Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

'yata" yana fadin haka yai waje da kallo Dalah ta bishi cikin jin dad'in nuna kulawarsa ga 'yar tasu guda tal kamar rai da yake.

Lokacin da yaje gidan Adama tace masa ta bar gidan tun d'azu nan fa yaji ya susuce da sauri cikin azama ya juyo yana kalle kallen inda zai ganta can ya hangota tana cikin yaran anguwa suna wasa karasawa yai yana cewa "Indo na me kike yi anan zo mu tafi gida" d'agowa Indo tayi ganin ubanta yasa da gudu ta mi'ke tana zuwa ta d'afe shi tana cewa "baba" daukarta Balarabe yayi yana cewa "me kika zo yi nan"? Tana washe baki tace "wasa" "wasan kuma har nan? Indo na muje gida kinji" to tace tana rike hannunsa yana tafe tana masa zance suka zo wucewa ta gefen wata mace dake zaune tana sakin 'kosai a wani kofar gida kana ganinta kaga 'yar duniya dan hatta bakinta yayi bakin busa haya'ki taje tayi rayuwa a gurare daban daban tasan harka har ta had'u da wani mutum alhaji me kud'i ya aureta ta haifi yarinyar gud'a d'aya Bahijjah kamar gaske suna zama cikin lumana rana daya ta aika shi lahira ta washe dukiyarsa tayo awon gaba da ita da yake ta haram ce tuni tasa tagaba ta 'kurmushe kamar yadda wuta ke cin audiga ta wajen inda take sana'arta Balarabe ya biyo daidai zai wuce cikin shishshigi ta d'ebi 'kosan a leda tana cewa.

" 'yan mata ga kosai".

"A'a ta gode kibar kayan ki" Balarabe ya fad'a batare daya kalli inda take ba kara matsowa tai tana cewa "haba kai kuwa ba kyau maida hannun kyauta baya dan Allah ka bari ta kar'ba" dakatawa Balarabe yai cikin jin haushin ta da sauri ta mi'kewa Indo ledar tana cewa "ki gaida mamanki" to Indo tace kafin ta sake magana fuuu Balarabe ya bar gurin da kallo ta bishi tana cewa wacce ke zaune kusa da ita.

"Ke Meroh kinsan wannan mutumin? A ina yake"?.

Dariya Meroh tayi tana gyara daurin kwalin kanta ta soke shi a gaban goshi tana cewa "meya faru kike tambaya"?.

Daidai Balarabe yasha kwana ya 'bacewa ganin ta tace "ba komai kawai kallo d'aya nayi masa naji ina son sa" zaro ido waje Meroh tayi "kai 'kawata kin d'ebo da zafi kinsan waye wannan har kikace kina son shi bazai ta'ba aurenki ba".

Jiki a sanyaye tace "meyasa kika ce haka"?.

Kai Meroh ta rausaya "saboda ba mata a gaban sa matar sa daya ce kamar rai sunanta Dalah yana matukar kaunar ta ita da wannan yarinyar da kika gani a hannunsa dan haka gara tun wuri ki saukewa kanki wahala".

Kai ta girgiza tana sake kallon hanyar daya bi tace "Meroh bazan iya ba ina son sa kuma dole saina aure shi ta dad'i kota akasin haka da yardarsa koda 'kinsa da amincewar sa ko da karfin hatsi nidai saina aure shi Meroh kiban shawara tun bayan rasuwar baban Bahijjah ban kara ganin Wanda ya kwanta min a rai ba sai shi yanzu ya zanyi"?.

Ta'be baki Meroh tayi "ya zakiyi kuwa Asabe bayan hakuri kece 'bakuwar zaman garin nan amma mu da bamuje ko'ina ba munsan waye balarabe ba mutum ne mai wargi ba baya daukar raini ki taka a sannu".

Shiru Asabe tai na d'an lokaci tana tunani kafin ta d'ago tana kallon Meroh tace "to amma kawata babu wata hanya da zanbi ya soni ko mu 'kulla mu'amala daga nan na samu kusanci dashi"?.

Zaro ido Meroh tai "ki samu kusanci da wa"? Lallai kam Asabe kice mu tanadi geron waina dan wallahi kinji na rantse miki idan kikai kokarin cusa kanki da masa shishshigi tofa maganar gaskiya wata rana saidai ki jiki a kabari dan balarabe mutum ne mai zafi".

Tsaki Asabe tai tana cewa "duk zafinsa yayi ta banza akwai inda zan kai shi a gama min dashi wanda sai yadda naga dama zan juya shi kamar yadda ake diban ruwa a randa yayin da ake jujjuyata yadda ake so kin gane".

Dariya Meroh tayi "humm Asaballiye tawa na gane mana wato akwai wani abu da kike shirin yi ko akwai wata muguntar da kike son had'awa".

Kai Asabe ta jinjina tana cewa "tabbas Meroh ina son wannan mutumin kuma duk rintsi saina aureshi kota tsiya kota arziki ko yana so ko baya so dan ban ta'ba ganin abu ina so na rasa ba kuma bazan fara akan sa ba a yau din nan basai gobe ba zan fara shiri na domin cika buri na idan naga dama nan da sati sai an daura mana aure dashi" sauke ajiyar zuciya Meroh tayi tana cewa "shikenan 'kawalliye romon gwada mukam 'yan rakiya ne idan abun ya tabbata" "ai ko zai tabbata Meroh ki zuba ido saina baki mamaki kinsan Marka aminiyata ce tasan lungu da sa'kon bokaye ita zan nema" Asabe ta karasa maganar tana sake kallon hanyar da balarabe yabi ha'ki'ka tana kaunar sa bazata cuci kanta ba zata samu mafita ita dai Meroh kallon Asabe kawai take tana tausayawa matarsa domin tasan wace Asabe indai ta 'kwallafa ranta akan balarabe bazata kyale shiba saita samu ta aureshi.

Ganin yadda gabadaya lamarin Ilyah ya cakud'e yasa hankalin Ramatu yai matukar tashi kuma ta kasa gane alhaki ke bin Ilyan na rashin biyayyar da yaiwa Baffah sai kawai ta fara zaton ko Salamatu ce tayi wa Ilyah siddabu dan haka ta dauri niyya ta tafi gurin boka da akai mata kwatance yana cikin wani ba'kin daji abun tsoro tafiya miliyon kasiran kafin ta isko inda yake.
Tsoro ne ya mamaye Ramatu jin wani irin 'kugi da gurnani kamar ta shiga tsakiyar dajin da namun dawa suke rayuwa jikinta ne ya fara rawa jin an daka mata tsawa yasa taci wani uban tuntu'be ji kake kifff tass ta kifa kasa wata tsawar aka kuma sakar mata wanda a wannan karon Ramatu yanke jiki tai tana fad'uwa kasa a sume wata ba'kar mahaukaciyar dariya aka saki saiga wani irin abu me dubu ya dira a gaban Ramatu tare da fara gewaya ta zuwa wani lokaci saiga Ramatu an d'aga ta sama ana jijjiga ta wanda wahala tasa tilas ta farka tana bud'e idonta ganin ta a sama ana majujuwa da ita yasa ta fara ihu tana kururuwa lokaci guda kuma tai tsit ta kame guri daya jin an daina juyata kasa ta le'ko taga shakka babu tayi nesa da 'kasa yanzu ya ita ya zatai tana cikin wannan tunanin taji an fisgota da mugun 'karfi yuuuuu tayo kasa ji kake tim ta daki 'kasa 'kara ta saki tana kiran "wayyo Allah na shikenan na mutu na lalace........................

"Rufa mana baki!!! Me ya kawo ki nan"?.

Jikin Ramatu nata kakkarwa ta mi'ke da sauri tana shirin zubawa a guje aka kuma jawota baya 'kiiiii tasss ta kuma kifawa nan guri ya kaure da kukan jirajirai zuwa wani lokaci kuma aka daina kukan sai dariya tuni Ramatu ta yada kwalin kanta dan gyale da takalmi tuni sun dad'e da fad'uwa.


"Ku kamotaaa ku ri'ko ta yau zamu sha jinin ta ku tatsilo mana ruwan idonta ku zu'ke kwakwalwarta๐Ÿ˜ฒ๐Ÿคฃ".

Jin haka yasa Ramatu wage baki cike da tsoro zata kurma ihu aka daka mata tsawa "durkusa anan ki sunkuyar da kanki kasa ki rufe ido idan kikai kuskure zaki hallaka" jiki na 'bari Ramatu ta durkusa tana runtse idonta da 'karfi.

'Dif taji gun yayi shiru kamar babu halitta mai rai daga baya taji iska da guguwa mai karfin bala'i tana kad'awa sai kuma taji saukar abu kusa da ita timmm ga tafiya diff diff anayi jikinta rawa yake sosai zuciyarta na bugawa tana nadama da danasanin zuwan tanan.

"Bud'e idonki kiyi kalloo๐Ÿ‘ป".

Da sauri Ramatu ta bud'e idonta ganin wasu kalar ba'ka'ken halittu tai suna yawo jikinsu duk gashi idanuwan su jawur ga babbansu zaune kamar dutse a kafe kato dashi ya gwalalo mata ido ha'koran sa za'ko za'ko.

WASH ALLAH NA GASKIYA FANS NA GAJI ๐Ÿ˜ž TYPING ๐Ÿ“ฒ DA WUYA GA AZUMI SAI ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH ZAN DORA MUKU INSHA ALLAHU.

Mrs Al'ameen Ahmad ce mai tambarin yma dutse Jigawa new world new life and new style ๐Ÿ‘Œ sabuwar duniya kuzo ku kallo dad'i yana Jigawa garin ilimi garin addini zaman lafiya Jigawa ๐Ÿ˜œ.

MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน


TYPING ๐Ÿ“ฒ {sat, Apr12 11:59AM}
YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

๐Ÿ’ŽME KAMAR SARKI ๐Ÿ’Ž


WhatsApp no:+234 8160983083

MRS AL'AMEEN AHMAD CE MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY ๐Ÿ’ƒ.

๐Ÿ‡ ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU 'YAN UWANA MUSULMAI BARKAN MU DA SHAN RUWA๐Ÿฅ› FATAN ANYI SALLAH LAFIYA๐Ÿ‡๐ŸŒน.

*****
KAMAR YADDA NA ALKAWARTA CEWA IN ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH DA RAI DA LFY ZAMU D'ORA LITTAFIN ME KAMAR SARKI ๐Ÿ‘‘ ALLAH YA KAWO MU DAN HAKA KU MATSO MU TAFI TARE DAN YAU ZAMU SHIGA DUNIYAR NISHADI ZAMU KWASHI FARIN CIKI YADDA YA KAMATA ๐Ÿ˜‚๐Ÿ™ˆ๐Ÿ˜.

Wannan page din naka ne d'an uwa rabi jiki inai maka barka da sallah fatan alkairin Allah ya kai maka duk inda kake kaida ahlinka d'an mutan kanawa.
YUSUF KING__SKEEBOY๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘‘๐ŸŽง๐ŸŽง SHATAN RAPPER๐ŸŽถ๐ŸŽถ REAGEA RP RAP DA KUMA HAUSA HIP HOP YAYAN ZAINAB (KALAR CAMERA) ๐Ÿ“ธ DA NA'IM.
๐ŸŽค๐ŸŽผ๐ŸŽ™๏ธ๐ŸŽง๐ŸŽน๐ŸŽต๐ŸŽธ๐ŸŽถ๐ŸŽท๐Ÿฅ๐ŸŽป๐ŸŽบ )(*(*()*)*)( ๐ŸŒน )(*(*()*)*)(


27~AL-BASIR
The all seeing
28~AL-HAKAM
The judge

14~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Mutta'kinah.

๐ŸŒ„ CARICATURE ND WREAK๐ŸŒ„
Episode 27_28
Kuka Ramatu keyi kamar ranta zai fita cikin wahala da gajiya ga wani masifaffan tsoro daya gama cikata na ganin wannan baka'ken halittun da'kyar take sauke numfashi tayi zaman dirshan a kasa.

"Ku kamotaaa naceeeeh".

Jin abinda wannan mummunan ba'kin dodan ke cewa yasa Ramatu zunbur ta mi'ke a gigice ta fita da gudu a gurin ko waiwaye babu a tunaninta suna binta sai datai nisa sosai ta fita daga dajin kafin ta waigo ganin babu kowa yasa taja burki tana haki ta tsaya tare da goge gumi ta kalli gabas ta kalli yamma har yanzu tana cikin dajin amma tasan duk tsiya ta tsira domin ta baro wajajen wadannan halittun.

Ganin abu tai ya dira gabanta tare dayin girgiza sai taga wannan katon dodon nan muryar shi kamar saukar tsawa yace.

"Hummm saiii yanzunn kika karaso? Barka da zuwa nan ma fadar muceeeeh".

Yana gama fad'in haka taga gurin ya cika da dodannin masu jan ido da gashi ga babban nasu yana mata kallon nama a dafe a kwano hannunsa ya d'aga yana nuna Ramatu sai ji tayi anyi sama da ita suuu zuwa wani lokaci taji tayo kasa taffff sai gata zaune a gaban sa kan wani dutsi na tsafi an kewaye ta tana tsiyayar wuta mai ci sosai a wannan lokacin kasa kuka Ramatu tai ta 'kame guri daya kawai tana jiran mutuwarta.

"Meye ya kawo ki nan, me kika zoyi a gurin muuu? Fad'i muna sauraron ki".

Bakin Ramatu ne ya soma rawa ta kasa magana tsabar tsananin tsoro sai kakkarwa take.

"Kiyi maganaaa mu ba'ai mana shiru anan idan kuma ba haka ba zamuyi farfesun ki"๐Ÿ˜.

Zaro ido Ramatu tai hawaye na zuba batasan lokacin data d'ora hannu aka ba tana cewa.

"Kuyi hakuri kada ku kashe ni dan Allah.................


Tsawa duk suka daka mata "rufe mana baki kafin mu cinye ki danya yanzun nan fad'i bukatar ki".

Da'kyar Ramatu ta iya saita kanta har lokacin muryarta bai daina rawa ba ta soma magana.

"Dama na kawo 'karar kishiya ta ne tayi wa d'ana Ilyah asiri ya daina sana'a duk kudinsa ya kare baya ta'buka abin arziki shine nace inaso itama yadda bata bari naji dad'i ba kar nata d'an ya jiyar da ita dad'i".

"Mun fahimce ki amma ba itace taiwa d'an ki asiri ba saidai dama mu ba'a neman mu da alkairi zalunci kadai muke sonyi yanzu me kike so ayi mata?.

Dan shiru Ramatu tayi tana tunanin muguntar da zata had'a mata kafin ta d'ago tana cewa.

"Boka so nake ayi mata abinda zaka kamu da jinyar kwanciya wacce har abada bazata 'kara tashi zaune ba dukiyar da take ta'kama d'anta yana dashi ta 'kare a wajen nema mata magani shine abinda nake so".

Dariya duk gurin suka kama sunayin wata wasu irin maganganu.

"Yadda zaki aikin ki bari sai 'kafa ta dauke cikin dare kowa yana barci zaki fito bayan gari da ruwa ki zuba magani a ciki saiki wanka da ruwan a gurin ga wani d'an gatari dashi zaki tonon da zaki binne maganin saiki kira sunan Salamatu sau uku kina kafta gatarin a kasa idan kin gama saiki mi'ke ki koma gida canma kije kiyi haka ki tababata babu wanda ya ganki to zaki nasara shikenan kin gama komai burin ki zai cika amma ki sani idan kika fara aikin mu babu dainawa duk randa wani ya kamaki zaki mutu idan kikai kuskure zaki mutu kuma ba'a mayar mana da aikin mu sannan abinda kika aikatawa wani ko wata rana zai dawo kanki".

Zaro ido Ramatu tai kamar zai fito waje tace "zai dawo kaina a'a boka na fasa na hakura zan canza wani guri...........

Marin da aka kifa mata ne ya hana ta karasa abinda take son cewa har ha'korin ta daya Saida ya fita cikin mamaki taga katon dodan ya dauka ya sashi a bakinsa ji kake karass kass yana taunawa kamar ya samu kwakwa yana ya bud'e bakinsa saiga wata tsuntsuwa ta fito ba'ka wuluk tazo ta sauka a gaban ta tana aje mata wasu abubuwa kafin ta koma wannan ha'korin nata daya fita.

Ihu Ramatu tai wanda hakan ya baiwa ha'korin dama komawa bakinta ya dasu a inda ya fito hannu tasa tana shirin d'id'oshi daga bakinta tsawar data sauka yasa a firgice ta matse jikin ta guri daya a bisa tsautsayi ta d'od'awa yatsarta cizo harda jini.

"Dauki kibar nan ladan aikin mu saiya ci zaki dawo nan da wata biyu idan kuma baki dawo ba mu zamu nemo ki har inda kike kada ki saki kiyi kuskure idan kin tafi ba waiwaye kada ki fad'awa wani koda d'anki ne".

Mi'kewa Ramatu tai jiki na 'bari tabar gurin ba takalmi ba d'an kwali balle gyale duk ta zubar dasu haka ta ri'ka cin gudu har taje bayan gari tsayawa tai tana haki ganin babu kowa yasa tayi ta shiga wani gida dake farkon gari sunyi shanyar kaya ta zari hijab babu tambaya tai gaba abinta.

Da yake tunda Ilyah ya gama gidansa ta koma can da d'akin ta da komai nata yasa kai tsaye ta wuce gidan a gaban murhu taga Bara'atu zaune tana aikin abinci batare da tai mata sallama ba ta wuce d'aki a gajiye tsaki Bara'atu taja cikin takaici tace.

"Wannan mata sai nayi maganinki da ina zaune lafiya haka kawai ya wani kawo min ita wannan ai jaraba ce duk tazo ta addabi rayuwa ta wallahi bazai yuwu ba bari ya dawo koya sauya min gida ko kuma ya sakeni gara na hakura da aurensa"..........

Jitai Ramatu tace "ke me kike cewa dan uwarki"?.

Mamaki ne ya kama Bara'atu jin yadda babu mutunci Ramatu take kallon tsabar idonta tana zakin iyayen ta.......

Katse mata tunani Ramatu tai "dake fa nake yar matsiyata wato na lura saboda da dacan kin samu guri kin bararraje kina cutar d'ana kina d'ebe masa kud'i ki kaiwa matalautan iyayen ki yanzu kuma nazo na kafa na tsare akan dukiyar d'ana shine kike zagina ko dan an rufa miki asiri an aureki shekara uku baki haihu ba amma keda za'a kora har kike batun a raba gida dan gwafar ubanki bari Ilyan ya dawo sai naga wanda zai za'ba tsanani na dake shed'aniya".

Ta karasa maganar tana daukar kwano taje ta dauko d'umamen tuwo ta koma d'aki tagumi Bara'atu tai cike da bacin rai wannan wacce irin masifa ce dan iyayenka basu dashi sai aita goranta maka harda haihuwa cigaba tayi da aikinta Ramatu dake d'aki sai aiko mata da zagi take ta tafar sauke bata ce mata ba.


Sai aikin sharar hawaye kawai take shigowar Ilyah kenan ganin tana kuka yace "ke kuma fa lafiya"?.

Daga d'aki Ramatu tace "dani ne ka saki wannan matsiyaciyar matar taka saina yi maganin ta zatasan wace Ramatu" d'an tsaki Ilyah yaja yana cewa "na saketa kamarya meye kuma ya faru"?.

"Au meye ya faru ma kake tambaya"? Jin yayi shiru yasa ta fitowa ganin ya juya zai fice daga gidan ga kuma ba'kar leda ya aje a kusa da Bara'atun yasa da gudu taje ta dauke har zaninta na neman fad'uwa kasa tace.

"Kai Ilyah zonan so'ko'kon banza so'ko'kon wofi har dan nayi maka magana akan wannan figaggiyar matar taka zaka wani fice ka barni ina 'ba'batu kamar zakar da take 'kwai wannan abun cikin ledar uban me ka sayo mata".

Dakatawa yai batare daya juyo ba yace "kifi ne zatai mana abinci dashi" yana fad'in haka yai waje.

"Kifii๐Ÿฆˆ๐Ÿ " Ramatu ta fad'a harda zaro ido tana bud'e ledar ganin su tayi da yawa kai ta jinjina "ah lallai kam yanzu wannan uban kifi daya sayo da bana nan shikenan saidai kici naci sauran ki tattara ki kaiwa almajiran gyatumin ki ko? To Allah ya tuno asirin ki yau ina nan za'a gama girki sai an zuba min nawa ina kallo dan baza'a ri'ka cuta taba haka kawai nida haihuwa keda morewa".

Ita dai Bara'atu tana shiru batace mata komai ba cikin hararrami Ramatu tace "ke ba dake nake magana ba dan 'kwanjin ubanki nace ki dauko kwano na juye" mi'kewa Bara'atu tai takaici fal ranta taje ta dauko tana kawo mata kad'an ta zuba tana cewa "wannan ya isa abincin wannan kuma nawa ne nan da gobe ina ci a hankali zan cinye kayana dauki kije".

Saida ta bari ta d'auke ta koma gaban murhun tana gyarawa da cire 'kaya saboda soyayye ne farat Ramatu tace "ke Barah tashi anan yau nice zanyi girkin bake ba daga yau bi da bi za munayi" tsananin mamaki ne ya kama Bara'atu har batasan lokacin da tace "bi da bi kuma? Sai kace kishiya ta".

Mi'kewa Ramatu tai daga inda take zaune tare da cewa "au sai kace kishiyar ki? Dan malafar ubanki nice kikewa haka dan darar ubanki shigiya tsinanniya mai siffar angulu zaki ban guri ko saina karya miki kafa kika tsaya ina magana kina kallo na da baka'ken idanu kamar kwallon d'inya ko nayi mike kama da tamilalliyar uwartaki ne me zubin itacen rimi da siraran kafafu kamar na sauro ai indai bala'i ne yanzu kika fara sha a gidan nan dan darar ubanki" ganin zata bangaje ta yasa da sauri Bara'atu ta matsa gefe ta bata gurin.

Zama Ramatu tai tana kallon yadda mai yake yawo a saman abincin tace "humm yo abune ga d'an talaka ba'a saba ba ansha fura an mutu idan ba tsabar ke ba'kar gidahuma bace taya zaki kwarar irin wannan man a cikin abinci sai kinsa mun harbu da ciwon bayamma au wato so kike Ilyasu ya sha mai da yawa ya mutu dan ki samu gado tunda baki haihu ba ko? Tab tirrr da halinki in Allah ya yarda saikin riga Ilyah mutuwa gadon da kike kwad'ayi baza ki samu ba balle har kiyi tunani gyarawa fatararrun iyayen naki ru'babben gidan su".

Ko bari abincin ya dahu Ramatu batai ba ta d'iba tare da zubawa akan kifin data baiwa Bara'atu asa a girki kawai ta koma d'aki tana cewa "na d'ebi rabo na sai kije kiyita cin kasa inda babu mai ba maggi muguwar mace wai ni zata asirce dama ai naji ance har rubutu kandiya take kawo miki kina mana abinci dashi dan ki mallake mu to bari kiji wallahi munfi karfin ki nan gani nan bari d'umamen maiya".

Shiru Bara'atu tai tana kallon kofar d'akin Ramatu kafin ta d'an girgiza kai tana daukar tukunyar tayi taku daya biyu taji sallamar 'kanwarta d'an waigawa tai cikin danne d'aci da takaicin da ta kwasa tace.

"Lawisa kece shigo mana ya kika tsaya anan"?.

Bata karaso ba tace "eh babah ce ta aiko ni wai......................

Bata karasa fad'ar abinda take son fad'a ba Ramatu ta fito daga d'aki da gudu tana zuwa inda suke cikin kalan fitina tace "me naji kina cewa kamar a taimakawa da mayunwatan iyayen ki abinci? Amma ba abincin gidan nan ba? Haram giya a gidan liman bazai yiwu ba idan Ilyasu yaci gaba da zama dake zaki talauta shi yau saidai ki kwanan gidan ku maza dauko gyalen ki ku tafi tare da shegiyar 'kanwartaki sakin uwar miji ma sakine dan haka kije na sake ki๐Ÿ˜‚ yanzun nan ki kwashi kayan ki kibar gidan nan kafin na shiga d'aki na fito" komawa d'aki Ramatu tai Lawisa dake ri'ke da baki tace "tabdijan yaya Barah kedin dama irin wannan zaman 'kuncin kike a gidan amma bakije gida kin fad'a an dau mataki ba gara da akai a gabana na gani muna zuwa gida zan zayyanewa baba baza ki dawo gidan Ilyah" tari dabai kama Bara'atu ba batai ba tana tsaye a guri daya ganin ta'ki dauko gyalen su tafi yasa Lawisa shiga ta dauko mata tana cewa "yau zaki barci cikin salama muje" kai Bara'atu ta girgiza cikin damuwa tace "Lawisa ki fahimta ba Ilyah ne ya sake ni ba bashine yace na bar masa gidan saba dan haka babu inda zanje domin shine yake aurena dan shi nake zaune".

Tun kafin Lawisa tai magana Ramatu tayo waje wuf tana cewa "au bazaki tafi ba naji kince ko? Yau kuwa zan nuna miki kalar nawa tsaurin idon" tana gama fadin haka tayi wajen turmi tare da dauko ta'barya tayo gurin su tana cewa "wallahi saina 'bare miki kai da ita" da gudu Bara'atu da Lawisa sukai waje yayin da Ramatu tabi bayansu har tsakar gidansu tana rafka kiran.

"Kandiya ke kande fito yau sainaci dambun uban 'ya'yanki".

Da sauri kandiya ta fito tana cewa "subahanallahi lafiya Ramatu na ganki da ta'barya ko takalmi babu balle mayafi".

Ramatu na haki take nuna Lawisa da yatse tace "yau saina ci uban daya haife ki zakisan wace Ramatu ke kuma nace na sake ki babu ke babu d'ana har abada idan kunne yaji jiki ya tsira matsiyaciya mara zuciya ana korarki kina mannewa saboda kinga kud'i ke kuma kandiya ya rage naki kiwa yarki fad'a ta rabu min da d'a idan ba haka ba sai munyi 'batacciya daku wallahi" tana fadin haka tai waje da ta'baryar ta a hannu kamar sabuwar kamu.

Mamaki ne ya kama kandiya tana kallon Bara'atu dake kuka tace "wai meya hada kune harda biyoki da ta'barya kuma"?.

Share hawaye Bara'atu tai tana cewa "babah kinsan halin matar nan ko ba'a fad'a miki dama da ya akai auren balle nayi shekara uku ban haihu ba akan haka tana goranta min da tsine min tace Ilyah ya karo aure wai ya auri Maimunan gidan san 'kira yar gidan malam Sa'idu to yau kuma sai ya shigo da kifi nasa a abinci ta kwace kifin ita kadai hakan bai isa ta zage ni ta hana na karasa dafa abincin ta goranta min sannan tace wai kina kaimin rubutu ina dafa musu abinci dashi ana haka Lawisa taje kawai dan taji muna zance shine tace wai kin aika a kar'bo miki abinci dan haka ta gaji sakin uwar miji ma saki ne naje ta sakeni".

Dafe kirji kandiya tai "kai jama'a mun shiga uku kinji wata masifar ko? Ni dama tun farko shiyasa ban goyi bayan auren nan naki da Ilyasu ba saboda nasan halin Ramatu koba dad'e koba jima sai wani tashin hankali ya shigo dacan ma maye balle yanzu kun dawo zama gida daya ni gara da haka ta faru ma ya sake ki yafi alkairi da wannan zaman damuwar da kike da mahaifiyarsa mu ri'ke talaucin mu bazaisa ki rasa wani mijin auren ba".

Tsaki Lawisa tai tana cewa "kinsan Allah innarmu da ace nice nake auren Ilyah wallahi Ramatu bata isa min haka ba koda taga Barah ba magana ce ta dameta ba da ace nice hummm da an d'ebi yan kallo".

Harararta kandiya tai "ke da Allah rufawa mutane baki sakarya kawai idan da ked'in cema me zaki iya yi wallahi a tsiwar ki yadda Ramatu bata da mutunci da yanzu ta dad'e da karya miki 'kafa tana daidai da zamaninki".

Ta'be baki Lawisa tai tana shigewa d'aki a ranta tana jin da fa ace itace bazata dauka d'in ba kamar yadda ta fada, kallon Bara'atu kandiya tai tana cewa "kinga Barah kiyi hakuri kinji shiga d'aki Allah yasa haka ne mafificin alkairi" Amin Bara'atu tace tana bin bayan Lawisa yayin da Kandiya tai zaman dirshan cikin jimami da damuwar tsiya da suka gayyatowa kansu na auren Bara'atun da Ilyah.


Har dare Ilyah bai dawo gida ba dan haka baisan me ake ba Ramatu kuwa

Please Login or Register in order to submit comment