Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafada maki sirrinshi kema kiyi saurin fada mashi naki, yau kikasan wannan mata, duk dade naga tanada hankali, amma banyarda kifada mata labarinmu ba, har se nan gaba idan nakara karantarta.

Banaso labarinmu yazama ana fadinshi babu sirri, bakisan kila lokacin dazaki fada mata ko wani yanaji ba, yanzu kila babu wanda yasan labarinsu seke, amma gashi nima naji,

Kuma bakusan najiba. Dan Allah Labiba kada kiyarda kifada ma kowa labarinmu kinji my dear? Tace to yace yauwa muma Allah ze kawo mana mafita.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 10 🔱 15

Washe gari kamar yanda Abbas yace karfe 4:30 suka tashi, alokacin babu wanda ya motsa acikin gidan, haka sukayi wankansu suka gama, bayan sungama shiryawa sukayi nafila har aka kira sallah sannan yafita masallaci.

Seda gari yafara wayewa sannan yadawo, alokacin Laure da Laraba suna bakin toilet suna jiran yaron laure daya shiga bandaki, da ganinsu basuyi sallah ba.

Da kallo suka bishi har yashige, Laure tace kai Laraba amma wannan mutum yana da kyau, laure tace ashe kema kin gani, wlh tunda naganshi nima naji yatafi dani,

Ina ma ace dan hannu ne, ai da munshana. Laraba tace kai wannan yafi karfinmu kina ganinshi kinsan akwai ibada, ko kallonmu fa betaba yiba. Uhm kede ba,a nan take ba, kibarni dashi kawai kiyi kallo.

Da sallama yashiga Labiba tana kwance bacci yafara daukarta, zama yayi yace Labiba da alama bacci be isheki ba ko? Murmushi tayi tace wlh kuwa, yace to nima matsamun in kwanta tunda bada wuri zanfita kasuwar ba.

Hayaniyar yara da matan gidan ce ta hanasu baccin kirki, gurin karfe 7 suka tashi, Labiba ta dafe kanta tace wlh Abbas kaina ciwo yakemun, gsky mutanan nan suna shiga hakkinmu.

Abbas yace ai se hakuri, kinsan gidan haya yagaji haka, Allah de ya hore mana mubar masu gidansu, tace amin, bari intashi indora mana ruwan zafi, yace to bari inje insiyo mana biredi ga wasu kudi nan da Jafar yabani jiya. Tace bazaka shiga bandaki ba? Yace kai a,a idan nafita nashiga bandakin masallaci.

Acikin bokitinta tayi fitsari bayan tagama ta kunna rishow ta dora masu ruwan zafi, bayan tagama tajuyeshi a flask takai masu kofuna afalo, bayan yadawo suka karya,

Misalin karfe 8 yace bari yatafi kasuwa kada Jafar yajirashi, kallonshi tayi tace mezan dafa mana? Murmushi yayi yace kidafa abinda kikeso nasan se da yamma zandawo idan yaso sekiyi mana na dare tare.

Kudi yabata yace gashi kiyi cefane sekiyi mana miya kinga anjima seki dafa shinkafa, wannan kuma kisiyo kifi da salak. Murmushi tayi tace yauwa nagode, amma kuma kaga bansan wazan aika ba,

Sede infita da kaina. Yace a,a to bari inje insiyo maki kawai amma anjima idan zandawo inde nasamu kudi kawai zanyo mana siyayya sbd banason siyan abu cire cire, tace to. Fita yayi, dayake acikin unguwar akwai masu kayan miya,

Bayan yakawo mata yace kiyi sauri ki markada a blender kafin su dauke wutar, idan kuma sun dauke seki tambayi Maman Zainab inda ake kaiwa, tace adawo lafiya mijina. Murmushi yayi yace yau babu rakiya ko? Tace a,a naga yanzu gidan bamu kadai bane, yace koma mu nawa ne, ni bandamu ba, yanda muka saba kirakani haka zakimun.

Tashi tayi tasa hijabinta tabishi suka fita yana rike da hannunta, suna fita suka cikaro dasu Laraba, zaune acikin inuwa, ko kallonsu beyi ba, yajata har zaure sannan yayi mata kiss a kumatu yatafi.

Bayan tadawo ta matsa kusa dasu tace sannunku ina kwananku? Ya mutsa fuska sukayi sukace lafiya lau, bakuwa se yanzu muke ganinki? Daure fuska tayi tace tunda kun ganni yanzun ma ai ya wadatar, wucewa tayi abinta tashiga dakin Maman Zainab.

Laure tace kan uban nan kai yasa, ke Laraba, kinajin wannan kwailar yarinyar me kama da karas har mu zata kalla tafada ma wannan maganar? Laraba tace aini nama kasa magana.

Kuma kina ganin tashige dakin waccan munafukar, to wai yaushe ma ta santa? Laure tace kinsan halin munafuka, jiya ina kallon lokacin data shiga dakinta, kuma ta dade aciki har seda mijinta yadawo tafito.

Laraba tace lallai damu suke magana, har mu za,a yima bariki, ai duk wanda yasanmu a unguwar nan anan yasamemu, kuma dole muyi yanda muke so. Kibarni dasu, ninasan mezanyi masu.

Zaune suke akasuwa shida Jafar, dan tunkafin yazo Jafar yayima uban gidanshi magana kuma ya amince, ze dauki Abbas aiki adayan shagonshi, dan shima yatausaya mashi dayaji labarinshi.

Jafar yace Abbas ina sarkin rigima Labiba? Murmushi yayi yace baiwar Allah tana can, nasan kadaici ya isheta, gashi bamuda kayan kallo duk mun saida bare tayi kallo, amma insha Allah idan komai ya dedeta zan siyamata.

Kai Jafar ya girgiza yace wato Abbas har yanzu bazaka yima kanka fada ba ko? A tunanina yanzu base wani yabaka shawara akan abinda yakamata kayi da kudi ba, domin ayanzu kafi kowa sanin DARAJAR MUHALLI.

Murmushi Abbas yayi yace wlh nima Jafar ina son inga na mallaki MUHALLI na, badan kowa ba, sedan Labiba, amma kasan halinta yanda kasan ta taso gidan masu kudi kwata kwata batasan babu ba.

Kana gani ko abinci bata yarda taci marar dadi ba, shiyasa wani lokacin hakanan nake hakura inbata ita taci medadi, kasan irin son danake mata, wlh bana so inga nabata mata rai, gaba daya se inji nashiga damuwa.

Kasan mutane dayawa acikin abokanmu har cewa suke wai Labiba bata barni haka ba. Nikuma nasan ba haka bane, nida Labiba akwai so me tsanani atsakaninmu, sede nasan sona yafi nata sosai, duk da itama tanamun so dede gwargwado.


Jafar yace hakane, nima sheda ne,akan irin son da kukema junanku, sede duk da haka, kasan son da take maka, da wanda kake mata be kai son Uwa da danta ba. Idan har Uwa zata iya sa hannu ta duki danta, saboda ta gyara mashi kuskuren dayayi,

Ina ganin babu wanda zece dan batason shine ta dokeshi, tayi hakane dan kada tarbiyarshi ta lalace. Ina ganin kaima danka hana Labiba wani abu, baza,ace bakasonta bane, arayuwa dole se mutum yarasa sannan yake samu.

Idan har zakaji ta tawa kadaure ka koyi hanata abinda takeso, bance kada ka kyauta tamata ba, idan ace yau katashi da naira 100, to kuyi hakuri kusami abinda zakuci na naira 50 kai kuma karike 50 a aljihunka, sbd tsaran laruri, ko kuma kasata cikin asusu.

Kasuwa bata da tabbas, ba kullum,ne muke samu ba, kaga duk ranar da bamu samu ba, zaka iya daukar cikin wanda kake tarawa kuyi amfani dasu, idan kasamu seka maida, da haka mutum yake iya tara nakanshi.

Amma wlh duk wanda yace zebiyema mata, yana tare da wahala, idan kana cikin budi zaka iya yimata komai, idan kuma babu se ku hakura, hakan ze koya mata samu da rashi, kuma koda wata rana bakayi mata ba, zata maka uziri.

Amma tun farko kaine ka koya ma Labiba duk abinda take maka yanzu, amma haryanzu lokaci be kure maka ba, tunda ko haihuwar farko batayi ba, zaka iya daurewa ka gyara rayuwarku, duk da nasan zaka fuskanci matsala, amma na tabbata idan har son datake maka na gaskiya ne, zatayi fushi daga farko, amma daga baya dole ta sauko.

Jinjina kai Abbas yayi bece komai ba. Dafashi Jafar yayi yace zaka iya abokina, kadaure dan Allah kayimun wannan alfarmar inaso daga yau kazama namiji kamar yanda nasanka abaya kafin haduwarka da Labiba.

Wannna ita kadaice alfarmar dana keso awajenka, nasan banida sama da kai, kuma kaima haka, ina tsoron ranar da mutuwa zata daukeni inbarka cikin wannan halin, nasan duk duniya babu wanda ze iya fada maka irin gaskiyar danake fada maka.

Duk wani wanda zezo gurinka dan ya cuceka zezo, dan Allah Abbas,,,, kwalla ne suka zubo mashi daga ido, dasauri Abbas ya kalleshi yace haba Jafar meye na kuka, kayi hakuri, nasan aduk duniya banida sama da kai, ko Ummata ayanzu bazata yimun abinda kake mun ba.

Nasan son da kakemun daga Allah ne, haduwar jininmu, ma dagavAllah ne, na dade ina rokon Allah kada yakawo ranar dazaka rokeni wani abu ni kuma banida halin yimakashi.

Alhamdulillahi, nagodema Allah dayasa yau ka tambayeni alfarmar dazan iya maka. Ni ABBAS ALEE nayi ma abokina JAFAR alkawarin daga yau zan canza halina, zan koma asalin duk wani da namiji me zuciya.
Zanyi kokarin tara kudi na halak koda zan kasance banci me kyau ba, insha Allahu sena kara mallakar MUHALLI nawa na kaina.

Dariyar farin ciki Jafar yayi ya rungume Abbas harda kwallanshi yana fadin nagode abokina, Allah yabaka ikon cika alkawarin daka dauka, zanfi kowa farin ciki. Insha Allah sekazamo abin kwatance acikin abokanmu dasuka juya maka baya. Se duniya tayi alfahari da kai ko bayanzu ba. Tashi muje kada Alhaji yajika shiru.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 15 🔱 20

Misalin karfe 6 Abbas suka tashi daga kasuwa, dari 500 Alhajin yabashi, hakan yasa Jafar yasiyo mashi wani katon asusu, dari 300 yabashi,yasaka 200 acikin asusun.

Cefane yayi masu na kayan miya na naira 50 yawuce gida bayan sunyi sallama da Jafar. Kafin yaje gida ankira magriba, hakan yasa seda ya tsaya masallacin unguwarsu yayi sallah sannan yashiga gida.


Kamar kullum suna zaune tsakar gida suna sana,ar tasu, da sallama yashiga yana ganinsu yayi saurin dauke kashi dan wasu kananan kayane ajikin Laraba, kanta ko dankwali babu, dasauri Laraba tace sannu da zuwa.

Ko kallon inda take beyi ba, yashige falo, dariya Laure tayi tace ai nafada maki wannan mutumin baze taba kulaki ba, shiyasa ma na hakura. Laraba tace wlh bazan hakura ba, inde muna cikin gidan nan zakiga yanda zanyi dashi, ai kowama ya iya kissa.

Abisa sallaya yasameta tana addu,a zama yayi harseda ta idar sannan yashafa, tashi tayi tana cire hijabi tace sannu dazuwa Abbas ya kasuwa? Murmushi yayi tare da jawota jikinshi yace lafiya lau, Labiba ta.

Yazaman kadaici? Dariya tayi tace babu dan muna tare da maman Zainab munsha fira da kuma kallo, murmushi yayi yace nikam inaji maki tsoron mutanan gidan nan,

Fuskarshi ta shafa tace kada kadamu Maman Zainab bata da irin halin sauran mutanan, itama kanta guje masu takeyi, kuma ni nayaba da hankalinta, tana sona sosai, yace toshikenan Allah yatemaka, tace amin.

Tashi tayi takawo masu abinci, anan suka zauna sunaci, kallonshi tayi, dan taji shiru haryanzu befada mata nawa yasamo akasuwa ba, kamar yanda yasaba.

Abbas yau naji shiru, ko baka samu komai akasuwar bane? Kallonta yayi ta gefen ido yayi murmushi yace kasuwa lafiya lau mana, gashi kina ganin har cefane nayo mana na abincin gobe da rana.

Shiru tayi tana kallonshi, duk seya tsargu dan besaba yimata haka ba, Hannunta yakamo yace yade Labiba naji kinyi shiru? Hannunta tacire, tace wlh bakai bane Abbas, tabbas akwai abinda aka koya maka a kasuwa yau.

Murmushi yayi yace bangane me kike nufi ba? Shikenan kawai dan nace maki kasuwa lafiya ai bawani abu bane, dannace haka. Tashi tayi ta daure fuska tace shikenan yayi maka kyau, daki tashige aranta tana fadin nasan yanzu zaka biyoni.

Murnushi yayi yace insha Allah Jafar zan cika maka alkawarinka. Tashi yayi yanufi masallaci, domin yin sallar isha'i. Shiru taji be shigo ba, tashi tayi ta leka, amma bata ganshi ba.

Dawowa tayi gaba daya hankalinta yatashi, tace meke samun Abbas zeshigo mani da wani hali wanda besaba mani dashi ba? Kalli dan cefanan daya kawo mana,ko nama babu bare kifi, wanda ada bahaka yake mani ba.

Komin kadan din kudi yana siyo mani abun dadi inde ze dawo, lallai bari yashigo inji dalili, tashi tayi ta kabbara sallah.

Bayan yadawo sukayi shirin kwanciya har yanzu tana fushi dashi, shikam yamaki kallonta dan kada ta karyar mashi da zuciya.

Abbas,yaji takirashi, inajinki Labiba meyafaru? Wai meyasa naga kamar kacanzamun ne? Ada bahaka kasaba mun ba, baka boyemun komai, amma ayau naga kacanza meye dalili?

Bakomai Labiba, dan Allah kibarni inyi bacci gobe dawuri zanfita banason damuwa, juya mashi baya tayi tasa kuka. Saurin runtse ido yayi, domin kukan jiyake tamkar ana zuba mashi garwashi.

Shima juya mata baya yayi dan bemanta halin dasuke ciki ba, runtse ido yayi yanajinta tana kuka amma haka yashareta dan be manta alkawarin daya daukarma Jafar ba. Ganin beda niyar kulata yasa tayi shiru da haka bacci yadauketa.

Washe gari tunda asuba sukayi wanka bayan ankira sallah yafita masallaci, yana dawowa tagaishe shi ya ansa mata yana fadin Labiba rigima, baki ta turo tana dira kafa tahaye gado. Murmushi yayi shima yakwanta tare da jawota suka koma bacci.

Da gari yawaye yafita yasiyo masu biredi na 100 yana kawowa, Labiba tace haba Abbas kasan fa jiya biredi mukaci, kuma kasan bana iya jera kwana 2 ina cin biredi , nadauka ma zaka taho mani da dankali tunda haka kasaba mani, kuma naga kayan miyan basuda yawa kuma baka siyo nama ba.

Shiru yayi yana kallonta dan zuwa yanzu tabbas tafara bata mashi rai, wanda ada betaba jin hakan ba, kome ze kawo mata idan takusheshi bayajin haushi, amma ayau yafara jin haushinta. Wasu kwalla ne yaji suntaho mashi, ganin zata bata mashi rai kawai ya aje mata biredin yadauki wayarshi yayi waje.

Zama tayi ta buga tagumi duk setaji babu dadi aranta, domin tana ganin lokacin da idonshi yakawo ruwa, kwanciya tayi tasa kuka, dan duk abunta batason taga bacin ran Abbas, kasa karyawa tayi, ruwan tea kawai tasha ta kwanta.

Akasuwa kuwa Abbas duk wanda yaganshi yasan yana cikin damuwa, hakan yasa Jafar yajashi gefe guda yana tambayarshi, anan yafada mashi duk yanda sukayi da Labiba,

Sosai Jafar yaji dadi ganin abokinshi yafara canzawa, haka yayita kara mashi kwarin guiwa akan yakara daurewa komai zezo karshe, alokacin seya nuna mata duk wani jin dadi.

Abbas yace Jafar ina tsoron kada Labiba takasa daurewa tabarni, Jafar yace bazata taba barinka ba, domin kunama junanku so me tsanani, kaide kawai karika nuna mata bakadashi, bawai kayi shiru ka kyaleta babu bayani ba.

Idan kana fadi mata tunda akwai so zata rika tausaya maka. Dan Allah Abbas. Murmushi yayi yace shikenan Jafar, naji zan gyara, kuskuren da nayi shine dabanyi mata bayani ba. Dariya yayi yace nagode abokina.

Tun daga ranar Abbas yakara dagewa gurin canza tsarin rayuwarshi, domin yanason yaga yasamu nakanshi, kuma akullum yana nunama Labiba takara hakuri samunshi nayanzu bakamar na da bane,

Tun tana jaje, har tafara hakura, domin kota bata mashi rai, saboda son datake mashi bata iya dogon fushi dashi, kuma akoda yaushe Maman Zainab tana kara nuna mata halin rayuwa, hakan yasa tafara saukowa, domin itama tafara gajiya dazaman gidan.

Kwata kwata basa shiri dasu Laraba, shikam Abbas bawan Allah yana aiki sosai dan ganin yasamu yatara kudi masu yawa, har kaya yana daukar ma masu siya yana kai masu bakin mota, duk da Alhajin yana hanashi, dan gani yake kamar yayi girma dayin hakan.

Amma shi gani yakeyi yana samu da hakan, tunda kowa da irin alkhairin dayake mashi idan yayi mashi dako, sannan kuma ga kudin sallamar shi da Alhajin yake bashi, hakan yasa yanzu yake zuba kudi masu yawa a asusun shi, dan har 1000 yana sakawa.

Jafar ne, tsungunne gaban Mamanshi tana ta faman fada, da kai nake kanaji na kamun shiru, ko kana tunanin duk halin da kake ciki kaida abokinka banida labari? To wlh baka isa ba, bazan haifama wani daba,

Ita uwar tashi meyasa bazata jashi gidanta yazauna ba, se kaine zaka rika yawon kama mashi gida duk bayan shekara, to kaji namaka rantsuwa wlh yazo karshe, dama ai nadade dasawa arika dubamun kai,

Ina sane wannan shine gida na 2 daka kama mashi, yanzu kuma har kasuwa aka cemun ka kaishi gurin Alhaji kanaso yazo yafika arziki ne? Dan haka daga yau naraba wannan alakar datake tsakaninku.

Kai barima kaji inyi maka megaba daya, wlh, wlh, wlh. Daga yau idan nakarajin labarin anganka kaida Abbas Allah ya isa banyafe maka ba, kuma inaso kaje gurin megidan daka kama mashi haya agurinshi, ya lissafa kwanakin dayayi yacire kudinshi.

Yabaka sauran, kuma tunda Alhajin dan uwanane zanyi mashi magana karyakara barinshi yayi aiki agurinshi. Idan kuma bakaji ba, daga yau kamanta cewa kana da Uwa. Haka nan kai baka da zuciya, kajawo mutum jikinka yazo yafika arziki.

Kuka sosai Jafar yakeyi kamar karamin yaro, haka yafara rokonta amma sam taki ta saurareshi, shi babban damuwarshi ma yasan Abbas yana zaune kofar gida yana jiranshi,

Dan tunda suka shigo bayan sun gaisa mamanshi tace ma Abbas yajira awaje zatayi magana da danta. Shikam Abbas dama tunda yaji haka yasan akwai wani abu, dan dama yadade da sanin maman Jafar bata sonshi.

Jafar ganin bazata saurareshi ba yamike tsaye, yanufi hanyar fita, seda ya tsaya zaure ya goge fuskarshi sannan yafita, ita ko mamanshi tana ganin yafita tabishi zaure.

Abbas yanajin alamun fitowarshi shima yayi saurin goge idonshi, dan duk abinda sukeyi yajisu, Jafar yakaraso gurinshi yana murmushin karfin hali, yace yi hakuri abokina Mama ce take bani sako.

Uban sako nake baka munafuki, ubanka neshi dabazaka iya fada mashi abinda nace ba? To tsaya kaji Abbas kake kowa? Daga yau narabaka da Dana Jafar, tunda ba ciki daya kuka fito ba, idan har son dakake mashi na gaskiya ne, kuma kanason kada fushin Allah yahau kanshi to karabu dashi.

Dan wlh bazan yafe mashi ba, matukar yacigaba da kulaka, kuma kaje kanemi gurinzama domin zansa a anso mani sauran kudin hayar daya biya. Haka kawai kaje ka goga mashi kashin tsiya, yo inba kashin tsiya ba, haryanzu ka kasa Mallakar MUHALLINKA.

Wannan itace maganata ta karshe, da kai. Haka tajuya takoma gida, gaba dayansu kuka sukeyi, bakamar Jafar, jijiyoyin kanshi duk sun fito, da kyar Abbas ya tsaida kukanshi yadafa Jafar yace,

Abokina kada kadamu, ninasan aduk duniyar nan banida kamarka, kayi mani abinda babu wanda yataba munshi, wlh kanada matukar muhimmanci arayuwata, kuma bazan taba mantawa da kai ba.

Babu komai, zanyi kokarin yin nisa da kai, bazanso ace saboda ni kasamu matsala da mama ba, zaka iya canza ni, amma bazaka iya canzata ba, bakomai insha Allahu gobe zanbar gidan damuke, koma ina ne, zankoma da zama,

Kuma zanbar kasuwarku gaba daya zankoma wani gurin insamu wani aikin tayanda bazamurika haduwa ba, ina rokonka dan Allah aduk inda kaganni, kayi kokarin boyewa, nima zanyi haka,

Domin Mama tace bata yarda ka karamun magana ba, dan haka idan har kanaso inji dadi to kabi abinda Mama tace, kada ka kara nemana, har se ranar da mama da kanta tace kanemeni, nasan bazan taba wulakanta ba.

Allah yahada fuskokinmu da alkhairinsa. Kuka Abbas yasa sosai, Jafar ya rungumeshi suna kuka, Jafar yace wata alfarma 1 nakeso kamun Abbas, inaso ka koma gidan Umma, duk da nasan daki daya ne agidan,

Kaninka ma ashagon kofar gida yake kwana, amma nasan zaka samu yanda zakayi. Abbas yace zanje Jafar dole ne, canne kadai yaragemun inda yazamar mani dolena,amma bazan iya takura Ummata ba, zanje induba asusuna nasan yanzu suntaru da yawa.

Insha Allahu komun lalacewar gida zansamu muzauna kafin Allah yakawo mana wani budin. Jafar yace toyanzu wace kasuwa zaka koma? Abbas yace ayau zanyi tunanin amma bazakaji ba, dan banason kama fara nemana.

Sakinshi Abbas yayi yana fadin Allah yasadamu da alkhairi Jafar, juyawa yayi yana goge idonshi yafara tafiya, Jafar yace Abbas,,,, yana juyowa yace narokeka da girman Allah kada talauci ya rudi zuciyarka kafada wata harka, bazan taba yafe maka ba, idan kabi hanyar haram domin kaji dadi.

Abbas yayi murmushi hawaye suna zubo mashi yace namaka alkawarin kozan kwana banci ba, bazan ci haram ba. Nafiso ingina rayuwata da halal. Haka yajuya yatafi, harseda Jafar yaga ya bille sannan yaduke anan yasaki kuka meban tausayi.

Tafiya yakeyi acikin adedeta amma gaba daya hankalinshi baya jikinshi, seyanzu yake kara ganin wautarshi daya biyema soyayya da kuma mace yazabeta yabar MUHALLINSHI. Daya sha wahala kafin yasameshi.


Maganar dan adedeta yaji yana fadin malam munshi unguwar, kudinshi yaciro yabashi yafita, har anfara kiran magriba, hakan yasa yashiga masallaci, koda aka gama zama yayi, yana tunani, har akayi isha'i sannan yanufi gida.

Da sallamar shi yashiga, sede besamu kowa awaje ba, hakan yasa yashige dakinsu, zaune yasamu Labiba tana linkin kaya, sallama yayi mata tace sannu dazuwa Abbas, yau naga ka dade, uhm kawai yace mata yashige daki, domin yanajin kanshi kamar ze tsage.

Tashi tayi tabishi, akwance tasameshi, yana kalon sama, tsayawa tayi tace Abbas yanaga kashigo hannu biyu, bakasiyo komai ba, kuma dazu nace maka kasiyo mana abinci awaje dan nayi wanki nagaji banajin zan iya dora wani abinci,

Amma naga kashigo haka, kuma gashi ka kwanta, katashi kaje kasiyo mana ko awara ce to. Shiru yayi bece mata komai ba, tace Abbas da kaifa nake magana amma kamun....... saukar marin dataji ne,yasata kasa karasa maganar datakeyi.

Hannu 2 tasa tarike kuncinta, hawaye suna zuba daga idonta, kallonshi take cike da tsoro, dan gaba daya fuskarshi tacanza kamar ba Abbas din data sani ba.

Abbas, yau nika mara? Hannu yadaga zekara mata tayi saurin yin baya, yace wlh kika kara wata magana senayi maki abinda baki zato, haba, wannan wace irin masifa ce,duk kece sanadiyar jefani cikin wannan wulakantatar rayuwar.

Ya isheki hakanan,wlh yanda nakeji ayanzu zan iya daukar kowane mataki akanki, kinsan irin masifar danake ciki yanzu? Amma dayake bakida hankali nadawo kina ganin yanda nashigo zaki faramun wata maganar banza.

To idan bazaki dafa abinci ba, sede ki kwana da yunwa, amma babu inda zani, kuma bari kiji, idan har kinason cigaba da zama dani, dole kicanza halinki, duk wannan wahalar danakeyi danwa nakeyinta? Kina tunanin inda ni kadai ne, bazan iya rayuwa me dadi ba?

Kuma inaso ki,kwana da sani zuwa gobe zamu bar gidan nan, zamu koma can gidan Ummata, nabaki daga nan zuwa gobe, kiyankema kanki hukunci idan har zaki iya cigaba dazama dani.

Saurin rungumeshi tayi tana kuka, tace haba Abbas wace irin magana kake fada haka? Yau da bakinka kake fadin zaka rabu dani. Ina alkawarin dakamun? Kasan irin son danake maka bazan iya rayuwa idan babu kai ba.

Dan Allah kayi hakuri kayafemun. Kuka tasa takifa kanta saman kirjinshi, hannu yasa yakara rungumeta shima yana kukan, sun dade ahaka kafin yacireta suka zauna,

Hannunta yakama yace kiyi hakuri Labiba, yau na aikata maki abinda bantaba yimaki ba, ayau ina cikin damuwa, amma muje intayaki kisamu wani abu kidafa kici, kallonshi tayi tace kaifa? Kanshi ya girgiza yace banajin akwai abinda ze iya shiga cikina.

Itama tace nakoshi, bari indafa mana ruwan zafi musha lipton yace toshikenan. Kwanciya yayi yana kara jin haushin marin dayayi ma Labiba, tabbas ayau yasan bakaramin so Labiba take mashi ba. Bayan sungama shan tea suka kwanta, haka yabata labarin duk abinda yafaru.

Sosai take kuka, tace Abbas kayi hakuri da duk irin abinda namaka, tabbas nasan nice silar saka ka cikin wannan halin dakake. Amma wlh nayi nadama, kuma hakan bazata kara faruwa ba, rungumeta yayi yace bakomai karki damu kanki, wannan kaddara tace, ko babu ke tunda Allah yarubuta hakan zefaru dani to seya faru. Tace nagode megidana, kuma namaka alkawarin duk inda zaka kaini zanyi hakurin zama.

Washe gari da asuba, bayan angama yadawo gida, yana zuwa dede kofar dakin Laraba,yaji an saka ihu ana fadin nashiga 3 maciji, har yawuce yaji ancigaba da ihun, saurin daga labule yayi yashiga.

Yana shiga falon yaji anturo kofar, abinda be saniba dama Laraba tun jiya tashirya plan dinta ita da Laure, sanin mazajensu basa nan, hakan yasa ta tura yaranta dakin laure, tunda yafita masallaci take lekenshi,

Yana tahowa, tayi saurin shigewa daki, gashi babu wuta. Saurin juyawa yayi alokacin dayaji antura kofar, Laraba yagani babu ko kaya ajikinta tana nufoshi fuskarta dauke da murmushi, saurin rufe ido yayi yana karanta addu,ar neman tsari, ita kam kamar yana kara mata karfi, haka tanufo kanshi gadan gadan.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 20 🔱 25

Hannu yasa yadauketa da mari, anan

Please Login or Register in order to submit comment