan Abbas da ita, tuni Abbas ya runtse idonshi yafara kalmar shahada, kamar daga sama sukaji karar bindiga, cike da tsoro wannan katon yayi saurin sakin Abbas, wanda har yafara jin kamshin mutuwa.

Gaba dayansu tsoro ne ya bayyana azuciyarsu, Alh, Bashir kam da gudu ya nufi hanyar motarshi, wani dan sanda yaruga ya cafkeshi, sauran ma kamasu akayi, Alh, Abbah kam gurin Abbas yanufa hankalinshi atashe.

Yana zuwa ya kwanceshi, rungumoshi yayi, dan gaba daya jikinshi rawa yakeyi, ga kanshi dayake sarawa sosai, haka ogan yabasu umarni suka tasa keyarsu zuwa motar yan sanda.

Abokin Alh, Bashir se kuka yakeyi yana fadin shikenan Alh, kajamana, seda nace kada kayi wannan abu amma dayake zuciyar kafirci gareka bakaji maganata ba.

Tsawa ogan yadaka mashi, yana fadin kamana shiru koma menen idan mukaje office zakuyi bayani. Alh, Abbah kam zaunar da Abbas yayi yafita dauko motarshi.

Abakin gate suka hadu, yacema ogan su wuce office zekai Abbas asibiti idan sungama zezo, haka yaje yadauki Abbas suka nufi asibiti, sukuma suka wuce office din yan sanda.

Suna zuwa asibiti aka ansheshi, dressing ciwon aka fara yimashi sannan aka jona mashi ruwa, haka Alh, yakasa zaune duk tausayin Abbas yagama kamashi, aranshi yake fadin shikenan da bezoba sede suji akanshe Abbas.

Agida kam hankalin Labiba da Umma duk yatashi, ganin har magriba Abbas bedawo ba, haka suka rika kiran

Please Login or Register in order to submit comment