Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace.

"Doctor ina son zamuyi wata magana ta sirri dakai batare daka sanar da wadanda suka kawo niba dan Allah ya zama sirri tsananin mu har abada kayi min wannan alkawarin🤲"?.

A zabure cike da tsananin mamaki doctorn ya d'ago yana kallon ta kafin ya bud'e baki yace "yaushe kika fara magana ko yanzu"?.

Kaita d'aga "eh doctor yanzu ne na fara duk da na dad'e da farfad'owa kuma na dad'e da sanin inda kaina yake hankali na ya komo jikina duk abinda ka nuna min zan fad'a maka meneshi dama dan 'yan uwana suna gurin ne shiyasa na'ki kulaka duk abinda kake tambaya tak sakamakon bana so susan cewa na dawo cikin hankalin nawa sosai zanyi amfani da wannan damar nayi wasu abubuwa amma saida taimakon ka please doctor"?.

Kai ya d'aga mata yana cewa "ok Ina jinki me zakice wanne abu zakiyi"?.

Huci Khimiyyan ta fitar tana jin ina ma ace yanzu tana gida dama ace an sallamesu sun koma masarauta hummmm 'kwafa tai tana kallon doctor tace "d'aukar fansa😠😳".

Cikin rashin fahimta doctor yace "ban gane d'aukar fansa ba me kike nufi"?.

Rufe idonta daya fara kad'awa tai tana cewa "Ina nufin zan d'auki fansa ne akan wanda yai min haka amma saida taimakon ka".

Gyara zama doctor yai cikin mamaki yace "oh wai dama mutum ne ya miki haka subahanallahi wanne irin jarumi ne kuwa tabd'ijan wallahi Khimiyyah all my thoughts ko daga irin benin na mai tsawo kika fad'o lokacin dana fara yi miki aiki haka nayi tunani"?.

Kai Khimiyyah ta girgiza "no mutum ne shiyasa nima nake so nayi amfani da wannan damar na rama abinda yayi min ta hanya mafi sau'ki doctor abinda zance maka shine zaka fad'a ma wadanda suka kawo ni"?.

Kai doctor ya d'aga yana cewa "ok ina jinki fad'i duk yadda kike so ace musu nikuma I will try to do my best na ganin na fad'a musu komai har su yarda da abinda na fad'a".

Murmushi Khimiyyah tai tana jinjina kai tace "doctor so nake ka fad'a musu cewa na samu lafiya na warware na dawo daidai amma game da wankin 'kwa'kwalwa da akai min dole wata rana ciwon zai d'an ri'ka tashi ana yimin uziri wasu lokatan bana cikin hankalina nake yin wasu abubuwan kuma koda a furuci ne shin doctor zakai min wannan taimakon"?.

Kaiya d'aga mata yana gyara zama yace "ok babu damu I'll but dole saidai na soke wannan papern na yau ayi wata ta qarya domin wannan result d'in ya nuna kin samu cikekkiyar lafiya ta haqiqa babu sauran matsala kinga idan aka basu ba damar dazan fad'a musu abinda kike so ayi miki kuma sa'a kikai naje reception nemansu naga basa nan maybe sun d'an fita da yanzu na basu takardan".

Zaro ido Khimiyyah tai tana sau'ke ajiyar zuciya tace "gara da basa nan doctor alhamdulillah na gode sosai da wannan taimako".

Mi'kewa doctor yai yana cewa "ok no vex🌹 karki damu ai dama muna irin haka a patient's😷 d'in mu bari naje office saina sake takardan" yana fadin haka ya bud'e kofa ya fita wani irin murmushi Khimiyyah ta saki tana jinjina kai tare da haskota sanda ta koma gida za'ai bele'u dan saita hana kowa zaman lafiya idan zata d'au fansarta komawa tai kwanta kawai tana tunano lokacin da Asad yake tumurmusarta da dukkan qarfin sa🤪😂 mtswww taja tana gyara kwanciyar ta kafin doctor ya dawo ta sake fad'a masa wani abu guda data manta bata fad'a masa ba.

🏕️'KAUYE 🏕️
Ilyah na zaune a kofar gidansa wani yaronsa daga cikin yaransa dake masa aikin bin kasuwanni da kayayyaki yana zaune a gefensa da kud'i Mai mugun yawa yana 'kirgawa dami dami Hassan da Hussaini suka fito ganin yasa suka tsaya Hassan ya kalleshi yana cewa.

"Wai baba Ina maganar mu ta kwana ne yarinyar nanfa ta dawo tayi kyau ta zama 'yar birni kaje kada wani yamin shigar sauri wallahi da saidai garin nan ya kama da wuta dan sai anyi mummunan ya'ki akan Amatu zan iya kashe mutum gara makaji ka sani".

Kallon sa Ilyah yai cike da fargaba kamar baisan akan me yake maganar ba cikin basarwa yace "batun mu name akan me kake magana yaushe zaku koma neman kud'in ku kafin ku dawo zansa a Gina muku manyan gidaje wanda babu irinsu a 'kauyen kuma ku auri duk yarinyar da kuke so?.

Ta'be baki Hassan yai shima jin yadda Ilyan ya kamo wani shafin da ba zancen suke ba yace "batun aurena da Amatu nake maka maganaa akai ba gini ba in a ruwana da gida idan zan gina bana bukatar taimakon ka koda bulo daya ne zanyi da kaina nidai damuwata kaje mun ro'kon arziki sonake a had'a bikinmu dana wannan shegiyar 'yar taka Nafisa idan kuma ba haka ba wallahi saidai itama a fasa natan sai lokacin daka amince da namu idan ka'ki zamu Bari sai saurayin nata yazo mu tumurmusa shi agabanka muyi masa tsinannan duka mu faffasa masa glass d'in motarsa sai naga ta tsiya haba idan banda gidadanci anace maka ga gabas kana ga yamma ana ga ruwa kana ga wuta kodan bari na sake maimaita maka watakila kud'i ya fara susutar maka da 'kwa'kwalwa cewa nai magana nake maka akan Amatu yar gidan kawu Habubakar gashi ta dawo so nake na aureta mubar nan garin nan ya isheni kandin kifi zanyi daga ruwa na koma mai Ina aurenta zaka nemi ni ka rasa nayi can zanje na bud'e sabuwar harka da sabuwar duniya yanzu Ina tunanin ka fahimta tunda nayi maka magana da yaren da zaka gane"?.

Takaici ne da ba'kin ciki suka rufe Ilyah yana kallon Hassan zaiyi magana Hussaini yace "yauwa Hassan fad'a masa dai baba Nima dai ta Hassan d'infa Ina maganar auren mu akan Aisha ta kwana domin gaskiya na matsu nayi aure kuma dai rana d'aya zamu bar nan kawai yanzu ka tashi muje tunda ga kud'i nan a gabanka kamar yayi kawai ka mike muje tare guri kawu Habubakar yanzu ayi neman auren nan a gabanmu tunda kawu Habun babanmu ne ba surukin muba".

Mugun had'e rai Ilyah yayi yana kallon su cikin 'bacin rai yace "wallahi babu inda zanje nemawa kowanne shege a cikin ku aure tunda baku da hankali baku mayar dani komai ba ai na dauka zaku iyayin auren batare da neman shawara taba sai kuje kuyi naga da yadda zakuyi d'in shashashun banza mahaukatan wofi wannan ba'kin cikin da kuke sani saikun gani kuma a 'kwaryarku".

Kallon juna sukai suna ta'be baki jin abinda yace kafin Hassan ya jinjina kai yana cewa "Aiko wallahi baba tunda kace haka zakaga yadda akai tijara mun shiga birni mun waye ba wani so'ko'kon dazai fad'a mana wayewa a garin nan banda matata Amatu Dan haka ko alkali sai munje ya d'aura mana aure dasu kuma zaka gani Hussaini zo mu tafi dan idan naci gaba da tsaiwa anan yadda baba yake karanta min wannan gidadancin zan iya wanka masa mari😲😳 mu tafi kawai na daina ganinsa kafin na fusata".

Dariya Hussaini yai ganin yadda Ilyah ya zaro ido sai kawai ya du'ka yana d'aukar d'aurin kud'i guda daya a jikin 'kyaro yace "wannan zaikai dubu hamsin Dan haka mun d'auki kud'in zance nida Hassan yau kaine zaka biya mana kud'in hirar da zamuyo" yana fad'in haka suka wuce muryar illyah na rawa kamar zai fashe da kuka yace.

"Hussaini ka dawo min da kud'in nan Kona tsine maka"?.

Waigowa Hussaini yai yana cewa "tsine min d'in mana idan ka tsine min nabi duniya wayai asara bayan kai ka rasa" yana kaiwa nan ya juya da sauri yaci gaba da tafiya dan Hassan tuni har yayi masa nisa bai tsaya sauraron maganar ilyan ba.

GIDAN BALARABE
Asabe dai fatan ta baici ba yadda take so bai samu ba da fari boka yace mata aiki zaici harta kwantar da hankalinta akan wannan batun ta manta ma da wani ilu sai gashi kwatsam rana tsaka taga su Inna sun sauka a gidanta da asubar fari😂 da Dan d'aurin kayansu kamar yadda suka zo a lokacin Indo tashin hankali ne 'karara ya bayyana a fuskar asabe wanda batasan sanda tad'au tabarya ta bisu da ita ba tana surutai a layi tayiwa su Innah korar kare fata-fata ta'ki kar'bar ro'kon arzikin Iluh kuwa daya fita tantiranci suka had'a baki shida Bahijjah ya rakasu gidan Markah yace Asabe ce tarosu wai ta kar'bi ro'kon arziki domin tana jin kunyar Bahijjah 'yarta ce ta fari Markah kuwa tayi kiran Mairo suka kar'bi komai tare Asabe batasan komai ba sai kusan kwanan ashirin da biyar a jita-jita taji wai-wai ana tayata murna a anguwa wai ashe auren Bahijjah zatai zata bata Iluh d'an garuwa jin abinda aka cewa yasa a hargitse tayi gidan Markah kamar zata tashi sama taje tana kwala mata kira tun daga layi harta shiga gidan ta ri'ka Danna mata zagi da masifa iri iri akan me zatai Mata haka dama tace ta kar'bi kayan wadancan tsinanun mutanen Markah kuwa ta nuna Mata ai itace ta turosu nan din dan Bahijjan ma haka tace ita da Iluh Asabe tayi kuka tayi ba'kin ciki da kiran ta shiga uku ta lalace Markah tace Mata kawai tayi ha'kuri tunda har anyi haka ta dangana ta ha'kura karta hana auren ba'a san me yake 'boye ba jinya kam Asabe tasha kamar bazata kai labari ba kuma dole ta warke saidai fa damuwa ta dama Mata 'kwa'kwalwa ga kuma hawan jini da ciwon zuciya rai da rai tana tare da magani a kusa da ita😣😞.

Allah sarki Malam Habu masu kar'bar kaya sunzo babu komai a gurin sa haka dole yasa hannu a takarda akan cewa gonarsa 'yar guda d'ayar da yake nomawa yanzu babu ta zama tasu yayi juyayi yayi bakin ciki ya kara dole ya dangana ya ha'kura yasan Allah ne ke bada komai kuma shizai bashi wata.

Hassan da Hussaini suna zaune a irin dabar samarin gari hangowa Ilyah sukai yana ta sauri yayi layin wajen gidan malam Habu yana tafe kamar zai kifa hada ido sukai da sauri suma suka mi'ke suna bin bayansa da gudu ba zato yaga sun sha gabansa cikin haki Hassan yace.

"Baba Ina zakaje haka kake sauri kamar zaka tashi sama"?.

A fusace ilyah yace "ban sani ba bani hanya".

Gira Hussaini ya d'age yana cewa gidan kawu Habubakar zakaje ko wato har wani ba'kin tsinannan munafikin yaje ya fad'a maka munyo masa cefane da kayan abinci a kasuwa ko shine kai kuma ka d'ebo qafa saboda baka juri zuga ba kayo gidansa da ba'kin ido so'ko so'ko🙊 ka taho gurin sa kazo ka tada masa hankali ko? to wallahi baza kaje ka tada masa hankali ba dan nasan akam wannan kayan abincin ne saboda bamu saya mun kai maka ba kana ubanmu mun kaiwa surikin mu shine zakaje ka tada qayar baya haka ne"?.

Cikin takaici Ilyah yace "inji ubanka nace maka haka Ina ruwana da wani shege abinci da kuka kai masa shine mitsiyaci mayunwaci😣 amma bani ba shine fa'kiri talakan talakawa shi yake bu'katar abinci bani ba".

Kai Hassan ya jinjina yana "To indai kasan ba abinda zai kaika ba kenan ka koma gida yanzu".

Muryar Ilyah da fushi da yadda suke bashi umarni a fusace yace "Bazan koma ba dan uwarka ka komar dani idan ka isa yau sainaga wanda ya tsayawa Habubakar a garin nan" ya fad'a yana shirin wucewa had'a ido sukai suna jinjina kai tare da tareshi suna d'aukarsa sukai hanyar gida dashi yana wutsul wutsul basu damu da yadda mutane suke kallonsu ba haka suka wuce dashi ana binsu da kallo ana gulma saida suka kaishi har kofar d'akinsa sannan suka direshi suna huci shima yana yi.

Ganin Ilyah d'auke a hannunsu sun shigo gida yasa daga manyan har 'ya'yan kowa ya fito jin Bara'atu tana salati sun d'auka ba lafiya ba.

Cikin alamun tambaya Maimuna tace innalillahi meya sameshi haka Hassan ko fad'uwa yayi a waje naganku kun rirri'koshi daga Ina dama baida lafiya ne"?.

Kad'a kai Hassan yai yana cewa "kalau umma Maimuh d'auko shi mukai a hanyar gidan kawun mu Habubakar wai saiyaje ya gargad'e shi akan dan muna son 'ya'yansa".

Jin haka yasa maimuna taja bakinta tai shiru ko tari bata 'kara ba duk da tana mamakin meyasa Ilyan baya so su Hassan su auri 'ya'yan 'kanin nasa kodan ya furta cewa talaka ne fa'kiri......

Kai Bara'atu ta jinjina cike da takaicin halayensu tace "anya ku mutane ne Hassan Hussaini Ina gargad'inku fa ubanku shine abun wulakancin ku kubi duniya a hankali".

Kau dakai Hassan yai yana cewa "wallahi umma nikam yanzu na fara tara tsinken tsikarar duniyar ma🙊 kinga ko taya zan bita a hankali gara na bita da gudu zamufi daidaitawa da kowanne so'ko'ko😳" A'A AN SHIGA 'DAKA JAMA'A ILYAH FA YA HAIFO RUWAN DUHUWAR KANSA😭.

Wani irin Sar'kekken numfashi wanda ya kusa tafiya da bugun zuciyarta Bara'atu ta sauke tana kallon su kamar ta d'ora hannu aka ta fasa ihun damuwa ko zasu fahimci halin da take ciki zatai magana Hussaini yace.

"Ai Hassan 'kyale ta na rasa wacce irin 'kwa'kwalwa gareta data kasa fahimtar inda muka dosa amma zamu ganar dasu dan wallahi ko hannu bamu saba a fara tara tsinken tsikarar duniyar ba saima nan gaba sannan munyi aure suna kallo zamu shiga duniyar nishad'i kuma mu d'ebi nishad'i yadda ya kamata a gabansu da 'ya'yan kawu Habubakar babu ruwanmu da mutum yana gurin saidai ya rufe idonsa ko yai bunga🤥 wannan matsalar sace muje kawai Hassan sharesu" ficewa sukai a gidan suka bar Bara'atu a tsaye ta qame guri daya kamar sanda ta rasa meyake damun wadannan yaran ace sam bakinsu bai mutuwa idan ka fad'a musu cuta sai sun fad'a maka mutuwa haka Ilyah ya shiga d'aki yanata share hawayen ba'kin ciki shima.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE😘.

Yusrah Musa Abubakar YUSEEN AL-AMEEN🏖️.

Much appreciated masoya💕tnks for ur supports💃 Allah ya barmu tare amin.

Nagode a bisa nuna kulawa da qaunarku ga littafin nan da kuma lambar yabo da kuka bashi Allah ya saka da alkhairi 🙏🤝.

YÚSRÃH MÛSÃ ABUBAKAR💋
[email protected]

TYPING 📲 wed Aug28/24 YUSRAH MUSA ABUBAKAR🤝.

💦🤟ME KAMAR SÄRKÌ💦🤟

________________________________
________________________________
________________________________
___________________
💫 ANNUR WRITER'S ASSOCIATION💫
Home of hospitality and harmony 🤙gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya🙅 ÀÑÑÙRÌ haske le'ka gidan kowa koda ma'kiya na kallon ka ramin kura sai'ya'yan ta.

FATIMA SHAMSUDDEEN
RAMLAT IBRAHEEM
RU'KAYYAH KABEER.
👇Wannan 📝page d'in naku ne duka mallakin ku 'ya'yana🍎 na kaina kuna farin cikin Yusrah ababen son Najaat muradin Zarah d'an Adam🤟.

59~AL-MU'IDU
The Reinstater Who Brings Back All
60~AL-MUHYI
The Giver of life.

29~Allahumma salli wa sallim wa barki ala sayyidina muhammadin 'Kuraishiyul Hashimiyyi.

🌄PRETENDING---NIGHT-MARE🌄
Episode 59&60
👑🌹PALACE🌹👑
Kamar yadda doctor yaiwa Khimiyyah alkawari haka ya samu su Mami da sabuwar takardan qarya yayi musu bayanin qarya yadda Khimiyyan ta buqata sannan yace daga haka babu wata mufita babu wani magani dazai sake tasiri a jikinta saidai suyi ha'kuri idan ciwon ya tashi sudai babu yadda suka iya bayan ya gama musu bayani suka masa godiya kwana uku a tsakani suma suka diro Nigeria wanda tun washe garin da suka dawo Mai martaba ya tattara familyn guri daya domin a warware matsalar dake tsakanin Khimiyyah da Asad babu yadda mai girma Alhussain baiyi akan abar maganar Mai martaba ya tsaya tsam yace a'a sai anyi cikin Khimiyyah ya kad'a ya d'uri ruwa rasa inda zatasa kanta tayi dan tasan komadai yayane itace mara gaskiya dan haka qarfi da yaji a gurin ta ri'ka sambatu kamar zararriya dan ace ciwon ya motsa duk kokarin da akai ganin cewa ya lafa tayi magana 'ki tayi dole sai ha'kura akai kwana uku tsakani Asad ya samu Mai martaba akan yana son komawa Marshalls islands Mai martaba bai barshi ya tafi ba ya sake dakatar dashi akan lamarin sa da Khimiyyan amma haka ta sake susucewar qarya tun daga part Sultana Hadizah take fisge fisge kamar mahaukaciya sai ri'keta su Shaukiyyah keyi Amma har wani fisgewa da zabura take a ranta kuwa dariya take qyalqyalawa ganin ta mayar dasu mahaukata ranar ma abun bai samu ba dan haka Mai martaba yacewa Asad d'in kawai ya shirya yai komawarsa tunda dama already yasan komai kafin nan saida ya zaunar da Asad tun ranar daya dawo yayi masa tambaya d'aya bayan d'aya a nutse Asad ya fad'a masa duk abinda ya shiga tsakaninsa da Khimiyyah amma bai nunawa kowa komai ba yafi so ayi ga Khimiyyah ga Asad hakan zaifi.

Asad yana kwance cikin barci yayi wani irin mafarki Mai bada mamaki gashi tare da mace wai yana nuna Mata so zalla babu algus tab a firgice ya farka yana tashi zaune ya dafe kai da hannu biyu tare da furta innalillahi wa Inna ilaihi raji'un wacece ita kuma wannan budurwar meya zata zo min cikin mafarki na miye had'ina da ita..........

Shiru yae sakamakon muryar mace dayaji ance "Aliyu Asad karka tsaya tunanin wace ita domin ka manta ta tsawon lokaci abun da yafi sau'ki gareka ka mayar da hankalin ka kan aikin ka shi yafi cancanta ko kana son saninta"?.

Cike da mamaki ya soma kalle kallen ta inda zaiga Mai maganar amma babu kowa babu alamar komai tsaki yaja mai qarfi a ransa yana tunanin meye damuwarsa da zaice saiya Santa me zatai masa me zata bashi shifa mace bata gabansa🤨 aikinsa ya sani bazai ta'ba yarda ya 'bata jarumtarsa da 'kuruciyarsa da kuma zuciyarsa akan wata soyayya ba ko Clarah ma da take damunsa yana d'aga mata qafa ne dan ra'ayi amma itama shirmenta take baiga ta yadda ta isa ya aureta ba balle wata yarinya danya ganta a mafarkinsa babu dalilin dazaisa ya zauna yana 'bata lokacinsa a kanta koda wasa ta sake kokarin zuwa masa cikin barci saiya kasheta🙊 koma wacece ita.

Komawa ya sake kwanciya batare daya sake bi takan wancan sokon mafarkin dayai ba ko minti sha biyar baiyi ba ya sake komawa barci sakamakon jiya kwana yai yana aiki komawa barcin nasa shi keda wuya ya ganshi a wani guri wanda ya kasance kamar dai daji ne kuma guri karkara ne yana tsaye baiga komai ba baiga kowa ba wani haske ya hango ya taho gurin sa hasken har kashe masa ido yake kamar yanayin hasken rana saida yazo gaf dashi sai yaga ya zama mutum kawai mace ta bayyana a gabansa da murmushi a fuskarta tace.

"Kaine Aliyu Asad ko d'a a gurin mai martaba Alhassan Aliyuideen kuma kaine kake neman wacece wacce ta gano wannan 'kungiyar da take da had'ari sannan take hallaka mutane 'kungiyar matsafa ce masu aiki da jini da kuma ba'kin sihiri Mai tasiri ga jiki Asad nice wannan budurwar da kake son ganowa kake son sani nice nasan asirin wannan 'kungiyar kana son saninta kaima kana son cika burinka na zama Bgs zaka zama Asad insha Allahu a wata rana a hankali zakasan komai saidai zan fad'a maka wani abu ka daina wahalar da kanka da yawa a kansu wajen ganin saika gano location d'insu hakan Mai wuya ne bazasu Bari ka gane ba domin a cikin wani irin ba'kin had'ararran daji Mai duhu abin tsoro suke wannan kungiyar ta kunshi mutane masu dubun yawa sannan dajin da suke ciki ba daji ne wanda kai tsaye za'a iya shiga ko a ganshi a fili ba dajine na sihiri iya sune suka San inda yake su kad'ai ne suke da ikon shiga cikinsa domin ba'a sararin kasa yake ba sun 6oyeshi ta yadda babu wanda zai ganosa har abada indai bada taimakonsu ba amma kalli nan".

Ta karasa maganar tana nuna masa wani guri da yatsarta kallon gurin yai a mamakin sa wani katon abu ya gani kamar zaikai girman kumbu🛸 kuma rataye yake shiba a sama ba kuma yabar qasa yana jujjuyawa ga wuta tana tartsatsi ta ko'ina a jikinsa.

Kallon Asad tai ganin shi kuma abun yake kallo yasa taci gaba da cewa.

"Asad wannan abunda kake gani a cikinsa dukkan muradinka yake abun nemanka yake wannan shine asirin su a cikinsa suke gudanar da komai daga waje zaka iya yimasa kallon karamin abu Amma idan ka shiga ciki zakai mamakin irin tabkekiyar duniyar da zakaga ka fada domin dajine na siddabaru Mai zaman kanshi sun tare komai a ciki Asad zaka zama Bgs a gaba in Allah yaso kuma ni zan kasance tare dakai zan taimaka maka ka cika burinka Ina so zan koma gida na barka lafiya".

Asad bai iya cewa komai ba sai binta da kallo yake tana gama fad'in haka ta juya ta fara tafiya dakatar da ita yai da cewa.

"Mene sunan ki"😜?.

TO ABUN YAZO INJI MAI FADAR AUREN SHI😂 ASAD KAI DA KACE IDAN TA SAKE ZUWA MAKA CIKIN MAFARKI SAIKA KASHETA🙊 YANXU KUMA YADA TAMBAYAR SUNANTA🤔 KODAI LOKACI GUDA KISAN YA KOMA UMMMMMM😃 BARI NAYI SHIRU🤐 KAWAI AIKO BAZAMU FAD'A MAKA SUNAN NAN NATA BA😕 .

Juyowa tai tana murmushi ta kalleshi tana cewa "kayi mamakin ya akai nasan sunanka ko gashi kai bakasan nawa ba kuma baka ta'ba gani naba? haka ne ni sunana Hau.........................

Bata qarasa fad'a masa ba kamar daga sama yaji ana jijjiga shi ana Kiran "Asad kai Asad ka tashi dallacan rana tayi fa sosai dan Allah ka tashi da uban waye ya hana kayi barcin da wuri sai gari ya waye sanda ake bukatarka kai kuma sannan xaka tsiri barci banza ka tashi nace" Ajeeb ya karasa maganar yana sake jijjigashi sosai bud'e idonsa yai bai saukesu akan kowa ba sai Ajeeb yana tsaye a kansa innalillahi bata fad'a masa sunanta ba dama a mafarki yaga wannan a tunaninsa azahiri ne gashi wannan d'an iskan Ajeeb d'in yazo ya katse masa baiji sunanta ba wani irin takaici ne ya kamashi baisan lokacin dayasa hannu ya fisgo Ajeeb d'in ba shima Ajeeb d'in bai farga ba sai jinsa yai ya fad'a saman gado wani irin duka Asad ya sakar masa a baya muryarsa da har lokacin bata fita daga muryoyin masu barci ba yace.

"Which rubbish is this Ajeeb wanne irin wulakanci ne wannan kake nuna min taya za'ai kazo kawai ka kama tashi na nasa kane"?.

Wata uwar harara Ajeeb ya sakar masa yana tashi zaune yace "danai maka uban me dama saika sani dana tasheka kai ka isa kaban umarni uwar me nayi maka yanzu ka fisgeni dan mugunta kana neman karya min kafad'a"?.

Tsaki Asad yai yana mi'kewa ya sauka akan gadon yai hanyar toilet yana cewa "dakai min ban sani uban mezanyi maka da kazo kana tashi na dama na dawo gida ne danka hanani sukuni".

tashi zaune Ajeeb yai yana cewa "ai wallahi indai irin wannan barcin zaka ri'ka yi baka isa na kyaleka ba kaji dakyau".

Asad bai sake kulashi ba sakamakon yana toilet amma a ranta yana tunanin gara ya shirya ya koma Marshall islands zaifi masa kwanciyar hankali idan yaci gaba da zama anan zai 'bata biyu dan Ajeeb bazai barshi yai abun arziki zai hanashi yin abinda ya kawoshi gidan sannan can ya baro aikinsa wanka yayo ya fito har lokacin Ajeeb yana zaune a bakin gado ya d'ora kafa d'aya kan d'aya yana duba wayarsa bai kulashi ba ya fara shiri saidai abunda ya'ki fita daga zuciyarsa shine wannan mamakantaccen mafarki da yayi wai wacece ne wannan yarinyar a ina zai sameta ko ba mutum bace saidai aljana taya ita zata san 'kungiyar bayan jajurtattun soldiers ma sun gagara gashi zata fad'a masa sunanta wannan banzan Ajeeb d'in ya wani zo ya tashe shi tsaki yaja da qarfi Wanda baisan ma yayi Shiba tsabar takaici d'agowa Ajeeb yai yana cewa.

"Malam kafa ishe ni da tsakin nan zaka iya rufe baki ka gane tsaka🦎 ma datai Allah ya tsine mata balle kai mutum"?.

Ko inda yake Asad bai kalla ba Saida ya gama shiri yana sa Kaya da komai sannan yadau phone d'insa yana yin hanyar fita mi'kewa Ajeeb yai shima suka fito tare saidai ganin baiyi hanyar zuwa gurin mai martaba ba ko gurin Mami yasa Ajeeb yace masa.

"Asad Ina zuwa"?.

"Inda ka aikeni Abba" yana fad'in haka yai gaba dakatawa Ajeeb yai yana jinjina kai daidai su Ameer sun karaso Annur yace "yadai lafiya"? Kai Ajeeb ya girgiza yana murmushi yace "ba komai nida d'anye gidanmu ne Asad yaron can sam bashi da hankali dole sai inai masa uziru muje idan wurin Abba zakuje"? Kai Ameer ya d'aga "eh zamu je d'in ma amma yanxu saimun je part d'in Sultana Umma Hadizah mun duba jikin Khimiyyah kafin muje can".

Kai Ajeeb ya d'aga "ok muje dama Nima yau banje

Please Login or Register in order to submit comment