Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita daga part d'in Mami gabadaya gidan fal yake ya cika dam ta ko'ina da mutane manyan ba'ki masu mu'kami su hud'un duka mota daya suka shiga sakamakon Shaukiyyah da Ameer su na gida ne dukka sai aka bari a d'aura a guri d'aya idan anje na Ajeeb d'in.

Alhamdulillah Malam Habu ma yasha kwalliyar tsadaddiyar shaddarsa mai kyau sosai lokacin da suka je har an d'aura auren Aisha da Safwan sai su ake jira a d'aura na Amatun suna zuwa babu 6ata lokaci aka fara abubuwa da addu'o'i an d'aura auren Aliyu Alhassan Aliyudeen akan sadaki wanda ake neman albarkar aure uhmm Allah yayi Shaukiyyah Alhussain Aliyudeen yau buri ya cika itama an d'aura musu aure da Aliyu Alhassan Aliyudeen (Ameer) akan sadaki kai tsaya da wancan.

Bayan an kammala komai mai martaba suka gaisa da Malam Habu yayi masa godiya cikin mutuntawa sannan su Ajeeb suka shiga cikin gidansu Amatu gaisuwar iyaye kowa kallonsu yake su hud'u kaya iri d'aya biyu kama d'aya biyu ma kama d'aya 'ya'yan sarkin gari guda.

Sai bayan karfe biyar suka koma gida Asad yayi mugun gajiya ko part din Mami bai samu ya koma gurin su Aunty Fadilah ba suna parking ya wuce part d'insa bai tsaya huta ba ya shiga toilet yai wanka ya d'auro alwala domin lokaci kad'an ya rage a kira sallah saida ya shirya ya wuce masallaci da akai sallar magriba ma bai fita masallacin ba saida akai isha sannan ya koma part d'insa shifa a yau ma baici komai ba ko ruwa bai sha amma maimakon yayi kokarin cin abinci sai kawai ya zauna a parlonsa ya bud'e laptop ya fara aiki.

Jin karar doorbell yasa yad'au remote ya bud'e kofar duk zatonsa Aunty Fadilah ce amma sai yaga Ajeeb ya shigo yana kare masa kallo kafin yace.

"Asad wai kaci abincine a yau ko haka kake zaune"?.

"Mene damuwarka in naci in banci ba"?.

"Dole na damu saboda ni d'an uwanka ne kome zakai wai Asad dan jaraba baka gajiya da aiki kamar agogo"?.

Batare da Asad ya d'ago ba yace "to ko agogon ne"?.

"Oho waya sani amma da alama shi d'in ne tunda naga rashin hankalin naka yayi yawa ko agogon ma ai batir dinsa yana sanyi".

"Ajeeb fice min anan".

"Bazan fita ba kasa a fitar dani" daina aikin Asad yai ya d'ago yana kallon sa zaiyi magana wayarsa tai kara bai kulashi ya d'aga ganin kiran Mai martaba ne magana yai masa wanda kawai amsa ya bashi da cewa to sannan ya rufe laptop d'in ko inda Ajeeb yake bai kalla ba ya fice dariya Ajeeb yai yana bin bayansa yace "wato yaron nan ka gama raina ni ko? Humm zan kama kane" shidai Asad bai sake nuna dashi yake ba kawai suka wuce 6angaren mai martaba kamar yadda ya bukaci suje.

Shaukiyyah tana bedroom d'insu a zaune taci wanka tayi kyau sosai Khaldiyyah Makiyyah harda Khimiyyah suna gefenta da sauran yan Mata a dangin Sultana Shafi'ah da suka zo kallonta Khaldiyyah keyi tana daukar ta a photo cike da burgewa tace.

"Shaukiyyah na taya ki murna Allah ya sanya alkairi burinki ya cika kin auri prince Ameer nima Allah ya taimakeni ya karkato min da hankalin Annur kaina ko na daina shan wahalar soyayya".

Murmushi Shaukiyyah tai tana kallon ta tace ''karki damu Khaldiyyah kamar yau ne insha Allahu zaki auri prince Annur".

"To Allah yasa Shaukiyyah amma ni gabadaya na karaya da lamarinsa ne kullum kara nesanta kansa da soyayya yake saidai banace ba ko hakan wata manufar ce dabam amma nikam gaskiya maganar Allah ina matukar son prince Annur har cikin raina".

Sauke ajiyar zuciya Makiyyah tai tana cewa ",humm kefa Khaldiyyah kukan dad'i kike gara ke da sau'ki zaki iya tunkararsa kai tsaye batare dajin tsoro ba amma nifa wallahi Asad idan na ganshi gabana har fad'uwa yake tsabar kwarjininsa wallahi Nima shine za'bina".

Ta'be baki Khimiyyah tai tana kad'a kai domin ita kam yanzu babu komai tsakaninta da Asad sai d'aukar fansa ko sauraren maganar bata yi iya su kad'ai suke tattaunawa a junansu.

Da sallama Asad ya shiga fadar mai martaba ya tarar mai girma Alhussain yana can ga Mami sannan kuma shima gasu shida Ajeeb zama yai yana gaidasu tare da yi musu barka da dare amsawa mai martaba yai yana kallonsa kafin ya mayar da hankalin sa kan Ajeeb wanda yai shiri yana kallon Asad kamar mai tunani gyara zama Mai Martaba yayi sosai yana fuskantar Asad yace.

"Asad ka saurare ni da kyau cikin nutsuwa kaji abinda zan fad'a maka kasan cewa Allah ne keyin abu da ayi ko duk dabarar mutum bai isa yayi maka wani abu wanda Allah bai nufa ba Asad Ajeeb d'an uwanka ne uwarku d'aya sannan ubanku d'aya yaga ya isa dakai yana da iko dakai zai iya yai maka abu kansa tsaye batare daya nemi yardarka ko shawararka ba shiyasa lokaci mai d'an tsawo yazo min da wata magana yaga yarinya mai nutsuwa wacce yaga ta dace dakai zai wakilceka ya aura maka ita amma ya rokeni alfarmar kada na sanar dakai sai ranar da aka d'aura auren saboda gudun fitinarka Asad Ajeeb baiyi maka haka dan ya bata maka raiba a'a yayi haka domin samun farin ciki da walwalarka dan Allah Asad kada ka tada hankalin ka akan wannan al'amarin ka d'auka kaddara ce ka kar'bi auren nan da hannu biyu kayiwa Ajeeb godiya".

Zabura Asad yai yana cewa "Abba dawa aka d'aura aure dani fa? Haba wannan zance ne".

Da mamaki Mai Martaba yace "Asad nine zan fad'i magana kace zance ne"?.

Da sauri Asad ya d'an daidaita nutsuwarshi yana cewa "kayi hakuri abba abunne yazo min a bazata amma dai dan Allah Abba kace min da wasa kake taya Ajeeb zaiyi min aure kamar ubana"?.

Kai mae Martaba ya girgiza ''a'a Asad bada wasa bane da gaske ne dakai aka d'aura aure ba Ajeeb ba duk wani abu da kaga Ajeeb yana yi domin kane ni na amince masa domin bada ka yayi maka hakan ba saida ya nemi shawarata data d'an uwana sannan aka aura maka ita"....

Cafff mai martaba yana rufe baki Asad ya mi'ke tsaye a fusace yana kallon Ajeeb yace "dama nace maka kayi min aure ne nace maka Ina bu'katar aurene"?.

Wata uwar harara Ajeeb ya sakar masa yana cewa "dama saika bu'kata da nayi maka isa nai dakai shiyasa na nuna maka isar tawa a aikace ka gane"?.

Ajeeb na rufe baki Asad ya dam'keshi da dambe ransa a mugun 'bace idonsa ya gama rufewa har wata jijjiga da saiwa yake kamar wanda tsumunsa ya tashi mai martaba yana zaune yana kallon su ko kad'an baiyi motsi ba balle yayi magana mai girma Alhussain ke tayi da bakinsa amma ko jinsa basayi haka Asad ya shakewa Ajeeb wuya yana cewa.

"Ka bani amsar dana tambaye ka nace maka kayi min aure ne''?.

Fisgewa Ajeeb yai shima ransa a had'e sosai yana cewa "kuma dama sai kace nayi maka isa nayi shiyasa nayi maka d'in kuma babu yadda zakai dani zama da matar ya zama dol.....................

Tsalle Asad yai ya sake sha'karsa sukaci gaba da dambe wanda in kaga yadda suke kaiwa juna duka sai kayi tunanin irin ri'kakkun abokan gaban nan ne duk sun hargitsa parlon har kujeru Saida suka san ba lafiya ba table na glass kuwa sun fasa kusan uku har show glass saida suka ruguzashi ganin abun nasu yad'au zafi yasa Mai martaba cewa.

"Ku saki junanku kafin ku 6ata min rai Asad wannan abun ya isa haka sake shi kaima Ajeeb ka sake shi kun haukace ne kome tsabar rashi hankali".

Sakin Ajeeb Asad yai yana turashi baya da karfi yai yuuu zai fad'i da sauri Mai girma Alhussain ya tareshi yana cewa "subahanallahi Asad me kake haka kada ka fasa masa kai da wannan fasassun glass d'in".

Wani irin huci Asad keyi ji yake kamar ya sake fisgo Ajeeb d'in ya dokashi da qasa yabi ya take jin zuciya taxo masa har wuya yasa da qarfi ya jawo rigar Ajeeb wanda mai martaba yace.

"Asad sake shi nace".

Runtse ido Asad yai da qarfi yana sakin rigar Ajeeb d'in kafin ya juya da sauri a fice daga gurin yana shiga part d'insa a gigice ya fara tattara kayansa a take bai sake minti biyar cikin masarautar ba ya fice zuwa airport ya koma Marshall islands.

Hankalin Mami in yayi dubu ya tashi bawai fad'an da sukai bama Abinda yafi d'aga mata hankali shine jin wai duk wannan fafutukar da jajircewar da Ajeeb keyi dama saboda ya aurawa Asad yarinyar ne bayan ya riga ya fad'a masa bazaiyi aure ba sai yayi retire kai innalillahi wa Inna ilaihi raji'un kallon Mai martaba tai tana cewa.

"U're highness nifa ban gane komai ba wai dama shi Ajeeb d'in kunyi dashi ba a kansa zaiyi aure ba Asad zaiyi wa kai Ajeeb miyasa kayi masa haka bayan ya riga ya fad'a maka bazai aure yanxu ba"?.

Sauke ajiyar zuciya Ajeeb yai yana kallon Mami kafin ya zauna yana cewa "Mami nifa banyi haka dan 'bata ran Asad ko wani daga cikinku ba nayi haka ne saboda ina son ganinsa cikin farin ciki Mami dan Asad murd'add'an mutum ne bazai iya bi a huce ya tsaya ya saurareni ba amma wallahi Amatullahi yarinyar hundred% ta dace dashi ita kad'ai ce zata iya dawo dashi hanya ta sanyaya zafin zuciyarsa".

Kai Mami ta jinjina tana cewa "tabdijan To kaima Ajeeb tunda a gabanka yayi maganar cewa saiyayi retire meyasa zakai masa haka dan kawai kasa hankalin mutane ya tashi kasan fa waye Asad ko"?.

Tun kafin Ajeeb yayi magana mai Martaba yace "Kuma dan yace sai yayi retire tsabar rashin hankali dama mu irinsa ne koda ace Ajeeb baiyi masa ba ni da zanyi masa aidai ni bazai kamani da kokawa ba abinda Ajeeb yayi shine daidai Allah yayi maka albarka sannan kayi zamanka ka kwana anan bazaka fita daga part d'in nan ayau ba saboda Asad yad'au fushi da yawa idan kuka had'u akwai matsala mai girma kuma koda gobe ne karka je inda yake".

Kai Ajeeb ya d'aga "to Abba nagode da kuka fahimce ni".

Sauke ajiyar zuciya Mami tai bata sake magana ba saidai ranta fal yake da tarin tunanin yanzu da Asad ya fita a haka Ina yayi me yake yi a wanne hali yake karfa ace............. Da sauri ta d'ago tana kallon Mai Martaba da suke magana da Mai girma Alhussain tace.

"Allah ya baka nasara bari naje kar ba'ki masu kawo amarya suzo Ina nan" ta fad'a tana mi'kewa sannan ta kalli Sultana Fatima wacce itama ta mi'ke tace "yauwa Fatima muje dan Allah kinsan ga Shaukiyyah ma bamuje mun kaita part d'in Ameer ba abubuwa sunyi yawa musamman wannan matsalar data shigo ciki amma Allah ya tsayarta da sau'ki ta 6angaren Asad domin shi nafi ji babyn Mami uhm muje" fita sukai suna shiga part d'in Mami har an kawo amarya su Aunty Fadilah sun kar'beta zama Mami tai cikin zulumi kafin ta kalli futuha tana cewa.

"Asad ya shigo nan ne"?.

Kaita girgiza "a'a bai shigo ba ai kila suna can tare da ango Ajeeb"?.

"Humm wanne irin ango Ajeeb ai futuha ki bar maganar in ana sallah ba'a magana duk wannan abu da Ajeeb yakeyi da rawar jikinsa ashe basaja ce wai Asad yake nemawa auren u're highness ya sani bai fad'a min sai yanzu da zancen ya tashi bakiga yadda suka hargitsa masa parlor ba ni damuwa ta a yanxu inda Asad d'in yake nasan ba lallai yana nan ba banaji a jikina yana cikin masarautar nan".

Zaro mata Aunty Fadilah tai tana kallon Mami da mamaki tace "da Asad aka d'aura auren kuma garin yaya haka ta faru shi da yace sai yayi retire miyasa Ajeeb zaiyi masa haka"?.

"Garin tsautsayi da karambanin Ajeeb wallahi Kinga ya jawo mana tashin hankali ana cikin nishad'i duk murna ta koma ciki".

Kai Aunty Fadilah ta d'aga "ok bari naje part d'in Asad d'in mu gani ko yana nan"?.

"A'a Fadilah karki tunkari Asad yanxu ba lallai ya gane kiba kada yayi miki kallon Ajeeb kina shiga ya sha'ke ki mu shiga uku ana kukan targad'e karaya ta samu"?.

Dariya Aunty Fadilah tai tana cewa "ayya kada ki damu bari na gano" ta karasa maganar tana fita nannauyan numfashi Mami ta fitar tana mi'kewa tace.

"Fatima muje muji da Shaukiyyah tukuna daga baya naji da wannan zafin dana dauka cakwakiya tayi min yawa dole saina bu'kaci ganin likita bayan biki".

'Yar dariya Sultana Fatima tana cewa "uhm Allah ya rufa asiri dai nikam saidai ki d'auki Futuha ko Aleemah kuje kin manta"?.

Dafe kai Mami tai "oh ha'kuri sha'afa nayi gabadaya a gigice nake ok bari muje" ta fad'a tana shiga bedroom d'inta Sultana Fatima kuma ta fita.

Aunty Fadilah kam bata samu kowa a part d'in Asad ba har Amjadd ta tambaya ko Asad yana ina ya fad'a mata ya ganshi goye da jaka ya fice ko tsayawa ya bar masa sa'kon stockyard d'insa bai samu dama ba saboda fushin daya d'auka.

Jin haka yasa Aunty Fadilah juyawa a hanya ta had'u da Mami tare da Aunty Futuha da Aunty Aleemah suka sake juyawa zuwa 6angaren mighty Alhussain tana fad'a mata abinda Amjadd yace mata itakam Mami bata iya cewa komai ba dan tasan gurin aikinsa ya koma amma hakan ma ta godewa Allah tanan hankalinta taji ya d'an kwanta sakamakon ba Asad d'in za'a fi jin sau'ki kowa zai zauna lafiya.

Sun shiga part tun daga nesa suke jiwo kuka da ihu a part d'in Sultana Shafi'ah mahaifiyar amarya Shaukiyyah da Makiyyah da sauri suka karasa shiga uhmm Makiyyah ce sai kururuwa da fisge-fisge take tana cewa.

"Wallahi bazan yarda ba saina aureshi ni Asad nake so taya za'a ce yayi aure bayan zaman jiransa nake zuciyata zata fashe wayyo Allah nashiga uku ku taimake ku ce min da wasane ko mafarki ba'a gaske bane Asad yai aure innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" ta karasa maganar tana gwara kanta a bango duk ta hargitsa jikinta ta dame kwalliyar fuskarta harda yankan wu'ka a hannunta inda ta she'ka aguje ta d'auko zata da'bawa cikinta aka kar'be garin kwatar wu'kar taji ciwo.

Gurum Mami tai tana kallon ta ta kasa koda motsin kirki jin abinda Makiyyan ce cewa tabd'i subahanallahi ana wata ga wata Makiyyah ma son Asad take wai amma fa akwai gagarumar matsala a gaba Asad Asad fa? Gaskiya ta d'auki abinda bazai kaita ba Asad mijin mace hud'u ne amma d'aya ma yana rabawa biyu zaiyi ko bazai yiba ga wacce Ajeeb ya za'ba masa sannan ita Makiyyah da take 'yar gida ya za'ai kena..................................

Tunanin Mami ya katse sakamakon zuwa da Makiyyah tai ta dur'kusa a gabanta tana ri'ke kafafunta da tsananin kuka sosai tace.

"Dan Allah mami ki taimaka min kar na mutu zuciyata a yanzu haka ci take da wuta ambaliyan jini take damuwa zata kasheni bazan iya cigaba da rayuwa a masarautar nan ba ina kallon matar Asad tana zarya wallahi zuciyata bugawa zatai please Mami ki tausaya min rayuwata tana cikin garari na fad'a shafin jarabtar soyayya ha'kuri na ya gama karewa dole na fito na bayyana kowa ya sani idan na mutu son Asad ne ya kashe ni ba komai ba".

Zaro ido Mami tai jin zata d'ora mata masifa idan ta fad'a a daidai ta mutun basai a camfa ri'ka cewa son Asad d'in bane bataji dad'in maganar Makiyyan ba amma ganin bata cikin hayyacinta yasa tacewa Sultana Shafi'ah ayi mata addu'a amma ko rufe baki Mami batai ba Sultana Hadizah tace.

"Humm yo wacce addu'a ba abinda take bukata daya wuce ku aura mata Asad d'in amma saiku tanadin kayan kar'bar gaisuwa ko tunda naga ta matsu taje ma'kabarta ki rasa wanda kike so sai azzalumi gaki nan gashi ai saiki aureshi tunda mutuwa kike sha'awa kina kallo yadda ya mayar da Khimiyyah zararriya kodan ba dama ka fad'a sai aga zafinka bayan an gama cutar ka".

Had'e rai Mami tayi dan dama tasan Sultana Hadizah saita magantu amma ko kallon inda take batai ba kawai abinda ya kawota part d'in tayi ta share Makiyyan ma take ta burgima a qasan carpet tana Kiran an ceceta Asad take so saboda takaicin maganar da Sultana Hadizah take fad'a kawai ta amso Shaukiyyah ta fito daga nan aka d'auketa a mota zuwa bangaren Sultana Fatima idan sun gama abinda xa'ai zuwa Nan da sha biyun dare sai tazo ta kaita part d'in mijinta Ameer sannan ta koma part d'inta bata ko zauna ba ta zarce yankin inda tasa akai Amatu ta sameta ita kad'ai duk 'yan rakiyarta sun tafi sai 'ya'yan Aunty Futuha da kuma su Hajir da Muyassara suna zaune suna hira iya su Amma banda ita tunani tayi kada daga zuwan yarinya ta sanyata a damuwa sai kawai ta cewa su Hajir d'in su tsaya anan su kwana tare da ita ba yau za'a kaita part d'in mijinta ba sai an gama biki duka tana fad'in haka ta juya ta fita ta barsu suna cigab da hirarsu.

Washe gari su Aunty Fadilah duka suka tafi gida har airport Mami tayi musu rakiya suka sake bankwana tana bada sa'kon gaisuwarta zuwa gurin sauran 'yan uwa sannan ta dawo gida tana shigowa falonta taga AJEEB zaune shi kad'ai yana breakfast kai ta jinjina tana murmushi batace komai ba ta karaso tana zama d'agowa yai yana kallonta ganin murmushi a fuskarta yace.

"Mami barka da safiya kin tashi lafiya"?.

"Lapia kalau Ajeeb ya jikin naka"?.

Da d'an mamaki Ajeeb yace "jikin me kuma Mami"?.

"Oh harka manta kenan ai Asad baya masarautar nan a jiya ya koma domin Amjadd ya fad'a"?.

Dariya Ajeeb yai yana cewa "humm Mami ki bar batun Asad d'in nan na rantse miki da Allah ko? wuya ya huce ya dawo zakiga yadda za'ai dashi akan yarinyar duk qarya ce da yake cewa sai yayi retire zaiyi aure yawan cika min bakin dai yake da nuna ban isa nayi wani abu a kansa ba yasa ni kuma nasa kansa yad'au caji na hukunta shi ta nan gaba ko ance yai min bazai ba".

Kai Mami ta girgiza tana cewa "kamar dai ka manta waye Asad kake cewa haka shine zai huce akan lokaci hum kawai kadai ka kyale bari nazo" mi'kewa tai tana shiga part d'in da tasa aka kai Amatu zuwa wani lokaci ta fito Amatun na biye da ita a baya tazo ta zauna a qasan carpet domin itakam batasan komai ba duk abinda akeyi batasan ma Ajeeb su 'yan biyu bane kuma kamarsu d'aya.

Kallonta Ajeeb yai yana cewa "Amatullahi dan Allah kafin nace miki komai zan fara da neman yafiyar ki akan abinda na aikata miki nasan ban kyauta ba banyi daidai ba amma ba nayi haka dan na cutar dake bane dan Allah ki fahimce ni zan fad'a miki komai yadda zaki gane ki yarda dani".

Cike da mamaki Amatu ta d'ago tana kallon sa me yake nufi kamar ya yafiyar ta tame yake nema Kuma.............................

Ji tayi Mami tace "a'a Ajeeb kayi shiru zanyi magana da ita"?.

"Ok Mami" Ajeeb ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya cikin tausayawa Amatu da rashin jin dad'in abinda yayi mata batare data sani ba yanzu baisan wanne irin kallo zatai masa ba?.

Dukka hankalinta Mami ta mayar kan Amatu tana cewa" Hauwa'u Amatullahi sunanki ko takwara tace ke lallai kam Asad bai sani ba¿ Sake qare mata kallo Mami tai gaskiya ta Ajeeb d'in fa yarinyar akwai nutsuwa da gani babu tambaya ko ba'a fad'a ba.

"Amatullahi ki saurare ni dakyau ki fahimci abinda dazan fad'a miki Ajeeb tunda yake zuwa gurin ki ya ta'ba fad'a miki shi d'an biyu ne kuma kamarsu d'aya ba'a bambance su''?.

Kai Amatu ta girgiza jiki a sanyaye tace "a'a bai fad'a min ba".

Cigaba Mami tai "ok yayi miki laifi sosai gaskiya Ajeeb su 'yan biyune akwai d'an uwansa sunan Asad dashi aka d'aura miki aure bada Ajeeb ba duk zuwa gurin ki da Ajeeb yake yi domin d'an uwansa yake badan kansa ba kuma baiyi haka dan ya 'bata miki raiba a'a yayi haka ne abisa kyakkyawar zuciya da kyakkyawar niyya da kuma kyakkyawar manufa fatan zaki fahimce shi sannan jin ba dashi akai auren ba kada ki tada hankalin ki wannan ba komai bane ki qaddara dama can ba Ajeeb d'in ne mijinki ba Asad ne kuma kada kiyi ba'kin ciki insha Allahu kinyi dace Asad na qwarai ne Ina fad'a miki haka a matsayina na uwa gareki bawai matsayin mahaifiyar Asad ba Amatullahi nice na haifi Asad na raineshi har ya girma dan haka nafi kowa sanin dukkan halayyarsa yana da zafi da saurin fusata sannan shi murd'add'an mutum ne wanda ba'a gane masa amma fa a cikin hakan idan kika bi wasu matakai ina tabbatar miki da Asad zai dube ki na farko ko maye zai faru kada ki kuskura a gabansa ki nuna raki kada ki nuna gajiyawa da karaya ko sarewa karki nuna kina jin tsoron magauci karki nuna masa bakida zafi karki nuna ke raguwa ce ki ri'ka nuna jarumtarki a fili koda a gabansa kada idan yayi magana ki razana ko ki firgita ki tsaya tsam ki saurareshi kuma ki fuskanceshi ki nuna masa cewa zaki iya ji da komai Amatullahi indai kika bi wadannan hanyoyi iya wannan kad'an d'in dana fad'a miki kina zaune Asad zai nemeki da kansa a lokacin da baki ta'ba tsammani ba abu na qarshe shine zanci gaba da 6oyeki anan bazan ta'ba nunawa Asad kina cikin masarautar nan ba koda ya dawo zanga zai nemeki ko zanyi min magana a kanki ki kwantar da hankalin ki kisa tunaninki guri d'aya kiyi rayuwa cikin farin ciki ina tare dake fatan kin fahimci duk wani abu dana fad'a miki"?.

Kai Amatu ta d'aga tana sau'ke numfashi a hankali tace "eh Mami na fahimta sosai kuma nagode Allah ya saka da alkhairi sannan Ajeeb yabar neman yafiyata babu abinda yai min na fahimce shi insha Allahu Mami zaki sameni mai ladabi da biyayya zanyi dukkan abinda kika umarce ni fatana Allah ya dafa min".

Cikin jin dad'i Mami tace "Amin takwara ta Allah ya miki albarka Allah ya baki nasara Allah yasa kece silar canzawar Asad".

Tun Amatu batai magana ba Ajeeb yace "Amin Mami saidai wani hanzari ba gudu ba Amatu na manta ban fad'a miki abu guda ba shi Asad ba doctor bane irina sannan baya d'aukar wargi abu 'kalilan zakiyi yanzun nan ki fusata shi soja ne shi" ya karasa maganar yana mata alamar harbi da bindiga.

Kallon Ajeeb Amatu tayi lokaci guda taji wata muguwar fad'uwar gaba ta sameta har tana d'an dafe 'kirji tare da cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un".

Dariya Ajeeb yai wanda Mami ta harareshi tana cewa "ya haka Ajeeb meye na tsorata ta dan soja ne sai akai ya? Kinga Amatu share shi kinji babu wani abu Asad yana da sau'ki sosai idan ka tsaya ka fahimce shi Ajeeb ya fad'i haka ne da wasa kada ma ki dama tunaninki a kansa kinji".

Kai Amatu ta d'aga "to Mami na gode".

"Ok takwara ta wanne sunan zan ri'ka kiranshi dashi ne domin gaskiya kin d'auko babban suna"? Mami ta tambaya tana kallon ta da murmushi.

"Ai kawai Mami ki ri'ka ce mata takwarar ma yayi idan Asad ya dawo yaji haka sunanki ne da ita maybe ya sau'ko da wuri".

"A'a Ajeeb ba takwara zance mata ba ni jewel✨ zance ai yayi"?.

"Wow jewel? Tab lallai kice ke Amatu kinzo a sa'a kiji sunan da Mami zata ri'ka kiranki dashi uhm mu kuwa daga Ajeeb sai Asad babu wanda ta saurayawa suna".

Murmushi Mami tai tana cewa "ai kuma ba sunan ku Ajeeb da Asad ba ko"?.

"Eh Mami sunan mu Aliyu, to amma ai itama sunanta Hauwa'u ake ce mata Amatullahi Kinga an raba ba wata jewel da zakice mata gaskiya idan ba haka ba nima saidai ki dawo ce min diamond😀"?.

Dariya Mami tai tana cewa "waye zan cewa diamond tab amma dai bakai ba saidai ka bari idan kayi aure kaima taka matar sai nace mata diamond tunda naga kishi kake da Asad ko"?.

''A'a niba kishi nake dashi ba Mami".

"To me kake inba kishin ba"?.

"Tsokana nake".

"Uhm ai a irin wannan tsokanar taka kake tsokano Asad d'in kazo kuyi tayiwa mutane hauka a gida kamar qananun yara Allah ya shirye ku dai".

"Amin Mami bari naje ina so Annur zai rakani wani wuri kar lokaci ya 'kure" ya karasa maganar yana mi'kewa tsaye.

"Ok sai kun dawo".

Fita yai yabar Mami da Amatu suna zaune su kad'ai

Please Login or Register in order to submit comment