Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tafadi kasa, yayi saurin bude kofar yafita, cikin ikon Allah babu wanda yaganshi, yana fita yashige dakinsu.

Afalo yazauna gaba daya ranshi yagama baci, hankalinshi yatashi, aranshi yake fadin inbadan Allah yasoshi ba, dayanzu ankamashi yazecema mutanan gidan?

Yazeyi da Labiba wanda yasan saboda kishi zata iya aikata wani abun. Godiya yayi ma Allah daya kareshi, aranshi yana fadin agaskiya koda maman Jafar batace subar gidan nan ba, da ayau seya barshi.

Ihu sukaji atsakar gida, ana fadin mutanen gidan nan kufito wlh yau Allah yakama kwarto adakin Laraba, kuma abun kunya acikin gidan nan,

Kowa yafito yaganshi da idonshi gashinan acikin dakinta. Dasauri Maman Zainab, tafito itama Labiba fitowa tayi daniyar fita setaga Abbas zaune afalo,

Kallonshi tayi tace Abbas bakaji ana ihu ba amma kazauna bazakaje kate makesu ba, kasan mazajansu basanan. Kallonta yayi yace tunda ke kinfito ai sekije,

Tashi yayi yace idan kingama kallon kishigo muhada kayanmu, anjima kadan zanje infada ma Umma, dan nasan mutumin nan yana iya zuwa akoyaushe yayi mana wulakanci, gara mucema mutanan gidan nan munsamu wani guri.

Jiki asanyaye tabi bayanshi, aranta tana fadin Abbas yasake hali, yanzu komai fada.

A waje kuwa Laraba tanajin Laure tafara ihu tayi saurin tashi tasa rigarta ta bude dakin tajawota tana fadin ke bakida hankali ne, zaki tara mana mutane?

Idan kuma sukazo basu ga kowa ba yazance masu? Laure tace yo bake kikace danaji anfara dawowa masallaci ba, idan aka dan jima infito inyi ihu zaki san yanda zakiyi Abbas yashigo dakinki, sekija mashi sharri.

Laraba tashare zufar datakeyi tace kede bari kawai nibanja mashi sharri ba, shiya kwasamun mari, anan tafada mata duk abinda yafaru

Hannu maman Zainab tafara tabawa jin irin mugun abunda wadannan mutanen sukaso su hadama Abbas, komawa daki tayi ta dauko hijabinta tafito tanufi dakinsu Labiba.

Da sallama tashiga falon, seda Labiba tajita ne ta fito, tana ganinta suka gaisa, Maman Zainab tace Labiba, yanaga kamar kuna hada kaya?.

Murmushi tayi tace wlh tashi zamuyi, Maman Zainab tace bangane tashi zakuyi ba, kuma shine baki fada mun ba, seda nashigo nagani da idona.

Zatayi magana taji muryar Abbas yana fadin dole ce tasa zamu tashi Maman Zainab, zaman gidan nan ba namu bane, domin mutanan gidan nan basuda halin kirki,

Gara inbar masu gidan tunkafin sujamun dauri,Labiba tajuya tana kallonshi dan ita batasan abinda yake faruwa ba. Maman Zainab tace wlh nima abinda kunnuwana suka jimani ne, nashigo infada maka.

Gaskiya Abbas ka tsallake rijiya da baya, tabbas Allah ya kubutar da kai daga sharrin Laraba, anan tafada masu maganar dataji sunayi data fito.

Kuka Labiba tasaka dajin wannan abu, Abbas yace to Maman Zainab kinji dalilin dayasa zamu tashi, gara mukoma gidanmu kafin musami wani gurin, domin nan gaba bansan wane irin sharri zata jamun ba.

Maman Zainab tace gaskiya kam nabaka goyon bayan kutashi, nima insha Allah Abban Zainab yana dawowa zanbashi shawarar mutashi, tunda yanzu abubuwa sun fara canzawa,

Kuma dama shima yafara maganar tashinmu, amma dayake yacemun sunfara cinikin wani karamin gida yanaso yakarasa tara kudin yasiya duk da yacemun gidan kasa ne, kuma daki daya ne me hade da falo, bandakinma yace ba rufaffe bane.

Amma yace gara mukoma can da zaman mu anan, ina maku fatan alkhairi, kuma insha Allahu tunda inada number dinki aduk inda kike wata rana zanne meki.

Abbas yace babu komai Maman Zainab, mungode da kulawarki, kuma shawarar dazan baki, ki kara karfa fama mijinki guiwa akan yakara dagewa yasayi wannan gidan, gara kukara hakuri anan din wata rana se labari.

Tace bakomai bari intayaku hada kayan, Abbas yace toni bari inje gida kafin kugama, fita yayi yabarsu suna hada kayan su. Labiba kuwa haryanzu kuka takeyi,

Maman Zainab tace haba Labiba godiya yakamata kiyima Allah daya tsare maki mijinki amma wannan kukan ya isa haka. Labiba tace hakane, amma wannan kukan harda kukan rabuwa dake.

Hakika bantaba zama da wata wadda naji tashiga raina ba, kamar ke, kuma babu wadda take fadamun gaskiya komin dacinta seke, abaya nayi kawaye dayawa amma babu abinda suka kareni dashi sema jefani cikin tashin hankali da sukayi.

Namaki alkawarin duk lokacin da kika ziyarceni zanbaki tarihin aure na da Abbas. Maman Zainab tace bakomai, insha Allahu wata rana rayuwarku zatayi kyau, harse mutane sunji sha,awarku.

Nide abinda nakeso ki kara hakuri aduk inda kike, kuma kizama me rike sirrinki dana mijinki, kada kibari wata kawa tazo tashiga jikinki tasamu damar rabaki da halayenki masu kyau.

Kuma kada kiji kyashin bada wani abu da kika mallaka ga mijinki domin ku rufama kanku asiri, ba maganar tonon asiri ba, amma duk abinda nasan ina dashi nabama mijina domin yasamu yahada danashi ya mallaki MUHALLINSHI.

Domin nice silar rabash danashi, shiyasa banajin haushin temakonshi, domin nasan irin wahalar damuka sha agidan nan. Allah yahada fuskokinmu.

Itama kukan tasa haka suka cigaba da hada kayansu, Maman Zainab tana kara bama Labiba shawara.

Zaune yake adakin Ummanshi bayan sungama gaisawa yayi shiru kanshi yana kallon kasa. Cike da kulawa tace Abbas bakinka da magana amma naji kayi shiru, idan baka fadamun damuwarka ba wakake dashi dazaka fada mawa?.

Gyara zama yayi yafada mata duk abinda yafaru tundaga korarsu da akayi daga wancan gidan har yanda Jafar yakama masu wannan gidan, da aikin daya sama mashi akasuwa, har zuwa abinda Maman Jafar tace.

Kwallan idonta ta goge domin bata taba sanin halin da danta yake ciki kenan ba, tun lokacin daya sake komawa gida na 2 bayan aurenshi datayi mashi fada akan yadena biyema mace yana kashe mata kudi yakasa tara komai, tundaga lokacin Abbas bekara fada mata halin dayake ciki ba.

A duk lokacin dayazo sede yafada mata suna lafiya, sam bayason abinda Ummanshi zata ce, yadena yima Labiba, hakan yasa yadena fada mata komai.

Kallonshi tayi tace yanzu Abbas da halin da kake ciki kenan amma baka fadamun ba? Har wata mata tana yimaka cin fuska saboda kawai kaddara tafada maka karasa naka MUHALLIN.

Ashe dama baka daukeni amatsayin uwar dazaka fadama damuwarka ba? Waye yafada maka duk duniyar nan akwai wanda ze iya rufa maka asiri inbanda mahaifiyarka?

Lallai kayi kuskure Abbas, wanda batun yau nasha fada maka matukar kabiyema mace tabbas kana tare da wahala, domin mace itace silar jefaka cikin wannan rayuwar,

Kawai namaka uzuri ne, saboda irin son da kake mata, kuma ina tsoron rabon dayake tsakaninku kada yazama ajalina shiyasa ban matsa ba, amma da tuni nasaka karabu da ita.

Amma babu komai, koda awaje zamu zauna yafiyemun kadawo kusa dani kazauna da kaje wasu suna walulakanta mun kai, ita Labiban seta zauna adakina, kai kuma sekaje dakin Umar kurika kwana duk da dakin bawani girma gareshi ba.

Amma abinda zan fada maka inaso kayi amfani da wannan abun daya faru da kai yazamar maka ishara, kayi kokarin dagewa gurin neman halak, kaima kasamu kasamu nakanka.

Godiya yayi tamata, yace Umma dama akwai wani asusu danakeyi, nasan kudin sun taru, zan fita gobe inje neman aiki, idan har nasamu zancigaba da tarawa, idan yaso ko daki daya ne, zanyi kokarin ginawa daga gefen tsakar gidan nan.

Murmushi tayi tace Allah yate makeka Abbas, Allah yasa kafi haka, babu komai, kayi hakuri insha Allah wata rana mutanan dasuka gujeka sesun dawo karkashinka. Tashi kaje kada suzo sumaku wulakanci.


Wata mota yasamu irin ta daukar kaya yatafi da ita, yana zuwa yasamu harsun gama, haka aka fara fita da kayansu, Laraba da Laure duk sunyi tsuru tsuru abakin kofa, dansu atunaninsu saboda abinda Laraba tayi ma Abbas ne, yasa zasu bar gidan,

Laraba duk tashiga damuwa, hakan yasa tana ganin Abbas yashiga dakinsu, taja Laure suka nufi dakin, afalo suka samesu suna sallama da Maman Zainab, se kuka sukeyi ita da Labiba,

Da sallama suka shiga dakin kamar mutanan arziki, suna shiga Laraba ta tsungunna tafara kuka, tace dan girman Allah Abbas kayi hakuri kayafemun, wlh nayi nadamar abinda na aikata maka, gashi ta dalilina zaku bar gidan nan.

Dan Allah kayafemun kada kutafi da hakkina. Murmushi Abbas yayi yace bakomai, Allah ya yafe mana gaba daya, kallon Labiba tayi tace kema Labiba kiyafemun, nasan tunda kukazo gidan nan babu abinda mukayi maki na kyautatawa, dan Allah kiyi hakuri.

Labiba tace bakomai nayafe maku Allah yahada kowa da rabonshi, kallon Maman Zainab sukayi itama suka nemi yafiyarta. Anan duk suka yafema juna. Sallamar dasukaji anayi ce hade da kuka yasa sukafito dasauri.

Yarinyar Laraba ce da Yaron Laure, tare da wani mutum wanda yarikosu, se kuka sukeyi, mutum yakara tallabar keyarsu yana fadin bazaku mana shiru ba, mutanan banza.

Laure tace malam lafiya zaka shigo mana gida da yara karika dukansu, aikensu fa mukayi su siyo mana koko da kosai. Laraba tamatsa kusa da diyarta tace meyafaru kike kuka?.

Mutumin yace siyen kosai kuka aikesu ko kuma yawon iskanci? Hakanan kawai kuna aiken yara bakusan halin dasuke ciki ba, tonide abinda nagani yasa nakasa hakura shine na bigesu kuma nasa su kawoni gidansu dan su fada maku abinda sukeyi.

Mamn Zainab tace dan Allah kayi hakuri kafada mana abinda sukayi. Mutumin yace to nazo wucewa tagurin wani kango senaji magana, kamar ance inleka, senaji yaron yanacema yarinyar kicire wondonki, yauma inkara yimaki irin abinda mukayi jiya, wanda nace maki haka Babana da Mamana naga sunayi.

Abun ya tsoratani sosai, ganin yarinyar tana shirin cire wondonta, shine nayi saurin shiga nakamosu, ga dukkan alamu ba wannan bane karo na farko dasuka fara, shiyasa amatsayina na uba nace gara inkawosu inma iyayensu magana.

Domin sudauki mataki, kuma su gane kuskuren dasukeyi, nizan koma, Allah ya kyauta gaba, amma ina baku shawarar kusaka yaranku makaranta, kuma ku gyara tarbiyarsu, hakan ze rage bannar da ake samu ayanzu.

Girgiza kai Abbas yayi, aranshi yana fadin Allah da manzonsa sunyi gaskiya, idan kazamo na kirki danka ko yarka zasu zamo na kirki. Addu,a yayi kan Allah yakara tsaresu daga sharrin shaidan.

Juyawa yayi yacema Labiba, muje mun tsaida me mota. Allah yakara kyautawa, mude semu cemaku sadon alkhairi, maman Zainab tabi bayansu tana kuka, su laure ma kuka sukeyi, suna kara dana sanin irin mugun halin dasuka aikata.

Bayan suntafi maman Zainab tashigo tana kuka, tsaye ta iske su suma suna kuka,tace wannan kukan baze kaiku ko ina ba, yakamata ke kiduba diyarki, idan akwai wata matsalar kutafi asibiti, Allah yakara shirya mana zuri,a. Hannun Zainab takama suka koma ciki.

Laure tace Laraba munga ta kanmu, tunkafin muje lahira Allah yafara nuna mana kuskuren mu tun aduniya. Laraba tace ni narasa abinda ma zance, insha Allahu daga yau, nadena aikata duk wani mugun abu danakeyi, ba yara kadai ba, mukammu yakamata mu koma makaranta, domin mukara samun ilimin dazamu bama yaranmu tarbiya. Laure tace Allah ya yafe mana.
Nace amin.

Tun ahanya Labiba tacema Abbas, kada asauke da kujerunta da gadonta, asauke masu kayan sawarsu da katifa da sif dinsu, kawai. Kallonta yayi yace meyasa kikace haka? Murmushi tayi tace kawai inaso akaisu kasuwa asaida.

Murmushi yayi yace mezakiyi da kudin? Tace nide dan Allah nace, idan ka kawo kudin zakaga abinda zanyi dasu, kaga yanzu ko munje babu inda za,a sakasu dan Allah kada kace a,a.

Jinjina kai yayi yace shikenan, tace yau nagode, shima aranshi yaji dadi sosai, dama tundazu yake tunanin inda za,a ajesu, bayason a ajesu awaje ruwa yabatasu. Kuma bayason yafara kawo mata maganar asaida dan tunda suke betaba saida mata wani abunta ba, se idan itace tace, ko kujerunta dasuka saida itace tace asaida suka sayi abinci.

Haka akayi, suna zuwa gidan yakira kaninshi Umar suka sauke kayan aka bar sauran amota, Umar yasa yashiga dasu shi kuma yawuce kasuwa dame motar, suna zuwa yaci sa,a aka siyesu da daraja, naira dubu 15 aka bashi kudin gado, kujeru kuma 18, cike da murna ya sallami me mota yahau adedeta yanufi gida.

Koda yaje harsun gama shirya kayan adakin Ummanshi. Duk da dakin beda wani girma amma kayan sun shiga, abinci Umma takawo masu dumamen tuwo, fita waje tayi tabasu guri dansuci.

Labiba kawai Abbas yake tausayi, dan tunda sukayi aure yau shekara 3 basu taba cin tuwo da safe ba, kallonshi tayi taga ita yake kallo, hakan yasa tayi murmushi ta tashi tadebo mashi ruwa akwano,

Hannunshi takama ta wanke itama ta wnke nata, sannan tafaraci, harda lumshe ido tace gsky Umma ta iya girki, jin hakan yasa yayi murmushi yasa hannu yafaraci. Amma azahirin gsky miyar babu magin kirki, hakanan Labiba take daurewa tana ci saboda Abbas.

Shikanshi sabo da cin girkin Labiba, hakan yasa yaji miyar babu dadi sosai, Labiba kuwa aranta take fadin bazata kara barin Umma tayi girki ba, gara tarika yimasu, kodan surika cin medadi.

Bayan sungama yadauko kudin kayanta yabata, yafada mata yanda aka siyesu, murmushin jin dadi tayi tace Allah yayi masu albarka, dubu 20 ta mika mashi, tace karba karike inaso kasa kasu cikin asusunka, bayan kasamu aiki seka fasa muga abinda aka samu nasan zasu isa kayi ginin dakin.

Wannan dubu 13 kuma inaso kamun izini infara abincin saidawa amma acikin gida, zanrikayin na safe dana rana, kaga babu ruwanmu da neman abincin safe da rana, sede na dare kawai, hakan ze kara temaka mana. Amma dan Allah kada kace a,a nasan komeye wata rana ze zama labari.

Wasu kwallan tausayi ne, suka zubo mashi, besan lokacin daya jawota ya rungume ba, itama kukan takeyi, yace nagode Labiba, bansan dame zan saka maki ba, fatana Allah yamun budi na alkhairi injiya maki dadi.

Bakomai nayi maki izini, Allah yasa kifara asa,a Allah ya kareki daga sharrin mahassada. Tace amin, yace bari inkira Umma infada mata,

Sosai Umma taji dadin abinda Labiba tayi, anan tayi masu addu,a dama Umma tana sana,ar saida magi dasu barkono, kuka gishiri. Tace se insa asamo maki almajiri dan kada wahalar tamaki yawa.

Haka Abbas ya karbi kudin yaje kasuwa yasiyo mata kayan abinci da robobi, cokula, yakawo mata, dama Umma tana da babbar tukunya da kaskon tuya. Umma da kanta taje makarantar wani malami anan kusa dasu tace yabata almajirai 2 haka yasamu masu hankali yabata.

Waken da zata rika kosai dashi Umma tasa aka kaishi barza dan kada Labiba tasha wahalar surfawa, ana kawoshi ta bakace shi, suka aje. Umar shine yafara yimasu talla agurin yan unguwar matasa.

Koda dare yayi Labiba kasa bacci tayi, domin yau itace rana ta farko dazata kwanta batare da Abbas ba tunda sukayi aure. Shima hakan ta kasance agareshi, shiyasa yayi alkawarin zeyi ginin dakin da kanshi, tunda beda kudin biyan masu aiki, dama kuma yariga daya saba.


Addu,arshi daya Allah yabasu sa,a aduk abinda zasuyi, dayaji baccin yakasa zuwa haka yafita yayo alwala yafara nafilfili, yana rokon Allah sa,a. Itama Labiba haka tayi, sallah tafarayi tana neman sa,a agurin Allah, gaba daya daren sun rayashi ne, da ibada.

Nikam nace ai duk me nema yana tare dasamu, kuma Allah yace duk wanda yarokeni nikuma zan amsa mashi. To Allah yabama su Abbas da Labiba sa,a.

Ur's.

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08927525263
[10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 25 🔱 30
INA FATAN KOWA YAYI SALLAH LAFIYA? ALLAH YA MAIMAITA MANA, YA KUMA SA IBADARMU KARBABBIYA CE. AMIN.

Washe gari tunda asuba suka fito anan suka hada kayan kosai gari yana fara haske aka bama almajiri yakai nika, yana kawowa Umma da kanta ta hura wuta sannan Labiba tahada kullun tafara bugashi.

Lokacin da gari yakara wayewa sungama hada komai, Labiba tafara tuyar kosai, koko Umma ta dama masu, tazuba ma Abbas da kosan taba Labiba takai mashi, ita kuma ta anshi tuyar.

Cikin ikon Allah sega mutane sunfara shigowa siyan kosai, dayan almajirin shine yake karbar kudin yana zuba masu.

Afalo tasameshi zaune, zama tayi tace sakko kaci abinci kada ka makara zuwa kasuwa, murmushi yayi, yana kallonta cike da tausayawa,

Hannunta yajawo, yace Labiba kiyi hakuri da duk wani hali damuke ciki, nasan nine silar sakaki acikinshi, yanzu gashi ta dalilina kinayin abinda baki taba yiba.

Murmushi tayi tace haba Abbas, nice yakamata infada maka haka, amma dan Allah daga yau, banaso ka kara tuna abinda yawuce, koma menene inaso mu manta da rayuwarmu ta baya hakan zesa mu fuskanci rayuwarmu tayanzu.

Abinci yafara ci yace toshikenan Allah yashige mana gaba, tace amin, fira tarika yimashi har yagama, tadauke kayan, bayan tadawo yace Labiba nizantafi kimun addu,ar samun sa,a.

Inaso inde nasamu aiki akasuwa infara ginin dakinmu, domin jiya banyi bacci ba, nasaba kwanciya tare dake, amma dalilin rashin MUHALLI jiya na kwanta batare dake ba.

Insha Allahu gobe zanyi ma malam musa megini magana semufara da wadannan kudin amma na kasa zanyi domin kudin su isa, nasan idan muka hadu nida Umar dashi malam musa zamuyi saurin gamawa.

Kinga kudin aikin malam musa kawai zan samu, tunda shine yafi sanin takan gini. Labiba tace hakane, gara de asamu ko marar tsawo ne sosai agina, inde ze ishemu rayuwa nida kai, zefimun dadi, da,ace baka kusa dani. Yace insha Allah, bara intafi.

Sallama yayi ma Umma tayi mashi fatan alkhairi sannan Labiba tara kashi har kofar gida, sukayi sallama tana yimashi addu,a sannan tadawo.

Koda karfe 7:30 tayi tuni har sun saida kosan, almajiran sukayi wanke wanke suka share tsakar gidan aka basu abincinsu suka nufi makaranta karatu. Bayan sungama karyawa suka fita domin gyara kayan miyan abincin rana.

Abbas kuwa yana fita yatari me adedeta yatambayeshi ina ze kaishi? Shiru Abbas yayi, yama rasa wace kasuwa zece mashi, sam bayason kasuwar dazatayi kusa datasu Jafar.

Kawai jiyayi bakinshi yace WAPA zaka kaini, duk da yasan ba kasuwa bace amma yasan acan ma ze iya samun aikinyi tunda gurin yan canji ne. Tafiya suka fara Abbas yana ta tunanin ta inda zefara.

Abakin gurin ya ajeshi, kudinshi yabashi yayi mashi godiya sannan yayi bismilla tare da addu,ar shiga kasuwa yafara tafiya, koda yashiga gurin, mutane yafara gani kowa yanata hidimarshi.

Haka Abbas yayi ta zaga yawa cikin Wapa amma yakasa samun inda zenemi aiki, wani katon shago yagani, da yara acikinshi sunata aiki, hakan yasa ya matsa kusa da gurin.

Sallama yayi masu, daya daga cikinsu yayi saurin tasowa, dan atunaninshi customer ne, hannu yabashi, bayan sungaisa yace ya Malam kanason canji dala ne ko sefa?

Shiru Abbas yayi yace a,a ina neman megidanku ne, kallon 3 saura kwata yaron yayi mashi yace bangane kana neman megida ba. Idan wani abune kafada nine babban yaronshi.

Gyara tsayuwa Abbas yayi tare da sosa kai, yace to bawani abu bane dama nafito neman aiki ne, nafi awa 2 ina zagaye cikin Wapa amma nakasa samun wanda zan tunkara da bukatata.

Shine danazo wannan shagon hankalina ya kwanta da gurin shine nace bara ingwada sa,a ta. Wani murmushin rainin hankali yaron yayi yace lallai kuwa malam wannan sa,ar taka bazata karbu anan ba.

Sede ka kara gaba, Abbas yace haba bawan Allah, naga kaima fa gurin nan banaka bane, shiyasa danazo nace megidanku nake nema, inda shine yafadamun haka zan iya hakura, amma kaima akasanshi ka keci.

Dariya yaron yayi, yace ka gyara kalamanka, domin duk wani wanda ka gani yana aiki a shagon nan ta hanyata yashigo, idan kana da wani abu me kauri kamiko kawai amaka hanya, idan kuma babu zaka iya karama kafarka iska.

Shiru Abbas yayi, tabbas yanason aiki amma yariga da yayima Allah alkawarin baze taba samun aiki ta haramtacciyar hanya ba, kuma wannan kudin da yaron yake magana tamkar cin hanci ne, amusulunci kuwa Allah yaharamta cin hanci.

Tsaki yaron yayi yace bakada magana tunda naga kayi shiru, dan haka kayi saurin barin kofar shagon nan tunkafi megida ya iso dan wlh zan jamaka sharrin dazakayi dana sanin zuwanka gurin nan.

Haka nan kawai daga zuwanka guri a kama adauke ka aiki, wama yasani ko barawo ne kai, ko kuma dan 4 1 9, kashigo jikinmu ka cucemu. Juyawa yayi yashige shago yana masifa.

Wasu zafafan hawayene suka zuboma Abbas, wai yau shine ake kira da barawo da dan 419 saboda yana neman aiki. Lallai wannan rayuwa idan baka dashi komai ma za,a kira ka dashi,

Yanzu wannan yaron ko kunyarshi bejiba amma yafada masa wadannan maganganun. Juyawa yayi yatafi, sede haryanzu zuciyarshi bata hakura da neman aiki ashagon ba, dan tunda yashigo layin yakejin gabanshi yana faduwa.

Alokacin daya iso bakin shagon kawai seyaji kamar ana ingizashi yashiga, nesa da gurin yasamu yazauna, kanshi ya kifa da guiwarshi, yana kara tunanin irin wannan rayuwa,

Ace yanzu aduniya idan kana neman aiki dole seka bada cin hanci za,a daukeka? Kasuwanci ma kenan, inaga aikin gwamnati? Addu,a yashiga yi yana neman temakon Allah, yana nan har aka fara kiran sallar azahar, hakan yasa yatashi yanufi masallacin dayake kusa da wannan shagon dayaje.


Akusa da wani mutum ya tsaya, bayan sungama sallah kowa yakama gabanshi, shikam Abbas zama yayi yanata addu,a yadade azaune agurin har wannan mutumin dayake kusa dashi wanda shima zama yayi bayan angama sallah, har seda yagama addu,oinshi sannan yatashi.

Bayan Abbas yagama yatashi da niyar zuwa yasiyi abinci, tashin dazeyi yaga wata babbar waya a inda mutumin nan yayi sallah, dukawa yayi yadauka yanakara juyata ahannunshi, ko ba,a fada mashi ba, yasan wannan wayar bata kananan mutane bace, domin daganinta zatayi tsada.

Aranshi yace tabbas naga mutumin damukayi sallah tare dashi, sede bazan iya gane fuskarshi ba, amma de naga kalar shaddarshi. A aljihu yasaka wayar yafita, yana fadin nasan za,a kira bara inje inci abinci.

Agida kuwa su Labiba kasuwa tayi riba, domin mutane da yawa sunzo siyan abincinta, kuma sun yaba da iya girkinta, domin Labiba akwai iya abinci kuma ga tsafta. Tas abincin yakare har ana nema.

Bayan sunyi wanka sunyi sallah, sukaci abinci, almajiran suka kwashi kwanukan suka wanke suka share gurin. Anan Umma da Labiba suka kirga kudin suka fitar da ribar, sannan suka cire Uwar, anan Umma tabama Umar kudin yaje kasuwa yasiyo cefanan gobe.

Labiba har kuka tayi dan murna, ganin sun sami riba sosai, kudin gishiri da magin Umma daza,ayi amfani dasu gobe tabata, domin tace agurinta zata rika siye yafi aje waje asiya.

Asusun da Umma tabata tadauko tazuba ribar data samu, sannan ta kwanta dan gaba daya tagaji, Umma se dariya take mata, tana fadin yaran yanzu bakusan wahala, abu kadan zakuyi ya gajiyar daku.

Bayan Abbas yagama cin abinci yana zaune nesa da wannan shagon dayaje dazu, zuwa yanzu yafara fidda ran ze samu aiki, har yafara tunanin ko yatafi kasuwar kwari kila adace acan, dan anfi samun dako,gara yaje yafara da dakon.

Mikewar dazeyi yaji wayar aljihunshi tana kara, sam shi yama manta da ita, dama tunda yaduba yanaso yakira seyaga akwai pass word hakan yasa kawai ya maidata yajiye.

Hamdala yayi, dan dama bayason tafiya batare daya bama me ita abinshi ba, dauka yayi tare da sallama. Shiru yayi yana sauraran abinda ake fada, yace e wlh nima a masallaci naganta, shine na aje inajiran akira.

Eyanzu haka ina bakin wani babban bene, shiru yayi can kuma yace to bari intambaya danni bakone , e insha Allah zan kawo maka, tunda kai sananne ne, dama abinda yakara tsaidani kenan, toshikenan inazuwa.

Kashe wayar yayi yakara maimaita sunan da,akace yatambaya. ALHAJI ABBAH HALA? Matsawa yayi jikin wani shago yayi sallama, da fara,a mutumin ya amsa mashi, yana fadin malam barka dazuwa, kanason canji ne?

Murmushi Abbas yayi yace a,a tambaya de nakeyi. Yace to Allah yasa nasani. Dama shagon Alh, Abbah Hala nake nema. Bata fuska yayi yace kaga malam idan canji kakeso kona nawane nima inayi, yanda zebaka nima haka zanbaka, kanama iya zuwa su kara maka farashi.

Kallon mutumin Abbas yakeyi cike da mamakin bakin ciki kiri kiri. Kai ya girgiza yace niba canji nazo ba, kawai shagon nake nema. Mutum yace to nima bansan shagon ba. Juyawa Abbas yayi yace to nagode.

Fita yayi ranshi yana me mamakin mutanan yanzu, wai ace babu kunya babu tsoron Allah arika maka bakinciki akan sana,arka, yanzu inda da gaske canji yazoyi haka ze kwacema Alh, ciniki.

Seda Abbas yashiga shago 3 amma duk irin abinda wancan mutumin yafada ake fada mashi, lokacin daya fito shagon karshe yayi alkawarin baze kara tambayar kowa ba, juyawa yayi yakoma masallacin dayayi sallah yazauna yace gara injira idan yakara kira ince yazo yakarba.

Ko minti 5 beyi dazama ba, aka kara kira, yana dauka yace mashi idan da hali yaturo atafi dashi shagon, ko kuma yazo da kanshi yakarba. Bansan me akace ba,naji yace toshikenan inajira.

Tun daga kofar shigowa masallacin yagane wanda yake shigowa, domin bemanta kalar kayan mutumin ba. Da sallama ya isa gurinshi, amsawa Abbas yayi, mutumin yamika mashi hannu suka gaisa.

Wayar Abbas yamika mashi yana fadin ai tunda kashigo nagane kayan, domin dazu akusa dani

Please Login or Register in order to submit comment