Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi maki, kawai shafen siminti ne akayi asaman ginin kasar, jiya jiyan nan mun wuce tagaban gidan daya gina,

Sede kiyi hakuri dan gaskiya gidan bawani girma gareshi ba, amma kuma fa yayi kokari dan gidan yasha fentin ruwa,dan irin wannan fentin da anyi rywan sama yake wankeshi.

Toni zanwuce dama wani guri zani na ganki shine nace bara inkaraso mugaisa,

Amma idan baki yarda ba, zaki iya hawa mashin dina inkaiki har gidan kigani. Wata irin zufa ce tarufe Labiba, tace muje wlh nafasa zuwa aiken idan nadawo zanje, hawa mashin din tayi Buba yana dariyar mugunta yaja mashin suka tafi,

Kuka Labiba tasaka alokacin dasuke shiga unguwar, hijabinta tasa tarufe hancinta saboda wari, da kyar suka isa kofar gidan saboda hanyar duk tayi rami,

Kallon gidan takeyi cike da takaici, ga rufin gidan ba irin nazamani bane, langa langa ne, akayi rufi dashi, kuka takeyi, tace dan Allah Buba muje ka kaini gida,

Haka suka tafi, zuciyar Labiba kamar zata fito, tun ahanya tayima Abbas message yazo tana son ganinshi, har kofar gida Buba ya ajeta, yana mata sallama amma bata kulashi ba, tashige tana kuka. Dariya Buba yayi yace muje zuwa Abbas.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 90 🔱 95

Zaune Abbas yake asaman dakalin kofar gidansu Labiba, yayi mamakin yanda sam Labiba taki yarda su shiga cikin gidan kamar yanda suka saba,

Gashi tunda yazo take kuka yama rasa yanda zeyi da ita, kallonta yayi yace Labiba kitashi mushiga ciki kinga nan mutane zasu ganki kina kuka,

Kai tadago tace maganar danakeso muyi bana so kaka taji, hakan yasa nace muzauna anan, kuma ai akwai duhu bakowa zeganni ba,

Ajiyar zuciya Abbas yayi yace tonaji, yanzu share hawayenki kifadamun abinda yake faruwa, tunkafin nima nafara kukan,

Gyaran murya tayi tace Abbas meyasa zakamun karya? Meyasa zaka ha'inceni? Wannan abun daka mun munafunci ne, cike da tashin hankali Abbas yace haba Labiba me kuma nayi maki? Dan Allah kimun bayani yanda zangane.

Uhm Abbas kenan dadina da ramin karya kurarrene, atunaninka karyar dakayi bazata fasu ba? Wato kaso ka cuceni, harse andaura mana aure ankaini gidanka sannan zanga irin gidan dakamun ko?

Anufinka dole inhakura inzauna tunda anriga da andaura. To bara kaji, wlh, wlh, wlh, kaji namaka rantsuwa 3, duk yanda nake sonka da ace seda aka daura aurenmu aka kaini wannan kaskantaccen gidan amatsayin gidan dazan rayu,

Wlh da aranar zan barmaka gidanka, kuma koyanzu infada maka da babbar murya wlh inde awancan gidan dakayi zaka sakani, wlh gara sonka yakasheni dade inzauna acikin gidanka, kai gara in mutu banyi aure ba da ace ankaini wancan abun dakake kira gida.

Barema nasan koyanzu nafasa aurenka inada wadan da zasu aure ni, aciki ma hada masu babban gida, kawai de saboda son danake maka ne, yasa nayarda na zabeka,

Amma kuma duk irin halarcin dana maka shine zaka sakamun da wannan gidan? Haba Abbas, ai nadauka yanda kake sona zakayi duk yanda zakayi kanemi kudi kodan kasama mun gurin hutu.

Shiyasa dazu da Buba abokinka yafadamun abinda kake boyemun bakaramun dadi naji ba, dan nasan duk wannan munafuncin wannan Banzan Jafar din ne, ya hadashi,

Ni nasan irin son dakake mun bazaka iya munafunta ta ba, kuma idan gaskiya ne, meyasa shi beyi ginin kasa ba? Shine kai ze zuga ka kayi mani, dan haka wlh nibazan zauna awannan gidan ba.

Dan haka zabi yarage naka, kode kasaidashi kasayi wani, ko kuma ka hakura da aurena, kamanta kataba sanin wata Labiba.

Fuskar Abbas da jikinshi kamar wanda aka kwarama ruwa, kuka yakeson yi amma zuciyarshi tabushe, Innalillahi Wainnailaihirrajiun kawai yake fada aranshi,

Yafi minti 10 ahaka bece komai ba, kuma be motsa ba, ganin yakasa motsi yasa Labiba tafara tsorata, hannu tasa ta dafa kafadarshi, saurin kallonta yayi, ganin ya motsa yasa tayi saurin daure fuska.

Ahankali yafara magana, Labiba dan girman Allah kada kimun haka, kinsan ina matukar sonki, nasha wahalar da tunda nake bantaba shanta ba kafin in mallaki wannan gidan nawa,

Idan kika sani nasayar da wannan gidan bansan inda zansamu cikon kudin dazan sake siyan wani ba, kuma ga lefe zan hada, ga kudin biki, kinsan de yanayin da gidanmu yake ciki base nayi maki karya ba,

Wlh Labiba da ina da kudi Allah kadai yasan irin gatan dazan nuna maki, amma kidena fadin zaki rabu dani kinsan da inrasaki gara inrasa komai na duniya inde zan sameki, zan iya hakura da komai.

Kuma kinsan duk abinda kikeso shinake so, dan haka kigoge kwallanki kifadamun duk yanda kikeso wlh na maki alkwari zanyi, kinsan ina sonki kamar rai na.

Murmushin farin ciki Labiba tasaki, wani irin son Abbas ne da tausayinshi taji sunkara shigarta, wata zuciyar tace mata tabarshi suzauna agidan, amma data tuna gidan Hauwa da yanda kawayensu suka rika yabon gidan setaji bazata iya hakura ba,

Kallonshi tayi tace yauwa Abbas dina shiyasa nake sonka sosai, kana son duk wani abu danake so, nima wasa nake maka danace zanrabu da kai, kasan inasonka dayawa, dan Allah duk abinda zan fada maka banaso kafadama kowa,

Kagade babu wanda zetayamu zama, idan akayi auren nan kowa tafiya zeyi yabarmu, dan haka kadena biyema Jafar kana shawara dashi akan aurenka, yace to Labibata fada inajinki, ni kuma bazan fadama kowa ba.

Gyara zama tayi tare da rage murya tace Abbas meze hana kasaida gidanka, tunda baka da kudin dazaka cika kasayi wani, nasan kudin zasuyi yawa, kaga semuje ka kama haya a irin gidan su Hauwa tacemun dubu 150 ne ashekara, kaga sauran kudin sekasayi mashin, shima baze wuce dubu 150 ba,

Kaga har yanzu kanada sauran kudi, seka ajesu acikin asusu, kaga bayan biki sekacigaba da tarawa, nasan kafin kudin hayarmu yakare arzikinka yafi nayanzu, kasan annabi yace idan talauci ma ya isheka ka kara aure,

To kai yanzu ma zakayi auren, kaga nan da wani lokaci zamuyi arziki, kaga zamu sayi gida me kyau, babu ruwanka da bata lokaci gurin gini, aginan nanshi zaka siya,mashin dinka ma zaka iya saidashi kasayi mota,

Shikenan fa, kaga kasameni, kasami gida kuma kasami mashin, kaga kawuce raini acikin abokanka. Shiru Abbas yayi zuciyarsa se bugawa takeyi dasauri, zufa haryanzu taki dena fito mashi,

Matsawa kusa dashi Labiba tayi takamo hannunshi takara rage murya tace, nasan Umma kake tunani, dannasan aduk duniya ita kadai zata iya hanaka yin abinda kake so,

Kasan ance tsakanin uwa da danta se Allah, kada kabari tasan zaka saida gidanka, nasan zataji haushi amma kuma yanda take sonka bazatayi fushi da kai ba, kasan Umma Akwai dogaro ga Allah.

Idan har zakayi abinka cikin sirri ko Jafar kada kabari yasan abinda zakayi, idan sukazo daukar amarya zasu sani, dan Allah Abbas kayarda da shawarata, kada kabari shedan yahanaka yin abinda nakeso, yin hakan dede yake da rasani na har abada, kuma......


Hannu yasa ya rufe mata baki, kallonta yake atsorace, yace Labiba kinaso zuciyata ta buga ne? Wlh gara kice inbada gidan dana gina kyauta, dakice zaki rabu dani, tunda har narasa mahaifina na kuma hakura babu abinda bazan iya sadaukarwa ba akan soyayyarki,

Naji kuma nayarda, amma inaso kema kada kifadama kowa zan saida gidana, insha Allah babu wanda zesan wannan maganar, kuma zamu rayu cikin jin dadi, zanmaki yanda kikeso, kibani sati daya zan gama komai.

Rungumeshi tayi tana fadin inasonka Abbas dina, tashi yayi yana murmushi sukayi sallama yatafi, tsallen murna tayi tadauko wayarta takira Hauwa, tana dauka tace wlh dole inbaki kyauta, wannan shawara taki tayi.

Hauwa tace, a,a wai da ke kintsaya soyayya, ai dama nabarki kunyi auren an kaiki wannan rubabbar unguwar, idan fa akayi ruwan sama haka zakiga ruwan kwata yana shigowa gidajen mutane,

Gashi gininku nakasa ne, wata rana kuna ciki gini zefado maku, shikenan ku mutu abanza, ai dama nafada maki, Abbas yana maki wani irin so, idan kinso zaki iya amfani da wannan damar kiyi abinda kikeso.

Yanzu gashinan dayake yaga yana shirin rasaki ya amince da bukatarki, ai wlh sekinyi da gaske, idan bahaka ba, ko kunyi aure shawarar abokinshi Jafar zerika dauka, garama tun wuri kirika hanashi shawara da kowa seke.

Labiba tace ai yanzu kam nadauki shawararki, bazan kara biyema so ba in cuci kaina, idan munyi auren mayi soyayyar, Hauwa tace yauwa yar gari. Godiya tayi mata takashe wayar tashige gida.

Aranar Abbas kasa bacci yayi, yarasa yanda ze bulloma wannan matsala data taso mashi, wani barin na zuciyarshi yana gargadinshi akan kada yasaida gidanshi, amma barin da son Labiba yafi yawa yakasa yarda da maganar dayan barin.

Daga karshe kawai ya yanke shawarar, gara ya saida gidan, ze iya gina wani, amma Labiba baze taba samun taba idan har yarasata, da wannan gurguwar shawarar bacci barawo yadaukeshi.

Washe gari tunda safe yana gaisawa da Ummanshi yace mata megidansu yana son ganinshi, addu,a tayi mashi yafita,

Yama rasa acikin abokanshi waze dauka suje neman mesiyan gida, yasan idan za,a saida gida mutum daya baya tsayawa shikadai, maganar Labiba yatuna datace Buba ne, yafada mata gidan dayayi.

Hanyar gidansu Buba yadauka, yana zuwa yasameshi yana shirin fita, bayan sungama gaisawa yafada mashi abinda yake faruwa. Wata irin dariya Buba yayi, yace yauwa abokina kokaifa, yanzu ne zaka shigo cikin manya,

Amma saboda kawai kanaso ka mallaki MUHALLINKA sekaje kayi ginin kasa, kuma kazauna aciki, haba Abbas, aishi MUHALLI da kake ganinshi, da kasameshi awulakance gara kazauna ana haya, ahankali seka mallaki naka. Kana ganin komasu kudi yanzu basu cika son gina gida ba, sunfi so su kama haya, hankali kwance.

yanzu kam dole intemaka maka, da fitama zanyi amma nafasa, muje gurin wani abokina dillali ne yanzun nan za,a siyar da gidanka. Abbas yace amma nagode, dan Allah kada kafadama kowa.

Buba yace haba Abbas babu wanda zan fadamawa, kaide muje zuwa. Cikin sa,a suka sami abokin Buba kuma yafada masu dama akwai wanda yakeson gida, nan yayi mashi waya, babu bata lokaci yace gashi nan zuwa.

Bayan yazo suka tafi ganin gida, mutumin yana ganin gidan yace yayi mashi, nan akayi ciniki gida yakama dubu dari 550, Abbas yanaji yana gani yadauki takardun gida yabayar,
Aka bashi takarda yarubuta shedar yasayar da gidan,

Kuka sosai yakeyi, kallonshi sukayi cike da mamaki, dillalin yace Buba mekuma yafaru naga yana kuka? Buba yace bakomai, kawai yatuna da mahaifinshi, sukace Allah sarki, tafiya sukayi dan sukarbi kudin.

Bayan anbasu kudin Buba yace yauwa munason gida na yangayu kasan bikinshi saura sati 3, to kuma sebayan biki zefara gina babban filinshi, shine yakeson gida me kyau wanda base anyi gyara ba, dan sufara zama shida amarya.

Dillali yace ai wannan ba matsala bane, akwai wani gida.... Abbas yace a,a ni nafison irin gidan gwamnati, dillalin yace me irin gininshi kake so ko? Yace E,

To gaskiya kaga yanzu lokaci yakure, amma akwai wani gida anan kasan gida na, kuma yana da sauki gaka de unguwar ba laifi tana da kyau, kuma zakuji dadin gidan, duka dubu dari 2 ne ashekara.

Abbas yace muje inga gidan, haka suka tafi, suna zuwa yaga gidan yakira Labiba yafada mata ansamu gida, Buba yabama wayar yayi mata bayanin yanda gidan yake, dariya tayi tace ai nayarda da kai, kawai akama.

Haka suka gama komai aka bama Abbas mukullin gida, sukayi mashi sallama, akan hanya Abbas yace Buba mashin nakeso insiya, tunda kaga yanzu kudin saura dubu dari 300 da kadan, sauran kudin kuma zan ajesu,

Buba yace kai amma dagajin wannan shawarar dakake fadi ba daga bakin Jafar tafito ba, dan nasan Jafar baze iya baka wannan shawarar ba? Murmushi Abbas yayi yace kaide kafadamun.

Buba yace haka ne, muje musiyo, amma ka kawoshi gidanka ka ajeshi bayan biki sekafara hawanshi, haka sukaje akayi cinikin mashin lifan baki, suka biya sabon gidan Abbas aka aje mashin din, dubu 10 Abbas yabama Buba, godiya yayi mashi suka rabu.

Haka Abbas yacigaba da shirin bikinshi, sam baya barin sudade suna magana da Jafar, siyayyar lefenshi ma shikadai yakeyi, damma Jafar shima yana tashi hidimar, amma shi lefenshi mamanshi ce take hada mashi.

Biki yana takara matsowa, har akayi jeran Labiba babu wanda yasan Abbas yasayar da gidanshi, haka yan uwan Labiba sukaje sunata yabon gidanta, ita kam se dadi takeji.

Jafar da Buba sune suka kai lefen Labiba, shikuma Jafar nashi mata ne, suka kai, kowa ya yaba kayan da aka sakama Labiba.

Umman Abbas dataga kayan tace amma Abbas kayi kokari wannan kaya haka, lallai ka hana kanka ci da sha, Abbas yace Umna hada gudummuwar abokaina na hada,

Tace gaskiya sun kyauta Allah yabiyasu yace amin, kallonshi tayi tace inafatan babu wata damuwa ko Abbas, nasan yanda hidimar biki take kuma banji kace inbaka wannan kudin dakace in aje maka ba? Abbas yace bakomai Umma tunda inada kudi kibarsu kema kiyi hidimar biki dasu, tace ai shikenan Allah yatemaka, yace amin.

Ayau ne aka daura auren Abbas Alee da Labiba Lawal, akan sadaki dubu 30, da misalin karfe 12:00, suna gama na Abbas kuma karfe 2:00 aka daura na Jafar da Maryam.

Da misalin karfe 5:00 aka dauki Labiba zuwa gidanta, shima Jafar alokacin aka dauki tashi amaryar, hakan yasa besan inda aka kai Labiba ba. Kawayenta se yaba gidan Labiba sukeyi, Hauwa tace gaskiya Labiba kin more gida dama nawa,

Dariya Labiba tayi tace, kinji Hauwa duk haduwar gidanki amma kike santin nawa? Wata kawarsu tace inde Hauwa ce, ai tacika ruwan ido, dariya suka saka.

Umar ne yashigo gidansu, hankali tashe, alokacin anyi magriba, yan biki duk sun watse, dama yawanci yan unguwa ne, se wasu yan uwan Umma mata guda biyu,

Umma tna ganin umar ta taso tana fadi lafiya nagana kamar kana cikin damuwa? Kwalla ne suka zubo mashi cike da damuwa taja hannunshi suka koma gefe guda, tace Umar kafadamun meke faruwa?

Umar yace Umma yanzu awaje agurin abokan yaya nakejin wani labari, wai Yaya yasayar da gidanshi yakama haya da kudin gidan,saboda Labiba tace bazata zauna agidan kasa ba,

Lokacin danaji banyarda ba, haka natafi gidan inazuwa nasameshi abude, sallama nayi sega wani mutum yafito, tambayarshi nayi ko da gaske gidanshi ne, yace mun ai tun sati 3 da suka wuce yabiya kudin gidan. Wlh Umma........... bekarasa maganar ba, Umma tazube agurin sumammiya.

Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡
DARAJAR MUHALLI
🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡

Nah
Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)

@House of Novella Association
(H,O,N,A)

[email protected]

Season 95 🔱 100

Cike da tashin hankali Umar yanufi gurinta, dagata yayi yashiga kiran sunanta amma ko motsi batayi, tashi yayi da gudu yanufi hanyar fita, azaure sukaci karo da Abbas shida Jafar sunzo yima Umma seda safe.

Rikeshi Abbas yayi yana fadin lafiyarka Umar zaka bige mutane baka gani ne? Kuka yasaka mashi yana fadin shikenan Yaya zamu rasa Umma, cike da fargaba Abbas yasakeshi yana fadin meyasamu Umman?

Da hannu yashiga nuna mashi hanyar cikin gida, ai shida Jafar har rige rigen shiga suke, kwance suka sameta yanda Umar yabarta, kusa da ita Abbas ya duka yasaka kuka.

Jafar ne, yayi saurin dauko ruwa yashiga yayyafa mata, cikin sa,a tasaki ajiyar zuciya, fita Jafar yayi yataro me adedeta, yana zuwa yacema Abbas yakamata sutafi asibiti.

Yan uwanta ne suka fito jin hayaniya, suma hankalinsu yatashi ganin abinda yake faruwa, nan Jafar yace masu zasuje sudawo, haka aka fita da Umma dan haryanzu bata dawo dede ba.

Suna zuwa asibiti aka karbeta, wani daki aka sata aka kwantar da ita saman gado, likita aka kira, yana zuwa yafara yimata gwaje gwaje, ya dauki lokaci kafin yagama,

Allurai yayi mata nan bacci yadauketa, fitowa yayi yace su sameshi office, bayan yagama rubutunshi yace menene sanadiyar sanyata tasuma? Shiru sukayi,

Jafar yace wlh bama gidan lokacin da abun yafaru, Umar ne, kuma yana gida. Dr, yace to da alama anfada mata wani abu wanda yadaga mata hankali har yayi sanadiyar sumanta.

Damma tana da karfin jini abun yazo dasauki, kunci sa,a bata da hawan jini da wannan faduwar datayi zata iya jawo mata matsalar shanyewar barin jiki.

Amma nayi mata allurai insha Allah zata samu sauki, tana farkawa ma zaku iya tafiya, sede a kula da duk wani abu daze daga mata hankali, domin akare lafiyarta.

Takarda yamika masu yace kusiyi wadan nan magungunan tashasu insha Allah babu wata matsala, godiya sukayi mashi suka fita, bayan sun dawo daga siyen maganin suka zauna akusa da dakin.

Abbas yakalli Jafar yace kozakaje gida kada Maryam taga kadade? Murmushi Jafar yayi yace haba Abbas, ai koba Umma bace aka kawo asibiti wani naka ne, bazan iya barinka kai kadai ba,

Bare kuma Umma, idan kuma mamanace aka kawo zan iya tafiya inbarta? Ai ko kwana zatayi bazan tafi ba, bare kuma yau zamu tafi, kawai zankirata, kaima ka kira Labiba kafada mata.

Haka suka zauna suna jiran Umma ta farka, gaban Abbas se faduwa yakeyi, yayi duk wani tunani amma yakasa gano dalilin dayasa Umma tashiga wannan halin, haka ya hakura.

Gurin karfe 9 ta farka, hakan yasa suka kira wata nurse bayan tagama dubata tace zasu iya tafiya, Abbas se sannu yake mata amma taki ko kallonshi, haka suka tafi gida abun yana damunshi, sede yadauka ko bata son magana ne.

Suna zuwa gida tashige dakinsu Abbas dayake zaure, mamaki ne yakamasu, Abbas yace Umma dakinmu ne fa kika shiga, kallon Jafar tayi tace kirawomun Umar kuzo nan inason magana daku can akwai mutane.

Zama Abbas yayi gabanshi se faduwa yakeyi, Umar yana zuwa Jafar yace to nizan tafi Allah yakara sauki Umma, dago kai tayi tace dawonan kazauna kaima maganar tashafeka,

Zama yayi shima gabanshi yashiga faduwa, shiru dakin yayi, can Umma tace Umar maimata abunda kafadamun dazu, dasauri Abbas yakalli Umar, saurin dukar da kai Umar yayi yafara magana.

Kaf yafadi abinda yafadama Umma dazu, wata irin zuface tafara zuboma Abbas, Jafar kuwa jiyake kamar amafarki, saurin kallon Abbas yayi dan yatabbatar da maganar Umar gaskiya ce.

Kwallan daya gani suna fitowa a idon Abbas ya tabbatar da maganar Umar gaskiya ce, Murmushin takaici Umma tayi tace amma Jafar meyasa kai bakazo kafadamun abinda Abbas yake shirin yiba tun kafin ya aikata?

Saurin kallonta Jafar yayi yace wlh, Umma yanda kikaji maganar nan daga sama haka najita, har garake tundazu kikaji nikam yanzu ne nasan da ita, kallon Abbas yayi wanda zuwa yanzu kukanshi ya tsananta yace,

Kayi magana Abbas dan Allah kacemun da wasa Umar yake baka saida gidan dakasha wahala kafin ka mallakeshi ba, kifar da kanshi Abbas yayi saman cinyoyinshi yacigaba da kuka.

Umma cike da bacin rai tace wlh ko katashi kayi mana bayanin yanda abun yafaru ko kuma idan kabari nafita daga dakin nan, wlh gidan zanbari kuma kungama ganina har abada,

Bazan tsaya bakin cikinka yakasheni ba, nagama da iyayena lafiya, nagama da mijina lafiya, saboda kai bazan bari hawan jini yakashe ni ba.

Saurin dago kai Abbas yayi yace dan Allah Umma kiyi hakuri wlh zanfada maki komai, ba laifina bane, kiyafemun, gyara zama yayi yashiga fada masu duk abinda yafaru.

Salati Umma tasa tana tafa hannu, Jafar da Umar kuwa kuka suke sosai, shima Abbas kukan yakeyi, Umma tace lallai Abbas kayi wayon banza, ashe dama duk hankalin dakake dashi na banza ne?

Ashe dama mace karama zata iya yimaka wayau? Wlh, wlh, wlh, kaji namaka rantsuwa har 3, da ace kafin adaura aurenku ne, nasamu wannan labarin da ko awajen daurin auren ne, senasa anfasa auren,

Sede rashin aurenta yazamo ajalinka da kake ikirari dashi, innalillahi wainna ilaihirrajiun, wannan abu dame yayi kama? Amma wannan yarinya bansan mezan cemata ba.

Kuka tasaka, hankalinsu gaba daya yagama tashi, matsawa kusa da ita Abbas yayi yana kuka yarike hannunta yace Umma nasan ban kyauta ba,na munafunceku amma dan Allah kada kiyimun baki,

Yau gashi ta dalilina kinzubar da hawayenki, dan Allah kiyi hakuri kada Allah yayi fushi dani, nasan nayi kuskuren da bazan iya gyarashi ayanzu ba, amma addu,arki kadai zatasa in gyara laifin danayi nan gaba.

Kallon Jafar yayi yace Jafar kayi hakuri, nasan ban kyauta maka ba, amma wlh sharrin zuciya ne, da son danake ma Labiba, wlh alokacin jinayi kamar raina zefita idan narasata, hakan yasa nayi saurin karbar sharadinta,

Dan Allah kazo katayani bama Umma hakuri, wlh idan yanzu kikace inrabu da Labiba nayarda zan rabu da ita inde hakan ze sanyaya zuciyarki, amma kada kiyi fushi dani Umma,

Matsowa Jafar yayi hada Umar suka shiga bama Umma hakuri, shiru tayi tana goge idonta yayin da tausayin Abbas yakamata, hakika tasan Abbas yarone me ladabi, kaddara ce da kuma sharrin mace yasashi ya aikata wannan abu,

Kamo hannunshi tayi tace shikenan Abbas na hakura, bazan ja da kaddarar da Allah yadora maka ba, kuma bazan rabaka da farin cikinka ba,tabbas nasan kana tsananin son Labiba,

Hakan yasa take amfani da wannan damar tana maka abinda taga dama, amma bakomai, nayafe maka, kaje kacigaba dazama agidan haya, sekayi kokari kasamu katara wasu kudin kasayi wani gidan,

Idan bahaka ba, wlh inde kabiye mata bazaka taba mallakar gidan kanka ba, kuma zaka ce nafada maka, duk ranar daka fara zama namiji ka iya tsayawa kaki bin yanda takeso to daga ranar zaka fara tara abun kanka.

Amma ayanzu soyayya ta rufe maka ido, bazaka taba gane abinda za,a fada maka ba akan matarka, amma kayi ahankali nibazan maka baki ba, addu,ata zata bika aduk inda kake,

Allah ya tsareka daga sharrin mace, kuma bazan raba aurenku ba, Allah kadai yasan rabon daya boye atsakaninku. Allah yabada zaman lafiya.

Kuka sosai Abbas yakeyi idanunshi har sun kumbura, Jafar se lallashinshi yakeyi, dago kai yayi yace nagode Umma da kika fahimceni, Allah nagode maka daka bani Uwa me saurin fahimta,

Insha Allah Umma bazan baki kunya ba, zan dage inga namayar da gidana dana rasa, sede idan wani hukunci na ubangiji. Umma tace Jafar kutashi kutafi dare yayi, Allah yayi maku albarka.

Magungunanta Jafar yabama Umar yace gashi da safe kabata tasha da rana ma haka, sallama sukayi mata, suna godiya suka fita, da kallon tausayi tabi Abbas.

Kallon Umar tayi tace Umar karika saka Yayanka acikin addu'arka, Allah ya jarabceshi Umar yace to Umma, muje ki kwanta, kuma dan Allah kada kisa abun aranki yadameki, kinga bakida wani ciwo ayanzu.

Seda Jafar yabi Abbas har gidanshi dan yaga gidan, tausayin abokinshi yakamashi ganin irin gidan da aka sashi yakama, yasan inba wani iko na Allah ba, Abbas baze iya biyan kudin gidan ba idan suka kare.

Jafar yace to Abbas asha angwanci lafiya nizan tafi, kamo hannushi yayi yace inafatan baka fushi dani? Jafar yace haba Abbas, wlh bana fushi da kai, sede inaso daga yanzu kasa aranka zaka cikama Umma alkawarinta, zakayi kokarin maida gidanka daka rasa?

Abbas yace insha Allah, murmushi Jafar yayi yace naji dadi, seda safe muhadu agidan Umma, Abbas yace angama, hannu yabashi sukayi sallama yashiga gida.

Bacci yasamu Labiba tanayi babu kowa dan dama yace mata idan suntafi ta kulle gidan tunda yana da mukulli idan yazo seya bude, tashinta yayi, tana tashi tace haba Abbas ina katsaya haka kalli agogo fa?

Zama yayi yace muna asibiti Umma badata lafiya, saurin tashi tayi tace meyasameta? Nan yafada mata duk abinda yafaru, kwalla ne suka fara zubo mata cike da tausayin Abbas tace dan Allah kayi hakuri, nasan nice silar komai,

Amma kayafemun, kuma gobe zamuje inbama Umma hakuri kaji? Murmushi yayi yace bakomai Labibata Umma batayi fushi ba, tace nide duk da haka dan Allah.

Yace shikenan Allah yakaimu goben tace amin, wlh duk shawarar Hauwa ce amma kasan ba halina bane, yace nasani Labiba, kuma insha Allah zan maida gidana, tace Allah yasa.

Washe gari tare sukaje duba Umma, sede abun mamaki sam Umma bata canza ma Labiba fuska ba, asalima ko maganar batayi mata ba, hakan yasa Labiba duk ta tsargu,

Dukar da kai tayi tace Umma nasan nayi maki laifi, amma dan Allah kiyi hakuri, wlh sharrin zuciya ne, da kuma bin shawarar kawa, amma nagane kuskurena insha Allah hakan bazata kara faruwa ba.

Murmushi Umma tayi tace bakomai Labiba, dama haka akeso idan mutum yayi badede ba, yagane kuskurenshi, inafatan zaki kiyaye da bin shawarar kawaye? Tace insha Allah Umma.

Sun dade kafin suka tashi suka tafi, gidan kakar Labiba suka wuce, tana ganinsu tace wane irin mutane ne ku? Duka yaushe aka kaita har zaka fara fitowa da ita? Abbas yace kaka gida mukaje duba Umma bata lafiya shine

Please Login or Register in order to submit comment