Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kashe min wannan mitsiyacin yaron idan taga baya duniya dole ta ha'kura dashi shege tsinanne mara tarbiyya yazo ya gur'bata min komai wayyo Allah na wayyo nashiga uku..................,..

Katseta Markah tai da cewa "a'a dan Allah Asabe kiyi shiru haka ki daina kiran masifa akanki tashi mu tafi gurin bokan zanyi masa bayanin komai abinda faruwa ina Mai tabbatar miki Bahijjah zata dawo gareki bazata ta'ba auren Iluh bs tashi mu tafi qawata a Bari ya huce yana kawo rashin sa'a kinga yanxu ma gashi kin koreta a gidan kuma ai kinga Baki wanke biyar ba kin bata goma tunda kinsan ko tantama Babu yanzu haka tana gurin sa".

Zabura Asabe tai ta tashi tana surar hijab tace "muje Markah mu tafi gurin boka kafin zuciyata ta buga da ba'kin cikin yarinyar nan wallahi kawai kashe shi za'ai bazan iyaba" Kai marka ta d'aga "kwarai Asabe wannan ce kad'ai mafita a kashe shin zaifi sau'ki muje" fita sukai Markah na ce mata ta goge hawayen fuskarta saboda kar mutane su gani a tsaya tambayar ba'asi.

Bahijjah Kam data samu ta fita da gudu daga gidan bata tsaya ko'ina ba sai kofar shagon Iluh yana zaune sai ganinta yai aguje tana waiwaye tana kuka mi'kewa cike da mamaki duk da yasan bazai wuce akan binsa datai garin su bane amma sae yace.

"Lafiya Bahijjah meya faru haka kiga harda jini a goshinki Babu kwali ba takalmi balle uwa uba hijabi"?.

Cikin kuka Bahijjah tace "Iluh kana sona"?.

Da sabon mamaki Iluh ya kuma kallon ta yana cewa "kamar ya wannan wacce irin tambaya ce kuma? Ina sonki mana".

Kai ta jinjina tana goge hawaye tace "zaka aure ni"?.

"Eh aurenki man zanyi".

"To Iluh indai da gasken kana sona aurena zakai ayau Iluh ka koma garin ku kazo da mahaifanka su kawo komai zuwa Nan da wata d'aya a d'aura mana aure shine abinda nake so kawai kayi min yanzu ka huce min zuciya".

Kai Iluh ya d'aga yana murmushi yace "shikenan karki damu yanxu ma kuwa zanje gobe zamu zo tare dasu karki damu ai ninace Ina sonki" jin abinda yace yasa Bahijjah goge fuskarta tana samun guri ta zauna koba komai tasan idan iyayen sa suka zo dole Asabe ta karbesu ta kuma yarda da auren idan ba haka ba saita d'ebo Mata 'yan hisba😳.

Nurain yayi waya da Nafisa ya sanar mata mahaifansa zasu zo rokon arziki tunda ya fad'a Mata take ihu har mutanen gidan sun d'auka ba qalau take ba fitowa daga d'aki tai da gudu tana cewa "

"Umma ki tayani murna yanzu Nurain yake sanar min cewa na fad'a muku a cikin watan nan mahaifansa zasu zo ro'kon arziki na garin nan"

Zaro ido Bara'atu tai tana washe baki tace "tofa 'yan binni zasu zo ashe kwanan nan zamuyi manyan Ba'ki tab bari babanki ya dawo na fad'a masa a fara tanadar kayan tararsu tun daga yau wadannan shashashun yayyin naki ma su dawo a sanar musu su kawo tasu gudun mawar kilar sunan can gidan fatararran can Habu😵...

Nafisa Kam saboda farin ciki take bata kula da zancen da Bara'atun datake Mata ba kawai Kira take "wayyo Umma wallhi harna hasko ni a binni umma na kusa zama yar gayu kun kusa fara cin shinkafa yar buhu da taliya haka zan ri'ka ciko mota ana kawo muku🤭.

Itama Bara'atu dariyar tai cike dason zuciya tace "yauwa Nafisa haka nake son ji ki tabbatar kina lalarsa kud'i masu tsoka kina turo mana zan ri'ka zuwa akai akai duk bayan sati biyu😲 Ina kar'bo komai kema kwanan nan sai kiga kin gaji ubanki a sai miki gonaki filaye da shanu da kuma awakai ko".

Kai Nafisa ta d'aga "kwarai umma meyasa tun farko Salma itama nace tacewa baba tana son d'ayan abokin Nurain amma ta'ki wai ita sai Adamu yana tafe daf da qasa kamar d'ingwai d'in kaza abu kamar tuntu'be gashi gidansu talakawa ne basu da kud'i ranar naganshi tare da babansa sun tafi 'kwadago noman kud'i gonar Mai gari sunata sauri kamar zasu kifa..........,...........

Rufe mata baki Bara'atu tai tana kallon kofar d'akin Maimuna tace "ke Dan ubanki kiyi shiru kar maimuna taji kina cin mutuncin surukinta dariya Nafisa tai tana tafa hannu Bara'atu dake le'ken ta inda Maimunan zata bullo murya ta d'aga tana cewa "Maimuh Maimuh kina nan"? Jin shiru yasa ta sake kwalla Mata Kiran da qarfi "Maimuh nace kina d'aki ne ko barci kike"?.

Jitayi daga wajen kofar kewayen shanunsu ance "a'a kin ganni nan Ina baiwa raguna dusa ne Bari nazo".

"Oh na d'auka kina cikin d'aki ai"Bara'atu ta fad'a tana kallon Salma data shigo tun kafin tayi magana Nafisa tace "Salma ki taya ni da na kusa tafiya binni a watan nan mahaifan Nurain zasu zo maganar auren mu".

Murmushi Salma tai cikin tausayawa Nafisan haka nan taji jikinta yayi sanyi hankalinta bai kwanta da auren Nafisa da Nurain ba amma dan kar suce ba'kin ciki take Mata yasa tace.

"Alhamdulillah na taya ki da murna sosai Nafisa Allah ya sanya alkairi kice kwanan nan zamu shiga cikin Kano muga yadda take"? Ta karasa maganar da yar dariya.

Cikin zumud'i Nafisa ta fara ido tana cewa "kwarai Salma ki tanadi Kaya masu kyau kafin na fitar da anko ki fad'awa Adamu ya d'inka miki kamar kala biyar domin ke acan za'a baro ki sai kinyi min sati biyu ko wata d'aya kafin nasa Nurain ya dawo dake".

Zaro ido Salma tai tana kallon Nafisa da mamaki take "niii kaza mijina zakara rufa min asiri ban shirya zaman binni ba ki barni a kauye na inda nafi wayo naci abinda nake dashi nasha ruwan rafi dana rijiya zanfi zama lafiya".

Nafisa zatai magana maimuna ta karaso gurin tana cewa" gani in kaji Kira an samu amma banda kiran Dan sanda lafiya miya faru tun d'azu naji sai dariya kuke"?.

Ai tun kafin Bara'atu tai magana Nafisa tai wuf tace "umma Maimuh ki taya ni murna mahaifan Nurain zasu zo ro'kon arziki na na kusa tafiya binni"🤔.

Ba Umma Maimuh ba hatta Bara'atu saida ta zaro ido ganin yadda Nafisa ke fad'ar magana kai tsaye Lallai kam zasu Sha kallo dariya Maimuh tai tana cewa "to kice mu shirya kar'bar ba'ki Allah ya kawo su lafiya".

"Amin umma Maimuh Wallahi harna hasko ni a binni".

Kai maimuna ta jinjina tana cewa "Allah dai ya kaimu lokacin Nafisa yasa ayi a sa'a sannan Allah yasa gidan zama ne".

Amin suka ce Nafisa daketa faman sambatu tace "umma a idon zuciyata har haskoni nake a binni wai".

Murmushi Bara'atu tai tana cewa harkin hasko ki a binni Kona haskoni saboda idan kikai aure naje miki ziyara sai nayi wata dazan dawo gida saina huta😮.
UMM INJI MAI CIWON BAKI.

Baki maimuna ta bud'e tana kallon Bara'atu tace "haba dai wata fa sai kace a garin ga'ba-ga'ba kije gidan mijin 'yarki kiyi wata ana zaune lafiya"?.

"To meye a ciki maimuna Dan nayi wata ko shekara zanyi nasan yadda wannan yaron yake da kud'i bazai gajiya da yimin hidima ba dan haka wallahi zuwa zan ri'ka yi akai akai Ina kwaso Mana kayan dad'i".

Kai maimuna ta jinjina tana cewa "to shikenan Allah ya kaimu lokacin Allah yasa ayi a sa'a shine fatan mu" Amin Bara'atu tace yayin da Nafisa ta mi'ke tana d'auko hijab tace Salma wai ta rakata gidan kakanunta "gidansu Bara'atu) ta fad'o musu Salma Kam tace bazataje a dawo lafiya fita Nafisa tai Wanda umma Maimuh taji mamaki da taga Bara'atu bata hanata ba ta d'auka zatai Mata magana sai taga tayi burus har wani bin Nafisan take da kallon burgewa wai tana abun wayayyu.

Yau kam gidan malam Habu a cike yake da murna Amatu ta dawo gida na dindindin Dutse saidai taje da sunan ziyara musamman Malam Habu kamar ya mayar da ita ciki haka yasata a gaba kawai yake ta kallonta har hawaye yana zuba a idonsa batare daya sani ba muryar Amatun ce ta dawo dashi daga tunani.

"Baba Dan Allah ka daina kukan haka zan shiga damuwa".

Murmushi Malam Habu yai cikin sauri ya goge hawayen fuskarsa yana cewa "mamana hawayen farin cikin ganinki ne saboda wata irin kewa da naji tana kama ni bansan taya zan kwatanta miki ki fahimta ba mamana dukanku Asma'u Jamilah Aisha dake yarana ne kuma ina tsananin sonku amma maganar gaskiya ke kin fita dabam acikin su arai nake jinki mamana fatana Allah ya d'aga darajarki Allah ya d'aukaka minke ya kaiki matsayin da ban ta'ba zato ba mamana................

Kukan da Amatu tasaka masane ya hanashi karasa abinda yake son cewa sai kawai yayi murmushi yana cewa kada ki damu kinji mamana insha Allahu albakata tana tare dake a koda yaushe kece nutsuwa ta bana so kiyi nisa dani saidai na sani dole wata rana zan bud'e ido na rasa ki a gidana tunda zaki aure Allah yasa wanda zaki aura mamana ya mutunta minke ya rikeki ya soki ya kyautata miki ya baki kulawa wacce bamuyi zato ba saboda da gudun kada a wahalarmun dake nake jin a raina kamar bazan iya bada aurenki ba mamana amma ya zama dole, murmushi yai yana kallon ta yace.

"Shikenan kada ki damu share hawayen jeki ku sake gaisawa da mahaifiyarki tunda kina shigowa kika tsaya a guna ya kamata kije itama taji dad'i ko" to Amatu tace tana mi'kewa ta shiga d'aki yayin da Malam Habu ya sake binta da kallo yana sauke ajiyar zuciya mai akarfi yadan rufe ido a ransa yana tunani da yace zaiwa Sadi magana su koma Cameroon amma fa yanzu ya fasa babu inda zaije bazai iya tafiya yabar Amatu a gida ba gashi Hassan sai damunsa yake akan dan Allah yaushe ne aurensu bayan kwanan baya Ilyah ya sameshi yamai tas uwa da uba akan wai ya fita hanyar 'ya'yansa dama son zuciya da zilama ce tasa yake kar'be duk abinda suka bashi yana musu faran faran idan ba so yake ya hadashi da hukuma ba a musu iyaka to yayi gaggawar hanasu Hassan zuwa gidansa! Bud'e ido Malam Habu yai cike da takaicin dan uwan nasa kafin ya mi'ke yana kallon kofar d'akin Binta iya ganin takalmin Amatu dayai a kofar d'akin ya sanya masa nutsuwa ji yake kamar ya shiga d'akin ya sake ganinta kafin ya fita amma ya danne kawai ya juya yana fita a gidan.

BAYAN SATI BIYU✌️
Malam Habu yana zaune a gida bakin kofar d'akinsa akan tabarma yayi shiru yana kallon iyalansa dake kai komo a tsakar gida kowa da aikin yake sakamakon yanzu ba laifi kowacce tad'an samu jari tana juya Alhaji Bashir ne ya baiwa Amatu dubu hamsin dazata taho shine Binta ta baiwa Saude aron dubu goma tace taci gaba da sana'a inta samu ta biya zama haka babu dad'i sannan ta baiwa A'i ma dashi yanzu suke samu su d'an yi wasu abubuwan.

Kallon Binta dake wanke kwanuka Malam Habu yai zaiyi magana sukaji muryar yaji'kira da lasifika📢📢 yana shela layi layi yana cewa "yekuwa jama'ar gari mai gari ya gaisheku yace a fad'a muku duk wanda yasan ya kar'bi bashin kayan noma yaje gurin sa yanzu ana nemansa kada ka bari sai an kiraka domin masu kawo kayan sunzo yekuwa jama'ar gari............haka san'kira yayi gaba yana shele anguwa anguwa.

Shiru Malam Habu yai yana tunada da ake sauke masa tirela guda yanzu kuwa ko a mashin ba'a kawomasa damai kud'i ake bushasha kila ma sun manta dashi duk da irin dad'ewar dayai yana sayan kaya a gurin su................................

Muryar Binta ce to dawo dashi daga d'an tunanin daya tafi "Malam fatan babu kai a ciki ko tunda naga yanzu ka daina harkarsu kayan kud'i sosai" ta tambaya cike da fargaba tana kallon sa.

Kai Malam Habu ya girgiza yana cewa "a'a babu ni aciki Binta kin manta rabon dana kar'bi kayan aikin gona a gurinsu shekaru nawa harna manta da su malam Balah su Mudi Tanko akewa shelar da yaya Ilyah tunda yanzu dai sune masu abun hannu kuma sune suke da gonaki suke harkokin kayan gona bangaren kayan abinci dana lambu amma nikam babuni a wannan shafin waye zai sako fa'kirai irinmu ana maganar masu shi".

Shiru Binta tai bata sake cewa komai ba taci gaba da aikinta amma haka nan taji zuciyarta na d'ar d'ar da fatan Allah yasa babu Malam Habun a ciki tunda yanzu wannan zamani zalunci yayi yawa dashi ake ado😞.............

Sallama sukaji anayi a kofar gida kuma muryar dai sun santa d'an gidan Mai gari ne Buba wanda ada yaso Asma'u uwarsa ta hana.

"Innalillahi malam kaji abinda nake tunani ko gashi ana sallama kuma wannan dai Buba ne"? Shiru Malam Habu yai zuwa wani lokaci kafin ya mi'ke batare da yace komai ba ya fita har kasa Buba ya dur'kusa ya gaidashi sannan ya fad'a masa ana nemansa a gurin babansa kai Malam Habu ya d'aga yana cewa.

"To muje Allah yasa lafiya".

Mi'kewa Buba yai suka tafi fal ya samu gurin mai gari mutane sun cika wasu duk gulma suka zo wadanda dai akazo gurin nasu gasu nan a gefe alhazawan garin su Ilyah Tanko alhaji Gambo Malam Sabo Balah Mudi sai hura masa hanci suke suna bud'e kafad'u😣.

Zama malam Habu yai yana gaida Mai gari sannan suka gaisa da kowa kafin ya juya hankalin sa kan mai garin yana cewa.
"fatan dai lafiya ina gida Buba yaje yana cewa kana nema na"?.

Kai Mai gari ya d'aga "eh nine nasa shi a kiraka amma wadannan ba'kin da kake gani sune suke nemanka sunzo da wata takarda me dauke da sunanka da rubutu ajiki gasu nan".

Mayar da hankalinsa kansu malam Habu yai yana cewa "sannunku da zuwa ina fata lafiya dai ko"?.

Gyara zama daya daga cikin su yana cewa "kaine Alhaji Abubakar wanda ake kawowa kayan aikin gona a tirela🚒 shekarun baya"?.

Kai malam Habu ya d'aga dan yasan dama da haka su suke kiransa Alhaji Abubakar sunan da suka rubuta kenan d'agowa yai yana kallon su yace "eh nine meya faru"?.

Wasu sabin buhuna guda goma😯 yaga an mi'ko masa ga zaren d'inke buhunan da allurar d'inkewar irin bisilan nan suna ce masa.

"Sa'ko ne daga kamfanin mu cewa an biyoka bashin shinkafa buhu biyar alkama buhu uku wake buhu biyu tun wancan lokacin ba'a binciko file d'inka ba sai a wannan satin aka d'auko shi shine akace mu kawo maka ka zuba ka d'inke mu tafi dasu" ya karasa maganar yana aje masa manyan sabin buhuna masu girman gaske a gabansa.

Wata irin daskarewa Malam Habu yai jikinsa yana rawa innalillahi wa Inna ilaihi raji'un😭 tashin hankali kenan wanda ba'a sa masa rana gumi ne kad'ai ke yanko masa ya kasa furta koda kalma d'aya ce dariya Tanko yai yana cewa.

"Tofa Alhaji Abubakar masu ruwan nairori a d'au buhu maza yanzun nan aje a d'ebo musu shinkafar nan da take jibge a d'aki".

Dariya Mudi yai Shima yana karewa yanayin Malam Habun kallo yace "yo wannan talakan talakawan Ina yaga zirin shikafa ko d'aya ce a gidansa saidai in tururuwa ce ta d'auka a waje takai masa da kake cewa yaje ya ciko dame indai bada 'kasa zai ciko musu ba ko ya sayar da yarinyarsa guda d'aya wama take da suna? Ya fad'a yana kallon malam Habu ganin baya tare dasu tsabar tashin hankalin daya shiga baima san me suke ba dariya Tanko yai yana cewa.

"Hauwa'u Amatu ko?? Mamarsa cene ko 'kanwarsa na rasa ma sunan da yake fad'a mata sai ya sayarta tunda wannan masifar ta sameshi ya biya"

Cikin tsokana da isgili Mudi yace "Amma bari muyi shiru kar muji kunya bamu sani ba ko d'an uwansa Alhaji ilyah zai biya masa"?.

Jin abinda Mudi yace yasa kowa ya mayar da hankalinsa kan Ilyan suji Mai zaice bud'ar bakinsa ba kunya ko kara sai cewa yai "tabd'ijan wanne Ilyan kuke magana amma dai baniba wanine dabam ko? Allah ya sauwake na biyawa Habubakar bashi wallahi yadda nake jin haushinsa akan su Hassan da yakewa wayo fatara tasa yana kar'be musu kud'i Aiko kashesa zasuyi su d'ora masa bindiga a ka dai ina kallo ace inban biya ba zasu harbe shi wallahi saidai yai bunga uban waya hanashi tashi ya nemi kud'in"? Ilyah na rufe baki guri ya d'auki sowa hhhhh suka kuma fashewa da dariyar mugunta har hawaye ne yake zuba a idanun Tanko yana kallon malam Habu yace.

"A'a malam Habu yadai ka zama mujiya mai ba'kin jini kana jin abinda d'an uwanka yace inaga mu iye mukuma muce maka me yanzu fad'a min Ina gasa maganar daka saba idan anyi maka magana yau bakin ya mutu ko umhum uwar bari ba shegiya bace da ubanta kaima yau ka shiga uku taka ta sameka".

Tari da bai kama malam Habu ba baiyi ba kawai kuma badan bazai iya mayar musu da martani ba a'a sai tsabar takaicin maganar da Ilyah ya fad'a a gaban mutane akansa wai uba d'aya? Amma yake tozarta shi haka a gaban mutane jin hawaye na neman zubo masa yasa cikin jarumta da sauri yayi kokarin mayar dasu ba tare daya d'ago kansa ba.

Ganin da me gari yayi kamar Malam Habu baya cikin nutsuwar shi yasa yace "wa kake da suna Alhaji Mansur kace ko? To dan Allah kuyi masa ha'kurin yau ku d'aga masa kafa zuwa nan da sati biyu sannan ya gama had'a muku saiku dawo ku d'auka na roka masa wannan alfarmar".

Kai Mansur ya girgiza yana cewa "ai ba'ace mana mu taho batare da wannan kayan nasa ba sakamakon ya dad'e da fa cewa akai a taho tare da 'yan sanda su tafi dashi saboda yasan ana binsa tsawon shekaru yai shiru bai nemi company ya mayar musu ba da'kyar wasu suka sa baki cewa tsohon costumer d'insu ne amma badan haka saidai yau ya kwana acan".

Kai Mai gari ya jinjina yana kallon malam Habu kafin yace "shikenan amma dan Allah kuyi masa uzirin nan zuwa sati biyun kawai saiku dawo insha Allahu zasu samu kayanku dan Allah kunji dole rayuwa saida uziri balle shi ba kamar yadda suka sanshi da yanzu ba haka yake ba ku masa afuwa"..

"Ok to shikenan ba matsala zamu dawo nan da sati biyun Amma kafin nan ya bada kayan a gurin ka kawai da munzo da mota sai mu d'auka"? Jin sun amince yasa Mai gari yace "eh ya amince zuwa sati biyun".

Bayan sun gama magana da sauran sun kar'bi kayan da zasu kar'ba komai ya shiga manyan motocin da sukazo dasu sannan sukaiwa Mai gari sallama suka tafi daga nan kowa ya fara bajewa sai gulmar malam Habu ake wai yanxu ya zaiyi mutumin da bashi da ko naira biyar akawo masa buhu ba d'aya ba har goma ya cikasu da kayan abinci tabbbb zasuga yadda wannan cakwakiyar zata kare.

Saida Mai gari ya bari kowa yabar gurin daga shi sai malam Habu da sauran wasu yan majalisarsa mutum biyu ya kalli malam Habu yana gyaran murya yace.

"Am nikuwa malam Habu idan bazaka damu ga wata shawara dazan baka ko Allah zaisa ka amince ta yadda zaka biyasu kayan nan batare da tashin hankali ba"..

Kallonsa malam Habu yai yana cewa "amma me gari taya kenan wannan kayan da suke bukata a gurina bana karamin kud'i bane dame zan biyasu na tabbata ko yar gonata guda daya da nake nomawa na sayar kud'in bazai isa Wanda zan basuba"?.

Gyara zama me gari yai yana kara yin kasa da murya yace "eh shiyasa nace idan ka amince za'a biyasu ta ruwan sanyi saidai zamuyita da wajewa ka fara bani abinda zan nema a gurin ka yanzu ni kuma nayi maka alkawari koda zasu karo wasu buhuna goman zan biya maka bashinsu amma saika yarda da farko to mekace mun zama abokan har'kalla"?.

Cikin rashin fahimta malam Habu yace "abokan har'kalla kamar ya nifa ban gane inda ka dosa ba me gari akan me kake magana ne kamin bayani a warware yadda zanfi fahimtarka"?.

Me gari yana gyara rawanin daya kusa fad'owa muryarsa da d'an in'kina sakamakon baisan a yadda malam Habu zai kalli maganar dazai fad'a masa ba yace "so nake ka bani auren 'yarka guda d'aya a cikin su hud'un😳 akwai wacce nake so jiyama tazo ta wuce ta nan gurin har nake tambaya wannan kuma daga Ina dan ban ganeta ba saboda girman data 'kara sai akace min wai 'yarka ce ko"?.

Cike da kad'uwa malam Habu yace "wacce daga ciki kake magana" ya fad'a yana 'kure me garin da kallo dan a iya kwatancen dayai ya fahimci kamar Amatu yake nufi😲.

Kamar a mafarki yaji me gari yace "sunanta Amatullahi ko?ita nake nufi wacce ta dawo daga tafiya kwanan nan ita nake so idan har ka yarda ka bani auren ta ni kuma zan biya maka bashin duka amma me kace"?.

Tabdijan🤪😡 wani irin kallon baka da hankali ka fara hauka ne malam Habu yaiwa Mai gari yana cewa "mamana kake nufi? Ai me gari ko auren babbar 'yata Asma'u bazan iya baka ba balle mamana indai sainayi maka haka dana biya wannan bashin da suke bina na za'bi zaman gidan yarin shekara ashirin ban amince ba ka barni Allah zai horemin na biya su.............

Cikin lallami me gari yace "haba kai kuwa malam Habubakar dame zaka biyasu bayan baka da ko sisi kazo na taimake ka arziki yana binka kana guduwa wallahi indai ka bani auren ta zan baka kyautar gona ta zan baka shanu ka had'a amalanke sannan zan baka jari kuma gidanka kaga duk katangun suna bukatar gyara zansa a gyara maka harda sutura zan d'inka maka masu yawa kaji🤔"?.

Mi'kewa malam Habu yai a fusace jin yana neman kawo masa zuciya wuya da zancen banzan da yake masa ya karkad'e rigarsa yana kallon me gari da shima ya bishi da kallo yace.

"Zan sake maimaita maka kaji ko 'yata Asma'u bazan iya baka aurenta ba balle mamana ka gane indai sai nayi haka ne zan biya bashi sai na sayar da 'yata gara nayi xaman gidan yarin shekara ashirin" yana fad'in haka zaiyi gaba me gari daya mike har rawanin nasa na fad'owa kasa bai tsaya d'auka ba yace.

"Haba malam Habubakar arziki ne yake binka tsiya na korewa ka yarda wallahi da gaske nake maka zan baka komai da kake so" jin maganar da yake sake maimaitawa yasa malam Habu jan tsaki cikin takaici ya bar gurin yayin da Mai gari ya bud'e murya yana 'kwala masa kira amma ko waigoshi baiyi ba.

Haka malam Habu ya shiga gida a susuce tun kafin yai magana yaga dukkan ahlin gidan kowa kuka yake babba da yaro wato har an samu wani magulmacin yazo ya sanar musu bai iya ce musu komai ba kawai ba'kin ciki ya gama rufeshi musamman yadda ya kalli Amatu tana kuka sosai ga maganar da me gari yake masa akan ya bashi aurenta baisan lokacin da wasu baka'ken hawayen damuwa suka fara zuba daga idonsa ba ga hajijiya na d'ibansa da sauri ya shige d'akinsa yana rufe kofa kawai ya kwanta shima yana rusa kuka kamar karamin yaro😥.

INDIA CHENNAI🍒
Sakamakon ganin jikin Khimiyyah da sau'ki alhamdulillah yasa Mami tace Ajeeb da Annur su taho gida kafin suma ita da Ameer da Khimiyyan su biyo bayansu saboda kadan ya rage ta karasa warkewa saboda anyi mata wankin 'kwa'kwalwar cikin nasara kuma likita ya tabbatar musu zata dawo cikin hankalin ta saidai har yanzu bata magana muryarta rawa yake bai fita sosai sakamakon sha'ke mata wuya da Asad yai a wancan lokacin.

Ranar da Mami tayi musu zancen tafiya gidan da yake suma a matse suke a ranar sukai duk abinda ya dace washe gari suka biyo jirgin sassafe suka dawo Nigeria saidai a Abuja international airport anan suka sauka dama already tun kafin suje Mai martaba yasa motocin taryarsu sunje suna sauka ba 'bata lokaci daga airport d'in Abujan suka wuto Kano.

Wani wuri a cikin asibitin inda aka rubuta silent please🙏 da manyan ba'ki wata qofa likita ya bud'e yana shiga zaune ya tarar da Khimiyyah a gefen gadon ta jingina bayanta da bango murmushi yai yana karasawa ganin aikin dayai mata kullum sake samun sau'ki take saidai abu d'aya ne wato har yanzu bata magana amma idan kayi mata zata nuna alamar tasan abinda kake cewa zama yai akan kujerar dake kusa da bed yana bud'e file d'inta ya d'auko certificate d'inta na wata takarda da aka kawo masa yanzu yana bi a hankali yana duba meya kamata gaba ayi mata dan a samu ta karasa warewa kamar daga sama ko a mafarkin haka yaji saukar muryarta

Please Login or Register in order to submit comment