Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kuke dibawa jikin ku zata tambaye ku sai lokacin tsufa" fuskar Aisha cike da damuwa tace "to ya zanyi Amatu rashi ne yasa nasan da baban mu nada shi duk haka bazata faru ba" sauke ajiyar zuciya Amatu tai tare da jinjina kai tace "haka ne amma dan Allah a rika ragewa aikin na yawa" dariya Aisha tai tana cewa "shikenan babbar aunty za a kiyaye kaka mai kamar uwa hajiya Hauwa's mai zamani" dariya sukai Amatu na mata hararar wasa tace "meye na Kiran suna na haka babu ko dan kara"? Har lokacin fuskar Aisha da fara'a tace " kakar mu na tuno duk da bamu Santa ba Allah sarki hajiya Hauwa naji mutuwar 'yar tsohuwar nan" maida hankalin ta kan littafi Amatu tai tana cewa "to ta zamuyi wanda ya fimu sonta ne ya karbeta duk wata kulawa da kauna da zamu gwada mata bayan nasa ne shike iko da kowa" sauke ajiyar zuciya Aisha tai tana kallon Saude data fito a d'aki tana mata kallon mamaki na ke kuma yaushe kika shigo mikewa tai tare da nufar ta yayin da Jamila ma ta mike tana daukar kayan miyar ta tafi gidan ni'ka.

Shiru Amatu tai tana kallon kowa da komai gida babban gida amma yanayin tsarinsa da gyara gashi babanta nada dangi amma duk laifinsa suke gani wai ya zauna kara zube ba sana'a yasa rashin zuciya gashi ya tara iyalai shiru tai ta nutsa cikin tunani lokacin da baban ta yaje gurin yayansa ya bashi kud'i zai biya mata ta zana jarrabawa ya hana dan rufe ido tai maganganun da kawu Ilyah ya fad'awa babanta na mata yawo a kunne daga lokacin data tambayi kudin jarrabawar.

Cikin mamaki shigowar malam habu ganin Amatu zaune tana kuka yasa ya karaso da sauri yana d'ago ta tare da goge mata hawaye cikin lallahi yace "Mamana kukan me kike ba na raka ki har makaranta ba meyasa kika dawo" Amatu na shashshekar kuka tace "baba wai malamin yace ban bada kud'i ba wannan shekarar ma bazan zana jarrabawa ba saidai na jira yan ajin baya" dafe kai malam Habu yai yana kallonta yace "kiyi hakuri Mamana kinji taho taso muje gurin yaya kila yau tunda yaga dake yaji tausayin na ko aro ya bani kudin nan na biya miki" rike hannunta yai suna fita daga gidan suka shiga dayan daya kasance gidan yayansa da sallama ya samu matansa zaune suna gyaran kaji gefe ga yara can suna ta fama da kan saniyar da sukai dafgensa abu yaji ya tsirga masa mai d'aci amma ya daure bayan sun gaisa yace "ko yaya na nan"? Da'kyar suka bashi amsa a wulakance ganin ko shi yayan nasa Ilyah yadda yake masa kenan yana tutture shi babbar matar ce ta budi baki tace "eh kamar dai yana ciki karasa ka duba".

"Karasa ka duba"? Malam Habu ya tambaya cikin mamaki yana juyowa ya kalleta a gadarance tace "eh haka nace ko kana tunanin muna aiki akwai wanda zai tashi maka wahala bayan kai kazo nema" ran malam Habu a 'bace yace "Bara'atu kinsan abinda kike fada kuwa" wani kallo tai masa tana cewa "ni nasan abinda nake cewa domin ni a hayyaci na nake ina ci ina sha banda matsalar komai saidai azo inuwa ta a ra'bu a fake kai kuwa fa tun karayar arziki ta same ka kullum kana yawon maula a gidan kamar duk kauyen nan mune muka fi kowa arzik..................


"BARA'ATU!!!😑 Malam Habu ya fad'a cikin tsawa wanda hatta yaran dake zaune gefe suna cin nama saida suka tsorata nuna ta yake da yatsa idonsa yai ja na bacin rai yace "Bara'atu ki iya bakin ki a kaina wadatar da mijin ki yake dashi baki isa kice zaki wulakanta niba domin uban mu daya dashi baki San wahalar saba kawai kin ganshi a saurayin sa kika aure shi kuma shine kike neman zagi na"? Tabe baki tai tana cewa "eh ai isa nai" malam Habu zai magana suka jiyo muryar Ilyah na cewa "ke Bara'atu ke dawaye ne anan nake jin hayaniya haka"? Mikewa tai tana shiga d'akin sa ta dade kafin ta fito tana sake wuce su ta shiga wani wuri da alama dakin ajiyar abinci ne sai gata ta fito da daurin leda tana cewa "dama maula ce abinda ya kawo ku shi kanshi ya fahimta gashi nan garin kwaki ne yace a baka koda gishi kwa tsama kuci" ta karasa maganar tana aje masa a gaban sa kafin ta koma ta zauna.

Cikin fushi malam Habu yai bol da wannan ledar garin ya tarwatse yana huci yace "ai dama d'an talaka bai iya samun waje ba wato ke harkin manta irin ke wahalar da kika sha a gidan ku yanzu kin samu guri har kike gorantawa wani meye a gidan naku wacce tsiyar ce fad'a min" mikewa Bara'atu tai ta fara masifa ta zazzaga bala'i irir iri wanda yasa sauran yan matan gidan fitowa da sauri Nafisa ta karaso tana cewa "wanne d'an hauren ne ya ta'bo ki umma? Gaskiya mu mun gaji da wannan maula da ake zuwa mana hakan ma bai isa sai anyi cin mutunci to wallahi bazamu dauka ba"..............


Tana rufe baki taji saukar zazzafan mari a fuskar ta Wanda yasa ta fasa Kara tana durkusawa a gurin ta fashe da kuka da sauri Ilyah ya fito wanda duk abinda ake da yana ji bai fito sai yanzu da aka mari yar lelensa cikin fad'a ya soma magana.

"Wai Habubakar wanne irin wulakanci ne wannan ka zagi mata ta ka goranta mata ka shigo gidana kai tsaye ba neman izni na duk hakan bai ishe kaba saika marar mun 'ya to yanzu kam ya isa haka na gode zaka iya tafiya ba an baka abinda kazo nema ba" a fusace malam Habu yace "yaya Ilyah yau ni kake fad'awa haka a gaban matan ka da 'ya'yan ka nagode kuma ka nuna min iya matsayi na" jan hannun Amatu yai suka fita yana fita Bara'atu taja tsaki tana cewa "wallahi ko kadan bakai sa'ar dan uwa ba haba inaga da baka fito ba saidai a debi gawata yadda ya zuciya ya hauro dinnan tsaki Ilyah yaja yana huci yace "ni na rasa me yake damun sa saikace nine dora masa talaucin duk yabi ya addabe ni tunda karayar arziki ta same shi ya hana naji dad'i amma zanyi maganinsa kodan yanzu ma alhamdulillah nasan shi da zuciya watakila bazai sake zuwa gidan nan ba ni kuwa haka nake so kuyi sauri ku gyara kajin nan a dafa su in anjima zanyi manya baki wanda nake sarar kaya a hannun yan kauyukan nan nake sarar musu daga binni zasu zo dan Allah ku tsara abincin nan sosai" ya karasa maganar yana komawa d'aki ta tafar sauke Habiba amaryar Ilyah batace saidai tana mamakin bakin hali irin na Ilyah ace kana da wadata d'an uwanka baida shi Amma saidai ka wadata bare ka barshi yana yarfe gumi yana aunar abinci a shago da kasuwanni Allah ya sauwake ta fad'a a ranta tanajin takaici da nadamar aurensa haka Nafisa ta share fuskar yatsunsa kuwa d'as a fuskarta sun fito hakan yasa ta dau alkawarin daukar fansan.

Malam Habu na fita daga gidan Ilyah yai nufin zuwa gidan dayan yayan nasa Sabi'u yai sa'a kuwa ya same shi a kofar gidan sa zaune mutane sun kewaye shi irin masu neman na kayan miyar nan ganinsa cikin jama'a yasa bayan yayi sallama sun gaisa ya nemi su d'an ke'be can nisa da mutane suka tafi karkashin wata bishiyan kuka malam Habu yasan da kamar wuya amma zai gwada kokarinsa yana fatan yakai nasara "ina jinka Habubakar ya akai ne na ganka duk a hargitse"?.

Ran malam Habu a bace yace "yanzu tsakani da Allah yaya abinda matar yaya Ilyah tai min tayi daidai yanzu shi daya goya mata baya bayan yanajin irin cin fuskar datai min ya kyauta min kenan ya kyautawa Bappan mu"?.

"Meya faru ne Habu meya hada ku me kaje yi gidan"?.

A hankali cikin nutsuwa malam Habu yai masa bayanin komai kai Sabi'u ya jinjina yana cewa "ai indai Bara'atu zatai yafi haka ba kirki gareta ba ta maganar kane dan talaka bai iya samun waje ba amma babu komai karka damu za'a biya mana ina maman namu take nawa ne kudin ai na fad'a maka duk wata matsalar ka idan ta tashi ka rika zuwa kana fad'a min ka kyale Ilyah indai ba harkar zumunci bane yanzu ka wannan maza da sauri kaje ka biya mata" karba malam Habu yai cikin jin dad'i da kaunar yayan nasa Wanda yake share masa kuka a duk sanda ya kawo korafin sa bai ta'ba nuna gajiwa ba ya mike yana sake masa godiya da fatan alkairi kafin yaje ya rike hannun Amatu suka wuce da kwarin gwiwa ya mayar da it's makarantar ya biya mata komai sannan ya shiga cikin gari dayake makarantar ba a garinsu take ba kusa da kauyen sune saida aka tashi ya biya ya dauketa suka tafi gida.

Sauke ajiyar zuciya Amatu tai tare share hawayen fuskarta bayan ta dawo daga tunanin da take ta sani mahaifin ta mutum ne na 'kwarai mai kyawawan halaye sannan ya na son farantawa ahlin sa amma babu ta gama mamaye shi sauke kanta kasa tai ganin Binta ta zo wuce wa dan kada taga cewa kuka take, Amma me tuni ta hango ta tun daga nesa Saida tazo saitin ta tace "Amatullahi me akai miki kike kuka"? Jin tambayar datai mata yasa wasu sabbin hawayen sake gangarowa da sauri tasa hannu ta goge bude baki tai kamar zatai magana ganin Bintan na tsaye a kanta tana jiran amsa sai kuma ta kasa cewa komai a karo na biyu Binta tace "mamar gida tambayan ki fa nake me akai miki kike kuka"?.

Kai Amatu ke girgizawa da'kyar tace "umma shin bazan iya taimakon baba ba"? Da mamaki Binta tace "kamar ya"? Cigaba Amatu tai da cewa "umma zan koma gurin su Abba Bashir 'kanin ki na fara kasuwanci domin na taimaki baba wannan damuwar dake damunsa na gaji da gani bazan iya ba a iyasani na mahaifi na mutum ne me annurin fuska amma yanzu koda yaushe baya ciki walwala ki tuna yadda ya ri'ka kula dani ya taso dani a cikin gata ya bani komai da nake bukata a rayuwa idan na zuba ido yaci gaba da zama a haka na yaudari kaina na cuci kaina bazan iya yafewa kaina ba umma ina bukatar taimako" ta karasa maganar cikin kuka sosai wanda ke fitowa daga asalin ainishin cikin Zuciyar ta".

"Kinga mamar masu gida kiyi hakuri haka kinji karki jawo hankalin mutan gidan a kanmu" rufe bakin umma keda wuya caraf sukaji A'i na cewa "aikin banza kenan rigar bayan salla meyi ake cewa tai shiru kar muji za'a boye mana ko saurayi tayi ko kuma wani laifin tai ba'a so mu sani iye a fad'a min domin idan baku fad'a ba kun barni cikin zulumi" juyawa Binta tai tana kallon A'i dake wanke kwanuka batare datai magana ba tace "Amatu tashi ki koma kinji ina zuwa" mikewa Amatu tai tana shiga kamar yadda umman ta umarce ta.

Tabe baki A'i tai tana cewa "oh ni Indo yanzu Binta abin har yakai ga haka kin fara hurewa yarki kunne dan ta raina ni ina matsayin matar ubanta saboda kina kishi dani".

Kallon ta sosai Binta keyi cikin mamaki wato ta fahimci A'i ba 'yar neman zaman lafiya bace wa ya sako da ita har zata dauka..........

Katse mata tunani A'i tai "dake fa nake Binta"? Wani kallon umma ta kuma aika mata dashi batare datai magana ta wuce uzurinta dariya A'i tai tana cewa "ahahaha hayye kai ni yar gidan baba gaskiya akwai tantirai a gidan malam Habu gashi kuwa sun fara bayyana Allah ya tonu asirin su suna shirye shiryen zuwa gurin boka to naji ku sai ku sake shiri ku taka a sannu idan ba haka ba yanzun nan na garzaya na sanar da mai gari" ko kula iskar ta umma batai ba balle tasa ran ta mayar da ita mutum kawai aikin gabanta take.

πŸ₯€πŸŒ»MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘 MAI TAMBARIN YMA DUTSE 🏞️''YAR MUSA JIKAR ABUBAKAR MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY πŸ’ƒ.

Mrs Al'ameen Ahmad ce mai tambarin yma dutse sabuwar duniya 🌍new world new life 🌌 and new style πŸ‘Œ.

🌹 Yusrah Musa Abubakar ta kowa ce kuma ni I have no girman kai if you are fushi dani tofa you are just 'batawa kan k lokaci πŸ•.

Manzon Allah mai Makkah mai birni da 'kauyuka.

A gaskiya naji dad'in comments dinku yan uwa matukar jin dad'i da yadda kuka gwada kauna ga littafin nan hakan da kukai ya faranta min kuma na sake samun sabon confident na gwarin gwiwa daga gare ku kuma albishirn ku insha Allah zan dage kamar yadda kuka bukata naga kullum nayi muku posting koda kadan ne ngd da yabawaπŸ’–πŸ’•πŸ‘.

Wannan page din naku ne yan uwa ina matukar kaunar ku soyayya ta a gare ku bata kwatantuwa hasashe bazai ta'ba iya hangowa ba Allah ya bar mu tare.
Ibrahim Musa Abubakar
Ummi Musa Abubakar
Salim Musa Abubakar
Yusrah Musa Abubakar
Naja'at Musa Abubakar
Fatima Musa abubakar
Aishat Musa Abubakar
Abubakar Musa Abubakar
Abdullah Musa Abubakar.
Banda kamar ku duk fadain duniya ku nake kallo naji dad'i kune jini na kune dangi na kune ahli na kune abun faharin na.

To 'yan uwa mu tsaya mu kwana anan sai mai duka ya kaimu gobe ya bamu aron rai da lafiya zanyi muku.

Think before you do 🚨
Be good be kind people will like u.

YUSRAHMS
Mrs Al'ameen Ahmad maman little Zaran aunty 😘😘😘.

πŸ‘Œ Till we meet.


TYPING πŸ“² Thu 9:48AM Feb may Allah open the door of success for all of u.

πŸ’ŽME KAMAR SARKI πŸ’Ž

πŸ’« ANNURI WRITER'S ASSOCIATION πŸ’«.

HOME OF HOSPITALITY AND HARMONY GIDAN KARBAR MUTANE HANNU BIYU DA ZAMAN LAFIYA ANNURI HASKE LEKA GIDAN KOWA KODA MAKIYA NA KALLON KA RAMIN KURA SAI'YA'YAN TA. TAKEN MU KENAN.

Dedicated to
MR HAUSA EBOOKS πŸ“š
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ““πŸ““πŸ““πŸ““
SHURAIHU USMAN CEO FAUNDER OF TASKAR NOVELSπŸ“šβœοΈ.

WHAT'S APP NO: 234 8160983083
Chat with me at always banda kira idan kasan kai na miji ne only female kawai πŸ’πŸ’š.


✍️ Yusrah Musa Abubakar story and written dedicated to my mum mama na ta kaina Allah ya kara girman matsayi ya kiyaye min ke mama na Amin πŸ‘.

05~ AS-SALAM
The source of peace and safety.
06~ AL-MUMINU
The guarantor.

Manzon Allah saw
Ya mai nasiha ga alumma muso juna mu rike gaskiya amana dan gudun kuna mu raya zuminci hanya ne na aljannah makiyin zumunci baya kusanci ceto ba.

4-Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Shahidina.


Wa alam anan nasra ma'as sabriπŸ˜” wa annal faraja ma'al karbi😒 wa anna ma'al usri yusrahπŸ€—πŸŒΉπŸŒΉπŸŒΉ.

πŸ—£οΈπŸ—£οΈπŸ—£οΈπŸ‘AYI HAKURI IDAN AN SAMU TYPING πŸ“² ERROR🚨 MATSALAR KEYBOARD NEπŸ€“.

πŸŒ„ EMPIRE ND RESEMBLANCE πŸŒ„
Episode 05 & 06
Babbar masarauta ce wacce ta shahara mai cike da dunbun tarihi da kafaffiyar daula da jajurtattun sarakuna wadanda sukai zamanin nika kuma har yanzu ake mulkin ta kamar da masarautar nada girma da tsari wanda bayan emire Aliyuddeen Abdulmalik mai mulkin ta ya kwanta dama sai babban d'ansa alhassan Aliyuddeen Abdulmalik yahau kuma ya jajirce kamar mahaifin sa har izuwa yau.

Emire Alhassan Sun kasance 'yan biyu ne shida d'an uwansa Alhussain kamar su daya sak ba'a bambance su kamar ma harta baci kuma da suka tashi haihuwa kowa Allah yake arzuta shi da 'yan biyu kuma masu kama daya saidai mai martaba Alhassan nasa dukka maza ne matansa biyu Princess Hauwa da princess Fatima suka haife su rana daya abin al'ajabi d'aya ta haihu da safe daya da dare farin ciki a wannan rana baya musaltuwa kuma abin sha'awa ya sanya musu sunan mahaifin sa marigayi Aliyuddeen duk su hudun sunan su Aliyu Aliyu an dauki lokaci mai tsawo a masarautar ana bikin murnar haihuwar su 'kasashe daban daban yanki iri iri anzo domin karrama Emire Alhassan da iyalan sa sai hussain shi kuma nasa 'yan mata su ma hudu 'yan biyu suna rayuwa ne cikin mulki daula da sarauta ga ilmi saima ka gansu kyawawa zarata masu kwarjini da aji.

Kuna ina ku fito ku kashe 'kaikayin idanuwan ku Kai tsaye ya kamata mu leka mu ganewa idanuwan mu abin yake faruwa cikin wannan kasaitacciyar masarautaπŸ’πŸ‘‘.

Zaune suke a wani irin kyakkyawan siritaccen 'kayataccen parlor suna da yawa samari da yan mata kyawawa farare tarr jawur dasu sun gaji da kyau ta ko'ina sun hadu saidai ko tari babu a parlon kamar masu zaman makoki sunkai kusan minti talatin a haka kafin a samarin daya ya d'ago yana kallon na kusa dashi dake ta aiki cikin laptop yana cewa.

"Ajeeb wai ina Asad ne tun shigowar mu banga yazo ba lafiya dai"? Batare daya d'ago ba yace "gaskiya ban sani ba domin nikam tun asuba muka rabu dashi a masallaci maybe yana part dinsa ko kuma gurin su Mami" ya karasa maganar tare da dagowa ya kallo yan matan yana cewa "ga Khimiyyah ma ban ganta ba uwar shashanci ai dama halin su daya da Asad din" dariya Ameer yai dan kowa a masarautar yasan jinin su baizo daya ba har bayi idan ka tambaya zasu ce maka haka.

'Daukan waya Shaukiyyah tai zatai Kira da sauri Khaldiyyah dake gefen ta tace "ke me zakiyi"? Kai tsaye tace "oh Asad zan kira naji inda yake"? Zaro ido Shaukiyyah tai da mamaki tace "ki kira shifa kikace? kin manta laifin da kikai masa jiya kenan zai miki dukan mutuwa Mami ta hana shi shine kuma yanzu kanki na rawa kike son taso mutuwa daga bacci ko? Allah ya taimaka mukam yan kallo ne da sannu yayin daya sauya miki halitta" ta karasa maganar tana kallon Annur wanda shi kuma hankalin sa sam baya kan maganar da suke Ameer yace "ai dakin barta taje ina tasan yana tattare da ita" shiru Shaukiyyah tai tana kallon su daya bayan daya domin ita badan sun tuno mata ba ta manta da tai masa laifi jiya.

Mikewa Ajeeb yai yana cewa "bari mu gani tsaya naje part dinsa" fita yai ya barsu duk inda ya gifta du'ka masa bayi suke cike da girmamawa tun daga nesa.
Ya nufi wata iriyar kyakkyawar kofa mai she'ki zaka iya jiyo kururuwa da ihu na mace tana kuka cikin tashin hankali da dana sanin abinda ta aikata.

Sanye yake cikin kayan sojoji kana ganinsa balarabe sak fari ne tarr kyakkyawan jarumtaccen sadauki wanda ba kamarsa a karfi kwarjini fuskarsa kamar ba'kin hadarin da yake gaf da zubar ruwa ransa a mugun 'bace idanuwansa sunyi ja kamar rana taje faduwa cikin tsananin bacin rai da tsantsan fushi yake kallon fuskarta da saitin inda yatsunsa suka fito da 'karfin gaske cikin taku yake yin wajen inda take kwance ganin ya kuma nufota kamar zakin daya hango nama yasa a zauce ta yunkura cikin dimuwa da gigita tana neman hanyar tsira daga hannun sa wani irin dan'ko gashin kanta yai yana jawo ta baya tare da wurgi da ita ta bugi jikin wasu kafaffun karafina tayo kasa ji kake tim ihu ta zunduma tana dafe kanta saiga jini ta hanci yana malala ko a jikinsa ya sake dan'ko wuyanta yana mikar da ita tsaye ya kuma sharara mata wani marin daidai Ajeeb ya bud'e kofar katafaren gate din part din yaga abinda ke faruwa da mugun gudu ya karaso yana cewa.

"Kai ASAD🦁 are you out of your sense baka da hankali ne ka sake mata wuya saika kashe ta mitai maka? ka bari fa nace ka sake ta" ko inda yake bai kalla ba balle yasan wai mutum ne ke masa magana sai kara matse wuyan nata da yake idanuwan ta duk sun fito waje sunyi jawur jini kuwa sai ambaliya yake ta hanci da baki ganin da Ajeeb yai idan ya zuba masa ido zai kasheta yasa da karfi ya soma kokawar kwaceta muryar Asad da tsananin fushi yace "AJEEB let's not get into this😠😑" shima Ajeeb cikin fushi yace "I won't spare you bazan 'kyale ka kashe ta ba wallahi ka saketa nace" a banza Ajeeb yake magana domin ko sauraron sa Asad baiyi ba kokarin kwatar ta Ajeeb keyi amma maimakon yai nasara sai ya jawo Asad din ya sake mata mugun rikon daya fi nada a susuce Ajeeb ya zaro pistol 'karamar bindiga dake aljihun wandon Asad ya harbeshi a hannu ko zai sake ta tuni jini ya wanke hannun amma tsabar tsaurin rai Asad bai sakar mata wuya ba "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda Ajeeb yake maimaitawa kenan cikin azama a guje ya fita ya nufi sashin mahaifansu dan yasan banda su ba wanda ya isa ya dakatar da Asad daga yunkurin kashe Kimiyyah duk bayin dake aiki a part din Asad kuwa kowa ya shiga taitayinsa sun rasa abinda yake musu dad'i tsoro ya hana suje su fad'a yanzu kuma sun san dole a hukunta su akan haka.

Dukkan ahlin gidan a gigice suka shigo domin mai martaba ko takalmi babu a kafarsa tsabar tashin hankali Mami dake gaba ganin halin da Kimiyyah ta shiga na rai ko mutuwa yasa da gudu taje tana kasarawa ta wanka masa mari sau biyu tare da fashewa da kuka tana rike hannunsa dake wuyan Kimiyyah tace "Asad ba ita ya kamata ka kashe ba nice ka saketa Asad ka rike nawa wuyan innalillahi wa inna ilaihi raji'un Asad ka sake mata wuya kada ka kashe yarinyar nan bazan yafe maka idan ka zama silar mutuwarta" ta karasa maganar tana sake jan hannun sa da karfi jin kukan da take da abinda tace yasa Asad sakin wuyan Kimiyyah tilas ba hakura ba hannunsa na tsiyayar jini inda Ajeeb ya harbeshi da bindiga Kimiyyah kam yana sake mata wuya ta 'kame tare da zunduma uban ihun tsananin azaba kafin ta yanke jiki ta fad'i kasa da sauri sukai kanta yayin da Mami ta fad'a jikin Asad tana kuka sosai.

Gaba daya jikin 'yan gurin rawa yake an rasa mai kwarin gwiwar cewa komai sai salati da ake ganin yadda Kimiyyah ke wata iriyar mi'kar tana sankarewa irin na mai 'ka'karin mutuwa hankali tashe Ajeeb yace "Abba muje asibiti dan Allah karta mutu" kasa magana mai martaba yai sai mikewa kawai dayai ya bar gurin da sauri Ajeeb da Ameer suka dauketa suna fita sauran suka bi bayan su har lokacin Mami bata daina kuka ba ta kasa shiru ga jikin ta sai rawa yake kamar maijin sanyi ko mai zazzabi da'kyar ta d'ago tana kallon fuskar jarumin d'an nata da har lokacin yana cikin mood altering ganin jini duk ya bata mata jiki yasa ta kalli hannun sa zaro ido tai ganin harbi da sauri tasa hannu cikin aljihunsa ta dauko wani d'an karamin towel fari ta daure masa hannu gabadaya ta kasa nutsuwa kuma tasan ba magana zaiyi ba amma dai tace "Asad mai Kimiyyah tai maka kake kokarin kashe ta meya kawota part dinka ya naga harbi a hannunka"? Shiru yai kamar kurma kuma dama haka take tunani rike hannunta yai yana fita da ita saida ya mayarta har part dinta kafin ya dawo ya cire bullet din hannunsa ya nad'e hannu yana tattare kayayyakin daya tarwatsa domin tun daga parlor ya soma dukanta har harabar part dinsa Saida ya gama sannan ya mike yana shiga bedroom ya cire kayan jikinsa ya shigo toilet saboda sanin irin zafin Zuciyar sa yasa ba mace ko daya da take aiki a part dinsa mazan ma sai taka tsantsan suke.


Ruwa mai matukar sanyi yake kwararawa jikinsa idanuwan sa a rufe hannunsa nakan kyakkyawan pink lips dinsa ya ma rasa mai tazo yi part dinsa uban waye ya turo ta mai take nema har ta samu damar shiga d'akin sirrin sa tai amfani da na'urarsa ta tura sako ta goge masa abubawa masu mahimmanci wanda yadau tsawon shekaru yana tarawa yau daya tasa yayi losing dinsu duka bude idonsa da har lokacin babu fari ko kadan yai tare da furzar da zazzafar iska ya dunkule hannunsa ya kaiwa mirron toilet din naushi take ya tarwatse ko'ina numfashi ya sauke cikin zafin Zuciya bad temper yafi awa biyu yana tsaye shower 🚿 na zubar ruwa a kansa kafin ya daura towel ya fita zama kawai yai gaban mirror yana zubawa had'ddiyar kyakkyawar fuskarsa ido mikewa yai a gurin yana

Please Login or Register in order to submit comment