Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sosai Abbas, Allah yabarmu tare. Murmushi Abbas yayi yace haba Jafar, ai harmu mutu bazan taba biyanka abinda kamun ba, ka temake ni alokacin dana rasa gatana, kaine farin cikina Jafar.

Nagode ma Allah daya barni araye har nima zan samu damar yimaka kadan daga cikin alkhairan daka mun, da bazance zan maka abinda kamun ba, wannan Allah ne kadai ze iya biyanka.

Abakin gate din gidan sukaga wasu mutane su 3, suna jingine da katangar gidan, hasken fitila ya haske su, Jafar yace kaga yallabai, ga wasu mutane can suna jiranka, Abbas yace habade, ai bankai wannan matsayin ba.

Kilade hutawa sukeyi, Jafar zeyi magana yaga sun nufosu, hakan yasa Abbas yafasa shiga da motar cikin gidan, parking yayi suka fito, da sallama mutanan suka karaso gurinsu.

Cike da mamaki Abbas yace suwa nake gani kamarsu Buba? Saurin kallonsu Jafar yayi, yace aikuwa Abbas sune, hada Usman, hannu Abbas yabasu suka gaisa, Jafar ma yamika masu hannu, yana kallonsu, daga ganinsu duniya ta juya masu baya.

Abbas yace ya kuka tsaya anan baku shiga ba? Buba yace wlh mun tambayi megadinka shine yace baka dawo ba, muka tambayeshi yaushe zaka dawo yace haka kawai besammu ba, zamu mashi wannan tambayar, shine yace mutafi,

Shine muka zauna muna jiranka dan musan kana gari, ko dazu munganka kana jawabi awaya. Murmushi Abbas yayi yace yana da gaskiya kasan yanzu duniya abun tsoroce, kuzo mushiga ciki to.

A falonshi suka zauna, nan Abbas yasa Labiba tabama me aikinta abinci da ruwa da lemu takawo masu, Buba sekara kallon falon yakeyi yana mamakin arzikin da Abbas yayi.

Bayan sun gama cin abinci, Buba yakalli Abbas yace dan Allah Abbas kayi hakuri da duk abinda mukayi maka, wlh munyi nadama, babu kamar ni, nine nafadama Labiba komai agame da gidan daka gina, gashi nazamo sanadiyar dayasa karabu da gidanka.

Segashi nima nasamu mata dede dani tasani narasa komai, ita bama sawa tayi narabu da gidana ba, yaudarata tayi harseda tasa namaida sunan takardun gidan da sunanta, daga baya tayi mani rashin mutunci wanda seda yasa nasaketa har saki 3,

Anan nace tabarmun gidana, se alokacin data dauko takardun gidan natuna da abinda nayi, haka mukayita rigima wadda takaimu har kotu, kuma alkali yabata gida, tunda ansamu sa hannuna abisa takardun.

Inaji ina gani haka nabar mata gidan, dama kuma bata bari mun haihu ba, haka rayuwa ta juya mun baya, hatta da mashin dina seda na saida, da kyar nasamu wani shago nake kwana aciki, yanzu haka bani da komai, dan Allah Abbas kayafe mani.

Sosai Abbas ya tausayama Buba, yace bakomai, ya yafe mashi, kuma yadauko kayanshi yadawo gidanshi akwai daki daya me hade da bandaki a boys quarters din da Umar yake ciki,

Godiya yayi tamashi, haka ya tambayi su Usman, sukace su sunada gidansu, kawaide kasuwancinsu ne, babu jari, anan yace suma zebasu jari, godiya sukayi mashi, tare da bashi hakuri akan abinda sukayi mashi, yace babu komai. Kudi yabasu yace gobe su sameshi a office.

Bayan sun tafi, Jafar yace Abbas kaga rayuwa ko? Abbas yace nagani Jafar, kalli Buba yanda yarasa gidanshi daya dade yana ginawa, akalla gidan nan yayi shekara 4 yana ginashi, tunkafin musan zamu fara gininmu. Jafar yace ai ita duniya yanzu tunkafin mutum yabarta take koya mashi hankali,

Kaga yanzu shima yadauki darasi, kuma naji dadin abinda kamashi dama haka akeso mutum yazama me saka alkhairi akan sharri.

Abbas yace nimafa gobe zanfara sabon ginina, jafar yace wannan bemaka bane? Kai Abbas ya girgiza yace wannan babu ko sisina aciki, kyauta Yaya yabani filin kuma yagina munshi, ada nakarbeshi amatsayin gidan dazan zauna, amma sanadiyar wani gori da akamun, yasa zanyi ginina da kaina.

Nan yabama Jafar labarin abinda yafaru, seda Jafar yayi kwalla, yace kayi dede Abbas, Allah yataya ka yabaka ikon kammalashi, Abbas yace amin Jafar,

Muje kugaisa da Labiba ko? Dariya Jafar yayi yace Labiba sarkin rigima ba, Abbas yace haba yanzu tazamo sarkin biyayya, Jafar yace da gaske? Abbas yace wlh kuwa aiyanzu nakara godema Allah dayasa banyi fushi abaya ba, nasan dayanzu bama tare da ita.

Amma gashi danayi hakurin daba kowane namijin zamanin nan ze iya yinshi ba, gashi yanzu ina cin ribar abun, dan ayanzu de bazan iya samun mace kamar Labibata ba, nan yafada mashi yanda take mashi biyayya da kuma kyautatawar datake mashi.

Jafar yace shiyasa nake kara baka hakuri, nasan Labiba tanada halin kirki, kawaide kasan halin wasu matan dasaurin yarda da kawaye, gaskiya natayaka murna Allah yabarku tare,

Kaga yanzu seka fara shirin karo ta 2, duka Abbas yakai mashi yace se lokacin dakayima Maryam kishiya zanyima Labiba, Jafar yace haba aini da Maryam takalmin kaza, mutu karaba.

Abbas yace nima haka nida Labibata, dariya suka sa suka fita, gurin Umma suka fara zuwa, taji dadi sosai ganin Jafar, Ansar da gudu ya haye Abbas yana gwarancinshi, jafar yace ikon Allah, gaskiya mundade bama tare, yanzu wannan danka ne?

Abbas yace a,a Ummace tayi aure shine ta haifeshi, pillow din kujera Umma tasa tajefeshi dashi, tashi yayi yana dariya yace ai da gaskiyata Umma, inbanda iskanci na jafar yaze tambayeni bayan ko makaho ya taba yasan Anasar dana ne.

Dariya Umma tayi tace wannan kuma tsakaninku, daukarshi Jafar yayi yace rabu dashi Umma, zan ramane, sallama sukayi mata zuka nufi gurin Labiba.

Sosai Labiba tayi farin cikin ganin Jafar, bayan sungama gaisawa yayi mata barka, anan yafara tsokanarta akan abinda yafaru abaya, dariya suka rikayimata shida Abbas, tashi tayi tana turo baki tana fadin wlh, zan rama akanka Dadyn Anasar.

Hannu 2 yasa yarufe bakinshi yana fadin nayi shiru laifin Jafar ne, dariya tasa tashige ciki, Jafar yace to seda safe tunda kinshige, haka suka fita da Abbas yatafi maidashi, kudi masu yawa yabashi yace semun hadu gobe a wapa, godiya yayi mashi yatafi.

Bayan yakoma yayi wanka suka kwanta, Labiba tace amma naga kamar Jafar yana cikin damuwa ko? Abbas yace wlh kuwa, anan yafada mata abinda yafaru, hada labarin su Buba, sosai ta tausaya masu, yace amma gobe zefara aiki a office dina, tace amma ka kyauta gaskiya, Allah yabiyaka,

Yace amin Labibata, tace dan Allah inaso gobe idan zaka fita ka kaini gidan kawu, idan kadawo se kadaukoni, Abbas yace angama matata, zata kara magana yarufe mata baki yace muyi bacci.

Washe gari bayan sun gama karyawa sukayi wanka Labiba tashirya cikin wani less mekyau da tsada, suka nufi gurin Umma, bayan sungama gaisawa Abbas yace dama Labiba ce zataje gidan kawu, shine zamu fita tare in ajeta idan natashi se indaukota.

Umma tace hakan yanada kyau, gara kirika zuwa dubashi, to Anasar dinfa? Labiba tace badashi zanje ba, Umma tace aiko sede kifasa tafiyar, inba kina zuwa dashi ba, yaza,ayi surika ganinshi?

Turo baki Labiba tayi tace Umma kawai kibarshi zanje dashi wani lokacin, kuma kinga zaki rasa dan fira. Umma tace nibawani dan fira dazan rasa, maganar ma me ya iya dazanyi fira dashi?

Dariya Abbas yayi yace nide zantafi tunda bazakije ba, saurin tashi tayi kamar zatayi kukaUmma tana dariya tace kayanshi kawai zaki dauko anyi mashi wanka, haka tadauko kayanshi sunkayi mata sallama,

Turare da sabulai Umma tabada akai masu, godiya Labiba tayi mata sukatafi, amota Abbas se dariya yake mata, yace meyasa bakison tafiya da yaro? Tace wlh takura gareshi, dariya yayi yace damma kinsamu ba,a gurinki yake ba, amma aigashinan zaki haifo mashi kanwa kwanan nan.

Dariya tayi tace nibani da komai, yace shikenan Allah ya kaimu ni naga komai ai, da haka suka isa gidan kawu, fita sukayi, Abbas yadauko tsarabar dasu kayi masu, daga gefen gidan su kawu sukaga wata me kosai, Labiba tace Dadyn Ansar wlh kosan can nakeso.

Dariya yayi yace mesan kosai ne, kenan? Baki ta turo tace kaide kacika fassara, kayan yamaida mota yace sede muje tare dan bazanje ni kadai ba, bayanshi tabi yana tamata dariya.

Sallama Abbas yayi yace baiwar Allah bamu kosai, dagowa tayi zata anshi kudin, karaf suka hada ido da Labiba, har suna hada baki gurin kiran suna, Labiba tace kamar Hauwa?

Hawayene suka zubo mata tace itace Labiba, mamakine yakama Abbas, yace karbi kudin kisamata muje sauri nakeyi kada inmakara a office, kosan tasa mata tace kabar kudin, ajemata yayi ya karbi kosan yace a,a dauki kudinki.

Kallon Labiba yayi wadda idonta yacika da kwalla yace muje ko, harsuntafi tadawo tace idan kingama kisameni gidan kawu zanso inji labarinki, hauwa tace yanzu kuwa.

Bayan sun shiga suka gaisa Abbas yabama Kawu kudi yayi masu sallama, godiya sukayi mashi, har bakin mota Labiba tarakoshi Hauwa sekara lekensu takeyi, hannunta Abbas yakamo yace banyarda kije gurin waccan ba.

Labiba tace bazanje ba, amma kayi hakuri nace tazo tasameni agidan kawu inaso inji labarinta dan Allah. Kai yadaga yace shikenan amma da sharadi, bance ki nuna mata gidanmu ba, koma menene tafada maki gidanta se asa akawo mata temako, zanfadama su kawu kadama sufada mata inda gidanmu yake,

Awannan karon bazan yarda da kawancenku ba, kuma bazan hanaki temakonta ba, nida kaina ma zan tayaki temakonta, amma maganar kawance babu ita, ina fatan kin fahimceni?

Kai tadaga mashi tace na fahimceka, kuma nima bazan bari wani abu yakara hada muba, kawai zanso inji labarinta, kuma intemaketa dan Allah badan halinta ba, kodan tagane duk irin cutar datamun gashi nayi mata rana, Abbas yace shikenan idan nadawo nima zaki bani labarinta. Murmushi tayi tace angama yallabai, adawo lafiya.

To masu karatu kunga laifin Abbas daya hana kawancen LABIBA DA HAUWA AKARO NA 2?

ZAMUJI LABARIN HAUWA A NEXT PAGE.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 125 🔱 130

Zaune suke adakin matar Kawun Labiba, seda Hauwa taci abinci takoshi sannan ta kalli Labiba tace dan Allah kifara bani labarinki kafin inbaki nawa, domin nasan naki seyafi nawa dadin sauraro.

Ajiyar Zuciya Labiba tayi tafara bama Hauwa labarinta tundaga ranar dasuka rabu ta ita datazo gidanta har zuwa yanzu, su dukansu kuka sukeyi kamar an aiko masu da mutuwa.

Goge kwalla Hauwa tayi tace lallai Labiba kinga rayuwa, na cutar dake, kindauke ni amatsayin babbar kawarki amma ni bahaka nadaukeki ba, na cuceki,

Tun ranar da kika nunamun Abbas amatsayin wanda zaki aura nafara jin haushi, ban kara jin haushinki ba, seda kika fadamun Abbas yana maku gini, tundaga ranar nafara tunanin yanda zanyi insa kiraba Abbas da wannan gidan,

Kema yazamana haya ze kama maku kamar yanda mijina ba gidanshi bane ka .Wlh Labiba karya nake maki danace mijina yanada gida a Danbatta, asalima beda wani gida, kuma dan garin nan ne.

Dalilin dayasa na zabeshi amatsayin wanda zan aura saboda naga kinsamu miji,kuma duk cikin samarina babu wanda yashirya aure,
hakan yasa nima aranar da muka hadu dashi kawai nayanke shawarar inrigaki aure.

Alokacin danayi mashi maganar aure yacemun shifa be shiryaba, asalima beda ko gidan daze sani, ayanzu haka gidan dayake aiki gidan wani uban gidanshi ne, baya zama sosai shine yakama gidan gwamnati idan yazo yake sauka amatsayin
guest house nashi.

Yace mun da ace yanada gurin daze ajeni daya aure ni, kudin aure bazasuyi mashi wahala ba. Nikam dajin haka na tambayeshi awace unguwa yake zaune idan megidanshi yazo, yacemun anan
unguwar yake alayin bayansu kawunki.


Kuma gidan daki daya ne se bandaki, shima gidan kakarshi ne, kuma danta ne yaci gidan data rasu, kasancewar dan nata yanada gida shiyasa yabashi yarika zama.

Alokacin har na hakura, amma wata zuciyar ta hanani, tambayarshi nayi wata nawa megidanshi yakeyi kafin yazo? Yacemun yanzu ma baya nan yayi tafiya kuma wata 6 zeyi bedawo ba.

Murmushi nayi nace mashi meze hana muyi aurenmu kawai akaini can kafin yadawo? Kallona yayi bece komai ba, nace mashi kada yadamu son danake mashine yasa bazan iya hakura dashi ba, nayarda idan megidanshi yakusa dawowa semutashi mukoma gidan kakarshi, dajin haka shikuma ya amince.

Kinji yanda akayi mukayi aure harna zauna agidan gwamnati, babban dalilin dayasa na zugaki kada kiyarda Abbas ya kaiki gidanshi saboda nasan nima zamana agidan nawani lokaci ne.

Haka muka zauna dashi harna tsawon wata 5, alokacin damuka shiga wata na 6 megidanshi yayi mashi waya yakusa dawo wa, kuma yasamu mata agarin nan daya dawo zasuyi aure kuma agidan ze ajeta.

Babu bata lokaci muka tashi muka dawo nan unguwar, kayana ko rabi basu shiga gidan ba, haka nayanke shawarar sayar da wasu. Da haka muka cigaba da zama acikin gidan,

Gaba daya rayuwa ta canza mani, dama dadin danakeji saboda kayan garata ne, amma suna karewa muka shiga cikin kunci, mijina koya fita baya samo komai, idan ma yasamo awaje yakecin abincinshi.

Ahaka har muka shekara daya da rabi, duk na rame nayi baki idan baki manta ba akwai sanda nazo gidanki kike tambayata meyasameni, nace maki rashin lafiya nayi, ganin zaki matsamun da tambaya nace maki zantafi.

Hakan yasa nadena zuwa gidanki, lokacin da wahala tamun yawa na yanke shawarar inzo insameki inroki gafararki, amma inazuwa na iske kuntashi, nakiraki bana samu, har nan gidan nazo suka ce basu san inda kuka koma ba.

Wlh Labiba har bara gidan mutane seda nafarayi, danaga hakan bazemun ba,shine nafara shiga gidan masu kudi ina neman aiki, nasamu aka daukeni, anan nafara samun sauki, kinsanni da son banza,

Wata rana matar gidan ta aje kudinta tashiga daki, inazuwa ni kuma nadauke, ashe tazo fitowa ta ganni, tun daga nan ta koreni, haka na koma rayuwar baya, mijina idan yatafi seyafi wata bedawo ba.

Ana cikin haka wannan dan kakarshi yazo ganin gidanshi, ganin yanda gidan ya koma yace mutashi zeyi gyaran gidanshi, mowakan mijina yabashi hakuri seya rufe ido yarika mashi rashin mutunci, nan ya fusata yace semunbar gidan.

Alokacin na koma gidanmu, seda nayi wata guda, kinsan kishiryar mamana batada kirki, ganin mamana tarasu shiyasa tashiga matsamun, gaba daya aikin gidan yadawo kaina, 'ya'yanta basa ragamun,

Ga Babana baya zama se dare, bayan wata guda mijina yazo gurin Babana yace yasamu angama gyaran gidan, dama haka muka cemashi, nan na bishi muka tafi.

Ashe hakuri yaje yabama dan uwanshi, shine yace gyaran gidan yakeyi yajira yagama zebashi daki daya, kinsan yanda ya gyara gidan? Ciki da falo ya maidashi, yazuba yan haya daga zauren gidan yayi wani karamin daki yaja karamar katanga daga gaba yayi mana wani karamin bandaki.

Ko gado na beshiga ciki ba, bare katifa, hakan yasa mijina yace sede mu saidasu musayi karamar katifa, haka yadaukesu yaje yasaido, ahanyarshi ta dawowa wata mota ta kadesu a adedeta, dagashi har me adedetar babu wanda yarayu.

Bakaramin tashin hankali nashiga ba alokacin da aka kawomun shi, haka dan uwanshi da mutane suka shiryashi aka kaishi, nasha kuka, duk da irin rashin kyautawar da yayi mani, amma daya rasu naji alokacin nake son zama dashi,

Sonshi da kaunarshi kamar alokacin aka dasamun su, haka nacigaba da karbar gaisuwa, tare da sadaka daga gurin mutane,


Bayan sadakar 7 dan uwan mijina yasameni yabani kudin da aka samu ajikin mijina da kuma sauran sadakar da aka samu, anan yake tambayata zan koma gida ne? Nace mashi inde zebarni inaso inzauna anan.

Yaji tausayina yace bakomai incigaba da zama, kudi nabashi nace yasayomun karamar katifa, kin karbar kudin yayi yaje yasiyomun yakawomun.

Haka nacigaba dazama ni kadai, alokacin da Babana yace kozan dawo gida, nace mashi yayi hakuri yabarni inzauna inyi takabata da iddata anan, shima tausayina yaji dan yasan zaman damukeyi da matarshi, haka yakawo kudi masu yawa yabani.

Ahankali ina cin kudina, har nafara maida jikina, kinsan zara bata barin dami, haka kudin suka dauko karewa, ganin idan suka kare zanshiga wahala yasa nayanke shawarar fara kosan saidawa.

Kasan cewar layinmu beda mutane siyasa nazo nan layin nafara kosai, ba laifi ina samu, da haka nake rike kaina harzuwa yanzu.

Kiyafemun Labiba, nasan hada hakkinki dana Abbas yake bibiyata, kuyafemun kona samu sauki.

Kuka ne yaci karfinta, Labiba ma kuka takeyi sosai, tausayin Hauwa duk yakamata, wayarta ta dauka takashe recording din datayima Abbas, dan bazata iya bashi labari ba, hakan yasa tayi mashi recording.

Hakuri tashiga bata, tace kiyi hakuri Hauwa, dama haka rayuwa take, duk wanda ya cuci wani shima seya ga rayuwa, nima na cuci Abbas shiyasa na tsinci kaina ahalin damuka shiga abaya, wannan abun daya faru ya ishemu darasi.

Ina maki ta,aziyar mijinki, Allah yajikanshi, Hauwa tace amin, nagode Labiba, dan Allah kicema Abbas ya yafemun, Labiba tace bakomi munyafe maki, Allah yakara yafe mana.

Amma shawarar dazan baki Hauwa mace duk inda take dole setana da me kula da ita, kibar ganin kamar kin girma, haryanzu yarinyace ke kawai wahalar rayuwa ce ta maidaki haka,

Kyan mace gidan iyayenta ko gidan mijinta, ko gidan 'ya'yanta, komin girman mace bata iya rike kanta dole seda mate maki, ina guje maki sharrin shaidan,duk yanda kikaso ki kame kanki zuciya batada kashi,

Wanda yake cikin wadata ma yana bin masu kudi bare kuma ma bukaci, kiyi hakuri da duk irin rayuwar dazaki tsinci kanki aciki wata rana komai ze wuce, gara ki koma gaban mahaifinki kowace irin wahala matar babanki zata baki bazata taba rabaki da numfashinki ba harse lokacinki yayi.

Ajiyar zuciya Hauwa tayi tace hakane Labiba, maganarki gaskiya ce, zuciya batada kashi, nagode da shawararki, insha Allah ayau ba gobe ba zanbar gidan danake, zanyi hakuri inzauna agidanmu kafin Allah yakawomun canji.

Kudi masu yawa Labiba tabama Hauwa tace takara jari tasayi wani abun tarika sana,a kuma tasayi kayan amfaninta. Godiya Hauwa tayi mata tace, awace unguwa kuke dazama yanzu? Labiba tace karki damu zanzo har gidanku indaukeki muje can, ai yanzu kingama iddarki ko? Hauwa tace E, tashi tayi tace bara inje infara hada kayana, Labiba tace to sekin ganni.

A Office Abbas ya iske Jafar,bayan sun gaisa ya nuna mashi wani table yace daga yanzu kazama PA na, dan haka ga kujerarka can, dariya Jafar yayi yace kai amma nagode, ashede Allah zenunamun ranar dazan samu aiki a office, ranar dazan rika shan iskan AC.

Abbas yace haka Allah yake al,amarinshi, Jafar yace amma kuma Auwal fa ? Abbas yace yana nan amatsayinshi, sede shi mefita ne, kai kuwa kana office, tashi muje gurin Yaya dan yacemun yau za,a fara gini.

Haka suka fita suka nufi gurin ginin Abbas, sosai Alh, Abbah yaji dadin irin matsayin da Abbas yabama Jafar. Bayan sun gama Abbas yanufi inda ake saida mashin, yasayama Jafar Lifan, sosai Jafar yaji dadin kyautar da Abbas yayi mashi, daga nan yayi masu siyayyar kayan abinci.

Seda suka fara zuwa gurin maman Jafar suka aje mata nata, hada kuka tayi tana kara rokon Abbas yafiya, yace bakomai, anan Jafar ya gwada mata mashin din da Abbas yasaya mashi, Abbas yasha addu,a haka yadauki kudi yabata yawuce dauko Labiba.

Bayan sundawo gida suka mika Ansar gurin Umma, wanka sukayi, Umma tabada abinci aka kawo masu, seda suka gama cin abincin sukayi brush suka kwanta, Abbas yace to azo abani labarin, kawarki.

Dariya Labiba tayi tace Allah sarki Hauwa, ai labarinta baze badu da baki ba, hakan yasa nayi maka recording dan insamu sauki, amsar wayar yayi ya kunna, shiru sukayi suna sauraro.

Tunkafin yakare hawaye suka fara sintiri afuskar Abbas, yaji tausauyin Hauwa sosai, bayan yagama ya ajiye wayar, itama Labiba kuka takeyi. Abbas yace Allah sarki, gaskiya na tausaya ma Hauwa, hakika taga rayuwa,

Allah yajikan mijinta da rahma. Labiba ko kin kula aduk cikin mutanan dasu kayi sanadiyar sakamu cikin rayuwarmu ta baya duk sunfimu fuskantar wulakanci? kinsan kome yasa? Saboda mu bamuda hakkin kowa akanmu, bamu cuci kowa ba.

Dama kuma haka rayuwa take, duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba, to tashi ko zafi bazatayi ba, yanzu inasu Alh, Bashir dasuka so halaka ni? Suna can suma sunga rayuwa, gobe ne wa,adinsu yake cika zasu fito, kinga koba komai sun rasa abubuwa da dama.

Amma kuma naji dadin shawarar dakika bama Hauwa, kuma insha Allah nima zantemaketa, zanga abinda zanyi insha Allah. Labiba tace Dadyn Ansar, nikam tundazu nake wani tunani,

Yace inajinki, dama naga shima Buba beda aure shine nacemeze hana muhadasu,murmushi Abbas yayi yace saboda kucigaba da kawance ko? Kai ta girgiza,
yace hmmm, Labiba bazan boye maki ba, wlh, Hauwa ta cutar dani, inbadan Allah yaso ba dabazan aureki ba inda ace nabiyema zuciya,


Dole inyi duk wani abu dazanga
na nisantaki da ita, amma kiyi hakuri, tunda ta gane kuranta, zanyi tunani akan maganarki, amma fa ko hakan yakasance dole zan sama masu gida nesa damu, dan shima Buban bangama yarda dashi ba, koda nace yadawo gidana, dande kawai akwai hidimar danakeyi yanzu,

Amma da komai ya kammalu shima zetafi, gara inbashi jari, idan kuma aurensu ya yuwu, itama zambata jari kuma insama masu gida nesa damu. Labiba tace hakan ma yayi nagode, yace bakomai.



Washe gari su Alh, Bashir suka fito daga gidan yari, duk sun kode, sunkara tsufa saboda wahala, acikin abokansu babu wanda yazo tarbarsu, mutum daya ne aka samu cikin yan uwan Alh, Bashir yazo daukarsu.

Tun amota yake tambayarshi ina yaranshi da matarshi, babu abinda yake cewa illa suna nan lafiya lau Alh, mujede gidan ka huta. Haka nan yarika jin gabanshi yana faduwa.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 130 🔱 135

LAST PAGE!!!!

A firgice Alh, Bashir yafito daga mota yana kara murtsike ido domin tabbatar da abinda idanunshi suke nuna mashi, faduwa yazoyi dasauri suka rikeshi zufa ce tafara keto mashi,

Kamashi sukayi suka sakashi mota yana fadin ina zaku kaini kubarni inje akwai abubuwan dazan dauka acikin dakina, dan Allah kada kucemun komai yatafi.

Lallashinshi suka farayi, kallon driver yayi yace dan Allah Kasim meyafaru kafada mun, tunkafin zuciyata ta buga? Kai Kasim ya girgiza yace Alh, kayi hakuri muje can gida na zakaji komai.

Zaune suke afalo Alh, Bashir yana zaune kasa rigarshi duk ta jike da zufa, idanu ya zubama Kasim yana sauraronshi.

Gyaran murya Kasim yayi yace wato Alh, abinda yafaru shine, yau tsawon shekara daya kenan iyalanka sukatashi cikin tashin hankali, sakamakon gobarar data tashi acikin gidanka.

Kuma ba komai bane ya haddasa ta ba, se karamin danka, ankunna inji da dare shikuma yadauki ashana yana wasa da ita, se mamarshi ta anshe, ta ajeta ashe yagani, bayan ta tafi yadauka seyatafi can baya inda ake aje injin,

Wata takarda yagani shine ya kunna ashanar ajikinta, dayake babu rabon ya kone, yana ganin takama shine yaji tsoro seyadauketa ya wurga ta baya shikuma ya ruga cikin gida, ashe kusa da injin yajefa,

Kafin mutanan gidan su ankara kawai aka ga wuta takama, nan kowa yafara neman yanda zeyi yafita, saukin da aka samu wutar tabaya tafara ci, haka kowa yafita, babu wanda ya tsaya daukar wani abu,

Matarka ce kawai tayi kokarin daukar kayan sarkokinta da jakarta, gashi alokacin mu muna masallaci sallar isha,i kasan wutar fetur, nan take gaba daya gidan yakama da wuta,

Lokacin da mutane sukazo aka fara zufa ruwa amma kamar ana kara mata mai,kafin akira masu kashe wuta tuni wutar tacinye gidan, haka sukazo aka kashe wutar babu abinda yayi saura na amfani, motocinka duka sun kone.

Kuka sosai Alh, Bashir yakeyi kamar karamin yaro, kallon Kasim yayi yace yanzu ina matata da yarana suke, nasan acikin jakarta akwai ATM dina, kuma nasan za,a iya samun wani abu agurinta, wlh Kasim bayan wannan kudin na account dina bani da sauran wani abu.

Kasan ni ba ma,abocin siyan kadara bane in aje, nafison inga zallar kudi a ahannuna ko acikin account dina, nasan narasa kudade masu yawa acikin dakina, amma dasauki tunda na cikin account sun tsira.

Dukar da kai Kasim yayi yace Alh, nibansan mezan cemaka ba, domin bayan komai yalafa Ummar mu tace da Hajiya sudawo gidanta su zauna kafin asamu agyara gidan ko kuma su sami wani gurin.

Kwananta 2 tace zataje unguwa, tun ranar data tafi haryanzu tsawon shekara daya babu ita babu labarinta kuma munsami labarin tasayar da filin gidanka daya kone, kuma kanina yafadamun yaganta aranar data tafi taje bank.

Alokacin da muka sami labarin tasayar da filin mukaje muka sami wanda yasayi gidan,takardun gidan yadauko mana kuma tabbas sune ga sunan matarka nan ajiki, hakan yasa mukashiga nemanta, amma

Please Login or Register in order to submit comment