Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da fatan alkhairi, tashi sukayi suka nufi falon Abbas, bayan sun gaisa shima yakara yimashi fatan alkhairi sukayi musayar number suka rakasu tare da alkawarin zasu zo.

Bayan sun koma Labiba ta hada mashi ruwan wanka, yace ai sekizo muyi tare ko? Tace to muje, murmushi yayi yana mamakin canjin dayake gani daga Labiba, ada yasan kafin suyi wanka tare seyasha fama amma ayanzu wasu abubuwa yake gani, haka suka shige bandaki dan suyi wanka.

Washe gari bayan yagama karyawa Labiba tace mashi tanason direba zata rika aikenshi, kallonta Abbas yayi yace amma ai mota daya ce agidan ko? Turo baki tayi tace nide to ko me adedeta ne, kasamu se arika biyanshi duk wata.

Dariya yayi yace Labiba rigima to wai mezaki da direban? Kwantawa tayi saman kafadarshi tace abincin rana zerika kaimaka banaso daga yau karika cin abinci awaje.

Murnushin jin dadi yayi yace ashema niza,ayima gata, nagode sosai My dear da irin kulawarki agareni, tabbas ayanzu nake bukatar kulawarki musamman dana kasance akoda yaushe cikin aiki,

Bakomai zanrika turowa adaukar mani, kafin Allah yakara budewa insayi wata motar, kinga idan akace za,a dauki me adedeta za,a bata mashi lokaci, idan lokacin daze dauki abinci yayi kuma baya kusa da gida kinga dole ze bata lokaci.

Amma idan turowa zanyi dakin gama sekimun waya kawai se inturoshi, dariya tayi tace yauwa nagode, yace nikeda godiya, muje mugaida Umma intafi kada in makara, wato yanzu de Ansar yadena kwana anan ko?

Dariya tayi tace ai yayeshi ma zanyi, yace dama yafi, kinga se asama mashi kanwa ko? Tashi tayi tashige daki tana murmushi, gyalenta ta dauko zuka wuce, bayan sungama gaisawa Abbas yace Umma kinji wai Labiba yaye Ansar zatayi.

Dariya Umma tayi tace nima haka nagama fada jiya, tunda yanacin komai, kuma baya shan nono da dare gara ayayeshi haka nan koyasamu kani ko kanwa, dariya Abbas yasa Labiba kuwa rufe fuska tayi.

Gyara zama Abbas yayi yace Umma anjima zandawo dawuri, zamuje gurin Kawu inaso muje da Labiba dashi Jigawa domin mugaida Iyayenta. Umma tace amma gaskiya kayi tunani, tunda su sunyarda zumunci gara kuje Allah zebaku ladar zumunci.

Kuma kema Labiba ai gara kije kigansu tunkafin ta Allah takasance, kada kidamu da duk abinda zasu maki, ayanzu tunda kinsamu arziki kitemaki yan uwanki Allah yanason meyin zumunci.

Abbas yace zamuyi waya da Kawu, anjima gurin karfe daya zandawo semutafi, Umma tace to Allah yakaimu, tashi yayi yace natafi Umma, addu,ar data saba yimashi akullum tayi mashi, tashi Labiba tayi dan tarakashi.

Murmushi Umma tayi aranta tace su Labiba anfara cire kunya kenan, amma ace dan kina gaba na bazaki iya raka mijinki ba, sekace kina cikin mutanan da, Allah ka kara hada kawunan wadannan yara nawa.

Bayan yaje Office yaje gurin Alh, Abbah, bayan sungaisa yake fada mashi ansamu fili babba miliyan daya da rabi, Abbas yace badamuwa yaya yayi, anjima zamuje jigawa munyi waya da Kawu yace semunzo,

Nasan kafin mudawo dare yayi zuwa gobe semuje abiya kudin ko? Murmushi Alh, Abbah yayi yace hakan ma yana da kyau, kuma naji dadi dazakuje, bakomai Allah yakaimu goben semuje.

Da karfe daya bayan yayi sallah yanufi gida, wanka yayi yaci abinci suka yima Umma sallama suka dauki Ansar suka nufi gidan Kawu, koda sukaje yashirya, haka suka dauki hanyar jigawa, Labiba da Kawunta gabansu se faduwa yakeyi dan basu san mezasu tarar ba.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 110 🔱 120

Mamaki ne, yakama kawu lokacin dasuka sauka gidan Yayansu, gaba daya ginin gidan ancanza shi, yakoma gidan yan gayu, gate din gidanma kanshi abin kallo ne,

Sauka sukayi suka kwankwasa gate din, wani mutum ne yafito, bayan sun gaisa Kawu yace dan Allah ko Yaya yana ciki? Kallon mamaki mutumin yayi masu yace wane yaya kuma? Abbas yace megidan muke tambaya.

Murmushi mutumin yayi yace ai megidan yana dubai shida iyalanshi, kuma senan da sati 2 zasu dawo, amma nayi mamakin da bansanku ba, kuma gashi har kuna kiranshi da Yaya?

Kawu ya goge zufar datake zubo mashi yace e Yaya nane uwarmu daya ubanmu daya, mutumin yace kai shifa wannan danake magana beda wa ko kani namiji, yan uwanshi duk mata ne, kuma bama anan suke zama sosai ba,

Aikine yakawoshi garin nan shine yasayi gidan nan agurin wani. Cike da mamaki Kawu yace ikon Allah, yi hakuri malam, wlh na dade banzo bane, bansan yasaida gidan ba, shikenan mungode bara muje can gidanmu mugani, sallama sukayi mashi suka tafi.

Labiba tace Kawu kode Abba yasamu budi ne har yasaida gidanshi kila wani yasaya? Murmushi Kawu yayi yace kila, ammade bara muje gida muji abinda yafaru.

Akofar gidan suka ci karo da mutane ana ta rigima, can kawu yahangi yan uwanshi guda 2 suna tayima Yayansu masifa, shi kuma yana zaune saman wata kujera kuka kawai yakeyi, ga mutane sunzagayeshi.

Cikin sauri kawu yaratsa tacikin mutanan ya isa gabansu, adede lokacin da wani kaninsu yakama kujerar yayansu yana shirin kadashi.

Rike kujerar yaji anyi, hakan yasa yayi saurin juyowa, cak ya tsaya ganin dan uwansu, Kawu yace haba Kabir mekakeyi haka? Kalli yanda kuka tara mutane akofar gidan nan, idan wata matsala ce tafaru ai yakamata ku tsaya cikin gida ku warwareta.

Amma yanzu kunfito kuna tonama kanku asiri, wanda aka kira da Kabir yace bazaka gane bane, wannan mutumin wane irin wulakanci ne beyi mana ba, lokacin yanada arziki shida matarshi da yaranshi,

Amma yanzu duniya tajuya mashi baya mun temakeshi shine zeyi mana rashin mutunci. Kawu yace ya isa dan Allah, yanzu tare mukeda sirikinku amma abun kunya munzo munsamu kuna fada.

Kallon mutanan gurin yayi yace dan Allah jama,a kowa yasan inda dare yayi mashi tunkafin inkira yansanda, ana fada kunkasa rabawa amma kunzo kuna kallon gulma, ai ko idasa rufe bakinshi beyi ba, kowa yakama gabanshi.

Kallon Yayansu yayi yace yaya tare mukeda baki kumu shiga ciki, haka yajuya yayima su Abbas iso suka shiga ciki, ababban falon gidan suka sauka, babu komai cikinshi se tabarma,

Kawu ne yabada aka siyo masu ruwa, bayan sungama gaisawa kawu yakalli Yayansu da tundazu beyi magana ba, se hawaye dasuke sintiri afuskarshi.

Yace Yaya wannan fa Labiba ce diyar marigayi Yaya Lawal, wannan kuma mijinta ne shine chairman na WAPA akano, wannan kuma dansu ne. Cike da mamaki kowa yabisu da ido yana kallonsu.

Kuka Yayansu yasaka, se alokacin yabude baki yayi magana, Labiba kece haka? Dan Allah kiyafemun, nasan na cutar dake, gashi ba,aje ko ina ba, hakkinki yafara tambayata,

Kalli yanda nakoma, banida komai, babu mata ba, yara babu gida, kuma duk wannan nasan yafaru ne, saboda hakkinki dana cinye, tabbas duk wanda yaci hakkin maraya se Allah ya tambayeshi, kuka yasaka.

Kawu ya kalli Kabir yace wai meyake faruwa haka? Gyara zama Kabir yayi yafara basu labarin abinda yafaru. Tun bayan da kazo mukayi fada akan Labiba, tun daga ranar shima Yaya yafara samun matsala,

Gaba daya kudinshi basa mashi albarka, matarshi da yaranshi inbanda sata babu abinda suke mashi,yaranshi maza gaba daya suka lalace da shaye shaye, matan kuma su 2 duka sukayi ciki, suka gudu.

Ahankali komai nashi yafara karewa, gashi ya aje aiki haka yaje yaciyo bashin banki yasayi mota kuma ya gyara gidanshi, mukammu seda mukayi mashi magana akan yabude shago da kudin yafi mashi,

Yayi mana wulakanci yace kudinshi ne bana wani ba, babu wanda yabama kudinshi dasuka fito, haka suka kashe shida matarshi, akwai lokacin da aka kwantar da yarona asibiti ana bukatar dubu 20, naje na tambayi Yaya amma seya koreni,

Yace shi kudinshi bana biyama mutane kudin asibiti bane, inaji ina gani yarona yarasu, tundaga ranar nadena zuwa gurinshi. Bayan wani lokaci matarshi ta sace mashi duka kudinshi ta kuma hada baki da wasu yanfashi akazo aka dauke motarshi.

Ta gudu, tundaga lokacin Yaya yazama wani iri, kuka kawai yakeyi, hankalinshi bekara tashi ba, seda banki tazo karbar kudinta, anan yashiga tashin hankali kuma banki baruwanta, haka tasa gidanshi kasuwa wani yasaya tadauki kudinta ta koreshi.

Shine yazo mute makeshi, ni kuma nace babu inda zan bashi yazauna, haka yayita bamu hakuri shine nace sede inbashi daki daya haya, kuma zan tausaya mashi yarika bada dubu 5, tofa shine yau sati 3 kenan ina mashi maganar biyan kudi amma daga karshe yafara mani fada, shine nikuma nace yabarmun gidana.

Ajiyar zuciya Kawu yayi yace ikon Allah, yaya Allah yakyauta gaba, damashi haka alhaki yake, gashi tunkafin aje ko ina Allah yanuna maka kuskurenka, kaima Kabir inamaka ta,aziyar danka, bansani ba,

Kodan kuncireni acikin yan uwanku saboda kawai son zuciya, kasa sukayi da kai, Kabir yace wlh ba haka bane, duk laifin Yaya ne, shine yake mana huduba akan mu kyaleka dan yaga kadauki Labiba shi kuma yana tunanin zaka iya kwatar mata hakkinta shiyasa yace muma murabu dakai,

Hakan zesa kashiga damuwa har ka kasa ansar mata hakkinta, amma wlh munyi dana sanin abinda muka aikata, gashi acikinmu babu wanda yasan gidanka akano, babu number waya hakan yasa bamu nemeka ba.

Amma dan Allah kayafe mana, kema Labiba kiyafe mana alhakinki yanata bibiyarmu, kudinmu basa mana albarka, kiyafe mana kozamu samu sauki.

Kawu yace bakomai Allah yayafe mana baki daya, dama haka rayuwa take, wanda ka raina wata rana shine yake maka rana, yanzu ku kalli Labiba ita kadai ta isa tazame maku ishara,

Wace irin wahalace baku bata ba, amma yanzu tana auren me kudi, sede Kabir akwai abinda banji dadinshi ba, koba komai Yaya dan uwammu ne, bamuda kamarshi aduniya, kome zemana bekamata kuyi mashi haka ba,

Meye daki daya? Ba daki ba, idan kanada hali gida ma zaka iya bashi, amma saboda zuciya wai seka anshi kudin hayarshi. Gaskiya banji dadin wannan abun ba, aduniya idan baka rufama dan uwanka asiri ba, babu wanda zaka rufamawa kaji dadi.

Kuma daga yau inde inada kaso acikin gidan nan to abama Yaya yazauna agurina bance yakara biyan komai ba, dukar da kai Kabir yayi yace kayi hakuri yaya insha Allah daga yau komai yawuce.

Mungode da tunatarwar daka mana, hakika dan uwa abin sone, munso mubiyema son zuciya kamar yanda Yaya yayi amma katunatar damu, kallon Yayansu yayi yace dan Allah yaya kayi hakuri da abinda mukayi maka.

Murmushi yayan yayi yace nikeda neman gafararku, na cutar daku amatsayinku na yan uwana wadan da muke ciki daya, ko Lawal wanda bamu fito ciki daya ba, betaba nuna mana bambanci ba, segashi nida nakasance babba acikinku nine azzalumin.

Kuyafemun dan Allah, mika hannu yayi yakarbi Ansar yana kuka, rungumeshi yayi yana fadin Labiba bakiyi magana ba, kiyafemun,wlh da ace inada kudi dazan biyaki kudinki dana cinye, amma ayanzu banida komi, wani lokacinma kudin abinci gagarata sukeyi.

Goge idonta tayi tace bakomai Abba nayafe maku Allah yamana gafara, kallon Abbas yayi yace mungode da yanda karike mana diya, koba,a fada ba munsan tana cikin kwanciyar hankali, Allah yabiyaka.

Abbas yace amin Abba,Kawu yace tomu zamu koma, nan da kwana 2 zandawo induba ku, hannu Abbas yasa yaciro kudi masu yawa yaraba masu, anan yace susa yara suzo sudaukar masu kayan abinci amota.

Godiya sukayi masu sosai, bayan sunfita Kawu ya kalli Kabir yace dan Allah kada ku kara barin Yaya yayi kuka, kuduka kuna da mata sekunbama yaya muhimmanci matanku zasu bashi, dande kwano daya so 3 arana dan Allah kudauke mashi.

Kabir yace insha Allah Yaya zaka dawo ka iske komai yacanza, zamu koma kamar da, Yaya baze kara kuka ba, komai ze canza, sosai kawu yaji dadi, haka shima yayi masu kyauta yafita, alokacin har ansauke kayan abincin haka suka tafi zuciyarsu cike da farin ciki.

Sosai Umma taji dadin abinda suka fada mata, kuma aranar aka yaye Ansar aka bama Ummashi yaye, su Abbas suka bude sabon shafin soyayya.

Washe gari su Abbas sukaje suka sayi fili shida Alh, Abbah, anan ne yake fada mashi yanda sukayi da yan uwan Labiba, shima yatausaya ma Yaya kuma yaji dadi dasuka shirya, bayan sunkarbi takardun fili duka shedu suka sa hannu,

Gidan Alh, Abbah sukaje, bayan sunci abinci mezanan gida yazo Abbas yazabi irin ginin dayake so,Alh, Abbah yace shikenan insha Allah gobe za,a fara zagaye filin. Tashi sukayi suka koma office.

Duk yanda su Alh, Bukar sukaso su hana Abbas aikinshi abu ya gagara, babu irin abunda basuyi mashi ba, amma hakansu becima ruwa ba, hakan yasa suka kara farashin Dala da kansu batare da kowa yasani ba, duk wanda yayi canji agurinsu to da tsada zeyi,

Zaune Auwal yake shida Saddik suna fira, dan Auwal tunda Alh, Abbah yace yarika sakama su Alh, Bukar ido yarage zama a office din Abbas sede idan zeyi aiki, wasu mutane sukaga sunfito daga office dinsu Alh, Bukar.

Daga ganinsu baki ne, tsayawa sukayi da jaka ahannunsu sunata magana, Auwal yace Saddik kana kallon wadan can mutanan kuwa? Naga sun fito daga office dinsu Alh, Bukar amma kuma suna magana.

Saddik yace kaine bakaga lokacin dasuka shiga tare da Alh, Bukar ba, tundaga waje naga suntaho dashi, har sauri yakeyi, kila sababbin costomers ne, shiyasa yake sauri yatarosu kada suje gurin wani.

Tashi Auwal yayi yace inazuwa, Saddik yace kai kuma ina ruwanka? Auwal yace kaide kazo muje idan zaka, haka suka nufi gurinsu, bayan sun gaisa Auwal yace ammade ku bakine ko?

Daya daga cikinsu yace wlh kuwa bakine mu, dan bamu san gurin nan ba, mundauko me adedeta mukace yakawomu inda ake canjin dala shine yakawomu nan, ana ajemu muka hadu da wani mutum shine muka tambayeshi,

Aiko bari beyi ba muka karasa maganarmu yace mubiyoshi, toshine yayi mana canji, amma abun mamaki yanda mukaji ance dala ta sauko semukaga agurinsu bahaka bane, shine kuka gammu anan,

Shawarar damukeyi mukoma mu karbi kudinmu dan gaskiya tafiyace gabanmu kuma kudin bazasu ishemu ba. Murmushi Auwal yayi yace kuzo muje gurin megidanmu acan za,a kwatar maku hakkinku.

Sosai Alh, Abbah da Abbas sukayi mamakin abindasu Auwal sukace, murmushi Alh, Abbah yayi yace ayau ne zaka nuna masu kanada iko dasu, tashi yayi yace kuzo muje office dinsu, idan sunso za,ayi abun cikin lalama,

Amma idan sun nuna taurin kai kowa zesan halin dasuke ciki kuma za,ayi zama da manya ayimasu hukunci, suna fita sukaga taro akofar office dinsu, mutane se hayaniya sukeyi,

Ganin Abbas agurin yasa kowa yayi shiru, tambayar su Abbas yayi abinda yake faruwa, anan wani yafada masu wasune sukazo canji shine aka basu bayanda aka tsaida farashin Dala ba, kuma su Alh, Bukar ne suka basu.

Wani irin kallo Abbas yayima su Alh, Bukar, tuni zufa tafara keto masu, cikin in ina Alh, Bukar yace kaga wannan magana bekamata ayita anan ba, kumuje ciki muyi magana.

Wani daga cikin yaran wajen yace wlh babu inda za,a je dama duk cikin Wapar nan kowa yasan irin zalincin da kuke ma mutane, se wani yazo yin canji gurin wanda yasaba dashi haka zakusa yaranku surika taresu,

To wlh bazamu yarda ba, ayau se an dauki mataki, Abbas yadaga hannu yace kuyi hakuri muma abinda yasa mukazo nan kenan, munsamu sun cuci wasu baki, dan haka kuyi hakuri yanzu zamu zauna da manya,

Kuma kowane irin hukunci yakamata ayi masu za,ayi masu, bazamu yarda da duk wani ha,inci ba acikin Wapar nan, dama kuma kowa yana sane da dokar da akasa alokacin da aka tsadai farashin Dala.

Kallonsu Alh, Bukar yayi yace kumu hadu adakin taro, kuma wadanda abin yafaru ku biyomu, se wakilan matasana Wapa, juyawa yayi yatafi office.

wayarshi ya dauko yakira Jafar, bayan sun gaisa yace Jafar kayi hakuri tunjiya bankira kaba, wlh munje Jigawa ne,

Amma yanzu idan baka komai kazo wapa muhadu, idan kuma kana aiki kabari idan muntashi zanzo nan gidanka. Jafar yace a,a ina kasuwa bari intaho,

Abbas yace a,a kayi aikinka nizanzo gidanka Jafar yace anyi haka? Dariya Abbas yayi yace amma gama.

Kashe wayar yayi yadauki wasu takardu yanufi dakin taronsu.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 120 🔱 125

Manyan yan kasuwa ne, na Wapa azaune, bayan sungama sauraran korafin dasu Abbas suka kawo, anan wani babban mutum kuma daya daga cikin manyan wakilai na Wapa yafara magana.

A sakamakon samunku da akayi da cin amanar mutane, ha'inci da kuma zalunci, wanda kunriga da kunsan dokar gurin nan dan kuba baki bane, asalima kai Alh, karike wannan mukami na Chairman agurinnan,

Amma kuma abun kunya ace hada kai acikin wannan zalunci, dan haka dole za,a yanke maku hukunci dede da laifinku, sannan kuma mubazamu koreku daga gurin nan ba, amma kuda kanku zakuji gurin ya isheku,

Domin ayanzu kowa yariga daya san mekuka aikata, dan haka kamar yanda mukace duk wanda aka kama da kara farashin Dala za,a cajeshi tara ta naira dubu dari, kuma haka zaku biya, munyi haka ne, domin mu nunama sauran mutane doka tana aiki, kamar yanda Chairman tun farko yaroka akafa wannan doka, wanda bamu taba samun cigaba kamar na wannan Chairman dinba.

Kuma zaku maida ma wadan nan mutane kudinsu dakuka karba, nagama maganata. Wani daga cikin mutanan yatashi yace shawarar dazan baku guda dayace, wannan hali dakuka dauka ba abu bane me kyau, zaku batama kanku sana,a ne, dan haka ku gyara tunda wuri.

Chairman ko akwai abinda zakace? Tashi Abbas yayi, fuskarshi dauke da murmushi, suna hada ido dasu Alh, Bukar sukayi saurin dukar da kai, gyaran murya yayi yace tonide abinda zance bawani abu bane,

Nasan ku duka agurin nan kungirmeni, dan haka zanyi maku tuni akan abinda kuka rigani sani, kawaide kila son zuciyane yasaku take sani, Alh, ina ganin kamar zalunci bayasa mutum yatara arzikin da Allah be bashi ba.

Kuma koya tarashi baze taba alfahari dashi ba, saboda bada gumin kanshi yatara ba, ni aganina mutum yatara kudi ko MUHALLI da gumin kanshi, kudin halak bana haram ba, wannan shine abin alfahari.

Amma duk abinda aka tarashi ta hanyar haram wata rana seya lalace, garama ace mutum maula yayi aka bashi zefi yin alfahari dashi, dan be cuci kowa ba, kawai kyauta aka bashi, kunga kuwa baza,a taba hada abinda aka bama mutum kyauta ba, da wanda mutum yatara ta hanyar zalunci, cin amana, ha'inci da yaudarar mutane.

Daga karshe ina baku shawara dakuji tsoron Allah, shi arziki idan Allah yace zakayishi kota yayane sekayi shi, mutane dayawa farkonsu talauci ne, amma daga baya Allah yana dagasu har suzo suwuce wadan da aka haifa cikin arzikin kudi.

Shiyasa arayuwa kada ka raina mutum daraja ce dashi, inafatan wannan abun daya faru zezame maku darasi, kuma zaku daukeshi amatsayin Allah yana sonku shiyasa yasa asirinku yatonu kozaku gyara halinku. Allah yatsare gaba, kuma yakaremu daga sharrin son zuciya.

Gaba daya jikinsu yagama sanyi, sosai maganar Abbas ta ratsa jikinsu, yaro karami amma yafada masu maganar dasuka kasa ganeta tun farko saboda idonsu yarufe, tashi Alh, Bukar yayi yana goge zufa dan shi Alh, yama kasa motsi.

Alh, Bukar yace hakika bamu kasance mutanan kirki ba, kuma wannan abu daya faru zanso kubamu dama domin munemi yafiya agurin mutanan gurin nan, domin tun bayau ba, muke zaluntarsu, tun lokacin da Alh, yarike mukamin Chairman muka kasance azzalumai,

Amma Allah yarufa mana asiri haka mukacigaba da tara dukiya ta haram, wadda babu wani abu dazata iya yimana alokacin dazamu tsaya agaban Allah ranar gobe kiyama, dan haka wannan magana inaso inyita agaban jama,a.

Tashi sukayi suka fita, aikuwa dama mutane duk sun taru agaban office din sunajiran suji hukuncin da aka yanke masu. Anan alkalin Wapa yayi ma mutane jawabin abinda aka yanke,

Nan guri ya rikice da hayaniya, mutane sunata jinjina ma Abbas, saboda andade ba,a samu Chairman me adalci kamarshi ba, ansha kama masu laifi irin haka abaya, amma da anshiga dakin taro anfito sekaji magana tawuce, amma yau gashi Abbas ya tsaya seda aka yanke ma masu laifi hukunci.

Anan Alh, Bukar yafara rokon gafarar mutane yana kuka, duk irin abubuwan dasuka aikata seda yafada masu. Bayan yagama abokinshi yatashi, danshi yama kasa kukan sede zufa datake tafaman zubo mashi.

Bayan yanemi gafarar mutane, yakalli Abbas, hannushi yakama yace, hakika ba girma bane hankali, kwakwalwa ce mutum, gashide kai yaro ne, amma kana da tunanin manya, lallai da ace za,a samu irinka acikin manyan kasar nan, da kasarmu ta cigaba.

Dayawan mutane, tsoro da Son zuciya shine abinda yake hanasu suyi yaki darashin adalci, amma kai bakada kodaya acikinsu, alokacin danake Chairman, nasan ana abubuwa dayawa agurin nan,

Amma saboda tsoron manyan gurin nan da kuma son zuciya irin tawa, nakasa daukar mataki, saboda ina tsoron kada inrasa matsayina, kamar yanda manyan gurin nan sukeyi mani barazana.

Aranar da mukazo mukayi maka barazana nadauka washe gari zaka zo gurinmu, amma abun mamaki se banga wani bacin rai da damuwa atare da kaiba washe gari, nan yafada ma mutane irin cin mutuncin dasuka yima Abbas a office dinshi.

Kowa seda yatausaya ma Abbas, kara rike hannun Abbas yayi yace kayi hakuri da irin abinda mukayi maka, da wanda kasani dama wanda baka sani ba, tabbas gara abani kyautar MUHALLI senafi ganin darajarshi da ace mallaki nane, amma bata hanyar halak na mallakeshi ba.

Munsami labarin ayanzu haka zaka fara gini naka na kanka, kuma hakan yasamo asaline saboda gorin damukayi maka, munyi hakane dan muci maka fuska, amma gashi agurinka yazamo alkhairi,

Tunda gashi zaka mallaki gidanka da guminka, dan Allah kayi hakuri, hannunshi yadaga sama yace inama duk kanin matasan gurin nan sha,awar zama kamar ABBAS ALEE.

Mutum me gaskiya da rikon amana, mutum me zuciyar nema, marar kasala, mutum marar tsoron dan uwanshi dan Adam, inafatan ka zarce abisa wannan matsayi da Allah yabaka, hakan zesa mukara samun canji acikin gurin nan, kuma kasuwarmu tazamo zakara akan sauran kasuwanni.

Gaba daya gurin aka dau tafi, kowa yana jinjina ma Abbas,masu daukar vedio taxwaya sunayi, hatta da yan jarida seda suka sami zuwa gurin, hakan yasa dan danan suka fara daukar abinda yake faruwa suna aikawa.

shikam Abbas seda kwalla tazubo mashi, anan kowa yace yayafema su Alh, Bukar kowa yakama gabanshi. Kallon su Alh, Bukar Abbas yayi yace bakomai, nayafe maku,

Abinda kukamun baku zalunceni ba, asalima temako na, kukayi, dabaku fadamun haka ba, bazan yi wannan tunanin ba, amma gashi ta dalilinku zan sake cikama iyayena burinsu, nagode Allah yabar zumunci. Hannu yamika masu sukayi musabaha, kowa yawuce suname yimashi godiya.

Wannan abu daya faru bakaramin kara daukaka darajar Abbas yayi ba, dan har a redio, gidan Tv, da jaridu seda aka buga, wannan shine abinda yasa Abbas yakara samun daukaka da suna agurin mutane.

Mutane daga guri daban daban suka rika zuwa kawai dan suganshi, manyan mutane kuwa duk gurinshi suka koma dayin canji, duk da kudin dayake samu baya rike mutane agurinshi,

Haka yake rarrabasu agurin sauran abokanan kasuwancinsa, domin kowa yasamu, wannan abunma dayayi yakara mashi daraja agurin yan Wapa. Dama kuma hakane, idan kayi niyar cutar bawan Allah, abun seya zamemashi alkhairi.

Bayan suntashi daga aiki yawuce gidan Jafar, acan yayi sallar magriba yadaukeshi suka nufi gidanshi, amota Abbas yabama Jafar labarin abinda yafaru dashi bayan rabuwarsu.

Sosai Jafar yaji dadin abinda Abbas yafada mashi, anan shima yafada mashi irin wahalar daya sha, sosai Abbas ya tausaya mashi, kallonshi yayi yace wlh Jafar dede da rana daya bantaba mantawa da kai ba,

A kullum ina cikin tunaninka, kuma inaso inzo inda kake, sede dana tuna da maganar Mama se inji tsoron kada injamaka bakinta yabika, haka nayita hakuri.

Jafar yace ni kaina ina tunaninka, sede maganar da Mama tafada ne, take hanani zuwa gurinka, amma yanzu tagane gaskiya, ita da kanta take maganarka yanzu.

Naji dadi sosai Abbas da Allah ya nunamun kai acikin kyakkyawar rayuwa, nafi kowa farin ciki, yau gashi Allah yadawo maka da MUHALLINKA daka rasa, kuma yakara maka da babban matsayi wanda ayanzu cikin garin nan harma da wajenshi mutane dayawa sun sanka.

Dazu ina kasuwa naji ana maganarka, abun da kukayi ayau, naga ana turashi awaya, wlh har kukan farinciki seda nayi dana ga yanda ake yabonka.

Dariya Abbas yayi yace haka rayuwa take, kaima daga yau kabar kwari, zaka dawo kusa dani domin bazan kara barin kamun nisa ba, dariya Jafar yayi yace wato zaka rabani da aikina ko? Kai Abbas yadaga yace tunda muka taso muke aiki akwari, gara yanzu asamu canji.

Jafar yace hakane, nagode

Please Login or Register in order to submit comment