Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nemansu bazasu kare ba, domin akullum kana fita nema.

Daga karshe ina mika godiyata ga mutane biyu masu matukar muhimmanci arayuwata, ba wasu bane se wadannan mutanan guda 2 nakusa dani, bazan taba mantawa dasu arayuwata ba.

Sunzama babban jigo arayuwata, akullum ina rokon Allah daya saka masu da abinda yafi komai alkhairi arayuwarsu, nagode sosai inama kowa addu,ar yakoma gidanshi lafiya, kuka ne yaci karfinsa hakan yasa yazauna.

Gaba daya gurin yadauki tafi, godiya yan jarida sukayi mashi suka tafi, haka taron ya watse kowa yana jinjina ma Abbas abisa rayuwar dayayi.

Bayan angama kwashe kayan gurin Alh, Abbah yayi masu sallama yatafi, godiya sukayi mashi yatafi, nan kowa yanufi gidanshi.

Wanka Abbas yayi yanufi masallacin cikin unguwa, akofa suka hadu da jafar suka nufi masallaci, bayan sunyi sallah zuka zauna seda akayi isha,i suka tafi.

Abinci kawai yaci ya kwanta, domin bakaramar gajiya yayi ba, cikin dare suna bacci Labiba ta tashi da nakuda, tashin Abbas tafarayi, cikin bacci yaji ana tashin shi, dasauri yatashi, ganin halin da Labiba take yasa yayi saurin tashi yasaka jallabiyarshi.

Jafar yakira awaya yafada mashi, kafin sufito harsu Jafar sunfito shida Maryam, nan suka nufi asibiti, suna zuwa aka ansheta dan takusa haihuwa.

Ko minti 30 bata yiba, ta haifi diyarta mace, albishir akayima su Abbas, cike da farin ciki suka nufi dakin, bayan takara minti 30 aka sallamesu, gida suka nufa cike da farin ciki.

Ranar suna yarinya taci sunan mamar Labiba Aminatu ana kiranta da MINAL, sunan yatara mutane dayawa, su Maman Zainab da Hauwa sune iyayen suna, harsu laure da Laraba seda sukazo dan sun hadu da Maman Zainab akasuwa ita take fada masu, kwatancen gidan tayi masu segashi sunzo, ita ma Maman Zainab cikinta ya tsufa.

Bayan suna da sati 2 akayi bikin Umar da amaryarshi Halima, sosai Abbas yakashe kudi abikin agidan da Ummansu take aka kai amarya abangaren Labiba na da, shikuma Umar yadauki bangaren Abbas, yarinya ce me hankali da ladabi, hakan yasa suke zaune lafiya da Umma.

Buba ne tare da Abbas yana fada mashi yasamu wani gida acikin darmanawa can layin wanzamai, nasayarwa ne, sede karamine, kuma yayi ciniki, shine yace zesiya.

Murmushi Abbas yayi yace meze hana kuyi zamanku anan, nida bazan tasheku ba, Buba yace wlh tunda naga rayuwa kuma naji labarinka tundaga lokacin nasama raina gida kona kara ne, insha Allahu sena mallakeshi da kudina, domin na lura babu abinda yakai MUHALLI DARAJA.

Kaduba kaga irin gidan daka gina amma fadi kake har duniya tanade bazaka gina gidan dazakayi farin ciki dashi ba kamar gidanka na farko, shiyasa nima nakeso insamu gida nawa na kaina, wanda kudi nane suka sayamun, komin kankantarshi nasan zuwa gaba zan samu wanda yafishi.

Kai Abbas ya jinjina yace amma Buba gaskiya ka burgeni, haka akeso mutum yazama me zuciyar nema, duk yanda mutum zebaka aron abu matukar ba kyauta yabaka kada kadogara dashi, domin rayuwa tana iya canzawa ko mutuwa tazo, kaga dole mutum yatashi yabar gidan.

Bakomai kaje kasiyi gidan ni kuma nadauki nauyin gyaranshi da komai, godiya Buba yayi mashi yatafi, sosai Abbas yaji dadin yanda Buba yayi wannan tunanin dan dama yaso ya bashi wannan shawarar, amma gudun kada Buba yace yana mashi kora da hali yasa ya kyaleshi.

Ayau ne, za,a kara zabar wadan da zasu sake fitowa takarar Chairman na Wapa, mutane dayawa Abbas sukace sunaso yafito, dan acikin yan takarar ma mutum daya ne, yafito, ada Abbas cewa yayi baze sake tsayawa ba, dan bayaso yashiga hakkin masu nema, amma yanda mutane suka rika damunshi,

Har gidan Alh, Abbah sukaje sunaso yasa baki Abbas yasake fitowa, ganin hakan ne yasa Alh, Abbah yayi mashi magana, baya iya musu da Yayanshi shiyasa ya amince.

Aranar da akayi zabe Abbas yacinye kuri'ar, kowa farin ciki yakeyi da wannan zabe, yasamu kyaututtuka dayawa, haka kowa ya watse Jafar da Abbas suka nufi gida.

Bayan wata 2 Abbas ya kaddamar da gidanshi daya gina afilinsu na gado, babban gida ne yayi me hawa 2, dakuna ne masu yawa yayi asama da kasa, kuma kowane daki ciki da falo,ne se bandaki da kitchen aciki, ginin yayi kyau,

Alokacin da akayi tallar gidan, babu bata lokaci mutane suka fara neman hayarshi domin Abbas yasaka kudin babu yawa sosai, dan dama yace saboda marasa karfi ya ginashi amatsayin sadaka ga Babansu.

Mutane sunyi mamakin yanda yayi wannan gida me tsari amma yasa mashi kudi kadan, domin gidan babu ruwanka da wani kowa da gurinshi, gate ne kawai daya se filin gidan, shima kuma Abbas da kanshi yadauki megadin gidan da kuma wanda zerika kula da tsaftar gidan dan gudun kada abarshi ya lalace.

Zaune suke afalon Umma sunzo dubata, su duka hadasu Jafar da Maryam, tare suke da Alh, Abbah da matarshi, Umma taji dadin wannan ziyara dan hada Maman Jafar.

Bayan sungama gaisawa Umma tace gaskiya naji dadin wannan ziyara, Allah yakara hada kanmu baki daya, Mama tace aminde, gashi Allah beyimu dayawa ba, acikin zuri,ata amma yau gashi mutanan arziki sunzama cikin zuri,ata.

Alh, Abbah yace dama haka rayuwa take, idan karasa ta wani guri, se Allah ya baka tawani gurin, kallon Abbas yayi yace kasan dazu wasu mutane sukazo gurina, irin dillalan nan ne, suna zama a tsohuwar unguwarku.

Wai sunzomun ne, da maganar gidanka daka bada haya, wai suna ganin bekamata ace kayi wannan gidan me kyau da tsari, wanda manyan mutane yakamata ace kabama haya amma kasa mashi kudi kadan, kuma kaje kabama talakawa hayarshi.

Kasan me nace masu? Kai Abbas ya girgiza, Alh, yace cemasu nayi acikinku akwai wanda yazuba jarinshi cikin gidan ne? Nan suka fara zare ido, suna kame kame,nace masu tunda de babu ko sisin ku aciki dan Allah kusama kanku salama kuje kuyi abinda yake gabanku.

Da de sukaga bazasu samu fuska agurina ba, shine sukatafi, dariya sukayi Jafar yace kasan yanzu mutane basuda wata sana,a se saka ido akan hidimar wani, ka duba kaga babu ko sisin su aciki amma sukazo suna gulma.

Nima jiya seda wani yace mun wai bekamata Abbas yasa kudi kadan ba, gida kamar kana cikin gidanka amma kuma kudi kadan, nima ban bashi fuska ba, haka yatafi. Abbas yace duk ku kyalesu zasuyi sugama,

Kuma insha Allah bazan kara kudin hayar ba, ina rokon Allah ya albarkaci wanda zasu bani, domin ba cika kudi agidan haya shine riba ba, albarkar kudin ita akeyimawa, wlh, tun lokacin da muka zauna agidanmu na karshe azaman haya, tun daga lokacin irin gidan ya fucemun arai.

Ace gidan mata 4 kowa da mijinta da yaranta amma dukansu abandaki daya zasuyi amfani, babu kitchen tsakar gida se wanda yaga dama ze shareta, ko wace irin matsuwa kake da ita sekajira wanda yashiga bandakin yafito.

Haba shiyasa akullum nake kara rokon Allah ya tsaremu daga sharrin zaman haya irin wancan
.
Bayan da Allah ya azurta ni, babu abinda yafadomun arai kamar in gina gidan haya, alokacin daza,a fara ginin me zanan yatambayeni wane iri nakeso, tunawa da irin wahalar da mukasha yasa nafada mashi irin wanda nakeso.

Wlh koyanzu na kwanta bacci da farin ciki nake kwana idan natuna mutanan dasuke haya agidana suma suna cikin wadata da farin ciki, agaskiya zaman haya beyi ba, matukar ba gidan mutum daya bane, kai gaba daya ma Allah yayi mana tsari dashi.

Umma tace amin, Abbas, Allah yakara buda maku kuci gaba da temakon nakasa daku, domin idan mutum yana da dukiya bayajin farin ciki meyawa idan har yatasata yacinye dagashi se nashi.

Amma matukar kafitar da ita kayi sadaka alokacin zakasamu farin ciki meyawa, Allah yakara shige mana gaba, sukace amin.

Abbas yagama gyarama Buba gidanshi, yayi kyau sosai, se godiya yake mashi, kuma aranar da aka gama saka kujeru da labulale suka koma gidan, Hauwa de har aranta taso suzauna agidan su Umma, duk da a boys quarters suke amma gani take yafi nasu, tunda akwai komai, ga wuta ga ruwa, idan babu ma akwai generator, hakade tayi shiru tabar abin aranta, dan kada tayi magana tajama kanta.( Lalai me hali baya taba barin halinshi, naga alamar Hauwa wannan halin nata ajininta yake, sede muce Allah yashiryeta, amin).

Motar da Abbas yake hawa yabarma Umar, motoci guda 3 yasa aka kawo mashi, 2 iri daya se dayar daban, cikin biyun yace ma Jafar ya zabi daya, sosai Jafar yaji dadin kyautar, baki yabude zeyi godiya, Abbas yace wlh idan kasake kamun godiya batawa zamuyi sosai ma.

Murmushi Jafar yayi yace towai kai ko haihuwar mutum kayi yamaka abun alkhairi ai godiya tazama dole, balle ni da ba haifaka nayi ba. Abbas yakara daure fuska yace toni banaso, kawai kamun addu,a senafi jin dadi, amma idan kanamun godiya banajin dadi araina, se inga kamar irin nabaka sadakar nan,kai kuma kafi karfin haka agurina. Dariya Jafar yayi yace shikenan angama Allah yabarmu tare, yakara tsaremu daga sharrin ma hassada, murmushi Abbas yayi yace yauwa kokaifa, amin.

Zaune suke shida Labiba bayan sungama cin abinci, Abbas yace kulle idonki, murmushi tayi tace naki wayonka haka nan kaci zalina kuma ka gudu, dariya yayi yace wlh babu abinda zan maki, amma idan baki kulle ba, zanje gurin mejin maganata insata ta kulle, kinga se inyi mata abinda zan maki.

Saurin kulle idonta tayi, dariya yasa yace ashede yan matan tawa tana tsoron kishiya? Hannunta yakamo yasa mata mukullin mota, yace bude, cike da mamaki tace kamar mukullin mota? Yace shine, kuma takice, jiya nasa aka kawo mana ita.

Su Umma da Maman, Jafar da Kawu karami kuma nabiya masu hajji, idan Allah ya kaimu wata shekarar kuma mu semuje. Rungumeshi tayi tana fadin bansan dawane baki zanmaka godiya ba, duk irin yanda na kuntatama rayuwarka abaya amma bakada burin daya wuce ka faranta mun.

Hakika Dadyn Ansar kai mijine da kowace mace yakamata tayi alfari da samun irinka, wlh nasan da wani nayima irin abinda namaka, ko be sakeni ba, idan ya tsinci kanshi a yanayinka nayanzu wlh seya auro mata har 3, kodan yabani haushi, amma kai inbanda alkhairi babu abinda kake bina dashi. Nagode Allah yabarmu tare, yabani ikon faran tamaka akoda yaushe.

Abbas yace amin matata, ai kema kin cancanci inyi maki duk wani abu daya kamata saboda kinyi mani halarcin daba kowace mace bace zata iya yimani abinda kikayi mani,akullum banida burin dayawuce infaranta maki, fatana Allah yabarmu tare,

Kuma daga yau banaso ki kara tuna rayuwarmu tabaya, kidena tunanin kinsani narasa MUHALLINA, dama can arubuce yake a kaddarata, ko ba ta dalilinki ba sena rasa gidana, kuma hakan daya faru kinga yazamar mun alkhairi tunda har na karbi kaddarar da Allah yadoromun, kinga canjin dana samu.

Ko ayanzu nasamu darasi, kuma nakara sanin DARAJAR MUHALLI, fatana Allah yashige mana gaba, Labiba tace amin mijina abin alfahari na.

ALHAMDULILLAH!!!

Ina mika godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wanna littafi nawa mesuna DARAJAR MUHALLI. Kurakuren dasuke ciki Allah ya yafe mana, duk wanda yasamu wani guri wanda bemashi dadi ba, koya bata mashi rai, iname bada hakuri, domin dan adam ajizi ne.

Ina mika godiyata ga dukkanin masoyana, da wadanda na sani dama wanda bansani ba, nagode da kulawarku da kuma addu'arku agareni, Allah yabar kauna da zumunci.

SADAUKARWA!!!

Na sadaukar da wannan littafi nawa DARAJAR MUHALLI ga Mahaifita HAJIYA RUKAYYA MUSA KALLAH. Allah yakara mata lafiya da daukaka, amin.

Sekunjini alittafina mezuwa insha Allah me suna RAYUWAR MATA AYAU.

BISSALAM.

UR'S.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment